2018/02/01

TANADI GA MUTUWA na Huzaifiy 16 Jumadal Ula 1439 daidai da 2 Fabarairu 2018 MASALLACIN MANZON ALLAH SAW








HUDUBAR MASALLACIN ANNABI صلى الله عليه وسلم
 JUMA'A, 16/JUMADAL ULA/1439H
Daidai da 2/FEBRAIRU/2018M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEHI ALIYU DAN ABDURRAHMAN AL-HUZAIFIY







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA





YIN SHIRI GA MUTUWA
   Shehin Malami wato: Aliyu dan Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: YIN SHIRI GA MUTUWA, Wanda kuma ya tattauna a cikinta, akan mutuwa da kasancewarta makura ko gaya ga kowace halitta, kuma karshen kowani rayayye, yana mai bayyana HANYOYIN DA MUTUM ZAI BI YA SHIRYA MATA da kyawawan ayyuka, kuma mafi girma daga cikin hanyoyin shine: TABBATAR DA TAUHIDI ga Allah ta'alah, kamar yadda ya bayyana sabuban samun kyakkyawan karshe, da kuma na mummunan karshe.

بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah Rayayye Tsayayye wanda baya mutuwa, Ma'abucin mulki da iko, da buwaya, da girma;   Ina yin godiya ga Ubangijina, kuma ina yin yabo a gare shi, ina tuba zuwa gare shi, ina kuma neman gafararSa.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake; bashi da abokan tarayya, Mai tankwasa  bayinSa, Wanda yake aikata abinda ya nufa, kuma yake hukunta abinda ya so.  
Ina kuma shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu; bawanSa ne kuma ManzonSa.   
Ya Allah ka yi dadin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka annabi Muhammadu zababbe,  da iyalansa da sahabbansa wadanda suke kan mikakkiyar turba.
Bayan haka:

Ku kiyaye dokokin Allah ta'alah da takawa, ta hanyar neman yardarSa, da nisantar saba masa, saboda takawar Allah itace sababin gyaruwar halayenku a cikin rayuwarku, kuma ita ce tanadi ko shiri don fiskantar abinda yake gabanku, na ababen da kuke tsoro, ko kuke kiyayarsu. Kuma takawa ita ce garkuwa ko kariya daga ababe masu halakarwa, kuma da ita ne Allah yayi alkawarin bada Aljannoni.

Ya ku bayin Allah!
Kowani Mutum yana yin aiki a cikin wannan rayuwar don samun amfaninsa, da gyara lamuransa, da samun ababen rayuwarsa;
Daga cikin Mutane akwai wanda ke gyara addininsa, tare da gyara duniyarsa, irin wadannan sune Allah Ta'alah ya ba su abu mai kyau a gidan duniya, a gidan lahira shima ya ba su mai kyau, kuma ya kare su daga azabar wuta.
Daga cikinsu kuma, akwai wanda ke yin aiki domin duniya, sai kuma ya tozarta rabonsa a lahira, su kuma irin wadannan sune wadannan da suke jin dadi (a duniya), kuma suke ci, kamar yadda dabbobi ke ci, kuma Wuta ce mazauni a gare su.

Kuma kowace NIYYA da AIKI suna da wani lokaci da zasu kare; ba za su wuce shi ba, Allah Ta'alah yana cewa: "Kuma lallai ne, makoma (da karewar lamura) izuwa ga Ubangijinka kawai su ke!" [Najm: 42].
        Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya sanya wani aiki ga kowace Rai, kuma ya sanya wa kowace Rai niyya da nufi, ta hanyar halitta wa kowani Mutum nufi da azama; har ya zama kowace rai tana yin aikinta idan ta nufe shi, ko ta ga dama, tana kuma barin yin aiki a lokacin da taga dama.
Saidai kuma nufin Allah da ganin damansa suna sama da kowani nufi ko ganin dama, Allah Ta'alah yana cewa: "Lallai ba za ku so (aukuwar wani lamari, sai ya auku kamar yadda kuka nufe shi ba) face idan Allah Ubangiji halittu ya yarda (kuma ya nufa)" [Takwir: 29].
Saboda haka, Duk abinda Allah ya nufa; ya kan kasance, Wanda kuma bai nufi aukuwarsa ba, to lallai baya kasancewa.

        ITA KUMA MUTUWA iyaka ce ga kowani halittan da ke doron kasa, kuma mutuwa ita ce karshen kowani mai rai a cikin wannan duniyar, Kuma lallai Allah ya rubuta mutuwa har ga  Mala'iku; Jibrila da Mika'iyla, da Israfiyla (عليهم السلام) –duka za su mutu-, Kuma shima Mala'ikan mutuwa (da xaukar rai) zai mutu; Allah Ta'alah yana cewa: "Dukkan wanda yake kan qasa mai qarewa ne * Kuma fuskar Ubangijinka Mai girman jalala da karimci ita ce take wanzuwa" [Rahman: 26-27].

        Kuma mutuwa ita ce karshen rayuwar duniya, kuma ita ce farkon rayuwar lahira; saboda Da mutuwa ne, jin dadin da ke cikin rayuwar duniya ke yankewa, sai wanda ya mutu ya gane wa kansa bayan mutuwa; ko dai ni'ima mai girma, ko kuma azaba mai radadi.

        Kuma ita mutuwa aya ce daga cikin ayoyin Allah, masu nuni akan: ikon Allah Mabuwayi da daukaka, da rinjayenSa ga halittunSa, Allah Ta'alah yana cewa: "Kuma (Allah) shine Mai rinjaye bisa ga bayinSa, kuma yana aikan masu tsaro akanku, har idan mutuwa ta je wa dayanku, sai manzanninmu su karbi ransa alhali, su ba su yin sakaci" [An'am: 61].

        Kuma mutuwa adalci ne, daga Allah; wanda dukkan halittu suke daidaituwa a cikinta, Allah Ta'alah yana cewa: "Dukkan Rai mai dandanar mutuwa ne, sa'annan izuwa gare mu ake mayar da ku" [Ankabut: 57].

        Kuma mutuwa tana yanke duk wani jin dadi, tana kuma karar wa jiki kowani motsi, kuma tana rarraba jama'a, tana katange mutum daga aikata ababen da ya saba aikatawa, Allah ya kebanta da kashewa tare da rayarwa, Yana cewa: "Kuma (Allah) shine wanda ke rayarwa, kuma yake matarwa, kuma a gare shi ne sabawar dare da yini suke, Shin, ba za ku hankalta ba" [Mu'uminun: 80].

        Ita Mutuwa Mai gadi, baya hana zuwanta, kuma Masu bada tsaro basa tunkude ta, kuma dukiya bata wadatarwa, ko ta hana ta, haka 'ya'ya ko abokai.       Karami baya tsira daga mutuwa haka babba. Ko kuma mawadaci ko fakiri. Ko mai girma ko kaskantacce, Allah Ta'alah yana cewa: "Inda duk kuka kasance, mutuwa za ta riske ku, ko da kuwa, a cikin benaye ne da aka inganta" [Nisa'i: 78]. Kuma Allah ta'alah yana cewa: "Ka ce: Lallai mutuwar da kuke gudu daga gare ta, to lallai ne ita mai haduwa ne da ku, Sa'annan a mayar da ku zuwa ga masanin fake da bayyane, domin ya ba ku labari ga abinda kuka kasance kuna aikatawa" [Jumu'a: 8].

        Kuma mutuwa tana zuwa kwatsam, idan ajalinta ya zo, Allah Ta'alah yana cewa: "Kuma Allah ba zai jinkirta wa wata rai idan ajalinta ya zo ba, Kuma Allah Masani ne ga abinda suke aikatawa" [Tagabun: 11].

        Kuma mutuwa ba ta neman izinin wani; in banda annabawa ba, Su annabawa kam, mutuwa ta nemi izininsu; domin matsayinsu a wurin Allah (عليهم الصلاة والسلام), wannan ya sanya mutuwa ta nemi izinin kowani daya daga cikinsu, Ya zo cikin hadisi cewa: "Babu wani Annabi face Allah ya bashi zabi tsakanin dawwama a duniya, sa'annan Aljannah, ko kuma mutuwa, amma sai ya zabi mutuwa".

        Allah Ta'alah ya nufi cewa dan-adam ya fice daga duniya ta hanyar mutuwa, domin ya yanke dukan alakokinsa da ita; har ya zamo babu wani gashi guda daya a jikinsa da zai so duniya; matukar ya kasance mumini, Hadisi ya zo daga Anas (رضي الله عنه) lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Babu wani da ke da wani matsayi a wurin Allah, da zai so ya sake dawowa duniya, a bashi duk abin da suke doron kasa, saidai wanda yayi mutuwar shahada; yana fatan ya komo duniya, don a sake kashe shi sau goma, saboda abinda ke gani na karamomi", Bukhariy ya ruwaito shi, da Muslim.

        Kuma ita mutuwa musiba ce, wanda babu makawa kan aukuwarta, kuma zogi ne wanda babu wani mutum da zai iya sifanta shi; saboda tsananinsa; Domin Rai ne ake zare shi daga magudanan jini da tsoka da jijiya.
Kuma duk wani zogi mai tsanani to bai kai zogin da mutuwa take da shi ba, Hadisi ya zo daga  A'isha (رضي الله عنها) ta ce: Na ga Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) a lokacin mutuwa, a wurinsa akwai kofi wanda a cikinsa akwai ruwa, yana tsoma ko shigar da hannunsa a cikin kofin, sa'annan sai ya shashshafi fiskarsa da ruwan, Sai kuma ya ce: "Ya Allah ka taimake ni akan magagin mutuwa, da mayen da ke cikin mutuwa", Tirmiziy ya ruwaito shi.
A wasu riwayoyin kuma: "Lallai mutuwa tana da maye".

Wani mutum ya ce wa mahaifinsa a lokacin da ke cikin halin fitan rai: Ka sifanta min zogin mutuwa domin daukar izina? Sai ya ce: Ya kai dana! Kamar wata kaya ce mai lankwasa a ke janta a cikin cikina, kuma kai ka ce numfashi nake yi daga kofa ko kafar allura.

Kuma an ce wa wani wanda yake cikin yanayi ko halin fitar rai, Yaya kake ji? Sai ya ce: Kai ka ce: Babbar wuka ce mai lankwasa take ta kai-komo a cikin cikina.

Wani kuma an ce masa, Yaya radadin mutuwa yake? Sai ya ce: Kai ka ce, wuta ce take ruruwa a cikin cikina.

Kuma duk wanda ya dawwamar da ambaton mutuwa to zuciyarsa ta kan yi taushi, aikinsa da halinsa kuma su kan gyaru. Kuma ba zai samu kwarin guiwar aikata sabon Allah ba, kuma ba zai tozartar da farillai ba, kuma duniya da kawarta ba za ta rude shi ba, kuma –a koyaushe- zai kasance ne cikin begen Ubangijinsa, da Aljannonin ni'ima.
Shi kuma mutumin da ya mance da lamarin mutuwa sai zuciyarsa ta kaikashe, sai kuma ya karkata zuwa ga duniya, aikinsa kuma ya yi muni, burinsa kuma ya yi tsayi.

Don haka; Tuna lamarin mutuwa shine mafi girman wa'azozi, saboda ya zo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"أكثروا من ذكر هاذم اللذات".
Ma'ana: "Ku yawaita ambaton mai yanke jin dadi; wato mutuwa", Tirmiziy ya ruwaito shi, da Nasa'iy, Kuma Ibnu-Hibbana ya inganta shi.
Ma'anar hadisin kuma shine: (A rika tuna ko ambaton) mai yanke jin dadi, mai gusar da shi.

An ruwaito daga Ubaiyyu dan Ka'ab (رضي الله عنه) ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance, idan daya bisa ukun (1/3) dare ya tafi sai ya tashi, Yana cewa: "Ya ku mutane! Ku tashi ku ambaci Allah! Busa mai girgiza ta yi kusan zuwa (wato: busan farko), Me biye mata kuma tana biye (wato busan kaho na biyu), Mutuwa da abinda ke cikinta, suna zuwa", Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma ya ce: Hadisi ne mai kyau.

An ruwaito daga Abud-darda'i (رضي الله عنه) yace: "Mutuwa ta isa ta zama mai wa'azi, Zamani kuma, ya zama mai raba jama'a, Yau kuna cikin gidaje, gobe kuma a cikin kaburbura", Ibnu-Asakir ya ruwaito shi.

        Rabauta cikakkiyar rabauta, da samun dacewa cikakken yin dace, da samu rabo cikakke, suna nan cikin yin shiri ko tanadi ga mutuwa, saboda kasancewar mutuwa ita ce farkon kofar shiga Aljannah, ko kuma ita ce farkon kofar shiga wuta.

        Shi kuma tanadi ga mutuwa yana kasancewa ne, da TABBATAR DA TAUHIDI ga Allah Ubangijin talikai, ta hanyar bautar Allah; ba tare da an hada shi da komai ba, da kuma nisantar nau'ukan shirka gaba dayansu, An ruwaito daga Anas (رضي الله عنه) ya ce: Na ji Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Ya kai dan Adam! da ace zaka zo min da kamar cikin kasa da zunubai, sa'annan ka gamu da ni, ba tare da ka hada ni da kowa ba, ni kuma zan zo maka da wata gafara, kamar cikin kasa”, Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma yace hadisi ne mai kyau.

Tanadi ga mutuwa yana kasancewa ta hanyar TSARE DOKOKIN ALLAH da FARILLAI , Allah Ta'alah yana cewa: "Da masu kiyaye dokokin Allah, kuma ka bada bushara ga muminai"[Tauba: 112].

        Tanadi ga mutuwa yana kasancewa ta hanyar NISANTAR MANYA-MANYAN ZUNUBAI DA SABO, Allah Ta'alah yana cewa: "Idan kuka nisanci manyan laifukan da aka hane ku aikata su, to za mu kankare munanan ayyukanku daga gare ku, kuma za mu shigar da ku mashiga ta karimci" [Nisa'i: 31].

Tanadi ga mutuwa yana kasancewa ta hanyar BADA HAKKOKIN HALITTU DA KUMA KIN TOZARTA SU, KO JINKIRTA BAYAR DA SU: Saboda hakkin Allah, mai yiwuwa ne ya yafe abinda yake kasa da shirka. Amma hakkokin halittu, to su kam Allah (تعالى) baya yafe su, sai ta hanyar daukar hakkin nan, daga wanda ya yi zalunci, da bayar da hakkin ga wanda aka zalunta.

Tanadi ga mutuwa yana kasancewa ta hanyar RUBUTA WASIYYA, da kuma kada mutum ya yi sakaci akan haka.

Tanadi ga mutuwa yana kasancewa ta hanyar Mutum ya kasance YANA SHIRYE KAN ZUWAN MUTUWA  a kowani lokaci, wannan ne kuma yasa yayin da fadin Allah Ta'alah, ya sauka:
"فمَن يُرد الله أن يهديه يشرح صدره للإسلام".
Ma'ana: "Duk wanda Allah ke nufin shiryar da shi, ya kan buda kirjinsa domin musulunci" [An'am: 125] Sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Haske ne Allah ya ke jefa shi a cikin zuciya", (Sahabbai) sai suka ce: Menene alamar wannan ya Ma'aikin Allah? Sai ya ce: "Mayar da lamari zuwa gidan dawwama (wato: lahira), da nisantar gidan rudi (duniya), da kuma yin shiri ga mutuwa, gabanin saukanta".

        Kuma samun rabo ko rabauta shine, Mai mutuwa a cike masa rayuwarsa da aikin alkhairi, saboda Ya zo a hadisi cewa: "Ayyuka suna kyau ne da abinda aka cike su da shi".
Kuma ya zo daga Mu'azu (رضي الله عنه) ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم)  ya ce: "Wanda karshen maganarsa ita ce: LA ILAHA ILLAL LAHU, Ya shiga Aljannah", Abu-Dawud ya ruwaito shi, da Alhakim da isnadi ingantacce.

        Kuma yana daga cikin sunnoni masu karfi: LAKKANA WA mutumin da ke kan yanayi na mutuwa kalmar shahada (لا إله إلا الله), cikin tausasawa, ta hanyar mutum ya rika ambaton wannan kalmar; domin mai mutuwan ya tuna ta, amma kada ya takura masa; saboda yana cikin musiba da bakin ciki mai tsanani, An ruwaito daga Abu-Sa'id Alkudriy (رضي الله عنه) ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ku lakkana wa mamatanku kalmar LA ILA ILLAL LAHU", Muslim ya ruwaito shi.

        Rashin rabo kuma da tabewa suna nan ne, cikin: Gafala da lamarin mutuwa da mancewa da ita, da kuma barin yin tanadi domin mutuwa, da tsaurin ido wajen aikata sabo da zunubai, da tozarta tauhidin Ubangiji Mabuwayi da daukaka, da ketare iyaka, da yin zalunci ta hanyar zubar da jini na haram, da cin dukiya ta haram, da tozarta hakkokin halittu, da lumewa ko aukawa cikin ababen sha'awa da jin dadi; wadanda aka haramta, har mutuwa ta sauka wa mutum, a lokacin da nadama ba za ta yi amfani ba, kuma ba za a jinkirta ajali ba, Allah Ta'alah yana cewa: "Har idan mutuwa ta je wa dayansu, sai ya ce: Ya Ubangijina, Ka mayar da ni (duniya) * Tsammanina zan aikata aiki na kwarai cikin abinda na bari, Kayya! Lallai ne ita kalma ce, da yake fadinta, alhalin, a baya gare su akwai wani shamaki har ranar da za a tayar da su" [Muminun: 99-100].

        A yinin kiyama bayyanar da hasara, da nadama suna kara girma, Allah Ta'alah yana cewa: "Kuma ku bi mafi kyan abinda aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, a gabanin azaba ta zo muku bisa kwatsam, alhali ba ku sani ba * Sai rai ta ce, Ya kaitona akan abinda na yi sakaci ta bangaren Allah, kuma lallai na kasance daga masu izgili * Ko, kada ta ce: Da Allah ya shiryar da ni, da na kasance daga masu takawa * Ko kada ta ce, a lokacin da take ganin azaba, Da ace ina da wata damar komawa (duniya) don in kasance daga masu kyautatawa * Na'am, lallai ne ayoyina sun je maka, sai ka karyata, kuma ka yi girman kai, kuma ka kasance daga kafirai" [Zumar:55-59].

Allah yayi albarka wa Ni da Ku cikin alkur'ani mai girma! Kuma ya amfanar da Ni da Ku da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, kuma ya amfanar da mu da shiriyar shugaban Manzanni, da maganganunsa mikakku.
Ina fadar maganata wannan, kuma ina neman gafarar Allah, wa Ni da Ku, da sauran Musulmai; sai kuma ku nemi gafararSa; saboda shi Mai yawan gafara ne, Mai jin kai.

HUDUBA TA BIYU
        Yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Mai mulki, Mai gaskiya, Mabayyani, yana da hikima cikakkiya, da hujja; da ta kai makura; Da yayi nufi; da ya shiryar da ku gaba daya. Ina yin yabo ga Ubangijina, kuma ina godiya a gare shi, ina tuba zuwa gare shi, kuma ina neman gafararSa, 
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya,  Mai karfi, Mai girma.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa, Mai gaskiyar alkawari Amintacce.
        Ya Allah kayi karin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu,  da iyalansa da sahabbansa, da wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
        Bayan haka!

        Ku kiyaye dokokin Allah iyakar kiyayewa,  saboda babu mai tsira face masu takawa, kuma babu mai hasara sai masu sakaci mabarnata.

        Ya ku musulmai…      
        Ku kula da yin aiki da sabuban jawo kyakkyawar karshe (حسن الخاتمة), ta hanyar tsayar da rukunannan musulunci guda biyar, da nisantar nau'ukan sabo, da dangogin zalunci.

        Kuma yana cikin manyan sabuban samun kyakkyawar karshe a wajen mutuwa: DAWWAMA AKAN ROKON ALLAH samun kyakkyawan karshe, Allah Mabuwayi da daukaka yana cewa: "Ku roke ni zan amsa muku, lallai ne wadannan da suke girman kai ga barin bauta a gare ni, za su shiga jahannama suna kaskantattu" [Gafir: 60].

        Kuma addu'a ita ce abinda ta tattara alkhairi gaba dayansa, An ruwaito daga Annu'uman dan Bashir (رضي الله عنهما), ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Addu'a shine bauta", Abu-Dawud ya ruwaito shi da Tirmiziy, kuma ya ce: hadisi ne mai kyau ingantacce.
Kuma ya zo cikin wani hadisi cewa: "Duk wanda ya yawaita fadin addu'ar:
"اللهم أحْسِن عاقبتَنا في الأمور كلها وأجرنا من خزي الدنيا وعذاب الآخرة".
 Ma'ana: "Ya Allah ka kyautata karshenmu cikin lamura dukansu, kuma ka tseratar da mu daga kunyar duniya da bala'inta, da kuma azabar lahira = TO WANNAN MUTUMIN ZAI MUTU GABANIN BALA'I YA RISKE SHI".

        Su kuma SABUBAN DA SUKE JAWO MUMMUNAN KARSHE  a lokacin mutuwa sune: Tozarta hakkin Allah, da hakkokin halittu, da dogewa akan aikata manyan zunubai da laifuka, da yin sako-sako da lamarin girman Allah, da karkata zuwa ga duniya, da mance gidan lahira

        Bayin  Allah!
"Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan annabin, ya ku wadanda su ka yi imani ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Duk wanda ya yi salati guda xaya a gare ni, to Allah zai salati a gare shi guda goma saboda shi".
        Sai ku yi salati, da sallama ga shugaban na farko da na qarshe, kuma jagoran manzanni.
Ya Allah! Ka yi salati wa annabi Muhammadu da iyalan annabi Muhammadu kamar yadda ka yi salati wa annabi Ibrahima da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abun godiya ne, Mai girma.
Ya Allah! Ka yi albarka wa annabi Muhammadu da iyalan annabi Muhammadu kamar yadda ka yi albarka wa annabi Ibrahima da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abun godiya ne, Mai girma.
Ya Allah! Ka yarda da sahabbai gabaxaya, da kuma khalifofi shiryayyu, kuma shugabanni masu shiryarwa; Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da sauran sahabban annabinka gabaxaya,
Ya Allah! Ka yarda da tabi'ai da waxanda suka bi su da kyautatawa (bi da bi) har zuwa ranar qarshe,
Ya Allah! Ka yarda da mu tare da su, da baiwarka, da rahamarka ya mafi rahamar masu rahama.
Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da musulmai (sau uku), ka kuma qasqantar da kafirci da kafirai, Ya Ubangijin talikai.
        Ya Allah ! ka qasqantar da bidi'a da 'yan bidi'a har zuwa tashin kiyama.
        Ya Allah ! ka sanya mu daga cikin waxanda suke yin riqo da sunnar Annabinka Muhammadu (صلى الله عليه وسلم).
        Ya Allah ! ka sanya mu daga cikin masu riqo da littafinka, da kuma sunnar Annabi (صلى الله عليه وسلم).
        Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka, da ka kyautata qarshemu cikin lamura gabaxaya, kuma ku tseratar da mu daga wulaqancin duniya da bala'inta, da kuma azabar lahira.
        Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka, da ka taimake akan magagi ko mayen da yake cikin mutuwa, Ya Ubangijin talikai.
        Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka, da ka sanya qarshen rayuwarmu a nan duniya shine ka yarda da mu, Ya Ma'abucin girman jalala da karramawa. Kuma ka sanya mafi alherin yininmu ya zama shine ranar da za mu sadu da kai, Wa wanda yafi masu karramawa girman karimci.
        Ya Allah ! Lallai mu muna roqonka aikata aikhairori, da barin aikata ababen qi, da son miskinai, Ya Ubangijin talikai.
        Ya Allah! Ka nuna mana gaskiya a matsayin gaskiya, kuma ka azurta mu da binta, kuma ka nuna mana qarya a matsayin qarya, ka azurta mu da nisantarta, kuma kada ka sanya varna ta cakuxe mana da gaskiya; tsoron kar mu vata.
        Ya Allah! Ka gafarta mana abinda muka gabatar, da abinda muka jinkirta, da abinda muka asirce, da abinda muka bayyana, da abinda kai ne kafi mu saninsa. 
Ya Allah ! Lallai muna roqonka aljanna da abinda ke kusantarwa zuwa gare ta na zance ko aiki, kuma muna neman tsarinka daga wuta da abinda yake kaiwa zuwa gare ta; na zance ko aiki.
Ya Allah! Ka taimake mu akan ambatonka da yin godiya a gare ka, da kyautata ibadarka, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka gafarta wa mamatanmu da mamatan musulmai, Ya Allah! Ka gafarta wa mamatanmu da mamatan musulmai, kuma ka yalwata musu kabarinsu akansu, kuma ka haskaka musu cikinsa, Ya Ma'abucin girman jalala, da karramawa. Kuma ka tsare su daga azabar qabari, Ya Mafi jin qan masu jin qai.
Ya Allah! Ya Mafi jin qan masu jin qai, Ya Wanda yafi dukkan masu karramawa yin baiwa, Kada ka dogarar da mu ga kanmu, koda daidai da kyaftawar ido.
Ya Allah! Ka gyara mana sha'anoninmu gabaxayansu.
Ya Allah!  Ka yaye baqin cikin masu baqin ciki daga cikin musulmai, Ya Allah! ka biya bashi wa waxanda ake binsu bashi daga cikin musulmai.
Ya Allah! Ka bada waraka ga marasa lafiyanmu da marasa lafiyan musulmai (sau uku), da rahamarka Ya Mafi jin qan masu jin qai.
        Ya Allah! Ka tseratar da mu, kuma ka tseratar da zurriyarmu, daga Iblis da zurriyarsa, da shaixanunsa da rundunarsa, da makircinsa Ya Ubangijin talikai (sau biyu), lallai kai mai iko ne akan komai.
        Ya Allah! Ka tseratar da musulmai daga Iblis da zurriyarsa, da shaixanunsa Ya ma'abucin girman jalala, da karramawa.
        Ya Allah! Lallai mu muna roqonka Ya Mafi jin qan masu jin qai, muna roqonka Ya Allah! Da bada mafita wa musulmai daga kowani baqin ciki, Ya Allah! Ka haxa tsakanin zukatansu, kuma ka daidaita su, ka shiryar da su hanyoyin shiriya, kuma ka fitar da su daga duffai zuwa ga haske.
Ya Allah! Ka lalata kaidin maqiya musulunci ya Ubangijin talikai, Ya Allah ka ruguza makircin maqiya musulunci, Ya Ubangijin talikai, Ya Allah! Ruguza tsare-tsaren maqiya musulunci; waxanda suke tsattsara su domin suyi kaidi wa musulunci da musulmai, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka kiyaye qasashenmu daga kowani mummuna, ko abun qi, lallai kai akan kowani abu mai iko ne.
Ya Allah! Ka saukar da aminci –Ya Ubangijin talikai- da imani a qasashen musulmai.
Ya Allah! Ka xauke wa musulmai fitintinu masu vatarwa.
Ya Allah! Ka xauke fitintinu masu vatarwa wa musulmai, Ya mafi jin qan masu jin qai, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka ciyar mai jin yunwa daga cikin musulmai, kuma ka tufatar da wanda ke cikin tsiraici, Ya Allah ka amintar da wanda yake cikin tsoro daga cikinsu, ya mafi jin qan masu jin qai. Kuma kada ka dogarar da su ga kayukansu koda daidai da kyaftawar ido.
Ya Allah! Ka yi taufiqin dace ga Mai hidiman harami biyu, zuwa abinda kake so kuma ka yarda, Ya Allah ka datar da shi zuwa ga shiriyarka, kuma ka sanya aikinsa cikin yardarka. Ya Allah ka taimake shi akan kowani alheri. Ya Allah ka taimaki addininka da shi, Ya Ubangijin talikai. Ya Allah ka azurta shi da lafiya, Ya Ubangijin talikai, kuma ka taimake shi a lamuran addininsa da duniyarsa, Ya Ma'abucin girman jalala da karramawa.
Ya Allah! Ka datar da masu na'ibtarsa guda biyu, zuwa ga abinda kake so kuma yarda da shi, da kuma zuwa ga abinda akwai alkhairi a cikinsa ga musulunci da musulmai, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka gafarta mana, lallai kai ka kasance Mai yawan gafara, kuma ka saukar da ruwan sama akanmu, na mamako, Ya Allah ka sanya mana albarka cikin abinda k aba mu.
Ya Allah! Lallai mu muna neman tsarinka daga gushewar ni'imarka, da canzawar lafiyarka, da zuwan uqubarka kwatsam, da kuma xaukacin abinda ke sa fushinka, Ya Mafi jin qan masu jin qai.
"Ya Ubangijinmu! Ka bamu mai kyau a duniya, ka bamu mai kyau a lahira, kuma ka kare mu daga azabar wuta" [Baqarah: 201].

Ya ku bayin Allah!  
"Lallai Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai riqa ambatonku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma, Lallai kuma Allah ya san abinda kuke aikatawa.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,
………………….


1 comment:

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...