HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله
عليه وسلم)
JUMA'A, 25/SAFAR/1438H
Daidai 25/NOBANBA/2016M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI HUSAINI XAN ABDUL'AZIZ ALU AL-SHEIKH
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
S
HUXUBAR FARKO
Godiya
ta tabbata ga Allah akan ni'imominsa da ba a qididdige su.
Kuma
ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke ba shi da
abokin tarayya, a lahira da duniya.
Kuma
ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa, annabi
zavavve, kuma bawa zavavve.
Ya
Allah! ka yi daxin salati da sallama da albarka a gare shi, da iyalansa da
sahabbansa, ma'abuta gaskiya da tsoron Allah ( taqawa).
"Ya ku waxanda suka yi imani ku bi dokokin Allah da
taqawa, kuma ku faxi magana ta daidai * Zai gyara muku aiyukanku, kuma ya
gafarta muku zunubanku, kuma duk wanda ya yi xa'a wa Allah da Manzonsa to
haqiqa ya rabauta da rabo mai girma" [Ahzab: 70-71].
'Yan'uwan Musulunci
A rayuwar al'ummarmu ta yau akwai fitintinu masu
tsanani, da musibu nau'i-nau'i, da qalu-bale masu hatsari, da tsare-tsare na
makirci.
Kuma lallai musulmai suna fatan ganin ababen
da za su gyara halayensu, su kawo sa'ida a cikin rayuwarsu, su kuma tabbatar
musu da farin ciki, da walwalar arziqi, sannan su tunkuxe musu tsanani da
cutuka.
Kuma lallai nasarar wannan al'ummar da rabautar ta da samun dukkan abinda ta ke
kwaxayi, da kuma samun tsira daga dukkan abinda ta ke tsoro, ko sauran ababen qi,
ba za su yiwu ba, sai idan ta yi riqo da gangariyar musulunci, wanda ke qunsar
tataccen tauhidi, da ingantacciyar aqida, da cikakken miqa wuya ga abin bautawa
guda xaya, a cikin dukkan nashaxoxin al'ummar da fagagen rayuwarta, Allah
ta'alah ya ce: "Haqiqa muminai sun samu babban rabo" [Mu'uminuna:
1].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ya ku
mutane, ku faxi: La ilaha illal lahu, sai ku samu rabo",
Ibnu-Khuzaimah ya ruwaito shi a cikin
"sahihinsa".
Ya ku
taron Musulmai!!
Al'umma ba
za tava samun sa'ada ba, kuma halinta ba zai tava gyaruwa ba, matuqar dukkan
tsare-tsaren rayuwarsu da dukkan abinda su ka fiskanta ba su gudanar da su a
qarqashin shari'ar Allah Mabuwayi da xaukaka ba, Allah (سبحانه) yana cewa: "Ya ku waxanda su ka
yi imani ku yi ruku'i da sujjada, kuma ku bauta wa Ubangijinku, ku riqa aikata
alheri, domin ku samu rabo" [Hajj: 77].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai
ya samu rabo, Wanda ya musulunta, kuma aka bashi arziqin buqatunsa, kuma Allah
ya bashi wadatuwa a zuciya, ga abinda ya bashi".
Kuma
wadacin arziqi ba zai tabbatu ba, da kwanciyar hankali, da walwala a cikin
raywa, da aminci da zaman lafiya ga wata al'umma musulma, face sun sallamaa
lamuransu ga hukuncin Allah, sun kuma yi aiki da shari'arSa, su kuma miqa wuya
ga shiriyar ManzonSa (صلى الله عليه وسلم),
Allah (تعالى) ya ce: "Kawai maganar
muminai idan aka kira su zuwa ga Allah da manzonSa, domin ya yi hukunci a
tsakaninsu ta kan kasance, su ce: Mun ji, kuma mun yi xa'a, kuma waxannan su ne
masu samun rabo" [Nur: 51].
Ya
al'ummar Musulmai!!
Tavewa
da dukkan nau'ukansa mabanbanta ba za su xagu ba, duk yadda mu ka yi qoqarin
rabuwa da hakan ta dukkan hanyoyi, matuqar ba mu tabbatar da tuba ta gaskiya ba,
daga abinda ke aukuwa a rayuwarmu na sassava wa tsarin Ubangijinmu, da kuma sunnar
annabinmu Muhammadu (صلى الله عليه وسلم).
Kuma
lokaci ya yi, ga wannan al'ummar, alhalin tana xanxanar raxaxi da baqin ciki
launi-launi (iri-iri), lokaci ya yi, ta koma ga Ubangijinta, tana mai qanqan da
kanta a gare shi, da tuba, ta kuma gyara dukkan sha'aninta, gwargwadon yardarSa,
Allah yana cewa: "Shin lokaci bai yi ba, ga waxanda su ka yi imani,
zukatansu su yi tawali'u ga ambaton Allah, da abin da ya sauka daga gaskiya" [Hadid:
16].
Kuma Allah (سبحانه) ya
ce: "Kuma ku tuba zuwa ga Allah gabaxaya, Ya ku muminai! tsammaninku ku
samu babban rabo" [Nur: 31].
Idan
kuma lamarin al'ummar ya cigaba akan turbar sabo, da kuma kukkutsawa cikin
haramun da aiyukan laifi, to ta sani lallai hanyar samun rabo yana nesa da ita, kuma kawo gyara ya yi hannun riga da
ita, "Ya ku waxanda su ka yi imani lallai, giya da caca da gumaka da kiban
quri'a qazanta ne daga aikin shexan, sai ku nisance shi, wa la'alla ku samu
rabo" [Ma'ida: 90].
Saboda,
Ga al'ummar, ga misali tana rayuwa cikin juya baya wa juna, da yanke zumunta,
da savani, da jayayya, da faxa, da qoqarin tunkuxe juna, wanda zubar da jini ke
biyo bayansu, da keta alfarmomi, har sashen mutane ya zama xanxanar bala'in
sashe, sai maganar Allah Mabuwayi da xaukaka ta tabbatu akan muatne: "Kuma kada ku yi
jayayya sai ku raunana, sai qarfinku kuma ya tafi"
[Anfal: 46].
Kuma maganar zavavven Annabi (صلى الله عليه وسلم) ta tabbatu akansu, a inda ya ce: "Kuma
matuqar shugabanninsu ba su yi hukunci da littafin Allah ba, to sai Allah ya
sanya faxansu ya dawo a tsakaninsu".
Kuma
ga al'ummar tana fama da koma-baya cikin tattalin arziqi, kamar yadda kuma hakan
shi ne halin da duniya gabaxaya ta samu kanta a ciki.
Saidai kuma hanyar tsira ga al'ummar annabi
Muhammadu daga durqushewar tattalin arziqi, da halin samun koma-baya ita ce,
yin tafiya kamar yadda tsarin Allah yarjejje ya shumfuxa, wanda duk lokacin da
al'umma ta kauce wa tsarin to sai ta faxa cikin cutuka da bala'oi "Ya ku waxanda su ka
yi imani kada ku ci riba ninki-ninki tivanye, kuma ku bi Allah da taqawa,
tsammaninku za ku samu babban rabo" [Ali-imrana: 130].
Ya ku
Musulmai!
Lallai
samun babban rabo yana qara rataya ne ga aikin al'ummar da ibadar umurni da
kyakkyawa, da hani kan aikata ababen qi, da yin nasiha wa juna, cikin abinda
zai kawo gyara a lamura, ya daidaita alqibloli, akan manhaji maxaukaki, da
uslubin zance wanda ke cike da haquri, da manufa maxaukakiya, da kuma hadafi
mai girma, Allah (سبحانه)
yana cewa:
((ولتكُن منكم
أمة...)) الآية.
Ma'ana: "Kuma wata al'umma
daga cikinku su kasance suna kira zuwa ga alkhairi, kuma suna urmurni da
kyakkyawa, kuma suna hani ga abin qi, kuma waxannan su ne samun babban rabo" [Ali-imran:
104].
Wasu maluman tafsiri su ka ce, kalmar "من" daga "منكم" a ayar, ba tana nuna sashe ne kawai ba,
a'a "MIN" ta qarin bayani ce.
Kuma
duk lokacin da musulmai su ka kauce daga wannan hanyar to, sai su auka cikin
hasara, su sake durqushewa, "Lallai ina rantsuwa da zamani * Lallai ne
Mutum yana cikin hasara * Face waxanda su ka yi imani, kuma su ka aikata
aiyukan kwarai, kuma su ka yi wa juna wasiyya da bin gaskiya, kuma su ka yi wa
juna wasiyya da yin haquri" [Asr: 1-3].
'Yan'uwa
Musulmai!
Kuma
lallai samun babban rabo yana qara rataya akan fahimtar tataccen musulunci;
addinin tsakaitawa, wanda ya yi nesa da wuce iyaka da qaqale da tsanantawa, (ta
xaya vangaren kuma) ya yi nesa da sakaci ko gajartawa, wanda ya zo cikin
hukunce-hukunce tabbatattu, a cikin wahayi biyu (na qur'ani da sunnah).
Saboda qetare iyaka wajen fahimtar addini (wato:
guluwwi), sau dayawa ya janyo wa musulunci da musulmai matsaloli masu girma, da
sharrace-sharrace da ba za a iya qididdige su ba, domin wuce iyaka, ya sava wa
abin da Allah ke nufi, da kuma sunnar Manzonsa zavavve (صلى الله عليه وسلم), "Kuma kamar haka ne, mu ka sanya ku
al'umma matsakaiciya" [Baqara: 143].
Ya ku taron Musulmai!!
Lallai samun babban rabo a duniyance, wanda
shi ne samun bunqasa a cikin al'umma, da samun wadacin jama'a, ta hanyar
tunkuxowar ni'imomi masu yawa, da albarkoki xaya bayan xaya, baya kasancewa
kawai da yin aiki da sabuba na zahiri, a'a, sai an haxa da yin aiki da sabuba
na ma'ana na haqiqa, kamar tsayuwa akan sunna, da dawwama akan aiki da tsarin
shari'a, Allah (تعالى)
yana cewa: "Kuma duk wanda ya bi Allah da taqawa, to Allah zai sanya masa mafita
* kuma ya azurta shi daga inda baya zato" [Xalaq: 2-3].
Kuma Allah wanda sha'aninsa ya xaukaka ya ce:
"Kuma da ma'abuta alqaryu sun yi imani, kuma su ka yi taqawa, to da
mun buxe albarkoki akansu daga sama da qasa" [A'araf: 96].
Ya al'ummar
musulunci!
Haqiqa
dayawa daga musulmai bayan gushewan zamanin mulkin mallaka sun jarraba a cikin
rayuwarsu, sun jarraba bin misalai na ra'ayoyin da aka shigo da su (daga wajen
islama) da waxanda su ka shigo, sai dai al'ummomin musulmai ba su samu komai
daga waxannan ra'ayoyi tsare-tsaren ba, face varna cikin ra'ayoyi, da rauni ta
fiskar soja, da koma-baya cikin tattalin arziqi, da lalacewar halayya, da
rabuwar kai a cikin al'umma, su waxannan ra'ayoyin duniya mutane bata gyaru da
su ba, kamar yadda ta lalata wa wasu (dayawa) addininsu.
Sai
dai lokaci ya yi bayan mun ga dalilai a zahiri (a qasa), lokaci ya yi mu koma
ga hasken wahayi guda biyu (qur'ani da sunnah), kuma lokaci ya yi ga wanda ya
ximauce saboda ruxuwa da ya yi da wayewar da su ke nuna halayya a zahiri,
waxanda dalilai kuma na zahiri waxanda aka shaida su ka tabbatar cewa qarya ne
da varna aka lulluve, wanda su ke bayyana a lokacin maslahohi ko amfani irin na-qashin
kai, don haka waxannan dokoki (ko tsare-tsare) suna kama ne da zane mai kyau da
aka tabbatar da rubutunsu a jikin kundayen qasashe, saidai kuma duk lokacin da
aka yi aiki da su, to suna rushe qasashen musulmai, da ababen da su ka mallaka,
sannan su zama sababi tabbatacce na kwashe alkhairorin (da dukiyar) qasashen,
saboda dokoki ne da su ka fice daga dabaibayin gyaran da Allah Ubangiji ya
yarda da shi, kawai manufar irin waxannan dokokin ita ce, rushe tsare-tsare
na addini, da halayya, da ladabi, da
mutum-taka, Allah Mabuwayi da xaukaka yana cewa: "… Babu wanda ya fi
Allah kyan hukunci, ga mutane masu yaqini" [Ma'ida: 50].
Ina faxar wannan maganar,
kuma ina neman gafarar Allah wa ni da ku da
sauran musulmai daga kowani zunubi,
sai ku nemi gafararsa, lallai shi Mai gafara
ne Mai rahama.
HUXUBA TA BIYU
Al'ummar
musulmai ta mallaki sabuban samun buwaya da nasara, irin abinda wata al'ummar
bata mallaka ba. Kuma wannan al'ummar ta kevanta da ababen da su ke tsayar da
gyara da sa'ada, irin abinda babu a wajen wata al'ummar.
Kuma
tarihin wannan al'ummar a qarnuka da suka shuxe babban mai shaida ne akan haka,
kuma hujja mafi girma.
Saidai
kuma samun nasararta an sharxanta masa wasu sharuxoxi, kuma na rataye da ababen
da su ke jawo shi, "Ya ku waxanda su ka yi imani idan ku ka taimaki Allah, zai
taimake ku, kuma ya tabbatar da dugaduganku " [Muhammadu: 7].
"Lallai ne mu za mu taimaki manzanninmu da
waxanda su ka yi imani a rayuwar duniya, da ranar da masu shaida su ke tsayawa"
[Gafir: 51].
Shima
kiyayewan da Allah zai yi ga wannan al'ummar ana sanya masa sharaxin yin aiki
ko xa'a ga shari'arSa, da nisantar mutane ga abinda ya tsawatar, "Lallai ne Allah
yana bada kariya ga waxanda su ka yi imani" [Hajji: 38].
A wata qira'ar sai aka ce, "يدفع" a gurbin "يدافع".
Kuma ya zo cikin hadisi ingantacce: "Ka kiyaye
Allah, sai ya kiyaye ka".
Amincin
wannan al'ummar da zama lafiyanta, da walwala a rayuwarta, a qulle ya ke da
tsayuwar al'ummar da imani, da duk abin da imanin ke hukuntawa, da kuma musulunci
da haqqoqinsa, "Waxanda su ka yi imani, kuma basu gauraya imaninsu da zalunci ba,
waxannan suna da aminci, kuma su ne shiryayyu" [An'am: 82].
Kuma
wannan al'ummar za ta samu xaukaka ne akan maqiyanta, ta yi rinjaye akansu,
gwargwadon abinda ke tare da ita na imani da haqiqaninsa da wajibabbunsa, kamar
yadda Ibnulqayyim ya ke faxan hakan.
Allah (تعالى)
yana cewa: "Kuma kada ku yi rauni, kuma kada ku yi baqin ciki, alhali kuwa kune
mafiya xaukaka, idan kun kasance masu imani" [Ali-imran: 139].
"Kuma lallai rundunarmu sune masu rinjaye"
[Saafaat: 173].
Ibnu-kasir (Allah ya yi masa rahama) a
qarqashin tafsirin faxin Allah Maxaukakin sarki : "Ya ku waxanda su ka
yi imani, ku yaqi waxanda suke kusa da ku daga kafirai, kuma su sami tsanani
daga gare ku, kuma ku sani cewa Allah yana tare da masu taqawa"
[Tauba: 123] Ibnu Kasir ya ke cewa: ((Kuma duk lokacin da wani sarki daga
sarakunan musulunci ya tsayu, ya kuma yi biyayya ga umurnin Allah, ya dogara ga
Allah, to sai Allah ya buxe masa garurruka, sai kuma ya dawo da wasu garurrukan
daga hannun maqiya, gwargwadonsa, da kuma gwargwadon abinda sarkin ya ke da
shi, na jivintar la,arin Allah –wato: walittaka-)).
Sannan
ku sani, lallai yana daga cikin mafi tsarkin abinda rayuwarmu za ta tsayu da
shi, shagaltuwa da yin salati da sallama
ga Annabi mai karimci,
Ya
Allah! Ka yi salati da sallama da albarka ga annabinmu kuma shugabanmu,
masoyinmu Muhammadu.
Ya
Allah! Ka yarda da khalifofi shiryayyu, shugabanni masu shiryarwa,
Abubakar da Umar da Usman da Aliyu.
Ya
Allah! Ka gyara halinmu da halin musulmai,
Ya Allah! Ka yaye baqin ciki, da
vacin rai.
Ya Allah! Ka tsamar da bayinka
musulmai, daga kowace fitina, da bala'i.
Ya Allah! Ka yi maqanin maqiya
musulmai, saboda su basu gagare ka ba, Ya Mai girma!
Ya Allah! Ka kiyaye 'yan'uwanmu musulmai
a kowani wuri,
Ya Allah! Ka kasance a gare su, Mai
taimako, mai basu nasara, Ya Mabuwayi Ya Mai tsananin qarfi.
Ya
Allah! Ka datar da mai hidimar harami biu maxaukaka, zuwa ga abin da ka ke
so, kuma ka yarda da shi, Ya Allah ka bada nasara ga addini da shi, kuma ka
xaukaka kalmar musulmai da shi, Ya Allah ka gafarta wa musulmai maza da
musulmai mata, rayayyu daga cikinsu da matattu,
Ya
Allah! "Ka bamu mai kyau a duniya, da mai kyau a lahira, kuma ka tsare mu
daga azabar wuta" [Baqara: 201].
No comments:
Post a Comment