HUXUBAR IDI
DAGA MASALLACIN ANNABI
(صلى الله
عليه وسلم)
LAHDI,01/SHAWWAL/1438H
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI DR. HUSAIN XAN ABDUL'AZIZ ALUS-SHAIKH
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
IDI
Shehin Malami wato: Husain xan Abdul'aziz Alus-Sheikh
–Allah ya
kiyaye shi- ya yi hudubar idin azumi na shekarar 1438H, mai taken: IDI, Wanda kuma ya tattauna a
cikinta, akan Yadda idi yake a musulunci, da abinda yake tattare da su na
walwala da bayyanar da farin ciki, da jin daxi, da annashwa, kuma a cikin
huxubarsa ya bayyana wajabcin aiki da shari'a, da kuma komawa izuwa ga ma'abuta
ilimi a lokacin matsaloli da fitintinu.
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
ALLAHU AKBAR
ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD
Idi a
musulunci yana xauke da manufofi maxaukaka, saboda a cikinsa ne musulmai ke
farin cikin kammaluwar xa'arsu (ta azumi) ga Ubangijinsu, kuma su ke yin
walwala ko nuna farin ciki; saboda buxa-bakinsu a bayan azuminsu, Manzon Allah
(صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Mai azumi yana da
farin ciki iri biyu; farin ciki a lokacin buxa-bakinsa, da wani farin cikin a
lokacin saduwarsa da UbangijinSa".
A cikin
idi, akwai tuna manyan ginshiqai masu girma, wanda daga cikinsu, akwai, YADDA
MUSULUNCI YA KWAXAITU WAJEN TABBATAR DA SOYAYYA A TSAKANIN MUSULMAI, DA KUMA HALIN
QAUNA TSAKANIN MUMINAI, Allah (تعالى) yana
cewa: "Kuma muminai maza da mata, sashensu majivinta sashe ne" [Tauba:
71],
Don haka,
wajibi ne, mu riqi idi a matsayin sababin qarin sadar da zumunci, da qauna, kuma
dama ta yin watsi da xabi'ar kyashi da qiyayya, Allah (تعالى) yana cewa: "Lallai ne muminai
'yan'uwana ne" [Hujurat: 10].
Kuma Manzon
Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Misalin muminai
cikin soyayyarsu da qaunar junarsu, kamar misalin jiki ne guda xaya".
A lokacin
idi, ana mana kiraye-kiraye da cewar mu riqa yaxa farin ciki, da shigar da shi
ga rayuka, da kuma qarfafa ma'anonin rahama da jin-qai, da kyautatawa, da taimako.
Manzon
Allah (صلى الله عليه وسلم) ya farlanta
zakkar fid-da-kai, kuma ya ce: "Ku wadatar da faqirai, daga fita neman
abinci, a yinin idi", Ad-daraquxniy ya rawaito shi.
'YAN'UWANA
MUSULMAI…
Daga jerin
qiyayyar maqiya, akwai wanda su ke quqqulla shi ga qasar harami guda biyu (ta
Saudia), qarqashin tsare-tsare na qarya, da launukan tsegumi masu munanan
manufa, wanda ake qulla makircinsu ga qasar da ta ke rayuwa akan addinin musulunci,
a matsayin manhaja ko tsarin rayuwa, Qur'ani kuma da Sunnah a matsayin
konsutushin.
Qasar da aikinta
da ya fi muhimmanci shi ne hidimar harami biyu, wanda su ka qunshi matattarar imani
(wato, Madina), da kuma wurin bege ko makomar zukatan Musulmai (wato, Makkah),
KU SAURARA!
Lallai wajibi
ne akan kowane musulmi, alhalin yana sane da cewa, lallai wannan qasar, qasar
kowani musulmi ne, kuma wurin begen kowani mumini, wajibi ne a kansa, ya samu
yaqinin cewa, lallai yin gaba da wannan qasar, gaba ne da ma'abutan musulunci
gaba xayansu, kuma tava tsaronta da zaman lafiyarta cutarwarsa da hatsarinsa
zai tava kowane musulmi.
YA KU TARON
MUSULMAI!...
Al'ummar
musulmai tana rayuwa cikin xinbin canje-canje, da tashin-tashina, da abubuwa
masu rikitarwa, da mushkiloli da tsanani da qunci.
Kuma lallai
qasar harami biyu, ita ce cibiyar da ta fi girma, kuma tushen qasashen
musulmai, kuma tava wannan qasar da sharri, lallai mafari ne na yin kaca-kaca ko
kekketa, wannan al'ummar, kuma shi ne gudumar rusau da zai rushe haxin kan
al'ummar, da wargajewar samuwarta, kuma saboda wannan qasar, ita ce ke bada
kulawa ga harami biyu, da lamarin hajji da umrah, don haka ita ce alamar buwaya
da xaukaka ga musulmai gaba xaya.
Kuma don
haka ne, ya zama wajibi a kula da waxannan ma'anonin, a kuma haxa hannu don
taimakon wannan qasar wajen aikata abinda a cikinsa alkhairin musulmai ya ke,
da kuma kawo gyara ga halin da su ke ciki, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma ku yi
taimakakkeniya, akan biyayya da taqawa, kuma kada ku yi taimakakkeniya akan
zunubi da zalunci" [Ma'idah: 2].
YA KU BAYIN
ALLAH…
Kuma lallai
abinda ya xoru na wajibi, akan mutanen wannan qasar, ya fi girma, kuma alhakin
da ya rataya a wuyansu lallai ya fi, wajen zama tamtar tsoka xaya, ko haxewa
tare da jagororinsu, irin haxewar da soyayya za ta riqa bayyana da ita, da kuma
girmamawa da jin umarninsu da yi musu biyayya, cikin abinda ba savon Allah ba, da
taimaka wa juna wajen samar da abinda a cikinsa yardar Allah Mabuwayi da
xaukaka ta ke, da kuma dukkan ababen da akwai maslaha da amfanin kowa-da-kowa, kuma
yin hakan lalura ne da ta zama dole a shari'a, kuma maslahar qasa ce, kuma
buqata ce ga dukkan mutane.
Kuma wajibi
ne, a kiyaye bin kowace fitina, ko hanyoyi, ko kiraye-kirayen da su ke barazana
ga qasarmu, ko za su iya shafar amincinta da zaman lafiyarta, kuma farillar da ta
zama wajibi a shari'a ita ce, tsayuwar dako (daga kowani mutum), a matsayin
sojoji, da su ke a haxe, su ke taimakakkeniya, don tunkuxe kowani mai jiran
ganin sharri, da wanda zai kawo hari, ko ya yi ta'addanci, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma ku yi riqo da
igiyar Allah gaba xaya, kada ku rarraba" [Ali-imrana: 103].
Kuma Allah (تعالى) ya
ce: "Ya ku waxanda su ka yi imani ku yi xa'a wa Allah, kuma ku yi xa'a ga
Manzonsa, da majivinta lamura daga cikinku" [Nisa'i: 59].
YA KU TARON
MUSULMAI!...
Lallai
mafi girman makami domin yaqar mushkilolin wannan al'ummar, da abinda ta ke
fiskanta na qalu-balen da su ke fiskantarta (a koda-yaushe), da xinbin hatsarin
da su ke kewaye da ita, shi ne YIN AIKI NA GASKIYA, DA XAUKACIN
KARANTARWAR MUSULUNCI, a matsayinsa na salo kammalalle da ya game dukkan
sha'anonin rayuwa. Tare kuma da yin aikin cikin da'irar 'YAN'UWANTAKA
TA MUSULUNCI, DA GAMAYYA TA IMANI, "Lallai ne Mutum
yana cikin hasara * sai dai waxanda su ka yi imani, kuma su ka yi aiki nagari, kuma
su ka yi wasici da gaskiya, kuma su ka yi wasici da haquri" [Asr:
2-3].
'YA'UWANA MUSULMAI!...
Yana daga
ni'imomimanya, ga wannan qasa (ta Saudia), DAIDAITUWAN LAMARI SHUGABANCI
DA JAGORANCI, Wanda da su maslahohi na xaukacin al'umma da na xaixaikunsu
gaba xaya su ke tsaruwa, kuma gamammun lomura da kevantattunsu su ke iya
daidaituwa, kamar yadda Aljuwainiy ya ke faxa.
Kuma yana daga
cikin haka, Abinda ya kasance a cikin waxannan dararen na zavin da ya
yi daidai, wanda Sarki mai hidimar harami biyu maxaukaka ya yi; (wato, na zaven
Yarimansa mai jiran gado, a cikin wani yanayi da ya cika da sanya albarka, daga
kowa-da-kowa, Don haka; godiya ta qara tabbata ga Allah, akan abinda ya cika
mana na ni'imar haxuwar zukata da rashin rarrabansu.
Kuma lallai
Mu, a lokacin da mu ke mubaya'a ga Yarima mai jiran gado, akan littafin Allah, da
sunnar ManzonSa, da kuma ji da biyayya, a cikin nashaxi ko tilasci, ko matsatsi
ko sauqi, lallai muna roqon Allah, da ya sanya albarka cikin ayyukan sarki mai
hidimar harami guda biyu, kuma ya tsawaita rayuwarsa cikin xa'ar Allah. Ya kuma
datar da Yarima mai jiran karagar mulki, ya taimake shi kan ayyukansa, cikin
abinda zai yardar da Allah (سبحانه), kuma
ya sanya shi, ya zamo mabuxin alherori, marfin toshe kowane sharri, kuma ya
sanya albarka cikin ayyukansa, kuma ya dabaibaye su da cin nasara da dace.
Allah ya
kiyaye wannan qasar, da sauran qasashen musulmai, kuma ya datar da su gaba
xayansu, zuwa ga ababen da yardarsa ta ke cikinsu.
ALLAHU
AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMD
Allah
yayi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da
KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, Ina faxar maganata wannan, kuma ina neman
gafarar Allah, ku nemi gafararSa,
lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
HUXUBA TA BIYU
ALLAHU AKBAR
ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD
YA KU
'YAN'UWANA MUSULMAI…
Ku daidaitu akan ayyukan
biyayya ga Ubangijinku, kuma ku yi gaggawar neman samun yardarsa, a dukkan
lokutanku, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma ka bauta wa Ubangijnka, har mutuwa ta zo maka" [Hijr: 99].
'YAN'UWANA
MUSULMAI…
Wasiqar aminci ne da
soyayya da gaisuwar idi za mu tura, ga zaratan sojojinmu, waxanda su ka xauki
nauyin kare iyakoki, muna muku gaisuwar wannan idin,
Allah kuma ya girmama ladanku,
ya ninninka sakayyarku,
Kuma ya kiyaye ku ta gaba
gare ku, da ta bayanku,
Kuma Allah ya karvi waxanda
su ka yi mutuwar shahada daga cikinku,
Ya kuma bada lafiya ga
marasa lafiyan cikinku,
Ya warkar da waxanda aka
musu rauni daga cikinku
Kuma ya qarfafi zukatanku,
ya tabbatar da duga-duganku.
YA KU TARON
MUSULMAI…
Musulunci addinin zaman
lafiya ne da dukkan ma'anoninsa, da kuma haxin-kai da dukkan kalolinsa, da jin
qai da tausayi da dukkan shakalolinsa, da kyautatawa da fiskokinsa masu yawa, sai
ku bayyanar da hakan cikin ayyukanku, ku fito da shi a sarari a cikin
mu'amalolinku, ku yaxa shi ga duniya, kamar yadda jerin halayyar Alqur'ani da
kuma Annabi su ke, wajen tabbatar da dukkan aiki managarci, da kuma magana mai
kyau.
Kuma hanyoyin qetare iyaka,
da tsanantawa, da bin hanyoyin wuce gona-da-iri da ta'addanci, dukkan waxannan
addinin musulunci ya yi hani akansu, kuma waxannan halayen ba su tsayawa a
madadin karantarwar musulunci da manufofinsa da abinda musuluncin ke qoqarin
cimmawa, "Kuma
bamu turo ka ba, face jin-qai ga talikai" [Anbiya'i: 107].
"Kuma kada ku yi ta'addanci, saboda Allah baya son masu ta'addanci" [Baqara: 190].
Kuma lallai, Muna Allawadan
kaiwan harin tsoratarwa, wanda ya auku kusa da xakin Allah mai alfarma, kuma
wannan lamari ne mai girman muni, wanda addini da hankali basu amincewa da shi.
Kuma lallai Muna tsawatar
da samarinmu, kan ruxuwa da irin wannan aikin, ko bin shexanun da su ke nufin ruguza
addinin samarin, ko halaka su.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,