2019/08/01

hudubar 1 zulhijja 1440 Subaitiy فضل العشر من ذي الحجة










HUƊUBAR MASALLACIN ANNABI SAW
JUMA'A 1/ZULHIJJAH/1440H
Daidai da 2/August/2019M






LIMAMI MAI HUƊUBA
Shehun Malami Dr. Abdulbariy ɗan Awwadh AsSubaitiy








TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA


بسم الله الرحمن الرحيم

Allah a kwanakin rayuwa ya sanya wasu lokatai na alheri, ya kuma bada damammaki domin a iya guzuri da ayyukan ɗa'oi, waɗanda Musulmi a cikinsu zai samu mafi ƙoƙoluwar darajoji, ya rabauta da samun rahamar Allah da falalarSa. Hakan (kawo lokutan alkhairi) ya kasance ne saboda hikimomi masu girma, da hanyoyin tarbiyyah maɗaukaka. Mafi girmar hikimar kuma itace, domin Bawa ya kasance mai ƙaƙƙarfar alaƙa da UbangijinSa.
Waɗannan lokatan suna ƙara imani, suna haɓaka taƙawa, suna kuma ɗaukaka maka ma'aunin ayyukanka kyawawa.
Waɗannan lokatan suna tsarkake ruhi, suna tsaftace rai, suna ƙarfafar himma, suna zama canji ga tawaya ko matsalar da ake samu a cikin ibada, suna tunkuɗe ɗabi'ar ƙosawa da ibada da samun raunin himma, ko rashin marmarin ibada, kuma suna bubbuɗe ƙofofi masu faɗi na tsere, Allah Ta'alah ya ce: "To, a cikin wannan, masu tsere sai su yi ta gwagwarmayar nema" [Mudaffifina: 26].
Yin gaggawa wajen aikata alkhairori, da neman maɗaukakan darajoji sifa ce ta Muminai makusanta Allah, Allah Ta'alah ya ce: "Da masu gaggawa masu tsere * waɗannan sune aka kusantar * A cikin Aljannonin ni'ima" [Waki'ah: 10-12].
Wanda ya ribaci lokatan ayyukan ɗa'a, kuma ya yi gaggawa zuwa ga aikata alkhairori, sai a bubbuɗe masa taskokin falala da taimako da rahama, kuma sai ya rabauta da rabo mai girma, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma muka sanya su  jagorori suna shiryarwa da umurninmu, kuma muka yi wahayi zuwa gare su; da su aikata alkhairori, da tsayar da Sallah, da bayar da zakkah, kuma sun kasance masu bauta ne a gare mu" [Anbiya'i: 73].

Haƙiƙa Allah ya umurci bayinSa da aikata alkhairori, da yin gaggawa gare su, kuma ya yaba wa ma'abuta waɗannan sifofin, a inda ya ce: "Sai ku yi tsere ga ayyukan alherori" [Ma'idah: 48]. Wannan kuma faɗakarwa ne ga himmomin ma'abuta hankula, da cewar su yi gaggawa ko saurin aikata ayyukan kwarai gabanin ƙurewar lokaci.

Kuma Allah ya yi bushara ga masu tsere cikin ayyukan alkhairi da cewar suna da tabbataccen rigaye, da rabauta da samun alƙawarin Allah tabbatacce, a inda ya ce: "Waɗannan suna gaggawar tsere a cikin ayyukan alherori, kuma su a gare su, masu samun rigaye ne" [Muminuna: 61].

Kuma Mutum, lallai idan damar kusanci da yin biyayya ta halarto, to sai ya yi azama iyakar azama, wajen ribatar wannan damar da yin gaggawa zuwa gare ta. Kuma gajiyawa ta tabbata ne cikin jinkirtata, da cewa zan yi abin da sannu. Kuma lallai mai nawa da jinkiri bashi da wani rabo, a filin tseren rigaggeniya, kuma idan falalar samun alkhairi ya kuɓuce masa to zai tauni yatsu; domin nadama, a lokacin da nadamar ba za ta masa amfani ba.

Manzon Allah -Sallal Lahu alaihi wa sallama- ya kwaɗaitar da mu; dangane da ribatar shekarun samartaka gabanin saukar furfura da tsufa, da ribatar faragar lokaci gabanin yawaitar ayyuka da shagali, da morar lafiyarka gabanin cuta ta rafke ka kwatsam, Allah Ta'alah ya ce: "Ya ku waɗanda suka yi imani, ku yi taƙawar Allah, kuma rai ta yi dubi kan abinda ta gabatar domin gobe, kuma ku ji tsoron Allah, lallai ne Allah Mai bada labari ne game da abinda kuke aikatawa" [Hashr: 18].

Allah Subhanahu ya bayyana cewa, lallai shiri domin fiskantar lokatan alheri -wanda kuma kadan ne mai wucewa- dalili ne da yake nuna gaskiyar Mutum, a inda Allah Subhanahu ya ce: "Don haka, idan al'amari ya ƙullu, to, da sun yi wa Allah gaskiya, lallai da hakan ya kasance mafifici a gare su" [Muhammadu: 21].

Wannan al'ummar tana da busawar rahama a cikin yinin zamaninta, Anas ɗan Malik -Allah ya ƙara yarda a gare shi- yana cewa: "Ku nemi alheri a tsawon zamaninku gaba ɗayansa, kuma ku bijiro da kayukanku ga wuraren busawar rahamar Allah Ta'alah; saboda Allah yana da wuraren busawar rahamarSa, wanda yake shafan wanda ya so da su daga Bayinsa".

Lokutan alheri basu yankewa a cikin al'ummar Musulunci, Yanzu haka, ga al'ummar ta fiskanci mafi falalar lokutan alheri wanda suka fi girma (wato, kwanaki goman farkon watan zulhijjah).
Allah ya yi rantsuwa da kwanakin, domin ya nuna mana matsayi da girman falalarsu, kuma Allah Mai girma, baya yin rantsuwa sai da abu mai girma, Allah Ta'alah ya ce: "Ina rantsuwa da alfijir * Da dararuwa goma" [Fajr: 1-2].
Dararen sune na sanannun yini; waɗanda Allah ya shar'anta yawaita zikirinSa a cikinsu, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma su ambaci sunan Allah a cikin 'yan kwanuka sanannu, saboda abinda ya azurta su da shi na dabbobin ni'ima" [Hajj: 28].

Manzon Allah -Sallal Lahu alaihi Wasallama- ya shaida mana cewa, kwanakin sune mafifitan kwanakin Duniya, a cikin faɗinsa: "Mafifitan kwanakin Duniya sune guda goma", yana nufin goman farkon zulhijjah. Sai aka ce: A cikin fita yaƙi fiysabililLahi babu kamar goman? Sai ya ce, e, babu kamarsu a cikin yaƙi fiysabililLahi, sai ga Mutumin da ya turbuɗe fiskarsa da turɓaya (ya mutu a wurin gumurzu). Albazzar da Ibnu-Hibbana suka ruwaito shi.

A cikin kwanaki goman akwai Yinin Arafah, yinin rukunin hajji wanda yafi girma, kuma yinin gafarar zunubai.

Kuma a cikin kwanakin akwai ranar layya, wanda shine gaba ɗaya mafificin yini, a wurin Allah.

Sababin da ya sanya kwanaki goman farkon zulhijjah suka yi fice da fifiko, shine domin haɗuwar jiga-jigan ibadodi a cikinsu, wanda su ne: Sallah, Azumi, Sadaka, da Hajji. Kuma lallai hakan baya yiwuwa a cikin wasu kwanakin idan ba su ba; Manzon Allah SAW ya ce: "Babu wasu yini wanda aiki nagari, ya fi soyuwa a cikinsu, a wurin Allah, fiye da waɗannan kwanakin", wato, goman farko na watan hajji. Sai su ka ce: Ya Ma'aikin Allah! Koda jihadi ne, fiy sabilillah? Sai ya ce: "Koda jihadi ne, fiy sabilillah, sai ga Mutumin da ya fita da kansa, da kuma dukiyarsa baki ɗaya, amma shi da dukiyar babu wanda ya koma". Isnadinsa ingantacce ne akan sharaɗin Bukhari da Muslim.
Don haka, duk aiki na kwarai da ya auku a cikin kwanaki goman farkon zulhijjah, to shine yafi soyuwa a wurin Allah Ta'alah, idan irinsa ya auku a cikin kwanakin da ba su ba.
Idan kuma aiki ya kasance shine mafi soyuwa to shine mafi falala. Kuma mai yin aiki a cikin kwanakin nan guda goma shine mafifici, akan wanda ya fita jihadi fiysabililLahi, matuƙar ya dawo da ransa da kuma dukiyarsa.


Ana fiskanta ko shiga waɗannan kwanakin ne guda goma, da tuba ta gaskiya, da kulla azama kan ribatarsu, da nisantar ayyukan saɓo, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ku tuba zuwa ga Allah gaba ɗaya -Ya ku Muminai- domin ku samu babban rabo" [Nur: 31].

Waɗannan kwanakin guda goma lokaci ne mai girma, kuma babbar ni'ima, sannan dama ce wanda ya wajaba a tsaya a ci gajiyarsu, kuma (mustahabbi ne) Musulmi ya keɓance su da ƙarin ibadodi, yana mai yaƙar zuciyarsa a cikinsu, domin ya yawaita fiskoki na alheri da ayyukan ɗa'a, Annabi SAW ya ce: "Babu wasu kwanaki da aiki ya fi girma kuma ya fi soyuwa a cikinsu, a wurin Allah fiye da waɗannan kwanakin goma; sai ku yawaita hailala a cikinsu". (Wato, faɗin: LA ILAHA ILLAL LAHU) da kabbara (faɗin: ALLAHU AKBAR) da hamdala (faɗin: ALHAMDU LILLAHI). Ahmad ya ruwaito shi.

Yana daga cikin waɗannan ayyukan: Yawaita sallolin nafilfili, Manzon Allah SAW ya ce:  "Ina horonka da yawaita sujjada ga Allah, saboda ba zaka yi sujjada ɗaya ga Allah ba, face ya ɗaukaka darajarka da ita, ya kuma kankare maka zunubi da ita". Muslim ya ruwaito shi.

Kuma yana daga cikin ayyukan: Yawaita sadakoki, da nufin samun kusanci zuwa ga Allah, da neman yardarSa da ladanSa, ko ta hanyar kyautuka da kyautatawa da toshe buƙatar faƙirai da Miskinai da marayu, Manzon Allah SAW ya ce: "Akan kowane Musulmi akwai sadaka, Sai suka ce: Ya Annabin Allah, Wanda kuma bai samu ba? Ya ce: Ya yi aikin hannunsa sai ya amfanar da kansa ya yi sadaka, Sai suka ce: Idan kuma bai samu ba? Ya ce: Ya taimaki gajiyayye. Sai suka ce: Idan kuma bai samu ba? Ya ce: Ya yi aiki da kyakkyawa, ya kuma kame daga aikata sharri, to lallai hakan sadaka ne". Bukhariy ya ruwaito shi.

Yana daga ayyukan kwarai: Sallolin dare; wato Bayi su tsayu suna neman gafara, suna zikiri, Allah Ta'alah ya ce: "Sune waɗanda suke kwana ga Ubangijinsu suna masu sujada da tsayuwa". [Furƙan: 64].


Huɗuba ta biyu

Yana daga cikin kyawawan ayyuka a waɗannan kwanakin guda goma: Tilawar Alƙur'ani, da zikirin Allah, da aadu'oi, da sadar da zumunci, da biya wa Musulmai buƙatunsu, da ziyartar marasa lafiya, da rakiyar gawa, da ciyar da abinci, da sauran ayyuka, tare da yawaita faɗin La ilaha illa Lah (Hailala) da Allahu Akbar (Kabbara) da faɗin Alhamdu lillahi (Hamdala), a cikin dukkan lokatai, a kuma kowane irin hali. Saboda idan Mutum ya san ƙimar abinda yake nema, to sai ya raina abinda yake bayarwa. Kuma lallai kayan sayarwar Allah yana da tsada, kuma lallai kayansan shine Aljannah, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ku yi gaggawa zuwa samun wata gafara daga Ubangijinku, da kuma Aljannar da faɗinta shine faɗin sammai da ƙassai, an tanade ta ga masu taƙawa" [Ali-imrana: 133].


Kuma yana daga cikin ayyukan: Yin azumi, wato azumtar kwanaki taran farko na watan zulhijjah, saidai wanda yafi muhimmanci a cikinsu shine azumin ranar Arafah ga wanda ba Mahajjaci ba. Kuma azumi yana cikin ayyuka mafiya fifiko, kuma Allah ya keɓe sanin azumi ga kansa, kamar yadda ya zo cikin hadisin Ƙudusiy: "Dukkan aikin Ɗan Adam nasa ne, in banda azumi, shi kam nawa ne, kuma nine Mai yin sakayya akansa". Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma Manzon Allah SAW ya kasance yana azumtar kwanaki taran farkon zulhijjah, kuma Manzon Allah SAW ya ce:  "Wanda ya yi azumin yini ɗaya fiysabililLahi, Allah zai nisantar da fiskarsa daga wuta na tsawon shekaru saba'in". Bukhariy ya ruwaito shi.
Addu'a ….
……………….



No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...