HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 4/Shawwal /1440H
daidai da 7/June/ 2019M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ALIYU DAN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
YI MA KAI HISABI KAN YIN KWAZO CIKIN XA'OI
(محاسبة
النفس والاجتهاد في الطاعات)
Shehin Malami
wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy–Allah ya tsare shi- ya yi
hudubar juma'a mai taken: YI,Wanda kuma
a cikinta ya tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo
ya tabbata ga Allah Mabuwayi Mai yawan gafara,
Mai haquri abin godiya, "Ya san yaudarar idanu,
da abinda qiraza ke voyewa" [Gafir: 19].
Ina
yin yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa akan ni'imominSa waxanda babu wanda
yake qididdige su idan ba shi ba, daga cikin waxanda muka sansu, da waxanda
bamu sani ba na bayar alkhairori, da tunkuxe ababen qi da sharrori
Ina
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake, bashi da
abokin tarayya, zuwa gare shi ake mayar da al'amurori.
Ina
kuma shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa,
wanda aka turo shi domin rahama ga Talikai, wanda Allah ya turo shi da shiriya
da haske.
Ya
Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka
Muhammadu, da IyalanSa da SahabbanSa masu gaggawar aikata aikin kwarai
lafiyayye.
Bayan
haka;
Sai
ku kiyaye taqawar Allah Ta'alah ta hanyar aikata abinda ya yi umurni, da
nisantar abinda ya yi hani akansa ya yi tsawa, saboda babu mai samun rabo sai
masu taqawa. Kuma babu mai yin hasara face saboda bijire wa Allah da bin son
zuciya, Allah سبحانه ya ce: "Amma
wanda ya yi girman kai * Kuma ya zavi rayuwa ta kusa (Duniya) * To lallai ne,
wutar Jahimu ita ce makoma * Amma wanda ya ji tsoron tsayuwa a gaba ga
UbangijinSa, kuma ya kange kansa daga son rai * To, lallai ne Aljannah ita ce
makoma" [Nazi'at: 37-41].
Ya
ku Bayin Allah …
Ku
sani lallai samun rabon Mutum da tsirarsa da jin daxinsa a cikin rayuwarsa da
bayan mutuwarsa, basu kasancewa, sai ta hanyar xa'a ga Ubangijin Talikai.
Ita
kuma xa'a bata tabbatuwa sai da bin umurnin Allah Ta'alah, da kuma barin abinda
Allah ya yi hani akansa.
Su
kuma waxanda suke yin aiki da umurnin Ubangiji Mabuwayi da xaukaka, kuma suke
qaurace wa hane-hanenSa, to lallai waxannan suna tare da "waxanda
Allah ya musu ni'ima, daga Annabawa da siddiqai (masu yawan gaskatawa) da
shahidai, da salihai. Kuma waxannan sun kyautatu ga zama abokan tafiya * Wannan
kuma falala ce daga Allah, kuma Allah ya isa ya zama Masani"
[Nisa'i: 69-70].
Amma
wanda ya yi aiki da xa'ar da aka yi umurni da ita, sai ya ke haye aikin savo,
to lallai ya yi biyayya wa Allah a cikin wani hali, ya kuma sava wa Allah a
cikin wani hali. Kuma lallai savon da ya yi wa Ubangijinsa Maxaukaki tana cutar
da aikinsa na xa'a, ta hanyar rage ladanta, kamar yadda zata iya lalata ladan
aikinsa mai kyau; idan ta kasance daga cikin masu ruguza aiki.
Don
haka, babu makawa ga wanda yake son yin xa'a ga Allah Ta'alah, cikakkiyar
biyayya, ya haxa tsakanin aikata nau'ukan xa'oi, ya kuma nisanci ayyukan haramun, kamar yadda
Allah Mabuwayi da xaukaka yake cewa: "Ya ku waxanda suka
yi imani ku yi xa'a wa Allah, kuma ku yi xa'a wa Manzo, kuma kada ku lalata
ayyukanku" [Muhammadu: 33]. Ma'ana: kada ku vata
ayyukanku na xa'a da aikata savo.
Kuma
Allah سبحانه ya ce: "Ka ce: Lallai ni an
umurce ni da na bauta wa Allah, ina mai tsarkake addini a gare shi * kuma an
umurce ni da na kasance farkon Musulmai * Kuma ka ce: Lallai ni ina tsoron idan na sava wa
Ubangijina azabar rana mai girma * Ka ce: Allah nake bauta ina mai tsarkake
masa addinina" [Zumar: 11-14].
Kuma
Allah Ta'alah ya ce: "Kuma kada ku kasance, kamar wadda ta
warware zarenta filla-filla bayan tukkarsa" [Nahl:
92]. Wannan kuma ya dace da kowace biyayya wanda savo da zai cutar da shi ya
biyo bayansa.
Kuma
Malamai suka faxa dangane da faxinsa سبحانه: "Shin xayanku yana
son cewa wani lambu daga dabino da inabobo ta kasance masa, wanda qoramu suke
gudana daga qarqashinsu, a cikinsa yana da kowane 'ya'yan itace, sai tsufa ya
same shi, alhali kuwa yana da zurriya masu rauni, sai guguwar da take da wuta a
cikinta ta same shi, sai ta qone? Kamar haka Allah yake bayyanar da ayoyi a
gare ku, tsammanin za ku yi tunani" [Baqara: 266].
Suka ce: Wannan misali ne wanda Allah ya buga shi ga ayyukan xa'a wanda zunubai
suke tafiyar da su, suke lalata su. A'uzu billahi Allah ya tsare.
An
ruwaito daga Sauban -رضي الله عنه- daga Annabi -صلى الله عليه وسلم- lallai shi ya ce: "Tabbas,
na san wasu Mutane daga al'ummata, waxanda za su zo ranar qiyama da ayyuka
kwatankwacin duwatsun Tihama farare, sai Allah ya sanya su kasance qura abar
watsewa. Sauban ya ce: Ya Ma'aikin Allah, ka sifanta mana su, ka fito da
lamarinsu fili, domin kada mu kasance daga cikinsu! Sai ya ce: Lallai su 'yan'uwanku, kuma daga irin
fatunku, kuma yin ibada a cikin dare kamar yadda kuke yi, sai dai su Mutane ne
waxanda idan suka keve da abubuwan da Allah ya haramta, sai su keta musu
alfarma", Ibnu-Majah ya ruwaito shi, kuma hadisi
ingantacce.
Kuma
wannan hadisin a cikinsa akwai tsawatarwa mai tsanani da tsoratarwa, ga Mutumin
da tsoronsa ga Allah bai hana shi aukawa cikin abinda ya haramta ba, kuma akwai
tsoratarwa ga Mutumin da yake biyar da munanan ayyuka a bayan kyawawa.
Ya
ku Musulmai…
Lallai
Allah Mabuwayi da xaukaka ya muku baiwar taimako daga wurinsa da kuma dacewa,
wajen aikata xa'oi da ayyukan kusanci a cikin watan alkhairori da albarkoki,
kuma Allah ya kiyaye ku a cikinsa daga laifuka masu halakarwa, kuma ya tsare
muku Shaixan, wanda yake kira zuwa ga aikata ayyukan haramun da nau'ukan vata;
sai lokuta a cikin watan Ramadhana suka zama masu tsarki a gare ku, kuma sai
awowinsa suka zama masu daxi a gare ku, har kuka ji daxin tilawa da sauraron
Ayoyi, kuma sai zukatanku suka tsarkaka da yin xa'a ga Mai rahama, kuma kuka
wulaqanta Shexan, kuma kuka kasance dangane da kyawawan ayyuka ana taimakonku.
Kuma lallai maqiyin Allah Shexan abin zargi korarre yana son ya xauki fansarsa
bayan an kunce xaurinsa (daga ficewar watan azumi), domin ya sanya ayyukanku
kamar qura abar watsewa, kuma yana son ya sanya fajirci a gurbin taqawa,
alkhairori kuma sharrace-sharrace, kuma ya vatar da wanda ya samu iko; domin su
kasance tare da shi a cikin wutar Jahannama, tir da ita a makoma, Allah Ta'alah
ya ce: "Lallai Shexan maqiyinku ne, sai ku riqe
shi maqiyi; kuma lallai yana qiran rundunarsa ne domin su kasance cikin
ma'abuta wutar Sa'ira" [Faxir: 6]. Kuma riqon Shexan
maqiyi yana yiwuwa ne da tabbatuwa akan xa'oi, da kuma qauracewa ayyukan haram;
don haka; Madalla, kuma lale da Mutumin da ya biyar da kyawawan ayyuka a bayan
kyawawa, Kuma aminci ya tabbata ga wanda ya biyar da kyawawa ayyuka a bayan
munana, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ka tsai da salla a
gefe guda biyu na yini, da wani yanki daga dare, lallai ne ayyukan qwarai suna
tafiyar da munanan ayyuka. Wannan tunatarwa ne ga masu tunawa" [Hud:
114]. Don haka; Mumini yana kyautata aikinsa, kuma yana roqon Allah koyaushe da
ya azurta shi kyakkyawan qarshe.
Kuma ba a
tunkuxe Shexan face da roqon Allah kyakkyawan qarshe.
Kuma bone
ya tabbata ga wanda ya biyar da munanan ayyuka a bayan munana, har mutuwarsa ta
zo masa, alhalin yana cikin mayen sha'awowi, to a wannan lokacin za a sanya
shamaki tsakaninsa da tsakanin Duniya, kuma abinda aka jiyar da shi daxi na
daxaxan abin Duniya ba zai amfanar da shi ba, sai kuma nadama ta sauko masa,
sai kuma raxaxin azaba ya dawwama, Allah Ta'alah ya: "Shin
ba ka gani ba ne, idan mu ka jiyar da su daxi na tsawon shekaru * sa'annan sai
abinda ake musu alqawali ya zo musu * Abinda suka kasance ake jiyar da su
daxin, ba zai tunkuxe azaba daga gare su ba" [Shu'ara'i: 205-207
].
Kuma Allah
ya ce: "Sai a shamakance tsakaninsu da tsakanin
abinda suke marmari kamar yadda aka aikata da irin qungiyoyinsu a gabaninsu,
lallai sun kasance a cikin shakka mai sanya kokonto" [Saba'i:
54].
Kuma
rayuwa tana bada shaida kan makomar vangarun nan guda biyu. Kuma mai hankali
shine yake xaukar darasi. Tavavve kuma shine wanda ya bijire wa shiriya, ya qi
wa'azantuwa.
Ya
kai Mutum>>>
Lallai
kai ba za ka je ga Ubangijinka da tarin dukiya ba, kuma lallai kai ba za ka je
wa Ubangijinka da iyalanka ba ko abokanka ba, kuma ba za je masa da wani abinda
zai amintar da kai daga faxawa cikin azaba ba. Kawai zaka je wa Ubangijinka ne
da aiki; idan ya kasance aiki ne na kwarai, to sai a shiryar da kai zuwa ga
bayar da amsa ga tambayar mala'ika Munkaru da Nakiru, sai kuma a maka albishir
da samun ni'ima tabbatacciya. Idan kuma aikin ya kasance ba na kwarai ba ne,
sai amsarka ta vace, sai kuma a maka albishir da azaba mai raxaxi, Allah
Ta'alah ya ce: "Kuma dukiyoyinku, haka
suma xiyarku basu zamo abinda yake kusantar da ku a wurinmu komai ba, face
wanda ya yi imani kuma ya aikata aikin kwarai, to waxannan suna da sakamakon
ninkawa, saboda abinda suka aikata. Kuma su amintattu ne a cikin benaye" [Saba'i:
37].
Abin
tijararka shine yin biyayya ga Ubangijin Talikai, kuma dalilin samun tsirarka
shine biyayya , kuma dalilin samun sa'adarka shine biyayya, xaukakarka shine
biyayya. Kuma aikin xa'a zai yi amfani ne idan ya tattara wasu lamurra a
cikinsa;
Al'amari
na farko: Tsarkake niyya da yin ikhlasi a cikin ayyukan, ta yadda za ka
nufin ganin fiskar Allah, babu riya ko yi domin a ji.
Al'amari
na biyu: Xa'oin su kasance akan shiriyar Annabi Muhammadu -صلى الله عليه وسلم-, da sunnarsa.
Al'amari
na uku: Shine ayyukan su tsira daga abubuwan da suke vata su.
Al'amari
na huxu: Dawwama akan aikin biyayya, kamar yadda Allah -سبحانه- ya ce: "Kuma ka bauta wa
Ubangijinka har mutuwa ta zo maka" [Hijir: 99].
Malaman
tafsiri suka ce: Yaqini shine mutuwa, saboda abu ne da ake da tabbaci akansa,
kuma saboda faxin Annabi -صلى الله عليه وسلم-: "Amma Usmanu xan Maz'un to haqiqa yaqini ya zo masa", wato mutuwa.
Kuma
duk wanda ya ce: Bawa idan ya kai ga samun darajar yaqini a cikin imani, to
ayyuka ibadodi za su sauka akansa, to wannan Shexan ne mai tsaurin kai vatacce
mai vatarwa, bashi da komai daga Musulunci koda gwargwadon kwayar zarra, koda
kuwa ya ce ya shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, saboda wannan
zancen ko aqidar yana lalata kalmomin shahada biyu. Kuma mai wannan aqidar da
makamancinsa yana cikin waliyyan Shexan ba waliyyan Allah Mai rahama ba, kuma
koda wasu abubuwan mamaki sun bayyana a hannunsu, to hakan daga ayyukan Shexanu
ne domin su vatar da Mutane. Saboda waliyyan Allah suna tsaida salla da sauran
rukunnan Musulunci da wasunsu, kuma suna tabbatar da tauhidi ta hanyar tsarkake
bauta da ikhlasin addu'a da yanka da bakance da neman taimakon Allah, masu
tabbatar wa Allah Ta'alah da sunayensa da sifofinsa da ayyukansa, ba tare da
tawili da korewa ba, kamar yadda sahabbai suka kasance da tabi'ai da waxanda
suka biyo su da kyautatawa.
Kuma
shin ayyuka sun sauka wa Annabi -صلى الله
عليه وسلم- da
sahabbansa?
Kuma
shin Manzon Allah SAW ya voye haqiqar ne, su kuma waxannan (shehunan xariqar)
vatattu jahilai suka sani?
Lallai
babu abinda ya kai wannan qaryar da suka yi wa Allah Mabuwayi da xaukaka, da
kuma ManzonSa -صلى الله عليه وسلم- girma, inda suke cewa: Shari'a tana da zahiri da baxini. Ko
faxinsu: Musulunci shari'a ne da haqiqa, kuma wai sune suka san baxinin da
haqiqar?
Waxannan
maqiyan addini ne, kai maqiyan dukkan Mutane ne, saboda suna kangewa daga shiga
hanyar Allah, suna vata Alqur'ani da sunnoni, kuma suna adawa da Allah.
Kuma
Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya yi gaskiya a inda yake cewa: "Malami
guda xaya, yafi tsanani ga Shexan fiye da masu bauta guda dubu".
Sai
ka bauta wa Ubangijinka -Ya kai Musulmi- matuqar ranka yana cikin
jikinka, kuma ka nisanci bidi'oi, waxanda suke kishiyantar abinda Annabin
shiriya; shugabanmu Muhammadu -صلى الله
عليه وسلم- ya zo da shi,
Allah Ta'alah ya ce: "Sai ka daidaitu kamar yadda aka
umurce ka, kai da waxanda suka tuba tare da kai, kuma kada ku qetare iyaka,
Lallai ne shi Mai gani ne ga abinda kuke
aikatawa" [Hud: 112].
Allah
ya yi mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI
da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman
gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi,
Ku nemi gafararSa, lallai shi Mai
gafara ne Mai rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA
TA BIYU
Godiya
ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai, Mai mulki Mai gaskiya Mabayyani. Ina yin
yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa akan ni'imominSa na zahiri da baxini,
waxanda muka sani da waxanda bamu sani ba.
Ina
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokin
tarayya; shaidar gaskiya da yaqini.
Kuma
ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa Mai
gaskiyar alqawari amintacce.
Ya Allah
ka yi daxin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu, da
iyalansa da sahabbansa gaba xaya.
Bayan
haka
Ku ji
tsoron Allah Ta'alah a asirce da kuma a bayyane, saboda Ubangijinku shine ya
cancanta a masa taqawa, kuma shine ya cancanta ga ya yi gafara.
Ya
ku Bayin Allah
Haqiqa
watan bauta da qari ya shuxe, Kuma Allah ya buxe wa wannan al'ummar qofofin
alhairori da kyawawan ayyuka, bayan ficewar watan Ramadhana; saboda ayyukan
farillai suna nan, kuma ladansu ana ninka su, kuma dukkan aikin kwarai da kuke
yi a cikin watan azumi, haqiqa an shar'anta kwatankwacinsa a wajen watan
Ramadhana, a matsayin wajibi ko mustahabbi.
Kuma
Ubangijinku Mai rahama ne Mai jin-qai, kuma daga cikin rahamarSa akwai ya
dawwamar wa Bayinsa abinda zai dawwamar da rahamarSa a gare su, da kuma kada ya
yanke musu falalarSa da kyautatawarSa.
Kuma
Ubangijinmu shine abin bauta a cikin sammai da qassai, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma shine abin
bauta a cikin sammai, kuma abin bauta a qassai, kuma shine Mai hikima Masani" [Zukhruf: 84].
Kuma
Allah shine abin bautawa a kowane zamani. Kuma shine Wadatacce da kansa, su
kuma halittu dukkansu suna da buqata; ba za su tsayu ba, sai da rahamar Allah
da iliminSa da ikonSa.
Kuma
Allah shine wanda yafi cancantar bauta, yafi cancantar zikiri, an ce wa: Albishir
Alhafiy: "Lallai wasu Mutane suna yi qoqarin bauta
a cikin watan azumi, Amma idan Ramadhana ya tafi sai su bari? Sai ya ce: Tir da waxannan Mutanen basu sanin Allah, sai
a cikin watan Ramadhana".
Kuma
yana daga cikin ibadodin da suke da sauqi, Yin addu'a da ambaton Allah
(zikiri); sai ku yawaita addu'a da zikiri.
Kuma
ku quntata wa maqiyinku Shexan da dawwama akan ayyukan kusanci, da barin
ayyukan haram. Kuma haqiqa tsinannen ya sani, cewa: Lallai rahamar Allah ta
game kowane abu, kuma hanyoyin biyayya suna da sauqi kuma suna da yawa.
Kuma
haqiqa Annabinmu -صلى الله عليه وسلم- ya kwaxaitar da mu yin azumi guda shida a watan Shawwal, kuma
ya bayyana cewa, idan suka haxu da na watan Ramadhana, to kamar azumtar shekara
ne.
Ya
ku Bayin Allah!
"Lallai
ne Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan Annabi, Ya ku wadanda suka yi
imani ku yi salati a gare shi, da sallamar aminci"
[Ahzab: 56].
No comments:
Post a Comment