1-
Wanda ya ribaci lokatan ayyukan ɗa'a, kuma ya yi gaggawa zuwa ga aikata
alkhairori, sai a bubbuɗe masa taskokin falala da taimako da rahama, kuma sai
ya rabauta da rabo mai girma.
2-
Manzon Allah -Sallal Lahu alaihi Wasallama- ya shaida mana cewa, kwanakin sune
mafifitan kwanakin Duniya, a cikin faɗinsa: "Mafifitan
kwanakin Duniya sune guda goma", yana nufin goman farkon
zulhijjah. Sai aka ce: A cikin fita yaƙi fiysabililLahi babu kamar goman? Sai
ya ce, e, babu kamarsu a cikin yaƙi
fiysabililLahi, sai ga Mutumin da ya turbuɗe fiskarsa da turɓaya (ya
mutu a wurin gumurzu). Albazzar da Ibnu-Hibbana suka ruwaito shi.
3-
A cikin kwanaki goman akwai Yinin Arafah, yinin rukunin hajji wanda yafi girma,
kuma yinin gafarar zunubai. Kuma a cikin kwanakin akwai ranar layya, wanda shine
gaba ɗaya mafificin yini, a wurin Allah.
4-
Sababin da ya sanya kwanaki goman farkon zulhijjah suka yi fice da fifiko,
shine domin haɗuwar jiga-jigan ibadodi a cikinsu, wanda su ne: Sallah, Azumi,
Sadaka, da Hajji. Kuma lallai hakan baya yiwuwa a cikin wasu kwanakin idan ba
su ba.
5-
Waɗannan kwanakin guda goma lokaci ne mai girma, kuma babbar ni'ima, sannan
dama ce wanda ya wajaba a tsaya a ci gajiyarsu, kuma (mustahabbi ne) Musulmi ya
keɓance su da ƙarin ibadodi, yana mai yaƙar zuciyarsa a cikinsu, domin ya
yawaita fiskoki na alheri da ayyukan ɗa'a.
6-
Kuma yana daga cikin ayyukan: Yin azumi, wato azumtar kwanaki
taran farko na watan zulhijjah, saidai wanda yafi muhimmanci a cikinsu shine
azumin ranar Arafah ga wanda ba Mahajjaci ba. Kuma azumi yana cikin ayyuka
mafiya fifiko, kuma Allah ya keɓe sanin azumi ga kansa.
No comments:
Post a Comment