SHARHIN TAMBAYOYIN
KABARI GUDA UKU
Lallai yabo na Allah ne;
muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman
tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan ayyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar,
babu mai batar da shi, Wanda kuma ya batar, babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya
ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanSa ne ManzonSa ne.
Bayan haka;
MATASHIYA GABANIN SHARHI
MAWALLAFIN LITTAFIN USULUS SALASA
Shi ne, Shehin Malami da ake masa lakabi da shehin
musulunci, mujaddadin da'awa zuwa ga Tauhidin Allah, Shugaba; abin koyi,
jagora; Muhammadu bn Abdulwahhab, dan Sulaiman, daga kabilar Tamim.
Alkunyarsa: Abul-Husain.
An haife shi, a garin Uyaynah, a shekarar hijira ta 1115H.
Ya yi wafati a garin Dir'iyyah, a shekarar 1206H.
ME YASA MUKE KARANTA TAUHIDI
(ILIMIN SANIN YADDA AKE KADAITA ALLAH)?
Saboda Allah ya halitta mu, domin
kadaita shi.
|
Saboda Allah baya karbar kowane aiki,
sai idan an kadaita shi da shi.
|
Babu mai shiga Aljannah sai mai
tauhidi.
|
Sababi ne na yawaitar lada.
|
Sababi ne na kankare laifuka.
|
Sababi ne na samun shiriya, da
tabbatuwan zaman lafiya.
|
Sababi ne na samun natsuwa.
|
Sababi ne na samun ceton Annabi صلى الله عليه وسلم
|
DALILAN DA SUKA SABBABA ZABAN
WANNAN LITTAFI, A FARKON NEMAN ILIMI
Yadda Magabatanmu na-kwarai, da Malumanmu; na Ahlus-Sunnah
Wal Jama'ah su ka baiwa wannan littafi mai albarka kulawa; saboda abinda ke
cikinsa na amfani da fa'idodi masu girma, wanda hakan ya mayar da shi, wani
ginshikin da 'Dalibin ilimi zai fari tafiyarsa ta kan wannan littafi, ya kuma
gina neman ilimin shari'a da ya ke yi akan wannan littafi, Wannan ya sanya mu
–a wannan zamanin- mu ke koyi da su, kuma muke binsu sau-da-kafa, akan wannan
manhaji.
* Suma sauran mutane –wadanda ba daliban ilimi ba- ba za
su dena bukatar wannan littafin ba, da kuma abinda littafin ya ginu akansu
na-ginshikai, wadanda babu makawa, dole Mutum ya yi imani da su, irin imanin da
baya karbar kokwanto da shakku.
WANNAN LITTAFIN –DA SAURAN
LITTATAFAN SHEHIN MUSULUNCI; MUHAMMADU BN ABDULWAHHAB رحمه الله- SUN YI FICE DA WADANNAN:
Saukin ma'ana da fitowa fili
|
Ambaton mas'aloli tare da dalilansu
|
Hada mas'aloli da jeranta su, da fadin
adadinsu, gabanin fara sharhinsu
|
Yawaita addu'a ga mai karanta ko
sauraron littatafansa.
|
BAYANIN MENENE الأصول
الثلاثة
"Usulus
Salasa", a takaice, sune: Tambayoyin kabari guda uku;
Wanene Ubangijinka?
|
Menene Addininka?
|
Wanene Annabinka?
|
WANE FA'IDA ZA MU SAMU, IDAN MUKA KARANTA "USULUS
SALASA"
Lallai idan ka karanci wadannan ginshikan uku, sai ka yi
aiki da su, sa'annan ka yi da'awarka zuwa gare su, sai kuma ka yi hakuri kan,
neman ilimi, da aiki da shi, da kuma da'awa zuwa ga hakan, to lallai –da izinin
Allah- za ka iya amsa tambayoyin kabari.
ABINDA KE CIKIN LITTAFIN "USULUS SALASA"
Wannan littafin ana kasa abinda ke
cikinsa zuwa kashi biyar;
MAS'ALOLI GUDA HUDU
(da suke cikin suratul Asr)
|
MAS'ALOLI GUDA UKU
(da suke magana kan karkasuwar Tauhid)
|
MUHIMMANCIN KARANTA TAUHIDI
|
"GINSHIKAI GUDA UKU"
(Tambayoyin kabari)
|
RUFEWA
|
1. MAS'ALOLI GUDA HUDU
1- ILIMI
|
2- AIKI DA ILIMI
|
3- DA'AWA ZUWA GA ILIMI DA AIKI
|
4- JURIYA GA CUTARWAR DA TAKE CIKINSU
|
2. MAS'ALOLI GUDA UKU
1- Tauhidin Rububiyyah da Tauhidin Asma'u
was Sifatu
|
2- Tauhidin Uluhiyyah
|
3- Barranta daga Shirka da ma'abutansa
(a zuciya da harshe, da sauran gabbai)
|
3. MUHIMMANCIN KARANTA ILIMIN TAUHIDI
(Shine abinda ya gabata, na amsar: Me ya sanya muke
karanta ilimin Tauhidi?).
4. GINSHIKAI GUDA UKU NA "USULUS
SALASA"
"Usulus Salasa", a takaice,
sune: Tambayoyin kabari guda uku;
Wanene Ubangijinka?
|
Menene Addininka?
|
Wanene Annabinka?
|
5. RUFEWA;
Wannan kuma yana farawa ne daga fadin Mawallafin "والناس إذا ماتوا يبعثون" har zuwa karshen littafin.
NA FARKO: MAS'ALOLI GUDA HUDU
بِسْمِ
اللهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ (Bismil Lahir
Rahmanir Rahim)
اعْلمْ رَحِمَكَ اللهُ (Ka sani –Allah
ya yi maka rahama-)
أَنَّهُ يَجِبُ عَلَيْنَا تَعَلُّمُ أَرْبَع مَسَائِلَ:
(Lallai yana wajaba akanmu mu
koyi mas'aloli guda hudu)
الأُولَى:
الْعِلْمُ: (Mas'alar farko:
ILIMI)
وَهُوَ
مَعْرِفَةُ اللهِ، وَمَعْرِفَةُ نَبِيِّهِ صلى الله عليه وسلم، وَمَعْرِفَةُ دِينِ
الإِسْلامِ بالأَدِلَّةِ
)ILIMI
Shine ilimin sanin Allah, da sanin AnnbinSaصلى الله عليه وسلم da sanin addinin
Musulunci, tare da dalilai).
الثَّانِيَةُ:
الْعَمَلُ بِهِ (Mas'ala ta biyu: AIKI DA ILIMIN).
(1)
SABABIN DA YA SANYA MAWALLAFINMU YA FARI LITTAFINSA DA "BISMILLAH"
1. Domin koyi da littafin Allah, da
Annabawa عليهم السلام.
|
2. Domin koyi da Maluman da suka gabace
shi, da magabatan kwarai; wadanda cikin al'adarsu akwai bude littatafansu da sunan
Allah (Bismillah).
|
3. Domin neman albarkar farawa da sunan
Allah Mai-karamci.
|
(2)
Kamar yadda muka yi nuni, a "MUKADDIMAH" cewa
yana daga al'adar Malam cikin wallafe-wallafensa, ya kan fara addu'a ga
'Daliban ilimi, kuma ya roka musu rahamar Allah; kuma cikin aikata haka, akwai
dalili akan:
Rahamar Maluman Ahlus-Sunnah Wal
Jama'a ga 'Dalibansu.
|
Lallai addinin Musulunci ga asalinsa
ya ginu ne akan jin-kai da rahama.
|
ILIMI: Shine: Sanin gaskiya, da dalilinsa. Kishiyan ilimi kuma shine Jahilci.
(3)
Domin bayanin alakar da ke tsakanin "ILIMI" da
"AIKI DA SHI" wani ke cewa: "ILIMI YANA HUKUNTA AIKI' IDAN HAR
YA AMSA MASA SHI KENAN, IDAN KUMA BA HAKA BA, SAI ILIMIN YA YI KAURA"; Don
haka, babu wata fa'ida ga ilimin da ba a yi aiki da shi ba, kuma idan mutum ya
koyi ilimi, to wajibi ne ya yi aiki da shi, idan kuma ba haka ba, to ya yi koyi
da Yahudawa; saboda Yahudu ne, suke da ilimi babu aiki, "SUNA SANINSA KAMAR YADDA SUKE SANIN
'YA'YANSU" [Bakara: 146]. Kuma farkon
wadanda za a fara babbakawa a cikin wuta sune mutane uku; daga cikinsu, akwai
wanda ya koyi ilimi, sai bai yi aiki da shi ba
KUMA MALAMIN DA BAI YI AIKI DA ILIMINSA
BA
ZA A AZABTA SHI GABANIN MASU BAUTAR
GUMAKA
الثَّالِثَةُ:
الدَّعْوَةُ إِلَيْهِ
(Mas'ala ta uku: YIN DA'AWA ZUWA GA ILIMI
DA AIKI).
DA'AWA TANA DA SHARUDDA DA
KA'IDODI, WANDA YA WAJABA TA GINU AKANSU, Wanda suka fi muhimmanci daga cikinsu
sune:
1.
Dole da'awar ta kasance an nufi Allah Ta'alah da ita.
|
2.
Dole a gina da'awa akan ilimin shari'a.
|
3.
Dole da'awa ta kasance da hikima, da hakuri.
|
4.
Sai kuma a kula da yanayin wadanda ake musu da'awar.
|
DALILI AKAN WADANNAN SHARUDDAN
Fadin Allah
Ta'alah: "KA CE: WANNAN CE HANYATA; INA KIRA ZUWA GA ALLAH; AKAN BASIRA NI
DA WADANDA SUKA BI NI, KUMA TSARKI YA TABBATA GA ALLAH, KUMA NI BAN ZAMA DAGA
CIKIN MASU SHIRKI BA" [Yusuf: 108].
"WANNAN CE HANYATA":
Abinda ake nuni da shi a nan shine abinda Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya zo da shi; na
shari'a.
"INA KIRA ZUWA GA ALLAH":
Mai yin kira zuwa ga Allah, shine Mai ikhlasin niyya wanda ke son isar da
mutane zuwa ga Allah.
"AKAN BASIRA"
Basira it ace ilimi, kuma a nan tana kunsar sanin:
1.
Sanin shari'a
|
2.
Sanin yanayin wanda kake masa da'awa
|
3.
Sanin hanyar da zata kaika ga manufarka.
|
Kai ka ce, Mawallafin yana cewa: Idan ka nemi ilimi, sa'annan ka yi aiki
da ilimin, to wajibi ne akan abinda Annabi صلى الله عليه
وسلم da Sahabbai da Magabatan kwarai suka kasance akansa, kamar
yadda Allah yake cewa:
"KA CE: WANNAN CE HANYATA; INA
KIRA ZUWA GA ALLAH; AKAN BASIRA NI DA WADANDA SUKA BI NI";
Kenan babu makawa kan da'awa.
الرَّابِعَةُ: الصَّبْرُ عَلَى الأَذَى فِيهِ.
(Mas'ala ta hudu: Hakuri kan cutarwa a
cikinsa).
وَالدَّلِيلُ
قَوْلُهُ تَعَالَى:
(وَالْعَصْرِ *
إِنَّ الإِنسَانَ لَفِي خُسْرٍ * إِلاَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا
الصَّالِحَاتِ وَتَوَاصَوْا بِالْحَقِّ وَتَوَاصَوْا بِالصَّبْرِ).
Dalili akan
abinda ya gabata shine fadinsa Madaukaki:
"INA RANTSUWA DA ZAMANI * LALLAI MUTUM
YANA CIKIN HASARA * FACE WADANDA SUKA YI IMANI, KUMA SUKA AIKATA AYYUKAN
KWARAI, KUMA SUKA YI WA JUNA WASIYYA DA BIN GASKIYA, KUMA SUKA YI WASIYYA DA
YIN HAKURI" [Asr: 1-3].
(1)
Mawallafin –Allah ya yi masa rahama- ya ambaci HAKURI bayan da'awa,
wato kamar yana ce maka: Lallai wanda zai bi hanyar da'awa, to lallai wasu
lamura (marasa dadi) za su kasance masa, kamar yadda suka kasance ga Annabawa
da Manzanni عليهم السلام; kenan babu makawa sai an yi hakuri.
HAKURI
|
Kalmar (الصبر) a
harshen Larabci: tana nufin killacewa.
|
A shari'a
kuma: Hana rai wasu abubuwa.
|
Imam
Ibnul-kayyim –رحمه الله- ya kasa hakuri zuwa kasha uku:
1.
Yin hakuri wajen biyayya ga Allah; har a iya aikata
bauta.
|
2.
Hakuri kan sabo, har a nisance su.
|
3.
Hakuri kan ababen da Allah ya kaddara masu radadi.
|
(2)
Bayan Ambato mas'alolin nan guda hudu, Sai Mawallafin –رحمه الله- ya koro
musu dalili daga littafin Allah, wanda shine suratul Asr.
Kuma lallai Mawallafin –رحمه الله- ga
dabi'arsa ya kan ambaci mas'ala, tare da dalilinta, Saboda me?
Domin ya
tarbiyyantar da 'Dalibi akan bin dalilai; ba taklidi (ko makauniyar bin
maluma) ba.
|
Har ya zama
akwai hujja a wurin 'dalibi, wanda zai iya mayar da martini ga wanda ya saba
wa gaskiya.
|
Har 'Dalibi
ya iya samun ciro hukunce-hukunce, daga dalilansu, akan lafiyayyun ka'idodi.
|
قَالَ
الشَّافِعيُّ -رَحِمَهُ اللهُ-: لَوْ مَا أَنْزَلَ اللهُ حُجَّةً عَلَى خَلْقِهِ
إِلا هَذِهِ السُّورَةَ لَكَفَتْهُمْ (1).
(Shafi'iy –رحمه الله- ya ce: Da Allah bai saukar
da wata hujja ga halittunsa ba, sai wannan sura, to da ta isar musu).
وَقَالَ
البُخَارِيُّ -رَحِمَهُ اللهُ-: بَابُ: العِلْمُ قَبْلَ القَوْلِ وَالْعَمَلِ؛
(Kuma Bukhariy –رحمه الله- ya ce: Babin da ya kunshi
bayani kan: Ilimi shine gabanin zance da aiki).
وَالدَّلِيلُ
قَوْلُهُ تَعَالَى: (فَاعْلَمْ أَنَّهُ لاَ اله إِلاَّ اللَّهُ وَاسْتَغْفِرْ
لِذَنبِكَ)[محمد:19]، فَبَدَأَ بِالْعِلْمِ قَبْلَ القَوْلِ وَالعَمَلِ) (2).
(Dalili akan
haka shine fadin Allah Ta'alah: SABODA HAKA, KA SANI, BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA, FACE ALLAH,
KUMA KA NEMI GAFARAR ZUNUBANKA) [Muhammadu:
19]. Sai Allah ya fara da batun ilimi gabanin zance da aiki).
(1)
Maksudin Mawallafin –رحمه الله- shine lallai wannan surar (wato, Asr) ita
kadai, ta wadatar wajen tsayuwar hujja akan halittu, kan su yi ilimi, su yi
aiki da shi, su yi da'awa, su yi hakuri.
(2)
Amirul-mu'uminina a ilimin hadisi; wato, Imamul Bukhariy ya kulla babi
a cikin littafinsa (na Sahihul Bukhariy) ya ce: BABIN DA KE BATU KAN YADDA
ILIMI KE RIGAYAR ZANCE DA AIKI, Sai ya ambaci dalilinsa; don haka, babu makawa,
dole sai an samu ilimi a farko gabanin zance da aiki; Kuma lallai baya inganta
bawa ya yi aiki ba tare da ilimi ba, idan kuma ya aikata hakan, to yay i
kamantacceniya da Nasara.
NA BIYU: MAS'ALOLI GUDA UKU
اعْلَمْ رَحِمَكَ اللهُ أَنَّه يَجِبُ عَلَى كُلِّ مُسْلِمٍ وَمُسْلِمَةٍ،
تَعَلُّمُ هَذِهِ الثَّلاثِ مَسَائِل، والْعَمَلُ بِهِنَّ (1):
(Ka sani, Allah ya yi maka rahama;
Lallai yana wajaba akan kowane musulmi namiji da mace, su koyi wadannan
mas'alolin guda uku, kuma su yi aiki da su).
(1)
Mawallafin ya fara magana kan
wannan bangaren ne, da yin addu'a ga 'Dalibi.
Kuma lallai Mawallafin –رحمه الله- a cikin littafin Usulus salasa, ya yi addu'a har a wurare uku
ga 'dalibi, A farkon mas'aloli guda hudu, sai kuma a nan, inda ke magana kan
mas'aloli uku, Wuri na ukun kuma shine inda ya ce: Ka sani, Allah ya shiryar da
kai zuwa ga 'da'arsa, lallai mikakken addini wato tafarkin Annabi Ibrahima...
MATASHIYA GABANIN SHARHIN MAS'ALOLIN UKU
TAUHIDI
A harshen larabci, Tauhidi –kadaita Allah-
tushen kalmar ya kadaita, yana kadaitawa, akan ce: ya kadaita abu, idan mutum
ya kudurci kasancewarsa guda daya.
|
A shari'a kuma, Tauhidi, kadaita Allah ne –سبحانه وتعالى- cikin abinda ya kebantu da su, na Rububiyyah, da Uluhiyyah,
da Sunaye da Sifofi.
|
TAUHIDI YA KASU KASHI UKU
TAUHIDUR RUBUBIYYAH
Shine kadaita Allah –سبحانه وتعالى- cikin ayyukansa.
Ko a ce:
Kadaita Allah –سبحانه وتعالى- cikin halitta, da mulki, da juya lamari.
|
TAUHIDUL ULUHIYYAH
Shine kadaita Allah –سبحانه وتعالى- da bauta.
|
TAUHIDUL ASMA'U WAS-SIFAAT
Shine, kadaita Allah cikin abinda ya sanya wa kansa, na
suna da sifa, a cikin littafinsa, ko ta harshen ManzonSa–صلى الله عليه وسلم-, ta hanyar tabbatar masa abinda ya
tabbatar wa kansa, da kore abinda ya kore wa kansa, ba tare da karkatar da
su, ko wofintar da su ba, kuma ba tare da fadar yanayinsu ko misaltawa ba.
|
Lamarin
sunayen Allah da sifofinsa abu ne da ake tsayawa kawai ga abinda ya zo cikin
littafin Allah, da sunnah; Wannan kuma ya kan kasance ta hanyar:
-
Tabbatar wa Allah abinda ya
tabbatar wa kansa, a cikin littafinsa, da kuma abinda, ManzonSa صلى الله عليه وسلم ya tabbatar masa.
-
Da kuma kore abinda Allah –سبحانه وتعالى- ya kore wa kansa, a cikin littafinsa, haka kuma ManzonSa –صلى الله عليه وسلم- ya kore masa, misalin fadinsa: "GYANGYADI
BAYA KAMA SHI, KUMA BARCI BAYA KAMA SHI" [Bakara: 255]. "KUMA 'YAR
WAHALA BATA SHAFE MU" [Kaf: 38].
Za a tabbatar masa da wadannan,
ba tare da karkatar da su, ko wofintar da su ba, kuma ba tare da fadar yanayin
sifofin ko misaltawa ba.
الأُولَى: أَنَّ اللهَ خَلَقَنَا، وَرَزَقَنَا، وَلَمْ يَتْرُكْنَا هَمَلا، بَلْ
أَرْسَلَ إِلَيْنَا رَسُولاً، فَمَنْ أَطَاعَهُ دَخَلَ الجَنَّةَ، وَمَنْ عَصَاهُ
دَخَلَ النَّارَ، وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى: (إِنَّا أَرْسَلْنَا
إِلَيْكُمْ رَسُولاً شَاهِداً عَلَيْكُمْ كَمَا أَرْسَلْنَا إِلَى فِرْعَوْنَ
رَسُولاً * فَعَصَى فِرْعَوْنُ الرَّسُولَ فَأَخَذْنَاهُ أَخْذاً وَبِيلاً)
[المزمل: 15، 16] (1).
(MAS'ALAR FARKO: Lallai Allah ya
halitta mu, kuma ya azurta mu, kuma bai bar mu kara zube ba, sai ya aiko mana
da wani Manzo; wanda ya masa biyayya ya shiga Aljannah, wanda kuma ya saba masa
ya shiga wuta).
Dalili akan haka, shine fadinSa Madaukaki:
"Lallai ne Mu, mun aiko wani Manzo zuwa gare ku, Mai
shaida akanku, kamar yadda muka aika wani Manzo zuwa ga Fir'auna * Sai Fir'auna
ya saba wa Manzon, saboda haka Muka kama shi, kamu mai tsanani" [Muzammil:
15-16].
MAS'ALOLI UKU, A
TAKAICE
MAS'ALAR FARKO:
Tauhidin Rububiyyah da Tauhidil Asma'i was sifaat
|
MAS'ALA TA BIYU:
Tauhidil Uluhiyyah
|
MAS'ALA TA UKU:
Barranta daga shirka, da ma'abutansa
|
(1)
Mas'alar farko: Mawallafin –رحمه الله- ya tabbatar wa Allah, tauhidin Rububiyyah, da Tauhidil Asma'i was
sifaat, cikin fadinsa: (Lallai Allah ya halitta mu), saboda shine Mahalicci,
(Kuma ya azurta mu) saboda shine Mai azurtawa. (Kuma bai kyale mu kara-zube
ba); babu umarni da hani ba, (Saidai ya turo mana da Manzo).
MANUFAR TURO MANZANNI –عليهم السلام-
Domin tsayar da hujja ga halittu; "BAMU
KASANCE MASU AZABTARWA BA FACE, MUN TAYAR MANZO" [Isra'i: 15].
|
Domin jin-kai da rahama, "BAMU AIKO KA BA
FACE, JIN-KAI GA TALIKAI" [Anbiya'i: 107].
|
الثَّانِيَةُ: أَنَّ الله لا يَرْضَى أَنْ يُشْرَكَ مَعَهُ أَحَدُ فِي عِبَادَتِهِ، لا
مَلَكٌ مُقَرَّبٌ، وَلا نَبِيٌّ مُرْسَلٌ؛
(MAS'ALA TA BIYU: Lallai ne Allah,
baya yarda a hada shi da wani cikin bautarsa; Mala'ika ne makusanci, ko kuma
Annabi Manzo).
وَالدَّلِيلُ
قَوْلُهُ تَعَالَى: (وَأَنَّ الْمَسَاجِدَ لِلَّهِ فَلاَ تَدْعُوا مَعَ اللَّهِ
أَحَدًا).
(Dalili akan haka kuma shine fadinSa
Madaukaki: "KUMA LALLAI WURAREN SUJJADA NA ALLAH NE; SABODA
HAKA, KADA KU ROKI WANI TARE DA ALLAH (A CIKINSU)"
[Jinn: 18]).
Dangane da
ma'anar "MASAJID a cikin ayar" akwai maganganu guda uku, kuma za a
iya hada maganganun
Masallatan da ake ginawa domin ayai bautar Allah a
cikinsu.
|
Gabban da ake yin sujjada da su.
|
Doron kasa, saboda hadisin: "Kuma an sanya min
kasa ta zama wurin sujjada, mai tsarki".
|
fadinSa: "NA ALLAH NE; SABODA HAKA, KADA
KU ROKI WANI TARE DA ALLAH (A CIKINSU)" kalmar, "WANI" tana game kowa-da-kowa, don haka ne Imam Muhammad bn Abdulwahhab
–رحمه الله-, a
farkon mas'alar ya ce: "Lallai ne Allah baya yarda a hada shi ko a masa
shirka da wani"; wato: ko-wanene shi, Annabi ne, ko Waliyyi, ko
Aljani, ko Salihi.
الثَّالِثَةُ: أَنَّ مَنْ أَطَاعَ الرَّسُولَ، وَوَحَّدَ اللهَ لا يَجُوزُ
لَهُ مُوَالاةُ مَنْ حَادَّ اللهَ وَرَسُولَهُ، وَلَوْ كَانَ أَقْرَبَ قَرِيبٍ؛ وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى: (لاَ تَجِدُ
قَوْمًا يُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ يُوَادُّونَ مَنْ حَادَّ
اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَلَوْ كَانُوا آبَاءَهُمْ أَوْ أَبْنَاءهُمْ أَوْ
إِخْوَانَهُمْ أَوْ عَشِيرَتَهُمْ أُوْلَئِكَ كَتَبَ فِي قُلُوبِهِمُ الإِيمَانَ
وَأَيَّدَهُم بِرُوحٍ مِّنْهُ وَيُدْخِلُهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا
الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ،
أُوْلَئِكَ حِزْبُ اللَّهِ، أَلاَ إِنَّ حِزْبَ اللَّهِ هُمُ الْمُفْلِحُونَ).
(MAS'ALA TA UKU: Lallai
duk wanda yay i da'a ga Manzo, kuma yay i tauhidin Allah, baya halatta a gare
shi, ya so ko ya jibinci wanda ya saba wa Allah da ManzonSa, koda kuwa dangin
da yafi kusanci ne).
Dalili kan wannan
mas'alar shine fadinSa madaukaki: "BAZA
KA SAMU MUTANEN DA SUKA YI IMANI DA ALLAH, DA RANAR KARSHE SUNA YIN SOYAYYA DA
WANDA YA SABA WA ALLAH DA MANZONSA BA; KODA KUWA SUN KASANCE UBANNINSU NE, KO
'YA'YANSU, KO 'YAN'UWANSU, KO DANGINSU, WADANNAN ALLAH YA RUBUTA IMANI A CIKIN
ZUKATANSU, KUMA YA KARFAFA SU DA WANI RUHI DAGA WURINSU, KUMA ZAI SHIGAR DA SU
ALJANNONI WADANDA KORAMU KE GUDANA KARKASHINSU, SUNA MASU DAWWAMA A CIKINSU,
ALLAH YA YARDA DA SU, KUMA SUMA SUN YARDA DA SHI, WADANNAN SUNE KUNGIYAR ALLAH,
KUMA LALLAI KUNGIYAR ALLAH SUNE MASU BABBAN RABO" [Mujadalah: 22].
Mas'ala ta uku:
Mawallafin –رحمه
الله- a cikinta ya bayyana wajabcin barranta
daga shirka da ma'abutanta.
BARRANTA
DAGA SHIRKA DA MA'ABUTANSA KAN KASANCE DA;
Da zuciya
|
Da harshe
|
Da kuma gabbai
|
1-
Da zuciya: Ta hanyar kin kafirai da idinsu, da bukukuwansu,
musamman shirkoki da bidi'oin da suke wurinsu.
2-
Da harshe: "LALLAI
NE NI, NA BARRANTA DAGA ABABEN DA KUKE BAUTAWA" [Zukhruf: 26].
"KA CE: YA
KU KAFIRAI * BA ZAN BAUTA WA ABINDA KUKE BAUTAWA BA * KUMA KU BAKU KASANCE MASU
BAUTA WA ABINDA NAKE BAUTAWA BA * KUMA NIMA BAN ZAMA MAI BAUTA WA ABINDA KUKE
BAUTAWA BA * KUMA BAKU ZAMA MASU BAUTA WA ABINDA NAKE BAUTAWA BA * SABODA
ADDININKU NAKU NE, NIMA ADDININA NAWA NE"
[Kafiruna: 1-6].
3-
Da gabbai: Ta hanyar kin tarayya da su cikin bukukuwansu da
alamomin ibada, ko tufafi, ko abinda suke kansa na akida.
NA UKU: MUHIMMANCIN KARANTA TAUHID
اعْلَمْ أَرْشَدَكَ اللهُ لِطَاعَتِهِ، أَنَّ الْحَنِيفِيَّةَ مِلَّةَ
إِبْرَاهِيمَ: أَنْ تَعْبُدَ اللهَ وَحْدَهُ، مُخْلِصًا لَهُ الدِّينَ. وَبِذَلِكَ
أَمَرَ اللهُ جَمِيعَ النَّاسِ، وَخَلَقَهُمْ لَهَا؛ كَمَا قَالَ تَعَالَى: (وَمَا
خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالإِنْسَ إِلاَّ لِيَعْبُدُونِ). وَمَعْنَى يَعْبُدُونِ: يُوَحِّدُونِ، وَأَعْظَمُ مَا أَمَرَ اللهُ
بِهِ التَّوْحيِدُ، وَهُوَ: إِفْرَادُ اللهِ بِالْعِبَادَةِ(3).
وَأَعْظَمُ مَا نَهَى عَنْه الشِّركُ، وَهُوَ: دَعْوَةُ غَيْرِهِ مَعَهُ، وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى
(وَاعْبُدُواْ اللّهَ وَلاَ تُشْرِكُواْ بِهِ شَيْئًا).
Ka sani –Allah ya
shiryad da kai zuwa ga biyayya a gare shi-, Lallai mikakken addini; tafarkin
annabi Ibrahima, shine: Ka bauta wa Allah, shi kadai, kana mai tsantsanta
addinni a gare shi, kuma da aikata haka, Allah ya umarci dukkan mutane, kuma ya
halitta su don haka, kamar yadda Allah Ta'alah ya ce: "KUMA BAMU HALITTA MUTUM DA ALJANI BA, FACE SU BAUTA MIN".
Ma'anar: "SU BAUTA MIN", shine su min tauhidi (kadaita Allah).
Kuma mafi girman abinda Allah ya yi umarni da shi, shine, Tauhidi, wanda
kuma shine: kadaita Allah a cikin bauta.
Kuma mafi girman abinda Allah ya yi hani akansa, shine shirka, wanda
kuma ita ce: Rokon wanin Allah tare da Allah.
Dalili shine fadinSa Madaukaki: "KU BAUTA WA ALLAH, KADA KU HADA SHI DA KOWA" [Nisa'i: 36].
HANIYFIYYA –addinin Annabi Ibrahim (A.S)
A harshen larabci kalmar an ciro ta ne, daga "hanaf",
mai ma'anar, karkata.
|
A shari'a kuma, "haniyfiyyah" ita ce addinin da ya
karkata, daga shirka, ya fiskanci ikhlasi da tauhidi da imani, "MAI 'DA'A NE
GA ALLAH, WANDA YA KARKATA YA BAR SHIRKA"; wato, wanda ya fiskanci Allah, ya juya baya ga shirka, saboda
kalmar "hanif" tana nufin mutumin da da'iman ke komawa ga tauhidi,
mai nisantar shirka.
|
(3)A nan Mawallafin –رحمه الله- da yake magana akan mafi
girman abinda Allah yayi umarni da shi, shine tauhidi, yana gaya mana dalilin
da ya sanya muke karanta Tauhidi ne, kuma a baya, mun yi bayanin muhimmancin
Tauhidi.
BAYANI AKAN TAUHIDI –kamar yadda muka gabatar-
A harshen larabci, Tauhidi –kadaita Allah-
tushen kalmar ya kadaita, yana kadaitawa, akan ce: ya kadaita abu, idan mutum
ya kudurci kasancewarsa guda daya.
|
A shari'a kuma, Tauhidi, kadaita Allah ne –سبحانه وتعالى- cikin abinda ya kebantu da su, na Rububiyyah, da Uluhiyyah,
da Sunaye da Sifofi.
|
Mawallafin yace: Ma'anar: "SU
BAUTA MIN", shine su min tauhidi (kadaita Allah).
Wannan maganar Abdullahi bn Abbas –رضي الله عنهما- ne,
a inda yake cewa:
إنَّ كل عبادة في القرآن معناها التوحيد، واعبدوا الله: وحدوا الله، "يأيها
الناس اعبدوا ربكم": يا أيها الناس وحدوا ربكم.
Lallai kowace ibada a
cikin Alkur'ani, ma'anarta shine: Tauhidi. "KU BAUTA WA ALLAH"; Wato, ku yi
tauhidin Allah. "YA KU MUTANE, KU BAUTA WA UBANGIJINKU"; Wato, Yak u mutane, ku kadaita Ubangijinku.
NA
HUDU: GINSHIKAI GUDA UKU
فَإِذَا
قِيلَ لَكَ: مَا الأُصُولُ الثَّلاثَةُ التِي يَجِبُ عَلَى الإِنْسَانِ
مَعْرِفَتُهَا؟
فَقُلْ:
مَعْرِفَةُ الْعَبْدِ رَبَّهُ، وَدِينَهُ، وَنَبِيَّهُ مُحَمَّدًا صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ (1).
فَإِذَا
قِيلَ لَكَ: مَنْ رَبُّكَ؟
فَقُلْ: رَبِّيَ اللهُ الَّذِي رَبَّانِي، وَرَبَّى جَمِيعَ الْعَالَمِينَ
بِنِعَمِهِ، وَهُوَ مَعْبُودِي لَيْسَ لِي مَعْبُودٌ سِوَاهُ؛ وَالدَّلِيلُ
قَوْلُهُ تَعَالَى: (الْحَمْدُ للَهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ)(2). وَكُلُّ مَنْ سِوَى اللهِ عَالَمٌ، وَأَنَا وَاحِدٌ
مِنْ ذَلِكَ الْعَالَمِ(3).
Idan aka ce maka: Menene ginshikai uku, wadanda ya zama wajibi mutum ya sansu?
Sai ka ce: Bawa, ya san UbangijinSa, da addininSa, da AnnabinSa; Muhammadu –صلى الله عليه وسلم-.
Idan aka ce maka: Wanene Ubangijinka?
Sai ka ce: Ubangijina, shine Allah, wanda ya ke rainona, kuma ya reni dukkan
talikai, da ni'imominSa, kuma shine abin bautata, bani da wani abin bauta, idan
ba shi ba.
Dalili akan haka shine
fadinSa Madaukaki:
"GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI". Kuma dukkan abinda ba Allah ba halitta ne, Ni kuma daya ne daga
cikin wadannan halittun
(1)
Mawallafin –رحمه الله- ya fara da ambaton ginshikai
guda uku, wadanda kuma sune tambayoyin kabari guda uku, kuma ya yi tambaya ne,
domin ya waigo da fadakar makaranci, ko mai sauraro da tambayar da ya jefo, Sai
kuma ya masar tambayar.
(2)
Mawallafin –رحمه الله- ya bada haske kan ginshikin
farko, a inda ya bayyana cewa, Lallai Ubangiji kuma wanda ya cancanci a masa
bauta shine Allah –سبحانه وتعالى-, sai
kuma ya ambaci dalili, wanda kuma shine fadin Allah Ta'alah: "GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI"; saboda Ubangiji shine
abin bauta.
"GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI" Wannan ayar ta hada nau'ukan tauhidi guda uku
"ALHAMDU" cikinsa akwai tabbatar wa Allah Tauhidin Asma'u was-sifaat
|
"LILLAHI" cikinsa akwai tabbatar masa da Tauhidin
Uluhiyyah.
|
"RABB" cikinsa akwai tabbatar masa da Tauhidin Rububiyyah
|
(3)
Yana nufin dukkan abinda Allah ba, halittarsa aka yi, Idan kuwa na
kasance, halitta, to dole ne na tsayu wajen godiya ga Mai halitta, Mai ni'ima,
Mai falala –سبحانه وتعالى-.
فَإِذَا
قِيلَ لَكَ: بِمَ عَرَفْتَ رَبَّكَ؟
فَقُلْ: بِآيَاتِهِ وَمَخْلُوقَاتِهِ، وَمِنْ آيَاتِهِ: اللَّيْلُ، وَالنَّهَارُ،
وَالشَّمْسُ، وَالْقَمَرُ، وَمِنْ مَخْلُوقَاتِهِ السَّمَاوَاتُ السَّبْعُ
وَالأَرَضُونَ السَّبْعُ وَمَنْ فِيهِنَّ، وَمَا بَيْنَهُمَا؛ وَالدَّلِيلُ
قَوْلُهُ تَعَالَى: (وَمِنْ آيَاتِهِ اللَّيْلُ وَالنَّهَارُ وَالشَّمْسُ
وَالْقَمَرُ لاَ تَسْجُدُوا لِلشَّمْسِ وَلاَ لِلْقَمَرِ وَاسْجُدُوا لِلَّهِ
الَّذِي خَلَقَهُنَّ إِن كُنتُمْ إِيَّاهُ تَعْبُدُونَ).
وَقَوْلُهُ
تَعَالَى: (إِنَّ رَبَّكُمُ اللّهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ فِي
سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَى عَلَى الْعَرْشِ يُغْشِي اللَّيْلَ النَّهَارَ
يَطْلُبُهُ حَثِيثاً وَالشَّمْسَ وَالْقَمَرَ وَالنُّجُومَ مُسَخَّرَاتٍ
بِأَمْرِهِ أَلاَ لَهُ الْخَلْقُ وَالأَمْرُ تَبَارَكَ اللّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ)(1).
وَالرَّبُ
هُوَ الْمَعْبُودُ، وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى: (يَا أَيُّهَا النَّاسُ
اعْبُدُواْ رَبَّكُمُ الَّذِي خَلَقَكُمْ وَالَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ
تَتَّقُونَ * الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ الأَرْضَ فِرَاشاً وَالسَّمَآء بِنَآءً
وَأَنزَلَ مِنَ السَّمَآءِ مَآءً فَأَخْرَجَ بِهِ مِنَ الثَّمَرَاتِ رِزْقاً
لَّكُمْ فَلاَ تَجْعَلُواْ لِلّهِ أَندَاداً وَأَنتُمْ تَعْلَمُونَ)(2).
قَالَ
ابْنُ كَثِيرٍ ـ رَحِمَهُ اللهُ تَعَالَى: الخَالِقُ لِهَذِهِ الأَشْيَاءَ هُوَ
الْمُسْتَحِقُّ لِلْعِبَادَةِ(3).
Idan kuma aka ce maka: Da me
ka san Ubangijinka?
Ka ce: Da ayoyinSa da halittunSa, Kuma daga cikin
ayoyinsa, akwai dare da yini, da rana da wata, Daga cikin halittunsa, akwai
sammai bakwai, da kassai bakwai, da abinda suke cikinsu da abinda suke cikinsu.
Kuma dalili shine fadinSa Madaukaki: "DAGA AYOYINSA AKWAI DARE DA YINI DA RANA DA
WATA, KADA KU YI SUJJADA GA WATA KO RANA, KU YI SUJJADA GA ALLAN DA YA HALITTA
SU, IDAN KUN KASANCE GA SHI KADAI KUKE YIN BAUTA".
Da fadinSa: "LALLAI NE UBANGIJINKU SHINE ALLAN DA YA HALITTA
SAMMAI DA KASA, A CIKIN YINI GUDA SHIDA, SA'ANNAN YA DAIDAITA A SAMAN AL'ARSHI,
YANA SHIGAR DA DARE YA RUFA YINI, YANA NEMANSA DA GAGGAWA, KUMA RANA DA WATA DA
TAURARI HORARRU NE DA UMARNINSA, KUMA HALITTA TASA CE, UMARNI NASA NE, ALBARKAR
ALLAH UBANGIJIN HALITTU TA BAYYANA".
Kuma Ubangiji shine abin bauta, dalili kuma shine fadinSa Madaukaki:
"YA KU MUTANE KU BAUTA WA
UBANGIJINKU DA YA HALITTA KU, DA WADANDA SUKE GABANINKU, DOMIN KU SAMU KARIYA *
WANDA YA SANYA MUKU KASA SHIMFIDA, SAMA KUMA GINI, KUMA YA SAUKAR DA RUWA DAGA
SAMA, SA'ANNAN YA FITAR DA ABINCI DAGA 'YA'YAN ITACE, DA SHI, SABODA KU, DON
HAKA, KADA KU SANYA WA ALLAH KISHIYOYI, ALHALI KUNA SANE".
Ibnu-kasir –رحمه الله- ya ce: "Wanda ya
halicci wadannan ababen shine ya cancanci bauta".
(1)
Mawallafin ya ambato tarin ayoyi
cikin duniya da halittu, wadanda suke nuni kan samuwar Allah, kuma suke
tabbatar da cewa, babu Ubangiji kuma babu Mahalicci, babu abin bauta, da
gaskiya face Allah, sai kuma ya kawo dalilai daga Alkur'ani, kamar yadda suka
zo cikin maganarsa.
·
Kowace halitta aya ce da take
nuna samuwar Allah –سبحانه وتعالى-, Saidai
Sheikhul Islma Muhammdu bn Abdulwahhab –رحمه الله- ya banbance tsakanin aya, da halitta, saboda aya tana
caccanzawa, misalin dare da yini, kuma wanda ke caccanza yanayi yafi karfin
dalili, akan halittar da bata canzawa.
(2)
Wanan ayar, da take cikin suratul
Bakarah, Wasu daga cikin Maluma, suka ce, a cikinta akwai kira na farko a cikin
Alkur'ani "YA KU MUTANE...", Kuma a cikinta, akwai umarni na farko
"KU YI BAUTA"; Ma'ana: Ku yi Tauhidi. Kuma a cikinta akwai, farkon hani a cikin
Alkur'ani, "KADA KU
SANYA KISHIYOYI GA ALLAH, ALHALIN KUNA SANE"; Wannan kuma hani ne kan
shirki.
(3)
Yana nufin, Wanda ya kadaitu
cikin Rububiyyah, ya zama wajibi a kadaita shi cikin Uluhiyyah.
وَأَنْوَاعُ
الْعِبَادَةِ الَّتِي أَمَرَ اللهُ بِهَا، مِثْلُ: الإِسْلامِ، وَالإِيمَانِ،
وَالإِحْسَانِ، وَمِنْهُ: الدُّعَاءُ، وَالْخَوْفُ، وَالرَّجَاءُ، وَالتَّوَكُّلُ،
وَالرَّغْبَةُ، وَالرَّهْبَةُ، وَالْخُشُوعُ، وَالْخَشْيَةُ، وَالإِنَابَةُ،
وَالاسْتِعَانَةُ، وَالاسْتِعَاذَةُ، وَالاسْتِغَاثَةُ، وَالذَّبْحُ، وَالنَّذْرُ،
وَغَيْرُ ذَلَكَ مِنْ أَنْوَاعِ الْعِبَادَةِ الَّتِي أَمَرَ اللهُ بِهَا،
كُلُّهَا للهِ تَعَالَى.
وَالدَّلِيلُ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (وَأَنَّ الْمَسَاجِدَ لِلَّهِ فَلاَ تَدْعُوا مَعَ
اللَّهِ أَحَدًا).
فَمَنْ
صَرَفَ مِنْهَا شَيْئًا لِغَيْرِ اللهِ؛ فَهُوَ مُشْرِكٌ كَافِرٌ؛ وَالدَّلِيلُ:
قَوْلُهُ تَعَالَى: (وَمَن يَدْعُ مَعَ اللَّهِ الهاً آخَرَ لاَ بُرْهَانَ لَهُ
بِهِ فَإِنَّمَا حِسَابُهُ عِندَ رَبِّهِ إِنَّهُ لاَ يُفْلِحُ الْكَافِرُونَ).
وَفِي
الْحَدِيثِ: (الدُّعَاءُ مخ الْعِبَادَةِ).
وَالدَّلِيلُ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (وَقَالَ رَبُّكُمُ ادْعُونِي أَسْتَجِبْ لَكُمْ
إِنَّ الَّذِينَ يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِي سَيَدْخُلُونَ جَهَنَّمَ
دَاخِرِينَ).
Kuma nau'ukan ibada wadanda Allah ya yi umarni da su,
misalinsu shine: musulunci, da imani, da ihsani, kuma daga cikin ibada akwai,
addu'a, tsoro, fata, tawakkali, bayyana kwadayi, da tsoro, da khushu'i, da
khashyah, da maida lamari ga Allah, da neman taimako, da neman tsari, da neman
agaji, da yanka, da bakance, da abinda wannan ba daga cikin na'ukan ibada,
wadanda Allah ya yi umarni da su, dukkansu ana yinsu ga Allah Ta'alah.
Dalili kuma shine: FadinSa Madaukaki: "KUMA LALLAI WURAREN SUJJADA NA ALLAH NE; SABODA HAKA, KADA KU ROKI WANI
TARE DA ALLAH (A CIKINSU)".
Kuma duk wanda ya aiwatar da wani abu na ibada ga wanin
Allah shi mushriki kafiri, dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "KUMA DUK WANDA YA ROKI WANI ABIN BAUTAR TARE DA,
BASHI DA HUJJA AKAN HAKA, TO LALLAI HISABINSA YANA WURIN UBANGIJINSA, KUMA
LALLAI SHA'ANIN, KAFIRAI BASA SAMUN RABO".
Ya
zo a cikin hadisi, "Addu'a itace ibada".
Dalili
kuma shine fadinSa Madaukaki: "KUMA
UBANGIJINKU YACE, KU ROKE NI, ZAN AMSA MUKU, LALLAI WADANDA SUKE GIRMAN KAI, BASA
MIN BAUTA ZASU SHIGA JANNAMA, SUNA KASKANTATTU"
Mawallafin ya yi ta'aliki ga maganar Ibnu-Kasir (da ta
gabata) ta hanyar ambato wani adadi (mai yawa) na ibadodin zuciya, da ibadodin
gabbai, tare da ambato dalilinsu daga littafin Allah, ga kowane aikin, kamar
yadda bayaninsu zai zo:
ADDU'A –kuma ya kasu zuwa kashi biyu-
ADDU'A TA IBADA
Addu'ar ibada shima kamar rokon bukata ne a fakaice,
kamar sallah da azumi da hajji.
Yin wannan addu'ar ga wanin Allah shirka ne mai girma
(da take fitarwa da ga musulunci).
|
|
ADDU'AR ROKON BUKATU
Wannan kuma shine rokon bukata, da harshe, kamar mutum
yace: Ya Allah! Ka gafarta min, Ya Allah ka mini rahama.
Hukuncin wannan addu'ar ya kasu kashi-kashi, kamar
yadda ke tafe:
|
|
ADDU'AR ROKON BUKATU TANA KASUWA KASHI BIYU NE:
Rokon abinda babu mai iko akansa in banda Allah.
Wannan kuma rokon wanin Allah shirka ne mai girma.
|
Rokon abinda bawa ke da ikon samar da shi,
Wannan yana halatta, idan aka cika sharuddan da ke
tafe:
|
Wanda za a rokan ya kasance rayayye;
Wannan ya haramta rokon ya kasance ga matacce.
|
Wanda za a rokan ya kasance halartacce;
Wannan ya haramta rokon wanda baya halarce.
|
Wanda za a rokan ya kasance yana da iko;
Wannan ya haramta rokon gajiyayye.
|
Sai kuma ya kudurta cewa, wanda yake rokonsa sababi ne
kawai, bashi da wani tasiri a karan-kansa.
|
Amma idan ya kudurta cewa wanda yake rokon, yana da wani
ikon juya abu a dukiya a boye, ko ya ji cewa, akwai wani ion janyo amfani ko
tunkude cuta a hannunsa, to wannan shirka ne.
·
Abin lura a nan:
Muna bayanin
hukunci ne akan aiki (muka ce hakan kafirci ne shirka), amma hukunci ga mutumin
da yayi aikin, shi kam yana bukatar tsayar masa da hujja, tare da kawar masa
shubuha, gabanin a kafirta shi.
Kuma Maluma
sune wadanda ke yin hukunci ga wanda ya yi aikin, suce, wannan mumini ne, ko
kafiri.
KARKASUWAN MUTANE KAN AKIDARSU DANGANE DA SABABI ZUWA
KASHI UKU
Wadanda suka sanya ko kudurta abinda Allah –سبحانه وتعالى- ya sanya shi sababi a matsayin sababi.
Wannan ya halatta.
|
Masu sanya ko kudurta abinda Allah bai sanya shi sababi
ba, sababi.
Kudurta hakan karamar shirka ce.
|
Sai wadanda suke kudurta cewa, shi sababi yana da
tasiri a karan-kansa, kuma janyo amfani da tunkude cuta tana hannun sababin.
Wannan kuma babbar shirka ne.
|
SABUBBA NA SHARI'A
Kamar karatun addu'oin ruk-ya, da yadda Allah –سبحانه وتعالى- ya sanya shi ya zama sababin dauke cuta.
|
SABUBBAN DA AKA SANI
Kamar shan magani, shima Allah ya sanya shi, a matsayin
sababin samun waraka.
|
Hadisin "Addu'a itace bargon ibada" hadisi ne mai rauni,
Wanda ya inganta shine fadin Annabi –صلى الله عليه وسلم- "Addu'a itace bauta".
Yaya addu'a zata zama itace ibada?
Aya tana nuna wannan, "UBANGIJINKU YACE: KU
ROKE NI ZAN AMSA MUKU, LALLAI NE WADANDA SUKE GIRMAN KAN BAUTA A GARE NI ZASU
SHIGA JAHANNAMA SUNA KASKANTATTU".
A nan Allah –سبحانه وتعالى- ya ce: "YIN BAUTA A GARE NI", wannan sai ya nuna cewa
lallai addu'a ibada ce.
وَدَلِيلُ الْخَوْفِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (فَلاَ تَخَافُوهُمْ
وَخَافُونِ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ) (1).
وَدَلِيلُ الرَّجَاءِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (فَمَن كَانَ يَرْجُو
لِقَاءَ رَبِّهِ فَلْيَعْمَلْ عَمَلاً صَالِحاً وَلاَ يُشْرِكْ بِعِبَادَةِ
رَبِّهِ أَحَدًا) (2).
Dalili kan ibadar tsoro shine, fadinSa Madaukaki:
"KUMA KADA KU JI TSORONSU, KU JI TSORONA IDAN KUN KASANCE MUMINAI".
Dalilin ibadar fata kuma shine fadinSa Madaukaki:
"DUK WANDA YA KASANCE YANA FATAN HADUWAR UBANGIJINSA, TO YA AIKATA AIKI
NAGARI, KUMA KADA YA HADA WANI CIKIN BAUTAR UBANGIJINSA".
(1)
TSORO: Ji ne a jika, wanda ke
kasancewa a lokacin tsammanin aukuwar abinda zai kawo halaka, ko cuta, ko
cutarwa.
Kuma hakika Allah –سبحانه وتعالى- ya yi hani, kan jin tosron majibintan Shedanu, sai kuma ya yi
umarnin a ji tsoronsa shi kadai.
TSORO KASHI UKU NE:
Tsoro na bauta da
girmamawa, a asirce
|
Tsoro na dabi'a (wanda
ake halittar bawa da shi)
|
Tsoro na haram
|
Shine tsoron mai bauta da yake
yinsa ga wanda yake bautawa, kuma a cikinsa akwai kan-kan-da kai, da
tawali'u, da girmama wanda ake masa bauta.
Wannan nau'in tsoron wajibi ne,
kautar da zuwa ga wanin Allah shirka ne babba.
|
Misalinsa shine kamar mutum ya
ji tsoron wuta, da abokin adawa, da dabbar da take farauta... ko makamancin
haka.
Wannan nau'in tsoron halal ne.
|
Misalinsa kamar tsoron da ya
kai ga debe tsammani daga rahamar Allah, ko ya ji tsoron mutum sai ya masa
biyayya cikin sabon Allah.
|
(2)
FATA: Mutum ya yi kwadayin wani lamarin
da samunsa a kusa yake, kuma zai iya kasancewa samunsa a nesa yake; amma sai ya
ajiye shi a matsayin abinda samunsa yake kusa.
Fatan da ya kunshi kan-kan-da
kai da tawali'u, baya kasancewa, sai ga
Allah –سبحانه وتعالى-.
Kuma kautar da shi ga wanin Allah
–سبحانه وتعالى- shirka ne babba.
Kuma ibadar fata abar yabo, bata
kasancewa sai ga wanda ya yi aikin biyayya ga Allah, sai ya yi fatan samun
ladanta, ko kuma ya tuba daga sabo, sai ya yi fatan karbar tubansa.
Amma fatan da aka yi ba tare da
aiki ba, to rudu ne, da guri, abin zargi.
ودَلِيلُ
التَّوَكُلِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: ( وَعَلَى اللّهِ فَتَوَكَّلُواْ إِن
كُنتُم مُّؤْمِنِينَ ). وقوله: (وَمَن يَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ فَهُوَ حَسْبُهُ)
(1).
وَدَلِيلُ
الرَّغْبَةِ، وَالرَّهْبَةِ، وَالْخُشُوعِ: قَوْلُهُ
تَعَالَى: (إِنَّهُمْ كَانُوا يُسَارِعُونَ فِي الْخَيْرَاتِ وَيَدْعُونَنَا
رَغَباً وَرَهَباً وَكَانُوا لَنَا خَاشِعِينَ ) (2).
Dalilin Tawakkali shine fadinSa Madaukaki: "GA ALLAH NE, ZA
KU DOGARA, IDAN KUN KASANCE MUMINAI".
Da fadinSa: "KUMA DUK WANDA YA
DOGARA GA ALLAH, TO YA ISAR MASA".
Dalilin ibadar kwadayi da fargaba da khushu'i, shine
fadinSa Madaukaki: "LALLAI NE, SU, SUN KASANCE SUNA YIN SAURIN
AIKATA ALKHAIRORI, KUMA SUNA ROKONMU CIKIN KWADAYI DA FARGABA, KUMA SUN KASANCE
A GARE MU MASU KHUSHU'I".
(1)
Hakikanin Tawakkali
A harshen larabci: Tawakkali
ga abu na nufin, dogaro akansa.
|
A shari'a kuma: Tawakkali,
shine gaskiyar dogaro ga Allah, tare da amintuwa da Allah, da riko da sabubba
na shari'a.
|
BABU MAKAWA SAI LAMURA
UKU SUN TABBATA GA TAWAKKALI
Gaskiya cikin dogaro ga Allah –سبحانه وتعالى-.
|
Amintuwa da Allah –سبحانه وتعالى- cewa zai cika abinda ya alkawarta.
|
Riko da sabubban
shari'a.
|
(2)
Ibadar kwadayi: Son isa
zuwa ga abinda kake so.
Ibadar fargaba: ita ce,
nau'in tsoron da ke haifar da gujewa abinda kake tsoro, don haka
"Rahbah" tsoro ne da ke hade da aiki.
Ibadar khushu'i: Kan-kan-da
kai ne da ke cakude da jin girman Allah, ta yadda mutum zai mika-wuya ga abinda
Allah ya hukunta na kaddara, da shari'a.
·
Mai tafiya zuwa ga Allah –سبحانه وتعالى- babu makawa, sai ya hada tsakanin ibadar tsoro da fata, kuma
ba zai rinjayar da sashe akan sashe ba; tsoron kada ya samu zamiya sai ya
halaka; don haka babu makawa sai an samu ibadar tsoro da fata a wurinsa, kuma
kamar fukafikan tsuntsu biyu suke a gare shi.
وَدَلِيلُ الْخَشْيَةِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (فَلاَ تَخْشَوْهُمْ
وَاخْشَوْنِي...) الآية.
وَدَلِيلُ الإِنَابَةِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (وَأَنِيبُوا إِلَى
رَبِّكُمْ وَأَسْلِمُوا لَهُ...) الآية.
وَدَلِيلُ الاسْتِعَانَةِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (إِيَّاكَ نَعْبُدُ وإِيَّاكَ
نَسْتَعِينُ). وَفِي الْحَدِيثِ: (...وإِذَا اسْتَعَنْتَ فَاسْتَعِنْ بِاللهِ).
وَدَلِيلُ
الاسْتِعَاذَةِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ). وَ(قُلْ
أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ).
وَدَلِيلُ الاسْتِغَاثَةِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (إِذْ تَسْتَغِيثُونَ
رَبَّكُمْ فَاسْتَجَابَ لَكُمْ...) الآية.
وَدَلِيلُ
الذَّبْحِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (قُلْ إِنَّنِي هَدَانِي رَبِّي إِلَى
صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ دِيناً قِيَماً مِّلَّةَ إِبْرَاهِيمَ حَنِيفاً وَمَا كَانَ
مِنَ الْمُشْرِكِينَ * قُلْ إِنَّ صَلاَتِي وَنُسُكِي وَمَحْيَايَ وَمَمَاتِي
لِلّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ * لاَ شَرِيكَ لَه وَبِذَلِكَ أُمِرْتُ وَأَنَا
أَوَّلُ الْمُسْلِمِينَ). وَمِنَ السُنَّةِ: (لعَنَ اللهُ مَنْ ذَبَحَ لِغَيْرِ
اللهِ).
Dalilin ibadar tsoro: shine fadinSa Madaukaki:
"KADA KU JI TSORONSU, KU JI TSORONA" (1).
Dalilin ibadar maida lamari ga Allah: shine
fadinSa Madaukaki: "KUMA KU MAYAR DA LAMARI ZUWA GA ALLAH, KU MIKA
WUYA A GARE SHI"(2).
Dalilin ibadar neman taimako: shine fadinSa
Madaukaki: "A GARE KA MUKE YIN BAUTA, KUMA DAGA GARE KA MUKE NEMAN
TAIMAKO".
Ya zo cikin hadisi: "Idan zaka nemi taimako,
ka nemi taimakon Allah"(3).
Dalilin ibadar neman tsari: shine fadinSa
Madaukaki: "KA CE: INA NEMAN TSARIN UBANGIJIN SAFIYA".
Da "KA CE: INA NEMAN TSARIN UBANGIJIN MUTANE"(4).
Dalilin ibadar neman agaji: shine fadinSa
Madaukaki: "A YAYIN DA KUKE NEMAN AGAJIN UBANGIJINKU, SAI YA AMSA
MUKU"(5).
Dalilin ibadar bakance: shine fadinSa Madaukaki:
"KA CE: LALLAI NE SALLATA DA YANKANA, DA RAYUWATA, DA MUTUWATA, NA ALLAH NE
UBANGIJIN TALIKAI * BASHI DA ABOKIN TARAYYA".
Ya zo cikin sunnah: "Allah ya tsine wa wanda ya yi
yanka, ga wanin Allah"(6).
(1)
Ibadar khashyah: Shine
tsoron da ya ginu akan ilimi ko sanin girman wanda ake tsoronsa da sanin
cikakken ikonsa.
(2)
Ibadar inabah: Shine
komawa ga Allah Ta'alah; ta hanyar yin da'a a gare shi, da nisantar saba masa, saboda
ma'anar "Wa aniybuw" shine, ku koma "zuwa ga Ubangijinku";
ta hanyar sallama lamarinka ga Allah –سبحانه وتعالى-; saboda kai bawansa ne, shi kuma bawa babu makawa dole ya
sallamawa shugabansa, shugaban kuma shine Allah, kamar yadda Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Shugaba shine Allah".
(3)
Ibadar isti'anah: tana
nufin, neman taimako, "A KAI KADAI MUKE BAUTAWA, KUMA A GARE KA MUKE
NEMAN TAIMAKO". A cikin wannan ayar an gabatar da abinda hakkinsa shine a jinkirta
shi, wannan kuma yana nuni kan takaicewa, wato, Baza mu yi bauta ba, sai a gare
ka, kuma baza mu nemi taimako ba, sai a wurinka.
(4)
Ibadar isti'azah: tana
nufin, neman tsari, daga abin ki, saboda kalmar "A'uzu" tana nufin, ina
neman mafaka, ina neman kariya.
(5)
Ibadar istigasah: tana
nufin, neman agazawa, wanda kuma shine tsamar da mutum daga tsanani da halaka.
Ibadodin neman taimako, da
neman tsari da neman agaji da ceto, ya halatta a neme su daga halitta cikin
abinda ke da iko akansa, da sharudda guda hudu; wato ya zama rayayye,
halartacce, mai iko, kuma kudurta shi sababi ne.
|
(6)
Ibadar yanka: Fitar da
rai, ta hanyar zubar da jinin dabba, a wani yanayi kebantacce.
YANKA YA KASU KASHI UKU
Yanka don Allah, kamar hadaya, da
lahiya, da yanka domin sadaka.
|
Yanka ba don Allah ba, cikin so da
girmamawa, kamar yanka wa Aljanu, da ma'abuta kabari.
Wannan shirka ne babba.
|
Yanka na halal, kamar yanka akuya don
cin nama, ko girmama bako, ko yanka domin sayar da nama.
|
·
Abin lura: Akwai karin bayani kan
mas'alar yanka, wanda zai zo a littafin Tauhid, da izinin Allah.
وَدَلِيلُ
النَّذْرِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (يُوفُونَ بِالنَّذْرِ وَيَخَافُونَ يَوْماً
كَانَ شَرُّهُ مُسْتَطِيرًا).
Dalilin ibadar bakance: shine fadinSa Madaukaki:
"SUNA CIKA BAKANCE, KUMA SUNA TSORON YININ DA SHARRINSA KE YADUWA" (1).
(1)
HAKIKANIN BAKANCE (ALWASHI)
A harshen larabci: nazr
yana nufin, alkawartawa da lazimtawa.
|
A shari'ance: Bakance,
shine mai hankali ya lazimta wa kansa wani abinda ba wajibi ba ne, akansa.
|
·
Abin lura: Bakance yana da kashe-kashe,
da sharudda, da kaffara, wanda karin bayani akansu zai zo a littafin Tauhid, da
izinin Allah.
NAU'UKAN BAKANCE
Alwashi don Allah
|
Alwashi da bakance ga wanin Allah
|
·
Mawallafin, ya ambaci ibadodin da
suka gabata, ba wai a matsayin sune kadai ibadodi ba, saidai a matsayin misali,
domin akwai dinbin ibadodin da ba a ambata ba. Saidai kuma darasin a nan shine,
duk wanda ya kautar da wani abu na wadannan ibadodin ko wasunsu ga wanin Allah,
to lallai ya yi shirka.
الأَصْلُ الثَّانِي:
مَعْرِفَةُ دِينِ الإِسْلامِ بِالأَدِلَّةِ.
وَهُوَ: الاسْتِسْلامُ للهِ بِالتَّوْحِيدِ، وَالانْقِيَادُ لَهُ
بِالطَّاعَةِ، وَالْبَرَاءَةُ مِنَ الشِّرْكِ وَأَهْلِهِ، وَهُوَ ثَلاثُ
مَرَاتِبَ: الإسْلامُ، وَالإِيمَانُ، وَالإِحْسَانُ. وَكُلُّ مَرْتَبَةٍ لَهَا
أَرْكَانٌ.
المرتبة الأولى: الإسلام(1). فَأَرْكَانُ الإِسْلامِ خَمْسَةٌ: شَهَادَةُ أَن لا
اله إِلا اللهُ(2)، وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ، وَإِقَامُ
الصَّلاةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ، وَصَوْمُ رَمَضَانَ، وَحَجُّ بَيْتِ اللهِ
الْحَرَامِ.
ASALI NA BIYU: SANIN
ADDININ MUSULUNCI, DA DALILAI.
SHINE, Mika wuya ga Allah, da tauhidi, da jawuwa gare shi da da'a, da barranta
daga shirka da ma'abutansa.
Kuma addini martabobi
uku ne, musulunci, da imani, da ihsani. Kuma kowace martaba tana da rukunnai.
Martabar farko:
Musulunci.
Kuma rukunnan
musulunci guda biyar ne:
Shaidawa babu anin bautawa
da gaskiya sai Allah, kuma annabi Muhammadu manzon Allah ne, da tsayar da
sallah, da bada zakkah, da azumin ramadhana, da hajjin dakin Allah mai alfarma.
(1)
Mawallafin
ya shiga Magana kan ginshiki na biyu, wanda shine, bawa ya san
addininsa, sai kuma ya fara bayanin hakikanin musulunci, a inda y ace:
MARTABAR FARKO: MUSULUNCI
Mika wuya ga Allah, da tauhidi, da jawuwa gare shi da da'a, da
barranta daga shirka da ma'abutansa.
|
Wannan shine hakikanin musulunci; wato, ka sallama lamarinka ga Allah –سبحانه وتعالى- saboda
kai bawa ne, kuma bawa dole ne ya sallama ga shugabansa, shugaban kuma shine
Allah, kamar yadda Annabi –صلى الله عليه وسلم-.
Sa'annan sai ya kasa addini izuwa ga martabobi guda uku:
(2)
Rukunnan
musulunci guda biyar ne, Na farkonsu:
Kalmar
shahada
فَدَلِيلُ الشَّهَادَةِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (شَهِدَ اللّهُ أَنَّهُ
لاَ اله إِلاَّ هُوَ وَالْمَلاَئِكَةُ وَأُوْلُواْ الْعِلْمِ قَآئِمَاً
بِالْقِسْطِ لاَ اله إِلاَّ هُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ).
وَمَعْنَاهَا: لا مَعْبُودَ بِحَقٍّ إلا اللهُ، لا إله نَافِيًا جَمِيعَ
مَا يُعْبَدُ مِنْ دُونِ اللهِ.
إِلا اللهُ مُثْبِتًا الْعِبَادَةَ للهِ وَحْدَهُ لا شَرِيكَ لَهُ فِي
عِبَادَتِهِ، كَمَا أَنَّهُ لَيْسَ لَهُ شَرِيكٌ فِي مُلْكِهِ.
وَتَفْسِيرُهَا
الَّذِي يُوَضِّحُهَا قَوْلُهُ تَعَالَى: (وَإِذْ قَالَ إِبْرَاهِيمُ لأَبِيهِ
وَقَوْمِهِ إِنَّنِي بَرَآء مِّمَّا تَعْبُدُونَ * إِلاَّ الَّذِي فَطَرَنِي
فَإِنَّهُ سَيَهْدِينِ * وَجَعَلَهَا كَلِمَةً بَاقِيَةً فِي عَقِبِهِ لَعَلَّهُمْ
يَرْجِعُونَ).
Dalilin Kalmar shahada shine
fadinSa Madaukaki: "ALLAH YA SHAIDA CEWA: LALLAI
NE BABU ABIN BAUTAWA DA CANCANTA FACE SHI, KUMA MALA'IKU DA MA'ABUTA ILIMI SUN
SHAIDA, YANA TSAYE DA ADALCI, BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA FACE SHI, MABUWAYI
MAI HIKIMA".
Kuma ma'anar kalmar (LA ILA ILLAL LAHU)
shine babu abin bautawa da cancanta, face Allah, saboda "LA ILAHA"
tana kore cancanta ne ga dukkan ababen da ake bauta musu, koma bayan Allah.
"ILLAL LAHU" kuma, yana tabbatar da
cancantar bautan ne ga Allah shi kadai; bashi da abokin tarayya cikin bautarsa,
kamar yadda bashi da abokin tarayya cikin mulkinsa.
Kuma tafsirin (LA
ILAHA ILLAL LAHU) wanda ke fito da ma'anarta a sarari shine, fadinSa Madaukaki:
"KA AMBATA, LOKACIN DA IBRAHIMU YA CE GA BABANSA DA
MUTANENSA, LALLAI NE NI NA BARRANTA DAGA ABINDA KUKE BAUTAWA * FACE WANDA YA
KAGI HALITTA TA, LALLAI SHINE ZAI SHIRYAR DA NI * KUMA YA SANYA (WANNAN
MAGANAR) KALMA MAI WANZUWA, A CIKIN ZURIYARSA TSAMMANINSU SU KOMA DAGA BATA".
A wannan wuri, Sai
Mawallafin –رحمه
الله- ya ambaci dalilin Kalmar shahada (LA
ILAHA ILLAL LAHU), ya kuma bayyana hakikanin ma'anarta, a inda yace:
BABU ABIN BAUTAWA DA
GASKIYA SAI ALLAH
Don haka; babu makawa
Kalmar shahada sai ta kunshi
Korewa da ya zo cikin
"LA ILAHA".
Tabbatarwa, wanda ya
zo cikin fadin "ILLAL LAHU".
Kuma wannan sigar,
tana nuna takaicewa, da tabbatarwa; ta yadda ta takaice, kuma ta tabbatar da
cancantar bauta ga Allah; shi kadai, kuma take kore ta ga wanin Allah, don haka
ne, Mawallafin –رحمه الله- ya ce: Kuma tafsirin (LA
ILAHA ILLAL LAHU) wanda ke fito da ma'anarta a sarari shine, fadinSa Madaukaki:
"KA AMBATA, LOKACIN DA IBRAHIMU YA CE GA BABANSA DA
MUTANENSA, LALLAI NE NI NA BARRANTA DAGA ABINDA KUKE BAUTAWA * FACE WANDA YA
KAGI HALITTA TA".
"NA
BARRANTA DAGA ABINDA KUKE BAUTAWA"
wannan shine ma'anar "LA ILAHA".
"FACE
WANDA YA KAGI HALITTA TA" Wannan shine ma'anar "ILLAL LAHU".
وقَوْلُهُ
تَعَالَى: (قُلْ يَا أَهْلَ الْكِتَابِ تَعَالَوْاْ إِلَى كَلَمَةٍ سَوَاءٍ
بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمْ أَلاَّ نَعْبُدَ إِلاَّ اللّهَ وَلاَ نُشْرِكَ بِهِ
شَيْئاً وَلاَ يَتَّخِذَ بَعْضُنَا بَعْضاً أَرْبَاباً مِّن دُونِ اللّهِ فَإِن
تَوَلَّوْاْ فَقُولُواْ اشْهَدُواْ بِأَنَّا مُسْلِمُونَ) (1).
Da fadinSa: "KA
CE, YA KU MA'ABUTA LITTAFI, KU TAFO, ZUWA GA KALMA MAI DAIDAITAWA, A TSAKANINMU
DA KU, KADA MU BAUTA WA KOWA, FACE ALLAH, KUMA KADA MU HADA KOME DA SHI, KUMA
KADA SASHENMU YA RIKI SASHE, UBANGIJI, BAICIN ALLAH, IDAN KUMA SUKA BIJIRE, SAI
KACE: KU YI SHAIDA CEWA, LALLAI NE MU MASU SALLAMAWA NE".
·
Da mai yin magana
zai ce: Hakikanin shaidawa babu abin bautawa, da gaskiya sai Allah, shine babu
wanda ake bauta masa face Allah?
Sai mu ce,
wannan maganar kuskure ce, saboda idan yace duk abinda ake bauta masa Allah ne,
kenan yana halatta yin bauta ga dukkan ababen bautawa. Saidai idan ya ce, abin
bautawa da cancanta, to wannan dalili ne na cewa, ya kafirce kuma baya tare da
dukkan ababen bautawa wadanda wasu suke bauta musu, koma bayan Allah, kuma yana
jin cewa babu wanda ake masa bauta da gaskiya ko cancanta face Allah.
·
Da mai magana
zai ce: ma'anar LA ILAHA ILLAL LAHU, shine babu Ubangiji Mahalicci na gaskiya
face Allah?
Sai muce: Wannan
maganar gaskiya ce, saidai kuma ba itace ma'ana ko tafsirin LA ILAHA ILLAL LAHU
ba, domin babu Mahalicci sai Allah, tauhidin Rububiyyah ne, wanda kafiran da
aka tayar da Annabi –صلى الله عليه وسلم- a cikinsu, suka yarda da shi, saidai
hakan bai shigar da su cikin musulunci ba.
(1)
"KA
CE, YA KU MA'ABUTA LITTAFI, KU TAFO, ZUWA GA KALMA MAI DAIDAITAWA, A TSAKANINMU
DA KU" Wannan ayar ta nuna cewa, akidar masu kawo kusanci tsakanin addinai kuskure ce.
وَدِليلُ
شَهَادَةِ أَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (لَقَدْ
جَآءكُمْ رَسُولٌ مِّنْ أَنفُسِكُمْ عَزِيزٌ عَلَيْهِ مَا عَنِتُّمْ حَرِيصٌ
عَلَيْكُم بِالْمُؤْمِنِينَ رَؤُوفٌ رَّحِيمٌ).
وَمَعْنَى
شَهَادَة أَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ: طَاعَتُهُ فِيمَا أَمَرَ، وَتَصْدِيقُهُ
فِيمَا أَخْبَرَ، واجْتِنَابُ مَا نَهَى عَنْهُ وَزَجَرَ، وأَلا يُعْبَدَ اللهُ
إِلا بِمَا شَرَعَ.
Dalili akan shaidawa lallai annabi Muhammadu manzon Allah ne,
shine fadinSa Madaukaki: "HAKIKA
WANI IRIN MANZO DAGA CIKIN KAYUKANKU YA ZO MUKU, ABINDA KE WAHALAR DA KU YANA
BUWAYARSA, KUMA MAI KWADAYI NE A GARE KU, GA MUMINAI KUMA MAI TAUSHI NE, MAI
JIN KAI".
Ma'anar shaidawa lallai annabi Muhammadu manzon Allah ne, shine: Yin
da'a a gare shi cikin abinda yayi umarni, da gaskata shi cikin abinda ya bada
labari, da nisantar abinda ya yi hani akansa; ya tsawatar, da cewar kada a
bauta wa Allah sai da abinda wannan annabin ya kawo na shari'a.
(1)
Mawallafin –رحمه الله- ya ambaci wannan ayar a
matsayin dalili kan shaidawa lallai annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- Manzon Allah ne, kuma lallai
Allah ya karfafa wannan shaidar a cikin ayar da abubuwa uku na karfafa zance,
sune: rantsuwar da ake kaddara ta, harafin, da kalmar "kad; wato lallai
hakika".
(2)
Mawallafin –رحمه الله- ya bayyana, hakikanin
ma'anar shaidawa lallai Annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- manzon Allah ne, da cewar lallai yana
wajaba, ga kowane musulmi namiji da mace, domin tabbatar da wannan kalma;
Yin da'a a gare shi cikin abinda yayi
umarni, da gaskata shi cikin abinda ya bada labari, da nisantar abinda ya yi
hani akansa; ya tsawatar, da cewar kada a bauta wa Allah sai da abinda wannan
annabin ya kawo na shari'a, kuma ya bayyana, salatin Allah da sallamarSa, su
kara tabbata a gare shi.
Abinda shaidawa lallai Annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- manzon Allah ne ke
hukuntawa, shine lallai shi, bawa ne da ba za a bauta mas aba, kuma manzo ne da
ba za a karyata shi ba, Wannan kuma yana hukunta:
Mu yi da'a a gare shi cikin dukkan
abinda yay i umarni da shi –صلى الله عليه وسلم-.
Saboda shi mai isar da sako ne daga Allah.
|
Gaskata shi, cikin abinda ya bada
labari –صلى
الله عليه وسلم-.
Saboda shi mai gaskiya ne, abin gaskatawa –صلى الله عليه وسلم-.
|
Nisantar abinda ya yi hani, kuma ya yi
tsawa;
Ta hanyar ka sanya abinda Annabi –صلى الله عليه وسلم-
ya yi hani akansa ta bangare guda, kai kuma ta wani bangare.
|
Kada a bauta wa Allah –سبحانه وتعالى- sai da abinda Annabi –صلى الله عليه وسلم-
ya zo da shi;
Cikin wannan kuma akwai raddi ko maida martini ga
masu kirkiro addini ('Yan bidi'a).
|
وَدَلِيلُ الصَّلاةِ، وَالزَّكَاةِ، وَتَفْسِيرُ التَّوْحِيدِ:
قَوْلُهُ تَعَالَى: (وَمَا أُمِرُوا إِلاَّ لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ
الدِّينَ حُنَفَآءَ وَيُقِيمُوا الصَّلاةَ وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ وَذَلِكَ دِينُ
الْقَيِّمَةِ)(1).
ودَلِيلُ الصِّيَامِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (يَا أَيُّهَا الَّذِينَ
آمَنُواْ كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ
لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ)(2).
ودَلِيلُ الْحَجِّ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (وَلِلّهِ عَلَى النَّاسِ
حِجُّ الْبَيْتِ مَنِ اسْتَطَاعَ إِلَيْهِ سَبِيلاً وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ الله
غَنِيٌّ عَنِ الْعَالَمِينَ)(3).
Kuma dalili kan sallah da zakkah da kuma fassarar tauhidi shine
fadinSa Madaukaki: "BA A UMARCE SU DA KOMAI BA,
FACE BAUTA WA ALLAH SUNA MASU TSARKAKE ADDININSU A GARE SHI KUMA MASU KARKATA
ZUWA ADDINI GASKIYA, KUMA SU TSAYAR DA SALLAH, SU BADA ZAKKAH, KUMA WANNAN
SHINE ADDINI MIKAKKE".
Kuma dalilin azumi shine fadinSa Madaukaki: "YA
KU WADANDA SUKA YI IMANI, AN WAJABTA MUKU AZUMI KAMAR YADDA AKA WAJABTA SHI GA
WADANDA KE GABANINKU, LA'ALLA KO ZA KU SAMU TAKAWA".
Kuma dalilin hajji shine fadinSa Madaukaki: "KUMA
ALLAH YA WAJABTA WA MUTANE HAJJIN DAKINSA GA WANDA YA SAMU HANYAR ZUWA GARE
SHI, KUMA WANDA YA KAFIRCE, TO LALLAI ALLAH YA WADATA DAGA TALIKAI".
(1)
RUKUNI NA BIYU:
SHINE SALLAH:
Sallah itace, Bauta wa Allah ta hanyar
aikata ayyuka da zantuka kebantattu, wadanda ake fara su da kabbara, a gama su
da yin sallama, kuma itace kashin bayan wannan addinin, kuma hakika an farlanta
ta, daga Allah –kai tsaye- zuwa ga AnnabinSa –صلى الله عليه وسلم-, a lokacin da aka yi mi'iraji aka tafi
sama da shi.
RUKUNI NA UKU: ZAKKAH:
A harshen larabci, zakkah tana nufin,
bunkasa abu da tsarkake shi.
Kuma zakka nau'uka biyu ce, zakkar
jiki, da zakkar cikin dukiya.
(2)
RUKUNI NA HUDU:
AZUMI:
Azumi, a harshen larabci, na nufin
kamewa.
A shari'a kuma, ana wani bauta ne ga
Allah, ta hanyar kamewa daga ababen da suke karya azumi, tare da niyya, daga
ketowar alfijir, zuwa ga faduwar rana.
Kuma azumi yana daga cikin mafi falalar
na'ukan ibadodi; domin tattaruwan nau'ukan hakuri guda uku, kuma saboda girman
sha'anin azumi ne, ya sanya Allah –سبحانه وتعالى- ya nasabta wa kansa, bada sakamako ga mai
azumi.
(3)
RUKUNI NA BIYAR:
HAJJI:
Hajji, a harshen larabci, yana nufin,
ka nufi wani wuri.
A shari'a kuma, Hajji bauta ne ga
Allah, ta hanyar zartar da wasu ayyukan harama, daidai da yadda sunnar Annabi –صلى الله عليه وسلم- ta zo da shi.
Kuma hajji, farilla ne aka kowane
musulmi, ya yi shi sau daya a tsawon rayuwarsa.
الْمَرْتَبَةُ
الثَّانِيَةُ: الإِيمَانُ، وَهُوَ: بِضْعٌ
وَسَبْعُونَ شُعْبَةً، فَأَعْلاهَا قَوْلُ لا اله إِلا اللهُ، وَأَدْنَاهَا
إِمَاطَةُ الأَذَى عَنِ الطَّرِيقِ، وَالْحَيَاءُ شُعْبَةٌ مِنْ الإِيمَانِ.
وَأَرْكَانُهُ
سِتَّةٌ: كما في الحديث (أَنْ تُؤْمِنَ بِاللهِ، وَمَلائِكَتِهِ، وَكُتُبِهِ،
وَرُسُلِهِ، وَالْيَوْمِ الآخِرِ، وَتُؤْمِنَ بِالْقَدَرِ خَيْرِهِ وَشَرِّهِ).
وَالدَّلِيلُ
عَلَى هَذِهِ الأَرْكَانِ السِّتَةِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (لَّيْسَ الْبِرَّ
أَن تُوَلُّواْ وُجُوهَكُمْ قِبَلَ الْمَشْرِقِ وَالْمَغْرِبِ وَلَكِنَّ الْبِرَّ
مَنْ آمَنَ بِاللّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ وَالْمَلآئِكَةِ وَالْكِتَابِ
وَالنَّبِيِّينَ).
ودليل القدر:
قَوْلُهُ تَعَالَى: (إِنَّا كُلَّ شَيْءٍ خَلَقْنَاهُ بِقَدَرٍ).
MARTABA TA BIYU: ITACE; IMANI;
Kuma imani sifofi ko rassa saba'in da wani abu ne, mafi kololuwarsu
shine, fadin LA ILAHA ILLAL LAHU, Kuma mafi kankantarsu itace, kautar da abu
mai cutarwa daga hanya, Kuma kunya reshe ne na imani.
Kuma rukunnan imani guda shida ne, kamar yadda ya zo cikin
hadisi, "Ka yi imani da Allah, da Mala'ikunSa, da LittatafanSa, da
ManzanninSa, da Ranar karshe, kuma ka yi imani da kaddara na alkhairinsa da
sharrinsa".
Kuma dalili akan wadannan rukunnan guda shida, fadinSa Madaukaki: "BA
KAWAI SHINE ADDINI BA, KU JUYAR DA FISKOKINKU, WAJEN GABAS KO YAMMA BA, AMMA
ADDINI SHINE GA WANDA YA YI IMANI DA ALLAH, DA RANAR KARSHE, DA MALA'IKU, DA
LITTATAFAI, DA ANNABAWA".
Kuma dalilin kaddara FadinSa Madaukaki: "LALLAI
NE MU, KOWANE ABU MUN HALICCE SHI DA KADDARA".
Martaba ta biyu: Imani
Imani a harshen larabci: Sakankancewa
cikin gaskatawa.
A shari'a kuma: Imani zance ne na harshe,
da kudurin zuci, da aikin gabbai –har da zuciya-, yana karuwa da aikin da'a,
kuma yana tawaya da sabo.
|
Shi imani na shari'a babu makawa, sai ya hada lamura guda biyar.
Ta yadda idan daya daga cikinsu ya samu tasgaro, to an fita daga
hakikanin imani, a wurin Ahlus-Sunnah wal Jama'ah.
Menene dalili akan wadannan lamuran
guda biyar?
Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "mafi kololuwarsu shine,
fadin LA ILAHA ILLAL LAHU", wannan dalili ne, akan zancen baka.
"mafi kankantarsu itace, kautar da abu mai cutarwa daga hanya",
wannan kuma aikin gabbai.
"Kunya kuma…", wannan aikin zuciya ne.
Da fadinSa Madaukaki: "WANENE
DAGA CIKINKU WANNAN SURAR TA KARA MASA IMANI?" WAnnan
dalili ne akan mas'alar karuwar imani, to kuma idan ya zama yana karuwa, to
babu makawa zai samu tawaya, kuma batun tawayar addini ya zo karara, cikin
fadinSa –صلى الله عليه وسلم-:
"Ban ga masu tawayar hankali da addini ba,…", wannan ya nuna addini
yana samu tawaya, ko nakasa.
RUKUNNAN IMANI GUDA SHIDA
Imani da Allah
|
Imani da Mala'iku
|
Imani da littatafai
|
Imani da Manzanni
|
Imani da Ranar karshe
|
Imani da kaddara mai kyansa da
mummunansa
|
RUKUNIN FARKO: IMANI DA ALLAH, yana
hukunta lamura guda hudu:
Imani da samuwar Allah –سبحانه وتعالى-,
kuma yak an kasance da lamura guda hudu:
|
Imani da tauhidin Rububiyyah
|
Imani da Tauhidin Uluhiyyah
|
Imani da Tauhidin sunaye da siffofi
|
Da dalilan
hankali
Saboda ahankalce ba zai yiwu ayi tunanin samun
halitta ba tare da samuwar wanda ya halicce shi ba, "KO AN HALITTA SU BA DA WANI ABU BA NE, KO KUMA SUNE MASU HALITTAR?".
|
Da dalilai
da ake iya ji ko gani, saboda mutum yakan iya kasancewa
cikin bakin ciki da tsanani, sai ya daga hannayensa sama yana cewa, Ya
Ubangijina, sai wannan bacin ran yak au, da izinin Allah –سبحانه وتعالى-.
|
Da dalilai
na halitta; saboda "kowane halitta aka haifuwarsa akan
akidar musulunci, iyayensa biyu suke mayar da shi bayahude ko banasare, ko
bamajuse".
|
Da dalilai
na shari'a; Ibnul kayyim –رحمه الله- ya ambata cewa, lallai babu wata aya a
cikin littafin Allah, face a cikinta akwai dalili akan tauhidi.
|
RUKUNI NA BIYU: IMANI DA MALA'IKU
Mala'iku: Halittu ne da
suke boye, Allah ya halitta su daga haske, suna yin da'a wa Allah basa saba
masa, suna da rayuka "RUHI MAI TSARKI",
da gangan jiki "YA SANYA MALA'IKU JAKADODI, MA'ABUTA FUKA-FUKAI,
BIBBIYU, DA UKU-UKU, DA HUDU-HUDU, YANA YIN KARI CIKIN HALITTA, DA ABINDA YA YI
NUFI", Suna da hankula da zukata, "HAR
IDAN AKA JIJJIGA ZUKATANSU SAI SUCE, MENENE UBANGIJINKU YA FADA?".
Muna yin imani da Mala'iku, da kuma abinda Allah ya sanar da mu na sunayensu,
(kamar Jibrilu, da Mika'ilu, da Isra'ila), da sifofinsu (BASU
SABA WA ALLAH CIKIN ABINDA YA UMARCE SU, KUMA SUNA AIKATA DUKKAN ABINDA AKA
UMARCE SU), da ayyukansu (misalin, daukar al'arshi), da dukkan labarum da suka
zo, a kansu, a dunkule, da labaru na dalla-dalla.
RUKUNI NA UKU: IMANI DA LITTATAFAI:
Ya wajaba muyi imani da
cewa, littatafan maganar Allah ne, hakikatan, kuma lallai littatafan saukakku
ne ba halitta ba, kuma lallai Allah ya saukar da littafi ga kowani manzo, sai
mu yi imani da littatafan, da dukkan abinda Allah ya bamu labara na sunayensu
da labarum littatafan da hukunce-hukuncen da suka kunsa, a dunkule, da na
dalla-dalla, matukar ba a soke yin aiki da su ba. Kuma sai mu yi imani cewa,
Alkur'ani ya soke dukkan abinda ke gabaninsa na littatafai, wadanda sune, Attaurah,
Injila, Zabura, da Takardun annabi Ibrahima, da takardun annabi Musa –عليهما السلام-.
RUKUNI NA HUDU: IMANI DA MANZANNI
Wajibi ne, mu yi imani da
cewar Manzanni mutane ne, basu da wani komai daga cikin sifofin Ubangiji, kuma
lallai su bayi ne na Allah, ba a yin bauta a gare su, kuma lallai Allah ya turo
su, ya kuma yi wahayi zuwa gare su, ya karfafe su da ayoyi, kuma lallai su, sun
isar da amana, sun yi nasiha ga al'umma, kuma sun isar da sakonsa, suka yi
jihadi domin Allah iyakar jihadi, muna yi imani da su, da kuma dukkan abinda
Allah ya ilmantar da mu shi; na sunayensu da sifofinsu da labarunsu, a dunkule,
da na dalla-dalla. Kuma lallai farkon annabawa shine Adam –عليه السلام-, kuma farkon Manzo shine
annabi Nuhu –عليه السلام-, Na karshen ko cikamakon annabawa da
manzanni kuma shine annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم-, kuma lallai shari'oin da suka gabata
dukkansu an soke yin aiki da su, da zuwan shari'ar annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم-. Kuma manzannin da ake musu
lakabi da ulul azmi, su biyar ne, an ambace su, a cikin surori guda biyu; wato:
Sutatush Shurah, da Ahzab, sune, (annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم, da annabi Nuh –عليه السلام-, da annabi Ibrahimu –عليه السلام-, da annabi Musa –عليه السلام-, da annabi Isah –عليه السلام-).
RUKUNI NA BIYAR: IMANI DA RANAR KARSHE
Imani da ranar karshe,
yana kunsar yin imani da dukkan abinda Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya bada labarin aukuwarsa bayan mutuwa,
misalign fitinan kabari (yin tambaya a cikinsa), da busa a cikin kaho, da
tashin mutane daga kabarinsu, da ma'aunanan auna ayyuka, da siradi, da dausayin
annabawa da tafkin alkausara, da ceto, da aljannah, da wuta, da ganin muminai
ga Ubangijinsu a yinin kiyama, da kuma a cikin aljannah, da wassunsu na lamuran
gaibu.
RUKUNI NA SHIDA: IMANI DA KADDARA NA
ALHERINSA DA SHARRINSA
Imani da wannan rukunin wajibi ne ya kunshi al'amura guda hudu:
ILIMI
Imani da cewa, lallai Allah –سبحانه وتعالى-
ya san kowane abu, a dunkule, da kuma dalla-dalla.
|
RUBUTU
Imani da cewa, Lallai Allah ya rubuta
kaddarar kowani abu, har zuwa tashin kiyama.
|
NUFI
Imani da cewa, abinda Allah ya nufa,
yak an kasancewa, abinda bai nufa ba kuma baya kasancewa, kuma lallai bawa
yana da nufi, saidai tana karkashin nufin Allah –سبحانه وتعالى-.
|
HALITTA
Imani da cewa, lallai bawa halitta ne
shi da ayyukansa, haka sauran halittu gaba daya, dalili akan haka; "ALLAH SHINE MAHALICCIN KOWANE ABU", "ALLAH SHI YA HALICCE KU DA ABINDA KUKE AIKATAWA".
|
Wadannan martabobin guda hudu, mai wake ya tattara cikin fadinsa:
Ilimi, da rubutun majibincinmu (Allah),
da nufinsa
Da halittarsa, wanda shine samarwa da
kasantarwa.
الْمَرْتَبَةُ الثَّالِثَةُ: الإِحْسَانُ
أركانه: وله رُكْنٌ وَاحِدٌ. كما فى الحديث: (أَنْ تَعْبُدَ اللهَ
كَأَنَّكَ تَرَاهُ، فَإِن لَمْ تَكُنْ تَرَاهُ فَإِنَّهُ يَرَاكَ).
وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى: (إِنَّ اللّهَ مَعَ الَّذِينَ اتَّقَواْ
وَّالَّذِينَ هُم مُّحْسِنُونَ). وقَوْلُهُ تَعَالَى: (وَتَوَكَّلْ عَلَى
الْعَزِيزِ الرَّحِيمِ * الَّذِي يَرَاكَ حِينَ تَقُومُ * وَتَقَلُّبَكَ فِي
السَّاجِدِينَ * إِنَّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ). وقَوْلُهُ تَعَالَى: (وَمَا
تَكُونُ فِي شَأْنٍ وَمَا تَتْلُو مِنْهُ مِن قُرْآنٍ وَلاَ تَعْمَلُونَ مِنْ
عَمَلٍ إِلاَّ كُنَّا عَلَيْكُمْ شُهُوداً إِذْ تُفِيضُونَ فِيهِ).
MARTABA TA UKU: IHSANI (KYAUTATA BAUTA)
Rukunnansa, Yana da rukuni daya ne, kuma shine ka kyautata bautar Allah,
kamar kana ganinsa, domin idan kai baka ganinsa, ai shi yana ganinka; dalili
kuma shine fadinSa Madaukaki: "LALLAI
NE ALLAH YANA TARE DA MASU TAKAWA, WADANNAN DA SUNE MASU KYAUTATA BAUTA".
Da fadinSa: "SAI KA YI TAWAKKALI GA
MABUWAYI MAI RAHAMA * WANDA KE GANINKA A LOKACINDA KAKE TSAYUWAR SALLAH * DA
JUJJUYAWARKA A CIKIN MASU SUJJADA * LALLAI NE SHI, SHINE MAI JI MASANI".
Da fadinSa: "BA ZA KA KASANCE CIKIN WANI
SHA'ANI BA, KO KA KARANTA KUR'ANI, KO KU AIKATA WANI AIKI, FACE MUN KASANCE
MUNA HALARCE, A LOKACIN DA KUKE KUKKUTSAWA A CIKINSA".
Martaba ta uku: Kyautata bauta,
Shine mafi kololuwar martabobin addini, kuma rukuni ne guda daya, saidai
a karkashinsa akwai martabobi biyu
Ibada
irin ta mai gani
Wannan itace ibada cikin kauna, da
kwadayi, da begen abinda ke wurin Allah.
Misalinta: ibadar Annabawa da
Manzanni –عليهم السلام-,
kuma waninsu zai iya kaiwa zuwa ga wannan martabar.
|
Ibadar
mai lura
Wannan itace ibada cikin tsoro, da
gujewa wuta,
Wannan martabar babu wani musulmin da
ke fita daga cikinta.
|
KARIN BAYANI: Wannan baya
nuni kan cewa, lallai ma'abucin wannan martabar kawai yana da so ko begen
Allah ne, banda tsoron Allah –سبحانه وتعالى-, saidai a wannan martabar, babban
abinda ke tunkuda bawa ya tayar da shi zuwa ga bautar Allah shine: son Allah
–سبحانه وتعالى-,
kuma daga cikin dalilan wannan akwai fain Annabi –صلى الله عليه وسلم-:
"Shin b azan kasance bawa mai yawan godiya ba!".
|
Dalili kuma daga cikin sunnah, shine shahararren hadisin mala'ika
Jibrila, wanda aka ruwaito shi daga Umar –رضي الله عنه- ya ce:
Wata rana muna zaune a wurin Manzon Allah –صلى الله عليه
وسلم-, Sai wani mutum ya bullo mana, mai tsananin farin tufafi, mai
tsananin bakin gashi, babu wata alamar tafiya a tattare da shi, kuma babu wani
daga cikinmu da ya sanshi, har ya zauna kusa da Annabi –صلى الله عليه وسلم-; Sai ya jingina guiwoyinsa zuwa
guiwoyinsa, ya kuma dora tafukansa akan cinyoyinsa, yace: Ya Muhammadu! Bani
labari akan Musulunci? Yace: Ka shaida babu abin bautawa da
gaskiya sai Allah, kuma annabi Muhammadu manzon Allah ne, kuma ka tsayar da
salla, ka bada zakka, ka yi azumin watan ramadana, ka yi hajjin daki; idan ka
samu hanyar zuwa gare shi. Sai yace: ka yi gaskiya, Sai muka yi mamakinsa;
yana tambayarsa kuma yana gaskata shi.
Sai
yace: ka bani labari akan imani? Yace: Ka yi Imani da Allah, da
Mala'ikunsa, da littatafansa, da Manzanninsa, kuma ka yi imani da kaddara; na
alkhairinsa dana sharrinsa.
Yace:
To ka bani labari akan "ihsani"? Sai yace:Shine ka bauta wa Allah
kamar kana ganinsa, idan kai baka ganinsa, to shi yana ganinka.
Yace:
To ka bani labari akan kiyamah? Sai yace: Wanda ake tambayarsa akanta bai fi
wanda yayi tambayar sanin lokacinta ba. Sai yace: To ka bani labari akan
alamominta? Sai yace: Baiwa zata haifi uwar gijiyarta, kuma zaku ga
marasa takalma, tsiraru, masu kiyon dabbobi suna yin gini masu tsayi.
Yace:
Sannan sai ya tafi, sai na zauna na wani lokaci, Sa'annan sai yace: Ya
kai Umar, shin ka san wanene mai yin wannan tambayar? Sai yace: Allah ne da
manzonsa suka sani.
Yace: Lallai
shi mala'ika Jibrilu ne, ya zo muku, domin ya karantar da ku addininku".
Wannan hadisin dalili ne da ya yi bayanin rukunnan musulunci, da
rukunnan imani, da rukunin ihsani.
Cikin fadinSa –صلى الله عليه وسلم-: "Wanda aka tambaya akan lamarin bai
fi mai tambayar ilimi akansa ba" dalili ne, akan babu wanda ya san lokacin
tsayuwar kiyama, in banda Allah.
fadinSa –صلى الله عليه وسلم-
"Kuyanga ta haifi uwargijiyanta".
|
Yana nuna, yawaitar cutar da iyaye.
|
Yana nuna yawaitar bautar da mutane.
|
Yana nuna, jujjuyawa ko caje-canjen
yanayi.
|
Yana nuna, mai mulki zai auri
kuyanga; sai ta Haifa masa yaro, sai wannan dan nasa ya dawo bayan rasuwar
ubansa ya zama sarki ko mai mulki, sai ya shugabanci uwarsa.
|
"Kuma za ku ga funtaye marasa takalma da tufafi, talakawa"
"Talakawa, masu kiyo awaki, suna gasar gina dogayen gine-gine";
wannan yana nuna caccanzawar yanayi da hali, ta yadda wannan talaucin zai
rikide zuwa ga kazami ko mahaukatan dukiya.
FA'IDODI DAGA HADISIN JIBRILU –عليه السلام-
1. Lallai akwai hakkoki guda shida akan dalibi, Hakkin kansa, da hakkin
shehunansa, da hakkin wurin da yake koyan ilimi a cikinsa, hakkin abokan
karatunsa, hakkin littafinsa, da kuma hakkin ilimin da ya ke koyansa.
-
Hakkin
dalibi na-karan kansa: Ilimi ibada ne (dole ayi ikhlasi,
da koyi da Annabi SAW a cikinsa), ka zama akan tafarkin magabatan kwarai,
tsoron Allah, da kulawa da dokokinsa, tawali'u da nisantar girman kai.
Wadatuwa da
kadan da zuhud ko gujewa duniya, da sifantuwa ko tasirantuwa da ilimi, da
kula da mutuntaka, da aiki da halin mazan kirki, da kauracewa rayuwar
kasaita.
Kauracewa
wuraren wargi, da sifantuwa da taushi, da tabbatuwa da bin diddigi.
Himma, da
nacin neman ilimi, da yin balaguro dominsa, da rubuce ilimi, da kiyayewa da
haddacewa, da muraja'ar abinda aka haddace.
Fik-hu ta
hanyar mayar da kananan mas'aloli cikin ginshikansu da manyansu, da sanya
mafaka zuwa ga Allah, da amanar ilimi, da gaskiya.
Garkuwar
dalibin ilimi itace, fadin Ban sani ba, kiyaye da rashin tozarta uwar jari,
wato lokaci, da baiwa rai damar hutawa, da samun wayewa ta hanyar sanin
muhimman lamura cikin kowane fanni na ilimi, da karatun gyaran kura-kurai, ko
don harda, da karatun bin manyan littatafa.
Kyautata
tambaya, da kyakkyawan sauraro, sai fahimta, da aiki, tattaunawa ba da
jayayya ba, muraja'ar ilimi, ka kasance tsakanin littafin Allah da sunnah da
ilmominsu, da kokarin samar ko neman kammala kayan aikin kowane fanni na
ilimi.
Yin aiki, da
gujewa son shugabanci, da son shahara, da son duniya.
Munana zato ga
rai, da kyautata shi ga mutane.
Bada zakkar
ilimi (da nufin bayyanar da gaskiya, yana mai yawaita umarni da kyakkyawa,
mai yawaita hani ga munkari, yana mai auna tsakanin maslaha da ababe masu
cutarwa, yana mai yada ilimi, da son amfanar da mutane, da tsayuwa wajen bada
mutunci, ko yin ceto mai kyau ga musulmai, a lokacin musibu na gaskiya,
sanannu).
Buwaya, kiyaye
ilimi, da boye abu don kubuta daga sharri (mudaraat), ba da nufin boye
gaskiya ba (mudahana), da nisantar daukar kai malami, ko bayyanar da kai gabanin
zuwan lokacin kaiwa ga hakan.
Matsayarka
idan malami ya yi kuskure, ko ga mas'alolin da maluma suka yi sabani.
Kawar da
shubuhohi, da nisantar kungiyancin da ake gina soyayya da kiyayya akanta.
-
Hakkin
shehinsa: A wannan lamarin mutane suna kasuwa bangarori
biyu, da matsakaita. Kuma da sannu bayanin zai zo mana cewa lallai shirkar
farko da ta auku a duniya, ta auku ne da sababin wuce iyaka kan salihai, don
haka babu makawa, sai mun kasance masu akidar tsakaitawa dangane da salihan
bayi; babu wuce iyaka ko gajartawa.
-
Hakkin
wurin da yake koyan ilimi a cikinsa.
-
Hakkin
abokin karatunsa: Allah –سبحانه وتعالى- yace: "KUN KASANCE MAFI ALHERIN AL'UMMAN DA AKA FITAR WA MUTANE",
Kuma Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "'Dayanku b azi yi imani
ba, face ya so ma kansa abinda yake so ma kansa".
-
Hakkin
littafi: Ta hanyar ya kiyaye littafin, saboda Allah –سبحانه وتعالى-
ya mana ni'amar wadannan littatafan, kuma dole ne a kanmu mu kiyaye su.
-
Hakkin
ilimi: Ta hanyar haddace ilimin, da muaraja'arsa
da'iman; koyaushe, da yin aiki da shi; saboda wajibi ne ga mutumin da ya koya
yayi aiki, sa'annan bayan haka, sai ya yi da'awa zuwa ga a nemi wannan
ilimin, domin wannan ni'imar babu makawa, sai anyi godiya a gar ta.
|
2. Daga cikin ladduban tambayar malami, dalibin ya kawo tambayar da yake
fatan idan an amsata za a samu amfani da fa'idah.
3. Wajibi ne akan dalibin ilimi ya kiyaye zuwansa cikin yanayi mai kyau.
4. Bayan wafatin Annabi –صلى الله عليه وسلم- ba a cewa, Allah da Manzonsa ne, suka fi
sani, saidai kawai a ce: Allah ne mafi sani.
الأَصْلُ الثَّالِثُ: مَعْرِفَةُ نَبِيِّكُمْ
مُحَمَّدٍ صلى الله عليه وسلم:
وهُوَ
مُحَمَّدُ بْنُ عَبْدِ اللهِ بْنِ عَبْدِ الْمُطَّلِبِ بْنِ هَاشِمٍ، وَهَاشِمٌ
مِنْ قُرَيْشٍ، وَقُرَيْشٌ مِنَ الْعَرَبِ، وَالْعَرَبُ مِنْ ذُرِّيَّةِ
إِسْمَاعِيلَ بْنِ إِبْرَاهِيمَ الْخَلِيلِ عَلَيْهِ وَعَلَى نَبِيِّنَا أَفْضَلُ
الصَّلاةِ وَالسَّلامِ.
وَلَهُ
مِنَ الِعُمُرِ: ثَلاثٌ وَسِتُّونَ سَنَةً، مِنْهَا أَرْبَعُونَ قَبْلَ
النُّبُوَّةِ، وَثَلاثٌ وَعِشْرُون َفى النبوة.
نُبِّئَ
بـ(اقْرَأ)، وَأُرْسِلَ بـ (الْمُدَّثِّرْ).
وَبَلَدُهُ
مَكَّةُ، وهاجر إلى المدينة.
ASALI NA UKU: SANIN ANNABINKU MUHAMMADU –صلى الله عليه وسلم-
Shine annabi: Muhammadu
dan Abdullahi bn Abdulmuddalib, dan Hashim, Hashim kuma daga kabilar Kuraishawa
ne, su kuma Kuraishawa daga al'ummar larabawa suke, larabawa kuma daga zurriyar
annabi Isma'il dan Ibrahimul Khalil, Allah ya yi karin mafificin salati da
sallama akansa, da kuma Annabinmu.
Ya rasu, yana da shekaru sittin da uku, shekaru arba'in gabanin annabta,
shekaru ashirin da uku yana annabi manzo.
An bashi annabta ne da saukar "Ikra'a", an kuma turo shi da
manzanci da saukar "Ya, ayyuhal muddasir".
Garinsa (na haifuwa) shine Makkah, ya kuma yi hijira zuwa ga Madina.
Wannan fakara ko sakin
layi, ta kunshi tarihin Annabi –صلى الله عليه وسلم- ta fiskar sunansa, da nasabarsa, da
shekarunsa, da wani abu na da'awarsa –صلى الله عليه وسلم-.
DOLE MU SAN WASU LAMURA DANGANE DA
ANNABI –صلى الله عليه وسلم-,
DAGA CIKINSU:
SUNANSA
DA NASABARSA
Shine annabi: Muhammadu dan Abdullahi bn
Abdulmuddalib, dan Hashim, Hashim kuma daga kabilar Kuraishawa, su kuma
Kuraishawa daga al'ummar larabawa, larabawa kuma daga zurriyar annabi Isma'il
dan Ibrahimul Khalil –عليهم السلام-.
|
SHEKARUNSA
Annabi ya rasu, yana da shekaru sittin da uku,
shekaru arba'in gabanin annabta, shekaru ashirin da uku bayan annabta.
|
SHEKARUN ANNABCINSA –صلى الله عليه وسلم- SUN KASU ZUWA:
Shekarun zama a garin Makkah
Wanda suka lankwame shekaru goma sha uku.
|
Shekarun zaman Madinah
Wanda ya lakume shekaru goma.
|
SHIN MANZON ALLAH –صلى الله عليه وسلم- ANNABI NE KO MANZO?
E, Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- Annabi ne, kuma Manzo, kuma lallai Manzon
Allah –صلى الله عليه وسلم-
ya zama Annabi ne, da saukar "ikra'a", sai
kuma aka tura shi da Manzanci, da saukar "Ya
ayyuhal Muddassir".
بَعَثَهُ
اللهُ بِالنِّذَارَةِ عَنِ الشِّرْكِ، وَبالَدْعُوة إِلَى التَّوْحِيدِ،
وَالدَّلِيلُ
قَوْلُهُ تَعَالَى: (يَا أَيُّهَا الْمُدَّثِّرُ * قُمْ فَأَنذِرْ * وَرَبَّكَ
فَكَبِّرْ * وَثِيَابَكَ فَطَهِّرْ * وَالرُّجْزَ فَاهْجُرْ * وَلاَ تَمْنُن
تَسْتَكْثِرُ * وَلِرَبِّكَ فَاصْبِرْ).
وَمَعْنَى:
(قُمْ فَأَنذِرْ): يُنْذِرُ عَنِ الشِّرْكِ، وَيَدْعُو إِلَى التَّوْحِيدِ.
(وَرَبَّكَ
فَكَبِّرْ): أَيْ: عَظِّمْهُ بِالتَّوْحِيدِ.
(وَثِيَابَكَ
فَطَهِّرْ): أَيْ: طَهِّرْ أَعْمَالَكَ عَنِ الشِّرْكِ.
(وَالرُّجْزَ
فَاهْجُرْ): الرُّجْزَ: الأَصْنَامُ، وَهَجْرُهَا: تَرْكُهَا، وَالْبَرَاءَةُ
مِنْهَا وَأَهْلُهَا، أَخَذَ عَلَى هَذَا عَشْرَ سِنِينَ يَدْعُو إِلَى
التَّوْحِيدِ، وَبَعْدَ الْعَشْرِ عُرِجَ بِهِ إِلَى السَّمَاءِ، وَفُرِضَتْ
عَلَيْهِ الصَّلَواتُ الْخَمْسُ، وَصَلَّى فِي مَكَّةَ ثَلاثَ سِنِينَ،
وَبَعْدَهَا أُمِرَ بالْهِجْرَةِ إِلَى الْمَدِينَة.
|
Allah ya turo shi da gargadi daga shirka, kuma
domin yay i kira zuwa ga Tauhidi;
Dalili kuma shine, fadinSa Madaukaki: "YA WANDA YA LULLUBA DA MAYAFI * KA TASHI DOMIN KA YI GARGADI * KUMA
UBANGIJINKA KA GIRMAMA SHI * KUMA TUFAFINKA KA TSARKAKE SU * GUMAKA KUMA KA
KAURACE MUSU * KADA KA YI KYAUTA KANA NEMAN KARI * KUMA SABODA UBANGIJINKA, SAI KA YI HAKURI".
Ma'anar: "KA
TASHI DOMIN KA YI GARGADI" wato yayi gargadi akan shirka,
ya kuma kira zuwa ga tauhidi.
"KUMA
UBANGIJINKA KA GIRMAMA SHI",
Ma'ana: ka girmama shi da tauhidi.
"KUMA
TUFAFINKA KA TSARKAKE SU", ma'ana: ka tsarkake ayyukanka
daga shirka.
"GUMAKA
KUMA KA KAURACE MUSU", Rujz: gumaka, kwaurace musu:
shine barinsu da barranta daga gare su, da ma'abutansu.
Ya dauki shekaru goma yana yin da'awa akan
tauhidi. Kuma bayan shekaru goma sai aka yi mi'iraji da shi zuwa sama, sai
aka farlanta masa salloli biyar, kuma ya yi salla a garin Makkah tsawon
shekaru uku, bayansu kuma aka umarce shi da yin hijira, zuwa garin Madina.
|
Fadinsa: "sai aka yi mi'iraji da shi zuwa sama" za mu fa'dantu
da:
1. Lallai abinda Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya bada labarinsa, na lamuran gaibu,
wajibi ne mu ce: Mun yi imani, mun gaskata, mun sallama.
2. Muhimmancin sallolin farillai, ta yadda Allah bai farlanta su ba, sai da
ya hawar da AnnabinSa sama.
WANI ABU DAGA TARIHIN ANNABI –صلى الله عليه وسلم-
Da'awar musulunci a rayuwar
Manzon Allah ta Makkah ta fi bada karfi akan kira zuwa ga Tauhidi ko kadaita
Allah, da yin watsi da shirka (hada Allah da wani), da ikhlasi ko tsantsance
bauta ga Allah; shi kadai. Kuma wannan da'awar ta cigaba, har tsawon shekaru
goma sha uku (13).
Sai aka yi umarnin hijira
ga Annabi –صلى الله عليه وسلم-
zuwa garin Madina, sai lamarin da'awa zuwa ga Tauhidi ya cigaba, a garin
Madina, tare da saukan sauran shari'oin addini; na ibadodi, da mu'amaloli, da
sauran lamuran rayuwa.
Don haka, mai yin nazari cikin rayuwar Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم-, da da'warsa, zai samu cewa:
Lallai da'awa zuwa ga Tauhidi, ta wanzu tana lazimtar Annabi –صلى الله عليه وسلم- har Allah yay i masa wafati.
Cikin wannan kuma akwai mai-da-martani, ga masu sace guiwar mutane kan koyan
ilimin tauhidi, ko suke cewa, wai tauhidi 'yan wadansu dakikoki kadan mutum ke
bukata wajen koyansa.
وَالْهِجْرَةُ:
الانْتِقَالُ مِنْ بَلَدِ الشِّرْكِ إِلَى بَلَدِ الإِسْلامِ، وَالْهِجْرَةُ
فَرِيضَةٌ عَلَى هَذِهِ الأُمَّةِ مِنْ بَلَدِ الشِّرْكِ إِلَى بلد الإِسْلامِ،
وَهِيَ بَاقِيَةٌ إِلَى أَنْ تَقُومَ السَّاعَةُ، وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ
تَعَالَى: (إِنَّ الَّذِينَ تَوَفَّاهُمُ الْمَلآئِكَةُ ظَالِمِي أَنْفُسِهِمْ
قَالُواْ فِيمَ كُنتُمْ قَالُواْ كُنَّا مُسْتَضْعَفِينَ فِي الأَرْضِ قَالْوَاْ
أَلَمْ تَكُنْ أَرْضُ اللّهِ وَاسِعَةً فَتُهَاجِرُواْ فِيهَا فَأُوْلَئِكَ
مَأْوَاهُمْ جَهَنَّمُ وَسَآءتْ مَصِيرًا * إِلاَّ الْمُسْتَضْعَفِينَ مِنَ
الرِّجَالِ وَالنِّسَآء وَالْوِلْدَانِ لاَ يَسْتَطِيعُونَ حِيلَةً وَلاَ
يَهْتَدُونَ سَبِيلاً * فَأُوْلَئِكَ عَسَى اللّهُ أَن يَعْفُوَ عَنْهُمْ وَكَانَ
اللّهُ عَفُوّا غَفُورا). وَقَوْلُهُ تَعَالَى: (يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ آمَنُوا
إِنَّ أَرْضِي وَاسِعَةٌ فَإِيَّايَ فَاعْبُدُونِ).
قَالَ
الْبُغَوِيُّ ـ رَحِمَهُ اللهُ ـ:نزلت هَذِهِ الآيَةِ فِي المُسْلِمِينَ
الَّذِينَ بِمَكَّةَ ولَمْ يُهَاجِرُوا، نَادَاهُمُ اللهُ بِاسْمِ الإِيمَانِ.
وَالدَّلِيلُ
عَلَى الْهِجْرَةِ مِنَ السُّنَّةِ: قَوْلُهُ ـ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
ـ: (لا تَنْقَطِعُ الْهِجْرَةُ حَتَّى تَنْقَطِعَ التَّوْبَةُ، وَلا تَنْقَطِعُ
التَّوْبَةُ حَتَّى تَطْلُعَ الشَّمْسُ مِنْ مَغْرِبِهَا).
|
Hijira: ita ce: kaura daga garin shirka, zuwa
garin musulunci.
Kuma hijira farilla ne, ga wannan al'ummar, daga
garin shirka, zuwa garin musulunci, kuma aiki da ita yana nan, har zuwa
tashin kiyama.
Dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "LALLAI WADANNAN DA MALA'IKU SUKA KARBI RAYUKANSU, ALHALIN SUNA MASU
ZALUNTAR KANSU, SU KAN CE MUSU: A CIKIN ME KUKE? SAI SUKA CE: MUN KASANCE
WADANDA AKA RAUNANA A CIKIN KASA, SUKA CE: ASHE KASAR ALLAH BATA KASANCE
MAYALWACIYA BA? DOMIN KU YI HIJIRA GARE TA, TO WADANNAN MAKOMARSU JAHANNAMA
CE, KUMA TA MUNANA TA ZAMA MAKOMA * IN BANDA MASU RAUNI DAGA MAZA DA MATA DA
YARA, WADANDA BASU IYA YIN WATA DABARA, KUMA BASU SHIRYUWA GA HANYA * TO
WADANNAN AKWAI TSAMMANIN ALLAH YA YAFE LAIFI DAGA GARE SU, KUMA ALLAH YA
KASANCE MAI YAFEWA NE MAI GAFARA".
Da kuma fainSa Madaukaki: "YA BAYINA, WADANDA SUKA YI IMANI, LALLAI NE KASATA MAI YALWA CE,
SABODA HAKA KU BAUTA MINI".
Bagawiy –رحمه الله- ya ce: "Sababin saukar wannan ayar
akan musulmin da suke garin Makkah ne, wadanda basu yi hijira ba ne, sai
Allah ya kira su da sunan imani".
Dalili kuma akan hijira daga cikin hadisai, akwai
fadinSa –صلى الله عليه
وسلم-: "Hijira bata yankewa har sai karban tuba ya yanke,
kuma tuba bata yankewa har sai rana ta fudo daga mafadarta".
|
HIJIRA TA KASU ZUWA KASHI KASHI UKU
Kaura
daga garin kafirci, zuwa garin Musulunci.
Hukuncinta wajibi ne.
|
Kaura
daga garin Makkah zuwa Madina.
Wannan kuma ta yanke, da bude garin Makkah, ta
hanyar shigar da musulunci.
|
Kaurace
wa dukkan abinda Allah ya wajabta kaurace masa, na aiki da mai aiki, da zamani
da wuri.
|
Aiki: Shine dukkan abinda Allah –سبحانه وتعالى-
ya haramta, daga cikin manyan ayyukan da ake kaurace musu, shirka.
Ma'aikacin da ake kaurace masa kuma, shine:
Kafirai, da munafikai da wasunsu.
Zamani ko lokaci da ake kaurace masa kuma, shine
kaurace wa dukkan lokutan da kafirai suke yin bukukuwa a cikinsu.
Wuri kuma, shine kauracewa dukkan wuraren da
kafirai suke yin bukukuwa a cikinsu.
|
Karbar tuba yana yankewa ne da 'dayan abubuwa biyu:
1. Fudowar rana daga mafadarta.
2. Ko ta hanyar zuwa mutuwa: "BA
TUBA BA CE, GA WADANDA SUKE AIKATA MUNANAN AYYUKA, HAR IDAN MUTUWA TA HALARCI
DAYANSU YA CE: LALLAI NE NI NA TUBA YANZU, KUMA BA TUBA BA CE, GA WADANDA SUKE
MUTUWA ALHALI KUWA SUNA KAFIRAI".
Fadinsa: "Babu hijira bayan fat-hu
Makkah (wato, shigar da musulunci garin Makka)", Wannan ishara ce daga
Annabi –صلى الله عليه وسلم-
wanda ta nuna cewa lallai garin Makkah ba zai yiwu ta koma garin kafirci ba.
فَلَمَّا اسْتَقَرَّ فِي
الْمَدِينَةِ أُمِرَ بِبَقِيَّةِ شَرَائِعِ الإِسْلامِ، مِثلِ: الزَّكَاةِ(1)، وَالصَّوْمِ، وَالْحَجِّ، وَالأَذَانِ، وَالْجِهَادِ، وَالأَمْرِ
بِالْمَعْرُوفِ وَالنَّهْيِ عَنِ الْمُنْكَرِ، وَغَيْرِ ذَلِكَ مِنْ شَرَائِعِ
الإِسْلامِ، أَخَذَ عَلَى هَذَا عَشْرَ سِنِينَ، وَتُوُفِّيَ صَلواتُ اللهِ
وَسَلامُهُ عَلَيْهِ(2)ـ وَدِينُهُ بَاقٍ وَهَذَا
دِينُهُ، لا خَيْرَ إِلا دَلَّ الأُمَّةَ عَلَيْهِ، وَلا شَرَّ إِلا حَذَّرَهَا
مِنْهُ، وَالْخَيْرُ الَّذِي دَلَّهَا عَلَيْهِ التَّوْحِيدُ، وَجَمِيعُ مَا
يُحِبُّهُ اللهُ وَيَرْضَاهُ، وَالشَّرُ الَّذِي حَذَّرَهَا مِنْهُ الشِّرْكُ،
وَجَمِيعُ مَا يَكْرَهُ اللهُ وَيَأْبَاهُ(3).
|
Yayin da ya zauna a garin Madina sai aka umarce
shi da yin aiki da sauran shari'oi, misalign zakkah, da azumi, da hajji, da
jihadi, da kiran salla, da umarni da kyakkyawa, da hani ga mummuna, da wasun
wadannan daga cikin shari'oin musulunci.
Ya dauki shekaru goma akan haka, bayan haka kuma
sai ya rasu, salatin Allah da sallamarsa su kara tabbata a gare shi.
Addininsa kuma mai wanzuwa ne, wannan shine
addininsa, babu wani alkhairi face ya nusar da al'umma a gare shi, kuma babu
wani sharri face ya tsawatar mata akansa.
Kuma alkhairin da ya nuna wa al'umma, shine
Tauhidi da dukkan abinda Allah yake sonsa, kuma ya yarda da shi.
Sharrin kuma da ya tsawatar akansa, shine: Shirka
da dukkan abinda Allah baya sonsa, kuma ya ke kinsa.
|
(1)
Sheikh Muhammadu
bn Salih Al-usaimin –رحمه الله- yana cewa: "Zakka a farkon lamari an
farlanta, a garin Makkah, sai dai ba a bayyanar da nisabinta, ko abinda ke
wajaba a cikinta ba, da aka yi hijira Madina sai aka sanya mata nisabobi, kuma
aka fadi abinda ke wajaba daga cikinta.
(2)
Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya rasu bayan hijira da
shekaru goma, kuma an bunne shi a dakin A'ishah –رضي الله عنها-.
(3)
Babu wani alheri
face Annabi ya nuna shi ga wannan al'ummar, kuma babu wani sharri face ya
tsawatar mata", Don haka, bau makawa, sai mun shaida cewa lallai Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya sauke amana, kuma ya isar
da manzanci, yay i nasiha ga al'umma, ya yi jihadi don Allah iyakar jihadi,
kuma ya bar mu akan farar turba, darenta kamar yininta; babu mai karkace mata,
sai halakakke.
MAFI
GIRMAN ABABEN DA AKA HARAMTA
Babbar shirka (mai fitar da mutum daga
musulunci).
|
Karamar shirka (wanda bata fitar da mutum daga musulunci).
|
Laifukan kaba'irai (sune, dukkan zunuban da suke
da kebantattun ukuba).
|
Saga'ir; wato kananan zunubai (dukkan haramun
dinda bashi da wata ukuba kebantacciya).
|
بَعَثَهُ اللهُ إِلَى النَّاسِ كَافَّةً، وَافْتَرَضَ طَاعَتَهُ عَلَى
جَمِيعِ الثَّقَلَيْنِ الْجِنِّ وَالإِنْسِ؛ وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى:
(قُلْ يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنِّي رَسُولُ اللّهِ إِلَيْكُمْ جَمِيعًا)(1). وَكَمَّلَ اللهُ بِهِ الدِّينَ؛ وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى:
(الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي
وَرَضِيتُ لَكُمُ الإِسْلاَمَ دِينا)(2). وَالدَّلِيلُ عَلَى
مَوْتِهِ ـ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ـ قَوْلُهُ تَعَالَى: (إِنَّكَ
مَيِّتٌ وَإِنَّهُم مَّيِّتُونَ * ثُمَّ إِنَّكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ عِندَ
رَبِّكُمْ تَخْتَصِمُونَ).
|
Allah ya aike shi da Manzanci
zuwa ga mutane gaba daya, kuma ya farlanta yin da'a a gare shi, akan dukkan
aljanu da mutane; Dalili kuma shine FadinSa Madaukaki: "KA CE: YA KU MUTANE, LALLAI NE NI 'DAN AIKAN ALLAH NE ZUWA GARE KU
GABA DAYA".
Kuma Allah ya cika addini, da
shi, Dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "A YAU NA CIKA MUKU ADDININKU, KUMA NA CIKE NI'IMATA AKANKU, KUMA NA
YARJE MUKU MUSULUNCI A MATSAYIN ADDINI".
Kuma dalili akan mutuwarsa –صلى الله
عليه وسلم-: "LALLAI NE KAI MAI MUTUWA NE, KUMA LALLAI SU MASU MUTUWA NE * SA'ANNAN
KU, A RANAR KIYAMA, A WURIN UBANGIJINKU, MASU YIN HUSUMA NE".
|
(1)
An
aiki Annabi –صلى الله عليه وسلم- zuwa ga
Mutane gaba daya, kuma an soke amfani da dukkar shari'ar da ta zo gabaninsa,
saboda haka, Yahudawa da Nasara, a zamanin Annabi –صلى الله عليه وسلم- da zamaninmu wannan, idan har musulunci ya kai gare su, sai suka
ki shiga wannan addinin, to su kafirai ne, koda kuwa sun kasance akan irin
abinda annabi Musa da Isa –عليهما السلام- suka
kasance akansa.
Daga cikin dalilan
haka akwai:
1-
fadinSa
–سبحانه وتعالى-: "KA CE: YA KU MA'ABUTA
LITTAFI, KU ZO GA WATA KALMA, DA ZATA DAIDAITA TSAKANINMU DA TSAKANINKU; KADA
MU YI BAUTA GA KOWA SAI ALLAH, BA ZA MU HADA SHI DA KOWA BA".
2-
Da
fadinSa –سبحانه
وتعالى-: "KU
YAKI WADANDA BASU YI IMANI DA ALLAH, KUMA BASU YI IMANI DA RANAR KARSHE BA,
KUMA BASU HARAMTA ABINDA ALLAH DA MANZONSA SUKA HARAMTA, BASU YIN ADDININ
GASKIYA, DAGA CIKIN MA'ABUTA LITTAFI".
3-
Fadin
Annabi –صلى
الله عليه وسلم-: "Ina rantsuwa da wanda
raina ke hannunsa; babu wanda zai ji labarin annabcina; bayahude ne ko
banasare, sai yak i yin imani da ni, face ya kasance daga ma'abuta wuta".
(2)
Wannan
ayar tana yin raddi ga 'yan bidi'a.
وَالنَّاسُ
إِذَا مَاتُواْ يُبْعَثُونَ؛ وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى: (مِنْهَا
خَلَقْنَاكُمْ وَفِيهَا نُعِيدُكُمْ وَمِنْهَا نُخْرِجُكُمْ تَارَةً أُخْرَى).
وقَوْلُهُ تَعَالَى: (وَاللَّهُ أَنبَتَكُم مِّنَ الأَرْضِ نَبَاتاً * ثُمَّ
يُعِيدُكُمْ فِيهَا وَيُخْرِجُكُمْ إِخْرَاجًا). وَبَعْدَ الْبَعْثِ مُحَاسَبُونَ
وَمَجْزِيُّونَ بِأَعْمَالِهِمْ، وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى: (وَلِلَّهِ
مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ لِيَجْزِيَ الَّذِينَ أَسَاؤُوا بِمَا
عَمِلُوا وَيَجْزِيَ الَّذِينَ أَحْسَنُوا بِالْحُسْنَى)(1).
وَمَنْ
كَذَّبَ بِالْبَعْثِ كَفَرَ، وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى: (زَعَمَ الَّذِينَ
كَفَرُوا أَن لَّن يُبْعَثُوا قُلْ بَلَى وَرَبِّي لَتُبْعَثُنَّ ثُمَّ
لَتُنَبَّؤُنَّ بِمَا عَمِلْتُمْ وَذَلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِيرٌ)(2).
وَأَرْسَلَ
اللهُ جَمِيعَ الرُّسُلِ مُبَشِّرِينَ وَمُنْذِرِينَ؛ وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ
تَعَالَى: (رُّسُلاً مُّبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ لِئَلاَّ يَكُونَ لِلنَّاسِ
عَلَى اللّهِ حُجَّةٌ بَعْدَ الرُّسُلِ).
وَأَّولُهُمْ
نُوحٌ عَلَيْهِ السَّلامُ، وَآخِرُهُمْ مُحَمَّدٌ ـ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ ـ وَهُوَ خَاتَمُ النَّبِيِّينَ؛ وَالدَّلِيلُ عَلَى أَنَّ
أَوَّلَهُمْ نُوحٌ قَوْلُهُ تَعَالَى: (إِنَّا أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ كَمَا
أَوْحَيْنَا إِلَى نُوحٍ وَالنَّبِيِّينَ مِن بَعْدِهِ)(3).
|
Kuma Mutane idan suka mutu za a
tayar su, dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "DAGA KASA MUKA HALITTA KU, KUMA ZUWA CIKINTA ZA MU MAYAR DA KU, KUMA
DAGA GARE TA ZA MU FITAR DA KU, A KARO NA GABA".
Da fadinSa Madaukaki: "KUMA ALLAH YA TSIRAR DA KU DAGA KASA TSIRARWA, SA'ANNAN ZAI MAYAR DA
KU CIKINTA, YA KUMA SAKE FITAR DA KU FITARWA".
Kuma bayan an tayar da su za a
musu hisabi, kuma za a sakanta musu da ayyukansu, Dalili kuma akan haka shine
fadinSa Madaukaki: "NA ALLAH NE, DUKKAN ABINDA
KE CIKIN SAMMAI DA KASSAI, ZAI SAKANTA GA WADANDA SUKA MUNANA AIKI DA ABINDA
SUKA AIKATA, KUMA YA SAKANTA WA WADANDA SUKA KYAUTATA DA ALJANNAH".
Duk kuma wanda ya karyata
lamarin sake tayar da mutane, to ya kafirta, Dalili kuma shine fadinSa
Madaukaki: "WADANDA SUKA KAFIRTA SUN RIYA CEWA, BA
ZA A TAYAR DA SU BA, KA CE, A'A, INA RANTSUWA DA UBANGIJINA, LALLAI NE ZA A
TAYAR DA KU, SA'ANNAN A BAKU LABARIN ABINDA KUKA AIKATA, KUMA WANNAN GA ALLAH
ABU NE MAI SAUKI".
Kuma Allah ya turo Manzanni gaba
dayansu, suna yin albishir, suna gargadi, Dalili akan haka, shine fadinSa
Madaukaki: "MANZANNI MASU ALBISHIR DA GARGADI".
Na farkonsu shine annabi Nuhu –عليه السلام-, Na karshensu kuma, annabi Muhammadu –صلى الله
عليه وسلم-, kuma shine cika-makin
annabawa.
Dalili akan farkon manzanni
shine annabi Nuhu –عليه السلام- shine fadinSa Madaukaki: "LALLAI NE MUN YI WAHAYI ZUWA GARE KA, KAMAR YADDA MUKA YI WAHAYI GA
NUHU DA ANNABAWAN DA KE BAYANSA".
|
(1)
Dukkan
mutane za su dandani mutuwa, babu shakka akan haka, kuma za a tayar da su ga
wani yini mai girma, wanda shine yinin kiyama, sa'annan za a yi musu hisabi,
kuma za a musu sakayya; kowanne gwargwadon aikinsa.
(2)
Duk
wanda ya karyata sake tayar da mutune bayan mutuwa, da yin hisabi, ya kafirce;
saboda ya musanta rukuni daya daga cikin rukunnan imani.
(3)
Annabi
Nuhu –عليه السلام- shine farkon manzanni, dalili kuma shine fadinSa Madaukaki:
"LALLAI NE MUN YI WAHAYI ZUWA GARE KA, KAMAR YADDA
MUKA YI WAHAYI GA NUHU DA ANNABAWAN DA KE BAYANSA".
Amma farkon Annabawa,
shine annabi Adamu –عليه السلام-, dalili
kuma, shine saboda an tambayi Annabi –صلى الله عليه وسلم- akan
annabi Adamu; shin Annabi ne, sai ya ce: "Annabi ne da Allah yay i zance
da shi".
Kuma karshen Annabawa da Manzanni shine
annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم-, dalili
kuma shine fadinSa –سبحانه وتعالى-: "MUHAMMADU
BAI ZAMA UBA GA WANI DAGA CIKIN MAZAJENKU BA, SAIDAI DAN AIKE DAGA ALLAH, KUMA
CIKA-MAKON ANNABAWA".
Don haka, Duk wanda ya yi da'awar annabci
ko manzanci a bayan annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- to
wannan makaryaci ne, kafiri, Kuma duk wanda ya gaskata wannan makaryacin to
shima kafiri ne kwatankwacinsa.
وكُلُّ
أُمَّةٍ بَعَثَ اللهُ إِلَيْهِا رَسُولا مِنْ نُوحٍ إِلَى مُحَمَّدٍ –صلى الله
عليه وسلم- يَأْمُرُهُمْ بِعِبَادَةِ اللهِ وَحْدَهُ، وَيَنْهَاهُمْ عَنْ
عِبَادَةِ الطَّاغُوتِ؛ وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى: (وَلَقَدْ بَعَثْنَا
فِي كُلِّ أُمَّةٍ رَّسُولاً أَنِ اعْبُدُواْ اللّهَ وَاجْتَنِبُواْ الطَّاغُوتَ).
وَافْتَرَضَ
اللهُ عَلَى جَمِيعِ الْعِبَادِ الْكُفْرَ بِالطَّاغُوتِ وَالإِيمَانَ بِاللهِ، قَالَ
ابْنُ الْقَيِّمِ ـ رَحِمَهُ اللهُ تَعَالَى: مَعْنَى الطَّاغُوتِ مَا تَجَاوَزَ
بِهِ الْعَبْدُ حَدَّهُ مِنْ مَعْبُودٍ أَوْ مَتْبُوعٍ أَوْ مُطَاعٍ.
وَالطَّوَاغِيتُ كَثِيرُونَ وَرُؤُوسُهُمْ خَمْسَةٌ: إِبْلِيسُ لَعَنَهُ اللهُ،
وَمَنْ عُبِدَ وَهُوَ رَاضٍ، وَمَنْ دَعَا النَّاسَ إِلَى عِبَادَةِ نَفْسِهِ،
وَمَنْ ادَّعَى شَيْئًا مِنْ عِلْمِ الْغَيْبِ، وَمَنْ حَكَمَ بِغَيْرِ مَا
أَنْزَلَ اللهُ؛ وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى: (لاَ إِكْرَاهَ فِي الدِّينِ
قَد تَّبَيَّنَ الرُّشْدُ مِنَ الْغَيِّ فَمَنْ يَكْفُرْ بِالطَّاغُوتِ
وَيُؤْمِن بِاللّهِ فَقَدِ اسْتَمْسَكَ بِالْعُرْوَةِ الْوُثْقَىَ لاَ انفِصَامَ
لَهَا وَاللّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ) وَهَذَا هُوَ مَعْنَى لا اله إِلا اللهُ، وَفِي
الْحَدِيثِ: (رَأْسُ الأَمْرِ الإِسْلامِ، وَعَمُودُهُ الصَّلاةُ، وَذِرْوَةُ
سَنَامِهِ الْجِهَادُ فِي سَبِيلِ اللهِ).
|
Kuma Allah ya farlanta wa dukkan bayi su kafirce wa
dagutu, su yi imani da Allah, Ibnul-kayyim –رحمه الله- ya ce: Dagutu, shine dukkan wanda bawa
ya wuce iyakarsa, na ababen bauta, ko wadanda ake bi, ko wadanda ake musu
da'a.
Kuma kowace al'ummar da Allah ya tura mata manzo,
tun daga lokacin annabi Nuhu har zuwa annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم-
yana umartarsu ne da ibadar Allah; shi kadai, kuma yana hana su bauta wa
dagutu, dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "KUMA HAKIKA MUN TAYAR MANZO GA KOWACE AL'UMMA; DA CEWAR; KU YI BAUTAR
ALLAH, KU NISANCI DAGUTU".
Dagutu suna da yawa, amma manyansu guda biyar ne;
Iblisu –Allah ya la'ance shi-, da wanda aka masa bauta alhalin ya yarda, da
wanda ya kira mutane zuwa ga bauta a gare shi, da wanda ya riya sanin wani
abu na ilimin gaibu, da wanda yay i hukunci ba da abinda Allah ya saukar ba,
Dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "BABU
TILASTAWA A CIKIN ADDINI, HAKIKA SHIRIYA TA BAYYANA DAGA BATA, DON HAKA,
WANDA YA KAFIRTA DA 'DAGUTU, KUMA YA YI IMANI DA ALLAH, TO HAKIKA, YA YI RIKO
DA IGAYA AMINTACCIYA".
Wannan kuma shine ma'anar (LA ILAHA ILLAL LAHU).
Kuma ya zo a cikin hadisi "Kan wannan
lamari, shine musulunci, kuma kashin bayansa shine salla, kuma tozon
kololuwarsa shine jihadi fiysabillahi".
|
Allah ya turo Manzanni da Annabawa domin yin
bushara da gargadi, kuma dukkansu sun hadu ne akan kira zuwa ga Tauhidi, da
yakar dagutai, da shirka da dukkan kalolinsa, Dalili kuma shine fadinSa
Madaukaki: "KUMA HAKIKA MUN TAYAR MANZO GA KOWACE AL'UMMA",
ma'ana: ga kowane bangare na mutane, "DA
CEWAR; KU YI BAUTAR ALLAH"; wato, ku kadaita Allah da
Tauhidi, "KUMA KU NISANCI DAGUTU";
wato ku sanya 'dagutai a bangare, sai ku kasance a daya bangaren, Fadin haka,
yafi nuna fasaha da kaiwa makura wajen jan kunne, ku umarnin a nisanci
'dagutai; Wannan kuma, domin ya tabbatar da a barranta daga shirka, da
ma'abutansa.
Kuma Allah ya farlanta wa
dukkan bayi, kafirce wa dagutai, da kuma imani da Allah, kuma babu makawa, a
farkon fari sai an kafirce da 'dagutu gabanin yin imani da Allah; "KUMA
DUK WANDA YA KAFIRTA DA 'DAGUTU, YA KUMA YI IMANI DA ALLAH".
Shi kuma 'Dagutu: shine
duk abinda bawa ya ketare iyakarsa; na ababen bauta (kamar duwatsu da
bishiyoyi), ko ababen bi (kamar maluman banza), ko wanda ake musu 'da'a (kamar
shugabannin da suka fice daga biyayya ga Allah).
Su kuma 'Dagutai suna
dayawa, amma manya-manyansu guda biyar ne, Iblisu wanda Allah ya la'ance shi (A
nan Mawallafin, ya tsine masa ne, a matsayin bada labari), da kuma wanda aka
masa bauta, koma bayan Allah, alhalin ya yarda da hakan, da wanda ya kirayi
mutane zuwa ga bauta ma kansa, da wanda ya riya sanin wani abu na ilimin gaibu,
da wanda yay i hukunci ba da abinda Allah ya saukar ba.
MAS'ALAR YIN HUKUNCI BA DA ABINDA ALLAH
YA SAUKAR BA TANA KASUWA
BABBAN KAFIRCI
Idan ya kudurce cewa, hukuncin mutane yana daidai
da hukuncin Allah, ko kuma ya fi na Allah.
|
KAFIRCIN DA BAI KAI GA MAI FITARWA BA
Wanda kuma ya kudurta cewa lallai hukunci ba da
abinda Allah ya saukar ba, barna ne, saidai kuma yana yin hukunci da hakan,
saboda bin son zuciya, ko saboda son mulki, ko saboda wani sababin na daban.
|
IBNUL-KAYYIM YA KARKASA JIHADI ZUWA
KASHI HUDU
JIHADIN KAI
Wannan ya kan kasance ta hanyar ilimi, da aiki da
shi, da d'awa fiysabililLahi, da kuma hakuri.
|
YAKAR SHE'DAN
Ya kan kasance, ta hanyar nisantar shubuhohi
(shirka da bidi'oi), da nisantar sha'awowi (manyansu da kanana).
|
YAKAR KAFIRAI DA MUNAFIKAI
Wannan jihadin ya kan kasance, a zuciya,da
harshe, da dukiya, da rai.
|
YAKAR MA'ABUTA ZALUNCI DA BIDI'OI DA
MUNANAN AYYUKA
Wannan jihadin shima ya kan kasance da hannu, da
harshe, da zuciya.
|
.
RUFEWA
WAJIBI NE GA KOWANE MAI HANKALI YA YI TUNTUNI CIKIN WANNAN LITTAFI MAI
GIRMA, YA BASHI KULAWA TA MUSAMMAN, MATUKA; SABODA ABINDA LITTAFIN YA KUNSA, NA
GINSHIKAI MASU GIRMA, WANDA KOWANE MUTUM KE BUKATARSU A CIKIN KABARINSA.
Allah ne mafi sani, Salatin Allah da
sallamarsa su kara tabbata ga annabi Muhammadu da iyalansa da sahabbansa.
|
USULUL SALASA
(sune, a takaice, Tambayoyin kabari), dalilansu, Me ya sa muke karanta
Tauhidi? Me yasa muke karanta Usulus Salasa? Menene fa'idar karanta ta?
|
Mas'aloli hudu
da dalilinsu (suratul Asr)
|
Mas'aloli uku
|
ILIMI
|
AIKI DA SHI
|
DA'AWA ZUWA GARE SHI
|
HAKURI KAN CUTARWAR
DA KE CIKINSA
|
TAUHIDIN RUBUBIYYA (Wanda ya
kadaitu da aikin rububiyya, ba makawa, shine za a kadaita shi da ayyukan
ULUHIYYAH), da Tauhidul ASMA'U WAS-SIFAAT.
|
TAUHIDIN ULUHIYYAH (Ikhlasi), da
cewa: Lallai ne Allah baya yarda kan a hada shi da wani cikin bautarsa,
Mala'ika ne makusanci, ko Annabi Manzo.
|
BARRANTA DAGA SHIRKA DA MA'ABUTANSA: Da zuciya (ta hanyar
kin kafirai), da kuma harshe (LALLAI NE NI NA BARRANTA DAGA ABINDA KUKE BAUTAWA), Da kuma gabbai (Kin tarayya da su, cikin idinsu da
bukukuwansu, da rashin kamantacceniya da su).
|
Sanin Allah, Sanin Annabin Allah
–صلى الله
عليه وسلم-, Sanin addinin Allah, da
dalilai (wato, Usulus salasa).
|
""ILIMI YANA HUKUNTA AIKI' IDAN
HAR YA AMSA MASA SHI KENAN, IDAN KUMA BA HAKA BA, SAI ILIMIN YA KAURA
KUMA MALAMIN DA BAI YI AIKI DA ILIMINSA BA
ZA A AZABTA SHI GABANIN MASU BAUTAR GUMAKA"
|
SHARUDDAN DA'AWA: Ikhlasi,
ilimin shari'a, sanin halin wanda wanda ake masa da'awa, hikima, hakuri.
|
Farkon abinda ake da'awa zuwa
gare shi, shine Tauhidi, kuma wannan it ace da'awar Annabawa da Manzanni.
Kuma mafi girman martabobin da'awa shine tauhidi, da kore shirka.
|
Hakuri kan biyayya ga Allah
kamar (salla), da hakuri kan barin sabo, kamar riya, da hakuri kan kaddarar
Allah masu daci, kamar talauci.
|
Wato, Hakuri kan ilimi, sa'annan
sai hakuri akan aiki, sa'annan hakuri akan da'awa.
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
USULUL SALASA
(sune, a takaice, Tambayoyin kabari), dalilansu, Me ya sa muke karanta
Tauhidi? Me yasa muke karanta Usulus Salasa? Menene fa'idar karanta ta?
|
|
|