HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 21/RAMADHANA/1438H
Daidai da 15 /YULI / 2017M
LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULMUHSIN XAN MUHAMMADU XAN ABDURRAHMAN
ALQASIM
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne;
muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman
tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan aiyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar,
babu mai vatar da shi, Wanda kuma ya vatar, to babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su qara
tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.
Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da
taqawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, kuma ku kiyaye shi, a asirce, da
kuma a bayyane (a lokacin ganawa).
Ya ku musulmai …
Ubangijinmu (S.W.T) Mai karmici ne, Mai baiwa, TaskokinSa
suna cike, Mulkin komai kuma, a hannunSa ya ke,
Ya zuba ni'imominSa ga
bayinSa, kuma ya biyar da kyauta da falaloli, xaya bayan xaya a kansu,
Babu mai hana abinda ya
bayar, kamar yadda babu mai bayar da abinda ya hana,
Kyautukan Allah basu da
iyaka ta fiskar yalwa da yawa,
Yana yin kyautar alkhairori
da karamomi,
Kuma kyautarSa tana ci-gaba
bata yankewa, ta kuma game dukkanin halittunSa; sai alkhairorinSa su ka
dawwama, falalolinSa da ni'imominSa su ka riqa saduwa,
Yana farar bayi da kyautar
ni'imomi gabanin su roqe shi, kuma yana musu baiwar fiye da abinda ke xarsuwa a
tunaninsu,
Babu wani a cikin sama da
qasa, wanda baya cikin baiwar Allah,
Don haka, Allah shi ne
wanda ya fi cancantar samun yabo da zikiri ko ambato akan ni'imominSa, ta
hanyar tsantsanta soyayya, da bauta a gare shi, da kuma jingina ni'imomin zuwa
gare shi, da yin amfani da ni'imomin cikin xa'a a gare shi.
Yana daga cikin BAIWOWINSA MAXAUKAKI afuwarSa
ga wanda ya nufa daga cikin bayinSa, Allah (ta'alah) yana cewa: "Lallai ne Allah Mai
afuwa ne, Mai gafara"
[Haj: 60].
Kuma Allah bai gushe ba yana afuwa ga zunuban bayinSa, ta
hanyar barin yin uquba, ga dayawa daga cikinsu, matuqar basu masa shirka, ko su
ka sanya masa kishiyoyi ba, Allah (ta'alah) yana cewa: "Kuma shi ne, wanda
ke karvar tuban bayinSa, ya ke afuwa akan munana, kuma ya ke sane da abinda ku
ke aikatawa"
[Shura: 25].
Mai afuwa ne, yana son afuwa, kuma yana son halittunSa su
riqa aiki tuquru, domin samar da sabbuban afuwarSa, ta hanyar istigfari, da
tuba, da imani, da ayyuka nagari.
A cikin watan ramadhana kyautukan Allah da afuwarSa suna qara
bayyana, watan falaloli da gafara, wanda a cikinsa ake ninninka ayyuka, ake
kankare kura-kurai da zunubai, kuma a cikinsa ake bubbuxe qofofin rahama da
aljannoni, ake sanya shexanu cikin qullin sarka, ake rurrufe qofofin wuta,
watan azumi da karatun alqur'ani, da biyayya da kyautatawa, kasuwanci a cikinsa
tare da Allah, ana ninninka shi, Ibnul-Jauziy –رحمه
الله-
ya ce: "Ladan aiki yana qaruwa, saboda darajar lokaci, kamar yadda ke qaruwa
idan aka halarto da zuciya, ko aka tsantsance niyya".
Sallar
dare, ita
ce mafificin nafiloli bayan sallolin farilla, kuma Allah ya yi yabo ga bayinSa
masu taqawa a cikin faxinSa: "Sun kasance a lokaci kaxan na dare su ke
yin barci"
[Zariyaat: 17].
Kuma ya zo cikin hadisi cewa: "Wanda ya yi
tsayuwar ramadhana (wato, sallar dararen watan) cikin imani da neman lada, to
an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa", Bukhariy da Muslim.
Kuma "Duk wanda ya yi sallolin
dare tare da liman, har ya idar, to an rubuta masa ladan tsayuwan daren", Tirmiziy ya rawaito
shi.
Kuma duk wanda ya lazimci sallolin dare to ya cancanci
shiga aljanna cikin aminci, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Ya ku mutane! Ku riqa yaxa sallama, ku
ciyar da abinci, kuma ku sadar da zumunci, ku riqa sallah cikin dare, a lokacin
da mutane ke barci, sai ku shiga aljanna da salama", Ahmad ya rawaito
shi.
Ita kuma SADAKA hujja ce kan imanin ma'abucinta, kuma kowani mutum
yana qarqashin inuwar sadakarsa, a yinin qiyama, kuma mai ciyarwa an masa
alqawarin samun xaukaka da gafara, Allah (سبحانه) yana cewa: "Kuma duk abinda kuka ciyar na kayan
ciyarwa, ko, wani bakancen da ku ka yi, to lallai Allah yana saninsa" [Baqara: 270].
Kuma ladan sadaka yana qara girma, idan aka gudanar da
ita, a kwanaki masu falala. Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance "shi ne, ya fi mutane kyauta, sai dai ya fi
yawaita kyautar a cikin watan ramadhana", Bukhariy da Muslim.
Kuma "yin UMRAH a watan azumi
yana daidai da yin hajji", Bukhariy da Muslim.
ADDU'A abu ne mai riba, wanda
bashi da wata wahala, kuma addu'a shi ne bauta, kuma shi ne qashin bayan bauta,
kuma da addu'a ake janyo wadaci, ake tunkuxe bala'oi, kuma mai azumi idan ya yi
addu'a ba a mayarwa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Mutane uku ba a mayar da addu'arsu; Mai
azumi har zuwa lokacin buxa-baki, da shugaba adali, da addu'an wanda aka
zalunta; Allah yana xaga ta saman girgije, kuma yana buxe mata qofofin sama,
kuma Ubangiji yana cewa: Na rantse da buwayata! Zan taimake ki, koda bayan wani
lokaci ne",
Tirmiziy ya rawaito shi.
ALQUR'ANI hujja ne, mai ceto, kuma
shiriya da waraka, ma'abutansa; masu aiki da shi, su ne zavavvun halittu, kuma
mafiya alheri, kuma su ne mutanen Allah, waxanda ya kevance, Allah ya yi musu
alkawarin samun sakamako, da kuma qari daga falalarSa, a inda yake cewa: "Lallai waxanda ke
karatun littafin Allah, kuma su ka tsayar da salla, kuma su ka ciyar daga
abinda muka azurta su da shi, a asirce da a bayyane, to lallai suna fatan
fatauci wanda bata tasgaro * domin Allah ya cika musu sakamakonsu, kuma ya musu
qari daga falalarSa, Lallai shi Mai gafara ne Abin godiya" [Faxir: 29-30].
LOKUTAN
RAMADHANA fili
ne mai faxi ga masu tsere a cikinsa, ayyukan biyayya da sadar da zumunci suna
yawaita a cikinsa, kuma rayuka suna tsaftatuwa, halaye kuma suna tsarkaka,
Halittu a tsakanin junansu suna kusantar juna, kuma sashinsu yana tausaya wa
sashe.
Lokaci ne mai albarka wanda musulmai su ke zage damtse a
cikinsa, kuma ake xaga darajoji a cikinsa,
Sai dai kash, ga kwanakin watan na ku (na ramadahana),
suna shelanta, qarewa, kuma mai hankali shi ne wanda ya ribaci gomansa (na
qarshe), sai ya rayar da su, da ayyukan kusanci, da xa'oi, ya kuma canza
munanan ayyuka da kyawawa, sai ya kiyaye yininsa, ya rayar da darensa, kuma ya
sanya Annabi (صلى
الله عليه وسلم) ya zama abin koyinsa, jagora, domin ya kasance, "yana qara qoqarin
bauta a goman qarshe, irin qoqarin da baya yi a sauran dararen", Muslim ya rawaito
shi.
Kuma "Idan waxannan goman
su ka shigo, ya kasance yana raya dare, yana kuma tayar da iyalansa, sai kuma
ya daxa qoqari, ya qara zage damtse", Bukhariy da Muslim.
A cikin waxannan dararen masu albarka, mustahabbi ne
yawaita zikirin Allah, da karatun alqur'ani, Ibnu-Rajabin –رحمه الله- yana cewa: "Amma, lokuta masu
falala, kamar watan azumi, musamman a dararen da ake neman lailatul qadari a
cikinsu, to lallai mustahabbi ne a yawaita karatun alqur'ani, domin ribatar wannan
zamanin".
Kuma ya dace, Musulmi a cikin waxannan kwanakin ya yi
kwaxayin aiki da ADDU'AR
DA TA FI AMFANI,
kuma ta fi gamewa, A'isha –رضي
الله عنها- ta ce: Ya Ma'aikin Allah, idan na yi dacen lailatul qadari, me
zan riqa faxa a cikinta? Sai ya ce: "Ki ce, ALLAHUMMA
INNAKA AFUWWUN TUHIBBUL AFWA FA'AFU ANNI, Ma'ana: Ya Allah, lallai ne kai, mai
afuwa ne, kana son afuwa, ka min afuwa". Ahmad ya rawaito shi.
I'ITIKAFIN waxannan goman sunnah ce
da ta zo a sharia'a, saboda Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya yi i'itikafinsu, sa'annan sai matansa su ka cigaba da
i'itikafinsu,
Ibnu-shihabin –Allah yayi
masa rahama- yace: "Mamakin lamarin musulmai, sun bar yin
i'itikaafi, alhalin Annabi (صلى الله عليه وسلم)
bai bar yinsa ba tun da ya shiga garin Madina, kowace shekara, a cikin kwanaki
goma na qarshen ramadhana, har Allah ya karvi ransa".
Kuma ya dace, Mai i'itikafi, ya tsayu domin yin bauta, ya
kuma shagaltu da manufar shar'anta i'itikafin, wanda ta fi girma, yana mai nisantar
yawaita hulxoxi, da magana, ko yawaita ci, da barci.
Kuma ba zai fita daga
masallacin ba, sai ga buqatar da babu makawa daga gare ta, Ibnul-qayyim –رحمه الله- ya ce: "Kuma manufar i'itikafi
da ruhinsa, shi ne killace zuciya ga Allah, da tattara ta, a gare shi, da
kevantuwa da shi, da yanke ko barin shagaltuwa da halittu, da shagaltuwansa da
Allah; shi kaxai (S.W.T), ta yadda ambaton Allah (zikirinsa) da qaunarsa, da
fiskantarsa, za su zama a gurbin tunani-tunanin zuciyarsa, da ababen da su ke
xarsuwa a gare shi".
Kuma a cikin DARAREN NAN GOMA NE, Musulmai ke neman dacewa da lailatul
qadari, Manzon Allah –صلى الله
عليه وسلم- ya ce: "Ku nemi lailatul qadari a darare goman
qarshe, na watan ramadhana", Bukhariy da Muslim.
Kuma an fi fatan samunta, a cikin dararen mara daga
cikinsu, Manzo Allah –صلى الله
عليه وسلم- ya ce: "Ku kirdadi lailatul qadari a cikin mara ko
wutirin darare goman qarshe, na watan ramadhana", Bukhariy ya rawaito
shi.
Kuma acikin darare bakwai na qarshe, an fi fatan samun
nata, saboda Manzon Allah –صلى
الله عليه وسلم- ya ce: "Ku neme ta -yana nufin: lailatul qadari- a
cikin goman qarshe, idan xayanku ya yi rauni ko ya gaza, to kada a rinjaye shi
akan darare bakwai masu wanzuwa –na qarshe-", Muslim ya rawaito.
Shekhul Ismlami Ibnu-taimiyyah –رحمه الله- yana cewa: "Sai dai wuturin zai
kasance ne, tare da kula da abinda ya gabata; sai a nemi daren ashirin da xaya
(21), da daren ashirin da uku (23), da kuma daren ashirin da biyar (25), da
daren ashirin da bakwai (27), da daren ashirin da tara (29), ko kuma ya kasance
tare da lura da dararen da su ka rage (daga watan), kamar yadda Annabi –صلى الله عليه وسلم-
ya ce: (a neme ta), ga darare tara wanda za su rage, ko ga bakwai waxanda za su
rage, ko ga biyar waxanda za su rage, ko ga uku waxanda za su rage. A kan
wannan, idan watan ya kasance kwanaki talatin ne (30), sai hakan ya kasance a
cikin kwanaki na shafa'i, Sai ashirin da biyu (22), ya kasance, shi ne darare
taran da su ka rage, sai kuma daren ashirin da huxu (24) ya kasance shi bakwai
da za su rage, kuma da haka Abu-Said –رضي الله عنه- ya fassara shi, a cikin
hadisi ingantacce. Kuma haka Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya tsayu a lamarin wata.
Idan kuma lamarin ya kasance kamar haka, to lallai ya dace, Mumini ya yi
kirdadon dacewa da lailatul qadari a cikin darare goman qarshen gab xayansu".
Daren LAILATUL QASARI dare
ne mai girma; ma'abucin matsayi da daraja, kuma Allah ya saukar da sura sukutum
akansa domin girmama sha'anin daren, da muhimmantar da lamarinsa, da xaukaka
sha'aninsa, a inda ya ce: "To, me ya sanar da kai abinda ake cewa:
Lailatul qadari?"
[Qadr: 2].
Allah ya sanya ta mai
albarka, mai yawan alheri, sai ya ce: "Lallai mu ne muka sauqar da shi a
cikin wani dare mai albarka" [Dukhan: 3].
Kuma yada daga albarkar
wannan daren, sauqar alqur'ani a cikinsa, Allah ta'alah yana cewa: "Lallai mu ne muka
sauqar da shi (Alqur'ani) a daren qaddara" [Qadr: 1].
Kuma a cikin daren Mala'iku ke sauka zuwa ga duniya, "Mala'iku da Ruhi
suna sauka a cikinsa, da izinin Ubangijinsu, da kowani lamari" [Qadr: 4].
Ibnu-kasir –رحمه الله- ya ce: "Saukar Mala'iku yana yawaita, a cikin
wannan daren ne, sabodab yawan albarkarta, kuma Mala'iku suna sauka ne tare da
saukar albarka, da rahama, kamar yadda su ke sauka a lokacin tilawar qur'ani, kuma
su ke kewaye halqoqin zikiri, kuma su ke shumfuxa fuka-fukansu ga xalibin ilimi
na gaskiya, domin girmama shi".
Dare ne na salama da aminci da natsuwa, Allah -تعالى- yana cewa: "Salama ne wannan
daren, har fitar alfijir" [Qadr: 5].
Wato, dare ne da ya kuvuta
daga sharrori.
Raya wannan daren da ibadodi riba ne mai girma, Allah -تعالى- ya ce: ''Lailatul qaradi ya
fi yawan alkhairi fiye da watanni dubu" [Qadr: 3].
An-Nakha'iy –رحمه الله- ya ce: "Yin aiki a cikin
wannan daren, ya fi alkhairi akan yin aiki a cikin watanni dubu".
Wanda ya rabauta da wannan daren, shi ne wanda ya tsayu a
cikinta, yana mai gaskata alqawarin Allah, yana kuma neman lada, ba wata manufar
ta daban ba; kamar riya, da makamancinta, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda ya yi
tsayuwar lailatul qadari cikin imani da neman lada, to an gafarta masa abinda
ya gabata daga zunubansa".
Kuma a cikin wannan daren ake qaddara dukkan qaddarar da
za ta samu halittu gaba xaya, na xaukacin shekara, sai ya a yanko shi daga jikin
lauhul mahfuz, zuwa ga Mala'iku marubuta, sai abin da zai kasance ya bayyana
musu, sai kuma Allah ya umarce su da aikata abinda aikinsu ne, kamar yadda
Allah -تعالى- ya ke cewa: "A cikin daren, ake
rarrabe kowani lamari da ake hukuntawa * Lamari ko umarni ne daga wajenmu,
lallai mun kasance masu aikewa" [Dukhan: 4-5].
BAYAN HAKA, YA KU MUSULMAI!
Ayyuka ana lura da abinda aka gama su ne, kuma lallai
abin luran shi ne kamalar qarshen ayyuka, ba tawayar farkonsu ba; don haka; duk
mutumin da a farkon watansa ya kasance ya mayar da lamari ga Allah, aikinsa
kuma ya yi dacen Sunnah, to sai ya qara kyautata gininsa, ya kuma yi godiya wa
Allah, kan ni'imomi, kuma kada ya kasance kamar wadda ta warware zaren saqarta,
bayan tukka ta yi qarfi, ya zama warwararru.
Wanda kuma ya munana a cikin kwanakin da su ka shuxe, to
sai ya tuba cikin abinda ya rage; saboda qofar tuba a buxe ta ke, kuma baiwar
Allah abar bayarwa ce.
Kuma "Kuma wanda ya bi
Allah da taqawa, Allah zai sanya masa mafita" [Xalaq: 2].
A UZU BILLAHI MINASH
SHAIXANIR RAJIM:
"Yak u waxanda su ka
yi imani, idan ku ka bi Allah da taqawa, zaisanya muku ma'aunin rarrabewa (na
ilimi)"
[Anfal: 29].
ALLAH YAYI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALQUR'ANI MAI
GIRMA. …
HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah
kan kyautatawarSa; Godiya kuma tasa ce
bisa ga datarwarSa da kuma ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya; Ina mai
girmama sha'aninSa.
Ina kuma shaidawa lallai
annabinmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa.
Ya Allah, ka yi daxin
salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da kuma sallama mai ninnukuwa.
Ya ku musulmai…
Duniya awowi ne da kwanaki, kuma tana da shekarun da aka
xibar mata, shekarun mutum a cikinta kuma, sune wanda ya yi aiki a cikinsu.
Lallai Mai rabo, shi ne
wanda ya dawwamar da ambaton duniya, da mafi kyan ayyuka, kamar yadda Wanda ya
ci nasara shi ne, ya ribaci daqiqoqin
lokacinsa, kuma bai yi sakaci cikin wani abu na zamaninsa ba.
Wanda ya faxi babu nauyi, kuma shi ne mutumin da
lamuransa su ka sakwarkwace masa, zuciyarsa ta gafala, ya kuma bi son
zuciyarsa.
Marashin rabo, shi ne wanda
aka hana shi aikin alheri a cikin watan azumi, tavavve kuma shi ne wanda ya yi
hasarar lakuta masu falala, Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- yana cewa: "Turvaya ta bugi hancin mutumin da, watan
Ramadhana ya shigo, har ya fita, sai ba a gafarta masa ba", Tirmiziy ya rawaito shi.
>>>
Sannan ku sani, lallai Allah ya umarce ku da yin salati
da sallama ga annabinSa, a cikin mafi kyan littafinSa, inda ya ce: "Lallai ne Allah da
Mala'ikunSa, suna yin salati ga wannan Annabin, Ya ku waxanda su ka imani, ku
yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa", [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama da albarka, ga
annabinmu Muhammadu,
Kuma Ya Allah! Ka yarda da khalifofi shiryayyu,
waxanda suka yi hukunci da gaskiya, kuma da shi, su ka kasance suke yin adalci,
Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, da kuma sauran sahabbai gabaxaya, Ka haxa
da Mu tare da Su, da kyautarka da karamarka, Ya Mafi kyautar masu kyauta.
Ya Allah! Ka xaukaka Musulunci da Musulmai, ka
qasqantar da shirka da Mushirkai, kuma ka ruguza maqiyan addini, Kuma ka sanya
–Ya Allah!- Wannan qasar cikin aminci da nitsuwa, da wadaci da walwala,
da kuma sauran qasashen Musulmai.
Bayin Allah!!!
"Lallai Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa
makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku
wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah Mai
girma da daraja zai ambace ku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari,
kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke
aikatawa.
No comments:
Post a Comment