HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 2/JUMADAL ULAH/1439H
Daidai da 19/JANAIRU/2018M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEHIN MALAMI ABDULBARIY DAN AUWADH AS-SUBAITIY
TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
ALBARKAR RAYUWA
Shehin Malami wato: Abdulbariy xan Auwadh
Al-Subaitiy –Allah
ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'ah, 2/ Jumadal Ulah, 1439H, mai taken: ALBARKAR RAYUWA, Wanda kuma a cikinta ya
tattauna akan aminci da zaman lafiya, da yadda sha'anonin rayuwa gaba daya su
ke rataye da shi, kuma cewa ba zai yiwu rayuwa ta miqe ba, ai idan akwai zaman
lafiya, sannan ya ambaci sabuban da su ke rushe samun zaman lafiya, ko su ke
girgiza gininsa, kamar yadda ya bayyana yadda ake samar da aminci da zaman
lafiya.
HUDUBAR FARKO
Yabo ya
tabbata ga Allah; Yabo ya tabbata ga Allah wanda ya mana baiwa da ni'imar samun
aminci da zaman lafiya, Ina yin yabo a gare shi (سبحانه) kuma ina godiya a gare shi, kuma ina
roqonsa wa'aztuwa da xaukar izina.
Kuma ina
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da
abokin tarayya, wanda ya ke cewa: "Kuma kowani abu a wurinsa yana da gwargwado"
[Ra'ad: 8].
Kuma ina
shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa,
yayi kira (da'awah) zuwa ga Allah cikin hikima, da gwanancewa. Allah yayi qarin
salati a gare shi da iyalansa matukar dare da yini suna canjin aiki.
Bayan haka:
Ina yin
wasiyya a gare ku, da ni kaina da bin dokokin Allah.
Allah,
ya sanya kasa a matsayin mazauni ga rayuwar bayi, ya kuma yi albarka a gare ta,
ya kuma cike ta da alkhairori, Allah (تعالى) ya
ce: "Kuma ya sanya, a cikinta, duwatsu kafaffu, daga samanta, kuma ya
sanya albarka a cikinta, kuma ya kaddara ababen ci, daga cikinta" [Fussilat:
10].
Allah
(تعالى) ya zabi
AnnabawanSa, kuma ya musu ni'imar albarka, a cikin rayuwarsu da ayyukansu,
Allah (تعالى) ya
ke fadi dangane da Annabi Nuh (عليه السلام): "A ka ce: Ya kai, Nuhu, ka sauka
cikin aminci daga gare mu, da kuma albarkoki akanka, da kuma wasu daga
al'ummomin da ke tare da kai" [Hud: 48].
A dangane da, annabi Isah (عليه السلام), Allah ya ce: "Kuma ya sanya ni, Mai albarka, a duk inda
nake" [Maryam: 31].
Kuma
albarkar Annabi (صلى
الله عليه وسلم) ta tabbatu, kuma sahabbansa –Allah ya
kara yarda a gare su- sun ganta, da idanuwansu.
Kuma
Alkur'ani yana da albarka; cikin binsa,da aiki da shi, kamar yadda Allah ya ke
cewa: "Kuma wannan littafi ne da muka saukar da shi, mai albarka; sai ku bi
shi, kuma kuyi takawa; domin ayi muku rahama" [An'am: 155].
Ita
kuma ALBARKA tana nufin, Bunkasa da daukaka, kuma idan albarka ta sauka ga abu,
kadan sai ta yawaita shi, idan kuma ta tabbatu ga wani wuri, sai tasirinta ya
bayyana, kuma alkhairinta ya yi yaduwa, kuma amfaninta sai ya game dukiya da
'ya'ya, da lokaci, da ilimi, da aiki, da gabbai gaba daya.
Allah
ya sanya albarka, ga dakinsa mai alfarma, da Madina gari mai dadin zama, da
kuma masallacin Aksah da ke garin Kudus da bagiren da ya kewaye shi; Sai Allah
ta'alah ya ce: "Lallai farkon dakin da aka sanya wa Mutane; shi ne ya ke garin
Makkah; Mai albarka, kuma shiriya ga talikai" [Ali-imrana: 96].
Kuma
Manzon Allah (صلى
الله عليه وسلم) ya ce: "Ya Allah ka sanya
wa garin Madina ninkin abinda ka sanya wa Makkah na albarka",
Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma
Allah (تعالى) ya
ce: "Tsarki ya tabbata ga wanda ya yi tafiyar Isra'i da bawansa, daga
Masallaci mai alfarma, zuwa ga Masallaci mafi nisa, wanda muka sanya albarka a
gefensa, domin mu nuna masa daga ayoyinmu" [Isra'i: 1].
Allah
ya sanya albarka ga al'ummar Annabi (صلى الله عليه وسلم) sai ta yi ta
bunksa dana samun daukaka, sai ta wayi gari ta rigayi dukkan al'ummai, Manzon
Allah (صلى الله عليه وسلم) ya
ce: "Lallai cikin bishiyoyi akwai wata bishiya, wanda ganyenta kadewa,
kuma wannan bishiyar it ace misalign musulmi, Ku ban labarin wace bishiya ce?", Ya
ce, Sai mutane suka yi ta ambaton bishiyoyin jeji da kauye, Abdullahi dan Umar
ya ce, sai ya darsu a zuciyata cewa it ace, bishiyar dabino. Sa'annan sahabbai
suka ce: Ka bamu labarin wace bishiya ce, ya Ma'aikin Allah? Sai ya ce: "Lallai ita ce,
itaciyar dabino", Bukhariy ya ruwaito shi.
Shi
musulmi yana kirdadon samun albarka a duk inda ta ke, domin ta game jikinsa da
rayuwarsa da duk abinda ya ke kewayensa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance idan
'ya'yan itatuwa suka nuna, akan zo masa da su, sai ya ce: "Ya Allah ka sanya
mana albarka ga Madinarmu, Ya Allah ka mana albarka cikin sa'inmu, Ya Allah ka
sanya wa mudunmu albarka, Ya Allah ka sanya albarka ga Madinarmu, Ya Allah, ka
sanya albarka biyu, a madadin daya", Muslim ya ruwaito shi.
Mumini
kan janyo albarka ga gidansa, ta hanyar dawwamar da ambaton Allah a cikinsa, da
karanta suratul bakara, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Idan dayanku ya
shiga gidansa, sai ya ambacin sunan Allah a lokacin shigansa, da lokacin cin
abincinsa, Sao Shedan ya ce: Bani da wurin kwana a wurinku da abinci",
Muslim ya ruwaito shi.
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ku karanta suratul
bakara, domin karantata albarka ne, Kuma masu sihiri basa iya ta",
Muslim ya ruwaito shi. Lafazin "بطلة"
da ya zo cikin hadisin ma'anarsa shi ne, masu sihiri.
Kuma
ana janyo albarka ta hanyar lazimtar "istigfari", a cikin addu'ar
annabi Nuh (عليه السلام)
Allah Mabuwayi da daukaka yana cewa: "Sai na ce: Ku nemi gafarar
Ubangijinku, domin shi ya kasance mai yawan gafara * Zai saki ruwan sama
akanku, mamako * Sai kuma ya karfafe ku da wata dukiya, da 'ya'ya, kuma ya
sanya muku lambuna, kuma ya sanya muku koramu" [Nuh: 10-12].
Mumini yana kirdadon samun albarka ta hanyar
lazimtar fita sallar asuba tare da jama'a, saboda a cikin sallar jam'i akwai
samun rabo mai girma.
Kuma ana samun albarka ta hanyar yin sammako,
Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya
ce: "Ya Allah ka sanya albarka wa al'ummata cikin sammakonta",
kuma Annabi (صلى
الله عليه وسلم) ya kasance idan zai tura zarata, ko
runduna, yak an tura su, da farkon yini. Kuma maruwaicin hadisin mai suna
Sakhar ya kasance mutum ne attajiri, sai ya kasance idan zai aika masu masa
tijara, yak an aika su, da farkon yini, sai ya yi kudi; kuma dukiyarsa ta
yawaita. Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma ya ce: hadisi ne, hasan. Kuma
Ibnu-Hibbana ya inganta shi.
Yin addu'an albarka shine mafi alherin abinda
ke janyo samun falalarta, kuma yana kwalalo ni'imarta, saboda an ruwaito daga
Akil dan Abu-dalib (رضي
الله عنه) lallai shi ya auri wata mata daga kabilar
Banu-Jushm, sai wadannan mutanen suka shigo wurinsa suka ce masa: Allah ya bada
daidaitar hali, da ciki da goyo, Sai ya ce: "Kada ku aikata
haka, Sai suka ce, to me za mu ce, Ya Abu-Zaid? Sai ya ce: Ku ce: BARAKAL LAHU
LAKUM, WA BARAKA ALAIKUM, addu'ar albarka, domin da fadin haka, muka kasance
ake umartarmu", Ahmad ya ruwaito shi, da isnadi ingantacce.
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance idan
zai yi addu'ar rakiyar ma'auraci, ya kan ce: "BARAKAL LAHU LAKA,
WA BARAKA ALAIKA, WA JAMA'A BAINAKUMA FIY KHAIRIN, Wato, Allah ya maka albarka,
ya sanya maka albarka, kuma ya sada tsakaninku da alkhairi",
Tirmiziy ya ruwaito shi da isnadi ingantacce.
Kuma albarka tana tabbatuwa, ta hanyar
lazimtar gaisuwar musulunci, wanda tana daga cikin abinda wannan al'ummar mai
albarka ta kebanta da su, Allah (تعالى) ya ce: "Idan za ku shiga
gidaje, sai ku yi sallama ga kayukanku, gaisuwa ce daga Allah, mai albarka mai
dadi" [Nur: 61].
A cikin tijarar kasuwanci kuma, ana janyo
albarka ne ta hanyar yin gaskiya, da bayyana aibin kaya,Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Mai saye da mai
sayarwa, suna da zabi matukar basu rabu ba, ko kuma ya ce: har zuwa su rabu.
Idan har suka yi gaskiya wa juna, suka bayyana aibi, sai a sanya musu albarka a
cikin kasuwarsu, Idan kuma suka boye, suka yi karya, sai a kwashe albarkar
kasuwarsu", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Shima sadar da zumunci yana tsawaita
rayuwa kuma yana sanya albarka a cikin arziki, Bukhariy da Muslim sun fitar da
hadisi daga Anas (رضي
الله عنه), cewa Annabi (صلى الله عليه وسلم), ya ce: "Duk wanda zai
faranta masa a yalwata arzikinsa, ko a tsawaita ajalinsa, to ya sadar da
zumuncinsa".
Shima dinke Baraka da hadin kai, Yana
janyo samun albarka, da saukarta, kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana
kwadaitar da sahabbansa kan hadin kai, da nisantar rarrabar kai, a cikin dukkan
yanayinsu, Sahabbai su ka ce, Ya MAnzon Allah, Lallai muna cin abinci, bama
koshi, Sai ya ce: "Shin kuna haduwa ne wajen cin abincinku, ko kuna ci a
rarrabe?" sai suka ce: A a muna ci ne a rarrabe, Sai ya ce:
"Ku rika haduwa akan abincinku, ku ambaci sunan Allah, sai a sanya
muku albarka", Ibnu-Hibbana ya ruwaito shi, a cikin sahihinsa.
Raunanan mutane a cikin
al'umma, wani fage ne ga mutumin da ke neman yawaitar albarka, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Shin za a baku
nasara ne, ko arziki, ba don raunanan cikinku ba?",
Bukhariy ya ruwaito shi. A wata riwayar kuma "Ku nemo min
raunanan cikinku, Shin za a baku arziki, da nasara ne, ba don saboda raunananku
ba?", Tirmiziy ya ruwaito shi da isnadi ingantacce.
Kuma idan albarka ta sauka, a cikin rayuwar
musulmi, sai Allah ya azurta shi da hankali nunanne da sanin addini, da zuciyar
da take raye da ilimi da imani, saboda an ruwaito daga Ibnu-Abbas (رضي الله عنهما) lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya shiga makewayi
domin biyan bukata, sai Ibnu Abbas ya sanya masa ruwan alwala, Sai ya ce:
"Wanene ya ajiye min wannan?" sai aka bashi labara, sai y
ace: "Ya Allah ka fahimtar da shi addini", Bukhariy ya ruwaito
shi. Sai Allah ya amsa wa Annabinsa, Sai Abdullahi dan Abbas –رضي الله عنهما- ya samu ilimi,
Wani daga cikinsu yace: "Na ga Abdullahi bn Abbas, alhalin dubban
daliban hadisi sun taru a wurinsa".
Kuma albarka tana bayyana a rayuwar musulmi
ta yadda za a datar da shi da yada ilimi mai yawa, da fitar da
rubuce-rubuce masu tarin alkhairi, daya-bayan-daya cikin lokaci kadan, ba tare
da wahala mai yaw aba, Wannan kuma taimako ne na musamman, da ake karfafar
mutum da shi, wanda ke zame masa agaji wajen aikin biyayya, da ibada.
Tsawon rayuwa, tare da kyan zance da aiki,
yana daga misalan albarkar da Allah ke bada ita ga wadanda ya datar da su, daga
cikin bayinsa, Manzon Allah (صلى
الله عليه وسلم) ya ce: "Albarka tana tare
da wadanda suka fi girman shekaru a cikinku", Ibnu-hibbana yay a
ruwaito sbhi a cikin sahihinsa.
Yana daga misalan albarka a rayuwar musulmi,
a azurta shi da mace saliha; tagari, mai yawan haihuwa da soyayya, sai kuma a
bashi zurriya na-kirki da ita, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ana auren mace
domin abubuwa hudu; saboda dukiyarta, da danginta, da kyanta, da kuma
addininta; sai ka rabauta da ma'abuciya addini hannayenka zasu damki turbaya",
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi. Ita kuma ma'abuciyar addini zata yawaita
albarka a cikin gidan, saboda turbaya alama ce bunkasa da karuwar alkhairi.
Allah ya kwalala wa mutum dukiya mai tarin
yawa, sannan ya datar da shi, wajen ciyar da wannan dukiyar ta fiskokin
alkhairi da kyautatawa, albarka ce a fili, kuma ni'ima mai gamewa, kuma albarka
tana kara albarka a duk lokacin da ake tsarkake dukiya daga abinda ka iya shiga
masa. Duk kuma wanda ya sanya dukiyarsa cikin fushin Allah, ya kuma hana hakkin
Allah, to sai a cire albarkar dukiyar, Allah (تعالى) ya ce: "Allah yana kwashe
albarkar riba, kuma yana kara albarkar sadakoki, kuma Allah baya son dukkan
yawan kafirci mai zunubi", [Bakara: 276].
Allah
yayi mini albarka ni da ku, cikin alkur'ani mai karamci, ya kuma amfanar da mu
da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, Ina fadar maganata wannan, ina kuma neman
gafarar Allah, wa NI da KU, da kuma sauran musulmai, ku nemi gafararSa, lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
…
HUDUBA TA BIYU
Alhaki
ne akan musulmai gaba daya, su rika neman albarka a cikin kasashensu da
al'ummarsu, da kokarin samar da sabubanta, Kuma babba daga cikin sabuban
albarkar shine: RAYA KASA DA YIN AIKI DA TSARI KO SHARI'AR ALLA, Allah (تعالى) ya ce: "Da ma'abuta alkaryu
za su yi imani, su yi takawa, da mun bubbude musu kofofin albarkoki, daga sama
da kasa, Amma kuma sun karyata sai muka kama su da abinda suka kasance suke
aikatawa", [A'araf: 96].
Kuma
babu mai hankali shiryayye da zai yi musun cewa lallai kawar da kai daga aiki
da tsari ko shari'ar Allah, sababi ne na gushewar albarka, da tafiyar alkhairi;
saboda Allah ya bamu labarin mutanen garin Saba'I; wadanda aka canza musu,
bayan basu albarka da bunkasa, aka canja musu, da kwashe albarkar, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma hakika saba'awa
(mutanen garin Saba'i) ya kasance suna da ayar lura a wurin zamansu; gonakin lanbu
biyu ta dama da hagu; sai muka ce musu ku ci daga arzikin Ubangijinku, kuma ku
yi godiya a gare shi; gari mai dadin zama, da kuma Ubangiji Mai yawan gafara *
Sai suka bijire, sai muka saki malalin arami na dam akansu, kuma muka musanya
musu gonakinsu biyu da wadansu gonaki masu 'ya'yan itace kadan; talakiya da
goruba, da wani abu na magarya kadan", [Saba'i: 15-16].
Ya Allah! kayi salati wa Annabi
Muhammadu da iyalanSa da sahabbanSa. Ya
Allah!Ka yarda da khalifofi gudahuxu shiryayyu; Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu da
iyalansa da sahabbansa masu krimci, ka haxa da mu da baiwarka, da rahamarka, Ya
mafificin masu rahama.
Ya
Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai, Ya Allah! ka xaukaka
musulunci da musulmai, kuma ka qasqantar da kafirci da kafirai, kuma Ya
Allah! Ka ruguza maqiyanka; maqiyan addini, Ya Allah! Ka sanya wannan
qasar ta zama da aminci, cikin nitsuwa, da sauran qasashen musulmai.
Ya
Allah! Ka karvi azuminmu da sallolinmu da ruku'inmu da sujadanmu, Ya
Allah! Ka sanya mu daga cikin waxanda ka karvi azuminsu da sallolinsu ya
mafi rahamar masu rahama.
Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka
aljanna, kuma muna neman tsarinka daga wuta.
Ya Allah! Muna roqonka alkhairi
gabaxayansa; na gaggawa daga cikinsa da na nesansa, wanda muka sani daga
cikinsa da wanda ba mu sani ba, kuma muna neman tsarinka daga sharri
gabaxayansa; na gaggawa daga cikinsa da na nesansa, wanda muka sani daga
cikinsa da wanda ba mu sani ba.
Ya
Allah! Lallai ne mu muna roqonka mabuxan alkhairi da qarshensu, da abinda
ya tattara su, da farkonsu da qarshensu, da zahirinsa da baxininsa, kuma muna
roqonka darajoji maxaukaka a cikin aljanna, Ya Ubangijin talikai.
Ya
Allah! Ka kiyaye rundunoninmu masu tottoshe kafofin varna (ribaxi), Ya
Allah! Ka kiyaye jami'an tsaronmu, Ya Ubangijin talikai. Ya Allah! Ka
kiyaye su a ko-ina suke, Ya Allah! Ka zama mai qarfafarsu, Mai taimakonsu, Mai
tagaza musu, Ya Allah! Ka karvi wanda ya mutu daga cikinsu yana mai shahada, Ya
Allah! Ka xaukaka darajarsu cikin darajar "illiyuna", Ya Allah! Ka
ninnika kyawawansu, kuma ka yi musu rangwame akan munanansu, kuma ka xinke
karayar iyalansu da danginsu, Ya Ubangijin talikai.
Ya
Allah! Wanda ya nufe mu, ko ya nufi musulmai da mummuna, to ka shagaltar da
shi da kansa, kuma ka sanya rugujewarsa cikin tsarinsa Ya mai amsa addu'a.
Ya
Allah! Ka sanya wannan qasar cikin aminci da zama lafiya da wadaci da
yalwa, da sauran qasashen musulmai, Ya Ubangijin halittu.
Ya
Allah! Ka datar da shugabanmu zuwa ga abinda kake so, kuma yarda, Ya Allah!
Ka datar da shi zuwa ga shiriyarka, kuma ka sanya aiyukansa cikin yardarka,
kuma ka bashi lafiya, Ya ubangijin talikai.
Ya
Allah! Ka datar da jagororin musulmai wajen yin aiki da littafinka da yin
hukunci da shari'arka, Ya mafi rahamar masu rahama.
"Ya Ubangijinmu! Mun
zalunci kayukanmu idan baka gafarta mana, ka yi mana rahama ba to zamu kasance
daga cikin masu hasara" [A'araf: 23].
"Ya Ubangijinmu! Ka
bamu mai kyau a duniya, kuma ka bamu mai kyau a lahira, ka kare mu daga azabar
wuta" [Baqarah: 201].
"SUBHANA RABBIKA RABBIL IZZATI AMMA YASIFUN,
WA SALAMUN ALAL MURSALINA, WALHAMDU LILLAHI RABBIL ALAMINA"
[]…..
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
No comments:
Post a Comment