HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 26/JUMADAL ULAH/1440H
daidai da 01/FABARAIRU/2019M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. SALAH DAN MUHAMMADU ALBUDAIR
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
NI'IMAR
SAMUN BASIRA A
CIKIN ADDINI
(نعمة البصيرة
في الدين)
Shehin
Malami wato: Salah bn Muhammadu Al-Albudair –Allah
ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken:NI'IMAR
SAMUN BASIRA A
CIKIN ADDINI, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Godiya ta tabbata ga Allah
wanda ya daga martabar ma'abuta BASIRA A CIKIN ADDINI, kuma ya sanya su
tsayayyu ga lamarin addini, masu riko da kyawawan ayyuka.
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake bashi da abokin tarayya, kuma
wanda ya yi shirka da Allah zai gamu da laifuka, kuma a dawwamar da shi a wutar
Jahannama yana wulakantacce.
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, kuma ya rabauta, wanda
Annabin ya kasance abin koyi a gare shi kuma jagora.
Ya Allah ka yi salati da
sallama a gare shi da iyalansa da sahabbansa salati mai dawwama, da aminci
wanda yake biye da aminci.
Bayan haka:
Ya ku Musulmai
Ku ji tsoron
Allah, saboda mai takawa ya rabauta, kuma mabarnaci shakiyyi ya yi asara, "Ya ku wadanda suka
yi imani ku ji tsoron Allah, iyakar tsoronsa, kuma kada ku mutu face kuna
Musulmai"
[Ali-imrana: 102].
Ya ku Musulmai
Yana cikin
jigajigan ni'imomi, da gwalagwalan baiwawwaki, NI'IMAR SAMUN BASIRA A CIKIN
ADDINI,
Kuma BASIRAH
Ita ce Tauhidi da yin watsi da shirka, da kuma barin da'a ga kowace halitta
cikin saba wa Allah Ta'alah.
Kuma BASIRAH
Ita ce, Hujja, da samun yakini da tabbatuwa a cikin addini, Allah Ta'alah
yana cewa: "Ka ce: Wannan ce
hanyata, ina kira zuwa ga Allah akan basira, ni da wadanda suka bi ni, kuma
tsarki ya tabbata ga Allah, ni ban kasance daga masu shirka ba" [Yusuf: 108].
Kuma BASIRAH Ita ce:
Wayo (hankali).
Ana cewa:
KUMA HASKEN IDANU YANA
DUSASHEWA, ALHALIN RA'AYI YANA DA TSANANIN HASKE.
KumaBASIRAH haske ne
wanda Allah yake jefa shi a cikin zuciya, sai Mutum ya rika banbance gaskiya da
barna da basirarsa, da kuma alheri da sharri, da halin kirki da na banza.
Ya ku Musulmai
MAKANCEWAR BASIRAH yafi tsananin muni da
girmar musiba, fiye da MAKANTAR GANI, saboda makancewar basira shine
makanta ta hakika. Allah Mabuwayi da daukakaya ce:"Shin ba za su yi
tafiya a cikin kasa ba, domin samun zukatan da za su rika hankalta da su, ko
kunnuwan da za su yi saurare da su, domin idanun ba su makanta, amma zukata
wadanda suke a cikin kiraza suke makanta" [Haj: 46].
KANA GANIN DUBBAN MASU IDO
BABU SHIRIYA
KAI KA CE, A SAMAN IDANUNSU
AKWAI SHAMAKI
Makaho na hakika ba shine
Mutumin da baya gani da idanunsa biyu ba, saidai makaho, shine wanda ya jahilci
hakkin Allah akansa,
Babban Malami a cikin
al'ummar Musulmai; wato Abdullahi dan Abbas –رضي الله عنهما-
ganinsa ya tafi, a karshen rayuwarsa, Sai ya yi wannan wakar:
IDAN ALLAH YA DAUKE HASKEN
IDANUNA GUDA BIYU
TO, A CIKIN HARSHENA DA
ZUCIYATA, AKWAI HASKE
ZUCIYATA MAI KWAZO CE,
HANKALINA KUMA LAFIYA YAKE
A BAKINA KUMA, AKWAI TAKOBI
(HARSHE) MAI YANKA, MAI HADISI
BASIRAH Ita ce, Alkur'ani da
sunnah, Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Hakika basirori sun zo muku daga
Ubangijinku, kuma wanda ya yi basira to ya yi wa kansa, wanda kuma ya makance
to ya makance wa kansa" [An'am: 104].
Ma'ana: Hakika dalilai da hujjoji sun je muku
wadanda Alkur'ani ya kunsa, da wadanda sunnar Annabi -صلى الله عليه وسلم- ta kunsa,
kuma sune hasken da suke cikin zukatanku, mai matsayin hasken da idanunku suke
gani, sai ku samu daukaka da basirorin Alkur'ani da sunnah, kuma kada ku
gangara cikin ramukan zato da zunubai.
Kuma ta yaya za ku auka cikin daudar sabo, alhalin
a tare da ku akwai cikakken haske na zahiri mai ban kaye, wanda shine littafin
Allah da sunnar Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم-,
Sai ku nemi mafi daukakar haske daga cikinsu, a
lamarin duffai kuma kada ku raina mafi karancinsu!
An ruwaito daga Abdullahi dan Amru dan Ass -رضي الله عنهما- lallai
wannan ayar da take cikin Alkur'ani, wato: "Ya wannan Annabin,
lallai ne mun turo ka, mai shaida, kuma mai albishir, kuma mai gargadi" [Ahzab: 45].
A cikin Attaurah kuma, "Ya kai wannan Annabin,
lallai ne mun turo ka, mai shaida, kuma mai albishir, kuma mai gargadi, kuma
garkuwa ga Larabawa, Kai Bawana ne kuma manzona, na sanya maka suna Mai
tawakkali (dogaro ga Allah). kuma shi ba mai mummunan hali, da kaushin harshe,
kuma ba mai shewa a kasuwa ba ne, kuma baya tunkude mummuna da mummuna, sai dai
ya kan yi afuwa ya yafe. Kuma Allah ba zai karbi rayuwarsa ba, face ya mikar da
karkataccen addini da shi, ta hanyar su ce, LA ILAHA ILLAL LAHU; sai ya bude
idanu makafi da wannan kalmar, da kunnuwa masu kurumci, da zukata rufaffu", Bukariy ya ruwaito shi.
Ma'ana sai ya bude da kalmar tauhidi (ta LA ILAHA
ILLAL LAHU) idanu makafi dagaganin gaskiya, ba makantar idanu ba, sai ya
kore shirka kuma ya tabbatar da tauhidi. Ita kuma "الملة العوجاءkarkataccen addini" shi ne addinin kafirci.
Kuma abinda ake nufi da tsayarwa da ita kalmar, shine ya fitar da ma'abutanta
daga kafirci zuwa imani.
Wanda ya ji wa'azozin Allah, da ayoyin littafinSa,
da hadisan AnnabinSa -صلى
الله عليه وسلم- sai ya kurumtar da
kunnuwansa daga gaskiya, ya kuma rufe idonunsa biyu da abin rufewan barna, to
wannan shine hakikanin makaho dimautacce a cikin duffan jahilci da bata,
Ma'abuta kafirci da fasikci da bata,
kurame ne ga barin gaskiya; basu jinta, makafi ne ga barin shiriya; basu
ganinta, saboda basu ji irin jin wanda ke amfana, kuma basu gani irin na mai
shiryatuwa, Allah Ta'alah ya ce: "Ba su kasance suna iya ji ba, kuma ba su
kasance suna gani ba" [Hud: 20].
Kuma Ubangijinmu Mabuwayi
da daukaka yake fada akansu, a sha'anin lahira da kiyama: "A'a, Lallai sun kasance
cikin shakka ne a lamarinta, a'a, sun dangane da ita makafi ne" [Naml: 66].
Amma Muminai to su kam
wayayyu ne ma'abuta basira, kuma mumini shine mai ingantaccen nazari, mai
karfin basira, mai kyakkyawan gurbi da aiki. Allah Mabuwayi da daukaka ya
fada: "Kuma
makaho ba zai yi daidai da mai gani ba *** da kuma duffai da haske" [Fadir: 19-20].
"Makaho ba zai yi daidai" wato wanda
ya makance daga addinin Allah, da ya turo AnnabinSa Muhammadu -صلى الله عليه وسلم- da shi ba, Ba zai yi daidai "da mai gani ba" wato, wanda ya ga
shiriyarsa a cikin addinin, sai ya bi annabi Muhammadu ya gaskata shi, kuma ya
karbi abinda Allah ya turo annabin da shi.
Abdullahi dan Abbas -رضي الله عنهما- ya ce: Ayar "Makaho baya zama
daidai..." har karshenta: Misali ne da Allah ya buga shi,
akan lamarin ma'abuta da'arsa da ma'abuta saba masa.
Ana cewa:
Kowane Mutum yana da
idanu guda hudu, Guda biyu sune a jikin kayinsa, domin sanin duniyarsa, Da kuma
idanu biyu a cikin zuciyarsa domin lahirarsa, idan idanun kayinsa suka makance,
sai idanun zuciyarsa suka zauna da basira, to makancewar idanunsa ba zai cutar
da shi komai ba. Idan kuma idanunsa kayinsa suka kasance suna gani, amma sai
idanun zuciyarsa suka makance, to lallai ganin idanunsa ba zai amfanar da shi
da komai ba.
Kuma meye amfanin ji da
gani, idan Mutum ba ya iya jin gaskiya da kunnuwansa, baya ganin shiriya da
idanunsa biyu!
Meye amfanin ido a wurin
Mutum
Idan haske da duhu suka
daidaita a wurinsa!
Allah ya sanya ni da ku,
daga cikin wadanda suke ganin gaskiya da zukatansu, sai ta zama jagora a
rayuwarsu, kuma haske a gare su, a cikin kabarinsu.
Ina fadan abinda kuke ji,
kuma ina gafarar Allah, sai ku nemi gafararSa, lallai shi ya kasance ga masu
komawa gare shi, Mai yawan gafara ne.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA BIYU
Godiya ta tabbata ga Allah wanda a cikin
tausasawarSa yake bada mafaka ga mai neman mafakarsa,
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da
gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, wanda cikin ni'imarSa
yake bada waraka ga wanda ya debe tsammanin waraka daga cutukansa,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma
shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonSa, wanda ya bi shi ya samu shiriya,
wanda kuma ya saba masa ya bace hanya,
Allah ka yi dadin salati a gare shi da
iyalansa da sahabbansa, salatin da ke wanzuwa, da sallama mai ninkuwa.
Ya ku Musulmai
Yana daga sifofin Ma'abuta imani,
kasancewarsu masu fadakakken zukata, masu hankali mai fahimta, suna kiyaye wa
Allah umurninSa da haninSa, da alwalinSa da narkonSa, Idan aka karanta musu
ayoyinsa, sai su karkata gare su, suna masu ji, masu kiyayewa, masu kula, da
kunnuwan da suke jin ayoyin, da kuma zukatan da suke kiyaye su, ba su gafala
daga wa'azinsa, kuma ba su girman kai kan ibadarSa, kamar yadda yasassun Mutane
suke yi, masu nuna girman kai, kurame wadanda ba su jin
gaskiya, makafi wadanda ba su ganin gaskiya, Ubangijinmu ya ce: "Sune wadanda idan aka tunatar da su
ayoyin Ubangijinsu, basu faduwa akansu kuramai, makafi" [Furkan: ].
Alhasan Albasariy ya ce: "Sau nawa, Mutum
yake karanta aya, sai kuma ya fadi akanta kurma kuma makaho".
Ya ku Musulmai
Lallai samun girma da daukaka, da matsayi da fifiko
da mukami yana nan, cikin SAMUN BASIRA A CIKIN ADDINI
Ya Allah ka sanya mu daga cikin ma'abuta basira a
cikin addini, masu yin sujjada domin kai, masu yin tasbihi da gode maka, masu
kankan da kai ga umurninka, masu girmama shari'arka! Ya Ubangijin Talikai
Sai ku yi salati da sallama ga Ahmad, Mai
shiryatarwa, mai ceton Mutane gaba daya
Domin idan Mutum ya masa salati guda daya, Allah Ta'alah zai masa guda
goma da shi
Ya Allah! Ka yi salati
da sallama ga bawanka kuma manzonka Muhammadu,
Kuma –Ya Allah- ka
yarda da iyalansa da sahabbai, ka hada da mu tare da su, Ya Mai karimci ya Mai
baiwa!
Ya Allah! Ka daukaka
Musulunci da Musulmai, kuma ka kaskantar da shirka da mushirkai, ka ruguza
makiya addini,
Kuma ka game kasashen Musulmai da aminci da wadaci, kuma ka kiyaye kasar
harami biyu madaukaka, daga kaidin masu kaidi, da makircin masu masu makirci,
da hassadar masu hassada, da kyashin masu kyashi, Ya Ubangijin Talikai!
Ya Allah ka datar da
shugabanmu majibincin lamarinmu mai hidimar harami biyu ga abinda kake so, ka
yarda da shi, kuma ka rike makyamkyamarsa da ayyukan da'a da takawa. Ya Allah
ka datar da shi da na'ibinsa ga abinda akwai daukakar Musulunci a cikinsa, Ya
Ubangijin talikai!
Ya Allah ka taimaki
rundunoninmu masu kiyaye iaykokinmu, Ya Allah ka kiyaye jami'an tsaronmu, kuma
ka saka musu da mafi alherin sakamako, Ya Ubangijin Talikai!
Ya Allah ka gafarta
mana kuskurenmu da gangancinmu, da warginmu da kuma gaskenmu, kuma dukkan hakan
akwai shi a wurinmu.
Ya Allah lallai ne muna
neman tsarinka daga mummuniyar rana, da mummunan dare, da lokaci mummuna,
Ya Allah, lallai muna
neman tsarinka daga annoba, da zuwan bala'i Ya Ubangijin Talikai
Ya Allah ka warkar da
marasa lafiyanmu, kuma ka bada lafiya wadanda aka jarrabe su daga cikinmu, ka
yi rahama ga mamatanmu, ka taimake mu akan mai gaba da mu, Ya Ubangijin
Talikai!
Ya Allah! Ka sanya
addu'armu ta zama abar ji, ka daga kiraye-kirayenmu, Ya Mai karramawa, Ya Mai
girma, Ya Mai jin kai.
No comments:
Post a Comment