HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 01/Rabiyul Awwal/1440H
daidai da 9/Nobenba/ 2018M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH SALAH BN MUHAMMADU ALBUDAIR
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
WASICI DA JIN-KAI
Shehin Malami wato: Salah
bn Muhammadu Albudair –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: WASICI DA JIN KAI, Wanda kuma a cikinta ya
tattauna, akan abinda ke tafe, Ya ce:
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah
Ma'abucin ni'imomi, Ya game kowane abu da ilimi, kuma ya game kowane abu da
rahama da kuma hakuri, kuma ya rinjayi kowane halitta da buwaya da hukunci,
"Yana sanin abinda ke gaba gare su, da abinda ke bayansu, kuma basu
kewaye da shi ga sani" [Daha: 110].
Kuma ina shaidawa babu
abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake bashi da abokin tarayya, yana
yin rahama ga masu jin-kai daga cikin bayinSa.
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa; cika-makon annabawa,
kuma jagoran zababbu, Annabin rahama, Mai kira zuwa ga hanyar UbangijinSa da
hikima, kuma mafi alherin annabin da aka tayar da shi zuwa ga mafi alherin
al'ummah.
Allah ya yi dadin salati
a gare shi, da kuma iyalansa nagari, da kuma sahabbansa masu haske 'yan
albarka, kuma ya yi sallamar amintarwa.
Bayan haka…
Ya ku Musulmai!!!
Ku yi takawar Allah,
saboda jiya ta shude, yau kuma aiki ne, gobe kuma buri, "Kuma abinda
kuka gabatar domin kayukanku na alheri za ku same shi a wurin Allah, yana mafificin
alheri (akan wanda kuka jinkirtar), kuma zaku same shi yana mafi girman lada"
[Muzzammil: 20].
'Yan albarka, sukan nuna
tausasawa da sadarwa da kyautatawa, kuma suna yin afuwa da rangwame, suna yin
wasici da jin-kai. Shi kuma yin wasici da jin-kai yana da fala mai girma, kuma
ibada ce mai daraja, Ubangijinmu Madaukaki Mabuwayi ya fada: "Sa'annan ya
kasance daga wadanda suka yi imani, kuma suka yi wa juna wasiyya da yin hakuri,
kuma suka yi wa juna wasiyya da tausayi * Wadannan sune ma'abuta albarka"
[Balad: 17-18].
Ma'anar "وتواصوا بالمرحمة"
Kuma suka
yi wa juna wasiyya da tausayi" shine sashensu ya
yi wasiyya ga sashe kan jin-kan Mutane, da tausasawa daukacin halittu, kuma
sashensu ya kwadaitar da sashe akan tausasawa da taushin hali da jin-kan fakiri
da miskini, da karamin yaro da maraya, da marasa lafiya da wadanda bala'i ya
auka musu, kuma suke tausayin jahilai da masu sabon Allah, ta hanyar yin nasiha
da wa'azi da tunatarwa da umurni da kyakkyawa da hana su aikata laifi. Kuma
cikin haka ne, rayuwar Mutane take, kuma da zaran sun dena irin wannan jin-kan,
to lallai zasu halaka.
Kuma Allah سبحانه ya sifanta masoyanSa da sifofi guda biyar,
daya daga cikinsu shine "أذلة على المؤمنين"masu tawali'u ga Muminai"
[Ma'idah: 54]. Abin nufi, masu taushin hali da sassautawa da tausayi da jin-kai
da tausasawa ga Muminai, kamar yadda Allah ya fada ga AnnabinSa: "Kuma ka
sassauta fikafikanka ga wadanda suka bika daga Muminai"
[Shu'ara'i: 215].
Kuma ya sifantsa
Sahabbansa da kwatankwacin haka, a cikin fadinSa: "Muhammadu
Manzon Allah ne, Wadanda kuma suke tare da shi, masu tsanani ne akan kafirai,
masu rahama ne a tsakaninsu", [Fat-h: 29]. Wato masu jin-kai da
tausayi da taushin hali a tsakaninsu.
Kuma Mumini, ya kan
kasance mai jin-kai da rahama, mai yawan dariya da bushasha a fiskar dan'uwansa
Mumini, Allah تعالى ya
fada dangane da sifar AnnabinSa –صلى الله عليه وسلم-: "Kuma ga
Muminai, mai tausayi ne mai rahama", [Taubah: 128].
…
Sai ku yi imani da wannan
Annabin, domin kar ku tabe ***
Ma'abucin alamar da Allah
ya tsaga masa (wato, zoben annabta)
Mai tausayi, Mai jin-kai,
Ma'abuta imani kuma yana musu rahama ***
Makusanci ga Ubangijin
kursiyyu, wanda aka masa rahama.
(Annabin), bai gushe ba,
yana umurtarmu da kyakkyawa ***
Yana shiryatar da Mutane,
da haskensa mai haskawa
Allah mai buwayar daukaka
ya kara salati a gare shi ***
Duk lokacin da haske ko
walkiya ta walka
Annabin, ya zo da lamarin
tuba, kuma ya zo da cewa a rika tausayin juna, a cikin fadinsa: "Ni
Annabin tuba ne, kuma Annabin tausayi ne".
Kuma ya ce: "Ma'abuta
tausayi Allah Mai rahama yana tausayinsu, sai ku ji-kan wadanda suke bayan
kasa, domin wanda yake sama ya ji tausayinku".
"Allah
baya tausayin wanda baya tausayin Mutane".
"Wanda
bai ji tausayin karamin cikinmu ba, kuma bai san hakkin babba daga cikinmu ba,
to lallai baya cikinmu".
"Ba a
cire tausayi, sai daga zuciyar Shakiyyi".
Kuma an ruwaito daga
Usamah bn Zaid –رضي الله عنهما-, ya ce: 'Diyar Annabi –صلى الله عليه وسلم- ta
aiko zuwa gare shi, cewa, Lallai 'Danta ya rasu; ka zo mana, Sai aka miko wa
Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- wannan yaron, alhalin ransa tana kokarin
ficewa, Sai idanunsa biyu suka zubar da hawaye, Sai Sa'ad ya ce: Menene wannan?
Sai Annabi ya ce: "Wannan tausayi ne, wanda Allah yake sanya shi
a zukatan bayinSa, kuma lallai Allah yana tausayin masu tausayi ne daga bayinSa",
Bukhariy ya ruwaito.
Kuma Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم-
Mutanensa sun karyata shi, sun yi mummunan cutar da shi, har A'ishah –رضي الله عنها-
take ce masa: Shin wani yini, ya zo maka, wanda yafi tsanani a gare ka fiye da
ranar yakin Uhud? Sai ya ce: "Hakika na hadu da abinda
na hadu da shi na cutarwa daga Mutanenki, kuma mafi tsananin abinda na hadu da
shi ya kasance ne a ranar bai'ar akabah, a lokacin da na bijiro da kaina ga:
Ibnu-Abdi-Yalil bn Abdi-Kulal, amma bai amsa min kan abinda na nema ba, sai na
tafi gaba alhalin ina cikin mummunan bacin rai, ban komo cikin hayyacina ba,
sai a wurin da ake kira: Karnus sa'alib, sai na daga kaina, sai ga wani
girgijen gajimare ya min inuwa, sai nayi dubi, sai ga mala'ika Jibrilu a
cikinsa, sai ya daga sauti ya kira ni; ya ce: Lallai Allah ya ji maganar da
Mutanenka suka gaya maka, da irin amsar da suka baka, kuma hakika ya turo maka
da Mala'ikan duwatsu, domin ka umurce shi da abinda kake son ayi da su! Sai
Mala'ikan duwatsu ya daga sauti ya kira ni, ya mini sallama, sa'annan ya ce:
Lallai Allah ya ji abinda Mutanenka suka gaya maka, kuma ni Mala'ikan duwatsu
ne, kuma hakika Ubangijinka ya turo ni zuwa gare ka, domin ka umurce ni da
umurninka; don haka duk abinda kake so; idan ka so sai in zirdo musu duwatsun
Akhshabaini biyu da suke da su akansu! Sai Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: A'A INA FATAN ALLAH DAGA TSATSONSU ZAI FITAR DA WANDA
ZAI BAUTA WA ALLAH SHI KADAI; BA TARE DA YA YI MASA SHIRKA DA KOMAI BA",
Bukhariy da Muslim.
Ibnu-hajar –رحمه الله تعالى- ya
ce: A cikin wannan hadisin, akwai bayanin tausayin Annabi –صلى الله عليه وسلم- ga
Mutanensa, da yawan hakurinsa da juriyarsa, wannan kuma daidai yake da fadin
Allah Ta'alah: "Kuma domin rahamar Allah ne a gare ka, kake tausaya musu",
[Ali-imrana: 159], da fadinSa: "Kuma bamu turo ka ba, sai don
rahama ga talikai", [Anbiya'i: 107].
Wannan shine hali ko
dabi'ar Annabinmu Muhammadu –صلى الله عليه وسلم-, wannan kuma itace sifarsa, wannan shine
da'awarsa, wancan kuma itace rahamarsa da tausayinsa, Wancan kuma shine
halayyar Muminai, Don haka, madalla da masu tausayi!
Ina fadan abinda kuke ji,
kuma ina neman gafarar Allah, sai ku nemi gafararSa, lallai shi ya kasance Mai
yawaita rahama da gafara.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA BIYU
Godiya ta tabbata ga
Allah Mai karamci Mai hakuri, ina yin yabo a gare shi kamar yadda ya dace da
girmansa maras iyaka, da kuma fiskarsa mai karamci.
Kuma ina shaidawa babu
abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake bashi da abokin tarayya, kuma
bashi da kishiya, bashi da abokin rabiya.
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu kuma shugabanmu bawansa ne manzonsa.
Allah ya yi salati da
sallama a gare shi da iyalansa da sahabbansa, mafi tsarkin salati da sallama,
Ya kai dan'uwana! Ya kai
dan'uwana!
Ka kasance mai tausayin
kanka da waninka, kuma kada ka zama mai kadaituwa da alherinka, wato, ka yi
rahama ga jahili da iliminka, Mabukaci kuma da matsayinka, Fakiri kuma da
dukiyarka, Mai yawan shekaru kuma da girmamawanka, Karami kuma da tausayawanka,
Masu sabo kuma da wa'azinka, Dabbobi kuma da tausasawanka,
saboda wanda yafi kusa da
samun rahamar Allah a cikin Mutane shine wanda yafi tausayin halittun Allah,
kuma duk wanda tausayawansa ga halittu ya yawaita, da yin rahama ga bayinSa,
sai Allah ya yi masa rahama da rahamarSa, kuma ya shigar da shi gidan
karamarSa, kuma ya kare shi daga azaba a cikin kabarinsa, da kuma firgicin
yinin kiyama, sai kuma ya sanya shi karkashin inuwarSa.
'Dan'uwana, lallai ina da
gogewa daga wadannan kwanakin ***
Cikin abinda nake zato,
kuma na samu ilimi tabbatacce mai warkarwa
Kada ka tafi a cikin
Mutane face kana mai tausayinsu ***
Kuma kada ka mu'amalance
su face da adalci
Ka yanke dukkan kullin da
kake boye shi (a zuci) ***
Idan mai tuntube ya maka tuntube,
ko idan mai laifi ya maka laifi
Ka nisantar da kanka daga
dukkan abinda babu gyara cikinsa ***
Kuma ka yalwaci Mutane da
kyautuka da baiwa
Kuma kada ka tona asirin
laifin mai laifi ***
Kuma ka sadar da zumuncin
dan'uwanka mai jafa'i da ya yanke,
Sai ka samu tsira daga
wannan Duniyar ***
Kuma ka rabauta da
mutunci cikakke kammalalle
Aiki yana kyau, idan ya
zama wajen samar da amfani ne ***
Marasa aikin, sukan zamo
masu shisshigi da tsegumi
Sai ku yi da sallama ga annabi
Muhammadu mai shiryatarwa, mai ceton Mutane gabadaya, domin wanda ya yi masa
salati guda daya, to Allah zai masa salati guda goma;
Ya Allah! Kay i salati da sallama ga bawanka kuma
manzonka Muhammadu, kuma ya Allah ka yarda da iyalansa da sahabbai, ka
hada mu tare da su, Ya Mai karamci Ya Mai yawan baiwa.
Ya Allah! Ka
daukaka musulunci da Musulmai, kuma ka kaskantar da shirka da Mushirkai, kuma
ka ruguza makiya addini, kuma ka sanya kasashen Musulmai cikin aminci da zaman
lafiya, da natsuwa, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah Ka
datar da shugabanmu kuma majibincin lamarinmu, mai hidimar harami guda biyu
madaukaka zuwa ga abinda kake so, kuma ka yarda, kuma ka kama makyamkyamarsa
zuwa ga aikin da'a da takawa.
Ya Allah ka
datar da shi, da na'ibinsa zuwa ga daukakar Musulunci da gyaruwan Musulmai, Ya
Ubangijin talikai.
Ya Allah ka
bada nasara ga rundunoninmu masu dakon iyakokinmu, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka
kiyaye jami'an tsaronmu, Ya Allah ka kiyaye jami'an tsaronmu, kuma ka sakanta
musu da mafi alherin sakamako, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka
warkar da marasa lafiyanmu, kuma ka yaye wa wanda yake cikin ibtila'i daga
cikinmu, ka yi rahama ga matattunmu, ka bamu nasara ga akan wanda yake adawa da
mu.
Ya Allah ka
sanya addu'armu ta zama abar amsawa, kiranmu kuma abin dagawa, Ya Mai karamci,
Ya Mai girma, Ya Mai jinkai!
No comments:
Post a Comment