HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 01 /Julhijjah/1437H
daidai da 02/ Satumba/ 2016M
LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
DARRUSAN DA ZA A XAUKA
DAGA HAJJIN BANKWANA
Shehin Malami wato: Abdulbariy
bn Auwadh As-subaity –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: DARRUSAN DA ZA A XAUKA
DAGA HAJJIN BANKWANA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan hajjin bankwana, da
sashin abinda za a ciro daga cikinta na darrusa da abun lura, wanda kuma muhimmai
daga cikinsu su ne: Tsawatarwa kan shirka, da haqqoqin 'yan'adamtaka a
musulunci, da gusar da qabilanci irin na jahiliyya, wanda ya kasance a tsakanin
mutane gabanin turo manzanci, da wassun haka daga ma'anoni masu girma, da
balaga, wanda huxubar ta qunsa.
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah,
yabo ya tabbata ga Allah wanda ya sauqaqe hajjin xakinsa alfarma, Ina yabo a
gare shi -سبحانه- akan dukkan alheri
da falala masu kwalala.
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai yak e bashi da abokin tarayya, abin
bautar na farko da na qarshe, Ubangijin mutane.
Kuma ina shaidawa lallai
shugabanmu annabinmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, mafi alherin wanda ya yi
sallah, da azumi, ya kuma yi haji, ya yi tsayuwan dare.
Allah ya qara salati a gare
shi, da iyalansa da sahabbansa, salati mai dawwama, har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka:
Ina yin wasici a gare ku, da
ni kaina da bin dokokin Allah da taqawa, Allah maxaukaki yana cewa: "Ya ku waxanda suka
yi imani ku kiyaye dokokin Allah iyakar kiyayewa, kuma kada ku mutu face kuna
Musulmai"
[Ali-imrana: 102].
Duk lokacin da watan zulhijja ya zo, lokatan shiga aiyukan
hajji suka sauko, sai fefa mai haske daga fefofin tarihin musulunci ta haska, da kuma matsaya
daga matsayoyin Annabi (صلى
الله عليه وسلم), su ma sai su walqa.
Yana
daga muhimman alamomin tafiyar hajji –qari akan aiyukan ibadodi- waxancan ma'anonin da
suke da gamewa, da kuma qa'idodi da aqidodi masu fasaha; waxanda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya faxa wa musulmai a hajjinsa na
bankwana.
Qa'idodi ne ko aqidu waxanda hawayen bankwana ya kwalala
tare da jumlolin da aka faxe su, don haka ne kuma aka sanya masa sunan HUXUBAR BANKWANA , Kuma a cikin huxubar ne
ya tsawatar daga AIKATA SHIRKA, wanda (shirka kuma) ita ce cuta mai tsanani
da take yin mummunan kamu ga mutane, tana mai rurrushe asalinsu (na ginuwa akan
tauhidi). Allah (تعالى) yana cewa: "A lokacin da mu ka
tanadi wurin yin xaki ga Ibrahimu; da cewa, Kada ku yi min shirka da kowa, kuma
ka tsarkake xakina ga masu xawafi, da masu tsayuwa da ruku'i da sujjada" [Hajji: 26].
Kuma yana daga shirka: Riya sanin ilimin gaibu, ko cewa mutum yana
karvar wahayi daga sama, da
qirqirar bidi'a, da tsarkake wasu mutane, da riqon wasu mazajen a
matsayin tsani izuwa ga Allah, ana riya cewa sai da su ake biyan buqatu, ko
kuma ake gafarta tuntuve da kura-kurai.
A cikin huxubar bankwana ne, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم ) ya ke cewa: "Lallai ne jinanenku, da dukiyoyinku, da mutuncinku haram su
ke akanku, kamar haramcin yininku wannan, a cikin garinku wannan –Makkah-, a
cikin watanku wannan". Bukhariy da Muslim suka fitar da shi.
Waxannan qa'idodi ne tabbatattu da suke da alaqa da HAQQOQIN XAN-ADAM, ,,,
Kuma domin saboda kare
jinin Mutune ne, Allah ya ke cewa: "Kuma kuna da rayuwa a cikin haddin qisasi" [Baqara: 179].
A domin kare dukiya kuma, Allah
ya ke cewa: "Kuma varawo namiji da varauniya, ku yanke hannayensu" [Ma'ida: 38].
Kuma domin bada kariya wa
mutunci ne Allah ya ke cewa: "Mazinaciya mace da mazinaci, ku yi
bulala wa kowani xaya daga cikinsu bulala xari" [Nur: 2], Wannan ga
wanda bai tava aure ba kenan. …. Amma shi kuma wanda ya tava yin aure (idan yayi
zina) to hukuncinsa shine jefewa, har sai ya mutu.
Musulunci yana gina lamarin SAMUN AMINCI a zuciyar musulmi, kuma
yana gina lamarin samar da alaqoqi masu karimci a tsakanin mutane, cikin wasu
qulle-qulle na imani,,, 'Yan'uwantaka
ce don Allah wacce ta ke da haqqoqi, kuma a kanta akwai abubuwa na
wajibi,,, kamar zumuncin da ake sadar da
shi don Allah,,, da biyayya wa iyaye, da
kyautata makwabta, da abota, da nitsuwa da auratayya.
KUMA YANA DAGA QA'IDODIN HAQQIN 'YAN-ADAMTAKA A MUSULUNCI: Kasancewar baya halatta (wato: haramun ne) mutum
ya cutar da xan'uwansa da yake halarce, ko kuma ya wulaqanta mutum a lokacin da
ba ya nan, ,,, haramcin haka ya ke, sawa'un cutarwar za ta kasance ne a
jikinsa, ko ga ransa, kuma da zance ne, ko cikin aiki, ,,, saboda haka,
Musulunci ya haramta yin duka wa mutane ba tare da haqqi ba, kuma ya yi hani
kan aibantawa cikin laqabi, ko suka, ko nuna mutum da idanu, ko da kai, ko da
levva da nufin aibantawa, ya kuma hana yin izgili, ko zagi,,, Bukhariy ya
ruwaito cewa: ((Lallai wani mutum an yi masa haddi
sau dayawa saboda shan giya, Sai aka sake zuwa da shi wata rana, Sai -Annabi-
ya yi umurni aka yi masa bulala, Sai wani daga cikin mutane ya ke cewa: Ya
Allah ka tsine masa, mamakin yawan yadda ake zuwa da shi! Sai Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: Ka da ku
tsine masa; Ina yin rantsuwa da Allah! Abin da na sani, shi ne: Lallai shi,
yana son Allah, da Manzonsa".
Kuma musulunci ya kiyaye wa musulmi, tare da bashi wata
girmamawa bayan mutuwarsa, ,,, Wannan ne
kuma sababin da ya sanya (musulunci) ya yi umurnin a yi masa wanka idan ya mutu,
a kuma sanya masa likkafani, a yi masa sallah, a kuma bunne shi, kuma ya yi
hani kan karya qashin mamaci, ko yin ta'addanci wa gawarsa, da lalata ta,
Bukhariy ya ruwaito cewa, lallai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم): "Ka da ku zagi matattu; lallai ne su, sun tafi
izuwa ga abinda suka aikata".
Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) a cikin huxubarsa ta bankwana ya ce: "Kowani abu daga lamuran
jahiliyya su na qarqashin dugadugaina biyu na take su, ,,,". Muslim ya ruwaito
shi.
Kuma haqiqa lamarin zubar
da jini da kisan kai sun kasance a zamanin jahiliyya abu ne mai sauqi, kuma ran
xan-adam –a lokacin- ta kasance bata da wata qima, Sai musulunci ya zo, domin
ya kafa wasu ginshiqai ga rayuwa, wanda su ka bada wata alfarma ko girma ga ran
xan-adam, kuma su ka sanya kashe rai ba tare da wasu dalilai ba a matsayin
babban laifi ga haqqin mutune gabaxaya; wanda aka yi masa tanadin uquba, a
cikin faxin Allah (تعالى): "Wanda ya kashe rai
xaya ba tare da wata rai, ko kuma yin varna a bayan qasa ba, to kamar ya kashe
mutane ne gabaxaya"
[Ma'ida: 32].
Kuma haqiqa QABILANCI ya kasance gabanin turo Manzon Allah saiwarsa sun
kakkafu, gininsa kuma ya yi qarfi, ,,, Sai Manzon Allah ya samu ikon tunvuke
lamarin wariya ko fifiko da qabilanci, da dukkan kalolinsa, daga cikin mutane
ko qasar da ta ke biki ko raya tunawa da qabilanci, kuma suke Shewa -da
qabilanci- da babbar murya, kuma suke gina alfahari akan qabila, Sai ya ce: "Ya ku mutane! Lallai
Ubangijinku guda xaya ne, kuma mahaifinku xaya ne, Balarabe bashi da wata
falala akan ba'ajame, haka ba'ajame bashi da wata falala akan balarabe, Jan
mutum bashi da wata falala akan fari, haka farin mutum bashi da wata falala
akan ja, sai da taqawa".
Kuma a yayin da tunani; irin na qabilanci ya so ya fara
sulalowa ko shiga sahun musulmai a
lokacin wani yaqi: wato, baqon tunani a cikin al'umma mai tsarki, Sai Manzon
Allah (صلى الله عليه وسلم) wanda shine ke kula
da tafiyar wannan al'ummar gabaxayanta ya ce:
"Kiraye-kiraye
irin na jahiliyya, alhalin ni ina nan a tsakaninku?".
A nan, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) bai yarda a samu mafarin
banbance-banbance irin na qabilanci ba, koda kuwa cikin laffuza ne.
Nan kuma, ga Abu-Zarrin (رضي الله عنه) ya aibanta wani mutum da mahaifiyarsa, ya
kuma kira shi da: Ya! Xan baqar mata, Sai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya yi fushi, sannan ya ce: "Ka aibanta
shi da Uwarsa; Lallai kai mutum ne da a tattare da kai akwai hali irin na
jahiliyya".
Wannan maganar kuma bata
kwace wa Abu-zarrin (رضي
الله عنه) falalarsa ta musuluncinsa da kuma jihadinsa.
Kuma duk wanda ya kafu don qoqarin raya qabilanci, ko yin shewa
da babbar murya akan qabilanci, ko qoqarin gina alfahari akan qabila to sai
Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce musu: "Ku bar
lamarin qabilanci; saboda tana da wari".
A cikin huxubar bankwana Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "kuma farko
riba wanda, zan fara murqushewa ita ce: Riba ta gidanmu; ribar Abbas bn
Abdulmuxxalib, lallai shi vatacce gabaxayansa, ,,,".
Musulunci ya haramta riba ne saboda girman cutarwar ta, da
yawan varnar da ke cikinta, saboda riba tana lalata zuciyar mutum (tare da sanya
masa lalaci), kuma tana lalata rayuwar mutane, saboda abinda ta ke yaxawa na
tsaban kwaxayi da son kai, ,,, tana kashe ruhin jama'a, tana sabbaba adawa,
tana kuma shuka qiyayya a cikin rayuka. Allah (تعالى) yana cewa: "Waxannan da su ke cin riba, ba za su tashi
ba, sai kamar wanda shexani ya ke shafansa da massu" [Baqara: 275].
A cikin huxubar bankwana Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Kuma ku bi
dokokin Allah da taqawa kan mata, saboda kun karvi mata da amanar Allah,,,".
Kuma haqiqa addini ya
kiyaye wa mace haqqinta, ya kuma karrama ta; tana uwa ne, ko mata ko 'ya.
Sai ya sanya jikin mace ya zama mai alfarma; wanda baya
halatta ajnabinta ya kalle shi, ,,, bayan kasancewar jikinta a zamanin
jahiliyya haqqi ne da kowa ya ke tarayya akansa.
Kuma (addinin musulunci) ya baiwa mace, haqqin cin gado,
da kuma haqqin neman ilimi.
Kuma (addini) ya daidata tsakanin mace da namiji cikin
lada da sakayya, da cikin aiyuka na ibada.
A cikin huxubar bankwana Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Kuma na bar
muku abinda idan ku ka yi riqo da shi ba za ku vata ba, littafin Allah, ,,,".
Littafin Allah yana shiryarwa zuwa ga hanyar da tafi miqe
wa a sha'anonin mu'amaloli, da alkalanci da hukunci, da na dukiya, da tattalin
arziqi, da sani da tarbiyya da ilimi, da halayya, da zaman lafiya da aminci, da
wadaci ko tattali, Allah (تعالى) yana cewa: "Da ma'abuta alqaryu
sun yi imani, kuma sun yi taqawa, da mun buxe musu albarkoki daga sama da qasa" [A'araf: 96].
Kuma Allah (تعالى) y ace: "Sai n ace: ku nemi
gafarar Ubangijinku, lallai ne shi ya kasance Mai yawan gafara * Zai sauke muku
ruwa a samanku, na mamako * Kuma zai qarfafe ku da dukiyoyi da 'ya'ya, kuma zai
sanya muku lanbuna, kuma zai sanya muku qoramu" [Nuh: 10-12].
Saidai kuma, a lokacin da musulmai su ka bar aiki da
shiriyar alqur'ani sai su ka kasance guntu-guntu, qungiya-qungiya, waxanda
sashensu ke dukan wuya ko kasha sashi, Wannan kuma shi ne abinda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya tsawatar akansa, a hajjinsa na
bankwana, saboda ya faxa a wasu daga cikin huxubobinta: "Kada a
bayana ku komo kafirai (masu butulci) sashenku yana dukan wuyan sashe".
Allah yayi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai
girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa
mai hikima, Ina faxar maganata
wannan, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran
Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa, lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah kan kyautatawarSa, kuma godiya tasa
ce, akan datarwansa, da baiwakinSa.
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya ina mai
girmama sha'aninSa.
Ina kuma shaidawa lallai
shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa, mai kira zuwa ga
samun yardarSa.
Allah yayi daxin salati da
sallama a gare shi, da kuma iyalanSa da sahabbanSa da (annabawa) 'yan'uwansa..
Bayan haka:
Ina yin wasiyya a gare ku,
da ni kai na da bin dokokin Allah.
Allah, yana da wasu kyautuka da rahamomi a wasu daga
cikin yini masu albarka, waxanda bayinsa da ya yi musu dace, su ke dacen
samunsu,
YANA DAGA CIKIN WAXANNAN
YININ:
Yini kwanaki goma na zulhijjah; wanda Annabi (صلى الله عليه وسلم) yake cewa dangane da su: "Babu aikin
da ya fi falala a cikin wasu yini fiye da yin aiki a cikin waxannan yinin, Sai su ka
ce: Koda jihadi fiysabillalh, Sai ya ce: Koda jihadin, sai ga mutumin da ya
fita yana shigar da ransa, da dukiyarsa cikin hatsari –na halaka a fagen
jihadi- Sai bai dawo da komai ba".
Waxannan su ne kwanaki goma na watan zulhijja (daga
gobe), lokuta ne ko fili, na yin tsere cikin aiyukan xa'a da biyayya, da
qoqartawa wajen ambaton Allah, da addu'oi, da kuma girmama Allah.
Yana daga abubuwan da aka shar'anta, a cikin waxannan yinin: Yawaita sallolin nafila,
da faxin La ilaha illal lahu, da yin kabbarori da hamdala, da karatun qur'ani,
da sadaka ga faqirai da mabuqata, da taimakawa waxanda aka zalunta, da yin
biyayya wa iyaye, da sallolin dare, ,,, da wanin haka.
Kuma
yana daga cikin aiyukan: Azumin mutumin da ba mahajjaci ba, azumtar abin da ya sauwaqa
masa daga cikin kwanakin nan guda goma, musamman kuma yinin arfah; saboda
abinda ya tabbata a cikin sahihu Muslim, Daga Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) lallai shi ya ce: "Ina fatan
Allah zai kankare zunubin shekarar da ta gaba ce shi, da shekarar da za ta zo
bayansa".
Yana
daga abinda aka shar'anta: Girmama Allah ta'alah da faxin Allahu akbar, (kuma kashi biyu
ne); Shi kabbarar da a sake ya ke, yak
an kasance a dukkan lokuta, cikin dare ne ko yini, har zuwa lokacin sallan idi.
Ammab kabbarar da ta ke da lokaci kuma ta kan kasance ne, bayan sallolin
farillai, waxanda aka sallace su a cikin jam'i, Kuma mutumin da ba mahajjaci
ba, zai fara su ne tun daga asubar yinin arfa, Shi kuma mahajjaci daga azahar
xin yinin layya, Sai su ci-gaba har zuwa la'asar xin rana na qarshe daga cikin
kwanakin TASHRIQ.
Kamar
yadda ake shar'anta:
Yin layya.
Kuma duk wanda ya yi nufin ya yi layya, Sai watan
zulhijja ya shiga, to bai halatta ya yanke wani abu na gashi, ko ya yanke
faratu ba, har sai ya yanka dabbar layyarsa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Idan ku ka
ga jinjirin watan zulhijja, Sai xayanku ya yi nufin ya yi layya, to sai ya kame
gashinsa da faratunsa".
انتهى.
Sai ku yi salati, -Ya ku
bayin Allah- ga Manzon shiriya, saboda Allah ya umurce ku da aikata haka, a
cikin littafinsa; a inda yake cewa: "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna
yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare
shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].
???
???
???
"Lallai Allah yana yin umurni
da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha
da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai
riqa ambatonku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah
shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.
,,, ,,, ,,,
No comments:
Post a Comment