HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 24/ZULHIJJAH/1438H
daidai
da 15/SATUMBA/2017M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI SALAH BN MUHAMMADU ALBUDAIR
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Ya ku musulmai …
Yabo ya tabbata ga Allah Wanda
rahamarSa ta game dukkan komai, kuma ta yalwace su, kuma ni'imarSa ta cika wa
bayi ta kuma girmama,
Muna yin yabo a gare shi aka ni'imominSa
da suka jeru akanmu, kuma suka yalwatu,
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da
gaskiya; shi kaxai yak e bashi da abokin tarayya; shaidawar da take tseratar da
wanda ya furta ta, a ranar da kowace mai shayarwa zata shagala daga abinda take
shayar da shi,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu
Muhammdu bawanSa ne manzonSa, Wanda ya yi jihadi iyakar jihadi domin Allah, har
Kalmar tauhidi ta samu xaukaka
Allah ka yi daxin salati da sallama a
gare shi, da iyalansa da sahabbansa, a duk lokacin da mahajjata suka qanqan da
kai a wuraren bauta masu girma, ko suka yi addu'a.
Bayan haka:
Ya ku Musulmai
Ku ji tsoron Allah, saboda taqawarSa
itace hajar da tafi riba, kuma ku kiyayi savon Allah; domin bawan da ya yi
sakaci kan lamarin Allah, ko ya tozarta umarninsa to haqiqa zai tave, "Yak u waxanda suka yi Imani ku yi taqawar Allah, kuma ku faxi magana
madaidaiciya * Sai ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku,
kuma wanda ya yi xa'a ga Allah da ManzonSa to lallai zai rabauta da babban rabo
mai girma", [Ahzab: 70-71].
Ya ku Musulmai
Yin bautar Allah shine muqamin da yafi
xaukaka, kuma darajar da tafi zama qololuwa.
Kuma a cikin kwanaki qalilan da suka
shuxe ne, Mahajjata suka kammala ibadar da tana cikin manya-manyan ibadodi, da
xa'ar kusantar Ubangiji wanda take daga jerin manyan xa'oi, wanda a cikinta
suka tove xinkakkun tufofinsu daga miqatai, kuma hawayen tuba ya bayyana akan
kumatu a filin Arfah, kuma sautukan bayyanar da buqata zuwa ga Allah suka
xaukaku
To, lalen yin hajji ga mahajjata!
Kuma lalen yin bauta ga masu bauta,
kuma lalen qoqarin da suka nuna!!
Ya Mahajjatan xakin Allah mai alfarma
Ku yi godiya ga Allah akan abinda ya
baku, kuma ku yaba masa akan abinda ya muku baiwa, saboda yadda ya jera
kyautarsa a gare ku, ya kuma sadar da muku da alkhairinsa, ya game ku da
kyautukansa, ya cika muku falalolinsa ya kuma kammala muku su, domin "Babu wata ni'imar da ke tare da ku face daga Allah ne", [Nahl: 53].
"Kuma idan
kuka so qidaya ni'imar Allah, baza ku qididdige su ba, Lallai ne Allah Mai
gafara ne Mai jin qai", [Nahl: 18].
Ya Mahajjatan xakin Allah mai alfarma
Ku yi zaton kyawawa daga Ubangijinku,
kuma ku yi fatan alkhairi mai yawa daga gare shi, kuna masu qarfafa fatan
Allahn ya karva muku hajjinku, ya kuma kankare muku abinda ya shuxe na
zunubanku, domin y azo a cikin hadisin qudusiy: "Allah Ta'alah ya ce: Ni ina wurin da bawana ya ke zatona", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Ya ku Musulmai
Ya waxanda
suka hajjin xaki mai girma,
Kuka fito daga kowani longu mai zurfi,
Kuka xauko talbiyya daga kowani vangare
mai nisa,
To, ga kun nan, bayan hajjinku ya cika;
ya kammalu,
Bayan kun yi tsayuwa a waxancan wuraren
bauta,
Kun sauke waxancan ayyukan ibadodi,
Ga kun, nan kuna ta shirin kokkomawa gidajenku,
Sai ku kiyayi komawa cikin zunubai da
kuma cakuxa da ayyukan haramun, da kutsawa cikin aibobi, da shumfuxa cikin
ababen zagi, "Kuma kada ku kasance kamar wanda ta warware zarenta bayan tukka", [Nahl: 92].
Wata mace, mai wauta, mai qarancin hankali, wanda take wahala
safiya da maraice wajen sassaqa gashin dabbobi, har zuwa lokacin da ya zama
zare lafiyayye mai karfi, sai ta dawo tana warware gashinsa, tana kukkunce shi,
har ta mayar da shi bayan qarfinsa warwarerre, kuma sincacce, kuma bata tsinki
komai ba daga aikinta wahalar da kai da vata lokaci,
To kada ku kasance kamar wannan mata, har ku rushe abinda kuka
gina, ko watse abinda kuka tattara, ko ku since abinda kuka kyautata tufkansa.
Mahajjatan xakin Allah mai alfarma
Haqiqa kun buxe wani shafi mai haske
mai tsafta a cikin rayuwarku, kuka bayan hajjinku kun sanya tufafi masu tsarki,
Don haka, wallahi ku kiyaye komawa
cikin ayyukan wulaqanci, da bin hanyoyi masu vatarwa, ko ayyuka masu aibi,
Saboda tsananin kyan aikata aikin kwarai bayan aiki mai kyau,
da kuma munin aikata mummuna a bayan mai kyau.
Ya ku Musulmai
Lallai hajji mabaruri yana da alama, kuma
dangane da karvuwarsa akwai alamar haske, saboda an tambayi Alhasan Albasariy –رحمه الله تعالى- cewa Menene hajji
mabaruri? Sai ya ce, Ka koma kana mai qauracewa duniya, kana mai kwaxayin
lahira.
Hajjinku ya kasance shamaki ne daga aukawa
wuraren halaka, kuma mai hani daga ababen zamiya masu vata aiki, kuma ya
kasance mai zaburar da ku kan qara alkhairori da aikata ayyukan kwarai.
Kuma ku sani, Lallai mumini babu wani
lokacin da zai gama aikata ayyukan kwarai, sai lokacin zuwan ajali.
Ya ku Musulmai
Abu ne mai matuqar kyau, mahajjaci
bayan hajjinsa ya koma ga iyalansa da qasarsa da xabi'a mafi kamala, da hankalin
da yafi cika, da natsuwar da tafi cika, da kuma mutuncin da ake matuqar kiyaye
shi, da xabi'u yardaddu, da halayya masu karamci.
Me yafi, ace mahajjaci ya koma da
kyakkyawar mu'amala ga abokan zamansa, mai karamcin mu'amala ga 'ya'yansa, yana
mai tsarkakakken zuciya, yana bin salo irin na gaskiya da adalci da aikata
daidai, abinda ke cikinsa ya kasance yafi alheri akan abinda ke waje, wanda ya
vuya kuma ya kasance yafi abinda ya bayyana.
Kuma lallai wanda ya koma bayan
hajjinsa yana xauke da waxannan sifofin masu kyau, shine wanda a haqiqanin
lamari ya amfana da hajjinsa, da kuma hikimominsa da darussansa da fa'idodinsa.
Ya ku Musulmai
Lallai mahajjaci tun daga lokacin
talbiyyarsa, har y agama hajjinsa ya qare; to lallai dukkan ayyukansa na hajji suna
sanar da shi Allah, suna kuma tunatar da shi kan haqqoqinsa, da abinda ya
kevanta da sun a cancantar bauta ko uluhiyya,
da kasancewar babu wanda ya cancanci ayi masa bauta idan ba Allah ba.
Ya Mahajjatan xakin Allah mai alfarma
Ya waxanda kuka hanu daga ababen da
haramarku ta tsawatar akan tava su, a lokacin yin hajjin xakin Allah, lallai
akwai abubuwan da aka yi hani akansu a tsawon zamani da shekaru da rayuwa, sai
ku kiyaye tava su, ko kusantarsu, Allah Mabuwayi cikin xaukakarsa yana cewa: "Waxancan iyakoki
ne na Allah kada ku qetare su, kuma duk wanda ya qetare iyakokin Allah, to
waxannan sune azzalumai", [Baqara: ].
Ya ku Musulmai
Wanda ya amsa wa Allah, a lokacin
hajji, yana mai amsa kiransa, ta yaya a bayan haka zai amsa ga wani lamarin da
ya sava wa Qur'ani da Sunnah, da kuma shari'a.
Wanda ya amsa wa Allah a lokacin hajji,
to ya amsa masa a kowani wuri da zamani, ta hanyar amsa umarninsa, a duk inda
abin hawansa ya fiskanta.
Ya kai bawan Allah
Ya wanda lokutan xa'oi da rahamomi suka
shuxe masa, alhalin ya dulmuya cikin wargi da laifuka ababen qi, Shin baka ga
tawagar mahajjata da masu umrah da masu bauta ba ne?
Shin baka ga yadda masu harama suka
tuve tufafi ba ne, da xaga hannayen masu kwaxayin rahama, da hawayen masu tuba
ba ne?
Shin baka jin sautin masu talbiyya da
kabbarori da hailala ba ne?
To me ya same ka, har mafi alkhairin
kwanakin duniya suka shuxe maka, alhalin kana cikin son zuciyarka da ta tamke
maka xauri?
Ya wanda ke kai-komo cikin savo safe da
yamma
Yana cewa, ai zan tuba, yau ko gobe
Ya wanda ya wayi gari cikin son zuciya,
a watse
Ya kuma yi yammaci a cikin jahilci, a
daskare
Ya kuma kasance cikin sha'awowinsa
cikin dabaibayi a xaure
Ka tuna daren da za kwana a cikin
qabari kai xaya!,
Sai ka yi gaggawan tuba, tunda kana
cikin lokacin haka
Ka kuma risko abinda ya wuce, gabanin
lokacin da ba a gyaran tuntuve,
Ka kuma tsaya daga aikata zunubai da
laifuka,
Kuma "Lallai ne Allah yana shumfuxa hannunsa da rana, domin wanda ya
munana aiki cikin dare ya tuba, kuma yana shumfuxa hannunsa da dare, domin
wanda ya munana da rana ya tuba, har rana ta fudo daga mafaxarta. Kuma wanda ya
tuba daga zunubi, kamar wanda bashi da zunubi ne".
Allah ya mini albarka Ni da Ku cikin
alqur'ani mai girma, Kuma ya namfanar da Ni da Ku da abinda ke cikinsu na
ayoyi, da hikima.
Ina faxar abinda kuke ji, kuma ina
neman gafarar Allah, ga Ni da Ku da Sauran musulmai, daga kowani zunubi da
laifi, Sai ku nemi gafararSa, lallai ne Shi Mai gafara ne Mai rahama.
HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah, wanda yana
bada mafaka ga wanda ya nemi mafaka daga tausasawarSa,
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da
gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu
Muhammdu bawansa ne manzonsa, wanda ya bi shi to ya kasance akan alkhairi da
shiriya, kuma ya sava masa ya kasanci cikin vata da halaka.
Allah ya yi qarin salati a gare shi da
iyalansa da sahabbansa, da sallama mai yawa.
Bayan haka
Ya ku musulmai
Ku ji tsoron Allah, kuma ku kiyaye shi,
kuma ku masa xa'a kada ku sava masa, "Ya ku waxanda
suka Imani ku bi dokokin Allah, kuma ku kasance tare da masu gaskiya", [Tauba].
Ya ku musulmai!!!
Lallai a duniya, abincin mutuwa ne,
kuma qasar bala'oi,
Kuma kune kuka maye waxanda suka
gabata, kuma da sannu kuma za ku kasance magabatan masu mayewa,
Sai ku ribaci zamaninku, kuma ku yaqi
kawunanku, saboda yin aiki hajar masu bauta ne, kuma shine jarin masu gujewa
duniya, kuma akansu gyaruwar rayuka a rataya, sai ku aikata daidaita, kuma ku
kwatanta, kuma ku yi aiki safe da yamma, da wani loto na duhun dare, kuma ku yi
aiki da tsakaita, domin ku isa ga tsira. Kuma ku rigayi fitintinu ta hanyar aikata
ayyukan kwarai, kuma ku nisanci fitinoni masu vatarwa, masu ruxarwa. Saboda an ruwaito
daga Abu-hurairah –رضي الله عنه- lallai Manzon Allah –صلى الله عليه
وسلم- ya ce: "Ku rigayi wasu fitintinu masu kama da yankin dare mai duhu, ta
hanyar aikata ayyuka na kwarai, wanda mutum zai wayi gari yana mumini, amma ya
yi yammaci yana kafiri, ko yayi yammaci yan mumini, amma sai ya wayi gari yana
kafiri, yana sayar da addininsa da wani abu na duniya", [Muslim ya ruwaito shi.
No comments:
Post a Comment