2017/06/24

hudubar idi 1 SHAWWAL 1438H Ta Madina








HUXUBAR IDI
DAGA MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
LAHDI,01/SHAWWAL/1438H







LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI DR. HUSAIN XAN ABDUL'AZIZ ALUS-SHAIKH




TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
IDI
     Shehin Malami wato: Husain xan Abdul'aziz Alus-Sheikh –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar idin azumi na shekarar 1438H, mai taken: IDI, Wanda kuma ya tattauna a cikinta, akan Yadda idi yake a musulunci, da abinda yake tattare da su na walwala da bayyanar da farin ciki, da jin daxi, da annashwa, kuma a cikin huxubarsa ya bayyana wajabcin aiki da shari'a, da kuma komawa izuwa ga ma'abuta ilimi a lokacin matsaloli da fitintinu.


بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD
Idi a musulunci yana xauke da manufofi maxaukaka, saboda a cikinsa ne musulmai ke farin cikin kammaluwar xa'arsu (ta azumi) ga Ubangijinsu, kuma su ke yin walwala ko nuna farin ciki; saboda buxa-bakinsu a bayan azuminsu, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Mai azumi yana da farin ciki iri biyu; farin ciki a lokacin buxa-bakinsa, da wani farin cikin a lokacin saduwarsa da UbangijinSa".
A cikin idi, akwai tuna manyan ginshiqai masu girma, wanda daga cikinsu, akwai, YADDA MUSULUNCI YA KWAXAITU WAJEN TABBATAR DA SOYAYYA A TSAKANIN MUSULMAI, DA KUMA HALIN QAUNA TSAKANIN MUMINAI, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma muminai maza da mata, sashensu majivinta sashe ne" [Tauba: 71],
Don haka, wajibi ne, mu riqi idi a matsayin sababin qarin sadar da zumunci, da qauna, kuma dama ta yin watsi da xabi'ar kyashi da qiyayya, Allah (تعالى) yana cewa: "Lallai ne muminai 'yan'uwana ne" [Hujurat: 10].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Misalin muminai cikin soyayyarsu da qaunar junarsu, kamar misalin jiki ne guda xaya".
A lokacin idi, ana mana kiraye-kiraye da cewar mu riqa yaxa farin ciki, da shigar da shi ga rayuka, da kuma qarfafa ma'anonin rahama da jin-qai, da kyautatawa, da taimako.

Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya farlanta zakkar fid-da-kai, kuma ya ce: "Ku wadatar da faqirai, daga fita neman abinci, a yinin idi", Ad-daraquxniy ya rawaito shi.

'YAN'UWANA MUSULMAI…
Daga jerin qiyayyar maqiya, akwai wanda su ke quqqulla shi ga qasar harami guda biyu (ta Saudia), qarqashin tsare-tsare na qarya, da launukan tsegumi masu munanan manufa, wanda ake qulla makircinsu ga qasar da ta ke rayuwa akan addinin musulunci, a matsayin manhaja ko tsarin rayuwa, Qur'ani kuma da Sunnah a matsayin konsutushin.
Qasar da aikinta da ya fi muhimmanci shi ne hidimar harami biyu, wanda su ka qunshi matattarar imani (wato, Madina), da kuma wurin bege ko makomar zukatan Musulmai (wato, Makkah),
KU SAURARA!
Lallai wajibi ne akan kowane musulmi, alhalin yana sane da cewa, lallai wannan qasar, qasar kowani musulmi ne, kuma wurin begen kowani mumini, wajibi ne a kansa, ya samu yaqinin cewa, lallai yin gaba da wannan qasar, gaba ne da ma'abutan musulunci gaba xayansu, kuma tava tsaronta da zaman lafiyarta cutarwarsa da hatsarinsa zai tava kowane musulmi.
YA KU TARON MUSULMAI!...
Al'ummar musulmai tana rayuwa cikin xinbin canje-canje, da tashin-tashina, da abubuwa masu rikitarwa, da mushkiloli da tsanani da qunci.
Kuma lallai qasar harami biyu, ita ce cibiyar da ta fi girma, kuma tushen qasashen musulmai, kuma tava wannan qasar da sharri, lallai mafari ne na yin kaca-kaca ko kekketa, wannan al'ummar, kuma shi ne gudumar rusau da zai rushe haxin kan al'ummar, da wargajewar samuwarta, kuma saboda wannan qasar, ita ce ke bada kulawa ga harami biyu, da lamarin hajji da umrah, don haka ita ce alamar buwaya da xaukaka ga musulmai gaba xaya.
Kuma don haka ne, ya zama wajibi a kula da waxannan ma'anonin, a kuma haxa hannu don taimakon wannan qasar wajen aikata abinda a cikinsa alkhairin musulmai ya ke, da kuma kawo gyara ga halin da su ke ciki, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma ku yi taimakakkeniya, akan biyayya da taqawa, kuma kada ku yi taimakakkeniya akan zunubi da zalunci" [Ma'idah: 2].

YA KU BAYIN ALLAH…
Kuma lallai abinda ya xoru na wajibi, akan mutanen wannan qasar, ya fi girma, kuma alhakin da ya rataya a wuyansu lallai ya fi, wajen zama tamtar tsoka xaya, ko haxewa tare da jagororinsu, irin haxewar da soyayya za ta riqa bayyana da ita, da kuma girmamawa da jin umarninsu da yi musu biyayya, cikin abinda ba savon Allah ba, da taimaka wa juna wajen samar da abinda a cikinsa yardar Allah Mabuwayi da xaukaka ta ke, da kuma dukkan ababen da akwai maslaha da amfanin kowa-da-kowa, kuma yin hakan lalura ne da ta zama dole a shari'a, kuma maslahar qasa ce, kuma buqata ce ga dukkan mutane.
Kuma wajibi ne, a kiyaye bin kowace fitina, ko hanyoyi, ko kiraye-kirayen da su ke barazana ga qasarmu, ko za su iya shafar amincinta da zaman lafiyarta, kuma farillar da ta zama wajibi a shari'a ita ce, tsayuwar dako (daga kowani mutum), a matsayin sojoji, da su ke a haxe, su ke taimakakkeniya, don tunkuxe kowani mai jiran ganin sharri, da wanda zai kawo hari, ko ya yi ta'addanci, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma ku yi riqo da igiyar Allah gaba xaya, kada ku rarraba" [Ali-imrana: 103].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Ya ku waxanda su ka yi imani ku yi xa'a wa Allah, kuma ku yi xa'a ga Manzonsa, da majivinta lamura daga cikinku" [Nisa'i: 59].

YA KU TARON MUSULMAI!...
Lallai mafi girman makami domin yaqar mushkilolin wannan al'ummar, da abinda ta ke fiskanta na qalu-balen da su ke fiskantarta (a koda-yaushe), da xinbin hatsarin da su ke kewaye da ita, shi ne YIN AIKI NA GASKIYA, DA XAUKACIN KARANTARWAR MUSULUNCI, a matsayinsa na salo kammalalle da ya game dukkan sha'anonin rayuwa. Tare kuma da yin aikin cikin da'irar 'YAN'UWANTAKA TA MUSULUNCI, DA GAMAYYA TA IMANI, "Lallai ne Mutum yana cikin hasara * sai dai waxanda su ka yi imani, kuma su ka yi aiki nagari, kuma su ka yi wasici da gaskiya, kuma su ka yi wasici da haquri" [Asr: 2-3].

'YA'UWANA MUSULMAI!...
Yana daga ni'imomimanya, ga wannan qasa (ta Saudia), DAIDAITUWAN LAMARI SHUGABANCI DA JAGORANCI, Wanda da su maslahohi na xaukacin al'umma da na xaixaikunsu gaba xaya su ke tsaruwa, kuma gamammun lomura da kevantattunsu su ke iya daidaituwa, kamar yadda Aljuwainiy ya ke faxa.

Kuma yana daga cikin haka, Abinda ya kasance a cikin waxannan dararen na zavin da ya yi daidai, wanda Sarki mai hidimar harami biyu maxaukaka ya yi; (wato, na zaven Yarimansa mai jiran gado, a cikin wani yanayi da ya cika da sanya albarka, daga kowa-da-kowa, Don haka; godiya ta qara tabbata ga Allah, akan abinda ya cika mana na ni'imar haxuwar zukata da rashin rarrabansu.
Kuma lallai Mu, a lokacin da mu ke mubaya'a ga Yarima mai jiran gado, akan littafin Allah, da sunnar ManzonSa, da kuma ji da biyayya, a cikin nashaxi ko tilasci, ko matsatsi ko sauqi, lallai muna roqon Allah, da ya sanya albarka cikin ayyukan sarki mai hidimar harami guda biyu, kuma ya tsawaita rayuwarsa cikin xa'ar Allah. Ya kuma datar da Yarima mai jiran karagar mulki, ya taimake shi kan ayyukansa, cikin abinda zai yardar da Allah (سبحانه), kuma ya sanya shi, ya zamo mabuxin alherori, marfin toshe kowane sharri, kuma ya sanya albarka cikin ayyukansa, kuma ya dabaibaye su da cin nasara da dace.

Allah ya kiyaye wannan qasar, da sauran qasashen musulmai, kuma ya datar da su gaba xayansu, zuwa ga ababen da yardarsa ta ke cikinsu.

ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD
            Allah yayi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Ina faxar maganata wannan, kuma ina neman gafarar Allah, ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.

HUXUBA TA BIYU
ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD

YA KU 'YAN'UWANA MUSULMAI…
Ku daidaitu akan ayyukan biyayya ga Ubangijinku, kuma ku yi gaggawar neman samun yardarsa, a dukkan lokutanku, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma ka bauta wa Ubangijnka, har mutuwa ta zo maka" [Hijr: 99].

'YAN'UWANA MUSULMAI…
Wasiqar aminci ne da soyayya da gaisuwar idi za mu tura, ga zaratan sojojinmu, waxanda su ka xauki nauyin kare iyakoki, muna muku gaisuwar wannan idin,
Allah kuma ya girmama ladanku, ya ninninka sakayyarku,
Kuma ya kiyaye ku ta gaba gare ku, da ta bayanku,
Kuma Allah ya karvi waxanda su ka yi mutuwar shahada daga cikinku,
Ya kuma bada lafiya ga marasa lafiyan cikinku,
Ya warkar da waxanda aka musu rauni daga cikinku
Kuma ya qarfafi zukatanku, ya tabbatar da duga-duganku.

YA KU TARON MUSULMAI…
Musulunci addinin zaman lafiya ne da dukkan ma'anoninsa, da kuma haxin-kai da dukkan kalolinsa, da jin qai da tausayi da dukkan shakalolinsa, da kyautatawa da fiskokinsa masu yawa, sai ku bayyanar da hakan cikin ayyukanku, ku fito da shi a sarari a cikin mu'amalolinku, ku yaxa shi ga duniya, kamar yadda jerin halayyar Alqur'ani da kuma Annabi su ke, wajen tabbatar da dukkan aiki managarci, da kuma magana mai kyau.

Kuma hanyoyin qetare iyaka, da tsanantawa, da bin hanyoyin wuce gona-da-iri da ta'addanci, dukkan waxannan addinin musulunci ya yi hani akansu, kuma waxannan halayen ba su tsayawa a madadin karantarwar musulunci da manufofinsa da abinda musuluncin ke qoqarin cimmawa, "Kuma bamu turo ka ba, face jin-qai ga talikai" [Anbiya'i: 107].
"Kuma kada ku yi ta'addanci, saboda Allah baya son masu ta'addanci" [Baqara: 190].

Kuma lallai, Muna Allawadan kaiwan harin tsoratarwa, wanda ya auku kusa da xakin Allah mai alfarma, kuma wannan lamari ne mai girman muni, wanda addini da hankali basu amincewa da shi.
Kuma lallai Muna tsawatar da samarinmu, kan ruxuwa da irin wannan aikin, ko bin shexanun da su ke nufin ruguza addinin samarin, ko halaka su.
,,,          ,,,          ,,,

,,,          ,,,          ,,,

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...