HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 11 /SAFAR/1438H
Daidai da 11 /11/ 2016M
LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULMUHSIN XAN MUHAMMADU XAN ABDURRAHMAN
ALQASIM
TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
TSWATARWA KAN
RARRABA AKA DA SAVANI
Shehin Malami wato: Abdulmuhsin xan Muhammadu Alqasim –Allah ya kiyaye shi- ya
yi hudubar juma'a ta 11 Safar, 1438H, mai taken: TSWATARWA KAN RARRABA AKA DA
SAVANI,
Wanda a cikinta ya tattauna, kan haxin kai, da na zukata, da riqo da littafi da
Sunnah, Yana mai bayyana falalarsa, da girman tasirinsa, da kasancewarsa sababi
ne na tsira ga wannan al'ummar daga fitintinu, yana kuma tsawatarwa kan
rarrabuwar kai da savani da jayayya; saboda abinda su ke sabbabawa na saukar
jarabawa da bala'oi ga musulmai, da rarrabuwar kalmarsu, da kecewar sahunsu.
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne;
muna yaba maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman
tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan aiyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar, babu
mai vatar da shi, Wanda kuma ya vatar, to babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su qara
tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.
Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da
taqawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, kuma ku kiyaye shi a asirce da a
bayyane.
Ya ku musulmai …
Allah ya halicci annabi Adamu, kuma ya halifantar da shi
a doron qasa, domin yin bauta a gare shi, sai zurriyarsa a bayansa suka haxu
akan tauhidin Allah da sonsa tsawon qarni goma, daga bisani, sai shexan ya
zamar da su, ya kuma karkatar da su daga addinin Allah da yin xa'a a gare shi,
sai su ka rarraba; bayan kasancewarsu al'umma xaya, Allah (تعالى) yana faxa a cikin hadisin qudusiy: " Na
halicci bayina akan miqaqqen addini gabaxayansu, kuma lallai su, shexanu sun zo
musu, sai su ka karkatar da su daga addininsu", Muslim ya ruwaito
shi.
Sai Allah ya zarge su, akan
sava wa junansu, kuma ya turo musu manzanni, domin su haxa kalmarsu, su kuma
daidaita tsakanin zukatansu akan gaskiya, Allah (تعالى) ya ce: "Mutane ba su,
kasance ba, face al'umma xaya, sai su ka yi savani, kuma ba don wata kalma da
ta rigaya daga Ubangijinka ba, da an yi hukunci a tsakaninsu cikin abinda su ka
kasance a cikinsa su ke sava wa juna" [Yunus: 19].
Sai Allah ya zavi banu-isra'ila, kuma ya sanya annabawa
da manzanni a cikinsu, amma sai su ka sava musu, su ka kuma watsar da littafi a
bayan bayansu, su ka rarraba izuwa qungiya-qungiya, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Yahudawa
sun rarraba zuwa qungiya saba'in da xaya, Nasara su ma sun rarrabu har zuwa
qungiya saba'in da biyu, kuma al'ummata za su rarrabu zuwa qungiya saba'in da
uku",
Ibnu-Hibbana ya ruwaito shi.
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya tsawatar akan rarrabuwar kai, a inda ya ce: "Kuma ina
hana ku rarraba kai!",
Tirmiziy ya ruwaito shi.
Sai kuma ya bada labari, cikin gargaxi cewa za a samu
aukuwar rarrabar kai a cikin wannan al'ummar, a inda ya ke cewa: "Yadda
sha'anin ya ke, lallai ne wanda ya rayu daga cikinku, zai ga savani dayawa", Ahmad ya ruwaito
shi.
Kuma Allah ya hani bayinSa daga rarrabar kai, a inda ya
ce: "Kuma ku yi riqo da igiyar Allah gabaxaya, kada ku rarraba" [Ali-Imraan: 103].
Kuma ya bada labari, cewa lallai hanyarsa guda ce, kuma
duk abinda ya sava wa littafin Allah, da Sunnah to hanyar shexan ne, yana raba
kan jama'a, kuma yana nisantar da su daga Mai rahama (wato: Allah), Allah (سبحانه) ya ke cewa: "Kuma lallai wannan hanyata ce miqaqqa, sai
ku bi ta, kada ku bi qananan hanyoyi, sai su kautar da ku daga hanyarSa [An'am: 153]
Kuma (Allah) ya yi wasici ga al'umma da abinda annabawa
su ka yi wasiyya da shi, na tsayar addini da nisantar rarrabar kai, a inda ya ke
cewa: "Ya shar'anta muku game da addini, abinda ya yi wasiyya da shi ga
Nuhu, da abinda mu ka yi wahayi izuwa gare ka, da abinda mu ka yi wasici ga
Ibrahima da Musa da Isa; cewa: Ku tsayar da addini sosai, kuma kada ku rarrabu
a cikinsa[Shura:
13].
Kuma Allah (سبحانه) ya zargi rarrabuwar kai, kuma ya aibanta wa ma'abutanta, a
inda ya ce: "Kuma waxannan da su ka sassava, a lamarin littafi, haqiqa suna cikin
savani mai nisa"
[Baqara: 176].
Kuma ya siffanta halinsu,
da faxinsa: "Sai su ka yayyanka lamarinsu a tsakaninsu guntu-guntu, kowace
qungiya da abinda ke wurinsu masu alfahari ne" [Mu'uminuna: 53].
Qoqarin samar da rarrabuwar kai, na daga sifofin
munafikai, Allah (سبحانه) yana cewa: "Waxannan da su ka
riqi wani masallaci domin cuta, da kafirci, da neman kawo rarraba tsakanin muminai" [Tauba: 107].
Kuma akan haka, aka
xabi'antar da su "Kana zatonsu a haxe, alhali kuwa, zukatansu daban-daban
su ke"
[Hashr: 14].
Kuma rarrabuwar kai, tana daga sifofin da mutanen
jahiliyya su ka kevanta da ita, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya fice daga xa'a, kuma ya
rabu da jama'a, sai ya mutu, to ya yi mutuwa, irin ta jahiliyya", Muslim ya ruwaito
shi.
Kuma Allah (سبحانه وتعالى) ya yi hani, kan kamantacceniya, da ma'abuta savani, ya kuma tsawatar
kan bin hanyarsu, a inda ya ce: "Kuma kada ku kasance, kamar waxanda su ka rarrabu,
kuma su ka yi sava wa juna, bayan hujjoji bayyanannu sun zo musu" [Ali-imrana: 105].
Kuma Allah ya barrantar da ManzonSa daga ma'abuta
rarraba, a inda ya ce: "Lallai waxanda su ka rarrabe addininsu, su
ka zama qungiya-qungiya, baka cikinsu a wani abu, kuma lallai lamarinsu yana
ga Allah, sa'annan ya basu labari akan abinda su ke aikatawa[An'am: 159].
Kuma ma'abuta rarrabar kai, masu sava wa annabi ne, masu
rabuwa da jama'ar muminai, Allah (تعالى) ya ce: "Duk wanda ya sava wa Manzo, bayan shiriya
ta bayyana masa, kuma ya bi wanin hanyar muminai, za mu jivinta masa abinda ya
jivinta, kuma mu shigar da shi jahannama, kuma lallai makoma ta yi muni" [Nisa'i: 115].
Kuma
mafi girman rarraba kai shi ne: kauce wa tauhidin Ubangijin talikai, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma kada ka roqi, baicin
Allah, abinda baya amfanar ka, baya cutar da kai, idan kuma ka aikata, to
lallai kai kana daga azzalumai" [Yunus: 106].
Kamar yadda qirqiro bidi'oi a cikin addini rabuwa ne da
bin fiyayyen manzanni, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya aikata wani aiki, da babu
umurninmu akansa, an mayar masa", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma ficewa xa'ar shugabanni da jagorori, da jayayyar
shugabanci ga ma'abutansa varna ne mai girma, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya
cire hannu daga xa'a, lallai shi zai zo a ranar qiyama bashi da wata hujja,
kuma duk wanda ya mutu, alhalin ya raba kansa da jama'a, to lallai zai mutu
mutuwa irin ta jahiliyya", Ahmad ya ruwaito shi.
Kuma ma'abuta ilimi jagorori ne a cikin al'ummai, kuma su
suka fi cancantar haxe zukatansu, da haxin kansu, kuma samun savani a
tsakaninsu ya kan jawo rashin karvar sakwanni daga gare su. Wannan ya sa, lokacin da Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya yi wasiyya ga Mu'azu da Abu-Musa (رضي الله عنهما) a yayin da ya tura su zuwa qasar Yaman, sannan
ya ce musu: "Ku sassauta kada ku tsananta, ku yi albishir, kada ku kori
jama'a, kuma ku daidaita a tsakaninku, kada ku riqa savani", Bukhariy da Muslim
suka ruwaito shi.
Kuma ya yi hani kan savani a cikin gaskiya, a inda ya ce:
"Ku karanta qur'ani idan zukatanku su ka haxu akansa, idan ku ka
yi savani a cikinsa, sai ku tashi", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
Rarrabuwa cikin lamarin tsayar da sallah da rashin haxuwa akanta
yana daga vatarwan shexan, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Babu mutum uku a alqarya ko a qauye
da basa tsayar da salla a cikinsu face shexan ya vatar da su, ina horonku da
jama'a, saboda kerkeci yana cinye dabbar da ta yi nisa ne", Abu-dawud ya
ruwaito shi.
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya yi inkarin karkasuwar mutane a lokacin jiran salla, Jabir
bn Samurah (رضي الله عنه) ya ce: "Manzon (صلى الله عليه وسلم)
ya fito zuwa gare mu sai ya ganmu halqa-halqa, sai ya ce: Me saya na ke ganinku
a rarrabe",
Muslim ya ruwaito shi.
Kuma ya hana masu sallah sassavawa cikin safunsu, kuma ya
faxi wa'iydi ga masu aikata haka, da cewar fiskokinsu za su rarraba, kuma hakan
zai kai ga rabuwar zukatansu, saboda savawar zahiri sababi ne na samun savani
har a baxini, Manzon Allah (صلى
الله عليه وسلم) ya ce: "Ko ku daidaita sahunku, ko kuma
Allah ya sassava tsakanin fiskokinku", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma sava wa liman a cikin aiyukan sallah na daga
alamomin savani da rarrabuwa na zahiri, waxanda musulunci ya yi hani akansu,
Manzon Allah (صلى
الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai an sanya liman ne domin a yi
koyi da shi, kada ku sava masa", Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma kamar yadda musulunci ya yi hani kan rarrabuwa cikin
lamuran addini, to kuma ya sake hana mutane rabuwa cikin lamuran
duniya,
saboda haxuwa akan abinci yana
gadar da albarka, yayin da rarrabuwa a cikinsa ke tafiyar da albarka, Wasu
Mutane sun koka wa Annabi (صلى
الله عليه وسلم) su ka ce: "Lallai muna cin abinci, saidai bama
qoshi, Sai ya ce: La'alla kuna rarrabuwa? Su ka ce: E, Sai ya ce: Ku
riqa haxuwa akan abincinku, ku kuma ambaci sunan Allah, sai a sanya muku
albarka a cikinsa",
Abu-dawud ya ruwaito shi.
A lamarin tafiya kuma, Annabi (S.A.W) ya sanya rabuwar abokan
tafiya da cewa hakan hanyar shexan ce, a inda ya ke cewa: "Lallai
rarrabuwarku a cikin waxannan hanyoyi da kwari, lallai aikata hakan daga shexan
ne",
Abu-dawud.
A cikin alaqoqin zamantakewar al'umma, ya yi hani kan qaurace wa
juna, da yanke hulxa ko alaqa a tsakanin musulmai, a inda ya ce: "Baya
halatta ga musulmi ya qaurace wa xan'uwansa fiye da darare uku, su haxu da
juna, sai wannan ya kawar da kai, wannan ya kawar da kai, kuma mafi alherinsu
shine wanda ya fara yin sallama daga cikinsu" Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
Kuma ya bada labari cewa "Lallai
qofofin aljanna ana bubbuxe su a ranar litinin da ranar alamis, sai a gafarta
wa kowani bawan da bai yi shirka wa Allah da komai ba, sai ga mutumin da a
tsakaninsa da xan'uwansa ya kasance akwai qiyayya, sai a ce: Ku jira waxannan
har sai sun yi sulhu, ku jira waxannan har sai sun yi sulhu" Muslim ya ruwaito shi.
Kuma ya yi hani kan qabilanci, da kururuwa irin na
jahiliyya, Wani mutum ya ce: Kururuwa ga mutanen Madina! Wani kuma ya ce:
Kururuwa ga ma'abuta hijira (daga Makka), sai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Me ya faru,
da kururuwa irin ta jahiliyya, ku qyale (qabilanci) domin tana da wari", Bukhariy da Muslim
suka ruwaito shi.
Kuma Allah baya son savawar bayinsa, kuma bai yarje musu
shi ba, kuma savani ba zai kasance a tsakaninsu ba, face daga wurin wanin Allah
ya ke. Kuma haqiqa dalilai na wannan shari'ar sun yi nuni kan haramcin dukkan
abinda ke wajabta rarrabuwar kai da savani. Kuma hakan yana daga manufofin hani
a addinan manzanni, sai hani ya zo akan kowace hanyar da za ta kai zuwa ga
rarrabuwar kai a tsakanin musulmai, na daga/ munana zato, da hassada, da
binciken asiri, da annamimanci, da riba, da sayarwa akan sayarwar musulmi, ko
neman aure akan neman aurensa, da bibiyar al'aurarsa, da algus.
Kuma Allah ya yi umurni da daxaxa zance, kuma ya yi hani
akan mummunan Magana, domin samar da haxin kai, da tunkuxe kishiyarsa, a inda
yak e cewa: "Kuma ka ce wa bayina, su faxi zancen da ya fi kyau, lallai shexan
yana zugi da waswasi a tsakaninsu" [Isra'i: 53].
Kuma mafi girman abinda ke janyo rarraba shi
ne: Shirka,
saboda shirka tana hukunta a samu banbanci, da yawaitan ababen bauta, koma
bayan Allah, Allah (تعالى) yana cewa: "Kada ku kasance
daga mushirkai * daga waxanda su ka rarrabe addininsu, su ka zama
qungiya-qungiya, kowace qungiya da abinda ke wurinsu, masu alfahari ne" [Rum: 31-32].
Amma musulmai kam, tun daga lokacin da Allah ya halicci annabiAdamu,
har qiyama ta tsaya, ba sa yin bauta sai ga Ubangiji guda xaya.
Shi kuma kawar da kai daga littafin Allah da Sunnah hanya ce ta jayayya da
savani. Kuma masu kawar da kansu daga gare su, su ne ma'abuta savani har zuwa
ranar qiyama.
Kumaduk lokacin da mutane suka bar sashin abinda Allah ya
umurce su da shi, sai gaba ta shiga tsakanisu, sai su rarraba. Kuma duk wanda
ya xauki sashin littafi, ya kuma bar sashi to yana kama da waxanda Allah ya ke
faxi akansu: "Kuma daga waxannan da su ka ce: lallai mu nasara ne, mun xauki
alqawarinsu, sai su ka mance wani rabo daga abinda aka musu gargaxi da shi, sai
muka rura gaba a tsakaninsu da qiyayya zuwa yinin qiyama" [Ma'ida: 14].
Kuma bin dalilai mutashabihai, karkata ne ga ma'abutansa,
kuma fitina ne ga halittu, "… Amma waxanda a cikin zukatansu akwai
karkata, suna bin abinda ya zama mutashabihi daga cikinsa, don neman fitina, da
neman tawilinsa"
[Ali-imrana: 7].
Shiga qofofin shubuhohi, da tafiya a bayan sha'awoyi cuta
ce, da ta vata al'ummai, ta kuma rarrabe kan mutanensu, Allah (تعالى) yana cewa: "Kamar waxanda suke
a gabaninsu sun kasance sun fi ku tsananin qarfi, kuma sun fi yawan dukiya da
'ya'ya, sai su ka ji daxi daga rabonsu, sai kuma ku ka ji daxi da rabonku,
kamar yadda waxanda su ke gabaninku su ka ji daxi da rabonsu, sai ku ka
kukkutsa kamar yadda su ka kukkutsa, Waxannan aiyukansu sun ruguje a duniya da
lahira, kuma waxannan su ne masu hasara" [Tauba: 69].
Kuma bin hanyoyin shexanu qarshensa shi ne rarrabar kai,
kamar yadda Allah (سبحانه) yana cewa: "Kuma kada ku bi
qananun hanya, sai su kautar da ku daga hanyarsa" [An'am: 153].
Kuma mutane ba za su yi zalunci ba, face sun rarraba,
Allah yana cewa: "Waxanda aka basu littafi basu yi savani ba, sai bayan
ilimi ya zo musu, suna masu yin zalunci a tsakaninsu" [Ali-imrana: 19].
Kuma duk lokacin da savani ya auku, sakamakon son zuciya,
ko qabilanci, ko zalunci, da taqlidi, ko ta'assubanci da qungiyanci, to hanya
ne na rabuwar kai, kuma wajibi ne a nisance shi.
Shi ma neman riaggageniya akan lamuran duniya sababi ne
na samun adawa da qiyayya, Manzon Allah (ى الله عليه وسلم) ya ce: "Na rantse da Allah! Ba talauci na
ke tsorace muku ba, saidai ina tsorace muku, a shumfuxa muku duniya kamar yadda
aka shumfuxa ta ga waxanda suka kasance gabaninku, sai ku yi tsere akanta, kamar
su ka yi, sai kuma ta halaka ku, kamar yadda ta halaka su", Bukhariy da Muslim
suka ruwaito shi.
Rayuwar ma'abuta rarrabar kai, tana cikin wargajewa, kuma
shexan ya xebe tsammanin za a bauta masa daga masu salla (wato musulmai) a
tsibirin larabawa, saidai zai yi ta ziga tsakaninsu da nufin vata su. Kuma
shexan baya samun kan wasu mutane sai bayan ya kawo rabuwar kai tsakaninsu,
Manzon Allah (صلى
الله عليه وسلم) ya ce: "Na hore ku da lazimtar jama'a, kuma
ina tsawatar da ku daga rarrabuwa, saboda shexan yana tare da mutum xaya, kuma
ya fi nisa daga mutane biyu", Tirmiziy ya ruwaito shi.
Wanda ya fi kusancin matsayi zuwa ga Iblis daga cikin rundunoninsa
shi ne wanda ya fi tsananin kawo savani a cikinsu, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai
Iblis yana sanya gado ko karagar mulkinsa kan ruwa, sannan sai ya tura
mayaqansa, wanda ya fi kusancin matsayi zuwa gare shi, shi ne wanda ya fi su
tsananin kawo fitina, Xayansu zai zo ya ce: Na aikata kaza, da kaza, Sai ya ce:
Baka aikata komai ba. Ya ce: Sai wani y azo ya ce: Ban barshi ba, har sai da na
say a rabu da matarsa (wato: shika), Ya ce: Sai ya kusantar da shi zuwa gare
shi, yana cewa: Madalla da kai!" Muslim ya ruwaito shi.
Yin savani cikin addini, da bin son zuciya ko ra'ayoyi
masu vatarwa suna kange mutane daga hanyar Allah da addininsa, kuma da su, ake
kaucewa daga hanyar annabawa da salon tafiyarsu, saboda dukkan annabawa sun yi
umurnin a tsayar da addinin Allah, da haxuwa akan gaskiya, da rashin rarraba
kai, a cikinsa.
Kuma idan savani ya auku, to sai ya lalata addinin
ma'abutansa, sais u watsar da littafin Allah, sai son zuciya ta yi rinjaye
akansu, sai qarfin hujjar ilimi da shiriya su tafi. Kuma rarrabuwar kai ake
samun savanin zukata, da yankewar alaqoqi na dangata, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Kada ku yi
savani sai zukatanku su rarraba", Abu-dawud ne ya ruwaito shi.
Kuma rabuwar kai shi ne
sababin gaba da qiyayya, Allah (تعالى) yana cewa: "Kada ku rarraba, ku tuna ni'imar Allah
akanku yayin da kuka kasance maqiya sai ya daidaita tsakanin zukatanku" [Ali-imrana: 103].
Kuma idan rarrabuwa ta auku sai ta bada qofa ga
manya-manyan zunubai, ta kai izuwa ga yaqi da zubar da jinane, Allah (تعالى) yana cewa: "Da Allah ya yi
nufi, da waxanda su ka zo a bayansu basu yi yaqi ba, bayan hujjoji sun zo musu,
saidai sun yi savani"
[Baqara: 253].
Mutane ba za su yi savani ba face sun wulaqanta sun yi
rauni, Allah (سبحانه) yana cewa: "Kuma kada ku yi
jayayya, sai ku wargaje, sai qarfinku ya tafi" [Anfal: 46].
Kuma idan savani ya auku a cikin wata al'umma, to ya
kasance awata alama ce ta fushin Allah akansu, Allah (تعالى) yana cewa: "Ka ce: (Allah) shi
ne Mai ikon ya turo muk da wata azaba daga samanku, ko daga qasan qafofinku, ko
kuma ya karkasa ku qungiya-qungiya, sai ya xanxana wa sashinku yaqin sashi" [An'am: 65].
Abdullah ibn Abbas (رضي الله عنه) ya ce: "qungiya,
wato soye-soyen zuciya da savani".
Uqubar rarrabuwar kai da ta fi gaggawa ita ce, maqiya su
mulke ku da qarfi, kuma Allah ya yi alqawari ga Annabinsa cewa "Ba zai
sallaxa maqiya ga al'ummarsa waxanda ba daga kayukansu ba, suna kwace
jagorancinsu ba, koda kuwa waxanda su ke sasanin duniya sun taru akansu, har
sai ya kasance sashinsu yana halaka sashi, kuma sashinsu yana riqar sashi
fursuna",
Muslim ya ruwaito shi.
Da yin jayayya, ko savani da rabuwar kai, gaskiya ke
vacewa, ake kuma rushen ginshiqan addini, ake kamantacceniya da mushirkai, da
yaxuwar vata, da maganganu ba tare da ilimi ba, da shagaltuwa da Magana, da
barin aiki da addini da karantar da shi, da da'awa zuwa gare shi, tare da
lalata alamomin addini na zahiri, na daga umurni da kyakkyawa, da hani kan mummuna.
Kuma da su (wato, savani, ko jayayya) ake xage ni'imomi; saboda an nuna wa
Annabi (صلى الله عليه وسلم) daren lailatul
qadari, sai ya fita domin ya bada labarin yaushe lailatul qadari za ta kasance,
sai mutane biyu daga cikin musulmai suka yi zage-zage, Sai ya ce: "Lallai ne
ni na fito domin in baku labarin lailatul qadari, kuma lallai ne wane da wane
sun yi zage-zage sai aka xage ta", Bukhariy ya ruwaito shi.
Mummunar qarshen savani shi ne halaka, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Kada ku yi savani,
saboda waxanda suka kasance a gabaninku sun yi savani sais u ka halaka", Bukhariy ya ruwaito
shi.
Kuma a lahira, fiskokin ma'abutan savani za su yi baqi,
Allah (تعالى) yana cewa: "Ranar da wasu
fiskoki za su yi hasken fari, wasu fiskokin kuma su yi baqi, Amma waxannan da
fiskokinsu su ka yi baqi, Shin, kun kafirce bayan imaninku, to ku xanxani azaba
saboda abinda kuka kasance ku ke yi na kafirci" [Ali-imrana: 106].
Abdullahi xan Abbas –رضي الله عنهما- ya ce: "Fiskokin
Ahlus-sunnah wal jama'a za su yi haske, ma'abuta rarrabuwar kai da savani kuma,
fiskokinsu za su yi baqi".
Kuma hannun Allah, yana kan jama'a, duk kuma wanda ya
fanxare to zai tafi wuta.
BAYAN
HAKA, YA KU MUSULMAI!
Rabuwar kai qasqanci ne, jayayya kuma sharri ne, savani kuma
rauni ne, karkasa lamura kuma lalata addini ne da duniya. Kuma dukkansu suna faranta
wa maqiya, kuma suna jawo rauni ga qarfin al'umma, kuma suna kawo tsaiko ko
jinkirta tafiyar da'awa, kuma suna toshe hanyoyin yaxa ilimi, kuma suna rura
wutar baqin cikin a qiraza, kuma suna sanya zukata su zama baqaqe, su tafiyar
da tsaftar rayuwa, su cinye lokuta, su kuma shagaltar da bawa daga aikata
aiyuka kyawawa, su kuma kawo duhu ga mutane masu zuwa, saboda ba a shirya musu
abinda za su amfana da sub a.
Mai hankali kuma shi ne
wanda ya kawar da kai ga barin savani, ya kuma yi riqo da Alqur'ani da Sunnah, ya
gyara kansa, da waninsa.
A UZU BILLAHI MINASH
SHAIXANIR RAJIM:
"Yak u waxanda suka
yi Imani ku yi biyayya wa Allah, ku yi biyayya ga Manzo, da jagororin lamura
daga cikinku, idan kuka yi jayayya cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga
Allah da manzo, idan kun kasance kun yi Imani da Allah da ranar qarshe, wannan
shi ne alkhairi, kuma mafi kyan makoma" [Nisa'i: 59].
ALLAH YAYI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALQUR'ANI MAI
GIRMA, ya kuma amfanar da ni, da ku da abinda ke cikinsa na ayoyi da tunatarwa
mai hikima, Ina faxan maganata wannan, kuma ina neman gafara wa ni da ku da
sauran musulmai daga dukkan zunubai, Sai ku nemi gafararSa, lallai ne shi ya
kasance Mai gafara Mai rahama.
HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah
kan kyautatawarSa; Godiya kuma tasa ce
bisa ga datarwarSa da kuma ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya; Ina mai girmama sha'aninSa.
Ina kuma shaidawa lallai
annabinmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa ne.
Allah yayi daxin salati a
gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da kuma sallama mai ninnukuwa.
Ya ku musulmai…
Yana mafi girman MANUFOFIN
MUSULUNCI tara kan ma'abutansa, da daidaita tsakanin zukatansu, da kawo sulhu a
tsakaninsu.
Kuma halitta ba za su gyaru
ba, sai idan sun haxu akan gaskiya da addini.
Kuma Allah ya yi hukunci
kan kasancewar muminai 'yan'uwan juna ne, ya ce: "Lallai muminai
'yan'uwan juna ne"
[Hujuraat: 10].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kamanta halin muminai
cikin soyayyarsu da jin qansu, da tausasawarsu, da misalign jiki guda xaya,
wanda idan wata gava ta tavu sai sauran jikin ya yi kururuwa domin ita, da
rashin barci ko jin zogi" Muslim ya ruwaito shi.
Kuma "Mumini ga
mumini kamar gini ne, sashensa yana qarfafar sashe" Bukhariy da Muslim
suka ruwaito shi.
Kuma hakan ni'ima ce da Allah ya bayar da ita ga bayinsa,
a matsayin falala daga gare shi da kyauta, Allah ta'alah ya ce: "Kuma ya daidaita
tsakanin zukatansu, da z aka ciyar da abinda ke cikin qasa gabaxaya da ba za ka
iya daidaita tsakanin zukatansu ba, saidai Allah shi ya daidaita tsakaninsu" [Anfal: 63].
Kuma yana wajaba akan musulmi, ya kiyaye wannan ni'imar
ta hanyar zama da zuciya lafiyayya, da kuma bayyanar da soyayyarsa ga mutane,
da yi musu nasiha.
Sannan ku sani; Lallai Allah ya umurce ku da yin salati da kuma
sallama ga Annabinsa …
Sai yace, a cikin mafi kyan
littafin da ya saukar: "Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yi salati
ga wannan annabin, Yak u waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da
sallamar amintarwa"
[Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama da
albarka, ga annabinmu Muhammadu,
Kuma Ya Allah! Ka yarda da khalifofi shiryayyu,
waxanda suka yi hukunci da gaskiya, kuma da shi, su ka kasance suke yin adalci,
Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, da kuma sauran sahabbai gabaxaya, Ka haxa
da Mu tare da Su, da kyautarka da karamarka, Ya Mafi kyautar masu kyauta.
Ya Allah! Ka xaukaka Musulunci da Musulmai, ka
qasqantar da shirka da Mushirkai, kuma ka ruguza maqiyan addini, Kuma ka sanya
–Ya Allah!- Wannan qasar cikin aminci da nitsuwa, da wadaci da walwala,
da kuma sauran qasashen Musulmai.
Ya Allah! Ka gyara halin Musulmai a kowani wuri.
Ya Allah Ka sanya qasashensu su zama wurin aminci
da zaman lafiya, Ya ma'abucin girma da karramawa.
Ya Allah! Ka haxa kalmarsu akan
gaskiya da shiriya, Ya Ubangijin halittu.
Ya Allah! Ka datar da shugabanmu zuwa ga
shiriyarka, ka sanya aikinsa cikin yardarka.
Kuma ka datar da xaukacin
jagororin lamuran musulmai zuwa ga aiki da littafinka, da yin hukunci da
shari'arka, Ya ma'abucin girma da karramawa.
Ya Allah! Ka taimaki rundumarmu, Ya Allah! Ka tabbatar
da dugadugansu, Ya Allah! Ka taimake su akan maqiya, Ya Mai qarfi, Ya
Mabuwayi.
"Ya UbangijinMu ka bamu mai kyau a duniya,
ka bamu mai kyau a lahira, kuma ka kare mu daga azabar Wuta" [Baqarah: 201].
Ya Allah Ka karva wa mahajjata hajjinsu, ka mayar
da su, garurrukansu, suna kuvutattu, masu riba, Ya ma'abucin girma da
karramawa.
Bayin Allah!!!
"Lallai ne, Allah yana yin umurni da adalci,
da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi,
da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah Mai
girma da daraja zai ambace ku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari,
kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke
aikatawa.
No comments:
Post a Comment