HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 09/MUHARRAM/1439H
daidai da 29/SATUMBA/ 2017M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH ALIYU BN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
,,
Shehin Malami wato: Aliyu
bn Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken:,,, Wanda kuma a cikinta ya
tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah Mai
hikima Maxaukaki, Ma'abucin nau'ukan girma, da xaukaka,
Ina yabo ga Ubangijina, kuma ina gode masa akan
ni'imominSa waxanda babu mai qididdige su, face Shi,
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya, sai Allah shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, ma'abucin
falala da baiwa.
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, Wanda aka kevance shi da
fiyayyun xabi'u da halaye,
Ya Allah! ka yi salati, da
sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka; Muhammadu, da iyalansa da
sahabbansa, masu gaggawar aikata kyawawan ayyuka.
Bayan haka:
Ku bi Allah Ta'alah
da taqawa, ta hanyar kusantarsa da abinda ya ke so, kuma ya yarda, da kuma nisantar
dukkan ababen da ya ke qi; baya so. Saboda taqawa, ita ce, ta ke gyara kowane
abu, a wannan rayuwar, kuma da ita ake samun darajoji a bayan mutuwa, Allah
Ta'alah ya ce: "Kuma duk wanda ya
yi taqawar Allah zai sanya masa sauqi a lamarinsa" [Xalaq: 4].
Kuma ya ce: "Wancan Aljannar ce
wacce muke gadar da wanda ya kasance mai aiki da taqawa, daga bayina" [Maryam: 63].
Ya ku, Musulmai…
!!!
Lallai shari'ar Allah mai
tsarki ta yi umarnin samar da haxin kai da daidaito (ittifaqi), ta kuma yi hani
kan savani da rabuwar kai, domin kiyaye addinin musulunci, wanda rayuwa bata tsayuwa face da shi, kuma ba a
samun Aljanna idan ba a yi aiki da musulunci ba. Kuma domin kiyaye zamentakewar
al'umma daga kekkecewa, da wargajewa, da zaman kara-zube, da jayayya, da
zalunci, da varna. Kuma domin kiyaye al'umma daga cin karo, da rabuwar kai, da
qiyayya, da yin faxa da juna. Kuma domin kiyaye maslahohi da amfanoni da haqqoqi
na xaixaiku da na al'umma. Kuma domin samar da kwanciyar hankali da adalci da
zaman lafiya, Kuma domin waxannan manufofin ne gabaxayansu, Allah (S.W.T) ya yi
umarni kan haxin kai, ya kuma yi hani kan savani, a inda ya ke cewa: "Kuma ku yi riqo da
igiyar Allah gaba xaya, kada ku rarraba, kuma ku tuna ni'imar Allah akanku, a
lokacin da kuka kasance maqiya, sai ya daidaita tsakanin zukatanku, sai kuka
wayi gari da ni'imarSa, 'yan'uwa. Kuma kun kasance akan gavar ramin wuta, sai
ya tsamar da ku daga gare ta, Kamar haka, Allah yake bayyana muku ayoyinSa,
domin ku samu shiriya"
[Ali-imrana: 103].
Kuma Allah ya ce: "Kuma ku taimaki
juna akan aikin kwarai da taqawa, kuma kada ku taimaki juna akan zunubi da
zalunci"
[Ma'ida: 2].
Kuma Allah Mabuwayi da
xaukaka ya ce: "Kuma mumunai maza da mumunai mata, sashen majivincin sashe ne" [Tauba: 71].
Kuma Allah Ta'alah ya ce:
"Kuma Lallai muminai 'yan'uwan juna ne" [Hujurat: 10].
Kuma Allah Mabuwayi da
xaukaka ya ce: "Sai ku tsayar da sallah, kuma ku bayar da zakkah, kuma ku yi riqo da
Allah; domin shi ne majivincinku, madalla da Shi ya zama majivinci, madalla da
Shi ya zama Mai taimako" [Hajj: 78].
Kuma Allah Ta'alah ya ce:
"Kuma duk wanda ya yi riqo da Allah, to lallai an shiryar da shi zuwa
hanya miqaqqa",
[Ali-imran: 101].
√Kuma an ruwaito daga Abu-Musa
(رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Mumini ga mumini,
kamar gine ne wanda sashensa ke qarfafar sashe", Sai ya shigar da
yatsu a cikin yatsunsa. Bukhariy da Muslim suka ruwaito.
Kuma an ruwaito daga
An-Nu'uman bn Bashir (رضي
الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Misalin muminai, cikin soyayyarsu da
jin-qai ga junansu, da tausasawarsu, misalin jiki ne guda xaya. Idan wata gava
ta yi rashin lafiya, sai sauran jikin ya taya ta rashin barci da jin zafi", Bukhariy da Muslim suka
ruwaito shi.
Kuma an ruwaito daga
Abu-hurairah (رضي
الله عنه), ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Kuma ku kasance –Ya ku bayin Allah-
'yan'uwan juna",
Muslim ya ruwaito.
Riqo da juna da haxuwar
kai, da kyakkyawar alaqa da daidaito da taimakon juna, da jin-qan juna, da
taimakon gaskiya, da watsar da savani ko rarrabar kai, garkuwa ne da al'umma ke
fakewa a jikinsu, kuma mafaka ce da ta wadaci dukkan mutane, kuma dalilin
aminci ne ga al'umma, kuma samun qarfi ne ga addini, kuma kariya ne na kiyaye
amfanonin duniya, kuma samaki ga fitintinu masu vatarwa, kuma aminci da samun
kariya daga makirce-makircen maqiya da cutarwarsu.
Kuma kamar yadda Allah
Ta'alah ya yi umarnin a kiyaye alaqar al'umma da qarfinsu da jin-qan da ke
tsakaninsu, To, haqiqa ya yi hani, kan yanke zumunci da baiwa juna baya, da
savani, da rabuwar kai, da zaman kara zube, da buxe qofar sharri; Allah Ta'alah ya ce: "Kuma kada ku
kasance kamar waxanda suka rarrabu, kuma suka sava wa juna, bayan hujjoji sun
zo musu, kuma waxannan suna da azaba mai girma", [Ali-imran: 105].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ka da ku yi
jayayya, har ku raunana, sai qarfinku ya tafi, kuma ku yi haquri, saboda Allah
yana tare da masu haquri" [Anfal: 46].
Kuma Allah (سبحانه) ya ce: "Kuma kada ku
kasance daga mushirkai * wato, waxannan da suka rarrabe addininsu, kuma suka
kasance qungiya-qungiya, kowace qungiya da abinda ke wurinsu suna masu alfahari" [Rum: 31-32].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Musulmi xan'uwan
musulmi ne, baya zaluntarsa, baya qin taimakonsa, baya yin qarya a gare shi,
kuma baya raina shi, … kowane musulmi ga xa'uwansa musulmi, jininsa da
dukiyarsa da mutuncinsa haramun ne", Muslim ya ruwaito shi, daga hadisin
Abu-hurairah (رضي
الله عنه).
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Musulmi xan'uwan
musulmi ne, baya zaluntarsa, kuma baya qyale shi", Bukhariy da Muslim
suka ruwaito shi, daga hadisin Abdullah ibn Umar (رضي الله عنهما).
Kuma Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Musulmi xan'uwan
musulmi ne, baya ha'intarsa, baya masa qarya, kuma baya qin taimakonsa", Tirmiziy ya ruwaito
shi, daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه).
Waxannan dalilai, hani ne da tsawatarwa kan tozartar da
haqqoqin (masu haqqoqi), waxanda tozarta sun ke rarraba kawunan musulmai.
Kuma yana daga WASIYYOTIN ANNABI MASU AMFANI, wanda ta qunshi umarni
kan, haxe kai, da zamewa abu xaya, da tara hankali wuri guda, ta kuma yi hani
kan, rarraba kai da savani, sai ta haxe lamarin addini da duniya = Faxinsa (صلى الله عليه وسلم) ga sahabbansa: "Ina muku wasici, da
taqawar Allah, da jin umarnin shugabanni, da kuma biyayya, koda bawa ne ya ke
mulkarku, saboda duk wanda ya yi tsawon rai daga cikinku, to zai ga savani
dayawa, sai ku yi riqo da sunnata, da sunnar khalifofi shiryayyu, ku yi riqo da
su, da fiqoqi. Kuma ina tsawatar da ku qirqirarrun lamura, domin kowace bidi'a
vata ce",
Abu-dawud da Tirmiziy suka ruwaito shi, kuma Tirmiziy ya ce: hadisi ne hasan sahih. Daga hadisin Irbadh bn
Sariyah (رضي الله عنه).
Kuma yana daga RAHAMAR
ALLAH ga musulmai, yadda ya tsawatar da su, kan FITINTINU MASU GAMEWA, a inda Allah
Mabuwayi da xaukaka ya ke cewa: "Kuma ku ji tsoron fitina, wanda bata samun
waxanda suka yi zalunci a cikinku a keve, kuma ku sani lallai ne Allah, Mai
tsananin uquba ne"
[Anfal: 25].
Maluman tafsiri, suka ce:
"Ku kiyayi sabubban kowace fitina mai cutarwa, wanda za su bijirar da
ku, ga uqubar Allah Ta'alah".
Kuma kamar yadda shari'a mai tsarki ta yi hani, kan
fitina mai gamewar cutarwa, kuma ta tsawatar akansu; saboda abinda ke cikinsu
na cutarwa, to lallai ta yi hani kan kevantacciyar fitina, wanda ta ke cutar da ma'abucinta, sai kuma
ta cutar da mutane gaba xaya, saboda shari'a ta tsawatar kan vangarewar
xaixaiku daga cikin jama'ar musulmai, domin an ruwaito daga Abu-zarrin (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Duk wanda ya rabu
da jama'a daidai da taqi xaya, to lallai ya sunce dabaibayin musulunci daga
wuyarsa",
Abu-dawud ya ruwaito shi.
Kuma an ruwaito daga Abdullah
ibn Umar (رضي الله عنهما), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Al'ummata ba za ta
haxu akan vata ba, sai ku yi riqo da jama'a, saboda hannun Allah yana kan
jama'a",
Xabaraniy ya ruwaito shi.
Kuma an ruwaito daga Mu'awuya
(رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya mutu,
alhalin babu bai'a a wuyansa, to ya yi mutuwa irin ta jahiliyya", Xabaraniy ya
ruwaito shi, a cikin mu'ujam Kabir.
Kuma an ruwaito daga Abu-zarrin
(رضي الله عنه) lallai shi, ya yi
inkari yin sallah a Mina raka'oi huxu, ga khalifa Usmanu (رضي الله عنه), sa'annan ya tashi ya yi raka'oi huxun
tare da shi. Da aka yi masa maganar cewa ya aibanta yin raka'oi huxu ga amirul
muminina, sai kuma ka aikata hakan. Sai ya ce: "Savani yana da
tsanani, savani sharri ne", Ahmad ya ruwaito shi.
Kuma yana daga abinda shari'a
ta TSAWATAR AKANSA, FITINUWA
DA DUNIYA, DA KUMA BARIN YIN AYYUKAN LAHIRA, KO MANCEWA DA ITA.
Kuma lallai, samun rabo, wato cikakken rabo, yana nan ne,
cikin yin aiki domin lahira, da kuma yin aiki don gyara duniya, da raya ta, da
dukkan abu mai amfani, da fa'ida, wanda zai xaukaka addini, kuma zai biya buqatun
musulmai, kuma ya bada kariya ga mutum musulmi daga qasqancin da ke cikin,
xabi'ar roqo, har ya shumfuxa hannunsa da ciyarwa, ta qofofin alkhairi, Allah
Ta'alah ya ce: "Ya ku mutane lallai alqawarin Allah gaskiya ne, don haka, kada
rayuwar duniya ta ruxe ku, kuma kada shexan maruxin nan ya ruxe ku, game da
Allah",
[Luqman: 33].
Kuma Allah ya ce: "Kuma wannan rayuwar
ta duniya ba komai ba ce, face abar shagala da wasa, kuma lallai lahira, ita ce
rayuwa, da sun kasance suna sani", [Ankabut: 64].
Kuma Allah Ta'alah ya ce:
"Kuma kowace rai mai xanxanar mutuwa ce, kuma kawai za a cika muku
ladanku ne, a ranar qiyama, kuma wanda aka nisantar da shi daga barin wuta,
kuma aka shigar da shi aljannah, to haqiqa ya yi babbar rabo, kuma rayuwar
duniya bata kasance komai ba, face jin daxin ruxi", [Ali-imrana: 185].
Saboda shi fiskantar duniya, ta hanyar tara kayan
cikinta, ta halal da haram, uquba ne ga ma'abucinsa, da cutarwa da sharri ga
xaukacin al'umma.
Kuma tara duniya, ta hanyar ta'addanci ga haqqoqin wasu,
da zaluntarsu cikin haqqoqinsu, da dukiyoyinsu, yana rarraba kan mutane, kuma
yana kawo raunin alaqoqi da danganta.
Shi kuma yin tseren tara duniya, tare da nuna kwaxayi da
rowa, da husuma, yana yin jagora, zuwa ga haifar da qiyayyar zukata, da
abaucewarsu, da nuna rashin sani ko sabo; An ruwaito daga Uqbah bn Amir (رضي الله عنه) ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya yi salla, ga waxanda aka kashe a yaqin
Uhud, sa'annan ya hau minbari, kamar mai yin bankwana ga rayayyu da matattu, a
inda ya ce: "Lallai ne Ni mai jiranku, a tafkin alkausara ne, kuma lallai faxinsa
kamar tsakanin garin Aila da Juhfa ne. Kuma lallai ne ni bana tsorace muku yin
shirka a bayana, sai dai ina tsorace muku duniyar da za ku yi rigaggeniyar tara
ta, har ku yi ta karkashe juna, sai ku halaka kamar yadda al'ummar da ke
gabaninku ta halaka",
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi, kuma lafazin na Muslim ne.
Kuma an ruwaito daga Abu-sa'id
(رضي الله عنه), lallai Manzon
Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai ne duniya, tana
da zaqi, kuma koriya ce, kuma lallai Allah zai baku mayewa a cikinta domin ya
ga yadda za ku aikata, ku saurara! Ku kiyayi duniya, kuma ku kiyayi mata", Muslim ya ruwaito
shi.
Kuma DUNIYA, Ita ce, ta kange yawa-yawan mutane, daga
addinin Allah Ta'alah, da qawan cikinta, da kayan daxinta dana sha'awowinta, da
kayan cikinta, Allah Mabuwayi da xaukaka ya ce: "Kuma bone ya
tabbata ga kafirai daga azaba mai tsanani * waxanda suka fi son rayuwar duniya
fiye da lahira, kuma suna kangewa daga hanyar Allah, kuma suna neman ta
karkace, waxancan na cikin vata mai nisa", [Ibrahim: 2-3].
Farkon savanin da aka samu a cikin wannan al'ummar ita
ce, vangarewar munafikai da ficewar khawarijawa ga shiryayyen shugaba; Usman (رضي الله عنه), Abinda ya janyo hakan kuma, son duniya
ne, kamar yadda ya tabbata, kuma ya ke rubuce a tarihi, sun yi hakan, suna masu
kwaxayin samun matsayi irin na duniya, sai dai basu sami komai ba face baqin
ciki da wulaqanci, da haramta musu buqatunsu, da qiyayya, kuma sai suka halaka
xaya bayan xaya, akan mummunan hali, A'uzu billahi. Allah Ta'alah ya ce: "Sai aka shamakance
tsakaninsu da tsakanin abinda suke sha'awa, kamar yadda aka aikata da irin
qungiyoyinsu a gabaninsu. Lallai sun kasance cikin shakka mai sanya kokonto" [Saba'i: 54].
Kuma lallai a cikin wannan zamanin wanda annabta ya qara
nisa, Duniya ta qare zamewa fitina ga mutane dayawa, saboda husumomi suna
kasancewa ne domin duniya, qulla alaqoqi da 'yan'uwantaka suna yi ne domin
samun amfanin duniyar, daidaito kuma suna samar da shi akan maslahohinta, qin
juna da yanke zumunci da qauracewa juna suna yi ne akan duniya, baiwa mutane
matsayi su kan alaqanta shi da saninsu ga duniya, sai Duniya ta zama babban
sababin sassavawar ra'ayoyi, sai kuma soyayya don Allah, samunta ya yi qaranci,
Abdullah ibn Abbas (رضي
الله عنهما) ya ce: "Haqiqa, yawa-yawan
'yan'uwantakar mutane a yau, ta kasance akan lamarin duniya, wannan kuma baya
amfanar da ma'abutansa da komai", Ibnu-Jarir ya ruwaito shi.
SAMUN KARIYA DAGA SHARRIN FITINAR DUNIYA, zai kasance ta
hanyar Musulmi
ya san, matsayin duniya a wurin Ubangiji Mabuwayi da xaukaka, da irin matsayinta a
wurin AnnabinSa (عليه
الصلاة والسلام), domin an ruwaito daga Sahl bn Sa'ad (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Da duniya ta kai daidai
da fiffiken sauro a wurin Allah, to da bai shayar da kafiri abinda ke cikinta,
ko daidai da kurvin ruwa xaya ba", Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma ya inganta
shi.
Da kuma tuna halin sahabbai (masu zaman masallaci) ma'abuta
suffa, daga cikin wanda suka yi hijira, da yadda suka qaurace wa duniya, domin Abu-hurairah (رضي الله عنه) ya ce: "haqiqa na ga mutane
saba'in daga cikin mutanen suffar masallaci, babu wani da ke da mayafi, sai dai
kwarjalle ko rigar da suka xaura ta ga wuyoyinsu, daga cikinsu akwai wanda ke
kaiwa izuwa rabin kwabrinsa, daga cikinsu kuma akwai wanda ke kaiwa ga idanun
sawu biyu, sai ya tattara tufan da hannunsa, tosron kada a ga al'aurarsa", Bukhariy ya ruwaito
shi.
Kuma an ruwaito daga
Abu-sa'id (رضي الله عنه) ya ce: "Na zauna a cikin
wata jama'a daga raunanan waxanda suka yo hijira (wato, muhajirai), kuma lallai
sashensu yana vuya a bayan sashe, saboda tsoron bayyanar tsiraici, sai Annabi
S.A.W ya zo ya tsaya akanmu, sa'annan ya ce: Albishirinku –ya ku talakawan masu
hijira- da samun cikakken haske a ranar qiyama, domin za ku shiga Aljannah
gabanin mawadatan mutane, da tsawon rabin yini, wannan kuma daidai da shekaru
xari biyar kenan",
Tirmiziy ya ruwaito shi, da Abu-dawud, kuma wannan lafazin nasa ne.
Kuma, Ku –ya ku taron musulmai- an shumfuxa muku arziqin
duniya ne, da jihadin da waxancan muhajiran suka yi, sai ku yi godiya wa Allah
akan hakan, kuma ku bauta masa, kada ku sava masa.
Saboda gujewa duniya (zuhudu) yana daga sabbuban samun
kariya daga husumomi da jayayya, Annabi (صلى الله عليه وسلم ) ya ce: "Ka guje wa duniya sai Allah ya so ka, kuma
ka guje wa abinda ke hannun mutane, sai mutane su so ka", Ibnu-Majah ya
ruwaito shi daga hadisin Sahal bn Sa'ad As-Sa'idiy (رضي الله عنه).
Nawawiy ya ce, hadisi ne
hasan.
Kuma zuhudu shi ne qauracewa haramun da barin haramun, da
wadatuwa da abinda Allah ya baka. Da yin aiki domin lahira, da rashin karkata
zuwa ga duniya, da rashin samun natsuwa da ita duniya, kuma ka hana ranka tava
abinda ke hannun mutane, kuma kada ka yi hassada ga wani, akan abinda Allah ya
bashi.
Ya
ku musulmai …
Lallai yana daga cikin
SABUBBAN KARE AL'UMMA DA KIYAYE SU, KUMA SU ZAMA ABU XAYA, SU YI QARFI, SU
TABBATU A GABAN GUGUWAR FITINTINU, HAR SU IYA TUNKUXE MAKIDAR MAQIYA, DA VARNAR
KOWANE MA'ABUCIN SHARRI, YIN DAWWAMAMMEN NASIHA GA
MAJINTA LAMARI (SHUGABANNI), DA IRIN SALON NASIHAR MAGABATAN KWARAI,Domin ma'anar faxin Allah
koyaushe ya tabbatu: "Kuma ku taimaki juna akan aikin kwarai da taqawa" [Ma'ida: 2].
Kuma Manzon Allah (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Lallai ne Allah ya
yarda da abu uku a gare ku, ya yarda ku bauta wa Allah kada ku haxa shi da
kowa, kuma ku yi riqo da igiyar Allah gaba xaya, kada ku rarraba, kuma ku riqa
nasiha ga wanda Allah ya jivintar masa da lamarinku", Muslim ya ruwaito
shi daga hadisin Abu-hurairah.
Allah Ta'alah ya ce: "Ya ku waxanda suka
yi imani ku yi xa'a ga Allah, kuma ku yi xa'a ga ManzonSa, da ma'abuta al'amari
daga cikinku. Idan ku ka yi jiyayya a cikin wani lamari, to ku mayar da shi ga
Allah da ManzonSa idan kun kasance kun yi Imani da Allah da ranar lahira,
wannan shine mafi alheri, kuma mafi kyau ga makoma" [Nisa'i: 59].
Allah ya yi mini albarka NI
da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI
da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman
gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi,
Ku nemi gafararSa, lallai shi Mai
gafara ne Mai rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah Mabuwayi Mai hikima, Mai haquri
Mai jin-qai, Ina yin yabo ga Ubangijna, kuma ina gode masa, akam ni'imominSa,
waxanda waninsa ba zai iya qididdige su ba,
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya,
Maxaukaki Maigirma,
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu shugabanmu Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa, wanda Allah ya shiryar
da halittunsa da shi, zuwa ga hanya madaidaiciya,
Ya Allah ka qara salati da
sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa, da
sahabbansa, masu bin tafarkinsa miqaqqe.
Bayan haka … !!
Ku yi tsoron Allah, a
sirrace da kuma a bayyane, saboda taqawar Allah ita ke kiyaye ni'imomin da suke
nan, kuma take qaro ni'imomi masu zuwa wanda basu nan, Allah Ta'alah ya
ce: "Yak u waxanda suka
yi imani ku bi Allah da taqawa, kuma ku faxi Magana madaidaiciya * Zai kyautata
muku ayyukanku, ya gafarta muku zunubanku, kuma wanda ya yi xa'a ga Allah da
ManzonSa, to lallai ya rabauta da babban rabo mai girma" [Ahzab: 70-71].
Ya ku Musulmai … !!
Lallai yana daga ABINDA
MUSULUNCI YA TSAWATAR AKANSA, KURAKURAN HARSHE DA AYYUKANSA MASU HALAKARWA,
saboda maganar baka, da rubutun alqalami, suna iya raba kan mutane, su wargaza
dunqulalle, har su kawo mummunan savani a tsakanin fiskoki, da samar da
mabanbantan ra'ayoyi, su vatar da mutane daga bin gaskiya, tare da faxaxa
girman da'irar savani, Manzon Allah (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Wanda ya yi imani
da Allah da ranar lahira, to ya faxi alheri ko ya yi shiru", Bukhariy da Muslim
suka ruwaito shi daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه).
Kuma a lokacin da Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya tsawatar kan fitintinu, sai bayyana
mana, ba sau xaya ba, ba sau biyu ba, cewa: lallai faxin varna a lokacin
fitina, halaka ne, a inda ya ce: "Harshe a cikin fitina yafi suka fiye da
tsananin sukar takobi",
Tirmiziy ya ruwaito shi da Abu-dawuda daga hadisin Abdullah ibn Amrin (رضي الله عنهما). Kuma ya sake cewa: "Kuma varnar harshe
a lokacin fitina kamar suka ne da takobi", Abu-dawud ya ruwaito shi daga hadisin
Abu-hurairah (رضي
الله عنه).
Ya faxi hakan, domin
jin-qan wannan al'ummar, kuma domin ya kashe wutar fitina.
Ya ku bayin Allah,
Ku nemi, dawwamar ni'imar
aminci da kwanciyar hankali da zaman lafiya, da wadaci a cikin rayuwa, ta
hanyar, kusantar Majivincinmu Allah, da ibadodi, da nisantar laifuka na
haramun, Allah Ta'alah ya ce: "Sai su yi bauta ga Ubangijin wannan xakin *
wanda ya ciyar da su daga yunwa, kuma ya amintar da su daga tsoro" [Quraish: 3-4].
Ya ku Musulmai… !!!
"Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga
wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da
sallama ta aminci"
[Ahzab: 56].
……………………………
,,, ,,, ,,,
No comments:
Post a Comment