2019/01/18

Husain AlusSheikh 12 Jumadal Ula 1440 daidai 18 Janairu 2019 daga Minbarin Annabi SAW












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 12/JUMADAL ULAH/1440H
daidai da 18/JANAIRU/2019M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. HUSAIN DAN ABDUL'AZIZ AL-ASHEIKH





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
DA'AWA ZUWA GA KYAUTATAWA
(الدعوة إلى الإحسان)
Shehin Malami wato: Husain bn Abdul'aziz Al-Sheikh –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: KIRA ZUWA GA KYAUTATAWA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO


Bayan haka:
Ya ku Musulmai
Yana daga KYAWAWAN LAMURA MASU GIRMA A CIKIN ADDININ MUSULUNCI, TABBATATTU A CIKIN DALILANSU NA YANKAN SHAKKU: DA'AWA ZUWA GA LAMARIN KYAUTATAWA (الدعوة إلى الإحسان), da dukkan surori da misalansa mabanbanta, Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Lallai Allah, Yana umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa ma'abucin zumunta" [Nahl: 90].
Kuma Allah (سبحانه) ya ce: "Kuma ku fadi magana mai kyau zuwa ga Mutane" [Bakara: 83].
Kuma an ruwaito cikin hadisi daga Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) lalllai shi ya ce: "Wanda ya kasance ya yi imani da Allah da kuma ranar karshe, to ya kyautatawa makwabcinsa, kuma wanda ya yi imani da Allah da kuma ranar karshe, to ya karrama bakonsa", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) yana fada, a inda yake tabbatar ko yin wasiyya kan riko da wannan dabi'a mai girma, da yin aiki da wannan ka'ida ko manufa abar karramawa: "Lallai Allah ya wajabta lamarin kyautatawa ga kowane abu" [Muslim]. Malamai masu sharhi suka ce: "abin nufi shine a kyautata wa kowane abu". Don haka, ana nufin, a game komai, kuma a mamaye komai da kyautatawa.

Ya ku taron Musulmai...
Lallai mabudin rahama shine kyautatawa, cikin bautar Mahalicci, da yin aiki cikin amfanar da BayinSa, Allah (سبحانه): "Lallai ne rahamar Allah a kusa take da masu kyautatawa" [A'araf: 56].
Kuma Musulmi, ya dace ya lazimci lamarin kyautatawa, cikin aiki da zance, cikin mu'amalolinsa, da kuma cikin rayuwarsa, don ya rabauta da alfano masu girma, da kuma fa'idodi manya, domin Ma'abucin kyautatawa yana cikin tarayya da Allah kebantacciya (المعية الخاصة), wanda take hukunta, samun kiyayewarSa, da karfafawa, da taufiki, da dacewa, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai ne Allah yana tare da wadanda suka yi takawa, da wadanda suke su masu kyautatawa ne" [Nahl: 128].
Kuma Allah Mabuwayi da daukaka yana cewa: "Kuma lallai Allah yana tare da masu kyautatawa" [Ankabut: 69].
Kuma lallai Mai kyautatawa zai rabautu da samun mafi girman abin nema, wanda shine, Soyayyar Allah Ta'alah ga BawanSa mai kyautatawa (محبة الله), to a wannan lokacin ne, zai rabauta ba; ba zai tabe ba har abada, a Duniya da Lahira, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ku kyautata, domin Allah yana son masu kyautatawa" [Bakara: 195].

'Yan uwa a cikin imani ...
Da lamarin kyautatawa ne, ake faranta zukata, kiraza suke yalwata, ake janyo ni'imomi, ake tunkude azabobi.
Kuma kyautatawa baya yaduwa a cikin wata al'umma, face gininta ya yi karfi, kuma an kare ta (wato al'ummar) daga aukawa cikin matsaloli, kuma sun kasance wayayyu madaukaka, wanda suka wofinta daga gurbatar rayuka da cutukan zuciya. Kuma da haka za su kubuta daga wutan fitintinu, da sabubban fadace-fadace da musibu. Domin haka ne, umurnin Ubangiji ga BayinSa ya zo akan lamarin kyautatawa cikin dukkan motsawansu, da yin rayuwa tare da shi, cikin mu'amalolinsu.
Allah Ta'alah ya ce: "Ka tunkude cuta da abinda yake mafi kyawu, sai wanda akwai kiyayya a tsakaninka da tsakaninsa ya kasance kamar Majibinci ne masoyi" [Fussilat: 34]. 
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ka fada wa Bayina su rika fadar kalma wadda take mafi kyau, lallai ne Shedan yana rura gaba a tsakaninsu" [Isra'i: 53].

Ya ku taron Musulmai...
Lamarin kyautatawa ta hanyar bada kyautayi da baza hannu, lamarinsa yana kara karfi ga hakkin ma'abuta matsayi da mukamai, da dukiyoyi da wadaci, Sai ka yi kwadayin aiki da wannan Ya wanda Allah ya kyautata maka, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ka kyautata, kamar yadda Allah ya kyautata maka" [Kasas: 77].
Ibnu-Kayyim –رحمه الله- ya ce: "Ba a janyo ni'imomin Allah, kuma a tunkude azabobinsa, da abinda yafi yin da'a a gare shi, da kyautatawa halittunSa".

'Yan uwa a cikin imani ...
Kyautatawar da shari'a ta kwadaitar akansa yana kunsar  dukkan amfani da kowane nau'i, ga kowane halitta, Mutum ne ko dabba, saidai ladansa yana banbanta, kuma falalarsa tana kara girma, gwargwadon wadanda aka gabatar da kyautatawar a gare su, da girman hakkinsu da matsayinsu, kuma mafi kololuwan wanda ya wajaba a kyautata musu sune iyaye biyu, sa'annan sai makusanta, sa'annan sai sauran halitta.
Kalmar ihsani (wato kyautatawa) tana dauke da ma'ana mai kyau, wanda take hukunta maka -Ya kai Musulmi- ka mu'amalanci waninka da dukkan aiki kyakkyawa, da kuma dadadan maganganu.
Kuma daga cikin kyautatawa akwai, kyautar da zaka gabatar, da dukiyar da zaka bayar, da wani amfanin da zaka gabatar, da kalma daddada, da lafazi mai kyau, tare da haduwa mai kyau, cikin walwala da sakin fiska, da kuma yin sallama.
An tambayi Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) wane lamarin Musulunci yafi alkhairi? Sai ya ce: "Ka ciyar da abinci, ka karanta sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma ya inganta daga gare shi (صلى الله عليه وسلم) lallai ya ce: "Murmushinka a fiskar dan'uwanka sadaka ne a gare ka".
Kyautatawa bayarwa ne wanda baya yankewa, da fadada karbar bakunci, ko agazawa na gaskiya, ko taimako a lokacin bukata.
Ya zo cikin littafin Sahihul Jami'i, daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Mutumin da Allah yafi so, shine wanda yafi amfanar da Mutane, kuma mafi soyuwan ayyuka a wurin Allah Mabuwayi da daukaka shine, farin cikin da ka sanya ga Musulmi, ko ka yaye masa wani bakin ciki, ko ka biya masa wani bashi, ko ka kore masa wata yunwa, Kuma nayi tafiya da 'Dan'uwana cikin wata bukata, lallai shine yafi soyuwa a gare ni fiye da nayi ibadar i'itikafi a wannan Masallacin -yana nufin Masallacin Madina- na tsawon wata guda", har karshen hadisin.
Kuma Muslim ya ruwaito cewa, Lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya kwaranye wani bakin cikin daga ababen bakin cikin Duniya ga wani Mumini, Allah zai kwaranye masa baki ciki daga bakin Lahira, Kuma wanda ya saukaka wa Mutumin da yake cikin kunci, Allah zai saukaka masa a Duniya da Lahira, Wanda ya suturce Musulmi, Allah zai suturce shi a Duniya da Lahira, Allah yana cikin taimakon Bawa matukar Bawan yana taimakon 'Dan'uwansa".

Ya ku Bayin Allah! ...
Kyautatawa shine shigar da farin ciki ga Musulmi, da bayar da mai kyau, da baiko ga wanda bashi da shi, da taimakon wanda aka zalunta, da tsamar da Mutum daga bakin ciki, da taimakon wanda ya fada bala'i, da ziyartar maras lafiya, da ciyar da mai jin yunwa, da sauran dukkan ababen da za su sanya Mutane cikin farin ciki, da walwala da jin dadi.
Allah Ta'alah ya ce: "Kuma suna ciyar da abinci, akan sonsa ga Matalauci da Maraya da Bawa * (Suna cewa:) Muna ciyar da ku ne, domin Allah, bamu nufin wani sakamako daga wurinku, kuma bamu nufin godiya" [Insan: 8].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Kuma suna fifita wdansu akan kawunansu, koda a tare da su akwai lalura (talauci)" [Hashr: 9].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Mai tafiya cikin lamarin bazaura da miskini, kamar mai jihadi ne domin daukaka kalmar Allah, ko kuma kamar mai tsayuwan dare, mai azumin yini", Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Kuma hakika naga wani Mutum yana jujjuyawa a gidan Aljannah, sakamakon wata bishiyar da ya yanke daga kan hanya, ta kasance tana cutar da Mutane", Muslim ya ruwaito shi.

Sai ku kyautata, domin Allah ya kyautata muku, kuma ya ninninka sakamakonsa a gare ku, "Wadanda suka kyautata, suna da abu mai kyawu, da kuma kari" [Yunus: 26].

Ina fadar abinda kuke ji, kuma ina neman gafarar Allah; sai ku nemi gafararSa, lallai ne shi ya kasance ga masu  komawa gare shi, Mai yawan gafara.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,


HUDUBA TA BIYU
        Bayan haka
Ya ku Musulmai
Lamarin kyautatawa a Musulunci, baya takaituwa kawai ga Mutane, a'a lamarin a kyautata yana game wadanda basu magana; na dabbobi, saboda Annabi (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Wata rana Wani Mutum yana tafiya akan wata hanya, kishin ruwa ya tsananta a gare shi, sai ya samu wata rijiya, sai ya shiga cikinta ya sha ruwa, sa'annan ya fita, sai ga wani kare yana lallagi yana cin kasa saboda kishi, Sai Mutumin ya ce: Lallai wannan karen kishi ya tsananta a gare shi, kwatankwacin yadda ya tsananta a gare ni! Sai ya shiga rijiyar, ya ciko huffinsa da ruwa, sa'annan ya rike shi da bakinsa, sai ya shayar da karen, Sai Allah ya gode masa, kuma ya gafarta masa, Sai suka ce:  Ya Ma'aikin Allah! Shin muna da wani lada akan dabbobi? Sai ya ce: Lallai cikin dukkan abu mai rai akwai lada", Bukhariy da Muslim suka ruwaito.
Sai ku yi salati da sallama ga

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...