1- Ku ribaci damar shekaru da
rayuwa, kuma ku gabatar da ayyukan da suka fi tsarki domin kanku, kada ku rika
jinkirta aiki, domin cikin hakan akwai hana rai aikin kwarai, sai ku ribaci
rayuwarku gabanin mutuwa, da faragarku gabanin shagaltuwa da ayyuka, da
wadacinku gabanin talauci, da samartaka gabanin tsufa, da lafiya gabanin cuta.
2- Shekara
ta kare, an rufe ayyukanta, an nade takardunta, madalla da Mutumin da ya ribaci
damarsa, ya mori lokacinsa, ya gyara ayyukansa.
3- Lokatan
rayuwa dama ne na yin aiki, kuma ni'ima ne da suke hukunta godiya, "Idan
za ku nemi kididdige ni'imomin Allah ba za ku iya lissafa su ba" [Ibrahim:
34]. Kuma lokaci yana wucewa, rayuwar kadan ce, ayyukan wajibai wani akan wani,
hakkoki kuma suna dayawa, don haka; babu damar wargi da wasa, kuma babu lokacin
hutawa da sakaci.
4- Ku ji tsoron Allah Ta'alah, kuma ku rigayi shekarunku da ayyukanku,
kuma ku tabbatar da zantukanku da ayyukanku; domin hakikanin rayuwar Mutum ita
ce abinda ya tafiyar da ita a cikin biyayyar Allah, kuma "Mai
hankali shine wanda ya yi ma kansa hisabi, kuma ya yi aiki domin abinda ke tafe
bayan mutuwa. Gajiyayye kuma shine wanda ya bi son ransa, sai kuma yake kwallafa
wa Allah buri".
5- Lallai
zalunci –Ya ku Musulmai- haramun ne a dukkan watanni, saidai Allah ya
girmama alfarmar watanni hudu masu alfarma, sai ya sanya aikata zunubi a
cikinsu yafi girma, kuma aiki na kwarai da lada a cikin watannin shima yafi
girma.
6- A cikin Sahihu Muslim, lallai Annabi –SAW- ya
ce: "Azumtar yinin Arafah, ina zata wa Allah cewa zai
kankare shekarar da take gabaninsa da wanda take a bayansa. Azumtar yinin
Ashurah kuma, ina zata wa Allah cewa zai kankare shekarar da take a gabaninsa".
No comments:
Post a Comment