HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 18/Muharram/1440H
daidai da 28/Satumba/ 2018M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ABDULBARIY BN AWWADH AL-SUBAITIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
KA CE: LALLAI SALLATA
قل إنّ صلاتي
Shehin Malami wato:
Abdulbariy bn Awwadh Al-Subaitiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai
taken:
KA
CE: LALLAI SALLATA,
Wanda kuma
a cikinta ya tattauna, akan abinda ke tafe, Ya ce:
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Godiya ta tabbata ga
Allah wanda ya karrama jinsin Mutum; sai ya sanya shi ya zama khalifa a bayan
kasa, ina yin yabo a gare shi Subhanahu kuma ina gode masa, akan ni'imar imani
da falala.
Kuma ina shaidawa babu
abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya,
wanda yin bauta a gare shi itace manufar samar da halitta.
Kuma ina shaidawa lallai
shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa, ya tsawatar daga
dabi'ar zage-zage da munanan halaye.
Allah yay i Karin salati
a gare shi, da kuma iyalanSa da sahabbanSa, ma'abuta kyawawan zukata.
Bayan haka:
Ina yin wasici a gare ku
da ni kaina da takawar Allah, Allah Ta'alah yana cewa:
"Ka ce:
lallai ne sallata, da yankena-yankena, da rayuwata, da mutuwata, na Allah ne
Ubangijin talikai * bashi da abokin tarayya, kuma da aikata hakan aka umurce
ni, kuma ni ne farkon masu sallamawa", [An'am: 162-163].
Wannan aya mai karamci,
ta zana hadafi da aiki da manufar wannan rayuwa, wanda kuma shine kasancewar
Musulmi, da rayuwarsa da mutuwarsa, na Allah ne Ubangijin talikai, na Allah ne
Mamallakin ranar sakamako, wanda ya halitta mu, kuma yake azurta mu, kuma ya bamu kyautar wannan rayuwar.
Tilawar wannan ayar, da
yin fadakarwa akanta, da yin tunani a cikin ma'anarta, yana rayar da fahimtoci
masu girma, kuma yana jaddada ma'anoni masu tsada, wadanda ya wajaba kada su
buya, ko su yi nisa ga kwakwale, ko su bace ta hanyar fadawa cikin da'irar gafala da mantuwa, wanda
kuma su ne: Ya kasance sallar Bawa, da yanke-yankensa, da rayuwarsa da
mutuwarsa ga Allah ne, kuma ya kankan-da-kai cikin dukkan sha'anoninsa ga wanda
ya halitta shi, kuma yake azurta shi, yake juya lamarinsa. Kuma Bawa a cikin
dukkan lamuransa ya fiskanci ko ya nufi fiskar Allah da ikhlasi; har ya zama
babu wani abin da Murum yake nufa idan ba Allah ba;
Kuma Mai nufin samun
yardar UbangijinSa baya yin magana sai domin UbangijinSa, baya yin wani aiki
sai domin UbangijinSa, a darensa da yininsa, da safiyarsa da maraicensa, saboda
dukkansu na Allah ne shi kadai bashi da abokin tarayya.
Ayar tana tunatarwa kan
samar da matsayi mafi daukaka, wanda shine yin bauta cikin dukkan abinda
Musulmi ke aikatawa ko ya bari; yana mai imani da Allah, yana mai tsarkake
niyya a gare shi, yana mai son Allah, yana shauki ko begensa, yana mai
tsoronsa, yana fatan samun falalarsa, yana mai cin halal, da barin cin haram,
da biyayyar iyaye, da sada zumunci, da kyautatawa makwabta, da kyautata
halayya, da runtse idanu, da sanya hijabi, da da'awa zuwa ga Allah, da umurni
da kyakkyawa, da hani ga mummuna.
Kuma idan bautar Allah ta
samu gindin zama a cikin zuciya, to sai Mutum ya 'yantu daga yin bauta ga wanin
Allah.
Fadinsa: "Ka ce:
lallai ne sallata, da yanke-yankena", [An'am: 162-163].
"قل إنّ صلاتي".
Ginshiki ne na abubuwan da
Bawa yake kusantar Ubangijinsa; Majibincinsa Mabuwayi da daukaka da shi; domi
ginshikin ibadodin da suka fi girma shine/ Yin farillan da Allah ya wajabta su
ga bayinSa.
Wanda kuma yake neman
lada mai yawa, to sai ya karfafi yin farillansa da ibadodin nafilfili da
sunnoni, kuma da aikata hakan Mutum zai samu soyayyar Allah, sai ruhinsa ta
samu daukaka, ransa kuma ta tsarkaka, Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa
sallama-: "Lallai ne Allah yana cewa: Wanda ya yi adawa da waliyyina,
hakika ina shelanta yaki da shi, Kuma
Bawana bai kusance ni da wani abu wanda yafi soyuwa a gare ni ba, fiye da
abinda na farlanta akansa…
Kuma ba zai gushe yana kusantata da nafilfili ba, har
sai na so shi, kuma idan na so shi sai in kasance jinsa da yake ji da shi, da
ganinsa wanda yake gani da shi, da hannunsa wanda yake damka da shi, da kafarsa
wanda yake tafiya da ita, kuma idan ya roke ni tabbas zan bashi, idan kuma ya
nemi tsarina to lallai ne zan tsare shi", Bukhariy ya
ruwaito.
Fadinsa: "Ka ce:
lallai ne sallata, da yanke-yankena", [An'am: 162].
"ونسكي".
Ya nuna cewa lallai yanka
domin Allah yana cikin manyan ibadodin da suka fi girma, kuma don haka ne
Allah Ta'alah ya gwama ambaton ibadar yanka tare da
sallah a cikin fadinSa: "Saboda haka, ka yi sallah ga Ubangijinka, kuma ka
soke (wato, rakumi)" [Kausar: 2].
Kuma wannan ibada ta
yanka, lallai tana da gaya da manufofi, wanda aka shar'anta a cikin kowace
shari'a; saboda Allah yana son ibadar yanka, kuma tana da yawan amfani.
Yanka domin Allah Ta'alah
yana daga cikin ginshikan imani, kuma lamari ne daga cikin lamuran da tauhidin
baya yake bayyanarwa, kuma yanka baya halatta a cikin Musulunci a gabatar da
shi, face ga Ubangijin talikai.
Kuma dabbar da aka yanka
tana zuwa a ranar Kiyama cikin fatarta da gashinta da kofatonta da dukkan
abinda ke tattare da ita, a cikin ma'aunin Bawa, idan har yankan ya kasance
domin Allah, ba domin wani abin da ba Allah ba; saboda ba a yin yanka domin
gunki, ko bishiya, ko kabari ko waliyyi, kawai ana yin yanka ne domin Allah (سبحانه وتعالى)
cikin tsarkin niyya da tauhidi.
Kuma yana daga cikin shirki
ga Allah, gabatar da ibadodi da yanke-yanken dabbobin yanka, ba domin Allah
Ta'alah ba, Aliyu –Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah –sallal
Lahu alaihi wa sallama- ya gaya min kalmomi hudu: "Allah ya
la'anci wanda ya yi yanka ga wanin Allah, Allah ya la'anci wanda ya tsine wa
iyayensa, Allah ya la'anci wanda ya bada mafaka ga mai bidi'a, Allah ya la'anci
wanda ya canza alamomin kasa", Muslim ya ruwaito
shi.
Fadinsa: "da
rayuwata, da mutuwata, na Allah ne Ubangijin talikai",
[An'am: 162].
"ومحياي ومماتي لله رب
العالمين".
Rayuwa ga Allah Ubangijin
talikai, itace rayuwa akan addininSa da shari'arSa, da umurninSa da haninSa, a
cikin dakikokinta, da bacin ranta da farin cikinta, da darenta da yininta, da
kuma dukkan abinda ke cikinta na tsayuwa da zama, da motsawa da natsuwa, da
barci da farkawa, da saye da sayarwa, da abinci da abin sha, da koyo da
koyarwa, da kwadago da aiki, dukkan wannan, da waninsa, na Allah ne Ubangijin
talikai.
Asara dukkan hasara, tana
cikin ace Musulmi ya mance da wadannan ma'anonin, ya kuma manta da UbangijinSa,
har ya wayi gari a dimauci cikin tafiyarsa, gafalalle daga hadafinsa da
manufarsa a cikin rayuwa, sai ya yi shirki wa abin bautarSa Makadaici da
UbangijinSa Mafi girma, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma kada ku kasance kamar wadanda
suka manta Allah, sai ya mantar da su kayukansu"
[Hashr: 19].
Musulmi yana
da abin bauta ne guda daya, shine Allah, Mamallakin mulki, wanda ya nufi Mutum
ya 'yantu daga dukkan ababen bauta, idan ba Allahn ba, kuma ya nufi rayuwar
Bawa ta kasance da ayyukansa da mayar da lamuransa, zuwa gare shi; ba zuwa ga
wanin Allah ba; sai ya rayu domin Allah, kuma cikin biyayyar Allah, "Kuma tsarki ya tabbata ga
Allah, a lokacin da kuke shiga maraice, da lokacin da kuke shiga safiya * kuma
godiya tasa ce, a cikin sammai da kasa, da kuma lokacin zawali"
[Rum: 16-17].
Wannan rayuwar idan muka
yi ta domin Allah, kuma daidai da ababen da suke yardar da shi, kuma muka so
abinda Allah yake so, muka ki abinda Allahn yake ki, muka rika rayar da zukata
da ambaton Allah, to lallai tabbas zata kasance rayuwa ce mai dadi da walwala,
Allah Ta'alah ya ce: "Wadanda suka yi imani, sai zukatansu suka natsu da
ambaton Allah, to lallai da ambaton Allah ne zukata ke samun natsuwa"
[Ra'ad: 28].
Wannan kuma shine halin
Musulmi a koyaushe, wato, lokaci ba zai shige alhalin yana nesa da UbangijinSa,
da zikirinSa, da bautarSa ba, don haka Musulmi yake sallah, yake azumi, yake
hajji, yake fitar da zakkar dukiyarsa, yake auna dukkan ayyukansa da ma'aunin
shari'a da imani.
Kuma rayuwa ta kan
kasance ta Allah ne Ubangijin talikai, idan aka yi amfani da lokacinta wajen
aikin ginawa da bunkasawa, da kuma yin aiki da hankali wajen rayar da Duniya,
da sana'a da noma, da gyara rayuwar al'ummai, da tabbatar da aminci da walwala,
Allah Ta'alah ya ce: "Kuma a lokacin da Ibrahimu ya ce: Ya Ubangijina!
Ka sanya wannan gari (na Makkah) amintacce, ka azurta mutanensa, daga 'ya'yan
itace, wanda ya yi imani daga cikinsu, da Allah da ranar lahira. Allah ya ce:
wanda ya kafirta ma ina jiyar da shi dadi kadan, sa'annan kuma in tilasta shi
zuwa ga azabar Wuta, kuma makomar ta munana", [Bakara: 126].
Allah ya yi mini albarka
NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI
da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai
hikima, Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina
neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani
zunubi, Ku nemi gafararSa, lallai shi Mai gafara ne Mai
rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA BIYU
Godiya ta tabbata ga
Allah Ubangijin talikai. Mai rahama mai jin-kai. Mamallakin ranar sakamako.
Kuma ina shaidawa babu
abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, abin
bautar nafarko da na karshe.
Kuma ina shaidawa lallai
shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, majibinci masu takawa.
Allah ya yi dadin salati
a gare shi da iyalansa da sahabbansa gaba daya.
Bayan haka:
Ina yin wasiyya a gare
ku, da ni da bin dokokin Allah, Allah Ta'alah ya ce: "Ya ku wadanda suka yi imani
ku ji tsoron Allah iyakar takawarsa kuma kada ku mutu face kuna Musulmai ",
[Ali-imrana: 102].
Irin wannan Musulmi wanda
ke mayar da rayuwarsa gaba dayanta ga Allah: ya kan zama kamar ruwan sama, duk
wurin da ya sauka sai ya amfanar, wato, zai rika raya kyakkyawar fata a cikin
zukata, ya rika karfafar aminta da Allah, yana yada jin-kai da tausayi a cikin
rayuwa, yana barbaza alkhairi, yana ciyar da miskinai, yana tsayuwa akan
sha'anonin raunanan Mutane da Marayu da Marasa lafiya, Allah Ta'alah ya
ce: "Kuma wanda ya rayar da wata
rai, to lallai kamar ya raya Mutane ne gaba daya",
[Ma'idah: 32].
Kuma duk wanda rayuwarsa
ta kasance domin Allah, to ba zai jira sakamako ko godiya daga wanin Allah ba,
zai cigaba da ayyukansa, ta yadda ba zai iya dakatar da shi ba; wanda ya yi
ranga-ranga ga hanya, ko ya ke musa alherinsa ko ya ki godiya a gare shi,
Kamar harshen 'dayansu
yana fadin: "suna cewa: Lallai ne mu, muna ciyar da ku ne domin newan yardar
Allah, bamu nufin samun wani sakamako daga gare ku, kuma bamu nufin godiya *
Lallai ne mu, muna tsoro daga Ubangijinmu wani yini mai gintsewa mai murtukewa
* Sai Allah ya tsare musu sharrin wannan yinin, kuma ya hada musu
annurin fiska da farin ciki * kuma ya saka musu -saboda hakurin da suka yi- da
Aljannah, da tufafin alharir", [Insan: 9-12].
Sai ku yi salati –Ya ku
bayin Allah- ga Manzon shiriya, saboda Ubangijinku ya umurce ku da aikata
hakan, a cikin littafinsa a inda y ace: "Lallai ne, Allah da
Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku
yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka
yi salati ga annabi Muhammadu da kuma iyalan annabi Muhammadu, kamar yadda ka
yi salati ga annabi Ibrahima, da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai abin godiya
ne mai girma.
Ya Allah! Ka
yi albarka ga annabi Muhammadu da iyalan annabi Muhammadu, kamar yadda ka yi albarka
ga annabi Ibrahima, da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai abin godiya ne mai
girma.
Kuma ya Allah, ka yarda
da khalifofi guda hudu masu shiryarwa, Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da
sauran sahabbai da iyalan Annabi masu karamci, ka hada mu da su da afuwarka da
baiwarka da kyautatawarka Ya mafi jin-kan masu jin-kai!
Ya Allah ka daukaka
musulunci da Musulmai