2016/09/16

HUdUBAR MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم) 15 ZULHIJJAH 1437H Daidai da 16 SATUMBA 2016M ta ABDULBARIY AS-SUBAITIY








HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 15/ZULHIJJAH/1437H
Daidai da 16/SATUMBA/2016M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY






TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
KANKARE ZUNUBI A LOKACIN HAJJI
     Shehin Malami wato: Abdulbariy xan Auwadh Al-Subaitiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a, 14 zulhijjah, 1437H, mai taken: KANKARE ZUNUBI A LOKACIN HAJJI , Wanda kuma a cikinta ya tattauna lokacin hajji, wanda aiyukansa su ka kusanci qarewa, da shirin mahajjata domin komawa qasashensu, Yana mai bayyana cewa babbar falalar aikin hajji shi ne kankare zunubai, da kasancewar mahajjaci zai koma kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi, da fefa sabuwa, Yana mai tunatar da mahajjata kan wajabcin kiyaye fefofinsu, tsarkaka daga zunubai,kamar yadda ya ambaci abubuwa na aiyuka masu falala, waxanda da sababinsu Allah ke kankare zunuban bayi.

بسم الله الرحمن الرحيم
Yabo ya tabbata ga Allah; Yabo ya tabbata ga Allah, yabo mai yawa, mai daxi, mai albarka a cikinsa.
Yabo ya qara tabbata ga Allah, gwargwadon abinda ke cikin sammai.  
Yabo ya tabbata ga Allah, gwargwadon abinda ke cikin qassai.
Yabo ya tabbata ga Allah, gwargwadon abinda ke tsakanin sama da qasa.
Yabo ya tabbata ga Allah, gwargwadon adadin kowani abu.

Yabo ya tabbata ga Allah, gwargwadon cikin sammai.
Yabo ya tabbata ga Allah, gwargwadon cikin qassai.
Yabo ya tabbata ga Allah, gwargwadon cikin sama da qasa.
Yabo ya qara tabbata ga Allah, gwargwadon kowani abu.

Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya.
Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu, kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa.
Allah yayi qarin salati a gare shi da iyalansa da sahabbansa, da qarin sallama.

Bayan haka:
Ina yin wasiyya a gare ku, da ni kaina da bin dokokin Allah,  Allah (تعالى) yana cewa: "Yak u waxanda su ka yi Imani ku bi dokokin Allah da taqawa, kuma ku kasance tare da masu gaskiya" [Tauba: 11].      

Ragowar aiyukan hajji sun kusanci karewa, Tawagogin Mahajjata su kuma sun fara daddaure kayayyakinsu domin komawa garurruka ko kasashensu, bayan gama hajji a wannan lokaci mai tarin nasara,wanda ya cika da tarin hidimomi da suka kammala, da kuma nasarori masu girma, da kuma aiyuka wanda dukkan bangarori na hukuma (wato: ma'aikatu) su ka yi aiki tukuru akansu, tare da bunkasa tunani-tunanin zamani, domin ganin sun yi hidima ga masu ziyara da mahajjata; Don haka;
Allah ya yi sakayyar alkhairi ga shugabannin wannan kasa, wadanda suka kashe dukiya a yalwace, kuma suka zuba ido a lokacin gudanar da aiyukan ...
kuma (Allah) ya yi albarka ga mazaje masu gaskiya da su ka aikata aikin daukaka, da kyautata tsare-tsaren hajji, sai su ka mayar da sharewar da ta ke ta haushi kurame, wadanda su ke munana surar nagartattun abubuwa, su ke kuma kirkiro labarun abubuwan karya, Shi hasken rana idan far ya fito, hannu baya boye shi!

Hakika Allah ya yi mana ni'imar lokutan xa'a, waxanda alherorinsu su ke bibiyar juna, kuma a cikinsu ne rahamomin Ubangiji (سبحانه) su ke lullube mu, da kuma gafara,,, 
Daga cikin waxanda aka yi musu gamda-katar ko dace -Allah ya ya sanya mu daga cikinsu; mu da ku- akwai wanda ya koma kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi (shi ne wanda ya yi hajj mabruur), 
Daga cikinsu kuma, akwai mutumin da Allah ya gafarta masa zunuban shekaru biyu...(shine mutumin da ya yi azumin yinin arfa kenan)

Wancan ita ce martaba maxaukakiya wanda mutanen da aka yi musu dace su ka kai izuwa gare ta, kuma sabuwar farar fefa mai tsarki wacce mutanen da suka zage damtse su ka same ta, ta kan tattara tunanin mai hankali, ta sanya shi yin aiki don kiyaye wannan xaukaka, da qoqarin wanzuwa akan wannan matsayi na xaukaka, wanda da shi ne, zai samu xaukakar gafara, da tatacciyar rahama.

Aiyukan masu taqawa a kowani lokaci shine tunkuxe munanan aiyuka da kyawawa, Allah (تعالى) yana cewa: "Lallai ne kyawawa suna tafiyar da munana" [Hud: 114].

            Qoqarin tsarkaka na yau da kullum, daga dauxoxin rayuwa, da dawwamammen tsarkake takardar aiki basa karewa, da karewar lokutan ibadu na musamman, kuma lamarinsu baya takaituwa da wani wuri kevantacce (kamar Makka da arfa, da Madina), ko da wani lokaci sananne (kamar: kwanaki goman zulhijja); wannan kuma kasancewar shu'umcin yin zunubai ya kan gadar da hana bawa aikata wani alheri, kuma ya haifar masa da tavewa, kuma lallai dabaibayin zunubai yana hana bawa tafiya zuwa ga biyayyar Allah, ko ya hana bawa gaggawa izuwa ga hidimar Ubangijinsa, Kuma don haka ne, Musulmi ya ke neman aiyukan da suke kankare zunubai, suke kuma xaga darajoji, domin ya tsarkake ransa, yana cikiyar samun tsarkaka da xaukaka.

YANA DAGA CIKIN MANYAN SABUBAN SAMUN GAFARA Tauhidin Allah da kaxaita shi cikin bauta; saboda duk wanda ya tabbatar da kalmar tauhidi a cikin zuciyarsa, to sai ta fitar masa so, da girmama, ko ganin kwarjinin duk abinda ba Allah ba, daga nan kuma sai zunubansa da kura-kurensa su qoqqone, gabaxayansu, koda sun kai kamar kunfan teku, kai wani lokacin suna ma iya juya zunuban zuwa ga aiyuka kyawawa.

Kuma ana kankare zunubai: Da yin guzurin bin dokokin Allah ko takawa, wanda shine mafi alherin guzuri, Allah ta'alah yana cewa: "Duk wanda ya yi takawar Allah yana kankare masa munanan aiyukansa, kuma sai ya girmama masa lada" [Xalaq: 5].

Kuma dukkan aiyuka masu falala suna kankare zunubai, kuma fage su ke, mai faxi don tsarkake rai daga dauxar sabo, kuma su kan yaye wa zukata qurar gafala da rafkana;
Kuma yana daga cikin haka: Kyautata alwala da xahara (tsarki), da girmama lamarin yin sallah a kan lokacinta, a cikin jam'i, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Shin ba zan nuna muku abinda Allah ke share kura-kurai da shi, kuma ya xaga darajoji da shi? Sai su ka ce: E, ka bamu labari ya Manzon Allah! Sai ya ce: Cika alwala a lokacin qin tava ruwa, da yawan taku zuwa ga masallatai, da jiran sallah bayan salla, yin hakan kamar ribaxi ne".
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Duk wanda ya yi tsarki –wato: alwala- daga gidansa, sai ya tafi zuwa ga wani xaki daga cikin xakunan Allah, domin ya aiwatar wata farilla daga cikin farillan Allah, takunsa guda biyu su kan kasance; xayan ya kan kankare masa kura-kurai, xayan kuma ya kan xaga daraja".
Kuma Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Kuna kuna, kuna kuna -idan ku ka aikata savo- amma idan ku ka yi sallar asuba sai ta wanke su. Sannan sai ku kuna, ku kuna, idan ku ka sallaci azahar sai ta wanke shi. Sannan sai ku kuna, ku kuna, idan ku ka sallaci la'asar sai ta wanke shi. Sannan sai ku kuna, ku kuna, idan ku ka yi sallar magrib sai ta wanke shi. Sannan sai ku kuna, ku kuna, idan ku ka yi sallar isha sai ta wanke shi. Sannan sai ku yi barci, ba za a rubuta muku savo ba har sai kun tashi daga barci".

Kuma ana kankare munana, ana xaga darajoji ta hanyar bayar da dukiya da ciyarwa da sadaka, Allah (تعالى) ya ce: "Idan ku ka yi sadaka a bayyane to madalla da ita, idan kuma ku ka voye ta, ku ka baiwa fakirai to alheri ce a gare ku, kuma sai ya kankare muku wasu daga cikin munananku" [Baqarah: 271], Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ita sadaka tana kashe tasirin laifi kamar yadda ruwa ke kashe wuta*.

Umurni da kyakkyawa, da hani da mummuna yana cikin ababen da suke kankare zunubai, su daga darajoji, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Fitina ko jarabawar da ake yi wa mutum cikin iyalansa da dukiyarsa da makwabcinsa salla tana kankare su, da azumi, da yin umurni da kyakkyawa da hani da mummuna*.

Yin gaskiya wa Allah, da yin gaskiya wa rai, da yin rayuwa cikin gaskiya suna daga ababen da suke kankare zunubai, Allah (تعالى) yana cewa: "Wannan, da ya zo da gaskiya, kuma ya gaskata shi, waxannan sune masu takawa * Suna da abinda suke so a wurin Ubangijinsu, wannan shine sakamakon masu kyautatawa * Domin Allah ya kankare musu mafi munin abinda suka aikata, ya kuma sakanta musu ladansu da mafi kyan abinda su ka kasance suke aikatawa" [Zumar: 33-35].

Kamar yadda imanin da ya samu tabbatuwa a lokacin da aka jarraba mutum shi ma yana kankare zunubai, kuma yana daga darajoji, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Babu abinda zai samu mumini na wahala ko gajiya ko cuta ko bacin rai, har damuwar da zata dame shi, face an kankare masa munanan aiyukansa da shi".

Bunqasa rayuwa ta hanyar raya qasa da gyara ta, shi ma yana kankare zunubai. Yin alheri ta hanyar kyautata wa Mutune shi kuma yana xaga darajoji, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wata rana wani mutum yana tafiya akan wata hanya sai ya samu reshen bishiyar qaya sai ya xauke shi, Sai Allah ya gode masa akan haka, kuma ya gafarta masa".

A tsakiyar nuna farin cikin isowar rayuka waxannan lokuta na musamman masu falala, da kuma kamfatar wani abu na falalansu da ladansu; Bawa ke qan-qan da kai, ya roqi Ubangijinsa cewa ya yi masa ilhama ko baiwar shiriya da tabbatuwa, sai ya riqa cewa, kamar yadda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance ya ke faxi: "Ya Allah lallai ne ni ina rokonka tabbatuwa cikin lamarin addini, da azama akan shiriya". Kuma yana cewa: "Ya Mai jujjuya zukata, ka tabbatar da zuciyata akan addininka".


            Allah yayi mini albarka ni da ku, cikin alqur'ani mai karamci, ya kuma amfanar da mu da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, Ina faxar maganata wannan, ina kuma neman gafarar Allah, sai ku nemi gafararSa,    lallai ne shi Mai gafara ne Mai rahama.
>>> 

HUXUBA TA BIYU
            Yabo na Allah ne wanda masu taqawa suka samu yardarSa.

Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, Muminai kuma sun tabbatar da haka.
            Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa, Masu binsa kawai su, za su samu cetonsa,
Allah ya yi qarin salati akansa da iyalansa da sahabbansa, duk lokacin da masu Ambato su ka ambace shi. 
           
Bayan haka:
Ina yi muku wasiyya da ni kaina da bin dokokin Allah, da taqawa.
Zikirin Allah ko ambatonsa yana kwararo da tarin albarkoki da rahamomi, kuma ya kan kasance cikin kalmomi marasa yawa, a cikin lokatai takaitattu, da niyya ta gaskiya, Sai kuma, a share zunubai, kuma Musulmi ya samu mafi kololuwar darajoji, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya ce: LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIR a cikin yini, sau 100, yana daidai da ya 'yanta bayi guda 10, kuma za a rubuta masa ladan kyawawa guda 100, a kuma, goge masa munana 100, kuma za su kasance tsari ne a gare shi daga shexan, tsawon wannan yinin nasa har ya kai yammaci, kuma babu wani mutum da ya zo da fiye da abinda ya zo da shi, sai mutumin da ya aikata fiye da nasa*.

Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya faxa a lokacin da ya ke jin mai kiran salla, WA ANA ASH-HADU AN LA ILAHA ILLAL WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, WA ANNA MUHAMMADAN ABDUHU WA RASULUHU, RADIYTU BILLAHI RABBAN, WA BI MUHAMMADIN RASULAN, WA BIL ISLAMI DIYNAN an gafarta masa zunubansa".

Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya ce: SUBHANAL LAHI WA BI HAMDIHI a cikin yini, sau 100, to an kankare masa kura-kuransa, koda sun kasance misalin kumfar teku ne".

Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya ce: SUBHANALLAHI sau 33 a bayan kowace sallah, ya ce: ALHAMDU LILLAHI sau 33, ya ce: ALLAHU AKBAR sau 33, sun zama 99, sai ya cikate xarin da faxin: LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIR to an gafarta zunubansa koda sun kasance kamar kumfar teku ne".

Wannan kaxan ne daga tarin rahama ko albarkokin Allah Mai karimci Mai baiwa.
Mai rabo kuma shine, wanda ke qoqarin neman karamomi, kuma ya ke qoqari domin a kankare masa zunubai, a kuma xaga darajojinsa, domin ya haxu da Ubangijinsa da fefofin aiyuka tsarkaka, tatattu; kasancewar Allah -Mabuwayi da xaukaka- yana shumfuxa hannunsa da dare, domin wanda ya munana a cikin yini ya tuba. Kuma yana shumfuxa hannunsa da rana domin mutumin da ya munana aiki cikin dare ya tuba, har zuwa lokacin da rana za ta fudo daga mafaxarta".

            Sai ku yi salati, -Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, sabodaAllah ya umurce ku da aikata haka, a cikin littafinsa; a inda yake cewa: "Lallai Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Yaku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].

Ya Allah! Ka yi salati wa Annabi Muhammadu da matansa da zurriyarsa, kamar yadda ka yi salati ga iyalan Ibrahima. Kuma ka yi albarka ga Muhammadu da matansa da zurriyarsa, kamar yadda ka yi albarka ga iyalan Ibrahima, lallai ne kai Abin godiya ne Mai girma.     
Ya Allah!Ka yarda da khalifofi guda huxu shiryayyu;    Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da iyalan Annabi da sahabbansa masu karimci, ka haxa da mu da afuwarka, da karramawarka, da kyautatawanka, Ya mafificin masu rahama.
            Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
kuma ka qasqantar da kafirci da kafirai, kuma
Ya Allah! Ka ruguza maqiyanka; maqiyan addini,
Ya Allah! Ka sanya wannan qasar ta zama da aminci, cikin nitsuwa, da sauran qasashen musulmai.
            Ya Allah! Duk wanda ya nufe mu, kuma ya nufi musulunci da mummuna, to ka shagaltar da shi da kansa, kuma ka sanya rugujewarsa cikin tsarinsa, Ya Mai amsa addu'oi.
Ya Allah! Duk wanda ya nufe mu, kuma ya nufi musulunci da mummuna, to ka shagaltar da shi da kansa, kuma ka sanya rugujewarsa cikin tsarinsa, Ya Mai amsa addu'oi.
Ya Allah! Duk wanda ya nufe mu, kuma ya nufi musulunci da mummuna, to ka shagaltar da shi da kansa, kuma ka sanya rugujewarsa cikin tsarinsa, Ya Mai amsa addu'oi.
Ya Allah! Ka kasance wa musulman da ake raunata su, a kowani wuri, Ya Allah ka kasance musu mai qarfafawa kuma mai taimako;
Ya Allah! Lallai su mayunwata ne, ka ciyar da su, marasa takalma, ka basu, tsirara sai ka tufatar da su, An zalunce su, sai ka taimake su, Ya Allah an zalunce su, ka taimake su, lallai an zalunce su, ka taimake su.
Ya Allah wanda ya saukar da littafi, mai gudanar da gajimare, mai rushe rundunoni; ka rushe maqiyanka; maqiya addini, kuma ka taimaki musulmai akansu, Ya Ubangijin halittu.
Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka aljanna, kuma muna neman tsarinka daga wuta.
Ya Allah! Muna roqonka alkhairi gabaxayansa; na gaggawa daga cikinsa da na nesa, wanda muka sani daga cikinsa da wanda ba mu sani ba, kuma muna neman tsarinka daga sharri gabaxayansa; na gaggawa daga cikinsa da na nesa, wanda muka sani daga cikinsa da wanda ba mu sani ba.
Ya Allah! Ka gyara mana addininmu wanda shi ne qashin bayan lamarinmu, kuma ka gyara mana duniyarmu wanda it ace mu ke rayuwa a cikinta, kuma ka gyara mana lahirarmu wanda it ace makomarmu, kuma ka sanya rayuwa ta zama qari ne a gare mu cikin kowani alheri, mutuwa kuma hutu daga kowani sharri, Ya Ubangijin halittu.
            Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka mabuxan alkhairi da qarshensu, da abinda ya tattara su, da farkonsu da qarshensu, da zahirinsa da baxininsa, kuma muna roqonka darajoji maxaukaka a cikin aljanna, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ka taimake mu, kada ka taimaki maqiya akanmu, ka bamu nasara, kada ka basu nasara akanmu, ka qulla mana akansu, kada ka qulla musu akanmu, kuma ka shiryar da mu, ka sauqaqe shiriya a gare mu, ka bamu nasara akan wanda ya zalunce mu.
            Ya Allah! Ka shumfuxa mana albarkokinka da rahamarka da falalarka da arziqinka.
            Ya Allah! Lallai ne mu muna neman tsarinka daga gushewar ni'imominka, da juyawar lafiyarka, da zuwan azabarka kwatsam, da xaukacin fushinka.
            Ya Allah! Ka gafarta wa iyayenmu da iyayensu, Ya Allah! Ka yi rahama ga mamatanmu, kuma ka warkar da marasa lafiyanmu, kuma ka jivinci lamuranmu, Ya Ubangijin halittu.
            Ya Allah! Ka datar da shugabanmu zuwa ga abinda kake so, kuma yarda, Ya Allah! Ka datar da shi zuwa ga shiriyarka, kuma ka sanya aiyukansa cikin yardarka, Ya Ubangijin halittu.
kuma ka datar da xaukacin majivinta lamuran musulmai, wajen yin aiki da littafinka, da hukunci da shari'arka, Ya Ubangijin halittu.
            Ya Allah! Ka kiyaye jami'an tsaronmu, Ya Ubangijin halittu.
Ya Allah! Ka kiyaye rundunoninmu masu tottoshe kafofin varna (ribaxi), Ya Allah! Ka kiyaye su cikin zurriyarsu da abinda su ka bari, da dukiyoyinsu, da 'ya'yansu, Ya Ubangijin talikai. Ya Allah! Ka kiyaye su da kiyayewarka, ka basu kariya da kulawarka, lallai kai mai iko ne akan kowani abu.
            "Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kayukanmu idan baka gafarta mana, ka yi mana rahama ba to zamu kasance daga cikin masu hasara" [A'araf: 23].
            "Ya Allah ka gafarta mana, da 'yan'unmu da su ka rigaye mu da imani, kuma kada ka sanya qyashi a zukatanmu, ga waxanda su ka yi imani, Ya Ubangijinmu lallai ne kai Mai tausasawa ne Mai jin qai" [Hashr: 201].
            Ya Allah! Ka kiyaye mahajjata xakinka mai alfarma, Ya Allah! Ka mayar da su zuwa garurrukansu suna kuvutattu masu ribata, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka sanya hajjin ya zama hajji na biyayya, kuma aiki abin godewa, da zunubin da aka gafarta, kuma aiki nagari karvavve lafiyayye, Ya Ubangijin talikai.
            "Ya Ubangijinmu! Ka bamu mai kyau a duniya, kuma ka bamu mai kyau a lahira, ka kare mu daga azabar wuta" [Baqarah: 201].


     "Lallai ne, Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanta, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,



No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...