HUXUBAR
MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 10 /ZULHIJJAH/1438H
daidai da 01/SATUMBA/ 2017M
LIMAMI
MAI HUXUBA
DR.
ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY
TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
Shehin Malami wato: Abdulbariy bn Auwadh As-subaity –Allah ya kiyaye
shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: RAYUWARMU TA GABA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna,
بسم الله الرحمن
الرحيم
HUXUBAR FARKO
Bayan haka:
Yana daga dacen da Allah ke yi wa bawa, mutum ya zartar da rayuwarsa
gaba xaya, a qarqashin inuwar BIYAYYA GA ALLAH, da kuma cikin
ni'imarta, Allah ta'alah ya ce: "Kuma ku sani lallai a cikinku akwai
Manzon Allah, dazai muku biyayya a cikin dayawa daga lamari, da kun faxa
wahala, saidai Allah ya soyar da Imani a gare ku, kuma ya qawata shi a cikin
zukatanku, kuma ya qyamatar da kafirci da fasicci da savo a gare ku, Waxannan
sune shiryayyu" [Hujurat: 7].
Biyayyarka ga
Allah, riska ce daga gare ka, na haqqin Allahn da ya halicce ka, kuma ya ke azurtaka,
ya karramaka, ya fifita ka, Allah ta'alah ya ce: "Ya ku mutane, ku
bauta wa Ubangijinku da ya halitta ku, da waxanda su ke gabaninku, tsammaninku
za ku samu kariya * Wannan da ya sanya muku qasa shumfuxa, kuma sama gina, ya
kuma saukar da ruwa daga sama, sa'annan ya fitar da 'ya'yan itatuwa, don su zama
azurtawa a gare ku, kada ku sanya wa Allah kishiyoyi alhali kuna sani" [Baqara: 21-22].
Biyayyarka ga Allah tana xaukaka mutum, kuma ta game rayuwar mutum
gaba xayanta, ta fiskar zantuka da ayyuka, da yin shiru da motsawa, Allah
ta'alah ya ce: "Ka ce, lallai ne sallata, da yanke-yankena, da rayuwata da mutuwata,
ga Allah ne Ubangijin talikai * Bashi da abokin tarayya, da aikata haka aka umarce
ni, kuma ni ne farkon musulmai" [An'am: 162-163].
Wanda ke tafiyar da rayuwarsa cikin biyayyarAllah ana karrama shi,
kuma zai sami xaukakar da ke cikin kasantuwa tare da zavavvun halittu, Allah
ta'alah ya ce: "Kuma waxannan da su ka yi biyayya ga Allah, da manzonsa, to waxannan
suna tare da waxanda Allah ya yi ni'ima akansu; na Annabawa da siddiqai, da
shahidai da salihai, kuma waxannan sun kyautatu su zama abokan tafiya * wannan
kuma falala ne daga Allah, kuma Allah ya isa zama masani" [Nisa'i: 69-70].
Wani mutum ya
tambayi Annabi (صلى الله عليه وسلم) akan qiyama, sai ya ce: Mai ka tanadar mata? Sai ya ce: Babu
komai, saidai Ni ina son Allah da ManzonSa (صلى الله عليه وسلم), Sai ya ce: "Kai kana tare da waxanda ka ke so",
Anas ya ce:
Sahabbai bamu yi farin ciki ba da wani abu, rin farin cikin da muka yi da faxin
Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم): "Kai kana tare da
waxanda ka ke so".
Biyayya ga Allah haske ne ga basira,
kuma garkuwa daga tozarta da ximauta, tana tsare mutum daga gafala da savo, da
kuma waswasin shexan, Allah ta'alah ya ce: "Ina rantsuwa da rayuwarka, lallai ne
su, suna cikin mayensu suna ta ximuwa" [Hijr: 72].
Biyayyar Allah, tana cike rayuwa da imani, Sai zuciya ta gyaru, Idan
kuma zuciya ta gyaru, sai sauran jiki ya gyaru, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ku saurara! Lallai a
cikin jiki akwai wata tsoka; idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru, idan kuma ta
vaci dukkan jiki ya vaci; Ku saurara! Ita ce, zuciya".
Biyayyar Allah, tana yin rini ga rayuwar mutum cikin al'umma, sai
ta sanya musulmi ya zama yana yin sabo, ana sabawa da shi, yana murmushi yana
bayarwa, yana kyautatawa, yana xebe kewa tare da 'yan'uwansa, yana sonsu suna
sonsa, mai buxaxxen qirji, mai tsarkin rai daga qulle mutane ko hassada, baya
zalunci ba a zaluntarsa, Allah ta'alah ya ce: "Kuma ya daidaita
tsakanin zukatanku, da z aka ciyar da abinda ke cikin qasa, gaba xaya, da baka
daidaita tsakanin zukatansu ba, saidai Allah shi ya daidaita tsakaninsu, lallai
shi ne Mabuwayi Mai hikima" [Anfal: 63].
Kuma Manzon
Allah (صلى الله عليه
وسلم) ya ce: "Rayuka rundunoni ne da suke cikin xamara, duk waxanda suka sami
sanayya daga cikinsu sai su haxe, duk kuma waxanda basu samu sanayya ba, sais u
sami savani".
Kuma alaqar musulmi da xan'uwansa tana qaruwa, a lokacin da ke
tafiya wajen bashi kyauta, da biya masa buqatarsa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Musulmi xan'uwan
musulmi ne, baya zaluntarsa, baya qin taimakonsa, Wanda ya kasance cikin
buqatar xan'uwansa, to Allah zai kasance a cikin buqatarsa, kuma wanda ya
kwaranye wani baqin ciki ga musulmi daga baqin cikin duniya, Allah zai kwaranye
masa, da shi wani baqin ciki daga baqin cikin lahira,kuma wanda ya suturta
musulmi Allah zai sutura shi a ranar qiyama".
Kuma Biyayyar bawa ga Allah tana gadar masa da qaunar mutane da
sonsu, kuma ana sanya masa karvuwa a bayan qasa, Allah ta'alah ya ce: "Lallai waxanda su
ka yi imani, suka yi aiki na kwarai, da sannu Mai rahama zai sanya musu so" [Maryam:
96].
Kuma Manzon
Allah (صلى الله عليه
وسلم) ya ce: "Idan Allah ya so bawa, saiya kira Jibrilu cewa, lallai Allah yana
son wane, ka so shi, Sai Jibriru ya so shi, Sai Jibrilu ya kira ma'abuta sama,
cewa: Lallai Allah yana son wane, ku so shi, Sai ma'abuta sama su so shi, sa'annan
sai a sanya masa karvuwa a bayan qasa".
Biyayyar Allah it ace takobin mumini, a yaqin da yak e yi da
shexan, da lokacin fito-na-fito da rai, domin ta nisanci alfasha, Allah ta'alah
ya ce: "Lallai ne shexan bashi da qarfin iko akan waxanda su ka yi imani,
kuma ga Ubangijinsu su ke dogara * Abin sani kawai, qarfinsa yana akan waxanda
su ke jivintarsa, kuma waxanda suke su, game da shi mushirkai ne" [Nahl: 99-100].
Kuma Allah ya ce:
"Kuma ka tsayar da
sallah, lallai ne sallah tana hani ga alfasha da abin kyama, kuma ambaton Allah
shine yafi girma, kuma Allah ya san abinda kuke aikatawa" [Ankabut:
45].
Alamar mumini ita ce farin ciki da lokutan xa'a, da jin bushara da
aikin biyayya, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Duk wanda aikinsa mai kyau ya faranta masa rai, mummunansa ya
baqanta masa, to wannan mumini ne". kuma Allah ta'alah ya ce: "Yak u mutane,
haqiqa wa'azi daga Ubangijinku ya zo muku, da warakar abinda ke cikin qiraza,
da shiriya, da jin qai ga muminai * Ka ce: da falalar Allah, da jin-qanSa, sais
u yi farin ciki, shi ne mafi alheri daga abinda suke tarawa" [Yunus:
57-58].
Don haka, musulmi mai basira yak an yi kwaxayin waxannan lokatan;
sai ya yi gaggawa, ya yi sauri, ya yi rige, domin ya tsinka daga kayan amfanin
lokatan maxaukaka, da falalolinsu waxanda suke jere, Allah ta'alah ya faxa,
dangane da annabinSa Musa (عليه السلام): "Kuma na yi gaggawa, zuwa gare ka, Ya Ubangijina, domin ka yarda" [Xaha: 84].
Kuma Allah ta'alah
ya faxa, dangane da annabinSa; Zakariyya: "Sai muka amsa masa, muka masa baiwar
Yahya, muka gyara masa matarsa, lallai ne su, sun kasance suna yin gaggawa
cikin alkhairori, kuma suna roqonmu cikin kwaxayi da tsoro, kuma sun kasance a
gare mu, masu tawali'u" [Anbiya'i: 90].
>>>><<<<
Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya
kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai
hikima, Ina faxar abinda ku ke ji wannan, kuma
ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga
kowani zunubi, Ku nemi gafararSa, lallai shi Mai gafara ne
Mai rahama.
,,,
,,, ,,,
,,,
,,, ,,,
HUXUBA TA BIYU
Bayan
haka:
Idan aka buxe wa musulmi qofar yin biyayya ga Allah, to sai ya
xaga hannayen qan-qan-da-kai, yana roqon majivincinsa, cewa, ya tabbatar da shi
akan aikin biyayya, kuma ya tsawaita masa alkhairi tsawaitawa, Allah ta'alah ya
ce: "Allah ya tabbatar
da waxanda su ka yi imani, da magana tabbatacciya, a rayuwar duniya, da kuma a
lahira, kuma Allah yana vatar da azzalumai, kuma Allah yana aikata abinda yak e
so"
[Ibrahim: 27].
Kuma Manzon
Allah (صلى الله عليه
وسلم) ya ce: "Lallai zukatan xan-adam gaba xayansu, suna tsakanin yatsu biyu, daga
yatsun Mai-rahama, kamar zaciya xaya, yana jujjuyata yadda ya ke so". Sa'annan ya ce:
"Ya Allah, ya mai
jujjuya zukata, ka juya zukatanmu zuwa ga biyayya a gare ka".
Lallai shiga cikin ayarin masu biyayyar Allah, da bin sabbuban da
za su kai zuwa ga samun hakan, yana daga sabbuban samun taufiqi daga Allah, Allah
ta'alah ya ce: "Kuma waxannan da suka yi qoqari akan hanyarmu za mu shiryar da su
hanyoyinmu" [Ankabut: 69].
Kuma yana dag tavewa: HARAMTAWA MUTUM NI'IMAR DACEN BIYAYYAR
ALLAH, Allah ta'alah ya ce: "Zan karkatar da waxanda suke yin girman
kai a cikin qasa, daga ayoyina" [A'araf: 146].
>>>>>>>>>>>><<<<<<<<<<<<<<<<
Sai ku yi salati, -Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, saboda
Allah ya umurce ku da aikata haka, a cikin littafinsa; a inda yake cewa: "Lallai ne, Allah da
Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi Imani, ku
yi salati a gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati wa
Annabi Muhammadu da matansa da zurriyarsa, kamar yadda ka yi salati wa
Ibrahima, da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abin godiya ne Mai girma. Kuma
ka yi albarka ga annabi Muhammadu da matansa da zurriyarsa, kamar yadda ka yi
albarka wa Ibrahima, da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abin godiya ne Mai
girma.
Ya Allah! Ka yarda da
khalifofi guda huxu shiryayyu; Abubakar da Umar da Usmanu da
Aliyu, da iyalan annabi da sahabbai masu karamci, ka haxa da mu da baiwarka, da
rahamarka, Ya mafificin masu rahama.
Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
kuma ka qasqantar
da kafirci da kafirai, kuma
Ya Allah! Ka ruguza maqiyanka; maqiyan addini,
Ya Allah! Ka sanya wannan qasar ta zama da aminci, cikin
nitsuwa, da sauran qasashen musulmai.
Ya Allah! Ka kasance wa musulman da ake raunata
su a kowani wuri, ka kasance musu, Mai qarfafawa, Mai basu nasara, kuma Mai
taimako,
,,,
,,, ,,,
No comments:
Post a Comment