HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 28/RABIYYUS SANIY/1440H
daidai da 4/JANAIRU/ 2019M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ALIYU BN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
RAYUWAR DUNIYA
(عمر الإنسان)
Shehin Malami wato: Aliyu
bn Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: RAYUWAN DAN ADAM, Wanda kuma a cikinta ya
tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah; Mabuwayi
Mai yawan gafara, Yana shigar da dare akan yini, kuma yana shigar da yini akan dare,
kuma kowane abu a wurinSa yana da wani gwargwado. Ina yin yabo ga Ubangijina
kuma ina gode masa akan ni'imominSa da falalolinSa.
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya, sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, Makadaici
Mai rinjaye.
kuma ina shaidawa lallai
annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne ManzonSa zababbe,
Ya Allah! ka yi dadin
salati, da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka; Muhammadu, da iyalansa
da sahabbansa zababbu,
Bayan haka:
Sai ku yi
takawar Allah Madaukaki kuma ku masa biyayya, domin yin da'a a gare shi, shine
hanya mafi mikewa kuma mafi karfi, kuma ku rika guzuri ga lahirarku, domin mafi
alherin guzuri shine tsoron Allah!
Ya ku, Bayin Allah
!!!
Ku rika
tunani kan lokaci dan kadan wanda aka dibar ma Duniya, da kayan kawanta
wulakantacce, da yadda halayenta suke yawan jujjuyawa, sai ku gane ko ku riski
matsayin Duniyar, kuma ku san sirrinta, domin duk wanda ya amintu da ita, to
lallai shi rudadde ne, kuma wanda ya amintu da ita, to lallai shi halakakke ne.
Kuma
karancin shekarun da aka dibar wa Duniya ya ta'allaka ne da karancin shekarun
da aka diba wa Mutum a cikinta.
Kuma
rayuwar Mutum tana farawa ne da awanni, bayan awowi kuma sai kwanaki, bayan
kwanaki kuma sai watanni, bayan watanni kuma sai shekara, bayan shekara daya
kuma sai shekaru, Sa'annan sai rayuwar Mutum gaba daya ta kare. Kuma Mutum baya
sanin abinda zai gudana a bayan mutuwarsa na manya-manyan lamura. Kuma shin
rayuwar wanda su ka zo a bayanka -Ya kai Mutum- rayuwarka ce?
Kuma
rayuwar kowace halitta, bangare ne na rayuwar al'umma gaba daya.
Kuma ita
Duniya dan mata'i ne, kuma ma'anan mata'i shine dan abinda ake jin dadi da shi,
a lokacinsa, sa'annan sai ya kare a wannan lokacin, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma lallai wannan rayuwar
dan jin dadi ne, kuma lallai Lahira ita ce gidan tabbata"
[Gafir : 39].
Kuma
Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ka buga musu mislain rayuwar Duniya,kamar
Ruwa ne wanda muka saukar da shi daga sama, sa'annan tsirin kasa ya gauraya da
shi, sa'annan ya wayi gari yana duddugagge, iska tana shikarsa, Kuma Allah ya
kasance Mai yawan ikon yi ne akan dukkan komai"
[Kahf: 45].
Kuma
Allah Subhanahu ya ce: "Kuma, ka bada labari, idan muka jiyar da su dadi a
shekaru! * Sa'annan abinda suka kasance ana musu wa'adi ya je musu * abinda
suka kasance ana jiyar da su dadin, ba zai tunkude azaba daga gare su ba!"
[Shu'ara'i: 205-207].
Kuma
Ubangijinmu Mabuwayi da daukaka ya bamu labari, kan gajartan zaman Mutane a
cikin kabarinsu har zuwa lokacin da za a tayar da su domin hisabi, da cewa
wannan lokaci mai tsawo kamar wani dan yanki lokaci ne takaitacce, Allah
Ta'alah ya ce: "Kuma ranar da zai tara su, kamar ba su zauna ba face sa'a guda daga
yini, wanda suke sanayya da juna a cikinsa" [Yunus: 45].
Kuma
Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ka yi hakuri, kamar yadda karfafan niyya daga
Manzanni suka yi hakuri, kuma kada ka yi musu gaggawa, Kamar dai su a ranar da
suke ganin sakamakon abinda aka musu wa'adinsa, ba su zauna ba, face sa'a guda
daga yini, isarwa (dai da Manzanci), Kuma babu wanda za a halakar face Mutane
fasikai" [Ahkaf: 35].
Kuma
Allah Ta'alah ya ce: "Kuma a ranar da sa'a ke tsayuwa, masu laifi na
rantsuwa, ba su zauna (a cikin kabari) ba face sa'a guda"
[Rum: 55].
Don
haka, nawa ne shekarunka -Ya kai wannan Mutum-, daga cikin wannan sa'ar wanda
Allah Ta'alah ya bamu labarin cewa, shine dan lokacin da aka dibar wa Duniya, a
lokacin da kiyama zata tsayu!
Kuma
ita wannan sa'ar wanda ita ce lokacin da aka dibar wa Duniya, kamar wani
bantare ne (karami) ko digo daya na ruwa daga tekun zamani na har abada!
Don
haka,
Abin
yabo, yana tabbata ga wanda ya yi aikin kwarai a cikin rayuwarsa takaitacciya,
kuma ya kaurace wa ayyukan haram, kuma ya kiyayi bin soye-soyen zuciya, da
hanyoyin zamiya da bacewa, sai ya rabauta a cikin rayuwarsa da aikata
alkhairori, kuma ya rabautu bayan mutuwarsa da samun yardar Allah a
cikin ni'imomin Aljannah!
Kuma
bone ya tabbata, ga wanda ya bi ye wa sha'awowinsa, kuma ya tozarta salloli da
ayyukan wajibai, kuma ya yi ta aukawa cikin zunubai masu halakarwa, har ya fada
cikin ramukan Jahannama, sai abincinsa ya kasance itaciyar zakkum (na danyen
wuta), abin shansa kuma ya kasance surkin jini (wato, diwa) da tafasasshen ruwa
(ruwan zafi),
Ya
wanda lafiyarsa ta sanya shi dagawa, sai ya rika aikata sabo!
Ya
wanda faragar lokacinsa ya lalata shi sai ya yi ta wasa da wargi!!
Ya
wanda dukiyarsa ta fitine shi, sai ya gangara cikin wuta!!!
Ya
wanda ya biye wa son zuciyarsa sai ya tuntsura kuma ya fadi!!!!
Ya
wanda samartakarsa ta rude shi, sai ya mance da tsufa!!!!!
Ya
wanda ya yi amfani da ni'imomin da Allah ya masa sai yake taurin kai da
dagawa!!!!!!
Shin ba
ka san cewa, Allah babu wani abu a cikin sama da kuma a cikin kasa wanda yake
gagaransa ba? kuma lallai shi, Mai tsananin ukuba ne!
Shin
baka da yakini kan mutuwa ne, da abinda yake bayanta na hisabi!
Ya
wanda nisan ajali ya sanya shi tsaurin kai ga UbangijinSa! Haka batun samun burinsa!
Har mutuwa ta fizge shi! Ta yaya irin wannan zai samu damar komawa Duniya domin
ya gyara aiki!!
Shin
lokaci, bai yi ba, Ya kai gafalalle, mai bijirewa, mai sabo, wanda a cikinsa
zaka tuba ga Ubangijinka ka kuma mayar da lamari zuwa gare shi!
Shin
lokacin da zaka farka daga irin wannan kurmar gafala, bai yi ba! Sai ka amsa wa
Ubangijinka!!
Shin
baka da abin lura, cikin lamarin karnuka masu karfi wadanda suka shude, da
wuraren zamansu wofantattu, bayan sun daddasa nau'oin bishiyoyi, sun gudanar da
koramai, sun gina biranai! Yaya suka kasance bayan gini sai dai alama, kuma
bayan daukaka sai labari!!! Kuma yaya aka dauke su daga benaye zuwa
kaburbura! Sai suka wayi gari suna jingine da ayyukansu, Sai ma'abuta kyawawan
ayyuka suka zama sune masu samun babban rabo, ma'abuta munana kuma, sune masu
yin hasara da nadama!
Shin
mutuwa, akwai mai tunkude ta?
Shin
akwai mai shiryatarwa, in banda Alkur'ani?
Lallai
cikin fiskantowar yini da shekara, da juyawan wani yinin da shekara, akwai abin
dubawa, saboda duk yinin da ka bar shi bayanka, to ba zai dawo ba, kuma wani
yinin kake fiskanta, har ajali ya kare, buri kuma ya yanke! Allah Ta'alah ya
ce: "Kuma Mutum bashi da komai face abinda ya aikata * Kuma lallai
aikinsa za a ganshi * Sa'annan a saka masa da sakamako mafi cikar ma'auni *
Kuma lallai, makoma izuwa ga Ubangijinka kawai take!"
[Najm: 39-42].
Sai ka
yi aiki domin gidan dawwama, wanda ni'imarta baya karewa, kuma baya raguwa, sai
ma karuwa! Samarin wannan gida tsufa bata zuwa musu, kuma basu tsoron cutuka,
Allah Ta'alah yana fada akanta: "Ku shige ta da aminci, waccan ita ce ranar dawwama
* suna da abinda suke so a cikinta, kuma tare da mu akwai karin ni'ima"
[Kaf: 34].
Kuma
Allah Ta'alah ya ce: "Ku shiga Aljannah ku da matan aurenku ana girmama
ku * Ana kewayawa akansu da akussa na zinariya da kofuna, alhali kuwa a cikinsu
akwai abinda rayuka suke marmari, kuma idanu su ji dadi, kuma ku a cikin
Aljannar madawwama ne * Kuma waccar ita ce Aljannar, wannan da aka gadar da ku
ita, saboda abinda kuka kasance kuna aikatawa * Kuna samun kayan marmari masu
yawa a cikinta, daga cikinsu kuke ci" [Zukhruf: 70-73].
Kuma ku
ji tsoron Wutar da ba a sassauta azaba ga ma'abutanta, ta hanyar aiki da
umurnin Allah mai karfi, da nisantar fushinsa mai tsanani, Allah Ta'alah ya ce:
"Kuma wadanda suka kafirta an yanka musu wadansu tufafi daga wata
irin wuta, ana zuba tafasasshen ruwa daga saman kawunansu * Da shi ake narkar
da abinda yake a cikin cikunansu, da fatun jikinsu * Kuma suna da wadansu gudumomin
duka na bakin karfe * A duk lokacin da suka yi nufin fita daga gare ta, saboda
bakin ciki, sai a mayar da su a cikinta, (a ce musu): Ku dandani azabar gobara"
[Haj: 19-22].
Sai ku
yi aiki -Ya ku bayin Allah- domin wannan Aljannar madaukakiya! Kuma ku nisanci
zunubai, wadanda suke wurga ma'abutansu cikin Wutar Hawiya mai zafi.
Kuma ku
sani, lallai babu komai tsakanin Mutum da shiga Aljannah ko Wuta, face mutuwa,
An rawaito daga Abu-hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi-, daga Annabi
-sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Ku
rigayi abubuwa bakwai da ayyuka, Shin wani abu kuke jira face, Talauci me
mantarwa, da wadaci mai sanya dagawa, ko cuta mai lalatawa, ko tsufa
mai kararwa, ko mutuwa mai daukewa, ko zuwa Dujjal, mafi sharrin wanda ake
jira, ko kuma zuwan kiyama, kuma zuwan sa'arta shine yafi tsananin masifa, kuma
mafi daci", Tirmiziy ya ruwaito.
Kuma ya
zo cikin wani hadisi cewa: "Ku yawaita ambaton mai
yanke jin dadi, wato mutuwa, domin ba a ambaton mutuwa ga abu mai yawa face ta
karanta shi, ko kuma ga kadan face ta yawaita shi".
Kuma
Annabi -sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Ya isa
mutuwa ta zama babban mai wa'azi ".
-Ya kai
Musulmi- Sai ka yi bankwana da ranakunka, da abinda ka samu ikon kunshe shi a
cikinsu na kyawawan ayyuka, kuma ka kiyaye takardun rubuta ayyukanka daga
munanan ayyuka, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ku gabatar da alheri
saboda kanku, kuma ku bi Allah da takawa, kuma ku sani cewa lallai ne ku masu
haduwa ne da shi, kuma ka bayar da bushara ga muminai"
[Bakara: 223].
Kuma ya
ce: "Kuma ku tsayar da sallah, ku bada zakkah, kuma duk abinda kuka
gabatar da shi ga kawunanku na alheri za ku same shi a wurin Allah, yana
mafifici, kuma zai fi girma ga sakamako" [Muzzammil: 20].
Allah
ya mini albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma, ,,,.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA
BIYU
Yabo ya
tabbata ga Allah wanda ya san sirri da abinda yafi buya, tsayayye akan kowace
rai da abinda ta aikata, yana kididdige ayyuka, kuma yana yin sakamako akansu
da mafi cikan ma'auni,
Ina yin
yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa, kuma ina tuba zuwa gare shi ina neman
gafararSa,
Kuma
ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, yana da sunaye mafiya
kyawu.
Kuma
ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa
zababbe,
Allah
ka yi dadin salati a gare shi da iyalansa da sahabbansa ma'abuta hakuri da
takawa,
Bayan haka
Ku ji
tsoron Allah iyakar takawarsa, kuma ku yi riko a Musulunci da igiya mai karfi,
Ya ku Bayin Allah
Lallai
Allah ya bude muku kofofin rahama, da abinda ya shar'anta muku na aikata
alkhairori, da nisantar laifuka ababen kyama,
Don
haka, kada wani Mutum ya toshe kofar rahama ga kansa, ta hanyar yakar Allah da
aikata zunubai, Saboda ALlah Ta'alah yana cewa: "Kuma rahamata ta yalwace
dukkan komai, sa'annan zan rubuta ta ga wadanda suke yin takawa, kuma suna
bayar da zakka, da wadanda suke a game da ayoyinmu muminai ne"
[A'araf: 156].
-Ya kai
wannan Bawa- ka ribaci zamanin lafiya (gabanin zuwan cuta), saboda an rawaito
daga Abdullahi dan Abbas -Allah ya kara yarda a gare su- ya ce: "Ni'imomi
biyu mafi yawan Mutane basu ribatarsu; lafiya da faragar lokaci".
Kuma an
ruwaito daga Abdullahi dan Umar -رضي الله عنهما- ya ce: Manzon
Allah -صلى
الله عليه وسلم- yana cewa: "Ka
kasance a Duniya kamar wani bako, ko kuma mai ketare hanya,,,,".
Ya ku
Musulmai
"Lallai ne Allah da
Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan Annabi, ,,,"
[Ahzab: 56].
No comments:
Post a Comment