2016/11/20

BUSHARORI GOMA GA MASU KIYAYE SALLAR ASUBA ( البشائر العشر للمحافظين على صلاة الفجر)






البشائر العشر للمحافظين على صلاة الفجر
(BUSHARORI GOMA GA MASU KIYAYE SALLAR ASUBA)





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA



بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشرف المرسلين، وعلى آله وصحبه أجمعين، أما بعد:
فهذا المقطع في ذكر البشائر العشر للمحافظين على صلاة الفجر، جعلنا الله منهم بمنه وكرمه.

البشارة الأولى
 قال النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
"بَشِّرِ الْمَشَّائِينَ فِي الظُّلَمِ إِلَى الْمَسَاجِدِ، بِالنُّورِ التَّامِّ يَوْمَ الْقِيَامَةِ".
أخرجه أبو داود والترمذي وصححه الألباني.

BUSHARAR FARKO
(CIKAKKEN HASKE RANAR KIYAMA GA MASU TAFIYA CIKIN DUFFAI ZUWA GA MASALLATAI)
 
Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama-  ya ce:
"Ka yi bishara ga masu tafiya cikin duffai zuwa ga masallatai, da samun haske cikakke a ranar kiyama".
Abu-dawud ya ruwaito shi, da Tirmiziy, kuma Albaniy ya inganta shi.

البشارة الثانية
قال النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
"رَكْعَتَا الْفَجْرِ خَيْرٌ مِنَ الدُّنْيَا وَمَا فِيهَا".
أحرجه مسلم.

BUSHARA TA BIYU:
(RAKA'OI BIYU BAYAN KETOWAR ALFIJIR SUN FI DUNIYA GABA DAYANTA ALHERI)
Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"Raka'oi biyu bayan ketowar alfijir sun fi alheri akan duniya da abinda ke cikinta".
Muslim ya ruwaito shi.

البشارة الثالثة
قال النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
"مَنْ خَرَجَ مِنْ بَيْتِهِ إِلَى الْمَسْجِدِ كُتِبَ لَهُ بِكُلِّ خُطْوَةٍ يَخْطُوهَا عَشْرُ حَسَنَاتٍ، وَالْقَاعِدُ فِي الْمَسْجِد يَنْتَظِرُ الصَّلاَةَ كَالْقَانِتِ، وَيُكْتَبُ مِنَ الْمُصَلِّينَ، حَتَّى يَرْجِعَ إِلَى بَيْتِهِ".
أخرجه أحمد.

BUSHARA TA UKU
(LADAN TATTAKI ZUWA GA MASALLACI, ZAMAN JIRAN SALLAH KUMA KAMAR YIN SALLAH NE)

Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"Wanda ya fita daga gidansa, zuwa masallaci, za a rubuta masa lada goma da dukkan takun da ya ke yi.
Wanda kuma ke zaune a masallaci yana jiran sallah kamar wanda ya ke tsayar da salla ne, kuma za a rubuta shi cikin masallata, har ya dawo gidansa".
Ahmad ya ruwaito shi.

البشارة الرابعة :
قال جل في علاه:
"أَقِمِ الصَّلاَةَ لِدُلُوكِ الشَّمْسِ إِلَى غَسَقِ اللَّيْلِ وَقُرْآنَ الْفَجْرِ إِنَّ قُرْآنَ الْفَجْرِ كَانَ مَشْهُودًا". 
سورة الإسراء : ٧٨.

BUSHARA TA HUDU
(MALA'IKU SUNA HALARTAR SALLAR ASUBA)
Allah Madaukaki yana cewa:
"Ka tsayar da salla daga gotawar rana, zuwa duhun dare, da tsawaita karatun alfijir, lallai sallar alfijir ta kasance abar halarta"
[suratul Isra'i: 78].

البشارة الخامسة
قال النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
"لَنْ يَلِجَ النَّارَ أَحَدٌ صَلَّى قَبْلَ طُلُوعِ الشَّمْسِ وَقَبْلَ غُرُوبِهَا، يَعْنِى الْفَجْرَ وَالْعَصْرَ".
أخرجه مسلم.

BUSHARA TA BIYAR
(KIYAYE SALLAR ASUBA DA LA'ASAR KARIYA NE DAGA SHIGA WUTA)
Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama-  ya ce:
"Ba zai shiga wuta ba, mutumin da ya yi salla gabanin fudowar rana, da faduwarta", yana nufin sallar asuba da ta la'asar.
Muslim ya ruwaito shi.

البشارة السادسة:
قال النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
"مَنْ صَلَّى الْعِشَاءَ فِي جَمَاعَةٍ فَكَأَنَّمَا قَامَ نِصْفَ اللَّيْلِ، وَمَنْ صَلَّى الصُّبْحَ فِي جَمَاعَةٍ فَكَأَنَّمَا صَلَّى اللَّيْلَ كُلَّهُ". 
أخرجه مسلم.

BUSHARA TA SHIDA:
(YIN SALLAR ISHA CIKIN JAM'I KAMAR SALLATAR RABIN DARE NE, YIN ASUBA CIKIN JAM'I KUMA, KAMAR SALLATAR DAREN NE GABADAYA):
Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"Wanda ya yi sallar isha, a cikin jam'i, kamar ya sallaci rabin dare ne, Wanda kuma ya yi sallar asuba a cikin jam'i, to, kamar ya sallaci daren ne gabadaya".
Muslim ya ruwaito shi.

البشارة الثامنة
قال النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
"مَنْ صَلَّى الْفَجْرَ ثُمَّ جَلَسَ فِي مُصَلاَّهُ، صَلَّتْ عَلَيْهِ الْمَلاَئِكَةُ، وَصَلاَتُهُمْ عَلَيْهِ: اللَّهُمَّ اغْفِرْ لَهُ، اللَّهُمَّ ارْحَمْهُ".
أخرجه أحمد.

BUSHARA TA BAKWAI
(YIN SALLAR ASUBA DA ZAMA A WURIN SALLAR, SABABI NE NA SAMUN ADDU’AR MALA'IKU)
Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"Wanda ya sallaci sallar asuba, sai ya zauna a wurin sallarsa, Mala'iku za su rika masa salati, kuma salatin da za su masa shine, Ya Allah! Ka gafarta masa, Ya Allah! Ka yi rahama a gare shi".
Ahmad ya ruwaito shi.


البشارة التاسعة
قال النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
"مَنْ صَلَّى الْغَدَاةَ  الفجر فِي جَمَاعَةٍ، ثُمَّ قَعَدَ يَذْكُرُ اللَّهَ حَتَّى تَطْلُعَ الشَّمْسُ، ثُمَّ صَلَّى رَكْعَتَيْنِ، كَانَتْ لَهُ كَأَجْرِ حَجَّةٍ وَعُمْرَةٍ تَامَّةٍ تَامَّةٍ تَامَّةٍ". 
أخرجه الترمذي وصححه الألباني.

BUSHARA TA TAKWAS
(YIN SALLAR ASUBA DA ZAMA DOMIN AMBATON ALLAH, DA RAKA'OI BIYU BAYAN FUDOWAR RANA, LADANSU KAMAR NA YIN HAJJI NE DA UMRAH CIKAKKU )
Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"Wanda ya sallaci sallar asuba a cikin jam'i sa'annan ya zauna yana ambaton Allah har rana ta fudo, sa'annan ya yi raka'oi biyu, ya kasance yana da ladan hajji da umrah, cikakku, cikakku, cikakku".
Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma Albaniy ya inganta shi.

البشارة العاشرة
قال النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
"مَنْ صَلَّى صَلاَةَ الصُّبْحِ فَهْوَ فِي ذِمَّةِ اللَّهِ، فَلاَ يَطْلُبَنَّكُمُ اللَّهُ مِنْ ذِمَّتِهِ بِشَىْءٍ، فَإِنَّهُ مَنْ يَطْلُبْهُ مِنْ ذِمَّتِهِ بِشَىْءٍ يُدْرِكْهُ، ثُمَّ يَكُبَّهُ عَلَى وَجْهِهِ فِي نَارِ جَهَنَّمَ".
أخرجه مسلم.

BUSHARA TA TARA:
(SALLAR ASUBA TANA SANYA BAWA CIKIN KULAWAR ALLAH)
Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"Wanda ya yi sallar asuba to yana cikin alkawari ko amana da kulawar Allah, kada Allah ya nemi wani abu daga abinda ya yi alkawari da ku akansa, saboda duk wanda Allah ya nemi abu daga cikin abinda ya dauki alkawari da shi, zai riske shi, sa'annan ya tuntsurar da shi cikin wutar jahannama akan fiskarsa".
Muslim ya ruwaito shi.



No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...