HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 07/RAMADHANA/1438H
daidai da 02/YUNI/2017M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH HUSAIN BN ABDUL'AZIZ ALUS-SHEIKH
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
TTT
Shehin Malami wato: Husain
bn Abdul'aziz Alus -Sheikh –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai
taken:
TTT, Wanda kuma a cikinta ya
tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Bayan haka:
Ya ku Bayin Allah…
!!
Lallai abin neman da ya fi
xaukaka, kuma buqatar da ta fi girma, ita ce: BAWA YA YI GAGGAGWAR AIKATA ALKHAIRORI, YA
KUMA RIBACI LOKUTAN ALKHAIRI; TA HANYAR SAMAR DA KYAWAWAN AYYUKA, "Da waxanda su ka yi
rigaye. Su waxanda su ka yi rigaye * Waxannan su ne waxanda aka kusantar …" [Waqi'ah: 10-11].
Kuma a cikin watan
ramadhana akwai, damammakin yin guzuri, na kyawawan ayyuka, da kusantar Allah
da dangogin xa'oi, kuma ya zo cikin hadisi, cewa: "Wanda ya azumci
watan ramadhana cikin imani da neman lada, an gafarta masa abinda ya gabata
daga zunubansa. Wanda kuma ya yi tsayuwar ramadhana (wato, sallar dararen watan)
cikin imani da neman lada, to an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa" An yi ittifaqi kan
ingancinsa.
Ya ku
Taron musulmai … !!!
Wanda aka masa taufiqin
dace, shi ne wanda ke kiyaye gavvansa, daga aikata ababen da aka hana, da kuma
laifuka masu halakarwa,
Kuma lallai yana daga cikin
hasara, da tavewa ko halaka, Musulmi ya yi aikin tara ko samun lada, tare da
gaggawar aikata xa'oi, sai kuma ya sake gaggawa wajen warware abinda ya qulla,
da rushe abinda ya gina, saboda talauci na haqiqa (a lahira), shi ne, wani ya
bayar da kyawawan ayyukansa, ga waninsa, sakamakon sakaci ga lamarin haqqoqin
halittun Allah, da zaluntarsu da kala-kalan nau'in zalunci, da cutar da su, da
dangogin cutarwa, ko yin ta'addanci akansu da na'uka mabanbanta na ta'addanci,
wanda Ubangijin halittu ya haramta, kuma annabinmu Muhammdu –صلى الله عليه وسلم- ya tsawatar, "Shin kun san wanene
fallasasshe?
Sai su ka ce:
Fallasasshe a cikinmu shi ne wanda bashi da dirhami ko kaya. Ya ce: Sai Annabi
–صلى الله عليه وسلم-
ya ce: Lallai fallasasshe daga cikin al'ummata, shi ne wanda zai zo a ranar
qiyama, da salloli, da azumi, da zakka, sai ya zo alhalin ya zagi wannan, ya yi
qazafi ga wannan, ya ci dukiyar wannan, ya zubar da jinin wannan, ya doki
wannan, sai a baiwa wannan daga kyawawansa, wannan daga kyawawansa, idan
kyawawan nasa su ka qare, gabanin a gama biyan abinda ke kansa, sai a xauko
daga zunubansu, a lafta akansa, sai a jefa shi cikin wuta" Muslim ya rawaito
shi.
Nawawiy ya faxa –a inda ke
sharhin wannan hadisin-: "Haqiqanin fallasasshe shi ne wanda zai halaka
cikakkiyar halaka, kuma shi ne aka rasa, rashin da babu samuwa a bayansa, ta
hanyar xaukar ayyukansa kyawawa ga masu binsa bashi, idan kuma kyawawan nasa su
ka qare, to sai a kwaso munanan ayyukansu, a lafta masa, sai kuma a wurga shi
cikin wuta, a nan ne kuma; Sai hasararsa da halakarsa da talaucinsa su gama cika".
Don haka; ka ji tsoron
Allah –Ya kai musulmi-, kana mai kiyaye ranka, daga dukkan laifuka, kuma
ka nisantar da ita, daga sabbuban halaka, da kuma dalilan yin hasara.
'Yan'uwana musulmai … !!!
Tsira, tana nan a cikin
kiyaye gavvai, samun sa'ada kuma a cikin lazimtar xa'oi, da kiyaye su daga
dukkan abinda zai gurvata su, ko kuma ya vata tasirinsu, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda a wurinsa
akwai zaluncin da ya yi wa xan'uwansa; cikin mutunci ne, ko dukiya, to ya nemi
warwarewa daga gare shi, gabanin ya zo a qiyama, a inda babu dinari ko dirhami,
kawai za a xauka ne daga kyawawan ayyukansa, idan kuma babu; to sai a xauki
munanan sahibinsa, sai a qara su akan munanansa, sai kuma a yi wurgi da shi
cikin wuta",
Bukhariy ya rawaito shi.
A cikin riwayar waninsa
kuma, Ibnu-Hubairah ya ce: "Xaukar fansar
qisasi, yana shiga cikin kowane kyakkyawa, har ya zama babu wani abu daga
cikinsa da zai saura".
Sai ka kiyaye –Ya kai Musulmi- daga faxawa cikin halaka,
kana mai cikakken kiyayewa, dangane da haqqoqin halittu, Annabi –صلى الله عليه وسلم- kuma, yana cewa: "Lallai za a bada
haqqoqi ga ma'abutansu, a ranar qiyamah, har sai an xau fansa ga akuyar da bata
da qaho, daga akuya mai qaho". Muslim ya rawaito shi.
Ma'anar hadisin shi ne, lallai Allah zai xau fansa ga
wanda aka zalunta, daga wanda ya zalunce shi, kamar yadda hadisan da su ka
gabata su ka bayyanar.
Daga wannan ne kuma, (za mu ce:)
Shi mai azumi yana cikin lokaci muhimmi; wanda a cikinsa
xa'oin muminai su ke yawaita, sai ya zama wajibi, musulmi ya riqa tuna cewa,
lallai haqiqanin azumi tarbiyya ne, kan samar da taqawa, "Ya ku waxanda su ka
yi imani an wajabta azumi a kanku, kamar yadda aka wajabta shi ga waxanda su ka
zo gabaninku, tsammaninku za ku samu taqawa" [Baqara: 183].
Kuma cikin faxakarwar Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- tabbatattu, akwai mafi girman tsawatarwa,
kuma mafi girman wa'azi, saboda Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- yana cewa: "Kuma idan ranar azumin xayanku ta zo, to
kada ya yi kwarkwasa, kuma kada ya yi Shewa (ihu), idan kuma wani ya zage shi,
ko ya aibanta shi, sai ya ce: Ni mai azumi ne…".
Sai ka kiyaye kyawawan ayyukanka –Ya kai musulmi-, kuma
ka kasance a kan, bada kariya ga labulan ayyukan xa'arka, kana mai bayyanar da matsanancin
kwaxayi a kan hakan, kuma mafi girmansa, saboda Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- yana cewa: "Wanda bai bar faxin
zancen qarya, ko aiki da shi ba, da kuma jahilci, to lallai Allah bashi da
buqatar ya bar abincinsa da abin shansa".
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUXUBA TA BIYU
Ya
ku waxanda su ka mallaki kafafen sadarwa!!!, Ya waxanda aka jarabbe su, da rubutu a
kafafen sadarwa, da na'ukansu dayawa!!!,
Ku ji tsoron Allah mabuwayi
da xaukaka, kuma ku kiyayi yaxa dukkan abinda ya sava wa wannan addini da
falalolinsa, ko ya ke yin suka kan tabbacin wannan addinin, ko kuma yaxa abinda
zai kai ga aukawa ga bolar ababen kyama, kuma munana, Saboda ya zo cikin
qa'idodin shari'a, cewa, duk wanda ya zama sababin faxawar halittu cikin savo,
to lallai yana da kwatankwacin zunubinsu, Allah ta'alah yana cewa: Kuma lallai za su
xauki kayan nauyinsu (na zunubi), da waxansu nauyayan zunubai, tare da kayan nauyinsu" [Ankabut: 13].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Wanda ya
sunnata mummunan sunna a cikin musulunci, yana da zunubinta, da zunubin mutumin
da ya yi aiki da ita, ba tare da an tauye komai daga zunubansa ba".
Kuma Allah ya yi rahama ga
Shaxibiy, a inda ke faxar maganarsa mai muhimmanci, cewa: "Madalla da
mutumin da ya mutu, sai zunubansa su ka mutu tare da shi, Bone kuma ya tabbata
ga wanda ya mutu, sai zunubansa su ka cigaba da wanzuwa, shekaru xari, ko
shekaru xari biyu, ana masa azaba da su a cikin qabarinsa, ana kuma tambayarsa,
har zuwa lokacin qarewarsu".
,,, ,,, ,,,
No comments:
Post a Comment