TSAWATARWA AKAN
WAKA, DAUKAR HOTO, ASKE GEMU, SAKE
TUFAFI GA MAZA, DA SHAN TABAR SIGARI
التحذير
من:
الغناء
والتصوير وحلق اللحية وإسبال الرجال وشرب الدخان
Na
Shehunan
Malamai
Abdul'aziz
Dan Abdullahi Ibnu-Baaz
Da
Muhammadu
dan Salkih Al’usaimin
Tarjamar
Abubakar Hamza Zakariyya Misau
TSAWATARWA
DAGA ASKE GEMU
(التحذير من حلق اللحية)
Na
Shehun Malami Muhammadu dan Salih Al-usaimin
Allah
ya yi masa rahama
Aske gemu haramun ne,
saboda saba wa Manzon Allah ne (S.A.W), domin Annabi (S.A.W)
ya ce: "Ku cika gemu, ku rage gashin baki". Kuma saboda
askwar ficewa ne daga shiriyar Manzanni, zuwa ga shiriyar masu bautar Wuta
(Majusawa) da Mushirkai.
IYAKAR
GEMU (LIHYAT) –Kamar yadda masanan harshen Larabci suka fada-
shine: Gashin
da ya tsiro a fiska, da muka-mukai biyu, da kumatu biyu; Ma’anar wannan shine:
Duk abinda ya tsira a jikin kumatu biyu, ko a muka-mukai biyu, da haba, to
wannan yana daga cikin gemu (lihyat). Kuma cire wani abu daga cikin hakan ya
shiga cikin sabo, domin Annabi (S.A.W)
ya ce: "Ku cika gemu", "Ku sake gemu", “Ku tara gemu”, “Ku ajiye gemu”.
Wadannan kuma sai suka nuna cewa, lallai bai halatta a cire wani abu daga jikin
gemu ba. Saidai saboda kasancewar sabo mataki-mataki ne, sai aske gemun gaba
dayansa yafi muni, akan yanke wani abu daga jikinsa, domin askewan yafi girma
kuma yafi rage shi nuna sabawar mai aikata hakan ga Sunnah. Wannan kuma shine
gaskiya, kuma ita ce, tafi cancantar a bi ta.
Kuma ka tambayi kanka: Mai zai hana ni karbar gaskiya, da yin aiki da
ita, domin yardar da Allah tare da neman ladansa? Don haka, kada ka fifita son
rai, da ganin damarka,ko abinda abokai suke so, akan yardar Ubangijinka, Allah
Ta’alah ya ce: "Amma
wanda ya ji tsoron tsayuwa ga UbangijinSa, sai ya hana ransa abinda take so *
To lallai Aljannah ita ce, makoma a gare shi”
[40-41].
Shi kuma rage gashin gemu, ya saba wa abinda
Annabi (S.A.W) ya bada umurni a cikinj
fadinsa: “Ku tara gemu”, "Ku bar gemu", "Ku sake gemu"; Don haka, Wanda ya so bin umurnin Manzon
Allah (S.A.W) da bin shiriyarsa (S.A.W), to kada ya ciri wani abu daga gemunsa;
domin shiriyar Manzon Allah (S.A.W) ita ce, kada
Mutum ya cire wani abu daga gemunsa. Kuma hakan (wato tara gemu) ita ce
shiriyar Annabawan da suka gabace shi, saboda dukkanmu mun karanta fadin Allah
Ta’alah dangane da Haruna ga annabi Musa: "Ya dan mamata: Kada ka kama min gemuna, ko kaina". Wannan kuma dalili ne akan cewa, lallai
Annabi Haruna yana da gemun da za a iya damkewa. Kuma hakan shine shiriyar
cika-makon annabawa; Muhammadu (S.A.W) domin
gemunsa ya kasance mai tarin yawa, cikakkke. Don haka; Duk wanda ya so ya bi
Annabi cikakken bi, ya kuma bi umurninsa
sau da kafa, to kada ya aske komai daga gemunsa; ta fiskar tsawonsa ko fadinsa.
Wasu Mutane a farkon farin fitowar gemunsu, ya
kan kasance gashi ne a rarrabe, sai Mutum ya ce: zai aske shi, domin gashin su
fito gaba daya a tare. Wannan kuma ba daidai ba ne; saboda Mutum zai iya askewan,
ya zama ya saba umurnin Annabi (S.A.W) da
aikata hakan, sai kuma ya mutu gabanin sake tsirowar gemun. Wajibin shine ya
bar gemun kamar yadda ya kasance,saboda idan gemun y agama girmansa ko
fitowansa, to ya kan taru cikin yanayi mai kyau.
Allah ne Mai datarwa ([1]).
TSAWATARWA
GA MAZA KAN TSAWAITA TUFAFI
(التحذير من إسبال الرجال)
Na
Shehun Malami Muhammadu dan Salih Al-usaimin
Allah
ya yi masa rahama
Sake tufafi nau’i biyu ne:
NA FARKO: Ya kasance da
takama da alfahari, Wannan yana daga cikin zunibin kaba’irai, kuma ukubarsa
tana da girma, domin ya zo a cikin Bukhariy da Muslim, daga hadisin Abdullahi
bn Umar, lallai Annabi (S.A.W) ya ce: Wanda yaja tufafinsa da takama, Allah
ba zai yi dubi gare shi ba, ranar kiyama". Kuma an
ruwaito daga Abu-Zarrin Algifariy (R.A), lallai Annabi (S.A.W ) ya ce: “Mutane
uku, Allah ba zai yi magana da su ba ranar kiyama, kuma ba zai yi dubi a gare
su ba, kuma ba zai tsarkake su ba, kuma suna da azaba mai radadi Ya
ce: Sai Annabi ya maimata hakan sau uku, Abu-Zarrin ya ce: Sun tabe sun yi
hasara Ya Ma’aikin Allah! Su wanene Ya Manzon Allah (S.A.W)?
Ya ce: Mai sake tufafinsa, da mai yin gori, da
mai tallata kayansa da rantsuwar karya”. Wannan nau’in shine sake
tufafin da ya hadu da takama (da girman kai), Kuma a cikinsa akwai narkon nan; na
azaba mai tsanani; wanda kuma shine fadin: Allah ba zai yi dubi ga mai aikata
shi ba, kuma ba zai yi magana da shi ba, kuma ba zai tsarkake shi a ranar
kiyama ba, kuma yana da azaba mai radadi.
Wannan gamewar
da ta zo a cikin hadisin Abu-Zarrin (R.A) an kebance ta, da abinda ya zo a cikin
hadisin Abdullahi bn Umar (R.A), sai narkon da ya zo a cikinsa ya kasance ga
wanda ya aikata hakan (wato, take tufafinsa) cikin takama (da girman kai)
kawai; saboda aikin da kuma horon iri daya ne, a cikin hadisan biyu.
NAU’I NA BIYU NA
TSAWAITA TUFAFI: Shi
ne ya take su bada takama ko girman kai ba, Wannan kuma haramun ne, kuma ana
tsoron ya kasance cikin laifukan kaba’irai, saboda Annabi (S.A.W) ya fadi narkon Wuta akansa, domin ya zo a
cikin Sahihul Bukhariy, daga Abu-Hurairah (R.A), lallai Annabi (S.A.W) ya ce: "Abinda
ya zama kasa da idanun sawu biyu, na tufafi, to yana cikin Wuta".
Shi wannan hadisin ba zai kasance an
kebance hukuncinsa da hadisin Abdullahi dan Umar ba (wato, ba za a ce, azabar
ta takaita ne ga wanda ya take tufafinsa da takama kadai ba); saboda ukubar da
ta zo a cikin hadisan biyu ta banbanta da juna. Da kuma saboda hadisin
Abu-Sa’id Alkhudriy (R.A) wanda ya ce: Manzon Allah (S.A.W)
ya ce: “Tufafin Mumini zuwa rabin kwabri ne,
Babu laifi ko ya ce: Babu matsala akan
abinda ya kasance a tsakanin kwabrinsa da tsakanin idanun sawu biyu. Amma
abinda ya kasance kasa da idanun sawu toyana cikin Wuta, Kuma wanda ya ja
tufafinsa da takama (alfahari) Allah ba zai yi dubi gare shi ba",
Malikya ruwaito shi, da Abu-Dawud, da Nasa’iy da Ibnu-Majah,da Ibnu-Hibbana a
cikin sahihinsa.
Sai Annabi (S.A.W)
ya banbance tsakanin wanda ya ja tufafinsa da takama (da girman kai), da
Mutumin da tufafinsa sukakasance a kasa da idanun sawunsa biyu (ba tare da
takamaba, ya bayyana narkon azabar kowanne daga cikinsu).
Saidai Mutumin da ya kasance
tufafinsa yana zamewa ko zobewa ya rufe masaidanun sawunsa biyu,ba tare da nufi
ba, alhalin yna bin tufafin nasa yana daga shi, to wannan babulaifi akansa,
domin a hadisin Abdullahi da Umar da ya gabata, lallai Abubakar (R.A) ya ce: "Ya Manzon Allah! Lallai daya daga cunar tufafina yana
zamewa,saidai idan ina binsa, (ina dago shi), Sai Annabi (S.AW) ya ce: "Kai
bakakasance daga cikin masu aikata hakan da takama (girman kai ba)"([2]).
TSAWATARWA
DAGA DAUKAN FOTO
(التحذير من التصوير)
Na Shehun
Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz
Allah
ya yi masa rahama
Yabo naAllah ne
shi kadai.
Salati da sallama
su kara tabbata ga wanda babu Annabi a bayansa, Bayan haka:
Hakika hadisai
masu yawa sun zo daga Annabi (S.A.W) a cikin
littatafan Sihah da Masanid da Sunan, masu nuni akan haramcin daukar foton
dukkan abu mai rai; dan adam ne ko waninsa, wasu kumaakan lamarin keta labulen
da a jikinsa akwai fotuna, da umurni kan shafe fotuna, da tsinuwa ga masudaukar
foto, da bayyana cewa sune Mutanen da
suka fi samun tsananin azaba a ranar kiyama.
Kuma lallai zan Ambato maka wasu daga cikin hadisai ingantattu,wadanda
suka zo a wannan babin, kuma sai na bayyana menene daidai a wannan
mas’alar,idan Allah ya so.
Ya zo cikin Sahihul Bukhariy da Muslim, daga Abu-Hurairah (R.A) ya ce:
Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Babu
wanda yafi girman zalunci, kamar wanda ya tafi yana yin halitta, kamar halitta
ta, sai su halicci kwayar zarrah, ko kwayar hatsi, ko alkama", Lafazin na Muslim
ne.
Kuma a cikin
Bukhariy da Muslim daga Ibnu-Mas’ud (R.A) ya ce: Manzon Allah (S.AW)
ya ce: "Lallai
Mutanen da suka fi tsananin azaba a ranar kiyama sune masu daukar foto".
Kuma ya zo a cikin
Bukhariy da
Muslim daga Abdullahi dan Umar (R.A) ya ce: Manzon Allah (S.AW)
ya ce: "Lallai
wadanda suke sana’anta wadannan fotunan za a musu azaba ranar kiyama, sai a ce
musu: ku rayar da abinda kuka halitta", Lafazin na Bukhariy ne.
Kuma Bukhariy ya ya
ruwaito a cikin Sahihinsa daga Abu-Juhaifah (R.A) lallai
Annabi (S.AW) ya yi hani kan cin kudin jini, da kudin kare, da
dukiyar karuwanci. Kuma ya la’anci mai cin riba, da wanda ya bayar da ita, da
mai canza halitta, da wanda ta nemi a canza mata, da mai yin foto".
Kuma an ruwaito
daga Ibnu-Abbas (R.A) ya ce: Na ji Manzon Allah (S.AW) yana cewa: "Wanda
ya dauki wani foto a Duniya, za a tursasa masa ya busamasa rai, kuma ba zai iya
ba", Bukhariy da Muslim.
Kuma Muslim ya
fitar da hadisi daga Sa’id dan Abul Hasan, ya ce: Wani Mutum ya zo ga Ibnu-Abbas
sai ya ce: Ni Mutum ne da nake daukar irin wadannan fotunan; ka min fatawa
akansu? Sai ya ce: Matso kusa da ni, sai ya kusance shi, har ya sanya hannunsa
akan kansa, sannan ya ce: "Dukkan mai yin foto yana cikin Wuta, za a sanya masa
dangane da kowane foton da ya dauka, za a sanya mata rai, ta rika azabtar da
shia cikin Jahannama". Sai ya ce: Idan babu
makawa sai ka yi, to ka yi foton bishiyoyi, da abinda bashi da rai.
Shi kuma Bukhariy
ya ruwaito fadinsa: Idan babu makawa sai ka yi, ne a karshen hadisin da ya gabata
kafin wannan, da irin lafazin da Muslim ya ambato shi.
Kuma wadannan
hadisan da abinda ya zo da ma’anarsu, suna yin nuni a zahiri, kan haramcin
daukan foton duk wani abu mai rai. Kuma sun nuna cewa aikata hakan yana daga
manyan zunuban da aka ambaci narkon Wuta akansu.
Kuma lallai sun
game, duk nau’ukan foto, sawa’un foto ne mai inuwa, ko maras inuwa, kuma
sawa’un foton a jikin Katanga ko labule ko riga ko madubi ko littafi ko a wanin
haka yake.
Kuma babu banbanci
a cikin haka, tsakanin foto masu jiki, da irin wadanda akazana su a jikin
labule ko littafi ko makamancin haka, ko tsakanin fotunan ‘yan Adam da wasunsu;
na daya daga halittu masu rai, ko tsakanin tsakanin fotunan masu mulki da
malamai ko wasunsu, ballamarin haramcin foton masu mulki da maluma da sauran
Mutanen da ake girmamawa shi yafi tsanani; domin an fi fitinuwa da wadannan.
Kuma kakkafa fotunansu a majalisosinsu da makamancin haka, da girmama su yana
cikin mafi girmar hanyoyin shirka, da yin bauta ga wanin Allah, kamar yadda
hakan ya auku ga Mutanen annabi Nuhu.
Salatin Allah ya
kara tabbata ga Annabinmu; Muhammadu, da iyalansa, da kuma amincinsa([3]). Amin.
TSAWATARWA
KAN WAKA DA KAYAN KIDA
(التحذير من الغناء وألات الطرب)
Na
Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz
Allah
ya yi masa rahama
Lallai
sauraron waka haramun ne, abun kyama, kuma yana cikin sabubban rashin zukata da
kaikashewarsu, da kangewa su daga ambaton Allah, da kin yin sallah.
Kuma
hakika mafi yawan ma’aboba ilimi sun fassara fadin Allah Ta’alah: "WA
MINAN NAASI MAN YASHTARIY LAHWAL HADISI".
“Daga cikin Mutane
akwai masu sayen zancen wargi …” zuwa karshen ayar, da cewa shine: Waka.
Kuma Abdullahi dan
Mas’ud (R.A) yana yin rantsuwa cewa lallai: shine: Waka.
Idan kuma ya zama
a tare da wakar akwai kayan wargi, kamar sharewa, da tsinke, da kamman, da
ganga, to haramcin yafi tsanani.
Wasu Malamai sun
ambaci cewa, Wakar da ta hadu da kayan wargi to haramun ne da ijma’i.
Don haka, wajibin
shine a kiyaye aikata hakan.
Kuma hakika ya
inganta daga Manzon Allah (S.A.W) lallai shi ya ce: (S.AW)
ya ce: "Wasu
Mutane za su kasance daga al’ummata, suna neman halatta zina (Alhira) da
alharir (ga Maza), da giya, da kayan kida".
Abun da ake nufi
da (Alhira) shine farji na haram, wato zina.
(Ma’azif) shine:
Waka, da kayan kida.
Ina maka wasiyya
da sauran Mutane da sauraron Iza’atul Kur’anil karim, da shirin: Nurun alad
darb, saboda a cikinsu biyun akwai fa’idodi mkasu girma, kuma sauraronsu aiki
ne da zai shagaltar da kai daga sauraron waka da kayan kade-kade([4]).
TSAWATARWA
DAGA SHAN TABAR SIGARI
(التحذير من
شرب الدخان)
Na
Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz
Allah
ya yi masa rahama
Hakika
dalilai na shari’a sun yi nuni cewa lallai shan tabar sigari yana daga al’amura
na haram a shar’iance, wannan kuma saboda abinda shan tabar ya kunsa na dauda
da cutarwa masu yawa, domin Allah Subhanahu bai halatta ababen ci da shag a bayinsa
ba face wadanda sukakasance masu dadi masu amfani.
Amma
wanda ya zama zai cutar da su; ga addininsu, ko duniyarsu, ko zai jirkita musu
hankulansu, to lallai Allah ya haramta susu su, saboda Allah Mabuwayi da
daukaka yafi tausayinsu akan kansu, kumashine Mai hikima Masani; cikin zantukansa
da ayyukansa da shari’arsa da kaddararsa; saboda baya haramta abu saboda wasa,
kuma baya halittar abu domin barna, kuma baya umurni face da abinda bayi suke
da fa’ida acikinsa, saboda Allah Shine Mafi hikimar masu hikima, mafi jin-kan
masu jin kai, kuma shine Masanin abinda yake dacewa da bayi, kuma mai amfani a
gare su; a nan da can, kamar yadda Allah ya ce: "Lallai Ubangijinka
Mai hikima ne Masani". Kuma Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Lallai Allah ya kasance Masani Mai hikima".
Kuma ayoyin da suke dauke da wannan ma’anar suna da yawa.
Daga cikin dalilan
Alkur’ani akan haramci taba akwai fadin Allah Ta’alah a cikin suratul Ma’idah: "Suna tambayarka me aka halatta musu? Ka ce: an halatta
muku abubuwa masu dadi". Kuma a cikin suratul A’araf ya ce,
ainda yake sifanta annabinmu Muhammadu: "Yana
umurtarsu da kyakkyawa, kuma yana hana su abin ki, kuma yana halatta musu
daddada, yana haramta musu dauda", har karshen ayar.
Sai Allah, a cikin
ayoyin nan biyu masu karamci ya bayyana cewa bai halatta wa bayinsa ba, face
daddadan abubuwa; wanda sune abin ci, da abun sha masu amfani. Amma nau’ukan
abin ci da abin sha masu cutarwa ga addini ko jiki ko hankali, to lallai suna
cikin munanan abubuwan da aka haramta.
Kuma hakika
likitoci da wadanda suka san mecece taba da cutarwarta,sun yi ijma’i cewa,
lallai taba tana cikin abun sha masu
cutarwa mai girma, kuma sun ambata cewa taba sababi ne cutuka masu yawa,kamar
cutar kansa, da mutuwar farat daya (tsayawar zuciya) da wasunsu.
Kuma duk abinda ya
kasance a haka, to babu makawa kan haramcinsa, da wajabcin kiyayarsa.Kumabai
dace mai hankali ya rudu da yawan masu shan taba a Duniya ba, domin Allah Ta’alah
a cikin littafinsa mabayyani ya ce: (S.AW)
ya ce: "Kuma
idan ka yi biyayya ga mafi yawan wadanda suke bayan kasa, za su batar da kai
daga hanyar Allah, ba komai suke bi ba face zato, kuma sub a komai ba ne, face
makaryata".
Kuma ya ce: (S.AW) ya ce: "Ko kana zaton mafi yawansu suna ji ko suna hankalta, su ba
komai ba face dabbobi, A’a! sune suka fi bacewa daga hanya".
Don haka, Tabar
sigari shanta baya halatta, ko sayar da ita ko ayi tijararta, saboda abinda ke
cikin hakan na cutuwa mai girma, da munanan abinda take haifarwa.
Kuma abinda ya
wajaba ga wanda yake shan taba (sigari) shine ya mayar da lamurransa ga Allah
Ta’alah, yay i nadamar abinda ya gabata, ya yi azamar, ba zai koma mata ba.
Wanda ya tuba da gaske, sai Allah Ta’alah ya karbi tubarsa, kamar yadda
Mabuwayi da daukaka ya fada: "Kuma ku tuba
zuwa ga Allah gaba daya –Ya ku Muminai-, domin ku samu babban rabo".
Kuma Allah ya ce: "Kuma ni mai yawan gafara ne, ga wanda ya tuba, kuma ya yi
imani, yay i aiki na kwarai, sannan ya shiryu". Kuma Annabi (S.AW) ya ce: "Wanda ya tuba daga zunubi, kamar wanda bashi da zunubi ne",
Ibnu-Majah ya ruwaito.
Muna rokon Allah
ya gyara halin Musulmai. Kuma ya tsare su daga dukkan abinda yake saba wa shari’arsa,
Lallai shi Mai ji ne Mai amsawa.