HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 7/MUHARRAM/1441H
daidai da 6/SEFTEMBER/ 2019M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ABDULLAHI BN ABDURRAHMAN ALBU'AIJAN
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
KWADAITARWA
KAN RIBATAR LOKATAI
(الحث على اغتنام الأوقات)
Shehin Malami wato:
Abdullahi bn Abdurrahman Albu'aijan –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai
taken:
KWADAITARWA
KAN RIBATAR LOKATAI, wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allahn
da ya halitta dukkan komai, kuma ya kaddara su kaddarawa, kuma ya sanya dare da
yini akan yanayi na mayewa ga wanda yake nufin ya yi tunani ko yake son ya yi
godiya.
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya, sai Allah shi daya ne Makadaici, bai Haifa ba, kuma ba a
haife shi ba, kuma babu wani da ya kasance tamka a gare shi.
kuma ina shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawansa ne Manzonsa amintacce, ya isar da manzanci, ya sauke
amana, ya yi nasiha ga al'umma, ya yi jihadi a al'amarin Allah iyakar jihadi,
har mutuwa ta zo masa.
Ya Allah! ka yi dadin
salati, da sallama a gare shi da iyalansa da sahabbansa, da wanda ya shiryatu
da shiriyarsa, ya bi sunnarsa, har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka:
Lallai mafi gaskiyar zance shine littafin Allah, kuma mafi karfin igiya
ita ce kalmar takawa (LA ILAHA ILLAL LAHU), mafi alherin addinai addinin annabi
Ibrahima, mafi kyan kissosi Alkur'ani, mafificin shiriya shiriyar annabi
Muhammadu –صلى الله عليه وسلم-,
mafi sharrin al'amura sune kirkirarrunsu, kuma kowace bidi'a bata ce.
Ya ku, Bayin Allah…
Ku yi takawar Allah
cikin abinda ya bada umurni, kuma ku hanu daga abinda ya yi hani kuma ya
tsawatar, "Ya ku wadanda suka
yi imani ku ji tsoron Allah, iyakar tsoronsa, kuma kada ku mutu face kuna
Musulmai"
[Ali-imrana: 102].
Ya ku, Bayin Allah…
!!!
Lallai cikin juyawar yini
da dare, da saurin zamani da canzuwan halaye, da zuwan sabin shekaru, da yadda
ajali ke kokarin riskar ma'abutansa, dukansu dalili ne akan al'amarin gushewa da
makoma, kuma abin lura ne, ga wanda ya ratayu da buri: "Allah yana juyar da
dare da yini, lallai ne a cikin wannan akwai abin kulawa ga ma'abuta basirori" [Nur: 44].
Ka yi tunani akan Duniya da
idon basira
Za ka ga Duniya walakantacciya
ta shude kamar a mafarki
Wanda suke cikinta gaba
daya, lallai za su kare
Sai fiskar Ubangijinka
Ma'abucin girma ta wanzu
"Lallai a
cikin halittar sammai da kassai, da sabawar dare da yini, da jiragen da suke
gudana a cikin teku da abinda yake amfanar Mutane, da abinda Allah ya saukar
daga sama na ruwa, sai ya rayar da kasa da shi a bayan mutuwarta, kuma ya watsa
a cikin kasa daga dukkan dabba, da juyawan iskoki, da girgijen da aka hore a
tsakanin sama da kasa, cikinsu gaba daya, akwai ayoyi ga Mutane masu hankalta" [Bakara: 164].
Ya ku taron Musulmai!!!
Kowace shekara ana
kaddarata da lissafi, sai a sanya lokatan kaddara a cikinta, da ajalin yara da
tsofi da samari, kuma ba a tsawaita shekarun mai shekara, kuma ba a tauye wani
abu daga rayuwarsa, face yana cikin littafin (kaddara).
Tsareku suna karewa,
burace-burace suna yankewa, ajali yana karewa, "Kuma dukkan wanda yake
kan kasa mai karewa ne * kuma fuskar Ubangijinka Mai girman jalala da karamci
ita ce take wanzuwa"
[ArRahman: 26-27].
Sai ku ribaci damar shekaru
da rayuwa, kuma ku gabatar da ayyukan da suka fi tsarki domin kanku, kuma kada
ku rika jinkirta aiki, domin cikin hakan akwai hana rai aikin kwarai, kuma ku
ribaci rayuwarku gabanin mutuwa, da faragarku gabanin shagaltuwa da ayyuka, da
wadacinku gabanin talauci, da samartaka gabanin tsufa, da lafiya gabanin cuta,
"Kuma ku mayar da al'amari zuwa ga ubangijinku, kuma ku sallama masa,
gabanin azaba ta zo muku, alhalin ku ba za a taimake ku ba * kuma ku bi mafi
kyan abinda aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku gabanin azaba ta zo muku
bisa auke, alhalin ku baku sani ba * sai rai ta ce: Ya nadamata akan abinda
nayi sakaci a cikin sashen Allah, kuma hakika na kasance daga masu izgili * ko
kuma kada ta ce: Da Allah ya shiryar da ni, da na kasance daga masu takawa * ko
kuma kada -a lokacin da take ganin azaba- ta ce: Da ace ina da wata komawa (ga
Duniya), domin in kasance daga cikin masu kyautatawa" [Zumar: 54-58].
Ya ku Musulmai!!!
Shekara ta kare, an rufe
ayyukanta, an nade takardunta, madalla da Mutumin da ya ribaci damarsa, ya mori
lokacinsa, ya gyara ayyukansa.
Ku saurara!
Lallai mun shiga farkon
sabuwar shekara, wanda hakan yake mana rakiya zuwa kaburbura, yake tafiya da mu
zuwa yinin tayarwa a bayan mutuwa, to ya dace da mu, mu rika tafiyar da
rayuwarmu cikin biyayyar Allah, "Kuma duk abinda kuka gabatar da shi na alheri
za ku same shi a wurin Allah" [Muzzammil: 20].
Ya ku Bayin Allah!!!
Mafi alherinku shine wanda
rayuwarsa ta yi tsawo, sai aikinsa ya yi kyau. Mafi sharri kuma shine wanda
rayuwarsa tayi tsawo, sai aikinsa ya yi muni.
Kuma daga cikinku kowa za a
tambaye shi akan rayuwarsa; yaya ya karar da ita, da samartakarsa ta yaya ya
tafiyar da ita?
Ya nadamarmu kan tozarta
mafi tsadar lokatai
Ya takaicinmu kan sakaci,
da mafi girman lokatai!
Dauki cewa, kuruciya tana
bayyanar da uzurin ma'abucinta!
To menene uzurin masu
furfurar da Shedan ya batar da su?
Ya ku taron Musulmai!!!
Lokatan rayuwa dama ne na
yin aiki, kuma ni'ima ne da suke hukunta godiya, "Idan za ku nemi
kididdige ni'imomin Allah ba za ku iya lissafa su ba" [Ibrahim: 34].
Kuma lokaci yana wucewa, rayuwar
kadan ce, ayyukan wajibai wani akan wani, hakkoki kuma suna dayawa, don haka
babu damar wargi da wasa, kuma babu lokacin hutawa da sakaci,
Ya ku bayin Allah! Sai ku
ji jankunne mai tsoratarwa, da tattaunawa mai kama kunne, a inda Allah Ta'alah zai
tambayi bayinSa: "Ya ce: Nawa kuka zauna a bayan kasa, na kidayar
shekaru? * Za su ce: Mun zauna yini daya, ko rabin yini, sai ka tambayi masu
kidayawa! * Ya ce: Ba ku zauna ba face kadan, da kun kasance kuna sani * Shin
zato kuke yi cewa, Mun halitta ku ne domin wasa, kuma lallai ku zuwa gare mu ba
za a mayar da ku ba!? * Allah Mamallakin Gaskiya ya daukaka, babu abin bautawa
face shi, shine Ubangijin al'arshi mai daraja" [Muminuna: 112-116].
Allah ya mini albarka NI da
KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da
KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA
TA BIYU
Yabo ya tabbata ga akan kyautatawarsa, kuma godiya tasa ce
akan datarwarSa da baiwarSa.
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya, ina mai
girmama sha'aninsa.
Kuma ina shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanSa ne ManzonSa mai kira ga samun yardarSa.
Ya Allah ka yi salati a
gare shi da iyalansa da sahabbansa da sallamar aminci mai yawa.
Ya ku Musulmai!!!
Ku ji tsoron Allah
Ta'alah, kuma ku rigayi shekarunku da ayyukanku, kuma ku tabbatar da zantukanku
da ayyukanku; domin hakikanin rayuwar Mutum ita ce abinda ya tafiyar da ita a
cikin biyayyar Allah, kuma "Mai hankali shine wanda ya yi ma kansa hisabi, kuma ya yi aiki domin
abinda ke tafe bayan mutuwa. Gajiyayye kuma shine wanda ya bi son ransa, sai
kuma yake kwallafa wa Allah buri".
Ya ku Bayin Allah!!!
Cikin shudewar zamani akwai
abin lura mai girma, kuma cikin jujjuyawar kwanaki akwai fadakarwa mai girma, "Lallai ne a
cikin sabawar dare da yini, da abinda Allah ya halitta a cikin sammai da kasa,
hakika akwai ayoyi ga Mutane masu takawa" [Yunus: 6].
Sannan ku sani!
Lallai Allah ya zabi
zababbu daga halittunSa, sai ya zabi manzanni 'yan aika daga cikin Mala'iku,
suma Mutane ya zabi manzanni daga cikinsu, daga cikin magana kuma ya zabi
ambatonsa, a doron kasa kuma ya zabi masallatai, daga cikin watanni kuma ya
zabi watan Ramadhana da watanni hudu masu alfarma, daga cikin kwanaki kuma
yinin juma'a, daga cikin darare kuma ya zabi lailatul kadari; sai ku rika
girmama abinda Allah ya girmama!
Ku saurara!
Lallai ku, ga ku a farkon
watan Muharram, kuma farkon shekarar hijira, kuma lallai wannan watan yana
cikin watanni masu alfarma (hudu) wadanda Allah ya girmama su, Allah Ta'alah ya
ce: "Lallai ne kidayar watanni a wurin Allah watanni ne guda goma sha
biyu, a cikin littafin Allah, a ranar da ya halicci sammai da kassai, daga
cikinsu akwai hudu masu alfarma, wannan ne addini madaidaici, saboda haka, kada
ku zalunci kanku a cikinsu" [Taubah: 36].
Lallai zalunci –Ya ku
taron Musulmai- haramun ne a dukkan watanni, saidai Allah ya girmama
alfarmar watanni (hudu) masu alfarma, ya sanya aikata zunubi a cikinsu yafi
girma, kuma aiki na kwarai da lada a cikin watannin shima yafi girma.
An ruwaito daga Abu-bakrah
–رضي
الله عنه-, daga Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai zamani ya
juya, kamar yanayinsa, a lokacin da Allah ya halitta sammai da kassai. Shekara
daya watanni goma sha biyu ne, daga cikinsu akwai guda hudu masu alfarma; guda
uku a jere; zul ka'adah da zulhijjah da Muharram, da kuma Rajab na kabilar
Mudar, wanda yake tsakanin jumadah da Sha'aban", Bukhariy da Muslim
suka ruwaito.
Kuma hakika Musulmai tun
zamanin khilafancin Umar –رضي الله عنه- sun yi riko da al'amarin hijirar Annabi –صلى الله عليه وسلم- daga garin Makkah
zuwa Madinah; sai suke kulle abin tarihi da shekarar hijira, saboda Allah ya
rarrabe tsakanin gaskiya da barna da al'amarin hijira. Kuma sahabbai sun fari kidayar
shekarar da watan Allah Muharram, sai lamarin ya tabbatu akan haka, kuma sai
al'umma gabadayanta ta rungumi hakan.
Ya ku taron Musulmai!!!
Lallai yana cikin shiriyar annabinmu Muhammadu –صلى الله عليه وسلم-, kuma yana cikin
abinda suke kankare munanan laifuka, kuma yana daga godiyar Allah da girmama
shi, yin azumin ranar Ashura, wanda shine ranar goma na watan Muharram.
An ruwaito daga Abdullahi
dan Abbas –رضي
الله عنهما- ya ce: Yayin da Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya iso garin Madinah sai ya iske Yahudawa
suna azumtar ranar Ashurah, Sai aka tambaye su akan haka, sai suka ce: Wannan
shine yinin da Allah ya bada nasara wa annabi Musa da Banu-isra'ila a cikinsa
akan Fir'auna, don haka muke azumtarsa domin girmama shi, sai Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Mune muka fi
jibintar Musa fiye da ku, sa'annan sai ya yi umurnin a azumce shi".
Kuma an ruwaito daga
Ibnu-Abbas –رضي
الله عنهما- ya ce: "Ban ga Annabi –صلى الله
عليه وسلم – yana kirdadon yinin da ya fifita shi akan waninsa ba, fiye da
wannan yinin –wato, ranar Ashurah, da kuma wannan watan, yana nufin watan
ramadhana",
Bukhari da Muslim ya ruwaito su.
A cikin littafin Sahihu Muslim, lallai Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Azumtar yinin
Arafah, ina zata wa Allah cewa zai kankare shekarar da take gabaninsa da wanda
take a bayansa. Azumtar yinin Ashurah kuma, ina zata wa Allah cewa zai kankare
shekarar da take a gabaninsa".
Kuma a yayin da labari ya kai ga Annabi –صلى الله عليه وسلم- a karshen rayuwarsa
cewa, lallai yahudawa suna rikon yinin Ashurah a matsayin idi, to sai yay i niyyar
ya azumci ranar tara da goma, a shekarar da take tafe, amma sai mutuwa ta shiga
tsakaninsu.
An ruwaito daga Abdullahi dan Abbas –رضي الله عنهما- ya ce –a lokacin da
Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya yi azumin yinin Ashurah, kuma ya bada umurnin a
azumce shi- sai su ka ce: Ya Manzon Allah! Lallai Ashurah yini ne da Yahudawa
da Nasara suke girmama shi, To sai Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya ce: "To, idan shekara
mai kamawa ta zo, insha Allahu, za mu azumci ranar Tara (Tasu'ah)", Yana nufin, tare da
goma (Ashura). Ya ce: Shekara mai kamawan bata zo ba, face Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya rasu. Muslim ya
ruwaito shi.
Don haka, abinda yafi falala –Ya ku Bayin Allah- shine
a azumci yini daya gabanin Ashurah, domin a saba wa Yahudawa. Wanda
kuma aka rinjaye shi ya kasa, to kada a rinjaye shi ga azumtar ranar Ashurah.
Ya Allah! Ka daukaka Musulunci da Musulmai…
Ya ku Bayin Allah…
!!!
"Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga
wannan Annabin, Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da
sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].
,,, ,,, ,,,
No comments:
Post a Comment