HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 24/ZULHIJJAH/1438H
daidai
da 15/SATUMBA/2017M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI SALAH BN MUHAMMADU ALBUDAIR
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Bayan haka
Ya ku musulmai
ku ji taoron Allah kuma ku kiyayeshi
ku masa biyayya kada ku saba masa ya ku wadanda suka yi imani ku bi dokokin
Allah iyakar bin dokokinsa kuma kada ku mutu face kuna musulmai hadisi ya zo
daga irbad binu sariya Allah ya kara yarda a gareshi ya ce: manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallam ya tashi a cikinmu yana mai wa'azi mai ratsa jiki
wanda zukata suka rawrawa daga gareshi idanu suka zubar da kwalla se aka ce ya
manzon Allah kamar mai yin wa'azin yin bankwana to ka yi mana wasiyya sai ya ce
: *ina foronku da bin dokokin Allah da ku ji wa shugabanni da biyayya koda kuwa
bawa ne mutumin habasha ya shugabanceku kuma da sannu zaku ga sabani mai
tsanani a bayana se ku lazimci sunnata da sunnar khalifofi na shiryayyu masu
shiryarwa ku yi riko a garesu da fikoki kuma ina hanaku bin kirkirarrun lamura
domin kowacce bidi'a bata ce* imamu ahmad da abu dawooda suka rawaitoshi
Ya ku musulmai ku tuna ni'imomin Allah a kanku a
lokacinda kuka kasance cikin rarrabuwan kai da rabewan lamura da kulle kulle na
kiyayya da adawowi da yakuka da kai farmaki se Allah ya shiryar da ku bayan
karkata ya wadatar da ku bayan talauci
Ya hada kanku a cikin wata daula itace mamlakatul
arabiyyatussu'udiyya wato masarautar can larabawa, kasar musulunci kuma wani
fage na samun aminci kasar da iyayenmu da magabata suka hadata bayan da tana
cikin rarrabuwa da yaguwan lamari da sabani kuma tana cikin rayuwan tsoro da
yunwa da bushewan lamura da kuma shekaru na fari busassu marasa kayan amfani
Wadanda suke jagorantan wannan kasa da wanda suka ginota
da kuma yayan wannan kasa mazansu da mata da rundunar wannan kasa da masu
kareta bazasu taba kyaleta ga wani maha'inci me yawan kawo wasa ko kuma me fita
daga Al'umma mutumin banza bazasu kyaleshi ya sanya wannan kasa ta zama fage na
yin saura wadda bata da manufa me haske makauniya wajen yin saura wato (filin
zanga zanga) maras manufa da kuma jayayya maras alkibila da kuma wani fili na
yin wasan mutane marasa hankali da wawaye kuma wadancan mutane da muka ambata
bazasu kyale wanda ya fice ga jama'a ya rabu da su wanda kuma ya kudurci
mummunar akida da abun kyama sannan ya dauko wani manhaji mummuna da kida ya tsatstsara
sharri da makirci bazasu kyaleshi ya rusa ginin da aka gina ba ko kuma ya kawo
dauda ga ruwa me tsarki ko kuma ya yada rashin aminci da sharrace
sharrace
Kasar masarautar larabawa ta saudiyya kasa ce ta
musulunci da zaman lafiya, kasace wacce a karkashin inuwar shari'a take rayuwa
haka kuma a karkashin dausayin aminci take kiwo kuma kasa ce da ta hada
bangarori na daukaka ta tattarasu wannan kasa da jininmu zamu bata kariya
kuma da rayukanmu zamu bata fansa kuma da kirjinmu zamu fiskanci wanda ke adawa
da ita kuma duk abinda ake cewa na karyace karyace da kuma maganganun banza to
de wannan itace akidarmu wadda muka gadota daga magabatanmu muka koyota daga
magabatanmu sannan muke mikata wa yayanmu kalama ce mai wanzuwa tabbatacciya a
cikin set set na mutane tsara bayan tsara da kuma zamani da zatayi ta gudana a
tsawon shekaru na rayuwa da lokuta Kuma ba za mu taba karban canji ba akan haka
ko kuma mu yarda da zargi ba za mu karba jayayya ba ko kuma mu karbi maganar
wani wannan de itace akidarmu kuma amincin kasar harami guda biyu madaukaka
shine amincin musulmai gaba daya to shine amincin dakin ka'aba abin girmamawa
dabkuma wurare na bauta wa Allah masha'ir irinsu arfa da mina da muzdalifa kuma
shine samun amincin hajji da alhazai kuma shine amincin
Kuma zaman lafiyar kasar harami guda biyu madaukaka
to fa shine zaman lafiyan dukkan musulmai a ko ina suke kuma shine samun aminci
da zaman lafiyan ka'aba madaukakiya da kuma wuraren ibada makka arfa muzdalifa
mina safa marwa madaukaka masu tsarki kuma shine amincin alhazai da kuma aikin
hajji masu samun amincin wannan kasa shine masallacin manzon Allah (saw) da
kuma madina me haske kuma shine amincin wuraren ibada su kuma mutanen wannan
kasa ta masarautan larabawa ta saudiyya dukkansu sojoji ne na kare kasarsu kuma
sulke ne da ze bada kariya wa garinsa kuma su wadanna mutanen zasu tsaya don su
zama kariya ga amincinsu kuma maau kiran mutane zuwa ga fitina basu isa su jasu
ba da kuma wadanda suka zama jela ga makiya su jasu ko wadanda suka zama
jagorori zuwa ga sharri wadanda suke tafiya a bayan kasa zuwa ga yada rashin
aminci da kuma tafiyar da tsare tsaren da suka tsara masu munanan manufa da
kuma qbinda suka sa a niyyansu mai dauda dangane da kasrmu da kuma da'awa da
suke ta yi zuwa ga cewa a bada dama kowa ya yi musharaka a cikin lamarin
shugabanci cikin motsa kasa da gudanar da ita wanda suke riyawa maimakon family
daya da kuma kokarin tsaida zanga zanga da kuma tafiya a cikin gari da jamhurin
mutane da zanga zanga da fito na fito a kasarmu mai aminci suan yin haka ko
zasuyi haka ko suna so suyi haka hidima ga ma'abota akidoji munana
Da kuma CID kasashe mabanbanta masu kiyayya da adawa
da mu da aiki ga wasu kasace wadanda ke da masu bincike da sa ido wadancan
mutanen suna CID ne wa kasashen da suke adawa da mu irin au iran irinsu
isra'ila irinsu amerca
Shi kuma kira na a motsa a fito kan titi da ake yi wanda
suke kira zuwa gareshi a kasar harami guda biyu to wannan kam babu shakka kan
haramcinsa da kasancewarsa daga cikin sabo da ketare iyaka saboda abinda hakan
ke jawowa tafiya akan titi da hargaduwan mutane ke jawowa na rahin aminci da
kuma rushe rushe da raba kan al'umma da fitina da kuam lalata zaman lafiyan
mutane da kwanciyar hankalinsu da kuma bata maslahohin rayuwarsu da abinda yake
jawowa na bata ma shugaba da fita daga da'a a gareshi da muma ficewa daga
jama'ar musulmai kuma lallai babu me karfafa wannan da'ar a fito a motsa se yan
bidi'a batacce wanda bayan ka shari'ar manzanni kuma baya kan turban magabata
wanda suka shude
Ita kuma nasiha ga majibincin lamari wato shugaba ko
shugabanni tana kasancewa ne ta hanyoyi wadanda musulunci ya shar'anta su wanda
suke tabbatar da maslaha da kauda barna amma nasiha wa shugaba bata kasancewa
ta hanyar fitowa kan tituna da tafi da kuma muzaharori
Duk kuma mutuminda zalunci ya auku a kansa ko kuma wani ya
yi ta'addanci a kansa to a sani kofofin shugabanni a bude suke se a kai kara
haka kofofin kotuna a bude suke kuma suna yin hukunci da adalci suna taimakon
wandabaka zalunta sanna suna tsawatar wa wanda yayi zalunci amma jawo rashin
zaman lafiya da aiki na wawta yana kawo rashin aminci kuma muzaharori da
fitowa kan titi gabadayansu basu da gurbi ko gindin zaman a kasar harami guda
biyu
Ya ku iyalanmu a kasarmu mai albarka
Ya ku samarinmu ya ku jama'armu wato musulmai masu
kin zalunci ku kiyayi duk wani sautin da ke kiranku zuwa ga rushe kasarku da
garurrukanku da kuma wargaje hadin kanku da kasancewarku cikin jama'arku da
kiyaye amincinku da zaman lafiyanku da tabbatuwanku ku yi taimakekeniya tar da
jami'an tsaro sa'annan ku isar musu da tsaro da ake da shi da labarin duk
mutumin da yake nufin sharri wa kasarku sannan ku yi dubi ga mutanen da
kasashen da ke kewaye da ku wadanda suke fama da yake yake da fitintinu da
jujjuyawan lamura da kauchewa addini ku dauki izina ku dauki darasi daga abinda
ya sauka a kansu sannan ku godewa Allah akan abinda ya baku na ni'imomi masu
girma domin lalle ku kuna rayuwa ne cikin lambuna wanda kewayenku a kewaye da
wuta kuma wuta ce ta gobara take tashi kuma lallai mutum me rabo shine wanda
aka masa wa'azi da waninsa shi kuma tababbe shine wanda aka masa wa'azi a shi
karan kansa amma shi kuma kiran a motsa a fito wadda ake iyawa da kuma masu
da'awa zuwa ga hakan lallai bazasu samu komai ba face tabewa da kuma aibi kuma
lalle da'awar da sukeyi zata koma zuwa ga kirazansu kuma ba za au samu abinda
auke so ba kuma bazasu ci nasara ba saboda lallai Allah baya gyara aikin
mabarnata
Kuma kuna jin abinda nake fadi kuma ina neman gafaran
Allah kuma ku nemi gafaransa lalle shi ya kasance ga masu komawa
gareahi me yawan gafara
HUXUBA TA BIYU
Ya ku musulmai
Ni'ima bata juya baya bayan ta fiskanto kuma ba a dauketa
bayan ta sauka ba a tattare wata karama da ka yiwa mutum bayan an bashi ita se
da sababin sabo wanda ba a yi inkarinsu ba ba a hana mutane aikatasu ba su suke
jawowa ko kuma da sababin wasu kyautayin da ka ayi wadanda mutane basu godewa
Allah a kansu ba saboda su ni'ima idan aka godewa Allah a kansu se su wanzu su
tabbatu idan kuma aka butulcewa Allah aka kafirce masa se su gudu se ku tunkude
sharrin da ya fara leko da kansa fitintinun da suka fara lekowa da kuma
hatsarori da suke nufin dubatanku da tunkudesu da tuba da kuma neman gafara ku
yi kokarin fita daga ababen da kuka aikata na zalunci da sabo kuma duk wanda ya
zalunci wani miskini ko wani fakiri ko kuma yayi jinkirin bashi hakkinsa bayan
ya masa aiki akan hakkinsa na wajibi to wajibi ne a kansa yayi gaggawa zuwa ga
bashi hakkinsa ko ya biyashi kuyi rahama wa junanku kuyi umurni da kyakyawa
kuyi hani kan aikata mummuna ku kiyaye sallali guda biyar na farilla wanda aka
rubuta muku kuma kada ku canza alamomi na wannan shari'a kuma kada ku yi rukuni
ko mika kai ga wadanda suke zalunci kada ku zauna da ma'abota munkari da
munanan ayyuka ku gyara abinda ke tsakaninku (gidajenku) kuma ku tuba zuwa ga
majibincin lamarinku ku fita daga aikata sabo se ya zama kun samu kiyayewa daga
ni'imominda kuke tare da su suke cikinku wannan se ya kiyye muku ni'imomin da
suke cikinku se kuma ku sake kokarin jawo ni'imomin da basu riga suka sauka a
cikinku ba sannan da haka ne kuma za ku tabbatar da dawwaman baiwa da kyautar
Allah da karramawarsa da kuma kyautarsa ku kiyaye ni'imominda kuke rayuwa a
cikinsu ku yi kokarin jawo wasu
ni'imomin sa basu riga suka sauka a cikinku ba sanna ku nemi dawwamar kyautar
Allah da baiwarsa.
No comments:
Post a Comment