HUDUBAR MASALLACIN ANNABI صلى الله عليه وسلم
JUMA'A, 13/RAJAB/1439H
Daidai da 30/MARIS/2018M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEHI HUSAINI DAN ABDUL'AZIZ AL-AS-SHEIKH
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah; yabo mai yawa mai
dadi, mai albarka, kamar yadda Ubangijinmu ke so, kuma kamar yadda ya yarda.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya saI
Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya; a Lahira da Duniya.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma
shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa; Annabi zababbe, kuma Manzo wanda
Allah ya zabo.
Ya Allah ka yi karin salati da sallama a gare
shi, da iyalansa da sahabbansa, ma'abuta falala da takawa.
Bayan haka;
Ya ku Musulmai
Ku ji tsoron Allah, kuma ku masa da'a; domin
idan mutum ya yi da'a a gare shi, Sai ya jiyar da shi dadi, ya kuma Allah ya yardar
da shi.
Ya ku musulmai
Kyawawan halaye alamar sa'idar
bawa ne da samun nasararsa da rabautarsa, kuma ba a iya janyo alkhairi, da
abinda yafi dabi'u kyawawa, ko ayyuka managarta.
Lallai nassoshin wahayin Kur'ani da hadisai,
sun zo ta hanyoyi masu yawa (na tawaturi), kan kiran halittu zuwa ga bin hanyar
daidai, da riko da kyawawan dabi'u.
Yana daga sifofi masu girma, da kyawawan
halayen fiyayyen halittuصلى
الله عليه وسلم Abinda UbangijinSa Mabuwayi da daukaka ya
siffatanta shi da su cikin fadinSa: "Kuma lallai hakika, kai kana kan
halayen kirki masu girma" [Kalam: 4].
Kuma Annabi –صلى الله عليه وسلم- lallai ya takaice
sakon da'awarsa a cikin ka'idodinta, a inda yake cewa: "Lallai an turo ni
ne, domin na cike kyawawan halaye", Ahmad da Malik suka
ruwaito, kuma hadisi ne ingantacce a wurin ma'abuta ilimi.
Kuma Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya fada a inda
yake kira domin riko da kyawawan halaye: "Ka ji tsoron
Allah a duk inda ka kasance, kuma ka biyar da mai kyau a bayan mummuna, domin
ya goge shi, kuma ka yi mu'amalla da mutane da kyakkyawan halaye". Tirmiziy
ya ruwaito shi, kuma ya ce: hadisi ne, mai kyau ingantacce.
Kyawawan
dabi'u halayya ne da suke kusantar da bawa ga MajibincinSa, suke daukaka
darajojinsa, suke girmama ladansa, Allah Ta'alah ya ce: "Ka tunkude
cutarwa da abin da ya fi kyau, sai wanda akwai kiyayya a tsakaninka da
tsakaninsa ya zama kamar Majibinci Masoyi * Kuma babu wanda zai samu
hakan sai wadanda suka yi hakuri, kuma babu mai samun hakan face ma'abucin rabo
mai girma", [Fussilat: 34-35].
Kuma Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Mumini wanda yafi
cikar imani, shine wanda ya fi kyan hali, Kuma zababbu a cikinku sune wadanda
suka fi alkhairi ga matansu", Ahmad da Tirmiziy ya ruwaito, kuma
yace: hadisi ne hasan sahih.
Kuma
Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya
ce: "Lallai mumini da kyan halinsa yana riskar darajar mai azumi da
tsayuwar dare", Abu-dawud ya ruwaito shi, kuma Ibnu-Hibbana ya
inganta shi.
Ya
ku Muminai!
Ma'abucin tsarkin hali, zai samu martaba
madaukakiya, da matsayi mai girma, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai wanda -a cikinku- yafi soyuwa a
wurina, kuma yafi ku kusancin wurin zama daga gare ni a ranar kiyama, shine
wanda yafi ku kyan hali", Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma yace
hadisi ne hasan.
Kuma an tambayi Annabi –صلى الله عليه وسلم- akan abinda yafi
yawaita shigar da mutane Aljannah, sai ya ce: "Tsoron Allah da
kyakkyawan halayya", Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma ya ce, hadisi ne
ingantacce garibi.
Kyakkayawan halaye suna daga sabbuban samun
yardar Allah Mai rahama, da nauyaya mizani ko ma'auni, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Babu abinda yafi nauyi ga ma'aunin bawa mumini a ranar kiyama, fiye da kyawawan halaye...".
Kuma Muslim ya ruwaito, lallai Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Biyayya, itace
kyakkyawar halayya".
Ya ku,
'yan'uwana Musulmai:-
Idan kun
fahimci abinda ya gabata, to lallai, kyakkyawan hali, ya game dukkan
zantukan harshe masu kyau, da kuma ayyuka managarta; don haka; kyawawan halaye
hanya ce yardadda ga shari'a, da dabi'a, a cikin ayyuka gaba daya, da
mu'amaloli dukkansu.
Kyakkyawan
hali shine yin aiki da ladduban shari'a,
wadanda suka zo cikin nassoshin ayoyi da hadisai; na zantuka masu dadi, da
ayyuka masu kyau, da sifofi ababen yabo, da halayya madaukaka.
Kyakkayawan
hali, shine dukkan aikin da mutum zai
aikata, sai masu jituwa da shi su yawaita, masu adawa da shi su karanta, sai
kuma lamura masu wahala su saukaka, kuma da kyakkyawan hali zukatan da suka cike
da bakin ciki suke yin taushi; domin matakan ma'abuta kyakkayawan halaye, a
cikin mu'amaloli gaba daya masu kyau ne, da taushi, da kyautatawa, tare da
sifantuwa da ababe masu falala da sauran halayya na girma. Annabi –صلى الله عليه وسلم-
yace: "Kada ka raina wani abu daga kyawawan aiki, koda
kuma ka hadu da 'dan'uwanka da sakakkar fiska ne", Muslim ya ruwaito.
Kuma yana
daga cikin misalan kyawawan halaye, ba da nufin kididdige su ba; Shumfuda
fiska, da sake ta, da sanya ta cikin walwala, da yin kyauta, da kamewa daga
cutarwa, da juriyar abinda ka iya kasancewa daga mutane; na munanawa da
kura-kurai.
Kuma yana
daga cikin kyawun hali, Kame fushi, da nisantar duk abinda bashi da amfani,
da nisantar aibantawa, da husuma, da jayayya.
Kyakkyawan
hali yana nufin mutum ya kasance mai
biyayya, mai jin-kai, mai karamci da kyauta, mai sauki, mai bayarwa daga zuci
da hannu; ba marowaci ko mai mammako ba, mai hakuri da godiya, mai yarda da
juriya, mai taushi da tawali'u, mai kamewa, da rashin boyo, mai tausayi, mai
saukin hali, mai taushi cikin dabi'arsa, mai yafiya cikin mu'amalolinsa, Allah
Ta'alah ya ce: "Kada ka karkatar da kumatunka ga mutane,kuma kada ka yi
tafiya a cikin kasa kana mai nuna fadin rai", [Lukman: 18].
Kuma Annabi –صلى الله عليه وسلم-
ya ce: "Shin ba zan baku labarin wanda wuta ta
haramta a gare shi, ko ya haramta ga wutar ba, Tana haramta ne, ga dukkan mutum
mai kusanci da sauki ko taushin mu'amala", Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma yace, hadisi ne hasan garib.
Yana daga Kyan hali: Tace ko
tsaftace laffuza, da kyautata zamantakewa, da taushin mu'amala, da nisantar
wauta, da abinda bai dace ba, ko abinda bashi da kyau. Kuma ma'abucin kyan
hali, a majalisosin zama ba a kiyaye lokacin da zai aikata ko ya fadi abin
aibi, ko ya yi tuntube, ko kuskure. Abdullahi bn Abbas –رضي الله عنه-
ya ce: "Tsakaitawa da natsuwa da kyawawan dabi'u,
bangare ne daga bangarori ashirin da biyar na annabta".
Ma'abucin madaukakan halayya, (a kullum)
zaka same shi natsattse, mai hakuri, ma'abucin tsanaki da bin abu a sannu-sannu,
kamamme, madaukaki, ba mai kaushi ko tsinuwa ba, ba mai shewa ko ihu ba, ba mai
gaggawa, ko alfasha ba.
Koyaushe yana
maida mu'amalar da mutane suka masa da abinda yafi kyau, yafi falala, kuma yafi
kara kusanci da biyayya ga Allah da takawa, wanda shine abinda yafi kamantaccewa
da ababen da ake yabo, kuma suke kaiwa ga daukakar mutane.
Yana daga mafi girman nau'ukan
kyawawan halaye halin kunya, kamar yadda Ibnul-kayyim yake fada: "Kunya itace mafificinsu, wanda kuma ta fi su girman matsayi". Uwar muminai; A'ishah –رضي الله عنه-
ta ce: "Shugaban kyawawan halaye shine, Kunya".
Kuma yana daga mafifitan halayya,
wadanda suka fi kyau: Halin fifita mutane, da suturce ko boye aibinsu, da bayar
da kyauta, da yin murmushi a lokacin saduwa da mutane, da maida hankalinka ga mutumin
da ke maka zance, da bubbuda wa mutane domin su samu wurin zama, da yada
sallama da yawaita yinta, da yin musabahar hannu da mutane a lokacin ganawa, da
yin sakayya akan kyautatawar mutane da fiye da abinda suka maka, da kokarin kubutar
da rantsuwar musulmi, da kawar da kai ga abinda ba damuwarka ba, da wautar masu
wauta; cikin hakuri da hikima.
Haka suma sauran ayyukansa, za su zama
masu kyau, ta yadda zai sanya babba daga cikin musulmai ya zama kamar uba a
gare shi, karaminsu kuma kamar 'da, matsakaicinsu kuma kamar 'dan'uwa. Kamar
yadda wannan mawakin ke cewa:
Yana ganin
musulmai suna da hakkoki akansa
Kamar aikin
uba, mai tausayi da jin-kai
Ya tattara daukacin ma'anar ka'idar
halayya, wannan zance wanda ke da kankanin lafazi, yake da girman ma'ana, daga
fadinsa –صلى الله عليه وسلم-: "'Dayanku ba zai yi imani ba, face
ya so wa 'dan'uwansa abinda ke so ga kansa".
Allah ya amfanar da mu da abinda muka
sani, kuma ina fadan wannan maganar, kuma ina neman gafarar Allah wa ni da ku
da kuma sauran musulmai, daga dukkan zunubai, sai ku nemi gafararSa; lallai shi
Mai yawan gafara ne Mai jin-kai.
HUDUBA TA BIYU
Ina yin yabo ga Ubangijina kuma gode masa, ina tuba zuwa
gare shi kuma ina neman gafararSa,
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da
gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi
da abokin tarayya
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu
Muhammadu bawansa ne Manzonsa
Ya Allah ka yi dadin salati da sallama
da albarka a gare shi, da iyalansa da sahabbansa
Bayan haka:
Ya kai
musulmi, Ka kasance daga cikin ma'abuta
kyawawan halayya, wanda yake yin sabo da mutane, suma suke sabawa da shi, domin
ya zo cikin hadisin da Ahmad ya ruwaito shi daga Annabi –صلى الله عليه وسلم-,
ya ce: "Mumini akan yi sabunta da shi, kuma babu alheri
ga wanda baya sabo, ko ayi sabunta da shi".
Ya ku bayin Allah
Wajibin da ya
zama dole, shine kada muyi bautar Allah, face da abinda dalilin Kur'ani da
sunnah suka zo akansa, don haka; Duk wanda ke riya cewa watan Rajab (wanda
muke ciki) ya kebantu da wasu falaloli, ga ibadodi, to lallai babu wani abu
daga shari'a da ta zo da hakan, kamar yadda maluma muhakkikai (na-yankan shakku)
suka tabbatar, kamar Ibnu-Hajar, da Ibnu-Rajab, da Nawawiy, da Ibnu-Taimiyyah,
da 'Dar'dushiy, da wasunsu dayawa.
Sai ku yi salati da sallama, ga
Muhammadu