HADISAI
KAN HALAYYAR MUSULUNCI DA LADDUBA
أحاديث الأخلاق
الإسلامية والآداب
TATTARAWA/TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم
الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشرف المرسلين،
وعلى آله وصحبه أجمعين، أما بعد:
فهذه طائفة كبيرة من الآثار النبوية التي تتعلق
بالأخلاق التي رغب إليها الإسلام، والتي
حذر منها، وبالآداب الإسلامية، والله أسأل القبول والإخلاص.
KAWAI,
hadisi ne guda daya za a tura, ta zaurenku, mai taken: DAGA TASKAR MA'AIKI (صلى الله عليه وسلم). Kuma ba za a kawo hadisi a wannan zauren
ba, Sai wanda ya inganta daga Manzon Allah (S.A.W), ta yadda za ka iya dauka
Kai-tsaye ka yi aiki da shi, Saboda KARATUN HADISI DA AIKI DA SHI, SHINE: TSIRA
Kuma za a iya yada su, a sauran zauruka domin, mu samu mu rabauta da yin aiki
da hadisin, da ke cewa: Ku isar daga gare ni, ko da aya ce guda. Idan kuma
hadisan suka taru; suka yi yawa: zamu tattara su a cikin wani littafi.
Allah
yayi mana albarka, mu da zurriyarmu gabadaya, Amin.
Lura
da shawara mai muhimmanci da na samu, daga karshe na fifita samar da abinda ake
ce masa "Broadcast list" maimakon group din da na bude. Don haka, a
sabon tsari, kowani aboki zai ga sakon hadisi, na kullum da nayi bayani ne ta
pravet dinsa, ba a group ba. Group din kuma zan goge.. . Ina godiya matuka.
الحديث الأول:
عن عُمَرَ بْنَ الْخَطَّابِ رضي الله
عنه قال: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ،
يَقُولُ: إِنَّمَا الأَعْمَالُ بِالنِّيَّاتِ، وَإِنَّمَا لكل امْرِئٍ مَا
نَوَى، فَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُهُ إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ فَهِجْرَتُهُ إِلَى
اللَّهِ وَرَسُولِهِ، وَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُه لدُنْيَا يُصِيبُهَا، أَوِ
امْرَأَةٍ يَنْكِحُهَا فَهِجْرَتُهُ إِلَى مَا هَاجَرَ إِلَيْهِ. متفق عليه
(خ: ١، م: ١٩٠٧).
HADISI NA FARKO
An
ruwaito daga Umar dan Alkhaddabi (r.a) ya ce: Na ji Manzon Allah (s.a.w) yana
cewa: Dukkan aiyuka suna tare da niyya, kuma lallai kowane mutum yana samun
sakamakon abinda yayi niyya; Wanda hijirarsa ta kasance saboda Allah ne da
Manzonsa to sakamakon hijirarsa tana ga Allah da Manzonsa. Wanda kuma hijirarsa
ta kasance saboda wata duniya ce da zai same ta, ko kuma wata matar da zai aure
ta, to sakamakon hijirarsa yana ga abinda yayi hijira dominsa.
Bukhariyy [1], da Muslim [1907]
suka ruwaito shi.
الحديث الثاني
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه
قَال:َ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّم:َ إِنَّ
اللَّهَ لا يَنْظُرُ إِلَى صُوَرِكُمْ وَأَمْوَالِكُمْ، وَلَكِنْ يَنْظُرُ إِلَى
قُلُوبِكُمْ وَأَعْمَالِكُمْ.
رواه مسلم (٢٥٦٤).
HADISI NA BIYU
An ruwaito daga Abu-hurairah (r.a)
ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Lallai ne Allah baya yin dubi izuwa ga
surar jikinku da dukiyoyinku, Saidai yana yin dubi ne izuwa ga zukatanku, da
aiyukanku.
Muslim [2564] ya ruwaito shi.
Muslim [2564] ya ruwaito shi.
Saboda hadisai biyu, da suka gabata, Sai mu tsayu Wajen gyara niyyoyinmu, da zukatanmu, da aiyukanmu, Allah ya taimake mu, Amin.
الحديث الثالث
عن أَنَس رضي الله عنهٍ: قَالَ: كَانَ
رَسُول اللَّه ِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَحْسَنَ النَّاسِ خُلُقًا.
متفق عليه (خ: ٦٢٠٣، م: ٢٣١٠).
HADISI NA UKU
An
ruwaito daga Anas (r) ya ce: *Manzon Allah ya kasance yafi dukkan Mutane kyan
hali*.
Bukhariyy [6203], da Muslim [2310] suka ruwaito shi.
Bukhariyy [6203], da Muslim [2310] suka ruwaito shi.
الحديث الرابع
عن عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رضي
الله عنهما أنه ذكر رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَال: لمْ
يَكُنْ فَاحِشاً وَلَا مُتَفَحِّشًا. وَقَالَ، قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى
اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: إِنَّ مِنْ خِياركُمْ أَحاسنَكُمْ أخْلُاقًا. متفق عليه (خ: ٣٥٥٩ م: ٢٣٢١).
HADISI NA HUDU
An
ruwaito daga Abdullahi bn Amrin -Allah ya kara yarda a gare su- lallai ne shi
ya ambaci Manzon Allah (S.A.W) sai ya ce: Manzon Allah bai kasance mutum mai
aikata ko fadin yasassun zantuka ba, kuma bai kasance mai kakalar hakan ba.
Sannan ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Lallai ne zababbu a cikinku sune
wadannan da suka fi kyan hali.
Bukhariy [3559], da Muslim [2321] suka ruwaito shi.
Bukhariy [3559], da Muslim [2321] suka ruwaito shi.
الحديث الخامس
عن أبي هريرة رضي الله عنه، قال: قال
رسول الله صلى الله عليه وسلم: أَكْمَلُ الْمُؤْمِنِينَ إِيمَانًا أَحْسَنُهُمْ
خُلُقًا، وَخِيَارُكُمْ خِيَارُكُمْ لِنِسَائِهِمْ خُلُقًا.
رواه أبو داود: برقم: ٤٦٨٢، والترمذي،
رقم: ١١٦٢، وقال: حديث حسن صحيح.
HADISI NA BIYAR
An
ruwaito daga Abu-Hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah
(S.A.W) ya ce: Muminin da yafi Muminai cikar imani shine wanda ya fi su kyan
hali. Zababbun cikinku kuma, sune wadanda suka fi kyan hali ga matansu.
Abu-Dawud [4682], da Tirmiziy [1162] suka ruwaito shi. Tirmiziy ya ce: *Hadisi ne mai kyau ingantacce*
Abu-Dawud [4682], da Tirmiziy [1162] suka ruwaito shi. Tirmiziy ya ce: *Hadisi ne mai kyau ingantacce*
الحديث السادس
عن أبي هريرة رضي الله عنه، قال: قال
رسول الله صلى الله عليه وسلم: الْإِيمَانُ بِضْعٌ وَسَبْعُونَ -أَوْ بِضْعٌ
وَسِتُّونَ- شُعْبَةً، فَأَفْضَلُهَا قَوْلُ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ،
وَأَدْنَاهَا إِمَاطَةُ الْأَذَى عَنْ الطَّرِيقِ، وَالْحَيَاءُ شُعْبَةٌ مِنْ
الْإِيمَانِ.
متفق عليه (خ: ٩ م: ٣٥).
HADISI NA SHIDA
An
ruwaito daga Abu-Hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah
(S.A.W) ya ce: Imani ressa ne guda saba'in da doriya, ko kuma ya ce: sittin
da doriya, Mafi girma daga cikinsu shine: Fadin LA ILAHA ILLAL LAHU. Wanda kuma
yafi kankanta shine: Gusar da ABU MAI CUTARWA daga hanya. Itama KUNYA reshe ne
daga ressan imani.
Bukhariy [9], da Muslim [35] suka ruwaito shi.
Bukhariy [9], da Muslim [35] suka ruwaito shi.
الحديث السابع
عن عمران بن حصين رضي الله عنه قال: قال رَسُول
اللَّهِ صَلَّى الله عليه وسلم: الحياء لا يأتي إلا بخير.
متفق عليه (خ: 6117م: 37). وفي رواية
لمسلم: الحياء خير كله.
HADISI NA BAKWAI
An
ruwaito daga Imrana bn Husaini -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon
Allah -Sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: Kunya ba ta zuwa face da
alkhairi.
Bukhariy [6117], da Muslim [37] suka ruwaito shi.
Bukhariy [6117], da Muslim [37] suka ruwaito shi.
A wata riwaya ta Muslim Kunya
dukkanta alheri ne.
الحديث الثامن
عن أَبِي ذرٍّ؛ جُنْدَبِ بنِ جُنَادَةَ
رضي اللَّه عنه قال: قال لي النبيُّ صلى اللَّه عليه وآله وسلم: «لاَ تَحقِرنَّ
مِن المعْرُوفِ شَيْئاً ولَوْ أنْ تلْقَى أخَاكَ بِوجهٍ طلقٍ».
رواه مسلم (2626).
HADISI NA TAKWAS
An
ruwaito daga Abu-Zarrin; wato: Jundub bn Junada -Allah ya kara yarda a gare
shi- ya ce: Manzon Allah -Sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce mini: Kada ka
raina kyakkyawan abu, koda kuwa ka hadu da 'dan'uwanka ne da fiska sakakkiya.
Muslim [2626] ya ruwaito shi.
الحديث التاسع
عَنْ أَبِي ذَرٍّ رَضِيَ اللَّهُ
تَعَالَى عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ: «تَبَسُّمُكَ فِي وَجْهِ أَخِيكَ لَكَ صَدَقَةٌ». رواه
التِّرْمِذِيُّ: ( 1956).
HADISI NA TARA
An
ruwaito daga Abu-Zarrin; -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah
-Sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: Murmushinka ga fiskar 'dan'uwanka, a
gare ka: sadaka ne.
Tirmiziy [1956] ya ruwaito shi, da
Ibnu-Hibbana [474, da 529], Tirmiziy ya ce: Hadisi ne mai kyau (hasan) .
الحديث العاشر
عن ابن عبَّاس رضي الله عنهما قال: قال
رسول الله صلى الله عليه وسلم للأشجِّ -أشجِّ عبد القيس-: «إِنَّ فِيكَ
خَصْلَتَيْنِ يُحِبُّهُمَا اللهُ: الْحِلْمُ، وَالأَنَاةُ»، رواه مسلم.
HADISI NA GOMA
An
ruwaito daga Abdullahi bn Abbas; -Allah ya kara yarda a gare su- ya ce: Manzon
Allah -Sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce wa Ashajju; wato: Ashajju na
kabilar Abdulkais Lallai ne a tattare da kai akwai sifofi guda biyu; da
Allah ya ke sonsu; Su ne: Hakuri da nitsuwa. Muslim [17] ya ruwaito shi.
الحديث الحادي عشر
عن عائشة رضي الله عنها، أن رسول الله
صلى الله عليه وسلم قال: إِنَّ اللَّه رَفِيقٌ َ يُحِبُّ الرِّفْقَ فِي
الأَمْرِ كُلِّهِ، رواه البخاري [6927].
وأخرجه مسلم [2593] بلفظ: إِنَّ
اللَّهَ رَفِيقٌ يُحِبُّ الرِّفْقَ، وَيُعْطِي عَلَى الرِّفْقِ مَا لا يُعْطِي
عَلَى الْعُنْفِ، وَمَا لا يُعْطِي عَلَى مَا سِوَاهُ.
HADISI NA GOMA SHA DAYA
An
ruwaito daga A'isha -Allah ya kara yarda a gare ta- Lallai Manzon Allah -Sallal
lahu alaihi wa sallama- ya ce: Lallai ne Allah mai tausasawa ne; yana son tausasawa
a cikin dukkan al'amura.
Bukhariy [6927] ya ruwaito shi.
Kuma Muslim ya fitar da hadisin
[2593] da lafazin:
Lallai Allah Mai tausasawa ne; yana son tausasawa, Kuma Allah yana bayarwa a kan tausasawa -na yabo da sakamako mai girma, a duniya da lahira- irin abinda baya bayarwa a kan tsanantawa, da kuma irin abinda baya bayarwa a kan wasu sifofin -kyawawa; wadanda ba shi ba-.
Lallai Allah Mai tausasawa ne; yana son tausasawa, Kuma Allah yana bayarwa a kan tausasawa -na yabo da sakamako mai girma, a duniya da lahira- irin abinda baya bayarwa a kan tsanantawa, da kuma irin abinda baya bayarwa a kan wasu sifofin -kyawawa; wadanda ba shi ba-.
الحديث الثاني عشر
عن عَائِشَةَ رضي الله عنها، عَنِ
النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: إِنَّ الرِّفْقَ لا
يَكُونُ فِي شَيْءٍ إِلا زَانَهُ، وَلا يُنْزَعُ مِنْ شَيْءٍ إِلا شَانَهُ.
أخرجه مسلم [برقم: 2594].
HADISI NA GOMA SHA BIYU
An
ruwaito daga A'isha -Allah ya kara yarda a gare ta- Lallai Manzon Allah -Sallal
lahu alaihi wa sallama- ya ce: Lallai tausasawa baya kasancewa cikin wani
abu, face ya kawata shi. Kuma ba a cire tausasawa daga wani abu, face ya munata
shi (ya bar shi da aibi).
Muslim [2594] ya ruwaito shi.
Muslim [2594] ya ruwaito shi.
الحديث الثالث عشر
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِك رضي الله
عنهٍ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: يَسِّرُوا
وَلاَ تُعَسِّرُوا، وَبَشِّرُوا وَلاَ تُنَفِّرُوا، متفق عليه [خ: برقم: 69،
م: برقم: 2593].
HADISI NA GOMA SHA UKU
An
ruwaito daga Anas -Allah ya kara yarda a gare shi- daga Manzon Allah -Sallal lahu
alaihi wa sallama- ya ce: Ku saukaka; kada ku tsananta, kuma ku yi bushara;
kada ku yi abinda zai kori mutane.
Bukhariy [69] da Muslim [1734] su ka ruwaito shi.
Bukhariy [69] da Muslim [1734] su ka ruwaito shi.
الحديث الرابع عشر
عَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها،
قَالَتْ: مَا ضَرَبَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
شَيْئًا قَطُّ بِيَدِهِ، وَلا امْرَأَةً، وَلا خَادِمًا، إِلا أَنْ يُجَاهِدَ فِي
سَبِيلِ اللَّهِ، وَمَا نِيلَ مِنْهُ شَيْءٌ قَطُّ فَيَنْتَقِمَ مِنْ صَاحِبِهِ،
إِلا أَنْ يُنْتَهَكَ شَيْءٌ مِنْ مَحَارِمِ اللَّهِ، فَيَنْتَقِمَ لِلَّهِ عز وجل.
رواه مسلم [ رقم: 2328].
HADISI NA GOMA SHA HUDU
An
ruwaito daga A'isha -Allah ya kara yarda a gare ta- ta ce: Kwata-kwata
Manzon Allah -Sallal lahu alaihi wa sallama- bai taba dukan wani abu da
hannunsa ba; kuma be taba dukan wata Mata ko wani hadimi ba, Saidai idan zai yi
jihadi fiySabilil lahi. Kuma ba a taba cutar da shi -cikin zance ko aiki- da
wani abu ba, Sai ya dauki fansa daga wanda ya cutar da shi, Saidai idan an keta
wani abu na alfarmar Allah; Sai ya daukar wa Allah Mabuwayi da daukauka fansa.
Muslim [2328] ya ruwaito shi.
الحديث الخامس عشر
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ
رضي الله عنه، قَالَ: كُنْتُ أَمْشِي مَعَ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَعَلَيْهِ رِدَاءٌ نَجْرَانِيٌّ غَلِيظُ الْحَاشِيَةِ،
فَأَدْرَكَهُ أَعْرَابِيٌّ، فَجَبَذَهُ بِرِدَائِهِ جَبْذَةً شَدِيدَةً نَظَرْتُ
إِلَى صَفْحَةِ عُنُقِ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَقَدْ
أَثَّرَتْ بِهَا حَاشِيَةُ الرِّدَاءِ مِنْ شِدَّةِ جَبْذَتِهِ، ثُمَّ قَالَ: يَا
مُحَمَّدُ مُرْ لِي مِنْ مَالِ اللَّهِ الَّذِي عِنْدَكَ، فَالْتَفَتَ إِلَيْهِ
رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَضَحِكَ، ثُمَّ أَمَرَ لَهُ
بِعَطَاءٍ. متفق عليه [خ: رقم: 5809، م: 1057].
HADISI NA GOMA SHA BIYAR
An
ruwaito daga Anas -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Na kasance ina
tafiya tare da Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- alhalin a jikinsa
akwai mayafi dan garin Najran, mai kaushin gefe, Sai wani Bakauye ya riske shi,
sannan ya fizge shi da mayafinsa fizga mai tsanani.
Anas ya ce: Da na yi dubi zuwa
jikin wuyan Manzon Allah -Sallal lahu alaihi wa sallama- sai ga mayafin ya bar
wata alama; saboda tsananin fizgar da aka yi masa, Sa'annan sai bakauyen ya ce:
Ya Muhammadu! Bani daga dukiyar Allah da take wurinka! Sai Manzon Allah
ya juya izuwa gare shi, sai ya yi dariya, sa'annan ya yi umurnin a bashi
kyauta.
Bukhariy [5809] da Muslim [1057]
su ka ruwaito shi.
الحديث السادس عشر
عن سُلَيْمَانَ بْنِ صُرَدٍ رضي
الله عنه، قَالَ: اسْتَبَّ رَجُلانِ عِنْدَ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّم ٌفجعل َأَحَدُهُمَا تحمر عيناه وتنتفخ أوداجه، فَقَالَ رسول اللهُّ
صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: إِنِّي لأَعْرف كَلِمَةً لَوْ قَالَهَا
لَذَهَبَ عَنْهُ الذي يَجِدُ؛ أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ.
متفق عليه [خ: 6115رقم: ، م: 2610].
HADISI NA GOMA SHA SHIDA
An
ruwaito daga Sulaiman bn Surad -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Wasu
mazaje biyu sun yi zage-zage a wurin Annabi -sallal lahu alaihi wa sallama- Sai
'Daya daga cikinsu idanunsa biyu suka yi ja, jijiyoyin wuyansa kuma su ka
kukkunburo, Sai Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: Lallai
ne na san wata kalmar da ya fade ta, to da abinda ya ke ji, ya tafi; ita ce:
A'UZU BILLAHI MINA AL-SHAIDANI AL-RAJIM.
Bukhariy [6115] da Muslim [2610] su ka ruwaito shi.
Bukhariy [6115] da Muslim [2610] su ka ruwaito shi.
الحديث السابع عشر
عَنْ أَبي هُرَيْرَةَ رَضِيَ الله عنه،
أَنَّ رسُولَ الله صلى الله عليه وسلم قَالَ: لَيسَ الشَّديدُ
بِالصُّرَعَةِ،إِنَّمَا الشَّديدُ الَّذِي يَمْلِكُ نَفْسَهُ عِنْدَ الْغَضَبِ.
متفق عليه [خ: رقم: 6114 ، م: 2609].
HADISI NA GOMA SHA BAKWAI
An
ruwaito daga Abu-Hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Lallai Manzon
Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: Ba wai mai karfi shine jarumi
ba (Wanda ke yawaita kayar da Mutane), Lallai mai karfi shine wanda ke
mallakar ransa a lokacin fushi.
Bukhariy [6114] da Muslim [2609]
su ka ruwaito shi.
الحديث الثامن عشر
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه،
أَنَّ رَجُلاً قَالَ لِلنَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم: أَوْصِنِى، قَالَ: لاَ
تَغْضَبْ، فَرَدَّدَ مِرَارًا، قَالَ: لاَ تَغْضَبْ. رواه البخاري[
6116].
HADISI NA GOMA SHA
TAKWAS
An
ruwaito daga Abu-Hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi, Lallai wani mutum ya
ce wa Annabi -sallal lahu alaihi wa sallama- Ka min wasiyya, Sai ya ce: Kada
ka yi fushi Sai ya maimaita tambayar dayawa, Sai ya ce: Kada ka yi fushi.
Bukhariy [6116] ya ruwaito shi.
الحديث التاسع عشر
عَنْ عَيَّاضِ بْنِ
حِمَارٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَال رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: إِنَّ اللَّهَ أَوْحَى إِلَيَّ أَنْ تَوَاضَعُوا؛
حَتَّى َلا يفخر أَحَدٌ عَلَى أَحَدٍ، وَلا يبغي أَحَدٌ عَلَى أَحَد"، أَخْرَجَهُ
مُسْلِمٌ [ 2865].
HADISI NA GOMA SHA TARA
An ruwaito daga Iyadh bn Himar
-Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa
sallama- ya ce: Lallai ne Allah ya yi wahayi zuwa gare ni; cewa: Ku
kaskantar da kai; har ya kasance wani mutum ba ya yin alfahari ga wani, kuma
wani ba ya yin ta'addanci ko zaluntar wani.
Muslim [2865] ya ruwaito shi.
الحديث العشرون
عنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، عَنْ رَسُولِ
اللَّهِ صَلَّى اللَّهم عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: مَا نَقَصَتْ صَدَقَةٌ مِنْ
مَالٍ، وَمَا زَادَ اللَّهُ عَبْدًا بِعَفْوٍ إِلا عِزًّا، وَمَا تَوَاضَعَ أَحَدٌ
لِلَّهِ إِلا رَفَعَه اللهُ. أَخْرَجَهُ مُسْلِمٌ [ 2588].
HADISI NA ASHIRIN
An ruwaito daga
Abu-Hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi-, Daga Manzon Allah -sallal lahu
alaihi wa sallama- ya ce: Babu wata sadaka da ta ke tauye dukiya, Kuma idan
bawa ya yi afuwa, Allah baya masa kari, face izza (da daukaka), Kuma
wani ba zai yi tawali'u, don Allah ba (wato:kaskantar-da-kai), face
Allah ya daukaka shi.
Muslim
[2588] ya ruwaito shi.
الحديث الحادي والعشرون
عَنِ الأَسْوَدِ بن يزيد، قَالَ:
سَأَلْتُ عَائِشَةَ رضي الله عنها: مَا كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ يَصْنَعُ فِي بَيْتِهِ؟ قَالَتْ: كَانَ يَكُونُ فِي مِهْنَةِ
أَهْلِهِ -تَعْنِي خِدْمَةَ أَهْلِهِ- فَإِذَا حَضَرَتِ الصَّلاَةُ خَرَجَ
إِلَى الصَّلاَةِ . أَخْرَجَهُ البخاري [676] .
HADISI NA ASHIRIN DA DAYA
An ruwaito daga Aswad bn Yazid, ya
ce: Na tambayi A'isha -Allah ya kara yarda a gare ta-; cewa: Yaya Annabi
-sallal lahu alaihi wa sallama- ya ke kasancewa a cikin gidansa? Sai ta ce: Ya
kan kasance cikin aiki wa iyalansa -tana nufin: Cikin yin hidima ga
iyalansa- Idan kuma salla ta halarto, Sai ya fita izuwa ga sallah. Bukhariy
[676] ya ruwaito shi.
الحديث الثاني والعشرون
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه: كُلُّ
سُلاَمَى مِنَ النَّاسِ عَلَيْهِ صَدَقَةٌ كُلَّ يَوْمٍ تَطْلُعُ فِيهِ الشَّمْسُ،
يَعْدِلُ بَيْنَ الاِثْنَيْنِ صَدَقَةٌ، وَيُعِينُ الرَّجُلَ عَلَى دَابَّتِهِ
فَيَحْمِلُ عَلَيْهَا أَوْ يَرْفَعُ عَلَيْهَا مَتَاعَهُ صَدَقَةٌ، وَالكَلِمَةُ
الطَّيِّبَةُ صَدَقَةٌ، وَكُلُّ خُطْوَةٍ يَخْطُوهَا إِلَى الصَّلاَةِ صَدَقَةٌ،
وَيُمِيطُ الأَذَى عَنِ الطَّرِيقِ صَدَقَة.
متفق عليه [خ: رقم: 2989 م: 1009].
HADISI NA ASHIRIN DA BIYU
An
ruwaito daga Abu-Hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: Manzon Allah
-sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: Kowace gaba a jikin mutane akwai
sadaka a kanta, a kowani yinin da rana ta fudo a cikinsa, Ya yi sulhu ko adalci
tsakanin mutane biyu sadaka ne, Ya taimaki mutum a kan dabbarsa; sai ya dora a
kanta, ko ya sauke masa kayansa daga kanta sadaka ne, Fadar kalma daddada
sadaka ne, Kuma dukkan taku da zai taka izuwa ga sallah sadaka ne, Kuma ya
gusar da abu mai cutarwa daga kan hanya sadaka ne.
Bukhariy [2989] da Muslim [1009]
su ka ruwaito shi.
Bincike ya
tabbatar da cewa akwai gabbai da suka kai 360 a
jikin dan'adam, kuma akwai sadaka akan kowane daya daga cikinsu; idan ya
wayi-gari, Saidai kuma yin sallar walaha ta kan isar ga hakan. Kamar yadda
hadisi ya tabbatar wadannan bayanan.
Godiya ta tabbata ga Allah.
الحديث الثالث والعشرون
عن أُمَّ كُلْثُومٍ بِنْتِ عُقْبَةَ رضي الله عنها،
أَنَّهَا سَمِعَتْ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
لَيْسَ الْكَذَّابُ الَّذِي يُصْلِحُ بَيْنَ النَّاس فَيَنْمِي خَيْرًا ِ
وَيَقُولُ خَيْرًا.
أَخْرَجَهُ البخاري [2692] ومسلم
[2605] .
HADISI NA ASHIRIN DA UKU
An ruwaito daga UmmuKulthum 'yar
Ukbatu -Allah ya kara yarda a gare ta-; lallai ita, ta ji Manzon Allah -sallal
lahu alaihi wa sallama- yana cewa: (Ko, ya yi karya) Ba Mai karya ba ne;
Wanda ke sulhunta tsakanin mutane; sai ya nufi alkhairi, ko ya fadi alheri.
Bukhariy [2692] da Muslim [2605]
su ka ruwaito shi.
Hadisin na nuna muhimmancin yin
sulhi tsakanin bangarori guda biyu na musulmai; (kamar miji da mata), koda
hakan zai hukunta ya yi karya. matukar babu wata hanyar idan ba ita ba.
الحديث الرابع والعشرون
عن أَبِي مُوسَى الأشعري رضي الله
عنه، قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا
جَاءَهُ السَّائِلُ أَوْ طلبت إليهُ ْحَاجَةِ قَالَ: اشْفَعُوا تُؤْجَرُوا،
وَيَقْضِي اللَّهُ عَلَى لِسَانِ نَبِيِّهِ مَا شَاءَ، أَخْرَجَهُ البخاري
[1432] ومسلم [2627] .
HADISI NA ASHIRIN DA HUDU
An ruwaito daga Abu-Musa
Al-ash'ariy -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah -sallal lahu
alaihi wa sallama- ya kasance idan mai rokon wani abu ya zo masa, ko aka nemi
wata bukata daga wurinsa, ya kan ce: Ku yi ceto -ta hanyar bayanin
muhimmancin biyan wannan bukatar- za ku samu lada. Allah Mabuwayi da
daukaka shi kuma, zai hukunta abinda ya nufa a harshen AnnabinSa -S.A.W-
-na biyan wannan bukatar, ko akasin haka-.
Bukhariy [1432] da Muslim [2627]
su ka ruwaito shi.
الحديث الخامس والعشرون
عَن ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما، في قصة بَرِيرَةَ
وزَوجها ... قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّم:َ لَوْ
رَاجَعْتِيه... قَالَتْ: يَا رَسُولَ اللَّهِ أَتَأْمُرُنِي؟ قَال:َ إِنَّمَا
أَنَا أشفع. قَالَت:ْ لا حَاجَةَ لِي فيه. أَخْرَجَهُ البخاري [1432].
HADISI NA ASHIRIN DA BIYAR
An ruwaito daga Abdullahi bn Abbas
-Allah ya kara yarda a gare su- a kissar Barirah da Mijinta... Annabi -sallal
lahu alaihi wa sallama- ya ce: Da kin koma karkashinsa? Ta ce: Ya
Ma'aikin Allah, Shin umurni ka ke ba ni? Sai ya ce: A,a, Ni kawai neman ceto
na ke yi, Sai ta ce: To, Bani da bukatarsa.
Bukhariy [5283] ya ruwaito shi.
الحديث السادس والعشرون
عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما، أن
رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: الْمُسْلِمُ أَخُو الْمُسْلِمِ لا
يَظْلِمُهُ وَلا يسلُمُهُ، ومَنْ كَانَ فِي حَاجَةِ أَخِيهِ كَانَ اللَّهُ فِي
حَاجَتِهِ، وَمَنْ فَرَّجَ عَنْ مُسْلِمٍ كُرْبَةً فَرَّجَ اللَّهُ عَنْهُ
كُرْبَةً مِنْ كُربات يَوْمِ الْقِيَامَةِ، وَمَنْ سَتَرَ مُسْلِمًا سَتَرَهُ الله
يوم القيامة.
أَخْرَجَهُ البخاري [2442] ومسلم
[2580] .
HADISI NA ASHIRIN DA SHIDA
An ruwaito daga Abdullahi bn Umar
-Allah ya kara yarda a gare su, lallai Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa
sallama- ya ce: Musulmi dan'uwan musulmi ne; baya zaluntarsa, baya tabar da
shi, Wanda ya kasance cikin bukatar dan'uwansa, Allah zai kasance cikin
bukatarsa, Duk kuma wanda ya yaye wa musulmi wani bakin ciki, to Allah zai yaye
masa wani bakin ciki daga tarin bakin cikin yinin kiyama, Wanda kuma ya rufa
asiri wa Musulmi, Allah zai rufa masa asiri a ranar kiyama.
Bukhariy [2442] da Muslim [2580]
su ka ruwaito shi.
الحديث السابع والعشرون
عَنْ أَنَس بْن مَالِكٍ رضي الله عنه
قَالَ: إن كَانَ النبي صلى الله عليه وسلم ليُخَالِطُنَا، حَتّى يَقُولُ لأَخٍ لِي
صغير: يَا أَبَا عُمَيْرٍ، مَا فَعَلَ النُّغَيْرُ؟.
أَخْرَجَهُ البخاري [6129] ومسلم
[2150] .
HADISI NA ASHIRIN DA BAKWAI
An ruwaito daga Anas bn Malik
-Allah ya kara yarda a gare shi, Ya ce: lallai ne Annabi -sallal lahu alaihi wa
sallama- ya kan yi mu'amala; yana hulda da mu, har ya ce; wa dan'uwana karamin
yaro: Ya Abu-Umair, Shin tsuntsun kanari, mutuwa ya yi?
Bukhariy [6129] da Muslim [2150]
su ka ruwaito shi.
Annabi
(S.A.W) ya kan fadi abinda ya gabata ne ga wani karamin tsuntsu; da Abu-Umair
ke wasa da shi, sai ya mutu-. Wannan kuma na nuna kyakkyawiyar mu'amalar Manzon
Allah (S.A.W) da sakewarsa, ko yadda ya ke damuwa da damuwar mutane, koda kuwa
yara ne kanana.
Haka
hadisin na nuna halaccin yin wasa da tsuntsu, ko sanya shi cikin keji, da
halaccin yin alkunya ga wanda bai samu haifuwa ba, ko halaccin yin alkunya ga
yaro karami (kamar ace: Abu-umair).
الحديث الثامن والعشرون
عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما، قال: قال رسول
الله صلى الله عليه وسلم: الْمُؤْمِنُ الَّذِي يُخَالِطُ النَّاسَ وَيَصْبِرُ
عَلَى أَذَاهُمْ أَعْظَمُ أَجْرًا، مِنْ الْمُؤْمِنِ الَّذِي لا يُخَالِطُ
النَّاسَ وَلا يَصْبِرُ عَلَى أَذَاهُمْ.
أخرحه البخاري في الأدب المفرد [393]
وابن ماجه [4032]، وحسن إسناده ابن حجر في بلوغ المرام [1446].
HADISI NA ASHIRIN DA TAKWAS
An ruwaito daga Abdullahi bn Umar
-Allah ya kara yarda a gare su- ya ce: Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa
sallama- ya ce: Muminin da ke cikin mutane, ya ke kuma yin hakuri kan
cutarwarsu ya fi girman lada akan muminin da baya cikin mutane, kuma baya
hakuri akan cutarwarsu.
Littafin/ Adabul mufrad na Bukhariy
[393] da Ibnu-Majah cikin sunan [4032]. Ibnu-Hajar a cikin littafin bulugul
maram [1446] ya ce: Isnadinsa hasan ne.
الحديث التاسع والعشرون
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله
عنه، قَالَ: أَسَرَّ إِلَيَّ نَبِيُّ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
سِرًّا، فَمَا أَخْبَرْتُ بِهِ أَحَدًا بَعْدُ، وَلَقَدْ سَأَلَتْنِي عَنْهُ أُمُّ
سُلَيْمٍ فَمَا أَخْبَرْتُهَا به.
أَخْرَجَهُ البخاري [6289] ومسلم
[2482].
وفي رواية لمسلم أنه قَالَتْ أم سليم
رضي الله عنها: لا تُحَدِّثَنَّ بِسِرِّ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ أَحَدًا.
قَالَ أَنَسٌ: وَاللهِ لَوْ
حَدَّثْتُ بِهِ أَحَدًا لَحَدَّثْتُكَ يَا ثَابِت.
HADISI NA ASHIRIN DA TARA
An ruwaito daga Anas bn Malik
-Allah ya kara yarda a gare shi, Ya ce: Annabin Allah -sallal lahu alaihi wa
sallama *ya gaya min wani sirri, amma ban taba bada labarinsa ga wani Mutum ba,
Kuma hakika Ummu-Sulaimin* (wato: mahaifiyarsà) *ta tanbaye ni akan wannan
labarin; sai ban bata labari akansa ba*.
Bukhariy [6129] da Muslim [2150]
su ka ruwaito shi.
A wata riwaya ta *Muslim*
Ummu-Sulaimin ta ce: Ka da ka bada labarin sirrin Manzon Allah -sallal lahu
alaihi wa sallama- ga wani.
Anas ya ce: Na rantse da Allah!
Da zan bada labarin wannan sirrin ga wani Mutum, to da na baka labari akansa ya
kai Sabitu! (Daya daga cikin manyan Daliban Anas).
الحديث الثلاثون
عن أَبي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رضي الله
عنه قال: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: إِنَّ مِنْ
أَشَرِّ النَّاسِ عِنْدَ اللَّهِ مَنْزِلَةً يَوْمَ الْقِيَامَةِ الرَّجُلَ
يُفْضِي إِلَى امْرَأَتِهِ، وَتُفْضِي إِلَيْه،ِ ثُمَّ يَنْشُرُ سِرَّهَا. أخرجه
مسلم [1437].
HADISI NA TALATIN
An ruwaito daga
Abu-Sa'id Alkhudriy -Allah ya kara yarda a gare shi, Ya ce: Manzon Allah
-sallal lahu alaihi wa sallama ya ce: Lallai ne, yana daga mutanen da su ka
fi sharrin matsayi a wurin Allah, ranar kiyama; Mutumin da ke saduwa da
matarsa, ita ma ta sadu da shi, sa'annan ya yada sirrinta (ko ita, ta tona asirinsa).
Muslim [1437] ya ruwaito shi.
الحديث الحادي والثلاثون
عَنْ أَبي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه
قال:ُ سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم يَقُولُ: كُلُّ أَمَّتِى
مُعَافًى إِلاَّ الْمُجَاهِرِينَ، وَإِنَّ مِنَ الْمَجَاهرة: أَنْ يَعْمَلَ
الرَّجُلُ بِاللَّيْلِ عَمَلاً، ثُمَّ يُصْبِحَ وَقَدْ سَتَرَهُ اللَّهُ،
فَيَقُول:َ يَا فُلاَنُ عَمِلْتُ الْبَارِحَةَ كَذَا وَكَذَا، وَقَدْ بَاتَ
يَسْتُرُهُ رَبُّهُ وَيُصْبِحُ يَكْشِفُ سِتْرَ اللهِ عَنْهُ.
أخرجه البخاري [6069]، ومسلم [2990].
HADISI NA TALATIN DA DAYA
An ruwaito daga Abu hurairah
-Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Na ji Manzon Allah -sallal lahu alaihi
wa sallama- yana cewa: Dukkan al'ummata za a musu afuwa, in banda masu
bayyanar da laifi, Kuma yana daga cikin bayyanar da laifi: Mutum ya aikata wani
aiki cikin dare, sai ya wayi gari alhalin Allah ya rufa masa asiri, yana cewa:
ya wane: ai jiya da dare, na aikata kaza da kaza; shi ya kwana Ubangijinsa yana
rufa masa asiri, sai ga shi ya wayi gari yana yaye sitirar da Allah ya yi masa.
Bukhariy [6069] da Muslim [2990]
su ka ruwaito.
الحديث الثاني والثلاثون
عَنْ أَبِي هُرَيْرَة رضي الله عنهَ،
عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: لا يَسْتَرُ عَبْدٌ
عَبْدًا فِي الدُّنْيَا إِلا سَتَرَهُ الله يوم القيامةُ. أخرجه مسلم [2590].
HADISI NA TALATIN DA BIYU
An ruwaito daga Abu hurairah
-Allah ya kara yarda a gare shi-, daga Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa
sallama- ya ce: Bawa ba zai rufa asirin wani bawa ba, a duniya, face Allah
ya rufa asirinsa ranar kiyama.
Muslim [2590] ya ruwaito.
الحديث الثالث والثلاثون
عَنْ أَبِي مَسْعُودٍ
الأَنْصَارِيِّ رضي الله عنه قَالَ: قال رسول الله صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ، قَالَ: مَنْ دَلَّ عَلَى خَيْرٍ فَلَهُ مِثْلُ أَجْرِ فَاعِلِهُ.
أخرجه مسلم [1893].
HADISI NA TALATIN DA UKU
An ruwaito daga Abu Mas'ud
Al-ansariy -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah -sallal lahu
alaihi wa sallama- ya ce: Wanda ya yi nuni zuwa ga wani alheri, to yana da
kwatankwacin ladan wanda ya aikata shi. Muslim [1893] ya ruwaito.
الحديث الرابع والثلاثون
عن أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه
أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: مَنْ دَعَا
إِلَى هُدًى كَانَ لَهُ مِنْ الأَجْرِ مِثْلُ أُجُورِ مَنْ تَبِعَهُ، لا يَنْقُصُ
ذَلِكَ مِنْ أُجُورِهِمْ شَيْئًا، وَمَنْ دَعَا إِلَى ضَلالَةٍ كَانَ عَلَيْهِ
مِنْ الإِثْمِ مِثْلُ آثَامِ مَنْ تَبِعَهُ لا يَنْقُصُ ذَلِكَ مِنْ أوزارهم
شَيْئًا. أخرجه مسلم [2674].
HADISI NA TALATIN DA HUDU
An ruwaito daga Abu hurairah
-Allah ya kara yarda a gare shi- lallai Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa
sallama- ya ce: Wanda ya yi kira zuwa ga wata shiriya, yana da lada
kwatankwacin ladan wadanda su ka bi shi; ba tare da hakan ya tauye wani abu
daga ladansu ba. Wanda kuma ya yi kira -da'awa- zuwa ga wata bata, yana da
zunubi kwatankwacin zunuban wadanda su ka bi shi, ba tare da hakan ya tauye
komai daga zunubansu ba.
Muslim [2674] ya ruwaito.
الحديث الخامس والثلاثون
عَنْ أَبِي مُوسَى الأشْعَرِيِّ رضي
الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم: الْمُؤْمِنُ
لِلْمُؤْمِنِ كَالْبُنْيَانِ يَشُدُّ بَعْضُهُ بَعْضًا وشبك بين أصابعه. متفق
عليه؛ [خ: 6026]، [م: 2585].
HADISI NA TALATIN DA BIYAR
An ruwaito daga Abu Musa
Al-ash'ariy -Allah ya kara yarda a gare shi- daga Annabi -sallal lahu alaihi wa
sallama- ya ce: Mumini ga mumini kamar gini ne; sashensa yana karfafa sashe.
Bukhariy [6026] da Muslim [2585]
su ka ruwaito.
الحديث السادس والثلاثون
عَنْ أَبِي مُوسَى الأشْعَرِيِّ رضي
الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم: إن الخازنَ المسلمَ
الأمينَ، الذي يُنْفِذُ -وربما قال: يُعطي- ما أُمرَ به، فيعطيه
كاملاً مُوَفَّراً، طيبةً به نفسُهُ، فيدفعُه إلى الذي أُمر له به؛ أحدُ المتصدقين.
متفق عليه؛ [خ: 2319]، [م: 1023].
HADISI NA TALATIN DA SHIDA
An ruwaito daga Abu Musa
Al-ash'ariy -Allah ya kara yarda a gare shi- daga Annabi -sallal lahu alaihi wa
sallama- ya ce: Lallai mai ajiyar dukiya ko taskance ta, musulmi amintacce
mai amana, wanda ke zartar -Ko, ya ce: wanda ke bayar da- abin da aka yi
masa umarni da shi; ya bayar da abin a kammale, a cike, ransa tana jin dadin
hakan, ya kuma tunkuda dukiyar izuwa ga wanda aka ce ya ba shi ita, Shi ma
dayan mutane masu sadaka ne guda biyu.
Bukhariy [2319] da Muslim [1023]
su ka ruwaito.
الحديث السابع والثلاثون
عَنْ تَمِيمٍ الدَّاريِّ رضي الله عنه
أَنَّ النَّبِي صلى الله عليه وسلم قَالَ: الدِّينُ النَّصِيحَةُ، قُلْنَا:
لِمَن؟ْ قَال:َ لِلَّهِ، وَلِكِتَابِهِ، وَلِرَسُولِه،ِ وَلأَئِمَّةِ
الْمُسْلِمِينَ، وَعَامَّتِهِمْ.
أخرجه مسلم [55].
HADISI NA TALATIN DA BAKWAI
An ruwaito daga Tamim Ad-dariy
-Allah ya kara yarda a gare shi- lallai Annabi -sallal lahu alaihi wa sallama-
ya ce: Addini nasiha ne, Sai mu ka ce: Ga wa? Sai ya ce: Ga Allah, da
kuma littafinSa, da ManzonSa, da kuma shugabannin musulmai, da sauran musulmai.
Muslim [55] ya ruwaito.
الحديث الثامن والثلاثون
عن جرير بن عبد الله البجلي رضي
الله عنه قال: بَايَعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى
إِقَامِ الصَّلاةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ، وَالنُّصْحِ لِكُلِّ مُسْلِمٍ، متفق
عليه؛
[خ: 57،
م: 56].
HADISI NA TALATIN DA TAKWAS
An ruwaito daga Jarir bn Abdullah
Albajaliy -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Na yi mubaya'a ga Manzon
Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- a kan tsayar da sallah, da bada
zakkah, da yin nasiha ga kowani musulmi.
Bukhariy [57] da Muslim [56] su ka
ruwaito.
الحديث التاسع والثلاثون
عَنْ عبد الله بنِ مَسْعودِ رضيَ الله
ُ عنهُ قال: قالَ رسول اللهِ صلى اللهُ عليْهِ وسلَم: لا
حَسَدَ إلاَّ في اثنَتَيْن؛ِ رَجُلٌ آتَاه
اللهُ مَالاً فسَلَّطَهُ عَلى هَلَكتِهِ في الحق، ورجل
آتَاهُ اللهُ الحِكْمَةَ فَهُوَ يَقضِي بِها وَيُعَلِمُّها،
متفق عليه؛ [خ: 1409م: 816].
HADISI NA TALATIN DA TARA
An ruwaito daga Abdullahi bn
Mas'ud -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah -sallal lahu alaihi
wa sallama- ya ce: Babu hassada sai cikin abubuwa biyu; Mutumin da Allah ya
bashi dukiya, sai ya dora shi akan batar da ita cikin abubuwan gaskiya, da
Mutumin da Allah ya ba shi hikima (ko ilimi); sai ya ke hukunci da hikimar, ya
ke kuma karantar da ita.
Bukhariy [1409] da Muslim [816] su
ka ruwaito.
الحديث الأربعون
عن عَدِيِّ بْنِ حَاتِمٍ رصي الله
عنه، قَالَ: ذَكَرَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ النَّارَ
فَأَعْرَضَ وَأَشَاحَ، ثُمَّ قَالَ: اتَّقُوا النَّارَ، ثُمَّ أَعْرَضَ
وَأَشَاحَ حَتَّى ظَنَنَّا أَنَّهُ كَأَنَّمَا يَنْظُرُ إِلَيْهَا، ثُمَّ قَالَ: اتَّقُوا
النَّارَ وَلَوْ بِشِقِّ تَمْرَةٍ، فَمَنْ لَمْ يَجِدْ فَبِكَلِمَةٍ طيبة،
متفق عليه؛ [خ: 6540م: 1016].
HADISI NA ARBA'IN
An
ruwaito daga Adiyyu bn Hatim -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon
Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ambaci wuta, Sai ya kawar da kai,
tsoron kada ta taba shi, sa'annan ya ce: Ku nemi kariya daga wuta,
sa'annan sai ya kawar da kai, tsoron kada ta taba shi, har sai da mu ka yi
zaton kai ka ce, yana yin dubi ne zuwa gare ta, sa'annan ya ce: Ku nemi
kariya daga wuta ko da da barin dabino ne, Wanda kuma bai samu ba, to, ko da da
kalma ce daddada. .
Bukhariy [6540] da Muslim [1016] su ka ruwaito.
Bukhariy [6540] da Muslim [1016] su ka ruwaito.
الحديث الحادي والأربعون
عن أبي هريرة رضي الله عنه
أن رَسُول اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عليه وسلم - قال: قال الله: أَنْفِق
يا ابن آدم أُنْفِق عليك متفق عليه؛ [خ: 5352 م: 993].
HADISI NA ARBA'IN DA DAYA
An ruwaito daga Abuhurairah -Allah
ya kara yarda a gare shi- ya ce: lallai Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa
sallama- ya ce: Allah ya ce: Ka ciyar* -Ya kai dan'adam- *zan ciyar da kai.
Bukhariy [5352] da Muslim [993] su
ka ruwaito shi.
الحديث الثاني والأربعون
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ
عَنْهُ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّم،َ قَالَ: مَا مِنْ
يَوْمٍ يُصْبِحُ الْعِبَادُ فِيهِ إِلا مَلَكَانِ يَنْزِلان؛ِ فَيَقُولُ
أَحَدُهُمَا: اللَّهُمَّ أَعْطِ مُنْفِقًا خَلَفًا، وَيَقُولُ الآخَرُ: اللَّهُمَّ
أَعْطِ مُمْسِكًا تَلَفًا. متفق عليه؛ [خ: 1442 م: 1010].
HADISI NA ARBA'IN DA BIYU
An ruwaito daga Abuhurairah -Allah
ya kara yarda a gare shi- ya ce: lallai Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa
sallama- ya ce: Babu wani yinin da bayi za su wayi-gari a cikinsa, face
Mala'iku guda biyu suna sauka, Sai dayansu ya ce: Ya Allah! Ka baiwa mai ciyar
da dukiya mayewa. Sai dayan kuma ya ce: Ya Allah! Ka baiwa mai rike dukiya -mai
rowa- lalacewa -ko asara-.
Bukhariy [1442] da Muslim [1010]
su ka ruwaito shi.
الحديث الثالث والأربعون
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ
عَنْهُ، قَالَ: أَتَى رَجُلٌ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ،
فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَصَابَنِي الجَهْدُ، فَأَرْسَلَ إِلَى نِسَائِهِ
فَلَمْ يَجِدْ عِنْدَهُنَّ شَيْئًا، فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَلاَ رَجُلٌ يُضَيِّفُهُ هَذِهِ اللَّيْلَةَ، يَرْحَمُهُ
اللَّهُ؟ فَقَامَ رَجُلٌ مِنَ الأَنْصَارِ فَقَالَ: أَنَا يَا رَسُولَ اللَّهِ،
فَذَهَبَ إِلَى أَهْلِهِ، فَقَالَ لامْرَأَتِهِ: ضَيْفُ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لاَ تَدَّخِرِيهِ شَيْئًا، قَالَتْ: وَاللَّهِ مَا
عِنْدِي إِلا قُوتُ الصِّبْيَةِ، قَالَ: فَإِذَا أَرَادَ الصِّبْيَةُ العَشَاءَ
فَنَوِّمِيهِمْ، وَتَعَالَيْ فَأَطْفِئِي السِّرَاجَ وَنَطْوِي بُطُونَنَا
اللَّيْلَةَ، فَفَعَلَتْ. ثُمَّ غَدَا الرَّجُلُ عَلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: لَقَدْ عَجِبَ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ -أَوْ
ضَحِكَ- مِنْ فُلاَنٍ وَفُلاَنَةَ، فَأَنْزَلَ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: {وَيُؤْثِرُونَ
عَلَى أَنْفُسِهِمْ وَلَوْ كَانَ بِهِمْ خَصَاصَةٌ} [الحشر: 9].
متفق عليه؛ [خ: 4889 م: 2054].
HADISI NA ARBA'IN DA UKU
An ruwaito daga Abuhurairah -Allah
ya kara yarda a gare shi- ya ce:
Wani Mutum ya zo wurin Manzon
Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- sai ya ce:
Ya Manzon Allah! Matsalar yunwa ce
ta kama ni,
Sai Manzon Allah ya tura wa
matansa; sai bai samu komai a wurinsu ba,
Daga nan sai Manzon Allah -sallal
lahu alaihi wa sallama- ya ce:
Shin babu wani mutum -Allah ya yi
rahama a gare shi- wanda zai karbi bakuncinsa a wannan dare?
Sai wani mutum daga cikin
"Ansaar" ya tashi ya ce:
Ni ne, Ya Manzon Allah.
Sai ya tafi zuwa ga iyalansa; ya
ce wa matarsa:
Bakon Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ne; kada ki hana shi komai,
Bakon Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ne; kada ki hana shi komai,
Sai ta ce: Wallahi! Babu komai a
wurina sai dan abincin yara,
Ya ce: To, idan yaran su ka bukaci abincin dare sai ki lallabe su har su yi barci, sai ki zo, ki kashe fitila, sai mu nade hanjinmu (wato: Mu kwana da yunwa) a wannan dare.
Sai ta aikata haka.
Ya ce: To, idan yaran su ka bukaci abincin dare sai ki lallabe su har su yi barci, sai ki zo, ki kashe fitila, sai mu nade hanjinmu (wato: Mu kwana da yunwa) a wannan dare.
Sai ta aikata haka.
Sai wannan mutumin ya yi sammako
zuwa ga Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- sai Annabi ya ce:
Hakika Allah Mabuwayi da daukaka ya yi
mamaki
-ko kuma, ya ce:
-ko kuma, ya ce:
Allah ya yi dariya- daga wane da wance
Sai Allah mabuwayi da daukaka ya saukar da:
Sai Allah mabuwayi da daukaka ya saukar da:
KUMA ANSAR SUNA FIFITA BUKATUN
WASU AKAN TA SU KODA A TARE DA SU AKWAI WATA BUKATA KO TALAUCI. [Hashr: 9].
Bukhariy [4889] da Muslim [2054]
su ka ruwaito shi.
الحديث الرابع والأربعون
عن أبي موسى رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ
قال: قال رسول الله صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّم: إن الأشعريين إذا أرملوا
في الغزو، أو قل طعام عيالهم بالمدينة جمعوا ما كان عندهم في ثوب واحد، ثم اقتسموه
بينهم في إناء واحد بالسوية، فهم مني، وأنا منهم، متفق عليه؛ [خ: 2486 م:
2500].
HADISI NA ARBA'IN DA HUDU
An ruwaito daga AbuMusa Al'ash-ariy
-Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa
sallama- ya ce: Lallai kabilar Ash'ariyyuna idan guzurinsu a wurin yaki ya
kare, ko kuma abincin iyalansu a garin Madina ya karanta, Sai su tattara abinda
ya rage musu a cikin tufa daya, sa'annan su raba shi a cikin koko daya, a
tsakaninsu daidai da daidai. A kan wannan; Su, suna daga gare ni, Nima, ina
daga gare su
(Ma'ana: Shiriyarsu da Halinsu, yana kusa da nawa, nima haka).
(Ma'ana: Shiriyarsu da Halinsu, yana kusa da nawa, nima haka).
Bukhariy [2486] da Muslim [2500]
su ka ruwaito shi.
الحديث الخامس والأربعون
عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِي رضي
الله عنهِّ، قَالَ: بَيْنَمَا نَحْنُ فِي سَفَرٍ مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذْ جَاءَ رَجُلٌ عَلَى رَاحِلَةٍ لَهُ، قَالَ: فَجَعَلَ
يَصْرِفُ بَصَرَهُ يَمِينًا وَشِمَالا، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: مَنْ كَانَ مَعَهُ فَضْلُ ظَهْرٍ، فَلْيَعُدْ بِهِ عَلَى
مَنْ لا ظَهْرَ لَهُ، وَمَنْ كَانَ لَهُ فَضْلٌ مِنْ زَادٍ، فَلْيَعُدْ بِهِ عَلَى
مَنْ لا زَادَ لَه.
قَالَ: فَذَكَرَ مِنْ أَصْنَافِ
الْمَالِ مَا ذَكَر،َ حَتَّى رَأَيْنَا أَنَّهُ لا حَقَّ لأحَدٍ مِنَّا فِي
فَضْلٍ.
أخرجه مسلم [برقم: 1728].
HADISI NA ARBA'IN DA BIYAR
An ruwaito daga AbuSa'id Alkhudriy
-Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Wata rana mun kasance a cikin wata
tafiya tare da Annabi -sallal lahu alaihi wa sallama- sai wani mutum a kan abin
hawansa ya zo masa.
Maruwaicin hadisin ya ce: Sai
mutumin ya rika jujjuya fiskarsa dama da hagu (kamar yana neman abinda zai
toshe wata bukata), Sai Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: Wanda
a wurinsa akwai abin hawa fiye da daya, to ya bada sadakarsa ga wanda bashi da
abin hawa. Wanda kuma ya ke da guzuri dayawa to ya bayar da sauran ga wanda
bashi da shi.
Maruwaicin ya ce: Sai Annabi ya
ambaci nau'uka da dama daga nau'in dukiya, har sai da mu ka ga, kamar Wani daga
cikinmu bashi da wani hakki cikin abinda ya saura, na daga dukiya.
Muslim [1728] ya ruwaito shi.
الحديث السادس والأربعون
عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رضي
الله عنهما، أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: أَرْبَعٌ
مَنْ كُنَّ فِيهِ كَانَ مُنَافِقًا خَالِصًا، وَمَنْ كَانَتْ فِيهِ خَصْلَةٌ
مِنْهُنَّ كَانَتْ فِيهِ خَصْلَةٌ مِنْ النِّفَاقِ حَتَّى يَدَعَهَا: إِذَا
اؤْتُمِنَ خَانَ، وَإِذَا حَدَّثَ كَذَبَ، وَإِذَا عَاهَدَ غَدَرَ، وَإِذَا
خَاصَمَ فَجَرَ، متفق عليه؛ [خ: 34م: 58].
HADISI NA ARBA'IN DA SHIDA
An ruwaito daga Abdullahi bn Amru
-Allah ya kara yarda a gare su-, lallai Annabi -sallal lahu alaihi wa sallama-
ya ce: Abubuwa hudu, Duk wanda su ka kasance a tare da shi, ya kasance
munafiki ne tatacce. Wanda kuma ke dauke da wata sifa daga cikinsu, to, yana
tare da sifar munafurci, har sai ya kyale ta; Idan aka bashi amana sai ya yi
ha'inci, idan kuma zai yi magana sai ya yi karya, idan kuma ya yi alkawari sai
ya ki cikawa, idan kuma ya yi husuma -fada- sai ya yi fajirci,
Bukhariy [34] da Muslim [58] su ka
ruwaito shi.
الحديث السابع والأربعون
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه،
عَنْ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: آيَةُ الْمُنَافِقِ
ثَلاثٌ : إِذَا حَدَّثَ كَذَبَ، وَإِذَا وَعَدَ أَخْلَفَ، وَإِذَا اؤْتُمِنَ خَانَ.
متفق عليه؛ [خ: 33 م: 59].
HADISI NA ARBA'IN DA
BAKWAI
An ruwaito daga
AbuHurairah -Allah ya kara yarda a gare shi-, daga Annabi -sallal lahu alaihi
wa sallama- ya ce: Alamomin munafiki guda uku ne; Idan zai yi magana sai ya
yi karya, idan ya yi alkawari sai ya karya, idan kuma aka bashi amana sai ya yi
ha'inci.
Bukhariy
[33] da Muslim [59] su ka ruwaito shi.
الحديث الثامن والأربعون
عن أبى مالك الأشعرى قال: قال رسول
الله -صلى الله عليه وسلم-: الطُّهُورُ شَطْرُ الإِيمَان،ِ وَالْحَمْدُ لِلَّهِ
تَمْلأُ الْمِيزَانَ، وَسُبْحَانَ اللَّهِ وَالْحَمْدُ لِلَّهِ تَمْلآنِ -أَوْ
تَمْلأُ- مَا بَيْنَ السَّمَوَاتِ وَالأَرْض،ِ وَالصَّلاَةُ نُورٌ، وَالصَّدَقَةُ
بُرْهَان،ٌ وَالصَّبْرُ ضِيَاءٌ، وَالْقُرْآنُ حُجَّةٌ لَكَ أَوْ عَلَيْك،َ كُلُّ
النَّاسِ يَغْدُو؛ فَبَائِعٌ نَفْسَهُ فَمُعْتِقُهَا أَوْ مُوبِقُهَا.
أخرجه مسلم [برقم: 223].
HADISI NA ARBA'IN DA TAKWAS
An ruwaito daga AbuMalik
Al'ash'ariy -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah -sallal lahu
alaihi wa sallama ya ce: Tsarki (wato: alwala) rabin sallah ne
(imani), Fadin: ALHAMDU LILLAH yana cika ma'auni, Fadin: SUBHANALLAHI WAL
HAMDU LILLAHI yana cika abin da ke tsakanin sama da kasa. Sallah kuma haske ce.
Sadaka kuma hujja ce, hakuri shi ma haske ne, Kur'ani kuma, hujja ne a gare ka
ko a kanka, dukkan Mutane su kan wayi gari, sai su sayar da ransu; ta hanyar
'yantar da ita, ko halakar da ita.
Muslim [223] ya ruwaito shi.
A
cikin suratul Bakara Allah ta'alah ya kira *sallah* da sunan *imani*, a cikin
fadinsa
وما كان الله ليضيع إيمانكم أي: صلاتكم.
Wannan kuma, saboda kasancewar
"sallah" tana da matukar muhimmanci, a cikin aiyukan imani,
Kenan, a cikin nassoshin shari'a ya tabbata, an kira "sallah" da
sunan *imani*,
Wannan kuma shine abinda ya sake
maimaituwa cikin hadisinmu na yau (48): "Alwala rabin imani ne" yana
nufin: "rabin sallah".
Allah ya fahimtar da mu addininsa,
amin.
الحديث التاسع والأربعون
عن صهيب رضي الله عنه قال: قال رسولُ
اللهِ صلى الله عليه وسلم: عَجَبًا لأمرِ المؤمنِ إِنَّ أمْرَه كُلَّهُ لهُ
خَيرٌ، وليسَ ذلكَ لأحَدٍ إلا للمُؤْمنِ، إِنْ أصَابتهُ سَرَّاءُ شَكَرَ فكانتْ
خَيرًا لهُ، وإنْ أصَابتهُ ضَرَّاءُ صَبرَ فكانتْ خَيرًا لهُ.
أخرجه مسلم [برقم: 2999].
HADISI NA ARBA'IN DA TARA
An ruwaito daga Suhaib -Allah ya
kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama ya
ce: Mamakin lamarin mumini; lallai lamarinsa dukkansa alheri ne a gare shi;
hakan kuma baya kasancewa ga wani sai ga mumini, Idan abin faranta rai ya same
shi, sai ya yi godiya, sai hakan ya kasance alheri a gare shi. Idan kuma abu
mai cutarwa ne ya same shi, sai ya yi hakuri, sai hakan ya kasance alheri a
gare shi.
Muslim [2999] ya ruwaito shi.
الحديث الخمسون
عن أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه، مَرَّ
النَّبِيّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِامْرَأَةٍ تَبْكِي عند قَبْرٍ
فَقَال: اتَّقِي اللَّهَ وَاصْبِرِي قَالَتْ: إِلَيْكَ عَنِّي، فإنك لم تصب
بِمُصِيبَتِي ولم تعرفه، فَقِيلَ لَهَا: إِنَّهُ النبي صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ، فَأَتَت باب النبي صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَلم تجد عنده
بوابين، فقَالَتْ: لَمْ أَعْرِفْكَ، فقَالَ: إنما الصَّبْرُ عِنْدَ الصدمَة
الأولى. متفق عليه؛ [خ: 1283 م: 926].
HADISI NA HAMSIN
An ruwaito daga Anas bn Malik
-Allah ya kara yarda a gare shi-, ya ce: Annabi -sallal lahu alaihi wa sallama-
ya iske wata mata tana kuka, a jikin wani kabari, sai ya ce: Ki ji tsoron Allah;
ki yi hakuri, Sai ta ce: ka yi nesa da ni, saboda ba a jarrabe ka da irin
musibar da ta sauka a kaina ba, sai dai ba ta gane wanene shi ba, Sai aka ce
mata, ai shi ne Annabi -sallal lahu alaihi wa sallama-, sai ta je kofar gidan
Annabi -sallal lahu alaihi wa sallama-, amma sai bata samu masu gadi a kofar
gidan ba, sai ta ce: ban san kai ba ne, sai ya ce: Lallai hakuri, shine
wanda ya kasance a lokacin bugun musiba; na farko.
Bukhariy [1283] da Muslim [926] su
ka ruwaito shi.
الحديث الحادي والخمسون
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ -رضي الله
عنه- قَالَ: سَمِعْتُ النَّبي -صلى الله عليه وسلم- يَقُولُ: إِنَّ اللَّهَ
قَال:َ إِذَا ابْتَلَيْتُ عَبْدِى بِحَبِيبَتَيْهِ فَصَبَرَ، عَوَّضْتُهُ
مِنْهُمَا الْجَنَّةَ، يريد عينيه. أخرجه البخاري [برقم: 5653].
HADISI NA HAMSIN DA DAYA
An ruwaito daga Anas bn Malik
-Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: na ji Annabi -sallal lahu alaihi wa
sallama yana cewa: Lallai ne Allah ya ce: Idan na jarrabi bawana da dauke
masoyansa biyu, sai ya hakura, zan yi masa canjin aljanna, da su. Yana
nufin: Dauke masa ganin idanunsa; biyu.
Bukhariy [5653] ya ruwaito shi.
الحديث الثاني والخمسون
عَنْ عَبْدِ اللَّه بن مسعود رضي الله
عنهِ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: *عَلَيْكُمْ
بِالصِّدْقِ، فَإِنَّ الصِّدْقَ يَهْدِي إِلَى الْبِرِّ، وَإِنَّ الْبِرَّ يَهْدِي
إِلَى الْجَنَّةِ، وَمَا يَزَالُ الرَّجُلُ يَصْدُقُ وَيَتَحَرَّى الصِّدْقَ
حَتَّى يُكْتَبَ عِنْدَ اللَّهِ صِدِّيقًا. وَإِيَّاكُمْ وَالْكَذِبَ، فَإِنَّ
الْكَذِبَ يَهْدِي إِلَى الْفُجُورِ، وَإِنَّ الْفُجُورَ يَهْدِي إِلَى النَّارِ،
وَمَا يَزَالُ الرَّجُلُ يَكْذِبُ، وَيَتَحَرَّى الْكَذِبَ حَتَّى يُكْتَبَ عِنْدَ
اللَّهِ كَذَّابًا. متفق عليه؛ [خ: 6094 م: 2607].
HADISI NA HAMSIN DA BIYU
An ruwaito daga Abdullahi bn
Mas'ud -Allah ya kara yarda a gare shi-, ya ce: Manzon Allah -sallal lahu
alaihi wa sallama- ya ce: *Ina horonku da yin gaskiya, saboda ita gaskiya tana
shiryarwa zuwa ga biyayya, kuma lallai biyayya tana shiryarwa zuwa ga aljanna,
kuma mutum ba zai gushe yana yin gaskiya ba, yana kuma kirdadon gaskiya, ba, face
an rubuta shi a wurin Allah: Mai gaskiya.
Kuma ina muku gargadi akan yin karya; saboda ita karya tana shiryarwa zuwa ga fajirci, shi kuma fajirci yana shiryarwa zuwa ga wuta, kuma mutum ba zai gushe ba yana yin karya, kuma yana kirdadon karya face an rubuta shi a wurin Allah: Makaryaci.
Kuma ina muku gargadi akan yin karya; saboda ita karya tana shiryarwa zuwa ga fajirci, shi kuma fajirci yana shiryarwa zuwa ga wuta, kuma mutum ba zai gushe ba yana yin karya, kuma yana kirdadon karya face an rubuta shi a wurin Allah: Makaryaci.
Bukhariy [6094] da Muslim [2607]
su ka ruwaito shi.
الحديث الثالث والخمسون
عن حَكِيم بن حزام رضي الله عنه، عن
النَّبِي صلى الله عليه وسلم، قال: الْبَيِّعَانِ بِالْخِيَارِ مَا لَمْ
يَتَفَرَّقَا، فَإِنْ صَدَقَا وَبَيَّنَا بُورِكَ لَهُمَا فِى بَيْعِهِمَا، وَإِنْ
كَذَبَا وَكَتَمَا مُحِقَتْ بَرَكَةُ بَيْعِهِمَا، متفق عليه؛ [خ: 2110 م:
1532].
HADISI NA HAMSIN DA UKU
An
ruwaito daga Hakim bn Hizam -Allah ya kara yarda a gare shi-, daga Annabi
-sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: Mai saye da sayarwa suna da zabi
matukar basu rabu ba; Idan suka yi gaskiya wa juna, su ka yi bayani sai a sanya
musu albarka cikin kasuwancinsu, Idan kuma su ka yi karya, ko su ka boye aibi,
sai a kwashe albarkar kasuwancinsu.
Bukhariy [2110] da Muslim [1532]
su ka ruwaito shi.
الحديث الرابع والخمسون
عن الحسن بن علي رضي الله عنهما، قال:
"حفظت من رسول الله صلى الله عليه وسلم: دَعْ مَا يَرِيبُكَ إِلَى مَا لا
يَرِيبُكَ؛ فَإِنَّ الصِّدْقَ طُمَأْنِينَةٌ، وَإِنَّ الْكَذِبَ رِيبَةٌ. أخرجه
الترمذي [رقم: 2518]، وقال: حديث حسن صحيح.
HADISI NA HAMSIN DA HUDU
An ruwaito daga Alhasan dan Aliyu
dan Abu dalib -Allah ya kara yarda a gare su- ya ce: Na kiyaye ko haddce, daga
Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- cewa: Ka kyale abin da ke
sanya ka kokwanto, zuwa ga abinda ba ya maka kokwanto, domin gaskiya nitsuwa
ce, ita kuma karya kokwanto ne.
Tirmiziy [2518] ya ruwaito shi,
kuma ya ce: hadisi ne mai kyau, ingantacce.
الحديث الخامس والخمسون
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، أن رَسُولَ
اللَّهِ ﷺ، قَالَ: بَادِرُوا
بِالأَعْمَالِ فِتَنًا كَقِطَعِ اللَّيْلِ الْمُظْلِمِ؛ يُصْبِحُ الرَّجُلُ
مُؤْمِنًا وَيُمْسِي كَافِرًا، أَوْ يُمْسِي مُؤْمِنًا وَيُصْبِحُ كَافِرًا،
يَبِيعُ دِينَهُ بِعَرَضٍ مِنْ الدُّنْيَا. أخرجه مسلم [118].
HADISI NA HAMSIN DA BIYAR
An ruwaito daga AbuHurairah -Allah
ya kara yarda a gare shi-, Lallai Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama-
ya ce: Ku rigayi wasu fitintinu da yin aiyuka (nagari), fitintinun da
wajen duhunsu su ke kama da yankunan dare mai duhu; Mutum -a cikinsu- ya
kan wayi-gari mumini, sai ya yi yammaci kafiri, -ko kuma ya ce:- ya kan
yi yammaci mumini, sai ya wayi-gari kafiri, yana sayar da addininsa da dan abin
duniya.
Muslim [118] ya ruwaito shi.
الحديث السادس والخمسون
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه،
أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: بَادِرُوا
بِالأَعْمَالِ سِتًّا؛ طُلُوعَ الشَّمْسِ مِنْ مَغْرِبِهَا، أَوْ الدُّخَان،َ أَوْ
الدَّجَّالَ، أَوْ الدَّابَّةَ، أَوْ خَاصَّةَ أَحَدِكُمْ، أَوْ أَمْرَ
الْعَامَّةِ. أخرجه مسلم [2947].
HADISI NA HAMSIN DA SHIDA
An ruwaito daga AbuHurairah -Allah
ya kara yarda a gare shi-, Lallai Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama-
ya ce: Ku rigayi abubuwa shida da yin aiyuka (nagari); Fudowar rana
daga mafadarta, da hayaki, da dujjal, da wata dabba, da abinda ka iya kebantar
daidaikunku, ko kuma al'amari na gama-gari. Muslim [2947] ya ruwaito shi.
الحديث السابع والخمسون
عن أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ
عَنْهُ قَالَ: جَاءَ رَجُلٌ إِلَى رسول الله صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
فَقَال:َ يَا رَسُولَ اللَّهِ أَيُّ الصَّدَقَةِ أَعْظَمُ أَجْرًا؟ قَالَ: أَنْ
تَصَدَّقَ وَأَنْتَ صَحِيحٌ شَحِيحٌ تَخْشَى الْفَقْرَ وَتَأْمُلُ الْغِنَى. وَلا
تُمْهِل؛ُ حَتَّى إِذَا بَلَغَتْ الْحُلْقُومَ قُلْت:َ لِفُلانٍ كَذَا وَلِفُلانٍ
كَذَا، وَقَدْ كَانَ لِفُلانٍ، متفق عليه [خ: 1419 م: 1032].
HADISI NA HAMSIN DA BAKWAI
An ruwaito daga AbuHurairah -Allah
ya kara yarda a gare shi- ya ce: Wani mutum ya zo wurin Manzon Allah -sallal
lahu alaihi wa sallama- sai ya ce: ya Manzon Allah! Wace sadaka ce ta fi girman
lada? Sai ya ce: Ita ce, ka yi sadaka alhalin kana cikin koshin lafiya
(ba a gargara ba), kuma a halin tsananin kwadayin dukiya; da tsoron talauci,
ko tsammanin wadaci. Kuma ka da ka bari ka jinkirta; har rai ta kai ga makoshi,
sai ka ce: A baiwa wane kaza, wane shima yana da kaza, kuma hakika kaza, ya
kasance ga wane.
Bukhariy [1419] da Muslim [1032]
su ka ruwaito shi.
الحديث الثامن والخمسون
عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ -رضي الله عنهما-
قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ -صلى الله عليه وسلم- يُعَلِّمُنَا
الاِسْتِخَارَةَ فِى الأُمُورِ كلها كَمَا يُعَلِّمُنَا السُّورَةَ مِنَ
الْقُرْآن،ِ يَقُول إِذَا هَمَّ أَحَدُكُمْ بِالأَمْرِ فَلْيَرْكَعْ
رَكْعَتَيْنِ مِنْ غَيْرِ الْفَرِيضَة،ِ ثُمَّ لِيَقُل:ِ
اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْتَخِيرُكَ بِعِلْمِكَ
وَأَسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْأَلُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيمِ، فَإِنَّكَ
تَقْدِرُ وَلاَ أَقْدِرُ وَتَعْلَمُ وَلاَ أَعْلَمُ وَأَنْتَ عَلاَّمُ الْغُيُوبِ.
اللَّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا
الأَمْرَ (...) خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي-أَوْ قَالَ: عَاجِلِ أَمْرِي وَآجِلِهِ- فَاقْدُرْهُ
لِي وَيَسِّرْهُ لِي، ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيه.
وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا
الأَمْرَ (...) شَرٌّ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي -أَوْ قَال:َ فِي عَاجِلِ أَمْرِي وَآجِلِهِ-
فَاصْرِفْهُ عَنِّي وَاصْرِفْنِي عَنْهُ، وَاقْدُرْ لِي الْخَيْرَ حَيْثُ كَان،َ
ثُمَّ أَرْضِنِي به. -قَالَ- *وَيُسَمِّي حَاجَتَهُ*، أخرجه البخاري [1166].
HADISI NA HAMSIN DA TAKWAS
An ruwaito daga Jabir bn Abdullahi
-Allah ya kara yarda a gare su- ya ce: Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa
sallama- ya kasance yana koyar da mu yin "istikhara" a cikin
lamura gabadayansu, kamar yadda ya ke koyar da mu "sura" daga
alkur'ani, yana cewa:
Idan dayanku ya nufi wani lamari,
to sai ya yi raka'oi guda biyu; wadanda ba na farilla ba; sa'annan ya ce:
ALLAHUMMA INNIY ASTAKHIYRUKA BI ILMIKA, WA ASTAKDIRUKA BI KUDRATIKA, WA
AS'ALUKA MIN FADLIKAL AZIM; FA INNAKA TAKDIRU WALA AKDIRU, WA TA'ALAMU WALA
A'ALAMU, WA ANTA ALLAMUL GUYUB.
ALLAHUMMA IN KUNTA TA'ALAMU ANNA
HAZAL AMRA (...) KHAIRUN LIY FIY DIYNIY WA MA'ASHIY WA AKIBATI AMRIY -ko ya ce: FIY AJILI AMRIY WA
AJILIHI- FAKDURHU LIY WA YASSIRHU LIY, SUMMA BARIK LIY FIYHI.
WA IN KUNTA TA'ALAMU ANNA HAZAL AMRA (...) SHARRUN LIY FIY DIYNIY WA MA'ASHIY WA AKIBATI AMRIY -ko ya ce: FIY AJILI AMRIY WA AJILIHI- FASRIFHU ANNIY WASRIF NIY ANHU, WAKDUR LIYAL KHAIRA HAISU KANA, SUMMA ARDINIY BIHI.
Ya ce: Sai ya fadi sunan bukatarsa,
Bukhariy [1166] ne ya ruwaito shi.
MA'ANAR ADDU'AR ISTIKHARA ITA CE:
Zabi ne, Shi bawa wanda bashi da
sani, kuma bashi da iko, ya ke baiwa UbangijinSa Masani Mai iko, neman ya yi
zabin alkhairi a gare shi.
A cikin fadinsa:
A cikin fadinsa:
Ya Allah! lallai ne ni ina neman
zabinka da iliminka, kuma ina neman ka bani iko, da kudurarka, kuma ina rokonka
daga falalarka mai girma, domin kai kana da iko, ni kuma bani da iko (sai wanda
ka ba ni), kuma ka sani, ni kuma ban sani ba (sai abinda ka sanar da ni), kuma
kai ne Masanin ababen da su ke fake; na gaibu.
Ya Allah! Idan ka san wannan lamarin (...) alheri ne, a gare ni, cikin addinina, da rayuwata, da karshen lamarina (lahirata), to ka kaddara mini shi, ka saukake min shi, sa'annan ka sanya min albarka a cikinsa.
Idan kuma ka san wannan lamarin (...) sharri ne a gare ni; cikin addinina, da rayuwata, da karshen lamarina (lahirata), to ka kawar shi daga gare ni, ka kawar da ni daga gare shi, kuma ka kaddara min alheri a duk inda ya ke, Sa'annan ka sanya, na yarda da shi.
Ya Allah! Idan ka san wannan lamarin (...) alheri ne, a gare ni, cikin addinina, da rayuwata, da karshen lamarina (lahirata), to ka kaddara mini shi, ka saukake min shi, sa'annan ka sanya min albarka a cikinsa.
Idan kuma ka san wannan lamarin (...) sharri ne a gare ni; cikin addinina, da rayuwata, da karshen lamarina (lahirata), to ka kawar shi daga gare ni, ka kawar da ni daga gare shi, kuma ka kaddara min alheri a duk inda ya ke, Sa'annan ka sanya, na yarda da shi.
الحديث التاسع والخمسون
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه
قَالَ: قَالَ رَسُول اللَّهِ ﷺ: الْمُسْتَشَارُ مُؤْتَمَنٌ.
أخرجه أبو داود [5128] والترمذي [2822]
وابن ماجة [3745]. وقال الترمذي: حديث حسن.
HADISI NA HAMSIN DA TARA
An
ruwaito daga AbuHurairah -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah
-sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: Wanda ake neman shawarinsa, amintacce
ne, kuma amana ake ba shi.
Abu-Dawud [5128] ya ruwaito shi, da Tirmiziy [2822] da Ibnu-Majah [3745] . Kuma Tirmiziy ya ce: hadisi ne hasan.
Abu-Dawud [5128] ya ruwaito shi, da Tirmiziy [2822] da Ibnu-Majah [3745] . Kuma Tirmiziy ya ce: hadisi ne hasan.
الحديث الستون
عَن النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ رضي
الله عنه، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ﷺ: مَثَلُ الْمُؤْمِنِينَ فِي تَوَادِّهِمْ
وَتَرَاحُمِهِمْ وَتَعَاطُفِهِمْ مَثَلُ الْجَسَدِ؛ إِذَا اشْتَكَى مِنْهُ عُضْوٌ
تَدَاعَى لَهُ سَائِرُ الْجَسَدِ بِالسَّهَرِ وَالْحُمَّى. متفق عليه [خ: 6011
م: 2586].
HADISI NA SITTIN
An
ruwaito daga Al-nu'uman bn Bashir -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce:
Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: Misalin muminai cikin
sonsu ga juna, da jin kansu, da tausasawarsu, kamar misalin jiki ne guda daya,
idan wata gaba ta koka (ta kamu da cuta), sai sauran jikin ya amsa mata;
da rashin iya barci, da kuma zazzabi (zafin jiki).
Bukhariy [6011] da Muslim [2586]
su ka ruwaito shi.
الحديث الحادي والستون
عَنْ جَرِيرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رضي
الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ﷺ: لا يَرْحَم الله من لا يرحم النَّاسَ. أخرجه
البخاري [7376].
وفي لفظ: من لا يَرْحَمِ النَّاسَ لا يَرْحَمْهُ
اللَّهُ عز وجل. أخرجه مسلم [2319].
HADISI NA SITTIN DA DAYA
An ruwaito daga Jarir bn Abdullahi
-Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa
sallama- ya ce:
Allah ba zai ji kan wanda baya jin
kan mutane ba.
Bukhariy [7376] ya ruwaito shi.
A wani lafazin kuma
Wanda ba ya yin rahama ga mutane, Allah mabuwayi da daukaka ba zai yi rahama a gare shi ba.
Wanda ba ya yin rahama ga mutane, Allah mabuwayi da daukaka ba zai yi rahama a gare shi ba.
Muslim [2319] ya ruwaito shi.
الحديث الثاني والستون
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، قَالَ:
سمعت أبا القاسم ﷺ يقول: لا تنزع الرَّحْمَة إلا من شقيٍّ. أخرجه
الترمذي [1923] وقال: حديث حسن.
HADISI NA SITTIN DA BIYU
An
ruwaito daga AbuHurairah -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Na ji
Abul-Kasimu -sallal lahu alaihi wa sallama- yana cewa: Ba a cire jin kai da
rahama (daga zukata), face daga ta shakiyyi (maras rabo; dan wuta).
Tirmiziy [1923] ya ruwaito shi, kuma ya ce: hadisi ne hasan.
Tirmiziy [1923] ya ruwaito shi, kuma ya ce: hadisi ne hasan.
No comments:
Post a Comment