2019/06/21

الحذيفي 18 شوال 1440 HUDUBAR MASALLACIN MANZON ALLAH SAW











HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 18/Shawwal /1440H
daidai da 21/June/ 2019M


LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ALIYU DAN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY



TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
YI MA KAI HISABI KAN YIN KWAZO CIKIN XA'OI
(محاسبة النفس والاجتهاد في الطاعات)
Shehin Malami wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy–Allah ya tsare shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: YI,Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah Mabuwayi Mai yawan gafara,  yana juyar da dare akan yini, kuma yana juya yini akan dare, lallai cikin haka akwai abin lura ga Ma'abuta basirori.
Ina yin yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa akan ni'imominSa waxanda babu wanda yake qididdige su idan ba shi ba, daga cikin waxanda muka sansu, da waxanda bamu sani ba, Sunayen Ubangijinmu sun tsarkaka, kuma sifofinsu sun girma, Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; Makaxaici Mai rinjaye
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa, Mai yin albishir da rahamar Allah da AljannarSa, Mai gargaxi kan uqubobin Duniya da faxawa Wuta.
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da IyalanSa da SahabbanSa masu biyayya.

Bayan haka;
Ku kiyaye taqawar Allah Subhanhu Wa Ta'alah ta hanyar neman yardarSa, da kiyayar fushinSa da uqubobinSa, Allah سبحانه  ya ce: "Kuma Ubangijinka yana halittar abinda ya ga dama, kuma yana yin zavi, Zabin bai kasance nasu ba ne, Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma (Allah) ya xaukaka daga barin abinda suke yi na shirka " [Qasas: 68].
Don haka, Ubangiji Mabuwayi da xaukaka ya halicci halitta da qudurarSa da iliminSa da hikimarSa da jin-qanSa. Kuma ya samar da wannan Duniyar da muke gani, kuma ya sanya masa iyakar da za su kai gare shi; ba za su qetare shi ba, kuma ya halicci sabubba a cikin wannan Duniyar da muke gani, kuma ya halicci abinda za su kasance da waxannan sabubban, don haka, shine Mahaliccin sabubba da abinda suke kasantuwa da sababinsu, don haka, duk abinda Allah ya nufa sai ya kasance, wanda bai nufa ba kuma ba zai kasance ba, Allah Ta'alah ya ce: "Allah ne Mahalicci ga komai, kuma shi ne wakili akan komai * shi ke da mabuxan sammai da qasa, Waxanda suka kafirta da ayoyin Allah, waxannan sune masu hasara" [Zumar: 63].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Ku saurara, Halitta tasa ce, da kuma bada umurni, Albarkar Allah Ubangijin talaikai ta yawaita" [A'araf: 54].
Mutum halitta ne daga cikin halittun Allah masu ban mamaki, wanda Allah ya tattara masa daga sifofin al'ajabin da suka rarrabu ga waninsa, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma haqiqa mun halitta Mutum cikin mafi kyawun tsayuwa" [Tin: 4].
Kuma Allah Subhanahu ya ce: "Kuma a cikin rayukanku (akwai ayoyi na al'ajabi), To ba za ku duba ba?" [Zariyat: 21].
Kuma Allah Subhanahu ya ce: "Yana daga ayoyinSa: yadda ya halitta ku daga turvaya, sai ga ku kun zama Mutane kuna watsuwa" [Rum: 20].
Kuma Allah Tabaraka Wa Ta'alah ya yi baiwar karramawa ga 'yan Adam, Allah Mabuwayi da xaukaka ya ce: "Kuma haqiqa mun girmama 'yan Adam, kuma muka xauke su a tudu da teku, kuma muka azurta su daga abubuwa masu daxi, kuma muka fifita su akan masu yawa daga abinda muka halitta, fifitawa" [Isra'i: 70].
Ita kuma karramawar Allah Ta'alah ga 'yan Adam, karramawa ce ga na kirki da fajiri, a cikin wannan Duniyar, ta hanyar basu ni'imomi. Kevantacciyar karramawa kuma a Lahira, da samun yardar Allah da Aljannonin ni'ima ga muminai ta ke, saboda Kafiri bashi da wani rabo a Lahira, kuma "Ubangijinka baya zaluntar kowa" [Kahf: 49]. Saboda Allah a Lahira baya karrama wani face wanda ya masa xa'a daga Mutane da Aljanu, Ibnu-Asakir ya ruwaito  daga hadisin Anas xan Malik -رضي الله عنه- daga Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya ce: Lallai Mala'iku sun ce: Ya Ubangijinmu, ka halicce mu, kuma ka halitta 'yan Adam, sai ka sanya suna cin abinci, suna shan abin sha, kuma suna sanya tufafi, kuma suna auren Mata, kuma suna hawan dabbobi, suna yin barci suna hutawa, mu kuma baka sanya mana wani abu daga cikin haka ba, to ka basu Duniya, mu kuma Lahira! Sai Allah Mabuwayi da xaukaka ya ce: Ba zan sanya wanda na halitta da hannuna ba, kuma na busa masa daga ruhina, ya zamto kamar wanda nace masa: Kasance, sai ya kasance ba.
 Hadisin yana da shahid daga hadisin Abdullahi xan Amru, a wajen Imam Axxabaraniy.

Kuma yana daga MANYAN NI'IMOMIN ALLAH GA 'YAN ADAM: ABINDA YA HORE MUSU NA AMFANI DA MASLAHOHI DA NI'IMOMI, Allah Subhanahu ya ce:  "Ashe, baku gani ba, cewa: Allah ya hore muku abinda yake cikin sammai da abinda ke a cikin qassai, kuma ya zuba ni'imominSa akanku, bayyannu da voyayyu" [Luqman: 20].
Kuma Allah Mabuwayi da xaukaka ya ce: "Kuma ya hore muku abinda ke cikin sammai da qasa, gaba xaya daga gare shi. Lallai a cikin haka, akwai ayoyi ga Mutanen da suke tunani " [Jasiya: 13].
Kuma hikimar zubo ni'imomi ga 'yan Adam, ita ce, domin su miqa wuya ta hanyar xa'a ga Allah Ta'alah, kuma su gode masa, kada su haxa shi da wani (shirka), Allah Ta'alah ya ce: "Kamar haka (Allah) yake cike ni'imominSa akanku, tsammaninku zaku sallama masa" [Nahl: 81].
Ibnu-Kasir -رحمه الله- a tafsirinsa ya ce: "Kamar haka, Allah yake sanya muku abinda kuke amfani da shi cikin al'amuranku, da kuma abinda kuke da buqatuwa gare shi, domin ya kasance taimako a gare ku, wajen yin xa'a a gare shi da kuma bautarsa", maganarsa ta qare.

Kuma Allah Mabuwayi da xaukaka bai azizita ambaton Mutum ba, tun daga lamarin halittar annabi Adamu -عليه السلام- da hannunSa, da abinda ya bayyana na matakai da halin Mutum, sai don ya bayyana masa aikinsa a cikin wannar rayuwar, kuma ya ilmantar da shi ayyukansa, da hikimar halittarsa; da cewar Mutum shine mahallin kallafawar Allah, da bashi umurni da hani, da kasancewarsa shine mai xaukar amanar shari'a, da samun xaukaka sakamakon ibadarsa ga UbangijinSa, Allah Ta'alah ya ce: "Shin, Mutum zato yake yi cewa, a barshi sagaga?" [Qiyama: 36].
Shafi'iy -رحمه الله- ya ce: "sagaga, wato, ba za a umurce shi, a hana shi ba!".
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Shin, zato kuke yi cewa, mun halicce ku domin wasa, kuma lallai ku zuwa gare mu ba za mayar da ku ba?" [Mu'uminuna: 115].

Daga abinda Allah Subhanahu ya bayyana mana na sunnonin gudanar da wannan Duniyar, da abinda ya halitta a cikin Duniya na sabbuba, lallai Allah Subhanahu wa Ta'alah ya bayyana mana sunnarsa a cikin wannan rayuwar, da kuma cewa: Lallai ayyukan Mutum suna kawo gyara ga rayuwa, matuqar sun kasance ayyuka nagari, kuma lallai varna tana shiga rayuwar halittu idan ayyukan Mutum suka zama gurvatattu. Kuma lallai ayyukan Mutum, lamarin kyansu da gurvacewarsu yana yin naso, har ga dabbobi da tsirrai, domin rahamar Allah da adalcinsa, kuma domin Mutum ya lazimci ayyukan xa'oi, ya riqa qaurace wa ayyukan haram, Allah Subhanahu yana faxa dangane da yadda rayuwa take albarka ake samun alherorinta, idan ayyukan Mutane suka zama nagari: "Da Ma'abuta alqaryu za su yi imani su yi taqawa, to haqiqa mun buxe musu albarkoki daga sammai da qasa, saidai sun qaryata sai muka kama su da abinda suka kasance suke aikatawa" [A'araf: 96].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Kuma da Ma'abutan littafi sun yi imani, kuma sun yi taqawa, da mun kankare miyagun ayyukansu, kuma da mun shigar da su Aljannonin ni'ima * Kuma da sun tsayar da Attaura da injila da abinda aka saukar zuwa gare su daga Ubangijinsu, haqiqa da sun ci daga samansu da kuma qarqashin qafafunsu" [Ma'ida: 65-66].

Alqur'ani shine littafin da Allah ya sauqar da shi ga Musulmai da kuma Ahlul kitabi, babu wani da iya canza abinda ke cikinsa, Allah Ta'alah ya ce: "Waxanda suka yi imani, kuma basu cakuxa imaninsu da zalunci ba, waxannan suna da aminci, kuma sune shiryayyu" [An'am: 82]. Wato, basu cakuxa imaninsu da shirka ba, kamar yadda Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya fassara shi da shi.
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Ya ku waxanda suka yi imani idan kuka taimaki Allah sai ya taimake ku" [Muhammdu: 7]. Wato, idan kuka taimaki addinin Allah, sai Allah ya taimake ku.
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Waxanda suke idan muka ba su iko a bayan qasa, sai su tsayar da salla, kuma su bayar da zakka, kuma su yi umurni da kyakkayawa, kuma su yi hani da mummuna, kuma aqibar al'amura ga Allah take" [Hajj: 41].
Ibnu-kasir a tafsirinsa ya ce: "Umar xan Abdul'aziz -رحمه الله- ya yi huxuba sai ya karanta wannan ayar, sannan ya ce: Lallai ayar ba ga shugaba shi kaxai take ba, saidai ta shafi shugaba da wanda ake shugabantansu, Shin ba zan baku labarin abinda naku akan shugaba daga cikin haka, da kuma abinda na shugaba akanku daga cikinta ba? Lallai kuna da haqqi akan shugaba daga cikin haka, ya kama ku da haqqoqin Allah wanda suke kanku, kuma ya karvi haqqin sashenku da yake kan sashe, kuma ya shiryar da ku ga hanyar da tafi miqewa, gwargwadon iko. Kuma lallai akanku akwai wajabcin yi masa biyayya".
Kuma a cikin faxinSa Maxaukaki "Kuma aqibar al'amura ga Allah take" [Hajj: 41]. Akwai bada aminci ga wanda ya tsayu da waxannan al'amurran guda huxu (tsayar da sallah, bada zakka, umurni da kyakkyawa, da hani ga mummuna), daga tsoron wasu da kuma kaidin maqiya, kamar yadda Allah Ta'alah ya ce: "Kuma idan kuka yi haquri, kuka yi taqawa, makircinsu ba zai cutar da ku da komai ba, lallai Allah ga abinda suke aikatawa Mai kewayawa ne" [Ali-imrana: 120].

Kuma kamar yadda gyaruwar ayyukan Mutum ya kan zama sababi na gamewar alkhairi ga halittu, to kuma haka alherin ya kan kevanci wanda yake aikin, kamar yadda Allah Ta'alah ya ce: "Wanda ya yi aiki nagari; daga cikin maza ko mata, alhalin yana Mumini, to lallai haqiqa za mu rayar da shi rayuwa mai daxi, kuma haqiqa za mu saka masa ladansa da mafi kyawun abinda suka kasance suna aikatawa" [Nahl: 97].
Kuma a daura da wannan, lallai lalacewar aikin Mutum yana cutar da Mutumin, kuma yana shigar da varna ga dukkan rayuwa, Allah Subhanahu ya ce: "Kuma da sarkiya (Allah) zai bi son zuciyoyinsu, da sammai da qasa da abinda ke cikinsu sun lalace" [Muminuna: 71].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Varna ta bayyana a sarari da teku, saboda abinda hannayen Mutane suka aikata, domin Allah ya xanxana musu sashen abinda suka aikata, tsammaninsu za su komo (gare shi)" [Rum: 41].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Kuma babu abinda zai same ku na musifa, face daga abinda hannayenku suka aikata, kuma Allah yana yafewar waxansu laifukan dayawa" [Shira: 30].

Kuma ka yi dubi -Ya kai Mutum- ga halin waxanda suka munana ayyuka, menene ya sauka akansu, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma dayawa muka karya wata alqarya, wanda ta kasance mai zalunci, sai muka qagi halittar waxansu  Mutane na daban a bayanta" [Anbiya'i: 11].
Kuma an ruwaito daga Abdullahi xan Umar -رضي الله عنهما- ya ce: Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Abu biyar suna aukuwa da abu biyar; Alfasha bata bayyana a cikin wasu Mutane, har su bayyanar da ita, face annoba da cutuka sun bayyana waxanda basu kasance a cikin Mutanen da suka gabace su ba, kuma matuqar shugabanninsu basu yi hukunci da littafin Allah ba, face Allah ya sanya faxansu a tsakaninsu, kuma Mutane ba za su hana zakkar dukiyoyinsu ba, face an kama su da fari da kuma kafewar ruwan sama, kuma ba don dabbobi ba, da ba a musu ruwa ba. Kuma ba za su tauye sikili ba face an kama su da fari, da zaluncin shugabanni. Kuma ba za su warware alqawarin Allah da alqawarin ManzonSa ba, face Allah ya qaqaba musu maqiya, sai su riqa xauke sashen abinda yake a hannunsu", Ibnu-Majah ya ruwaito shi.
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Kuma Mutum ba shi da komai face abinda ya aikata * Kuma lallai aikinsa za a ganshi" [Najm: 39-40].

Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
            Godiya ta tabbata ga Allah Mabuwayi Mai yawan gafara, Mai haquri abin godiya. Ina yin yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa, kuma ina tuba gare shi ina neman gafararSa; domin yabo na Ubangijina ne, a Duniya da Lahira, akan falalarSa da ni'imominSa, waxanda muka sani da waxanda bamu sani ba.
            Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokin tarayya; Masani abinda ke cikin qiraza.
            Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa wanda aka turo shi da shiriya da kuma haske.
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa masu rigaye zuwa ga dukkan aiki managarci.

 Bayan haka
Ku ji tsoron Allah Ta'alah, domin ku riqi hanya zuwa ga Allah; zai shigar da ku AljannoninSa, kuma za ku rabautu da samun yardarSa.

Ya kai Mutum
Ka duba abinda Allah ya maka na ni'imomi, wanda babu mai ikon ya qididdige su, sai ka tsayu da godiyarsu. Kuma da za a xauke maka mafi qarancin ni'ima, to babu wani wanda ba Allah ba wanda ke da ikon ya mayar maka da ita, tare da cewa babu kaxan ko qarami daga ni'imomin Allah.

Kuma lallai kai, -Ya kai Mutum- da daidaituwanka, da qoqarin kawo gyaranka, da yadda kake shuka alkhairi, da kange kai daga sharri, zaka kasance mai taimako wajen kiyaye al'ummarka, mai tsamar da kanka daga sharrace-sharrace da uqubobi.
Kuma ka sani, lallai kai abin tambaya ne kan ayyukanka, a cikin rayuwarka, da bayan mutuwarka, Sai ka yi dubi kan abinda za ka gaya wa Ubangijinka, Allah Ta'alah ya ce: "Ya kai Mutum, lallai ne kai mai aikin wahal da kai ne ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, kuma kai mai haxuwa da shi ne * To, amma wanda aka baiwa littafinsa da damansa * to za a yi masa hisabi, hisabi mai sauqi * kuma ya juya ga iyalansa (a cikin Aljannah) yana mai raha * Amma wanda aka baiwa littafinsa daga bayan bayansa * to za shi dinga kiran halaka * kuma ya shiga wutar sa'ira" [Inshiqaq: 6-12].
Kuma ya zo cikin hadisi cewa: "Qafar Mutum ba za ta gusa ba, face an masa tambayoyi kan abu guda huxu; akan rayuwarsa ta yaya ya qarar da ita, da samartakarsa yaya ta qare, da dukiyarsa ta yaya ya neme ta, kuma yaya ya vatar da ita, da kuma iliminsa me ya aikata da shi".

Kuma ka sani -Ya kai Mutum- lallai gidanka mai wanzuwa mai dawwama itace take gabanka, bayan mutuwa, to madalla idan har ka rayar da ita da ayyukan kwarai, kuma bone ya tabbata akanka idan ka yarda da Duniyarka, ka manta da Lahirarka; saboda Duniyarka zata juya maka, kana so ko kana qi, Ita kuma Lahira tana fiskanto ka, akan abinda ka aikata.

Bayin Allah!
"Lallai ne Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan Annabi, Ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi, da sallamar aminci" [Ahzab: 56].
Har qarshen addu'a.

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...