HUDUBAR
MASALLACIN ANNABI (r)
JUMA'A 2/ZUL KI'IDAH/1440H
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI Husain bn
Abdul'aziz AlusSheikh
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
Huɗubar
farko
Cikin zuwan zamani wani
bayan wani, akwai abin lura, kuma cikin sassaɓawar dare da yini akwai abin
tunani, Allah Subhanahu yana cewa: Kuma shi ne ya sanya dare da yini akan
mayewa, ga wanda yake son ya wa'azantu, ko yake nufin ya yi godiya [Alfurƙan:
62].
Abin nufi da faɗinSa
khilfah shine masu maye wa juna, a fiskar halitta da ƙaddara, ma'ana ɗayansu ya
kan zo ya maye gurbin ɗayan, kuma kowanne yana zama mayewar ɗan'uwansa, wannan
a bayan wannan, ɗaya bayan ɗayan; da
haske ko dufu, ko tsawo ko nuƙsani, kamar yadda Allah Subhanahu ya ce: Sai muka shafe
ayar dare, kuma muka sanya ayar rana
mai sanya a iya gani [Isra'i: 12].
Kuma Allah Mabuwayin
Sha'ani ya ce: Kuma dare aya ce a gare su Muna feɗe rana daga cikinsa, sai ga su suna masu shiga dufu
[Yashin: 37].
Kuma kalmar Khilfah tana
iya zuwa da ma'anar da take alaƙa da
shari'a, domin Allah ya sanya dare da yini kowannensu yana zuwa a bayan ɗayan,
saboda abinda ya kufce na aikin da ake yinsa ga Allah a cikin wani lokaci, a
iya ramukonsa a wani lokacin na-daban.
An ruwaito daga Shaƙiƙ,
ya ce: Wani Mutum ya zo wurin Umar ɗan
Khaddab -RA- sai ya ce: Sallahta
ta kuɓuce min, a wannan daren? Sai ya
ce: Ka riski abinda ya kuɓuce maka na sallar darenka a cikin yininka.
Don haka, ya zo a cikin sunnah ko hadisi faɗinsa SAW: Babu wani Mutum wanda sallar
dare zata kasance masa, ko wani abu na
bauta a cikinsa, (wanda bai yi su ba),
sai ya karanta shi a tsakanin sallolin
asuba da na azahar, face Allah ya rubuta masa ladan sallarsa, shi kuma barcinsa
zai kasance sadaka ne, a gare shi. Muslim ya ruwaito shi.
Wannan ya sanya Mutum
idan ya yi barci bai yi sallar wutiri ba, ko ya manta, ko suka kuɓuce masa, sai
ya sallaci abinda ya saba sallatarsu a cikin dare, da rana, zai rika sallama
duk bayan raka'oi biyu, sai kuma ya sanya wuturin ya zama raka'oi biyu, da
niyyar wutiri, A'isha -R.A- ta ce: Annabi -SAW- Idan barci ko cuta suka shagaltar da shi bai yi sallar wutirinsa
ba, sai ya sallaci abinda ya kuɓuce masa
raka'oi goma sha biyu a cikin yini. Muslim ya ruwaito.
Lallai cikin sassaɓawar
dare da yini, da jirkitan sifofin zamani, akwai babban abin lura wanda zai
jagoranci Musulmi yin tunani kan girman kudurar Allah da ikonsa, da cikakken
ganin damarsa, da gane girmarsa wanda
bata da iyaka, sai hakan ya masa
jagora izuwa ga ƙanƙan da kai da
risinawa ga Mahaliccinsa Mai girma, sai kuma ya kwashe shi ga miƙa wuya a gare
shi, da amsa masa kan shari'arsa
miƙaƙƙiya, Allah Ta'alah ya ce: Ga wanda ya so ya wa'azantu, ko ya yi nufin
godiya.
Kuma lallai Ma'abuta
imani, sune suke wa'azantuwa mai amfani, sai hakan ya haifar musu da tsoron
Mahaliccinsu, da tsoron uƙubarSa, da kiyayarSa; sai ya samar
musu da kammalallen taƙawa, da cikakken imani, da tauhidi mai tsarki,
Allah Ta'alah ya ce: Lallai cikin mayewar dare da yini da abinda Allah ya
halitta a cikin sammai da ƙassai akwai ayoyi ga Mutane masu taƙawa [Yunus: 6].
Kuma Allah Mabuwayin
sha'ani ya ce: Shine Wanda ya sanya muku dare domin ku natsu a cikinsa, yini
kuma abin ayi gani, lallai ne cikin haka
akwai ayoyi ga Mutane masu ji [Yunus: 67].
Na'am, saboda masu ji
sune suke amfanuwa da ayoyin Allah na halitta, sai su wa'azantu da su, su kuma
samu abin lura, sai hakan ya haifar musu da imani na gaskiya, da aiki mai
tsarki, Allah Ta'alah ya ce: Ashe basu gani ba, lallai mun sanya dare domin su
natsu a cikinsa, yini kuma mai sanya gani, lallai cikin wannan akwai ayoyi ga
Mutane masu imani [Naml: 86].
Ya kai Mumini, Ka riƙi
wa'azi da tunatarwa daga sassaɓawar
zamani, kuma ka kasance -a cikin halayenka- mai godiyar Allah, mai aiki da ɗa'oinsa,
mai nisantar nau'ukan saɓa masa, Allah Ta'alah ya ce: Yana daga rahamarSa, Ya
sanya muku dare da yini domin ku natsu a cikinsa, kuma domin ku nema daga falalarSa, kuma tsammaninku za ku
yi godiya [Ƙasas: 73].
Ibnu Kasir -Allah ya yi
masa rahama- ya ce: Ma'ana ku yi godiya ga Allah ta hanyar aiki da nau'ukan
ibadodi a cikin dare da yini.
'Yan'uwa Masu imani
Yana daga abin lura da
wa'azozin sassaɓawar sifofin zamani, abinda halittu suke samun kansu a lokacin
bazara na tsananin zafi, sai Mutane su riƙa neman hanyoyin samun inuwa mai inuwantarwa, da iska
mai sanyi da daɗi, to shin Musulmi -da irin
wannnan- yana tuna wutar Jahannama da zafinta, Allah ya tsare mu daga hakan, Allah Ta'alah ya ce: Kuma suka
ce: Kada ku fita zuwa yaƙi a cikin zafi, Ka ce: wutar Jahannama ce mafi
tsananin zafi da sun kasance suna fahimta [Taubah: 81].
Kuma ya zo a cikin
Bukhariy da Muslim, lallai Annabi -SAW- ya ce: Wuta ta kai kuka ga Ubangijinta,
ta ce: sashena yana cinye sashe! Sai ya
mata izinin ta riƙa numfashi biyu, na
farko a lokacin sanyi, da kuma a lokacin zafi, kuma shine mafi tsananin abinda
kuke samu na zafi, da abinda kuke samu na jaura (wato, sanyi). Bukhariy da
Muslim.
Sai kayi sauri da
gaggawar aikata dukkan aiki na kwarai; wanda zai kusantar da kai ga Mabuwayi
Mai girma, kuma ka kiyaye ayyukan saɓo masu halakarwa, Allah Ta'alah ya ce:
Kuma ina muku gargadin wuta mai babbaka * Babu mai shigarta sai mafi shagawa *
Wanda ya ƙaryata kuma ya juya baya * kuma lallai za a nesanta mafi taƙawa daga
faɗawa cikinta * Wanda ya bayar da dukiyarsa yana neman tsarkaka * alhalin babu
wani da ya ke da wata ni'imar da ake neman sakamakonta * face dai neman yardar
UbangijinSa mafi ɗaukaka * Kuma da sannu zai yarda.
Kuma Magabatan kwarai
dangane da al'amarin kulawa da sassaɓawan zamani lallai suna da sha'ani mai
girma, Ga Umar -Allah ya ƙara yarda a gare shi- yana yin wasiyya ga ɗansa cewa,
ya riƙa aiki da sifofin imani, kuma daga cikinsu sai ya ambaci, Yin azumi a
lokaci matsanancin zafi.
Kuma a lokacin da Umar
ya yi jinyar ajalinsa sai ya ce: Ya
Allah! lallai ka san ba ina son zama a Duniya ne, domin janyo ƙoramai, ko
dashen bishiyoyi ba, sai domin ƙishin azumi a lokutan zafi, da yin ibadar dare,
da shiga jikin Malamai a halƙoƙin zikiri.
Kuma an hakaito daga
Abdullahi ɗan Umar da wasu daga magabatan kwarai -Allah ya ƙara yarda a gare
su- lallai su idan suka sha ruwan sanyi sai su yi kuka, suna masu tuna faɗin
Allah Ta'alah dangane da kafirai: Ku zubo akanmu daga ruwa, ko daga abinda
Allah ya azurta ku. Sai su ce: Lallai ne Allah ya haramta su ga kafirai
[A'araf: 50].
Huɗuba
ta biyu
Watan Zulƙi'idah yana
cikin watanni hajji, kuma yana cikin watanni huɗu masu alfarma, waɗanda Allah
ya ɗaukaka, kuma ya basu girma da alfarma, Abdullahi ɗan Abbas -Allah ya ƙara yarda a gare su- ya ce:
Allah ya kebance watanni guda huɗu, ya sanya suka zama masu alfarma, kuma ya
girmama alfarmar tasu, kuma ya sanya aikin zunubi a cikinsu ya zama mafi muni,
kuma ya sanya aikin kwarai da lada a cikinsu suka fi girma.
Kuma Ma'abuta ilimi sun
bayyana cewa yin Umrah a watan Zulƙi'idah sunnah ne, saboda umrar Annabi SAW
guda huɗu dukansu sun kasance a cikin Zulƙi'idah kamar yadda ambaton hakan ya zo cikin Sahihul
Bukhariy da Muslim daga Anas -Allah ya ƙara yarda a gare shi-.
Kuma an ruwaito daga
A'isha -Allah ya ƙara yarda a gare ta- ta ce: Manzon Allah SAW- bai taɓa yin
umrah ba, sai a cikin watan Zulƙi'idah. InbuMajah ya ruwaito shi da isnadi mai
inganci.
Ibnul-Ƙayyim -Allah ya
yi masa rahama ya ce: Saidai Allah bai kasance zai zaɓa wa AnnabinSa a al'amarin umrorinsa ba, face lokutan da
suka fi dacewa, kuma suka fi cancantar ayi umrar a cikinsu.
No comments:
Post a Comment