1- Allah
a kwanakin rayuwa ya sanya wasu lokatai na alheri, ya kuma bada damammaki domin
a iya guzuri da ayyukan ɗa'oi, waɗanda Musulmi a cikinsu zai samu mafi
ƙoƙoluwar darajoji, ya rabauta da samun rahamar Allah da falalarSa. Hakan (kawo
lokutan alkhairi) ya kasance ne saboda hikimomi masu girma, da hanyoyin
tarbiyyah maɗaukaka. Mafi girmar hikimar kuma itace, domin Bawa ya kasance mai
ƙaƙƙarfar alaƙa da UbangijinSa.
2- Waɗannan
lokatan suna ƙara imani, suna haɓaka taƙawa, suna kuma ɗaukaka maka ma'aunin
ayyukanka kyawawa. Waɗannan lokatan suna tsarkake ruhi, suna tsaftace rai, suna
ƙarfafar himma, suna zama canji ga tawaya ko matsalar da ake samu a cikin
ibada, suna tunkuɗe ɗabi'ar ƙosawa da ibada da samun raunin himma, ko rashin
marmarin ibada, kuma suna bubbuɗe ƙofofi masu faɗi na tsere.
3- Haƙiƙa
Allah ya umurci bayinSa da aikata alkhairori, da yin gaggawa gare su, kuma ya
yaba wa ma'abuta waɗannan sifofin, a inda ya ce: "Sai ku yi tsere ga ayyukan
alherori" [Ma'idah: 48]. Wannan kuma faɗakarwa ne ga himmomin ma'abuta
hankula, da cewar su yi gaggawa ko saurin aikata ayyukan kwarai gabanin ƙurewar
lokaci.
4- Lokutan
alheri basu yankewa a cikin al'ummar Musulunci, Yanzu haka, ga al'ummar ta
fiskanci mafi falalar lokutan alheri wanda suka fi girma (wato, kwanaki goman
farkon watan zulhijjah). Allah ya yi rantsuwa da kwanakin, domin ya nuna mana
matsayi da girman falalarsu, kuma Allah Mai girma, baya yin rantsuwa sai da abu
mai girma, Allah Ta'alah ya ce: "Ina rantsuwa
da alfijir * Da dararuwa goma" [Fajr: 1-2]. Dararen sune na
sanannun yini; waɗanda Allah ya shar'anta yawaita zikirinSa a cikinsu, Allah
Ta'alah ya ce: "Kuma su ambaci sunan Allah a
cikin 'yan kwanuka sanannu, saboda abinda ya azurta su da shi na dabbobin
ni'ima" [Hajj: 28].
5- Duk
aiki na kwarai da ya auku a cikin kwanaki goman farkon zulhijjah, to shine yafi
soyuwa a wurin Allah Ta'alah, idan irinsa ya auku a cikin kwanakin da ba su ba.
Idan kuma aiki ya kasance shine mafi soyuwa to shine mafi falala. Kuma
mai yin aiki a cikin kwanakin nan guda goma shine mafifici, akan wanda ya fita
jihadi fiysabililLahi, matuƙar ya dawo da ransa da kuma dukiyarsa.
6- Yana
daga cikin kyawawan ayyuka a waɗannan kwanakin guda goma: Tilawar
Alƙur'ani, da zikirin Allah, da aadu'oi, da sadar da zumunci, da biya wa
Musulmai buƙatunsu, da ziyartar marasa lafiya, da rakiyar gawa, da ciyar da
abinci, da sauran ayyuka, tare da yawaita faɗin La ilaha illa Lah (Hailala) da
Allahu Akbar (Kabbara) da faɗin Alhamdu lillahi (Hamdala), a cikin dukkan
lokatai, a kuma kowane irin hali. Saboda idan Mutum ya san ƙimar abinda yake
nema, to sai ya raina abinda yake bayarwa. Kuma lallai kayan sayarwar Allah
yana da tsada, kuma lallai kayansan shine Aljannah.
No comments:
Post a Comment