HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 23/Sha'aban/1438H
daidai da 19/Mayu/ 2017M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH ABDULLAHI BN ABDURRAHMAN ALBU'AIJAN
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
SHIRI GA AZUMIN RAMADHANA
Shehin Malami wato:
Abdullahi bn Abdurrahman Albu'aijan –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai
taken:
SHIRI GA AZUMIN RAMADHANA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah; wanda
ya saukar da Qur'ani a watan azumi, yana mai shiriya ga mutane, da hujjoji
bayyanannu, daga shiriya, da kuma rarrabewa, kuma Ya fifita ramalana akan
sauran watanni, da zamani.
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya, sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, shaidawa
irin ta gaskiya da imani,
kuma ina shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa, jagora ga qabilar Adnan, kuma mai ceton
talikai, a yinin da yara a cikinsa ke fitar da furfura,
Allah ka yi qarin salati a
gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da waxanda su ka bi su, da kyautatawa.
Bayan haka:
Ya ku bayin Allah;
Lallai ne Allah yana da
kyautuka da baiwa, da kuma lokutan alkhairi da xa'oi, wanda a cikinsu rahamomi
ke sauka, albarkoki kuma su ke gamewa,
Kuma yana daga cikin
waxannan lokutan, tsarkaka masu daxi; WATAN DA A CIKINSA AKE RURRUFE QOFOFIN WUTA, SAI KUMA
A BUXE QOFOFIN ALJANNONI,
Kuma haqiqa, ajalin wannan
lokacin ya kusanto, zamaninsa kuma ya qarato, saboda babu abinda ya rage a
tsakaninku da shi, face wasu yini qididdigaggu,
Sai ku zaburo, a cikinsa da
aikata xa'oi, da kuma ninninka kyawawan aiyuka, tare da rabauta da samun kankare
munanan ayyuka,
Kuna masu qara zage-damtse,
kuma ahir xinku da jinkirin alkhairi, ko samun rauni, domin watan ramalana
kwanaki ne qidayayyu, kuma awowi, qididdigaggu, wanda kuma babu fagen wargi a
cikinsu ko wasa, kuma babu fagen nuna kasala, kuma ramalana ba fage ne na
aikata savo ko munana ayyuka ba, saboda ayyuka, a cikin watan ana ninninka su, "Kuma wanda ya yi rowa, to
haqiqa yana yin rowa ne a kansa" [Muhammadu: 38].
"Kuma duk wanda ya kafirce, to
kafircinsa zai koma kansa" [Faxir: 39].
"Kuma wanda ya yi tsirfar
zunubi, to yana tsirfarsa ne, kawai a kan kansa" [Nisa'i: 111].
"Kuma wanda ya warware, to
lallai yana warwarewan ne, kawai akan kansa" [Fat-h: 10].
Don haka; ku nuna wa Allah
alkhairin da ke cikin rayukanku, saboda shaqiyyi, shi ne wanda a cikin watan
ramalana aka haramta masa samun rahamar Allah.
Tilas, ku yi tanadi da
shiri, kuma ku tuba, kuna masu bin dokoki da taqawa, saboda tsoron Allah shi ne
mafificin guzuri, "Ya ku waxanda su ka yi imani, an wajabta muku azumi, kamar yadda
aka wajabta shi ga waxanda su ka zo gabaninku, tsammaninku za ku samu taqawa" [Baqara: 183].
Ya ku Bayin Allah … !!!
Allah ya shar'anta yin azumin
ramalana, kuma Ya farlanta muku shi ne, ba domin yunwa da qishi ba, ba kuma
domin qishi da gajiyarwa ba, sai domin ku samu taqawa, saboda taqawa manufa ce
abar nema, kuma "dayawa daga masu azumi, basu da komai daga
azuminsu, face yunwa, da qishi", haka kuma masu sallar dare dayawa, basu da
komai daga tsayuwansa, face hana kai barci, da gajiya.
"Kuma duk wanda bai bar
maganar qarya ba, da yin aiki da ita, to Allah bashi da wata buqata; kan ya bar
abin cinsa, da abin shansa".
"Kuma azumi
garkuwa ne, don haka; idan yinin azumin xayanku ya zo, to kada ya yi 'rafasu' (wato, batsa cikin zance da iyali ko jima'i), kada kuma ya
yi ihu, Idan wani ya zage shi, ko ya nemi yin faxa da shi, sai ya ce: Ni Mutum
ne mai azumi".
Don haka; ba zai yiwu a
kusanci Allah ta'alah a halin azumi da barin ababen da mutum ke sha'awa na
halal ba, sai bayan an kusance shi, ta hanyar nisantar abinda Allah ya haramta,
a cikin kowani hali, kamar qarya da zalunci, da yin ta'addanci ga mutane, cikin
jinanensu da dukiyoyinsu da mutuncinsu.
Sai ku azumci watan
ramalana, kuma ku kiyaye shi, kuma ku sani lallai ku masu haxuwa ne da
Ubangijinku.
Ya ku bayin Allah … !!!
Ramalana, wata ne na gafara,
wanda ake 'yanta mutane a cikinsa, sai ku kusanci rahamar Allah, kuna masu aiki
da sababi, saboda shi Allah, Mai baiwa ne, Mai karamci, Mai yawan kyauta, An
ruwaito daga Anas –Allah ya qara yarda a gare shi- yana cewa: "Annabi ya hau matakalan farko
na minbari, sai ya ce: AMIN!
Sai kuma ya sake hawa
matakala na biyu, sai ya ce: AMIN!!
Sa'annan ya hau matakala na
ukun, sai kuma ya ce: AMIN!!!
Sannan, ya daidaita; ya
zauna, Sai sahabbansa su ka ce: Akan me ka ce, AMIN?
Sai ya ce: Mala'ika Jibrilu
ne ya zo mini, sai ya ce: Allah ya turbuxa hancin mutumin da aka ambace ka a
wurinsa, sai bai maka salati ba, Sai na ce: Amin.
Sai ya sake cewa: Allah ya
turbuxa hancin mutumin da ya riski iyayensa biyu, sai ba a gafarta masa ba, Sai
na ce: Amin.
Sai ya ce: Allah ya turbuxa
hancin wanda ya riski watan azumi, sai ba a gafarta masa ba. Sai na ce: Amin".
Ina neman tsarin Allah daga
hanin aikata alkhairi da tavewa, da kuma mummunan qaddara, da riskar tavewa.
Kuma hadisi ya zo daga Abu-hurairah -Allah ya qara yarda a gare shi-, ya ce: daga
Annabi (SAW) yana cewa: "Wanda ya yi azumin ramadana yana mai
imani, da neman lada: an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa.
Wanda kuma ya yi tsayuwar dare yana mai imani da neman lada an
gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa.
Wanda kuma ya yi tsayuwar lailatul-kadri, yana mai Imani, da kuma
neman lada to an gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa".
Ya ku, bayin Allah…!!
Azumi yana cikin manyan
ibadodi da ake kusantar Allah, da kuma xa'oi, waxanda su ka fi girma, da aiyuka
mafiya girman lada, kuma lallai shi azumi ibada ne na masu haquri, kuma guzuri ne
ga masu taqawa, kuma tanadin masu neman samun rabo, ladansa kuma, yana da girma,
kuma alherinsa yana da yawa, kuma amfaninsa bashi da makamanci, saboda azumi
waraka ne ga cutuka, kuma yana bada lafiya da qarfi da kuzari da magani, ga
rayuka da jiki, kuma yana tarbiyya, kuma yana bada hutu ga jiki, sama da haka
kuma gaba xaya, azumi ya kasance xa'a ne ga Ubangiji, kuma gafara, ga zunubai,
Kuma ya ishi azumi falala, kasancewar Allah ta'alah,
da ya raba ayyukan 'yan'adam kashi biyu, Ya sanya azumi ya kasance kaso xaya mai
cin gashin kansa, kuma ya jingina shi ga kansa, sannan kuma, ya sanya sauran
ayyukan 'yan'adam (gaba xayansu) a matsayin xaya kason, An ruwaito daga Abu-Hurairah –Allah ya qara
yarda a gare shi- yana cewa: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Dukkan ayyukan xan adam ana ninninka masa, kyakkyawa
da kwatankwacinsa goma, har zuwa ninki xari bakwai. Allah ta'alah ya ce: Sai
dai kawai AZUMI, lallai shi kam nawa ne, kuma nine zan yi sakayya akansa, yana
barin sha'awarsa da abincinsa domin Ni.
Mai azumi yana
da farin cikin iri biyu, da zai yi su, farin cikin farko, a lokacin
buxa-bakinsa, sai kuma wani farin ciki, a lokacin ganawa da Ubangijinsa.
Kuma lallai
warin bakin mai azumi, ya fi daxi, a wurin Allah, fiye da turaren almiski".
Kuma haqiqa Allah ya keve wa masu azumi shiga ta wata
qofa daga cikin qofofin aljannah, wanda ba za a musu cinkoso ba ta wannan
qofar, kamar yadda ya keve musu wata liyafa wanda ba za a yi tarayya da su
cikin amfani da ita ba, An ruwaito daga Sahal bn Sa'ad –Allah ya qara yarda a
gare shi- ya ce: Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Lallai a
aljanna akwai wata qofa, wanda ake ce mata: AR-RAYYANU, Wanda masu azumi ke
shiga ta cikinta ranar qiyama, babu wani wanda ba su ba, da zai shiga tare da
su, za a ce: Ina masu azumi? Sai su shiga ta wannan qofar, Idan na qarshensu su
ka shiga, sai a rufe ta, kuma babu wani da zai shiga ta wannan qofar, kuma duk
wanda ya shiga zai sha ruwa, kuma duk wanda ya shiga ba zai ji qishi ba, har
abada".
Allah ya sanya ni da ku, daga cikin masu riskar azumi, waxanda
za su samu karvuwa.
Ina faxan abinda ku ke ji,
…
Allah ya yi mini albarka NI
da KU, cikin alqur'ani mai girma, kuma ya azurta mu da bin sunnar AnnabinSa mai
karamci, da kuma lazimtar shiriyarsa miqaqqa, ina faxin abinda ku ke ji wannan,
kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai, sai
ku nemi gafararSa, lallai shi Mai
gafara ne Mai rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya ke karvar tuba daga
bayinSa, kuma ya ke yafe laifuka, kuma yana sane da abinda ku ke aikatawa.
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, rahamarSa
ta game kowani abu, kuma ni'imarSa ta game komai.
Kuma ina shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa, kuma zavavve daga cikin halittarSa, kuma
badaxinSa, kuma Shi ne ya fi jivintar muminai fiye da kansu, kuma matansa Uwayensu
ne, kuma cetonsa shi ne tsiransu, addu'oinsa kuma shi ne rabautarsu,
Allah ya qara salati da
sallama a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da wanda ya shiryatu da shiriyarsa,
kuma ya yi addu'ar neman yarda ga sahabbansa.
Ya ku bayin Allah !! …
Musiba a cikin addini ita
ce, mafi girman musiba, (Malam) As-Saffariniy yana cewa: "Musibu; wata ta fi wata,
sai dai kuma wanda ta fi su girma, ita ce musibar da ta kasance a cikin addini
–Muna
neman tsarin Allah daga hakan-, saboda ta fi kowace musiba, kuma mutumin da
aka wawashe, shi ne wanda aka xauke masa addininsa;
Saboda,
dukkan karaya, ana fatar
Allah zai yi xorin ta
Sai dai babu xori ga
karayar da ta kasance, a addini
Don haka,
idan ka ga wani mutum,
baya damuwa da abinda ya same shi ta vangaren addininsa, kamar ta fiskar aikata
zunubai da laifuka, ko barin juma'a da sallar jam'i, da sakaci da lokutan xa'a,
ko aukawa cikin haramun, kamar keta alfarmar shari'a, da qetare iyakokin Allah,
da tsallake su, to ka san, lallai wannan mutumin an jarrabe shi, alal haqiqa,
sannan ka qara sani cewa, lallai wannan ya mutu; shi yasa ba ya jin raxaxin
wannan musibar".
Musibarsa ta yi girma, kuma
ta fanqama, kuma abin a masa taziya ya yi girma, nadamarsa kuma za ta yi tsayi,
Wa? Mutumin da ya tozarta damarsa ta yin azumin ramadana, har lokacin hakan ya
wuce.
Haqiqa an gafarta zunubai,
kuma an suturce aibuka, an kankare laifuka, kuma an yi afuwa ga kura-kurai, an
xaukaka darajoji, an ninnika kyawawa, shi kuma, dolon an haramta masa (waxannan
gaba xaya), kuma ya halaka kansa, kuma bai yi rahama ga raunin ransa ba, kuma
bai xora karayar ransa ba, ya kuma wuce iyakar shari'a akan haka, muguntarsa ta
halaka shi, kuma walaqancinsa ya tavar
da shi, baqin ciki kuma, ya dabaibaye shi.
Ya mai neman aikata
alkhairi, ka fiskanto!
Ya mai neman aikata sharri
–kaitonka- ka taqaita!
Ya kai mutumin da ya yi
sakaci a ramadanan da ya gabata, ya tozarta watan, ya bar shi ya wuce, Sai kuma
Ubangijinsa ya masa baiwar qarin lokaci a rayuwa, har ya sake riskar wani
ramadanan na daban, To ka gode wa Allah, a kan wannan ni'imar (riskar
ramadana), kuma ka fiskanci Ubangijinka, gabanin mutuwa ta zo kwatsam, ko
rayuwarka ta qare cikin tavewa, ko qarfinka ya yi rauni, furfura kuma ta yi
qarfi,
A lokacin, (babu abinda zai
rage) sai, YA HASARATA! YA KAITONA!! YA BAQIN CIKINA!!!
"Ya Ubangijina! Don me ba ka
yi mini jiinkiri ba zuwa ga wani ajali makusanci, domin in gaskata, kuma in
kasance daga salihai"
[Tagabun: 10].
"Ya Ubangijina! Ku mayar da ni
(duniya) * tsammanina in aikata aiki na kwarai, cikin abinda na bari, Kayya,
lallai ne ita kalma ce da ya ke faxinta, alhali a baya gare su, akwai wani
shamaki, har ranar da za a tayar da su" [Mu'uminuna: 99-100].
"Kuma Allah ba zai jinkirta wa
rai ba idan ajalinta ya zo" [Munafiquna: 11].
KAITONSA!!! Kuma sannan KAITONSA!!!
Ya ku bayin Allah…!!
Lallai wahalar da ke cikin
aikin xa'a tana tafiya, sai daxinta ya wanzu a cikin wannan rayuwar, Ladanta
kuma a lahira, taska ce da aka tanada,
Kuma daxin da ke cikin savo
yana tafiya; ya qare, sai tavewa ta wanzu na tsawon zamani, wahalar cikinta
kuma na tsawon rayuwa, A lahira kuma uquba, da hasara.
Daxi na qarewa daga mutumin da
ya samu madararta
Daga haramun, sai zunubi da
aibi su wanzu,,,
Aqibar mummunan abu yana
wanzuwa a qarshensa
Babu alheri, ga daxin da wuta
ce a bayansa,,,
Daga qarshe,
Ya ku bayin Allah…!!
Lallai Allah ya kwararo mana ni'imomi, kuma ya karrama mu da
aminci da zaman lafiya, ya kuma nisantar da mu fitintinun da mu ke ganin suna
sauka ga wasunmu a wannan zamanin, har su halaka shuki da 'ya'ya, sannan su rarraba
haxin kan mutane.
Don, haka, Ya wajaba akanmu mu yi ta godiya a kowani
lokaci, kuma GODIYA TA TABBATA GA ALLAH a kan ni'imar zaman lafiya da imani,
kuma godiya ta qara tabbata ga Allah, wanda mu ke roqon ya kai mu watan
ramadana.
Kuma wajibi akanmu, mu tsayu sahu xaya, a fiskar wanda
ransa ta ke saqa masa, ya kawo mana barazana ga zaman lafiyarmu, ko kuma ya
shuka fitina a cikin tafiyarmu da haxin kanmu, ko domin ya raunata qarfinmu.
Saboda abinda ake nufin a lalata mana –Ya ku taron
'yan'uwa- shine aqidarmu da addininmu,
Kuma duk lokacin da
musulmai su ke shirin shiga wani lokaci na musamman, daga cikin lokutan
addininsu, sai a qulla musu makirci, domin a hana su amfana da shi, a kuma kikkitsa
musu qulle-qullen fitina.
Kuma lokutan zartar da
rukunnan musulunci, masu shaida akan haka; lokutan ramadana suma sun shaidi
hakan, lokutan aikin hajji da umrah suma sun shaidi hakan,
Sai dai kuma imaninmu da
Allah, da amintuwar da mu ka yi da jagororinmu shiryayyu, da aqidarmu
tabbatacciya, za su sanya masu ha'intarmu yin hasara, rabonsu kuma ya zama tavewa,
kaidin da su ka qulla kuma, ya koma ga qirazansu, saboda "makircin cuta baya faxawa,
sai ga mutanensa"
[Faxir: 43].
Kuma daularmu ba za ta canza
daga aqidarta, ko haxin kanta ba.
Kuma da sannu Allah zai
kiyaye amincinmu, da kuma addininmu, "Sai su bauta
wa Ubangijin wannan xakin * Wanda ya ciyar da su daga yunwa, kuma ya amintar da
su daga tsoro"
[Quraish: 3-4].
Ya
Allah! Ka
kiyaye wannan qasar da kiyayewanka,
Ya Allah! Ka dawwamar mata da amincinta da zaman lafiyanta, da haxin kanta,
Ya Allah! Ka kiyaye ta daga fitintinu; wanda
su ka bayyana daga cikinsu da waxanda su ka vuya,
Ya Allah! Wanda ya nufi qasar nan da
mummuna, ka shagaltar da shi da kansa, kuma ka mayar da kaidinsa zuwa ga
qirjinsa
Bayin Allah
"Lallai ne, Allah da
Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku
yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa
Annabi Muhammadu, kuma ka yarda da khalifofinsa shiryayyu masu shirayarwa; Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da
sauran sahabbai gabaxaya, ka haxa da mu, da baiwarka, ya mafi baiwar masu
kyauta.
,,, ,,,
,,,
No comments:
Post a Comment