HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 07/RABI'UL AUWAL/1437h
Daidai da 18 /DISAMBA/2015m
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI HUSAIN XAN ABDUL'AZIZ ALUSH SHEIKH
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
Godiya ta tabbata
ga Allah; Majivincin mumunai, Wanda yake tsare masu bin dokokinSa, Ina shaidawa
babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; Shi kaxai yake ba shi da abokin
tarayya; Abun bautar na-farko da na-qarshe.
Kuma ina
shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa; Zavavve
Amintacce.
Ya Allah ka yi salati a gare shi da sallama,
da albarka, Shi; da iyalansa da sahabbansa gabaxaya.
Bayan
haka:
Ya ku Musulmai!!
Ina yin
wasiyayya a gare ku da Ni kaina, da kiyaye dokokin Allah (taqawa), saboda bin
dokokinSa shine tsira, kuma yin xa'a a gare shi shine rabauta.
Ya ku
Musulmai!!
Cikin
tarin matsalolin da suka addabi al'ummarmu ta Musulmai masu yawa, a cikin vangarorin
siyasa, da tattalin arziqi, da zamantakewa, da aminci ko zaman lafiya, da wassu
vangarorin. Da kuma abinda al'ummar take rayuwa a cikinsa na halin rauni da
rarrabuwa, da kuma xanxanar nau'ukan qasqanci da wulaqanci, da shan bonen
rarrabuwar kai da qungiyanci. To lallai
Ma'abuta hankula suna jira ko fatan ganin lokacin da za a tsamar da wannan
al'ummar daga munanan abubuwan da suka addabe ta.
Kuma lallai Masana sun faxi albarkacin
bakinsu, Shugabanni suma sun kawo irin mafitar da suke gani, Marubuta
suma sun ambaci abinda suka yi nazari. Maganganu sun yi yawa kan menene
sabbuban da suka janyo hakan, kuma ra'ayoyi sun banbanta kan mafita, da kuma
hanyoyin da za a warware matsalolin.
Saidai kuma, Lokaci yayi ga al'ummar Musulmai
gabaxayanta; qasashensu da xaixaikunsu, Shugabanni da waxanda ake shugabanta,
Su ga haqiqanin waxannan matsaloli, sannan su fitar da nagartattun hanyoyin da
za a bi don magance su, daga abinda ya tabbata daga addininsu, da kuma
ginshiqansa da ake dogara a kansu.
Kuma
lallai al'ummar Musulmai ba za su tava samun nagartattun magani ga cutukansu
ba, da kuma mafita daga halin da suke ciki da kuma mushkilolinsu ba, Sai kawai ta
hanyar kyakkyawar fahimta ga LITTAFIN ALLAH DA SUNNAR ANNABINMU MUHAMMADU (صلى الله عليه وسلم).
'Yan'uwan
Musulunci!
(A yanzu) za
mu saurari wasiyya ce mai girma wacce Malamin duniya kuma shugaban halitta ya
aiwatar da ita a gare mu; wato Annabinmu Muhammadu (صلى الله عليه وسلم), a lokacin da ya ke faxakar da
al'ummarsa, kuma yake bata wasiqar da za ta tabbata har abada; wacce kuma za ta
gyara wa al'umma rayuwarta idan suka bi abinda ke cikinta, sannan xaixaikunta
su rabauta, su kuma samu bunqasa idan suka yi aiki da ita.
Wasiqa ce, da ya zama wajibi a ko-da-yaushe ta
zama, a gaban idanunmu, Yin aiki da ita kuma ya game dukkan aiyukanmu, ta
hanyar faxakar da mu cikin kowani motsawarmu, da yin gyara cikin nufinmu ko
qudurinmu, da aiyukan da muka fiskanta.
Wasiqa ce, da ba tana dubi ko rinjayar da
maslahar wassu mutane ba, ko kuma raya qabilanci, ko kuma warware matsalar yau
(kawai) ba.
Wasiqa ce da ta fito daga wanda baya yin
Magana daga son zuciya, kuma baya cewa komai sai daga wahayin da ake aiko masa.
Wasiqar da Annabi Muhammadu (s.a.w) yazo da
ita, kuma wasiyya mai haske, Wacce za ta bunqasa Musulmai zuwa ga rayuwa
maxaukakiya, wacce ta cika da alkhairi da rinjayen buwaya, da aikin nagarta, da
samun qarfi,
"Ya ku waxanda suka yi imani! ku amsa wa
Allah, da kuma Manzo, idan ya kiraye ku zuwa ga abinda zai raya ku" [Anfal:
24].
Irin Rayarwa gamammiya, ga xaixaikun Mutane da
kuma jama'a, da kuma rayuka da kaya masu qima wanda aka mallaka. Irin rayuwar
da ake gina ta akan QARFIN IMANI, wanda babu makawa sai da shi, gabanin a iya
fiskantar matsaloli. Rayuwar da take nufin: Bunqasa; da faffaxar ma'anarta, da
kuma dukkan surorinta, wacce za ta tattara wa al'ummar Musulmai samun walwala,
da rayuwa cikin aminci da tsaro, da alherori da bunqasa, da samun xaukaka a
kowani fage daga cikin fagagen rayuwa.
Ya
ku Musulmai!!
Lallai
samun buwaya Na nan ne kawai cikin aiki da wannan wasiqar, kuma lallai samun
girma a duniya da lahira idan aka yi aiki da abinda ta qunsa abu ne da ake da
tabbacinsa, Allah mabuwayi da xaukaka yana cewa:
"Kuma lallai haqiqa mun saukar zuwa gare ku,
da wani littafi, a cikinsa akwai xaukakarku" [Anbiya'i: 10]. Kuma
Allah yana cewa:
"Kuma wanda ya yi taqawa, kuma ya gyara
aikinsa, To, babu tsoro akansu, kuma ba su yin baqin-ciki"
[A'araf: 35].
Xaixaikun
Mutane, Idan har ba su yi aiki da wannan wasiyar ba, suna cikin tozarta. Kuma
suma al'ummomi idan suka yi nisa da abubuwan da ta qunsa za su wargaje; su
rushe.
Wasiqa
ce da take qulle Musulmi da asalinsa, tare da sadar da shi da zamaninsa. Ta kuma
tattara masa bin abinda shari'a ta zo masa da shi, da dacewa da samun abinda
zamani ya hukunta. Wasiqa ce wanda yin aiki da ita shine hanya guda xaya kwara
da za a magance matsalolin da suke
fiskantar al'ummar Musulmai, waxanda kuma suke fiskantar ginshiqanta da abinda
suke girmamawa da abubuwan da suke kevance ta, don su lalata. Umar Alfaruq (رضي الله عنه) yace:
"Lallai kawai kun rigayi Mutane ne,
da taimakon wannan addinin".
Sai
mu saurara –Allah ya kare ku-
Don
jin wannan wasiyyar mai girma, kana kuma wasiqa mai dawwama, Ji irin na amsawa
da aiki, da kuma bi da miqa wuya, Abdullahi xan Abbas (رضي الله عنهما) yace:
Na kasance a
bayan Manzon Allah (S.A.W) wata rana sai yace da ni, “Ya kai yaro! Zan sanar da
kai wasu kalmomi: Ka kiyaye Allah, sai ya kiyaye ka; ka kiyaye Allah za ka same
shi a gaba gare ka (yana yi maka jagoranci); idan zaka roqa to ka roqi Allah;
idan zaka nemi taimako ka nemi taimakon Allah. Ka sani, da al’umma za su taru
domin su amfane ka da wani abu, ba za su iya amfanar da kai komai ba , sai da
abinda Allah ya rubuta maka. Idan kuma da al’umma za su taru domin su cuce ka
da wani abu, ba za su cuce ka ba, sai da abinda Allah ya rubuta maka. An xauke
alkaluma, takardun kuma sun bushe”. Tirmiziy [2516] ya ruwaito shi, yace hadisi ne mai kyau
ingantacce.
A riwayar wanin Tirmiziy kuma: “Ka kiyaye dokar Allah, zaka samu Ubangiji a gabanka, ka nemi sanin Allah a lokacin da ka ke cikin yalwa, zai san da kai a lokacin da kake cikin tsanani. Ka sani! Duk abinda ya kuskure maka, to bai kasance zai same ka ba. Duk kuma abinda ya same ka bai kasance zai kuskure maka ba. Ka sani, lallai cin nasara yana tare da haquri, yayewa kuma tana tare da baqin ciki, kuma lallai a tare da tsanani akwai sauki”.
A riwayar wanin Tirmiziy kuma: “Ka kiyaye dokar Allah, zaka samu Ubangiji a gabanka, ka nemi sanin Allah a lokacin da ka ke cikin yalwa, zai san da kai a lokacin da kake cikin tsanani. Ka sani! Duk abinda ya kuskure maka, to bai kasance zai same ka ba. Duk kuma abinda ya same ka bai kasance zai kuskure maka ba. Ka sani, lallai cin nasara yana tare da haquri, yayewa kuma tana tare da baqin ciki, kuma lallai a tare da tsanani akwai sauki”.
Ma'abuta
ilimi suka ce:
Lallai
wannan hadisin yana qunsar wasiyyoyi masu girma, da kuma qa'idodi daga cikin
muhimman lamuran addini, Har wassunsu suka ce:
Na yi
tunanin wannan hadisin sai ma'anarsa ta sanya ni cikin ximuwa, har na yi kusan
Na kixime, Saidai abin haushin shine: Yadda Mutane suka jahilci wannan
hadisin, kana suke da qarancin fahimta, ga ma'anarsa.
Ya ku
Musulmai!!
KIYAYE
ALLAH (احفظ الله) da
ake nufi a cikin wannan hadisin shine:
KIYAYE DOKOKINSA, DA AIKIN BASHI HAQQOQINSA,
DA TSAYUWA GA UMURNINSA DA BINSU, WAJEN HANINSA KUMA DA NISANTA, Allah mabuwayi
da xaukaka yana cewa:
"Wannan shine abinda ake yin alkawari a gare
ku ga dukkan mai yawan komawa ga Allah, mai kiyaye dokokinsa *
Wanda yaji tsoron Mai rahama a
fake, kuma ya zo da wata zuciya mai tawakkali" [qaf: 32-33].
KIYAYEWA
NE, da ya haxa da kiyaye KAI da abinda ya tattara (NA HARSHE DA JI DA GANI), da
kiyaye CIKI da abinda ya qunsa (NA FARJI DA QAFA…), Imam Ahmad da Attirmiziy
sun fitar daga hadisin Abdullahi xan Mas'ud (رضي الله
عنه), daga Annabi (صلى الله
عليه وسلم), yace:
"JIN KUNYAR ALLAH IYAKAR JIN
KUNYARSA shine: Ka kiyaye KAI da abinda ya tattara, da kuma CIKI da abinda ya
qunsa".
KIYAYEWA
NE da yake hana gavvai zamewa da aikata
laifuka, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم)
yace:
"Duk wanda ya kiyaye min abin da ke
tsakanin havansa biyu, da abinda ke tsakanin qafofinsa Na lamunce masa shiga
aljanna", Bukhariy ya ruwaito shi.
KIYAYEWA NE da yake kare sha'awa daga bauxewa
zuwa ga vata daga ma'abucinta, ko ta karkace da su daga kyawawan halayya abun
yabo zuwa ga kishiyan haka, Allah mabuwayi da xaukaka yana cewa:
"Da masu kiyaye farjojinsu maza da mata masu
kiyaye farjojinsu, da maza masu ambaton Allah dayawa, da kuma mata, Allah ya
musu tanadin gafara da wani lada mai girma" [Ahzab: 35].
Ya
ku taron Muminai!!
Yana daga
qa'idodin addini Lallai sakamako, ya kan zama daga jinsin aiki; Don haka; Duk
wanda ya samar da KIYAYE ALLAH da irin ma'anarsa da ta gabata, To, sai ya samu
KIYAYEWAR ALLAH DA KULAWARSA DA BADA KARIYARSA; Kiyayewar da ta haxa da
vangaren addininsa da duniyarsa, ya kuma tabbatar wa bawa maslaha da dukkan
nau'ukanta, da kuma tunkuxe masa cutuka da dukkan kalolinsu.
Ma'abuta
ilimi sun ce: KIYAYEWAN DA ALLAH KE YI WA BAWANSA, Nau'uka biyu na kiyayewa
ne ke shiga qarqashinsa:
NA
FARKONSU: Kiyayewan da Allah ke yi wa bawa, cikin addininsa, da imaninsa;
ta hanyar kiyaye shi daga faxawa cikin cutukan SHUBUHOHI (BIDI'OI) masu vatar
da Mutane, da kuma SHA'AWOWI na haram; Sai ya sanya masa abinda zai katange shi
daga faxawa cikin abubuwan da za su lalata masa addininsa, Allah mabuwayi da
xaukaka yana cewa:
"Kamar haka dai, Domin mu kawar da mummunan
aiki da alfasha a gare shi, lallai ne shi ya kasance daga cikin bayinmu zavavvu" [Yusuf:
24].
NAU'I
NA BIYU: Ya kiyaye shi cikin maslahohinsa na duniya, kamar Allah ya kiyaye
masa jikinsa, da 'ya'yansa, da iyalansa, da dukiyoyinsa, Allah mabuwayi da
xaukaka yana cewa:
"(Mutum) yana da Mala'iku masu maye wa
juna a gaba gare shi, da baya gare shi, suna tsare shi, da umurnin Allah"
[Ra'ad: 11].
Abdullahi xan Abbas (رضي الله
عنهما) yace:
"Mala'iku suna kiyaye shi, da
umurnin Allah, Saidai Idan qaddarar da aka qaddara masa ta zo, sai su qale shi".
Alhafiz Ibnu-rajab –Allah yayi masa rahama-
yace:
"Daga abin mamakin kiyayewar Allah
ga wanda Allah zai kiyaye, shi ne: Allah ya sanya dabbobin da a xabi'arsu
cutarwa suke yi, su kiyaye bawa daga wani abinda zai cutar da shi, kamar yadda
hakan ya gudana ga Safinatu; 'yantaccen bawan Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم), a lokacin da jirgin kwale-kwale ya karye
da shi, ya fita zuwa ga wani tsibiri, sai ya ga wani zaki, sai zakin yayi ta
tafiya tare da shi, har sai da ya nuna masa hanya", Ta
qare.
Kuma
lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya
qarfafa wannan ma'anar, a cikin wannan wasiyar, a inda yace: “Ka kiyaye dokar Allah, zaka
samu Ubangiji a gabanka"; Don haka, duk wanda ya kiyaye dokokin
Allah, ya kuma lura da haqqoqinsa Sai Allah ya kewaye shi da tsarewarsa, ya
kuma yi baiwa a gare shi da datarwarsa da daidaitawarsa, Ya dawo masa da
qarfafarsa da taimakonsa, Allah yana cewa:
"Lallai Allah, yana tare da masu taqawa,
waxanda suke su masu kyautatawa ne" [Nahli: 128].
Qatadah (رضي الله عنه) yace: "Wanda ya yi
taqawar Allah, Allah ya kan kasance tare da shi, Duk kuma wanda Allah ya
kasance tare da shi To yana tare da jama'ar da ba a rinjayarta, da kuma mai-gadin
da baya barci, da mai shiryarwar da baya bacewa".
Wani daga cikin magabatan kwarai ya rubuta
wasiqa zuwa ga 'xan'uwansa; Ya ce:
"Bayan haka: In har Allah ya kasance
a tare da kai, To wa zaka ji tsoro? Idan kuma ya kasance akanka To wa za ka yi
fata?".
'Yan'uwan
Musulunci!!
Yana
daga abinda wannan NAU'IN ya qunsa: Kasancewar Allah ya kan tsare, ko ya kare
zuriyar salihin bawa, a bayan mutuwarsa, kamar yadda Allah mabuwayi da xaukaka
yake cewa:
"Kuma Ubansu ya kasance salihin mutum"
[Kahf: 82]. Maluma suka ce: Waxannan marayun guda biyu an basu tsarewa da
kariya ne, saboda kasancewar ubansu salihi.
Kamar yadda Allah mabuwayi da xaukaka yake
cewa:
"Kuma waxanda suke, da sun bar zurriya masu
rauni a bayansu, za su riqa tsorace musu, To su kiyayi Allah (dangane da
marayun da suke hannunsu), kuma su riqa faxar Magana madaidaiciya" [Nisa'i:
9].
Kuma
duk wanda ya KIYAYE ALLAH (DA DOKOKINSA) A CIKIN QURUCIYARSA DA QARFINSA Sai
Allah ya tsare shi a lokacin tsufansa da raunin qarfinsa, kuma ya jiyar da shi
daxi; da jinsa, da ganinsa, da wayonsa da qarfinsa. Wani daga cikin magabatan
kwarai ya qetare shekaru xari, alhalin yana cikin qarfinsa da hankalinsa, Sai
wata rana ya kai cafka ga wani abu da qarfi, Sai aka yi masa Magana akan haka, Sai
ya ce:
"Waxannan gavvai ne, da muka tsare
su daga savon Allah a lokacin quruciya, Sai Allah ya kiyaye mana su, a lokacin
tsufanmu".
Jama'ar
Musulmai!!
Lallai wannan
al'ummar; xaixaikunta da jama'ointa, da kuma mabanbantan matsayinsu, da irin
nauyin da ke hawa wuyansu, Duk lokacin da suka kiyaye addinin Allah; suka yi
Imani na gaskiya da Allah, suka miqa wuya ga lamarinSa cikin kowani sha'ani,
suka nemi kuvuta daga bin son rayuka, da sha'awowin zukata, kuma halinsu na
siyasa da tattalin arziqi da zamantakewa da wassunsu suka kasance kamar yadda
tsarin Allah, da sunnar Manzon Allah (صلى الله
عليه وسلم) suka hukunta, Duk lokacin da al'ummar ta
sanya, Musulunci, tatacce, ya zama cikakken tsarin rayuwarta, a cikin dukkan
matakai, da kuma cikin dukkan alaqoqin da za ta yi, da dukkan motsawanta da
shirunta, To, a lokacin ne za su samu KIYAYEWAR ALLAH a gare su, dangane da
dukkan abin qi, da wahalhalu, da fitintinu da matsalolin da al'ummar suke fama
da su, Kuma a lokacin ne, za su samu AMINCI da ZAMAN LAFIYA, da BUWAYA, da
TAIMAKO, Allah mabuwayi da xaukaka yana cewa:
"Waxanda suka yi imani, kuma basu gauraya
imaninsu da zalunci ba, waxannan suna da aminci, kuma sune shiryayyu"
[An'am: 82].
Kuma
lallai al'umma a duk lokacin da IMANI DA ALLAH, da NEMAN KOYI DA MANZONSA (صلى الله عليه وسلم) ya game dukkan rayuwarsu, kana hakan ya
jagoranci dukkan abinda zasu fiskanta, da duk motsawansu To, sai AMINCI da
dukkan nau'ukansa ya kasance a gare su; kamar amintuwa daga abokan gaba, da
abubuwa masu hatsari, da aminci daga abubuwan tsoro da cutuka, da aminci cikin
shugabanci da siyasa, da aminci cikin tattalin arziqi, da aminci cikin
zamantakewa, Kuma duk lokacin da
Musulmai gabaxayansu suka tsayu wajen bin addininsu da karantarwar
Musuluncinsu, suka kuma nisanci son rayuka da bin sha'awowi, kuma suka yi aiki
tuquru da gaskiya wa Musulunci, tare da yin aiki da sabbuban samun xaukaka da
bunqasa da cin nasara, da kuma yin tanadi wa maqiya, To, a nan ne, Allah zai basu kafuwa a bayan
qasa, ya kuma qarfafa su, ya bada buwaya ga kalmarsu, ya kuma sanya tsoronsu a
cikin zukatan maqiyansu, tare da game su, da basu alheri, da adalci, da zaman
lafiya,
"Allah ya yi alkawari ga waxanda suka yi
imani, daga cikinku, kuma suka aikata aiyuka kyawawa, lallai zai shugabantar da
su a cikin qasa kamar yadda ya shugabantar da waxanda suke daga gabaninsu, kuma
lallai ne zai tabbatar musu da addininsu wanda ya yarda musu, kuma lallai ne,
zai musanya musu, daga bayan tsoro, da wani aminci, suna bauta mini basa haxa
ni da komai. Kuma wanda ya kafirta a bayan wannan, lallai waxancan, sune
fasiqai" [Nur: 54-55 ].
Taron
jama'ar Muminai,,,,,
Lallai
wannan al'ummar duk lokacin da bala'i ya sauka a cikinta, kuma ta xanxani
jarabawar rayuwa, Ta samu tsoro sai ta nemi aminci, ko ta qasqanta Sai ta nemi
hanyar samun buwaya, ko ta ci-baya Sai ta nemi fatan samun khilafanci a bayan
qasa da zaman lafiya, Saidai ba za ta tava samun daman hakan ba, kuma al'umma
ba za ta tava samun abubuwan da take fatan samunsu ba matuqar basu tsayu wajen
aiki da sharaxin da Allah ya kafa ba; na tsayuwa da yin xa'a wa Allah da
Manzonsa (صلى الله عليه وسلم), da kuma yarda
cikakkiya, da shari'ar Allah, da kuma aiki da wannan tsarin na Musulunci abin
yarda, To, kuma a lokacin ne varna za ta kau, da koma-baya, sannan tsoro da
firgici da rashin aminci su kau daga gare su, kuma a wannan lokacin babu wani
qarfi daga cikin masu qarfin duniya za su tsaya akan hanyarsu, Allah mabuwayi
da xaukaka yana cewa:
"To, idan wata shiriya daga gare Ni ta zo
muku, to, wanda ya bi shiryarwarta, to baya vacewa, kuma baya wahala *
Kuma duk wanda ya bijire daga ambatona (alqur'ani) to, lallai ne rayuwa
mai qunci ta tabbata a gare shi, kuma za mu tayar da shi a ranar qiyama yana
makaho" [Xaha: 123-124].
Kuma Allah (تعالى)
yace:
"Duk wanda ya bi shiryarwa ta to babu tsoro
akansu kuma ba za su yi baqin ciki ba" [Baqara: 38].
'Yan'uwan
Musulunci!!
Babu wata
al'umma Musulmai a tsawon tarihi, wanda
za su sava wa wannan tsarin (na Musulunci), face ta ci baya; ta koma qarshen
tawaga, sai ta qasqanta, kana a kore ta daga jagoranci, sai kuma tsoro ya
mamaye ta, Maqiya kuma face sun yi mata xauki-xaxxaya, kamar yadda Allah
mabuwayi da xaukaka yake cewa:
"Shin, a lokacin da wata musiba ta same ku,
alhalin kuwa kun samar da irinta guda biyu, Sai kuka ce: Daga ina wannan yake?
Ka ce, Wannan daga rayukanku yake?"[Ali-imrana: 165].
Ya tabbata daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), a matsayinsa na Mai rahama da Tausayi ga
al'ummarsa, Yace:
"Idan kuka yi kasuwanci irin na
iynah (sayar da abu da bashi zuwa wani lokaci, sannan ya sake sayansa da kuxi a
hannu, qasa da na farkon), kuma kuka kama jelar shanu (kiyo), kuma kuka yarda
da noma, sai kuka bar yin jihadi, to Allah sai ya xora muku wani irin qasqanci;
ba zai cire shi ba har sai kun koma zuwa ga addininku".
Al'ummar
Musulunci, a kowani wuri !! Mu sani, Lallai alqawarin Allah a tsaye yake,
duk yadda aka samu canjin zamani ko na hali; Duk lokacin da sharaxin da aka
ambata ya tsayu; ya tabbatu; Don haka:
Duk wanda ya ke son tabbatuwan wannan
alqawarin sai ya yi aiki da sharaxin; "Kuma wane ne, mafi cikawa ga
alqawarinsa fiye da Allah? (Babu!)" [Tauba: 111].
Wannan
ya sanya, Magabatan kwarai daga cikin sahabbai da waxanda suka zo, a bayansu
suka tafi akan wannan tsarin (na Musulunci) suna masu samun amintuwa da Allah,
da dogaro a gare shi, da qarfafa imaninsu da shi, da tabbatuwa cikin azama, da
yin haquri a lokutan wuya ko tsanani, da cikakken bi, ga mafi alherin jagora;
Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم),
tare da yin jihadi, da qoqartawa, da aikata aiyukan alkhairi ba tare da
qaqqautawa ko yankewa ba, Kuma a lokacin ne, Allah ya tsayar da ginin wannan
addinin da Su, kuma daular Musulunci mai qarfi ta kafu a sasanin duniya, Wannan
kuma saboda, Sun auna DUNIYA da ma'auninta na haqiqa, kuma ba su karkata zuwa
gare ta ba, kuma sun san cewa ita (duniya) qasqantacciya ce, mai saurin
gushewa; sai ba su yarda suka yaudari kansu da ita ba, Sun kuma SAN LAHIRA; Sai
suka bata matsayin da ta cancanta, kuma suka sanya ta, gaba ga idanuwansu; Don
samun tabbatuwa a cikin ni'imominta suka kasance suke yin aiyuka, kuma akan
haka suke kwallafa kwaxayinsu, Sai aiyuka masu tsabar wahala suka yi sauqi a
gare su, saboda haka.
Ibnu-Kasir
–Allah yayi masa rahama- ya ambata, cikin abubuwan da suka auku a
shekarar hijira ta xari huxu da sittin da uku (463h) cewa:
((Mai mulkar kafiran Rumawa sai ya
fiskanto cikin rundunonin da ba za su qirgu ba; saboda yawa, misalin duwatsu,
da tanadi mai yawa, da kuma jam'i mai tayar da hankali, Yana kuma daga cikin
niyyarsa; Wai ya tunvuke Musulunci, da ma'abutansu, Sai jagoran Musulmai ya
haxu da shi, a cikin rundunar da bata wuce Mutane dubu ashirin ba, ya kuma ji
tsoron yawan mushirkai, Sai faqihin Malami Abu-Nasrin; Muhammadu xan Abdulmalik
mutumin garin Bukhara ya bashi shawarin cewa lokacin gwabzawa a yaqin ya
kasance ranar juma'a ne bayan rana ta yi zawali; a lokacin da masu huxuba suke
yin addu'oi ga masu jihadi, Kuma a lokacin da vangarorin guda biyu suka
fiskanci juna don fara yaqin sai shugaban Musulmai ya sauka daga dokinsa, ya
faxi ya yi sujjada wa Allah mabuwayi da xaukaka, ya kuma roqe shi maxaukaki, ya
nemi nasararSa, Sai Allah ya saukar da nasararSa ga Musulmai, ya kuma mallaka
musu kafaxun Mushirkai, sai hakan ya kasance nasara ce mai qarfi mai girma)). Maganarsa
ta qare.
Shi
kuma halin da Musulmai suke cikinsa a yau, yana buqatar sake nazari, da kuma
yin gyara na gaskiya.
Taron
Musulmai!!
Ta yaya
alkawarin tsarewa da kiyayewa zai tabbata a yau? Ga Mutanen da suka kawar da
kansu daga hukuntar da wahayin alqur'ani da Sunnah, sai suka gudu zuwa ga
tsare-tsaren da suka sanya da kansu da kuma kundayen da Mutane suka samar?
kamar yadda hakan shine halin da al'umma ta kasance a cikinsa tun fiye da
shekaru xari. Kuma dayawa daga cikin qasashensu basu gushe ba a cikin haka, har
zuwa yau.
Kuma
ta yaya, nasara da buwaya da gyara zai kasance, ga Mutanen da fiskantar wanin
Allah ya yawaita a cikinsu, kamar yadda hakan shine halin da ake ciki a wajen
wassu qaburbura, a wurare dayawa waxanda ba voyayyu ba ne, daga garurrukan Musulmai!
Kuma
ta yaya wassu Mutane za su rabauta; alhalin tsarinsu na tattalin arziqi, ya
ginu akan riba da aka haramta, da kuma sauran mu'amalolin da suka sava wa
littafin Allah, da sunnar ManzonSa Muhammadu (صلى الله
عليه وسلم)? Sai kuka wayi gari suna koyi da kafiran
gabacin duniya ('yan gurguzu), ko na yamma ('yan jari hujja).
Kuma
ta yaya wassu Mutane za su rabauta? Kuma ta yaya al'umma zata tsira, alhalin
munanan abubuwa sun yaxu a cikinta, da abubuwan kyama, kamar yadda haka halin
yake a wassu daga cikin garurrukan Musulmai a yau!
Kuma
ta yaya wassu Mutane za su xaukaka, alhalin bada rashawa da karvarta sun yaxu a
cikinsu? Sannan kuma qarya da fajirci da algus da yaudara sun yaqe su, Sannan,
a cikin dayawa daga cikin mu'amalolinsu an rasa gaskiya da amana, da dukkan
nau'ointa?
Kuma
ta yaya halayen dayawa daga cikin Musulmai za su gyaru, alhalin kuma a wajjen
wassu daga cikin 'ya'yan Musulmai an rasa tutar soyayya don Allah, da kuma
qiyayya don Shi, Sai duniya (da kuxi) suka wayi gari su suke hukunta, soyayya,
da barranta (ko qiyayya).
Ya Allah! Ka gyara yanayin Musulmai!
Ya Allah! Ka gyara yanayinmu da
yanayin Musulmai!
Ya Allah! Ka gyara yanayinmu da
yanayin Musulmai! Ya mafi rahamar masu jin qai!
Allah
yayi albarka wa NI da KU, cikin alqur'ani, kuma ya amfanar da MU da abinda ke
cikinsa na ayoyi da bayani. Ina faxar wannan maganar, kuma ina neman gafarar
Allah wa NI da KU da SAURAN Musulmai, daga kowani zunubi, ku nemi gafararsa;
lallai shi mai yawan gafara ne mai rahama! …
HUXUBA TA BIYU:
Gidiya ta tabbata ga Allah shi
kaxai, kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai;
bashi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawansa ne
kuma manzonsa. Ya Allah ka yi salati da sallama a gare shi, da iyalansa da
sahabbansa gabaxaya.
Bayan
haka:
Ya ku Musulmai!!
Duk wanda
ya kiyaye dokokin Allah; Sai Allah ya lare shi, kuma sai ya sanya masa yayewa
daga kowani baqin ciki, da kuma mafita daga kowani qunci, Sannan ya azurta shi
ta inda baya tsammani .
Ya ku taron Muminai!!
Lallai kwanaki
da lokatai suna ta wucewa alhalin 'yan'uwanmu a qasar Falasxinu suna fama da
yanayi mai tsoratarwa na zubar da jininsu da ake yi, da sassara su
(gunduwa-gunduwa), da korarsu da kakkashe su, Wucewan kwanaki zai yi wuya ya
goge hakan, ko kuma kwakwale su manta su, Tsoratarwa mummuna, daga Yahudawan
kama-wuri zauna (Sahayinah); masu kwace gidaje, Wanda masu kashe Mutane da
zubar da jini suke zartar da shi akansu; da dukkan nau'ukansa da shakalinsa.
Ya
kai mai gani! A ina wai, masu sanya doka suke na duniya, a lokacin da suke
ganin wannan sharrin yana tunbatsa, da wannan zaluncin da yake ta girma?!
Kwaxayin kwace abin wani, wanda ba shi da
iyaka, ko ma'auni, Daga yahudawan Sahayina masu kwace!
To,
Duniya gabaxayanta ta sani, lallai mafita kawai tana nan ne, cikin bayar
da haqqoqi ga ma'abutansu, da kuma yaxa adalci na haqiqa a tsakanin Mutane
gabaxayansu (ba tare da wariya ba), tare da kiyaye karamar Mutum da matsayinsa
wanda Musulunci ya zo da shi.
Ya
ku 'Ya'yan al'ummar annabi Muhammadu (صلى الله
عليه وسلم) wannan lamarin yana da hatsari mai girma,
kuma tambaya a gaban Allah tana da girma dangane da taimakon lamuran Musulmai,
kuma wajibi ne mu tsaya daram tare da 'yan'uwanmu Muminai da suke qasar
falasxinu ko waninta daga cikin wuraren Musulmai, Ina haxa ku da Allah, ina haxa ku da Allah,
wajen sauke wannan wajibin; kowani Mutum gwargwadon ikonsa, cikin abinda zai iya,
Ku aika musu dukiya, da gamsuwar zuci, Ku fiskanci Allah mabuwayi da xaukaka da
yin managartan addu'oi a gare su, a kowani lokaci da zamani, ALLAH SHINE WANDA
AKE NEMAN TAIMAKONSA, ZUWA GARE SHI AKE YIN KOKE, KUMA AKANSA AKE DOGARA, KUMA
LALLAI SHI, YA ISAR MANA, MADALLA DA SHI, ABIN DOGARO.
Sannan ku sani, Lallai mafi tsarkin abinda
rayuwarmu za ta tsayu akansa shine: Shagaltuwa da yin salati da sallama ga
Annabi mai karamci.
Ya Allah! Ka yi
salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka; annabinmu Muhammadu.
Ya Allah! Ka yarda da khalifofi
shiryayyu, kuma jagorori masu shiryarwa; Abubakar da Umar, da Usman, da Aliyu.
Ya Allah! Ka gyara halinmu da halin
Musulmai.
Ya Allah! Ka yaye baqin ciki, ka
kore ababen baqanta rai.
Ya Allah! Ka tseratar da bayinka
Musulmai daga kowani ibtila'i da fitina.
Ya Allah! Ka yi maganin maqiyan
Musulmai; Lallai su, basu gagare ka ba, Ya Mai girma!
Ya Allah! Ka kiyaye 'yan'uwanmu
Musulmai a kowani wuri, Ya Allah ka kasance mai taimako a gare su; Ya
Mabuwayi ya Mai matsanancin qarfi.
Ya Allah! Ka datar da Mai hidiman
Masallatan harami biyu zuwa ga abinda kake so, kuma ka yarda da shi, Ya
Allah ka taimaki addininka da shi, kuma ka xaukaka kalmar Musulmai da shi.
Ya Allah! Ka gafarta wa Musulmai maza
da Musulamai mata; rayayyu daga cikinsu da kuma matattu.
Ya Allah! Ka bamu mai kyau a Duniya,
a Lahira itama mai kyau, kuma ka kare mu daga azabar Wuta.
No comments:
Post a Comment