HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 24/ZULHIJJAH/1438H
daidai
da 15/SATUMBA/2017M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI SALAH BN MUHAMMADU ALBUDAIR
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Ya ku musulmai …
Mutane sun kasance akan addini guda
xaya, shine MUSULUNCI, Har daga baya suka bauta wa gumaka, shirka kuma ta auku
a cikin mutane bayan da babu ita, Sai Allah ya tayar da manzanni zuwa gare su,
kuma ya rufe Manzancin da zavavven Manzo, kuma mafificinsu, wato annabinmu kuma
shugabanmu annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- wanda Allah ya tayar da shi da hujjoji masu haske, da kuma
dalilai na yankan shakku, ya turo shi zuwa ga mutane gaba xaya.
Yana daga MANYA-MANYAN MANUFOFIN TURO
SHI, DA MANZANCINSA, Mutane su bauta wa Allah, su kaxaita shi, kada su haxa shi
da kowa. Kuma su nisanci dukkan abin bauta koma-bayan Allah, kamar Shexanu, da
bokaye, da gumaka da qaburburan da ake bauta musu koma bayan Allah, Allah
Mabuwayi da xaukaka ya ce: "Kuma lallai, haqiqa,
mun aike Manzo daga kowace al'umma, (Ya ce:) Ku bauta wa Allah, kuma ku nisanci
Xagutu" [Nahl: 36].
Amru bn Abasah As-Sulamiy ya ce: "Na kasance, tun a lokacin jahiliyya, ina zaton mutane akan vata
suke, kuma su ba akan komai suke ba, a lokacin suna bautar gumaka, sai na ji
labarin wani mutum a garin Makkah, yana bada wasu labarai, sai na hau raqumata,
na zo wurinsa, sai ga Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- a halin yana voye da'awarsa, Mutanensa kuma suna masu feqe ido
(jara'a) a gare shi, Sai na bi da-sannu-sannu, har na shiga wurinsa, a garin
Makkah, Sai na ce masa: Wanene kai? Sai ya ce: Annabi, Sai na ce: menene kuma
annabi? Sai ya ce: Allah ne ya turo ni, Sai na ce masa: Da wani abu ya turo ka?
Sai ya ce: Ya turo ni da, sada zumunci, da kakkarya gumaka, da kuma a kaxaita
Allah; kada ayi masa shirka da komai",
Muslim ya ruwaito shi.
Sai Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya xauki dukkan nauyin
da ke tattare da Manzanci.
Kuma yana daga cikin KEVANTATTUN
SIFOFINSA DA SUKA HAXA KAMALA, KWAXAYINSA KAN
KIYAYE VANGAREN TAUHIDI, DA YADDA YA TOTTOSHE DUKKAN HANYOYIN DA SUKE KAIWA
ZUWA GA SHIRKA.
Kuma a cikin
Sunnar Annabi da tarihinsa akwai gamsassun bayanai na cikakkiyar nasiharsa, da
tausasawarsa da rahmarsa da jin-qansa ga al'ummarsa, da yadda ke nuna kwaxayinsa
, da yadda ya kai maqura wajen tsawatar musu kan dukkan abinda zai cutar da su.
An ruwaito daga
Sa'ad bn Abiy-waqqas –رضي الله عنه- ya ce: "Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya shige ni, alhalin ina
addu'a da yatsuna, Sai ya ce: Ka kaxaita!, ka kaxaita!! Sai ya yi nuni da
manuniyar yatsa", Abu-dawud ya ruwaito shi.
Wato, yana nufin, ka yi nuni da yatsa guda xaya, saboda wanda kake
roqon nasa abin bauta ne guda xaya, babu wani da ya cancanci a masa bauta, ko
addu'a idan ba shi ba.
Kuma Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ga kuros a wuyan
Adiyyu bn Hatim, sai ya ce: "Ya kai Adiyyu bn
Hatim, ka jefar da wannan gunkin daga wuyanka".
Kuma wasu fatake
sun zo wurin Annabi –صلى الله عليه وسلم- sai ya ji su suna kiran wani mutum daga cikinsu da sunan Abdulhajar
(wato, bawan dutse), Sai Annabi –صلى الله عليه
وسلم- y ace: Menene sunanka? Sai ya ce: Bawan
dutse, Sai ya ce: Kai Abdullahi ne.
Sai wannann ya yi nuni kan haramcin sanya sunan da aka bautar da
shi ba ga Allah Ta'alah ba, kamar AbdulMasihi, da AbduMuhammad, da AbdulHusain,
da AbdunNabiyy.
Kuma mutane sun
kasance suna zubar da jinin dabbobi ga qaburburan shugabanninsu, kuma suna jawo
dabbobin ni'ima a gare su, domin su zubar da jinane akan kaburburan, Sai Manzon
Allah –صلى الله عليه وسلم-
ya ce: "Ba a zubar da jinin dabbobi ga qabari, a
musulunci",
Don haka, yana daga cikin bautar gumaka da ayyukan jahiliyyah, yin
yanka ga qaburburan manyan-mutane da waliyyai da salihai, sai su yanka raqumi
ko Saniya, ko tumakai, ga qabarin wane, suna masu zubar da jinin dabbar a
vangarorin qabarin, ko a wurin kan mai qabarin, sai su riqa cewa: Sayyadi
waliyyi wane, babu wani da zai yi yanka a wurin qabarinsa domin wata buqata,
face an biya wannan buqatar, ko kuma maras lafiya face ya warke, ko kuma wanda
ke cikin vacin rai face an yaye masa, Sai jahilai su yi xa'a ga wannan maganar
ta varna, sai su jawo raqumi ko Saniya, ko su xauko akuya, zuwa ga qabarin
wane, sai su riqa cewa, wannan xan maraqin naka ne, ya kai Shehi wane, wannan
akuyar itama abin yankanka ce, ya kai shehi wane, suna masu qudurta cewa,
shehin zai kawo musu wani amfani, ko ya tunkuxe musu cutuka.
Kuma haqiqa Allah
Ta'alah ya haramta, a harshen annabinSa Muhammadu –صلى الله عليه
وسلم- yin yanka ga qaburbura, da kuma a wurin
qabari, ko domin qabari, kamar yadda ya haramta yanka ga gumaka, kamar yadda ya
haramta yin sujjada ga qabari, da yin salloli akansu, ko ana fiskantarsu, da
mulka fiska da qasa, ko kumatu aka qasar kabari, ko kuma xawafin qabari, ko
gina masallaci akan qaburbura, ko bunne matattu a cikin masallatai, saboda
Annabi –صلى الله عليه وسلم-
ya ce: "Duniya dukkanta masallaci ne, in banda
maqabarta, ko banxaki", Tirmiziy ya ruwaito shi, da
Ibnu-Majah.
Kuma ya ce: "Kada ku zauna akan
kabari, kuma kada ku yi sallah kuna fiskantarsu", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma ya ce: "La'anar Allah ta
tabbata akan Yahudawa; saboda sun riqi kabarin annabawansu masallatai. Yana
tsawatarwa kan abinda suka aikata",
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma uwar muminai; Ummu-Habiba, da Ummu-Salmah –رضي الله عنهما- sun ambata wa Manzon
Allah –صلى الله عليه وسلم-
wani cocin da suka gani a qasar Habasha, a cikinsu akwai hotuna, Sai Manzon
Allah –صلى الله عليه وسلم-
ya ce: "Lallai waxancan mutanen, idan mutum
salihi daga cikinsu ya mutu, sai su gina masallaci akan qabarinsa, sai su xauki
waxancan hotunan a can, waxannan sune ashararen halittu a wurin Allah, ranar
qiyama", Bukhariy da Muslim suka ruwaito
shi.
Kuma yana daga
cikin bautar gumaka, abinda jahilai ke aikatawa na sarrafa addu'a ga wanin
Allah Ta'alah; sais u riqa roqon waxanda suke cikin kabari, suna neman agajinsu;
suna cewa: Ya sayyadina, Ya madogarata, Ni ina cikin girmanka, ina cikin
kulawarka, sai ka bani xa, ka warkar da maras lafiyana; wane, da wassun wannan,
daga abinda masu bautar qabari, da masu cin abinci da kaburbura, da 'yan
xariqoqin bidi'a suke yi.
Allah Ta'alah ya ce: "Lallai waxanda
kuke roqonsu koma-bayan Allah, bayi ne misalinku, ku roqe su, su amsa muku,
idan kun kasance masu gaskiya"
[A'araf: 194].
Kuma ya ce: "Kada ka roqi
wanin Allah, abinda ba zai amfane ka ba, ba zai cutar da kai ba, Idan hark a
aikata, to lallai, kai ka kasance daga cikin azzalumai", [Yunus: 106].
"Wancan shi ne Allah Ubangijinku, Mulki
nasa ne, Waxannan da ku ke roqo baicinsa, basa mallakar fatar gurtsun dabino *
Idan kuka roke sub a za su ji addu'arku ba, koda sun ji ba za su amsa muku ba,
kuma a ranar kiyama za su kafirce wa shirkarku, kuma babu mai baka labara kamar
masani", [Faxir: 13-14].
Kuma mutane a
jahiliyya gabanin musulunci sun kasance suna rataya bit da tsirkiya da duwatsu,
da zare, da sadafar lu'ulu'un da suke kawo su daga teku, suna rataya su a
qiraza, ko a jikin yaransu, da raquma da dokuna, da dabbobi, domin neman
tunkuxe kanbun-baka da maita da cutuka, da matsaloli, da zogi-zogi.
Akwai daga mutane, waxanda suke riqan
wani tsumma, ko takarda, ko fatar da aka rubuta zane-zane xalasim waxanda ba a
san ma'anarsu ba, da kuma sunayen wasu aljanu da shexanu, sai ya riqa neman
agajinsu, ya riqa kiransu, sa'annan ya rataya shi ga damtsensa, ko wuyansa, wai
yana neman kariya da kambun baka, da cuta.
Kuma haqiqa wasu musulmai sun aukan
cikin haka, saboda jahiltar Allah, da qarancin basira. Kuma haqiqa Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya yi umarnin a yanke
layoyi, kuma ya yi hani kan rataya tsirkiyoyi ga dabbobi, kuma ya tura a cikin
dakarun yaqi wanda zai gusar da wannan, kuma ya tsinka tsirkiyoyi, kuma ya ce:
Kada a bar wata sarqa a wuyan wani raqumi, na tsirkiya, face an yanke ta daga
wuyan. Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma Annabi (SAW) y ace wa sahabi
Ruwaifi'I bn Sabit –رضي الله عنه- "Ya kai Ruwaifi'i, la'alla
rayuwa zata maka tsayi a bayana, sai ka baiwa mutane labari, cewa lallai wanda
ya xaure gemunsa, ko ya rataya wata tsirkiya, ko kuma ya yi tsarki da kashin
dabba, ko qashi, to lallai annabi Muhammadu ya barranta daga gare shi", Ahmad ya ruwaito shi da Nasa'iy.
Kuma an ruwaito daga Uqbah bn Amir
Aljuhaniy, ya ce: "Wasu mata sun zo wurin Manzon
Allah –صلى الله عليه وسلم-
domin su masa mubaya'a, sai ya yi mubaya'a ga mutane tara, bai yi mubaya'a ga
xayan ba, Sai aka ce masa: Ya Ma'aikin Allah! Me yasa baka yi mubaya'a ga
wannan ba? Sai ya ce: Lallai yana rataye ne da laya a jikinsa. Sai ya shigar da
hannunsa sai ya yanketa, Sai Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya masa mubaya'a, sa'annan sai Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: Wanda ya rataya
laya, to lallai ya yi shirka",
Ahmad ya ruwaito shi.
Kuma sahiri da dabo da rufa-ido da
bokanci sun yaxu a zamanin jiya da yau, a wajen maza da mata, daga kowane
mataki, da vangarori, Sai Manzon Allah –صلى الله عليه
وسلم- ya ce: "Baya cikinmu, wanda ya yi canfi ko aka masa canfi, ko ya yi bokanci,
ko aka masa bokanci, ko ya yi sihiri ko aka masa sihiri. Kuma duk wanda ya je
wurin boka, sai ya gaskata shi akan abinda y ace, to haqiqa ya kafirce da abinda
aka saukar wa annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم-", Albazzar ya ruwaito shi.
Kuma ya ce: "Wanda ya je wurin boka, ko mai duba, sai ya gaskata shi kan abinda ya
ke faxa, to haqiqa ya kafirce da abinda aka saukar wa Muhammadu –صلى الله عليه وسلم-", Abu-dawud ya ruwaito shi da Tirmiziy.
Kuma ya ce: "Wanda ya je wurin mai duba, sai ya tambaye shi kan wani abu, ba za a
karva sallar darare arba'in ba",
Muslim ya ruwaito shi.
Kuma yana daga cikin munanan hanyoyi,
Neman tsarkake mutane da shehunai, da wuce iyaka ga zatinsu, ko qudurta cewa
suna da ikon jujjuya duniya, ko wani tasiri a cikinta, da riya cewa sun san
gaibu.
Kuma daga cikinsu akwai wanda ke
gudurta cewa, lallai gani sau xaya daga waliyyi, ko samun karvuwa daga gare
shi, yana tseratar da muridi daga faxawa wuta, ko ya amintar da mutum daga
azaba, ya rubuta masa karvuwa. Kuma wani fajircin ne, da karkacewa da vata,
yafi wannan girma!
Daga cikinsu kuma akwai wanda ke
tabarrakin neman albarka da yawun waliyyi, ko shehi, ko gashinsa, ko jikinsa. Kamar
yadda sahabbai suke tabarrakin neman albarka da zatin Annabi –صلى الله عليه وسلم-. Sai dai kuma tir da waxancan
kwakwalen da suke yin qiyasin wani mutum ko wani shehi, da shugaban manzanni;
annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- har su ajiye shi a matsayinsa!!
Daga cikinsu akwai waxanda suka xauki
zikiri a matsayin abu na cashew da suka qirqiro, kamar rawa da kekkewayawa, da
tunzura, da tsalle-tsalle, da gudu, da karkata kayuka, da kafaxu, da ruku'i.
Sai ku kiyaye –Ya ku bayin Allah- daga
waxancan casun na bidi'a, waxanda suke lalata addini, kuma suke caccanza
alamomin shari'a, suke kawo qari a cikin musulunci da abubuwan da basa cikinsa,
kuma suke yin qari a cikin ibada da abinda shugaban halittu annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- bai bautar da mutane
da shi ba, ko kuma wani daga cikin Sahabbai. Wanda kuma ana qirga ta a matsayin
fita daga Sunnah ko shiriyar ma'aiki. Alhalin kuma baya halatta ga wani mutum
ya sunnanta wa mutane nau'i xaya daga ibada, ko addu'oi da zikirori, baicin
abinda Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya sunnanta. Kuma baya halatta ga wani daga cikin musulmai ya
yi xa'a ga musu qirqiro abubuwa, su cusa su cikin addini.
Kuma a cikin abinda aka shar'anta, na Sunnah,
akwai samun manufofi maxaukaka, da hikimomi mabayyana.
Ina faxan abinda kuka ji, kuma ina
neman gafarar Allah; sai ku nemi gafararSa, Lallai shi ya kasance Mai yawan
gafara.
HUXUBA TA BIYU
Ya ku musulmai!!!
Ku
sanya Allah ya zama ajiyanku domin lokacin buqata, kuma mafaka a gare ku, kuma
abin nufinku, saboda shine ya cancanci yabo mafi cika, da godiya mafi girma, da
maxaukakin girmamawa, kuma bauta bata dacewa, sai a gas hi, kuma qan-qan-da kai
baya dacewa sai ga girmansa, Maxaukaki, Mai tsarki, Abin yabo Mai girma,
Mabuwayi, saboda Allah ya xaukaka daga barin abokin tarayya, ko kini, ko uwa ko
xa, shi ne "Ubangijin Sammai da qasa, da abinda ke
tsakaninsu, sai ka bautata masa, kuma ka jure wajen yin bauta a gare shi, Shin
ka san wani takwara a gare Shi", [Maryam:
65].
Shin –Ya Muhammadu- dangane da Ubangijinka da muka umarce ka da
yin bauta a gare shi, da kuma haqurtar da rai kan yin xa'a a gare shi, shin ka
san wani takwara a gare shi, ta fiskar kyautarsa da baiwarsa, sai ka bauta
masa, kana mai fatan samun falalarSa da ni'imarSa, in ba Allah ba. A'a! lallai babu
wani abu mai kama da haka.
Wanda ya rataya
ga Allah, to ya wadace shi, wanda kuma ya dogara akansa, sai ya kare shi, wanda
ya nemi mafaka a wurinsa sai ya kiyaye shi, ya jivinci lamarinsa.
Ta yaya, bawa zai
firgita a lokacin buqatarSa, ko cikin tsanani, zuwa ga qabari da matattu, ko
duwatsu da gawa, ko zawiya da maqamomin shehunai.
Kuma ta yaya mutum zai nemi agajin
matattu, yana roqonsu, ya xaga sauti yana qabari da maqamomin shehunai, yana
nuna fatansa.
Kuma ta yaya mutum zai nemi tsarin
matattu, ko ya nemi mafaka daga abinda babu shi.
Kuma yaya mutum zai nemi taimako daga
tsirkiya da guraye da layoyi da abubuwan da ake ratayawa, kuma ya qudurta cewa
sune masu tunkuxe bala'oi ko kiyaye mutane, suke basu kariya, suke warkarwa,
suke tsarewa, alhalin Ubangijinmu yana cewa:
"Kuma idan
Allah ya shafe ka da wata cuta, to babu mai yaye masa idan ba shi ba, Idan kuma
ya shafe ka da wani alkhairi, to shi mai iko ne akan komai * Kuma shine
Maxaukaki a saman bayinsa, kuma shine Mai hikima Masani", [An'am: 17-18].
Sai ku ji tsoron Allah –Ya ku musulmai-,
kuma ku nisanci abinda zai lalata muku addininku, kuma ku bi shiriyar Annabi
zavavve –صلى الله عليه وسلم-,
kuna masu lazimtar sunnarSa, kuma ku yi riqo da littafin Alqur'ani da Sunnah,
saboda sune kariya daga kowani sharri da fitina da bala'i.
Sai
ku yi salati da sallama ga Ahmad Mai shiryarwa, Mai ceton mutane gabaxaya;
saboda idan Mutum ya yi salati a gare shi guda xaya, sai Allah
ta'alah ya yi masa guda goma,
Ya Allah ka yi salati da sallama ga
bawanka kuma manzonka Muhammadu,
Kuma ya Allah ka
yarda da dukkan iyalan Annabi da sahabbai,
Ka haxa da mu, Ya Mai
karimci, Ya Mai yawan baiwa,
Ya Allah ka xaukaka musulunci da
musulmai,
Kuma ka qasqantar da shirka
da mushirkai,
Kuma ka halaka maqiya
wannan addinin,
Ka sanya wannan qasa ta
zama cikin aminci da zaman lafiya da sauran qasashen musulmai.
Ya Allah ka datar da shugabanmu
kuma jagoranmu izuwa ga abinda ka ke so, kuma ka yarda,
Ka kama qeyarsa izuwa
biyayyarka da aikin taqawa
Ya Allah ka datar da xaukacin masu
jagorantar lamuran musulmai izuwa ga yin hukunci da shari'arka,
da bin sunnar annabinka
Muhammadu (صلى الله عليه وسلم), Ya Ubangijin
halittu.
Ya Allah ka zama mai taimakon garin
Halab da Shaam,
Ya Allah ka tausaya wa rauninsu,
Ya Allah ka yaqi wanda ya yaqe su,
Ya Allah ka yaqi wanda ya yaqe su,
Ya Allah ka yaqi wanda ya yaqe su,
Ya Allah ka saukar da azaba da
qasqanci da fushinka ga wanda ya rushe gidajensu akansu,
Ya Allah ka kashe su da makaminsu,
ka qona su da wutar da su
ka fura,
Ya Ubangijin halittu.
Ya Allah ka tseratar da waxanda ake
ta raunana su daga cikin musulmai, a kowani wuri, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka kawo aminci a
iyakokinmu,
ka kare rundunoninmu,
ka taimake su akan
maqiyanka kuma maqiyansu,
Ya Ubangijin halittu.
Ya Allah ka karvi matattunsu cikin
shahidai,
ka warkar da wanda aka yi
masa rauni daga cikinsu,
Ya Mai amsa addu'a.
Ya Allah ka sanya addu'anmu ya zama
karvavve,
Sautinmu kuma abun xagawa,
Ya Mai karimci, Ya Mai
girma, Ya Mai jin qai.
No comments:
Post a Comment