2019/01/04

28 Rabiyus Saniy 1440












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 28/RABIYYUS SANIY/1440H
daidai da 4/JANAIRU/ 2019M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ALIYU BN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
RAYUWAR DUNIYA
(عمر الإنسان)
Shehin Malami wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: RAYUWAN DAN ADAM, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO

Yabo ya tabbata ga Allah; Mabuwayi Mai yawan gafara, Yana shigar da dare akan yini, kuma yana shigar da yini akan dare, kuma kowane abu a wurinSa yana da wani gwargwado. Ina yin yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa akan ni'imominSa da falalolinSa.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, Makadaici Mai rinjaye.
kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne ManzonSa zababbe,
Ya Allah! ka yi dadin salati, da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka; Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa zababbu,

Bayan haka:
Sai ku yi takawar Allah Madaukaki kuma ku masa biyayya, domin yin da'a a gare shi, shine hanya mafi mikewa kuma mafi karfi, kuma ku rika guzuri ga lahirarku, domin mafi alherin guzuri shine tsoron Allah!

Ya ku, Bayin Allah !!!
Ku rika tunani kan lokaci dan kadan wanda aka dibar ma Duniya, da kayan kawanta wulakantacce, da yadda halayenta suke yawan jujjuyawa, sai ku gane ko ku riski matsayin Duniyar, kuma ku san sirrinta, domin duk wanda ya amintu da ita, to lallai shi rudadde ne, kuma wanda ya amintu da ita, to lallai shi halakakke ne.
Kuma karancin shekarun da aka dibar wa Duniya ya ta'allaka ne da karancin shekarun da aka diba wa Mutum a cikinta.
Kuma rayuwar Mutum tana farawa ne da awanni, bayan awowi kuma sai kwanaki, bayan kwanaki kuma sai watanni, bayan watanni kuma sai shekara, bayan shekara daya kuma sai shekaru, Sa'annan sai rayuwar Mutum gaba daya ta kare. Kuma Mutum baya sanin abinda zai gudana a bayan mutuwarsa na manya-manyan lamura. Kuma shin rayuwar wanda su ka zo a bayanka -Ya kai Mutum- rayuwarka ce?
Kuma rayuwar kowace halitta, bangare ne na rayuwar al'umma gaba daya.
Kuma ita Duniya dan mata'i ne, kuma ma'anan mata'i shine dan abinda ake jin dadi da shi, a lokacinsa, sa'annan sai ya kare a wannan lokacin, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma lallai wannan rayuwar dan jin dadi ne, kuma lallai Lahira ita ce gidan tabbata" [Gafir : 39].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ka buga musu mislain rayuwar Duniya,kamar Ruwa ne wanda muka saukar da shi daga sama, sa'annan tsirin kasa ya gauraya da shi, sa'annan ya wayi gari yana duddugagge, iska tana shikarsa, Kuma Allah ya kasance Mai yawan ikon yi ne akan dukkan komai" [Kahf: 45].
Kuma Allah Subhanahu ya ce:  "Kuma, ka bada labari, idan muka jiyar da su dadi a shekaru! * Sa'annan abinda suka kasance ana musu wa'adi ya je musu * abinda suka kasance ana jiyar da su dadin, ba zai tunkude azaba daga gare su ba!" [Shu'ara'i: 205-207].
Kuma Ubangijinmu Mabuwayi da daukaka ya bamu labari, kan gajartan zaman Mutane a cikin kabarinsu har zuwa lokacin da za a tayar da su domin hisabi, da cewa wannan lokaci mai tsawo kamar wani dan yanki lokaci ne takaitacce, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ranar da zai tara su, kamar ba su zauna ba face sa'a guda daga yini, wanda suke sanayya da juna a cikinsa" [Yunus: 45].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ka yi hakuri, kamar yadda karfafan niyya daga Manzanni suka yi hakuri, kuma kada ka yi musu gaggawa, Kamar dai su a ranar da suke ganin sakamakon abinda aka musu wa'adinsa, ba su zauna ba, face sa'a guda daga yini, isarwa (dai da Manzanci), Kuma babu wanda za a halakar face Mutane fasikai" [Ahkaf: 35].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Kuma a ranar da sa'a ke tsayuwa, masu laifi na rantsuwa, ba su zauna (a cikin kabari) ba face sa'a guda" [Rum: 55].
Don haka, nawa ne shekarunka -Ya kai wannan Mutum-, daga cikin wannan sa'ar wanda Allah Ta'alah ya bamu labarin cewa, shine dan lokacin da aka dibar wa Duniya, a lokacin da kiyama zata tsayu!
Kuma ita wannan sa'ar wanda ita ce lokacin da aka dibar wa Duniya, kamar wani bantare ne (karami) ko digo daya na ruwa daga tekun zamani na har abada!

Don haka,
Abin yabo, yana tabbata ga wanda ya yi aikin kwarai a cikin rayuwarsa takaitacciya, kuma ya kaurace wa ayyukan haram, kuma ya kiyayi bin soye-soyen zuciya, da hanyoyin zamiya da bacewa, sai ya rabauta a cikin rayuwarsa da aikata alkhairori,  kuma ya rabautu bayan mutuwarsa da samun yardar Allah a cikin ni'imomin Aljannah!
Kuma bone ya tabbata, ga wanda ya bi ye wa sha'awowinsa, kuma ya tozarta salloli da ayyukan wajibai, kuma ya yi ta aukawa cikin zunubai masu halakarwa, har ya fada cikin ramukan Jahannama, sai abincinsa ya kasance itaciyar zakkum (na danyen wuta), abin shansa kuma ya kasance surkin jini (wato, diwa) da tafasasshen ruwa (ruwan zafi),
Ya wanda lafiyarsa ta sanya shi dagawa, sai ya rika aikata sabo!
Ya wanda faragar lokacinsa ya lalata shi sai ya yi ta wasa da wargi!!
Ya wanda dukiyarsa ta fitine shi, sai ya gangara cikin wuta!!!
Ya wanda ya biye wa son zuciyarsa sai ya tuntsura kuma ya fadi!!!!
Ya wanda samartakarsa ta rude shi, sai ya mance da tsufa!!!!!
Ya wanda ya yi amfani da ni'imomin da Allah ya masa sai yake taurin kai da dagawa!!!!!!
Shin ba ka san cewa, Allah babu wani abu a cikin sama da kuma a cikin kasa wanda yake gagaransa ba? kuma lallai shi, Mai tsananin ukuba ne!
Shin baka da yakini kan mutuwa ne, da abinda yake bayanta na hisabi!
Ya wanda nisan ajali ya sanya shi tsaurin kai ga UbangijinSa! Haka batun samun burinsa! Har mutuwa ta fizge shi! Ta yaya irin wannan zai samu damar komawa Duniya domin ya gyara aiki!!
Shin lokaci, bai yi ba, Ya kai gafalalle, mai bijirewa, mai sabo, wanda a cikinsa zaka tuba ga Ubangijinka ka kuma mayar da lamari zuwa gare shi!
Shin lokacin da zaka farka daga irin wannan kurmar gafala, bai yi ba! Sai ka amsa wa Ubangijinka!!
Shin baka da abin lura, cikin lamarin karnuka masu karfi wadanda suka shude, da wuraren zamansu wofantattu, bayan sun daddasa nau'oin bishiyoyi, sun gudanar da koramai, sun gina biranai! Yaya suka kasance bayan gini sai dai alama, kuma bayan daukaka sai labari!!!  Kuma yaya aka dauke su daga benaye zuwa kaburbura! Sai suka wayi gari suna jingine da ayyukansu, Sai ma'abuta kyawawan ayyuka suka zama sune masu samun babban rabo, ma'abuta munana kuma, sune masu yin hasara da nadama!
Shin mutuwa, akwai mai tunkude ta?
Shin akwai mai shiryatarwa, in banda Alkur'ani?
Lallai cikin fiskantowar yini da shekara, da juyawan wani yinin da shekara, akwai abin dubawa, saboda duk yinin da ka bar shi bayanka, to ba zai dawo ba, kuma wani yinin kake fiskanta, har ajali ya kare, buri kuma ya yanke! Allah Ta'alah ya ce: "Kuma Mutum bashi da komai face abinda ya aikata * Kuma lallai aikinsa za a ganshi * Sa'annan a saka masa da sakamako mafi cikar ma'auni * Kuma lallai, makoma izuwa ga Ubangijinka kawai take!" [Najm: 39-42].
Sai ka yi aiki domin gidan dawwama, wanda ni'imarta baya karewa, kuma baya raguwa, sai ma karuwa! Samarin wannan gida tsufa bata zuwa musu, kuma basu tsoron cutuka, Allah Ta'alah yana fada akanta: "Ku shige ta da aminci, waccan ita ce ranar dawwama * suna da abinda suke so a cikinta, kuma tare da mu akwai karin ni'ima" [Kaf: 34].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Ku shiga Aljannah ku da matan aurenku ana girmama ku * Ana kewayawa akansu da akussa na zinariya da kofuna, alhali kuwa a cikinsu akwai abinda rayuka suke marmari, kuma idanu su ji dadi, kuma ku a cikin Aljannar madawwama ne * Kuma waccar ita ce Aljannar, wannan da aka gadar da ku ita, saboda abinda kuka kasance kuna aikatawa * Kuna samun kayan marmari masu yawa a cikinta, daga cikinsu kuke ci" [Zukhruf: 70-73].
Kuma ku ji tsoron Wutar da ba a sassauta azaba ga ma'abutanta, ta hanyar aiki da umurnin Allah mai karfi, da nisantar fushinsa mai tsanani, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma wadanda suka kafirta an yanka musu wadansu tufafi daga wata irin wuta, ana zuba tafasasshen ruwa daga saman kawunansu * Da shi ake narkar da abinda yake a cikin cikunansu, da fatun jikinsu * Kuma suna da wadansu gudumomin duka na bakin karfe * A duk lokacin da suka yi nufin fita daga gare ta, saboda bakin ciki, sai a mayar da su a cikinta, (a ce musu): Ku dandani azabar gobara" [Haj: 19-22].
Sai ku yi aiki -Ya ku bayin Allah- domin wannan Aljannar madaukakiya! Kuma ku nisanci zunubai, wadanda suke wurga ma'abutansu cikin Wutar Hawiya mai zafi.
Kuma ku sani, lallai babu komai tsakanin Mutum da shiga Aljannah ko Wuta, face mutuwa, An rawaito daga Abu-hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi-, daga Annabi -sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Ku rigayi abubuwa bakwai da ayyuka, Shin wani abu kuke jira face, Talauci me mantarwa, da wadaci mai sanya dagawa, ko cuta mai lalatawa, ko  tsufa mai kararwa, ko mutuwa mai daukewa, ko zuwa Dujjal, mafi sharrin wanda ake jira, ko kuma zuwan kiyama, kuma zuwan sa'arta shine yafi tsananin masifa, kuma mafi daci", Tirmiziy ya ruwaito.
Kuma ya zo cikin wani hadisi cewa: "Ku yawaita ambaton mai yanke jin dadi, wato mutuwa, domin ba a ambaton mutuwa ga abu mai yawa face ta karanta shi, ko kuma ga kadan face ta yawaita shi".
Kuma Annabi -sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Ya isa mutuwa ta zama babban mai wa'azi ".
-Ya kai Musulmi- Sai ka yi bankwana da ranakunka, da abinda ka samu ikon kunshe shi a cikinsu na kyawawan ayyuka, kuma ka kiyaye takardun rubuta ayyukanka daga munanan ayyuka, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ku gabatar da alheri saboda kanku, kuma ku bi Allah da takawa, kuma ku sani cewa lallai ne ku masu haduwa ne da shi, kuma ka bayar da bushara ga muminai" [Bakara: 223].
Kuma ya ce: "Kuma ku tsayar da sallah, ku bada zakkah, kuma duk abinda kuka gabatar da shi ga kawunanku na alheri za ku same shi a wurin Allah, yana mafifici, kuma zai fi girma ga sakamako" [Muzzammil: 20].
Allah ya mini albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma, ,,,.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,
HUDUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah wanda ya san sirri da abinda yafi buya, tsayayye akan kowace rai da abinda ta aikata, yana kididdige ayyuka, kuma yana yin sakamako akansu da mafi cikan ma'auni,
Ina yin yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa, kuma ina tuba zuwa gare shi ina neman gafararSa,
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, yana da sunaye mafiya kyawu.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa zababbe,
Allah ka yi dadin salati a gare shi da iyalansa da sahabbansa ma'abuta hakuri da takawa,
Bayan haka
Ku ji tsoron Allah iyakar takawarsa, kuma ku yi riko a Musulunci da igiya mai karfi,
Ya ku Bayin Allah
Lallai Allah ya bude muku kofofin rahama, da abinda ya shar'anta muku na aikata alkhairori, da nisantar laifuka ababen kyama,
Don haka, kada wani Mutum ya toshe kofar rahama ga kansa, ta hanyar yakar Allah da aikata zunubai, Saboda ALlah Ta'alah yana cewa: "Kuma rahamata ta yalwace dukkan komai, sa'annan zan rubuta ta ga wadanda suke yin takawa, kuma suna bayar da zakka, da wadanda suke a game da ayoyinmu muminai ne" [A'araf: 156].
-Ya kai wannan Bawa- ka ribaci zamanin lafiya (gabanin zuwan cuta), saboda an rawaito daga Abdullahi dan Abbas -Allah ya kara yarda a gare su- ya ce: "Ni'imomi biyu mafi yawan Mutane basu ribatarsu; lafiya da faragar lokaci".
Kuma an ruwaito daga Abdullahi dan Umar -رضي الله عنهما- ya ce: Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- yana cewa: "Ka kasance a Duniya kamar wani bako, ko kuma mai ketare hanya,,,,".
Ya ku Musulmai
"Lallai ne Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan Annabi, ,,," [Ahzab: 56].

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...