2017/06/09

hudubar 14 RAMADANA 1438 daidai 9 June 2017 ta AsSubaitiy daga MASALLACIN ANNABI







HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 14/Ramadhana/1438H
Daidai da 09/Yuniyo/2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI ABDULBARIY XAN AUWADH AS-SUBAITIY






TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
SIFOFIN BAYIN MAI RAHAMA
     Shehin Malami wato: Abdulbariy xan Auwadh Al-Subaitiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'ah, 14/ Ramadhana, 1438H, mai taken: SIFOFIN BAYIN MAI RAHAMA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna akan.

HUXUBAR FARKO
Bayan haka:
A cikin kwanaki da dararen da mu ke ciki (na ramadhana), muna ganin yadda bauta ke bayyana a cikin mafi qayatarwar surarta da ma'anoninta, (ta fiskar) daxin azumi, da zaqin qur'ani, da kyan tsayuwa cikin sallolin dare, da sadaka da ciyarwa, ga kuma harasa, suna furta zikiri ko ambaton Mai rahama,
Gavvai, da soyayya, da zukata, sun rusuna ga Allah, cikin ibadar da ake yi ba da tilasci ba, wacce ginshiqinta shi ne soyayyar zuciya, wanda kuma za ta kai ga samun rabauta, a duniya da lahira.
Ibada bata rabuwa da musulmi, a duk inda ya sauka, a kuma dukkan lokutan da ya kasance a cikinsu, na matakan rayuwarsa, har ajalin da aka yanke masa ya same shi, alhalin yana cikin hali mai kyau, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma, ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka" [Hijr:  99].
Zuciya tana rausayawa, rayuwa kuma, tana xaukaka, a lokacin da kunnuwa ke jin yadda Allah ke siffanta halittunSa da kalmar YA KU BAYINA!
Kuma duk wanda ya faxa qarqashin wannan kira, ya kuma rabauta da xaukakar da ke cikin kalmar YA KU BAYINA! to lallai, ya samu babban rabo, mai girma.
Kalmar YA KU BAYINA! tana tultulo da natsuwa cikin zukata, kuma tana amintarwa daga tsoro, kuma alamar samun yardar Ubangiji ne, da falalarSa da ni'imarSa, Allah ta'alah yana cewa: "YA KU BAYINA! a yau, babu tsoro a kanku, kuma ku, ba masu yin baqin ciki ba ne * Waxanda su ka yi imani da ayoyinmu, kuma su ka kasance masu miqa wuya * Ku shiga aljanna, ku da matayenku, ana girmama ku" [Zukhruf: 68-70].
Rai natsattasiya, wacce imani ya tabbatu a cikinta, kuma ta natsu da tsantsance bautarta; na ikhlasi, kuma ta yi tawakkali ga Mahaliccinta, Ubangijinta lallai ya xaukaka ta da bushararSa mai girma; wanda ta zo a cikin faxinSa: "Ya ke Rai mai natsuwa * Ki koma zuwa ga Ubangijinki, alhali kina mai yarda, abar yardarwa * Sai ki shiga cikin BAYINA! * kuma ki shiga aljannata" [Fajr: 27-30].

Allah yana siffanta halittarSa ne da YA KU BAYINA! domin ya xebe musu kewa, kuma ya musu albishir da cewa, Shi (Allah) a kusa ya ke, kuma domin mutum ya iya shumfuxa buqatunsa, ya kuma watso damuwowinsa, yana mai xaga kokensa ga UbangijinSa; Mai jivintar lamarinsa, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma idan BAYINA! su ka tambaye ka, a kaina, to, lallai Ni Makusanci ne, Ina amsa kiran mai kira idan ya roqe Ni, sai su nemi amsawata, kuma su yi imani da Ni, tsammaninsu su shiryu" [Baqara: 186].


Kalmar YA KU BAYINA! tana yaye qiraza, kuma tana waigo da dubin mutane, zuwa ga rahamar Allah, wanda ta rigayi fushinsa, da tausasawarSa ga bayinSa, da jinqanSa, Allah ta'alah yana cewa: "Ka baiwa BAYINA! labari lallai ne, Ni Mai gafara ne Mai jin qai * Kuma lallai azaba ta, ita ce azaba mai raxaxi"[Hijr: 49-50 ].
A cikin ayar, yayin da Allah Mabuwayi ya ambaci rahama da gafara, sai ya kai maqura wajen qarfafa lamarinsu, da lafuza guda uku, wanda su ne, "ANNIY" da "ANA", da "ALIF DA LAAMUN" na nuna gamewa, ya ce:
(أنّي أنا الغفور الرحيم)
A lokacin da ya ambaci azaba kuma, bai ce: "LALLAI NE, NI NE MAI YIN AZABA", kuma bai siffanta kansa da hakan ba, kawai abinda ya ce, shi ne: "Kuma lallai azabata, ita ce azaba mai raxaxi".
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai Allah Maxaukaki ya halicci jin qai a ranar da ya halicce ta, rahama guda xari (100), sai ya riqe rahama casa'in da tara (99) a wurinsa, ya kuma saki guda xaya a cikin halittunSa gaba xaya, don haka; Da kafiri, ya san dukkan abinda ke wurin Allah na rahama, to da bai xebe tsammani daga samun rahama ba, Da kuma mumini yana sane da dukkan abinda ke wurin Allah ta'alah na azaba, to da bai aminta daga faxawa wuta ba".
Saboda haka,
Duk wanda ya kyautata bauta, zai kyautata zatonsa ga UbangijinSa, ya kuma amintu da yalwar rahamarSa, kuma sai ya ji cewa, lallai ababen da Allah ke qaddara wa mutane alkhairi ne, a haqiqanin lamarinsu, koda kuwa a zahirinsu musibu ne ababen qi, masu ciyo, Allah ta'alah yana cewa –kamar yadda Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya bada labari: "Ni ina wurin da BAWANA ya yi zatona".

Allah ta'alah yana kiran muminai ne da faxinsa: YA KU BAYINA! domin su shiga inuwar bauta a gare shi, akan kowace qasa, a kuma inuwar kowace sama, Allah ta'alah yana cewa: " YA KU BAYINA! waxanda su ka yi imani, lallai fa qasata mai yalwar faxi ce, saboda haka, ku bauta mini; ni kaxai" [Ankabut: 56].

"YA KU BAYINA" kalma ce mai taushi, wacce ta ke zaburarwa, kan yin aiki, kuma da wannan kalmar ce Mahalicci, ya kirayi bayinSa muminai, domin ya ilmantar da su ibadarsa da ta fi girma, wanda kuma ita ce tushen ibadodi (wato, sallah), da kuma xa'oin da su ka fi girma, su ka fi falala, domin su ribaci damar da ke cikin rayuwa, "Ka ce wa BAYINA! waxanda su ka yi imani: Su riqa tsayar da sallah, kuma su ciyar daga abinda mu ka azurta su, a asirce, da kuma a bayyane, gabanin yinin da babu ciniki a cikinsa ya zo, kuma babu abotaka" [Ibrahim: 31].

Don haka, Musulmi yana bautar UbangijinSa a kowani lokaci, kuma a cikin kowani hali; kamar cikin cinsa da shansa, da lokacin barcinsa da farkawarsa, a safiyarsa da maraicensa, Allah ta'alah yana cewa: "(sune) waxanda su ke ambatar Allah a tsaye, da a zaune, da kuma akan kuivinsu" [Ali-imraana: 191].

            Allah ya kira muminai ne, da faxinsa: YA KU BAYINA! domin ya zana musu hanyar samun taqawarsa, ya kuma faxakar da su yadda za su yi aiki da ita, a cikin faxinSa: "YA KU BAYINA! Ku bi ni da taqawa" [Zumar: 16].
Sai kuma Allah ya yaba musu akan aiki da taqawar, yabon da bashi da makamanci, a cikin faxinSa: "Kuma ya lazimta musu, kalmar taqawa, sai su ka kasance mafi dacewa da ita, kuma ma'abutanta" [Fat-h: 26].
Saboda babu wata qima a rayuwa wacce ta fi girma akan samun taqawa, "Lallai mafificnku daraja a wurin Allah shi ne mafificinku a cikin taqawa" [Hujuraat: 13].
            Shi kuma samar da taqawa, shi ne BABBAR ALAMAR WATAN AZUMI, Allah ta'alah yana cewa: "Ya ku waxanda su ka yi imani an wajabta azumi a kanku, kamar yadda aka wajabta shi ga waxanda su ka zo gabaninku, tsammaninku za ku samu taqawa" [Baqara: 183].
            Taqawa a watan ramadhana, tana haifar da tsarkake  rai da tarbiyyantar da ita, daga munanan halaye, ta kuma sabar mata da yin aiki da halaye masu kyau, kuma taqawar za ta koyar da bawa sanin ransa, da buqatuwar ran, da rauninta da buqatarta ga Ubangijinta (SWT), kuma ta riqa tuna mata girman ni'imomin Allah a kanta, da talauci ko buqatar 'yan'uwansa faqirai, sai ya lazimta mata godiyar godiyar Allah (SWT), da kuma yin amfani da ni'imominSa wajen yin xa'a a gare shi, da taimakon 'yan'uwansa faqirai, da kyautata musu.

            Lokacin da mumini ke jin yadda Allah ya siffanta halittunSa, da YA KU BAYINA! zai ji a jika, cewa lallai shi ya fake ga qaqqarfar madogara, da garkuwa mai bada kariya, da kuma kariya a gare shi daga dukkan shexani mai tsaurin kai, Allah ta'alah yana cewa:   "Lallai su BAYINA baka da wani qarfi akansu, Kuma Ubangijinka ya isa ya zama wakili" [Isra'i: 65].
Don haka; zuciyar da ta sadu da Allah; wato wanda rayuwarta ya cika da bauta da son Allah, shexan bashi da qarfin iko akan wannan zuciyar da ta ke haxe da Allah, kuma irin wannan zuciyar ta cancanci ta samu kariyar Allah, kuma a jikin wannan kariyar ne, kaidin shexanu dukkansa ke lalacewa.

            Allah yana siffanta salihan halittarSa da YA KU BAYINA! sai -a zukatansu- ya tayar musu da qarfin fatan samun mayewa da mallakar duniya, da hasken fatan nasara, kuma Allah ya isa ya zama Mataimaki, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma haqiqa mun rubuta a cikin littatafai, baicin lauhul mahfuz, lallai qasa, BAYINA salihai ne za su gaje ta" [Anbiya'i: 105].
Don haka, mallakar qasa, baiwa ce daga Allah, kuma alqawari ne, wanda manufarsa shi ne tabbatar da bauta ga Allah.

            "YA KU BAYINA!" kalma ce mai taushi, kuma salon magana ne tattausa, wacce ma'anarta ta ke gamewa har da masu laifi, da waxanda su ka gajarta ayyuka, matuqar sun tuba, sun kuma mayar da lamari zuwa ga Allah, Allah ta'alah yana cewa: "Ka ce: YA KU BAYINA, waxanda su ka yi varna a kan kayukansu, kada ku yanke qauna daga rahamar Allah, Lallai ne Allah yana gafarta zunubai gaba xaya, lallai shi, shi ne Mai gafara Mai jin qai" [Zumar: 53].
Bukhariy da Muslim da wasunsu sun rawaito daga Abdullahi ibn Abbas –Allah ya qara yarda a gare su- cewa, lallai wasu mutane, daga cikin ma'abuta shirka sun kasance sun yi kisa sun yawaita, sun kuma yi zina sun yawaita, sai su ka zo ga annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- su ka ce: "Lallai abinda ka ke faxa, kuma ka ke yin kira gare shi abu ne mai kyau, da za ka bamu labarin cewa: lallai akwai kaffara ga abinda mu ka aikata (na shirka da kisa da zina), sai faxin Allah ya sauqa: (Kuma su ne waxanda ba su kiran wani Ubangiji tare da Allah, kuma ba su kashe ran da Allah ya haramta kashe ta face da haqqi, kuma ba su yin zina" [Furqan: 68], sai kuma aka saukar: "Ka ce: YA KU BAYINA, waxanda su ka yi varna a kan kayukansu, kada ku yanke qauna daga rahamar Allah".
            Kuma Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Allah tabaraka wa ta'alah yana cewa: Ya kai xiyan Adamu, Lallai ne kai, matuqar za ka roqe ni, ka yi fatana, to zan gafarta maka, abinda ya kasance daga gare ka, ba zan damu ba, Ya kai xiyan Adamu, lallai ne kai, da zaka zo da kamar cikin qasa, ko abinda ya yi kusa da cikinta, na kura-kurai, sa'annan ka sadu da ni baka haxa ni da komai, to zan zo maka da gafarar da ta kai cikin qasa".

            Allah ya kyautata wa halittunSa, a inda ya siffatanta su, da YA KU BAYINA domin ya kira su zuwa ga kyautata zance, ko yin maganar da ta fi tsarki, da kuma kyautatawa cikin dukkan ayyuka, da kuma dukkan zance, da kuma dukkan sha'anonin rayuwa, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma ka ce wa: BAYINA, su riqa faxin kalmar da ta ke mafi kyau" [Isra'i: 53].
            Allah yayi mini albarka ni da ku, cikin alqur'ani mai karamci, ya kuma amfanar da mu da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, Ina faxar maganata wannan, ina kuma neman gafarar Allah, wa NI da KU, da kuma sauran musulmai, ku nemi gafararSa, lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.

HUXUBA TA BIYU
Waxancan, wanda Ubangijinsu ya kira su da faxinSa: YA KU BAYINA yana daga sifofinsu: KWAXAITUWARSU GA SALLOLIN DARE, DA QOQARINSU CIKIN HAKA, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma bayin Mai rahama su ne waxanda ke yin tafiya a kan qasa da sauqi, kuma idan jahilai su ka yi musu magana, sai su ce: salama (a zauna lafiya) * Su ne waxanda su ke kwana ga Ubangijinsu suna masu sujada da tsayi" [Furqan: 63-64].
Kuma yana daga cikinmafificin ayyuka a cikin wannan wata (na ramadhana) mai karamci, salloli ko tsayuwan dare, saboda ya zo cikin sahihan littafi biyu, lallai Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda ya tsayu a ramadhana da sallar dare cikin imani da neman lada, an gafarta abinda ya gabata na zunubansa".
Kuma haqiqa tsayuwa don sallar dare ya kasance al'adar Annabi ne –صلى الله عليه وسلم- da sahabbansa.

Kuma yana daga sifofin bayin Mai rahama: TAUSHIN GEFE, DA KAWAR DA KAI DAGA JAYAYYA DA JAHILAI, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma bayin Mai rahama su ne waxanda ke yin tafiya a kan qasa da sauqi, kuma idan jahilai su ka yi musu magana, sai su ce: salama (a zauna lafiya)" [Furqan: 63].

Kuma yana daga sifofin bayin Mai rahama: TSAKAITAWA WAJEN CIYARWA, saboda babu varnatarwa, kuma babu kwauro (ko mammaqo), Allah ta'alah yana cewa: "Kuma sune waxanda idan za su ciyar, basu varnatarwa, kuma ba su yin kwauro, kuma ciyarwarsu ta kan kasance a tsakanin wancan, tsakaitawa" [Furqan: 67].
Kuma varnatar da dukiya a cikin watan azumi da wanin wannan watan, abu ne da aka yi hani akansa, domin kashe dukiya wajen sayan waxannan ni'imomin, sa'annan a tuntsurar da su (ba tare da sun amfanar ba), lamari ne da shari'a ta yi inkarinsa, kuma ta haramta shi, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma ku ci, kuma ku sha, kuma kada ku varnatar; lallai ne shi (Allah) baya son mavarnata" [A'araf: 31].
            Sai ku yi salati, -Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, sabodaAllah ya umurce ku da aikata haka, a cikin littafinsa; a inda yake cewa:
"Lallai Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Yaku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].
,,,          ,,,          ,,,

,,,          ,,,          ,,,

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...