HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
صلى الله عليه وسلم
JUMA'A, 26/RAMADAN/1437H
Daidai da 01/Yuli/2016M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI ALIYU XAN ABDURRAHMAN AL-HUZAIFIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah Ma'abucin girma da
buwaya da xaukaka da karramawa, Wanda ya kwarara ni'imomi ga halittunSa, kuma
ya kwaxaitar da halittunSa kan godiya a gare shi domin ya musu qari; kuma domin
su kai ga samun cikar ni'ima, Ya kuma tsawatar musu kan yin butulci ga
ni'imominSa domin kada ya kwace su, kuma domin su tsira daga wulaqancin
uqobobin ma'abuta kafirci da fasiqanci da laifuka.
Ina yin yabo ga Ubangijina, kuma ina yin godiya
a gare shi, kuma ina tuba zuwa gare shi, ina neman gafararSa.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai
Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokan tarayya, Mamallaki, Mai tsarki wanda ya
kubuta daga naqasa da aibi.
Ina kuma shaidawa lallai annabinmu kuma
shugabanmu Muhammadu; bawanSa ne kuma manzonSa, wanda a lamarin ibadodi ya kai
ga samun mafi qololuwan matsayi .
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da
albarka ga bawanka kuma manzonka annabi Muhammadu, da kuma iyalansa da
sahabbansa masu karimci.
Bayan haka:
Ku kiyaye dokokin Allah da taqawa, Wanda ya
halitta ku, ya kuma shumfuxa muku daga falalarSa. Saboda Ubangijinmu ya
cancanci abi dokokinSa, kuma ya cancanci a qulla fata akanSa, saboda a hannunSa
ne duniya da lahira suke. Kuma lallai ba zai tave ba; Wanda ya yi bauta a gare
shi, ya yi fatanSa, Haka ba zai rabauta ba; Wanda ya butulce wa ni'imomin Allah
(ya kafirce musu) sannan ya bi son zuciyarsa!
Ya ku Musulmai!
Wannan shine watanku (na ramadana) shugaban
watanni, wanda a cikinsa rahama daga Allah ta lulluve ku, kuma ni'imomi a
cikinsa suka cika a kanku. Wata ne da Allah ya sauqar da alqur'ani mai girma a
cikinsa, wanda (qur'ani kuma) shine mafi girman rahama, kuma shi ne mafi girman
ni'ima. Kuma a cikinsa ne (watan ramadana) masu rabo suke rabauta, kuma ake
haramta aiki a cikinsa ga shaqiyyai tavavvu. Allah (تعالى)
yana cewa:
"Lallai wannan Qur'anin Ya kan shiryar izuwa
ga hanyar da tafi miqewa, kuma yana yin bushara ga muminai waxanda suke aikata
aiyuka na kwarai cewa lallai suna da
wani lada mai girma" [Isra'i: ].
Kuma Allah (تعالى) ya
ce:
"Waxancan ayoyin littafi ne mai hikima *
Shiriya ne da rahama ga masu kyautatawa" [Luqman:].
Kuma
Alqur'ani mai karimci shi ne mafi girman mu'ujizar annabinmu Muhammadu (صلى الله عليه وسلم). Babu wani da zai saurari alqur'ani
alhalin yana sanin ma'anoninsa face yayi imani da shi da gaskiya da
sakankancewa ta yaqini, da soyayya. Kuma babu wanda zai kafirce wa alqur'ani
face sakamakon girman kai da taurin kai da kawar da kai. Sai muminai suka rabauta,
su kuma masu kawar da kai ga bin alqur'ani suka tave suka yi hasara.
Lallai
wannan qur'anin mai girma, yana da qarfin tasiri ga rayuka da zukata, a cikin
watan ramadana da waninsa, Saidai kuma qarfin tasirin alqurani ga zukata a
cikin watan azumi yafi tsanani kuma yafi qarfi; wannan kuma, kasancewar ruhi ko
zukata su kan zama a tace, sakamakon yin azumi da sauran dangogin nau'ukan
bauta, Sai (ka ga) zukata sun karkata izuwa ga alqur'ani, suna masu ni'imtuwa
da shi. Sai kuma ababen da suke jan mutane zuwa ga sharri su yi rauni a cikin
jiki, sakamakon raunin ababen da suke qarfafan sharrori, da kuma yadda (mutane)
suke nisantar ababen da aka haramta, A lokacin, sai vangaren ruhi ya yi qarfi,
ya rinjayi son zuciya da fizgar shexanu.
Sai
ku yawaita tilawa da karatun wannan littafin (na Qur'ani) a cikin yininku da
suka rage (na ramadana), kuna masu yin tadabburinsa (tunanin ma'anoninsa);
saboda Allah bai saukar da wannan littafin mai girma ba, face don ya muku
rahama da shi,,,
Kuma duk wanda ya bibiyi ayoyi da hadisai zai
bayyana masa qarara cewa, lallai SAMUN RABO
gabaxayansa yana komawa ne ga/ KARATUN ALQUR'ANI MAI GIRMA, DA YIN
AIKI DA SHI, Allah (تعالى)
yana cewa:
"Lallai waxannan da suke karatun littafin
Allah, kuma suka tsayar da sallah, suka ciyar daga abinda muka azurta su, a
asirce, da a bayyane, suna aikata wata tijara ce, da bata halaka * Domin ya cika musu ladansu, kuma
ya musu qari daga falalarSa, lallai shi Mai yawan gafara ne abun godiya" [Faxir:
29-30].
Kuma Allah (تعالى)
yana cewa: "Kuma rahamata ta game kowani abu, kuma zan rubuta ta ga waxannan da
suke bin dokoki da taqawa, kuma suke bada zakka, waxannan da sune dangane da
ayoyinmu suke yin imani" [A'araf: 156].
Kuma an ruwaito daga Abdullahi xan Abbas, Wani
mutum ya ce: Ya Manzon Allah! Wani aiki yafi soyuwa a wurin Allah? Sai ya
ce: "Mai sauka da tashi, Saiya ce: Menene kuma mai sauka da tashi,
Sai ya ce: Shine wanda yake bugowa daga farkon alqur'ani har zuwa qarshensa,
duk lokacin da ya sauko, sai ya koma" Tirmiziy ne ya ruwaito shi.
Kuma an ruwaito daga Abdullahi xan Amru (رضي الله عنهما), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Za a ce wa
ma'abucin karatun alqur'ani, ka karanta, sai ka xaukaka, kamar yaddab kake
karanta shi da tartili a duniya; saboda matsayinka yana nan ne a qarshen ayar
da ka karanta ta", Tirmiziy ya tuwaito shi, da Abu-dawud.
Kuma
duk wanda ya yi aiki da alqur'ani, to yana cikin MA'ABUTA ALQUR'ANI koda kuwa
bai hardace shi ba.
Wanda kuma bai yi aiki da alqur'ani ba to baya
cikin MA'ABUTA ALQUR'ANI koda kuwa ya hardace shi.
Kuma
haqiqa alqur'ani ya sauka ne saboda MANUFOFI guda biyu masu girma, da kuma
aiyuka biyu manya-manya, NA FARKONSU: Kiyaye mutum daga zaluntar kansa,
Saboda wanda yafi girma daga cikin maqiyan Mutum shine Ransa da son zuciyarsa,
Allah (تعالى) yana cewa:
"Lallai, haqiqa Rai mai yawan umurni ne da mummuna"
[Yusuf: 53].
Kuma zaluntar da Mutum yake yi wa kansa yak an
kasance ne, ta hanyar fiskantar da dangogin bauta waxanda haqqin Allah ne (shi
kaxai), da kuma aiwatar da su ga wani abun halitta; ko ta hanyar roqon halitta,
ko rataya fata akansa, ko zartar da addu'a ko neman agaji daga halitta, Allah (تعالى) yana cewa:
"Lallai ne shirka zalunci ne mai girma" [Luqman:
13].
Kuma mutum ya zalunci kansa yana kasancewa ta
hanyar: BIN ABABEN JIN DAXINSA NA HARAM, DA TOZARTA FARILLANSA, Allah (تعالى) yana cewa: "Sai masu mayewa a
bayansu suka maye, kuma suka tozarta sallah, suka bi sha'awowi, kuma da sannu
za su haxu da kwarin azaba" [Maryam: 59]. Kwari ne a cikin wutar
jahannama.
MANUFAR QUR'ANI MAI HIKIMA NA BIYU kuma Shi
ne: Domin ya kiyaye mutum daga zaluntar xan'uwansa mutum; a cikin jininsa, ko
dukiyarsa, ko mutuncinsa, Kai, Alqur'ani ya haramta zaluntar dabba, saboda shi
zalunci shari ne gabaxayansa, ko wani mutum bai halaka ba, ko wata al'umma sai
saboda zalunci da qetare iyaka, Allah (تعالى)
yana cewa: "Kuma waxancan alqaryoyi ne, waxanda muka halaka su a yayin da suka
yi zalunci" [Kahf: 59].
Kuma Allah (تعالى) ya
ce: "Kuma dukkansu mun kama shi da zunibinsa, Daga cikinsu akwai wanda
muka tura masa iska, daga cikinsu akwai wanda tsawa ta kama shi, daga cikinsu
akwai wanda muka sanya qasa ta kama shi, daga cikinsu akwai waxanda muka
dulmuyar, Kuma Allah bai kasance zai zalunce su ba, saidai sun kasance
kayukansu suke zalunta" [Ankabut: 40].
Kuma
Alqur'ani ya zo a cikin watan azumi domin yaxa adalci, da kyautatawa, da
tunkuxe varna, Allah (تعالى)
yana cewa: "Lallai ne Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa
makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci " [Nahli: 90].
Kuma yana daga cikin MAFI GIRMAN ZALUNCI DA QETARE IYAKA:
Tauye wa mutane haqqoqinsu na ma'ana, da watsar da falalar da suke da ita, da
yin hassada a gare su, akan abinda Allah ya basu na ni'imomi, da aibanta su, ko
rage musu karamominsu, ta hanyar wani aiki ko maganar da zata rage matsayinsu
da martabarsu, da raina baiwar da suke da ita.
Kuma idan akwai wani qoqari na hana wani haqqi; na ma'ana
ne, ko na matsayi, da hana isar haqqin ga wanda ya cancane shi To lallai wannan
girma akan a zalunci mutum cikin dirhami ko dinari (dukiya).
Kuma a irin wannan halin,
kada ka tona cutuwar xan baiwar da ake masa hassada. Kuma lallai waxanda babu
wanda zai iya qididdige su (saboda yawansu) sai Allah suma za su iya cutuwa da
cutuwan wannan mutumin.
Kuma lallai, Bone ya
tabbata ga wanda masu husuma da shi cikin haqqoqi na ma'ana suka yi yawa
akansa.
Kuma kayi mamakin girman rahamar Allah, ta fiskar kare
mutum da alqur'ani daga dangogi ko nau'ukan zalunci da qetare iyaka gabaxaya,
Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma kada ku tauye wa mutane, kayansu" [A'araf:
85, Hud: 85, Shu'ara'i: 183].
Shi tauye
haqqi na ma'ana, ya fi tsananin zalunci, kuma ya fi girman ciyo ga rayukan da
basu ji ba, basu gani ba.
Kuma Allah
(تعالى) ya ce: "Bone na azaba ya
tabbata ga masu tauyewa * Waxannan da idan za su auna daga mutane su ke neman
cikawa * Idan kuma su ka zo aunar musu, ko gwada musu to sai su tauye * Shin,
waxannan ba sa zaton, cewa lallai su za a tayar da su * domin wani yini mai
girma * Yinin da mutane su ke tashi zuwa ga Ubangijin talikai" [Muxaffifina:
1-6].
Kuma, lallai daxin da ake samu a lokacin
zalunci, irin na hassada, ya kan qare cikin qanqanin lokaci, sai kuma ya bar wa
mutum nadama har zuwa tashin qiyama.
Bayin
Allah!
Wanda duk
ya kyautata aiki a cikin wannan watan, cikin abinda ya gabata daga cikinsa to
sai ya gode wa Allah, sai kuma ya qara qoqari.
Wanda kuma ya yi sakaci to sai ya tuba, ya
kuma yi qoqarin rufe watansa da aiyukan alkhairi; saboda aiyuka suna kyautata
ne da ababen da aka cike su da su.
Kuma kowani musulmi ya riqa roqan
kyakkyawar qarshe koyaushe, Ya zo daga Albara'u xan Azib, Ya ce: Wani mutum
da ya tare kansa da qarfe y azo wajen Annabi (صلى الله عليه وسلم) sai ya nce: "Shin zan yi yaqi, ko na musulunta? Sai ya ce: Ka
musulunta, sannan ka fita yaqi, Sai ya musulunta
sannan ya fita yaqi, Sai aka kasha shi, Sai manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace: Ya yi aiki
kaxan, an bashi lada dayawa"Bukhariy
da Muslim suka ruwaito shi.
Ka yi dubi, zuwa ga kyakyawan qarshe, da yadda
ya cika da aiki….
Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma ku gabatar wa
kayukanku, ku bi dokokin Allah da taqawa, kuma ku sani lallai ku masu saduwa ne
da shi, kuma ka yi bushara ga muminai" [Baqara: 223].
Allah
yayi albarka wa Ni da Ku cikin alqur'ani mai girma! Kuma ya amfanar da Ni da Ku
da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, kuma ya amfanar da mu
da shiriyar shugaban Manzanni, da maganganunsa miqaqqu.
Ina faxar Magana ta wannan, kuma ina neman
gafarar Allah, wa Ni da Ku, da sauran Musulmai; sai ku nemi gafararSa.
HUXUBA TA
BIYU
Godiya
ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Ina shaidawa babu abin bautawa da
gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, Mai matsanancin qarfi.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma
shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa.
Ya
Allah kayi qarin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka annabi Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa gabaxaya.
Bayan
haka!
Ku
kiyaye dokokin Allah da taqawa iyakar kiyayewa.
Bayin Allah!
Allah ya farlanta zakkar fid-da-kai don ta zama tsarki ga mai
azumi, da kuma An ruwaito daga Abu-Sa'id Alkhudriy, ya ce:
"Lallai Manzon Allah ya farlanta zakkar fid-da-kai, sa'iy xaya na
alkama, ko sa'iy na sha'ir, ko sa'iy na dabino, ko sa'iy na zabib, ko sa'iy na
aqid -cukui-".
Kuma yana isarwa a fitar da ita (wato: zakatul fixr) daga abincin gari,
kamar shinkafa, da masara, da dawa, da makamantansu.
Kuma gwargwadonta shi ne: Kilo uku (3kg), in banda xan
wani abu kaxan, saidai abinda ya fi tsantseni shine a bayar da kilo ukun.
Kuma
ana fitar da ita ga babban mutum da yaro, da namiji da mace.
Kuma ya halatta a fitar da ita gabanin idi da
yini xaya ko yini biyu. Saidai abinda yake da fifiko shine a fitar da ita
gabanin sallar idi.
Kuma sunna ne a dare da yinin idi, a yawaita
kabbarori, har zuwa fitowan limami, saboda faxin Allah (تعالى): "Kuma domin ku cika qidaya, kuma
domin ku yi kabbara wa Allah saboda baku shiriya da yayi, kuma domin ku yi
godiya" [Baqara: 185].
Bayin
Allah!
"Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga
wannan annabin, ya ku waxanda su ka yi imani ku yi salati a gare shi, da
sallamar amintarwa"
[Ahzab: 56].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Duk wanda
ya yi salati guda xaya a gare ni, to Allah zai yi salati a gare shi guda goma
saboda shi".
Sai ku yi
salati, da sallama ga shugaban na farko da na qarshe, kuma jagoran manzanni.
Ya Allah!
Ka yi salati wa annabi Muhammadu da iyalan
annabi Muhammadu kamar yadda ka yi salati wa annabi Ibrahima da iyalan annabi
Ibrahima, lallai kai Abun godiya ne, Mai girma.
Ya Allah!
Ka yi albarka wa annabi Muhammadu da iyalan
annabi Muhammadu kamar yadda ka yi albarka wa annabi Ibrahima da iyalan annabi
Ibrahima, lallai kai Abun godiya ne, Mai girma.
Ya Allah!
Ka yarda da sahabbai gabaxaya, da kuma wanda
su ka bi su, da waxanda su ka bi su da kyautatawa har zuwa ranar qiyama.
Ya Allah!
Ka yarda da khalifofi shiryayyu, kuma
shugabanni masu shiryarwa; Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da sauran
sahabban annabinka gabaxaya,
Ya Allah!
Ka yarda da tabi'ai da waxanda suka bi su da
kyautatawa (bi da bi) har zuwa ranar qarshe,
Ya Allah!
Ka yarda da mu tare da su, da baiwarka, da
rahamarka ya mafi rahamar masu rahama.
Ya Allah!
Ka xaukaka musulunci da musulmai,
Ya Allah!
Ka xaukaka musulunci da musulmai
Ya Allah!
Ka xaukaka musulunci da musulmai,
kuma ka qasqantar da shirka da mushirkai, ka
qasqantar da kafirci da kafirai, Ya Ubangijin talikai.
Ya
Allah !
Ka ruguza miqiyanka, maqiya addini,
Ya Allah!
Ka bada nasara ga littafinka da sunnar
annabinka, Ya Mai tsananin qarfi.
Ya Allah!
Ka daidaita tsakanin zukatan musulmai, kuma ka
gyara abinda ke tsakaninsu, da rahamarka ya mafi rahamar masu rahama,
Ya Allah!
Ka haxa kansu akan gaskiya, Ya Ubangijin
talikai, lallai kai Mai iko ne akan komai,
Ya Allah!
Ka xauke abinda ya sauka ga musulmai na ababen
baqin ciki, a kowani wurin da aka takura musu,
Ya Allah!
Ka xauke abinda ya sauka a gare su, na ababen
baqin ciki, da musibu, da abubuwa masu tsanani.
Ya Allah!
Ka ciyar da mayunwacinsu,
Ya Allah!
Ka wadatar da faqirinsu, Ya Ubangijin
talikai,
Ya Allah!
Ka amintar da tsoron masu tsoro daga cikinsu,
Ya Allah!
Ka saukar da aminci da rahama da yalwar
arziqi, da Imani, a garurrukan musulmai, Ya Ubangijin talikai,
Ya Allah!
Ka yi maganin azzalumai, waxanda su ke
zaluntar musulmai cikin jinanensu, su ke zaluntarsu cikin mutuncinsu, kuma su ke
zaluntarsu a cikin addininsu, kuma su ke takura musu cikin addininsu,
Ya Allah
Ka
yi maganinsu, saboda su, ba za su gagare ka ba.
Ya Allah!
Ka ji qan halin musulmai a qasar siriya, kuma
ka yi rahama wa halin musulmai a qasar Iraqi,
Ya Allah!
Ka gyara halin musulmai a qasar Yaman, da rahamarka
ya Mafi rahamar masu rahama.
Ya Allah!
Ka yi rahama da jin qai ga halin musulmai a
garin Sham, lallai kai akan komai Mai iko ne, Ya Ubangijin talikai, Ya
Ubangijin talikai. Kuma ka ji qan halin musulmai a kowani wuri, saboda suna da
buqatuwa zuwa ga rahamarka, lallai kai ne Mai iko akan komai.
Ya Allah!
Ka kiyaye qasashenmu, Ya Allah ka kiyaye
qasashenmu, daga 'yan ta'adda, da azzalumai, Ya Ubangijin talikai,
Ya Allah!
Ka kiyaye rundunoninmu,
Ya Allah! Ka datar da harbinsu
Ya Allah!
Ka kiyaye rundunoninmu a kowani wuri, ka
daidaita jifansu, kuma ka datar da su, kuma ka kiyaye su cikin dukkan abinda su
ke tsoronsa, Ya Ubangijin talikai, lallai kai Mai iko ne akan komai.
Ya Allah!
Ka datar da bawanka, mai hidimar harami biyu
maxaukaka, zuwa ga abinda ka ke so, kuma ka yarda da shi.
Ya Allah!
Ka datar da shi, zuwa ga shiriyarka, kuma ka
sanya aikinsa cikin yardarka, Ya Ubangijin talikai!
Ya Allah!
Ka taimaki gaskiya da ma'abutanta da shi,
Ya Allah!
Ka taimaki gaskiya da ma'abutanta da shi,
Ya Allah!
Ka taimaki gaskiya da ma'abutanta da shi, Ya
Ubangijin talikai, Ya Allah! Ka bada nasara waaddininka da shi, lallai kai mai
iko ne akan komai. Kuma ka datar da na'ibansa guda biyu, daga abinda ka ke so,
kuma ka yarda, kuma zuwa ga alkhairi ya ke cikinsa ga muslunci da musulmai, Ya
Ubangijin talikai.
Ya Allah!
Ka tsare mu da zurriyarmu daga Iblisa da
zurriyarsa da shexanunsa da rundunoninsa.
Ya Allah!
Ka tsare mu daga sharrin kayukanmu, da munanan
aiyukanmu.
Ya Allah!
Lallai ne mu muna neman tsarinka daga mummunan
qaddara, da dariyar qeta daga maqiya, da riskar tavewa, da wahalar da ke cikin bala'oi.
Ya Allah!
Lallai mu, muna roqonka Ya Ubangijin talikai
aikata alkhairori, da barin munanan aiyuka, da son miskinai.
"Ya Ubangijinmu ka
bamu me kyau a duniya, a lahira, me kyau, kuma ka kare mu daga azabar wuta" [Baqara: 201].
Ya ku bayin Allah!
"Lallai ne Allah
yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin
hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama
masu tunawa"
[Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai
ambace ku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shi ne
mafi girma, Lallai Allah ya san abinda ku ke aikatawa.
No comments:
Post a Comment