HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 15/RABIYYUL AWWAL/1440H
daidai da 23/NOBENBA/ 2018M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ALIYU BN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
ADDINI NASIHA NE
(الدين النصيحة)
Shehin Malami wato: Aliyu
bn Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: ADDINI NASIHA NE, Wanda kuma a cikinta ya
tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah; Ma'abucin
buwaya da karamci, Wanda ya kagi halitta, Mai yalwar falala da ni'imomi, Ina
yin yabo ga Ubangijina, kuma ina gode masa kan ni'imominSa wadanda muka sani,
da kuma wadanda bamu sani ba.
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya, sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, Mafi
girman buwaya da karamci,
kuma ina shaidawa lallai
annabinmu Muhammadu bawansa ne Manzonsa, Wanda Allah ya bashi dunkulallun
kalmomi (na jawami'ul kalim).
Ya Allah! ka yi dadin
salati, da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka; Muhammadu, da iyalansa
da sahabbansa, wadanda aka shiryatar da su ga hanyar da ta fi mikewa,
Bayan haka:
Sai ku yi takawar Allah Mabuwayi da daukaka, ta hanyar neman kusanci
zuwa gare shi da aikata kyawawan ayyuka, da kuma nisantar ayyukan haramun,
saboda babu mai tsira (a wurin Allah) face masu takawa, kuma babu mai tabewa ya
yi hasara face masu bin soye-soyen zukata, da masu sakaci.
Ya ku, Musulmai…
!!!
Ku yi hisabi ga kayukanku
gabanin a
muku hisabi, kuma ku farkar da zukatanku daga gafalarsu, kuma ku kame rayuka
daga aukawa cikin dadi irin na haramun, kuma ku yi gaggawan tuba, gabanin
saukowar ajali, da yankewar guri, da katsewan yin ayyuka, domin kuna ganin
saurin tafiyar shekaru, da gaggawar tafiyar kwanaki.
Kuma babu komai a bayan
wannan rayuwar face mutuwa, kuma babu komai a bayan mutuwa face shiga gidan
ni'ima, ko gidan azaba mai radadi.
Kuma kamar yadda kuke aiki
domin duniya mai karewa, to sai ku yi aiki domin lahira mai wanzuwa, Allah
Ta'alah ya ce: "Kawai, kuna fifita rayuwa ce ta Duniya * alhalin Lahira itace mafi
alheri kuma mafi wanzuwa" [A'alah: 16-17].
Ya ku, Musulmai…
!!!
Ku rungumi littafin
Ubangijinku, domin daukakarku da rabautarku da gyaruwar lamuranku, duka a
cikinsa suke, kuma a cikinsa samun rabonku bayan mutuwarku yake, da kariyarku
da tsirarku daga fitintinu wadanda suke yawaita duk lokacin da Kiyamah ta kara
kusantowa, fitintinu wadanda suke da sarkakiya a farkon faruwarsu, sai kuma su
bayyana su fito sarari a karshen lamuransu; don haka, babu wanda zai tsira daga
fitintinu sai wanda yayi riko da Alkur'ani da Sunnah, kuma ya lazimci jama'ar
Musulmai;
Sai ku yi tadabburi, ko nemi
sanin ma'anar littafin Allah Mabuwayi da daukaka, kuma ku yi aiki da shi,
sannan ku haddace abinda addini zai tsayu da shi, na sunnar Manzon Allah صلى الله عليه وسلم, kuma akida ta ingantu da shi, itama ibada
ta samu kamala da shi, musamman hadisan da ma'anoninsu ya game hukunce-hukuncen
Musulunci, wadanda suka kunshi falaloli, sai ku san ma'anoninsu, domin ku yi
riko da su kuma ku yi aiki, domin wannan shine MANHAJIN MAGABATA NA KWARAI, wadanda
Allah Ta'alah ya fada, akansu: "Masu rigayen farko daga Muhajirawa da
Ansarawa, da wadanda suka bi su da kyautatawa, Allah ya yarda da su, kuma suma
sun yarda da shi, kuma ya musu tanadin gidajen Aljannoni, koramu suna gudana a
karkashinsu, suna masu dawwama a cikinsu har abada, wannan shine rabo mai girma" [Tauba: 100].
Kuma –a wannan matsaya- zan
kawo hadisi daya daga cikin dunkulallun magana (Jawami'ul kalim), wanda ya
wajaba kowane Musulmi namiji da Musulma suyi aiki da shi, a cikin kowane hali,
kuma dole ne mazaje da mata su rika aiki da hadisin matukar akwai rai a cikin
jikinsu, Wannan kuma shine, fadinSa –صلى الله عليه وسلم-: "Addini nasiha ne, addini nasiha ne, addini
nasiha ne. Sai muka ce: Ga wa Ya Ma'aikin Allah? Ya ce: Ga Allah ne, da
littafinSa, da ManzonSa, da kuma shugabannin Musulmai, da kuma sauran gama-garinsu", Muslim ya ruwaito
shi, daga hadisin Tamim Ad-dariy (رضي الله عنه). Kuma wasu Maluma dayawa banda Muslim, suma sun ruwaito shi;
daga cikin Maluman hadisi.
Kuma hadisi ne mai girman
sha'ani, Imam Abu-dawud ya ce: "Fik-hu yana gudana akan hadisai guda biyar;
hadisin halal a bayyane yake, haram a bayyane yake, da hadisin babu cuta babu
cutarwa, da hadisin: dukkan ayyuka suna tare da niyyoyinsu, da hadisin: addini
nasiha ne, da hadisin: Abinda na hane ku, ku nisance shi, wanda kuma na umarce
ku, to ku zo da shi gwargwadon iko".
Kuma Alhafiz Abu-Nu'aimin
ya ce: "Wannan hadisi ne da yake da sha'ani mai girma, Muhammadu bn Aslam
Ad-duwsiy ya ambaci cewa, lallai hadisin addini nasiha ne, daya ne cikin kashi
hudu na addini".
Yana daga cikin dalilan da
suka nuna cewa; lallai wannan hadisin, wajibi ne ga kowane Musulmi namiji da kuma
mace musulma, su yi aiki da shi, koyaushe, Lallai Allah Ta'alah ya dauke wasu
ibadodi, ga wasu daga cikin Mutane, saboda wani uzuri, ko saboda wasu sababi,
amma bai dauke yin nasiha ba, karkashin kowane uzuri, ko cikin kowane hali,
Allah Ta'alah ya ce: "Babu kunci ga Maraunana, kuma babu laifi, ga majinyata,
da wadanda basu samu abinda za su ciyar ba, matukar sun yi nasiha ga Allah da
ManzonSa, kuma babu wata hanya (ta cutarwa) ga masu kyautatawa, Allah shine Mai
yawan gafara, Mai jin-kai" [Tauba: 91].
Sai Allah ya bayyana cewa,
ba za a yi uzuri ga wani Musulmi ba, kan yin watsi da nasiha, daidai da
kyaftawar ido (koda yana da uzuri).
Sahabbai basu yi tambaya
kan ma'anar nasiha ba, saboda sahabban sun san abinda kalmar take nuni akansa
na ma'anonin addini mai fadi ta kowace fiska, domin hakikanin nasiha ya
kunshi, martabobin addini uku na Musulunci da Imani da Ihsani.
Kawai abinda sahabbai suka
tambaya, shine Ga wa ake nasihar, kuma wanene suka cancanceta?
Kuma asalin ma'anar
nasiha, shine Tsamo abu ko cire shi daga abubuwan da suka shiga masa domin
gurbata shi, a larabci ana cewa; Nasahal asala, wato ya tace zuma, idan Mutum ya
tsaftace zumar daga kwansonsa.
Kuma MA'ANAR YIN NASIHA GA ALLAH TA'ALAH ya kunshi, Son Allah, da kan-kan-da-kai a gare shi, da
rusuna masa, da mika-wuya ga shari'arsa, domin neman yardarSa da ladanSa, da
kuma tsoron fushinSa da azabarSa, Allah Subhanahu ya ce: "Kawai masu imani da
ayoyinmu, sune wadanda idan aka fadakar da su da ayoyin, sai su fadi suna masu
sujada, kuma suna yin tasbihi game da gode wa Ubangijinsu, alhali ba su yin
girman kai * sasanninsu suna nisantar wuraren kwanciya, suna kiran Ubangijinsu
bisa ga tsoro da tsammani, kuma suna ciyarwa daga abinda muka azurta su" [Sajada: 15-16].
Kuma AllahTa'alah ya ce:
"kuma Masu imani sune masu tsananin so ga Allah" [Bakara: 165].
Kuma Annabi صلى الله عليه وسلم ya
ce: "Ku so Allah daga dukkan zukatanku, saboda abinda yake ciyar da ku da
shi, na ni'imomi".
Kuma mafi girman nasiha ga Allah, itace bauta masa
Subhanahu, ba tare an hada shi da abokin tarayya ba, cikin tsarkake niyyah, da
aiki da Sunnah da bin shiriyar annabi Muhammadu صلى الله عليه وسلم, da kebance Ubangiji da na'ukan ibadodi
dukkansu, kamar addu'a da neman taimako, agaji, da tawakkali, Allah Ta'alah ya
ce: "Ka ce, lallai kawai ina rokon Ubangijina ne, ba zan masa shirki ko
hada shi da kowa ba"
[Jin: 20].
Shi kuma Ubangiji Mabuwayi da daukaka ana masa bauta ne,
saboda abinda yake da su na sifofin kamala da girma, da kuma yadda ya tsarkaka
daga sisfofin tawaya (nakasa), da kuma saboda abinda Allah yake da su na
ni'imomi ga halittunSa, da bukatuwan bayi zuwa ga rahamarSa; don haka: Ita ibada
sababi ce na samun alherorin Allah, kuma sababi ce na tunkude sharrace-sharrace
ga Mutum, a cikin rayuwarsa da kuma bayan mutuwarsa.
Kuma nasiha ga Allah Tabaraka wa Ta'alah tana
kasancewa ta hanyar tabbatar wa Allah abinda ya tabbatar wa kansa a cikin
littafinSa, da kuma abinda ManzonSa ya tabbatar masa da su; na sunaye da
sifofi, akan abinda magabata na-kwarai suka kasance akansa, Allah ya yarda da
su, amin. An ruwaito daga Abu-Umamah رضي الله عنه daga Annabi صلى
الله عليه وسلم, Allah Ta'alah ya ce: "Mafi soyuwan
abinda bawana ya bauta min da shi, shine yin nasiha a gare ni", Ahmad ya ruwaito
shi, da 'Dabaraniy a cikin mu'ujam kabir.
Kuma ma'anar yin nasiha ga Manzon
Allah صلى الله عليه وسلم itace: son annabi da darajanta shi da girmama sunnarsa, da aiki
da umurninsa, da hanuwa da haninsa, da yin bauta wa Allah da shari'arsa, da
bibiyar shiriyarsa, da gaskata labarunsa, da yada hadisansa, da yin da'awa zuwa
ga addininsa, Allah Ta'alah ya ce: "Ka ce: Ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a
ga Manzo, amma idan kuka bijire, to lallai akansa akwai abinda aka aza masa,
kuma akanku akwai abinda aka aza muku, kuma idan kuka masa da'a zaku shiryatu" [Nur: 54].
Kuma ma'anar yin
nasiha ga Littafin Allah Ta'alah itace: Girmama Alkur'ani mai karamci, da sonsa, da
yin kokari wajen koyan karatunsa da karantar da shi, da neman sanin
hukunce-hukuncensa, da yin tilawarsa tilawa ingantacciya, da yin aiki da
umurnin Alkur'ani, da barin haninsa, da dawwama kan tilawarsa, da kiyaye
harrufansa da iyakokinsa, da sanin tafsirinsa da ma'anoninsa, da abinda aka
nufa da shi, da yin tunani cikinsa, da dabi'antuwa da shi, da yin raddi ga
wadanda suka karkata wajen fahimtar Alkur'ani da sunnah, tare da ruguza
barnace-barnacensu, da tsawatarwa akansu, Allah Subhanahu ya ce: "Lallai wannan
Alkur'anin yana shiryatarwa zuwa ga hanyar da tafi kyawu" [Isra'i: 9].
Kuma ma'anar yin
nasiha ga Shugabannin Musulmai itace: So musu alheri, da son su yi adalci, da yin
farin-ciki idan aikinsu ya yi dace, da nisantar algus a gare su, da kin
ha'intarsu, da kuma (uwa uba) kada Mutum ya yi fito-na-fito da su, ko ya
taimaki makiya akansu, tare da taimaka musu cikin lamarin gaskiya, da yin
biyayya a gare su cikin abinda ba sabo ba, da yin addu'ar dace a gare su, da addu'ar
dacewa da gaskiya a cikin hukuncin da suke yi, An ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), ya ce: "Lallai Allah yana
yarje muku abu uku, yana yarje muku, ku yi bauta a gare shi; kada ku hada shi
da kowa, kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kada ku rarraba, kuma rika
nasiha ga wadanda Allah ya jibinta musu lamuranku", Muslim ya ruwaito
shi.
Abdullahi bn Mas'ud رضي الله عنه ya ce: "Lallai abinda kuke
kyama alhalin kan jama'a yana hade shine mafi alheri akan abinda kuke so, a
halin rarrabuwa".
Kuma an ruwaito dagan
Jubair bn Mud'im, daga Annabi صلى
الله عليه وسلم ya fada a cikin hudubarsa a masallacin Khaif (dake Minah):
"Abu uku zuciyar Mutum Musulmi baya daukar kyashi akansu; Tsantsanta
aiki ga Allah, da yin nasiha ga Majibinta lamura (shugabanni), da lazimtar
jama'ar Musulmai",
Ahmad ya ruwaito shi da Alhakim.
Kuma an ruwaito daga
Ma'akil bn Yasar, daga Annabi صلى
الله عليه وسلم ya ce: "Babu Mutumin da Allah zai bashi wani abin
kiyo, sai bai kewaye su da nasiharsa ba, face ba zai shiga Aljannah ba", Bukhariy da Muslim
da Ahmad suka ruwaito shi.
Ita kuma ma'anar
nasiha ga dukkan Musulmai itace: Fadakar da su zuwa ga maslahohinsu, da ilmantar da su
lamuran addininsu, da sitirce al'aurarsu, da kokarin toshe ko biya musu bukatu,
da nisantar algus ko ha'intarsu, da nisantar yin hasada a gare su, Allah
Ta'alah ya ce: "Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba" [Ali-imrana: 103],
kuma Allah Ta'alah ya ce: "Lallai Muminai 'yan'uwan juna ne", [Hujurat: 10]
Allah ya yi mini albarka NI
da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI
da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, Na fadi abinda ku ke ji, kuma ina neman
gafarar Allah Mai girma ga Ni da KU da sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku
nemi gafararSa, lallai shi Mai gafara
ne Mai rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah Masanin abinda ya buya na gaibu, Mai
jujjuya zukata, Mai yaye musibun da suka sauka da bakin ciki, Ina yin yabo ga
Ubangijina kuma ina gode masa akan ni'imominSa gaba daya; wadanda suka gabata
da wadanda zasu zo,
Kuma ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya, Mai yawan
gafarar zunubai,
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu Muhammadu bawanSa ne ManzonSa zababbe,
Ya Allah ka kara salati da
sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu, da iyalansa, da
sahabbansa madaukaka, masu takawa.
Bayan haka … !!
Sai ku yi takawar Allah
Ta'alah, a asirce, da kuma a bayyane, domin da takawa ne zaku samu mafi
kololuwar daukaka, kuma ku rabautu da alkhairori a wannan rayuwar, da kuma bayan
mutuwanku,
Ya ku Bayin Allah …
!!
Ku yi tunani akan fadin
Allah Ta'alah: "Kuma Muminai maza da mata, sashensu majibincin sashe ne, suna yin
umurni da kyakkyawa, kuma suna hani da abinda ba a so, kuma suna tsayar da
sallah, kuma suna bayar da zakka, kuma suna da'a ga Allah da ManzonSa, wadannan
lallai Allah zai yi rahama a gare su, Lallai Allah Mabuwayi ne Mai hikima" [Tauba: 71]. A cikin
wannan ayar akwai taimaka wa juna, da tallafar juna, da nasiha wa juna, da
agaza wa juna, da 'yan'uwantaka, da jin-kai da rahama da kauna.
Kuma an ruwaito daga Jarir bn Abdullahi, ya ce: "Na yi
mubaya'a ga Manzon Allah صلى الله عليه وسلم akan tsayar da
sallah, da bada zakka, da yin nasiha ga kowane Musulmi", Bukhariy da Muslim
su ka ruwaito shi.
Kuma Abubakar Almuzaniy ya
ce: "Abubakar رضي الله عنه bai fi sauran Sahabban Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
yawan azumi ko salla ba, saidai ya yi fice ne da wani abu da ya tabbatu a cikin
zuciyarsa",
Ibnu-Ulayyah ya ce: "Abinda ya kasance a
zuciyar Abubakar shine, soyayya don Allah Mabuwayi da daukaka, da yin nasiha ga
halittarSa".
Kuma an ruwaito daga Hakim bn Abiy-Yazid, daga Babansa, daga
Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: "Idan dayanku ya
nemi nasihar dan'uwansa, to ya masa nasiha", Ahmad ya ruwaito shi, da 'Dabaraniy
a cikin mu'ujam kabir.
.
Ya ku Bayin Allah… !!!
"Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga
wannan Annabin, Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da
sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa
Annabi Muhammadu, ……………………………
,,, ,,, ,,,
No comments:
Post a Comment