HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 12/RAMADHANA/1437H
Daidai da 17 /YUNI/2016M
LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULMUHSIN XAN MUHAMMADU XAN ABDURRAHMAN
ALQASIM
TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
AIYUKAN KWARAI A WATAN
RAMADHANA
Shehin Malami wato: Liman Abdulmuhsin
xan Muhammadu Alqasim –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: AIYUKAN KWARAI A WATAN
RAMADHANA,
Wanda kuma ya tattauna a cikinta, akan Watan Ramadhana, da abinda ke mamaye
yininsa da dararensa na aiyukan kwarai, waxanda bai dace ga bawa ya tozarta su
ba.
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne;
muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman
tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan aiyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar babu
mai vatar da shi, Wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su qara
tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.
Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da
taqawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa,
kuma ku riqa kula da Shi (Allah) a cikin sirri da a lokacin ganawa.
Ya ku Musulmai …
Samun xaukakar Mutum tana
cikin miqa wuya ga umurnin Allah, da tabbatar da bauta a gare shi, Shi kaxai;
ba tare da an haxa shi da wani ba. Wannan kuma shine ma'aunin fifiko a tsakanin
bayi. Duk wanda ya yi nufin samun rabo na har abada to sai ya lazimci qofar
bauta. Kuma zamani lokaci ne mai faxi don yin tsere a tsakanin bayi cikin
bauta. Wanda aka yi masa dace shine Mutumin da ya ribaci lokacin numfasawarsa
cikin ababen da suke yardar da UbangijinSa. Kuma lallai Allah a cikin yininSa
(da ya halitta) yana da wasu lokutan da yake yin baiwa da su ga bayinSa. Shi
kuma Mutum mumini yana bijiro da kansa (ta hanyar yin bauta) don yayi dacen da
babu tavewa a bayansa har abada.
Ga nan ramadhana wanda
shine jagoran sauran watanni ya halarto, wanda kuma lokaci ne na alkhairori, da
yin gaggawa cikin aiyukan samun qarin kusanci, A cikin kwanakin watan kyautukan
Allah da albarkoki da baiwa suna yawaita kuma suna qaruwa, saboda Allah a
cikinSu yana girmama lada, kuma yana gwavava kyautayi, kuma yana bubbuxe
qofofin alkhairi ga dukkan mai kwaxayi. Allah ya kevance ramadhana da falaloli
akan sauran watanni, kuma ya kevance al'ummarmu da wannan wata akan sauran
al'ummai, a tsawon zamani. Yin aiki a cikinsa abun godiya ne, Shi kuma mumini a
cikinsa mai farin ciki ne. lallai ramadhana ya sauka a cikinku, kuma bayan
lokaci kaxan zai tafi ya bar ku, kuma zai yi shaida (a wajen Allah) a gare ku,
ko a kan ku. Kuma watan yana shelanta rabautar wasu mutane, da tavewar wasu.
Ramadhana wata ne mai
albarka, Allah a cikinsa ya saukar da mafi girman littafinSa, Allah (سبحانه) ya ce:
"Watan ramadhana
wanda aka saukar da alqur'ani a cikinsa" [Baqara: 185].
Kuma a cikinsa ake bubbuxe
qofofin aljannah, a rufe qofofin wuta, a sanya shexanu cikin sarqa da aljanu
masu tsaurin kai. Wata ne da aka kewaye shi da rahama da yin gafara da samun
yardar Allah.
Kuma a cikin ramadhana ake samun LAILATUL QADARI dare mai
albarka wanda yafi alkhairi akan watanni dubu, kuma saboda falalar wannan dare
Mala'iku suke sassuka a cikinsa, har da mala'ika Jibrilu, Kuma a daren aminci
har ketowar alfijir.
Wata ne da ake kankare zunubai a cikinsa da aiyukan savo,
Manzon Allah (صلى
الله عليه وسلم) ya ce:
"Da
ramadhana zuwa ramadhana, masu kankare abinda ke tsakaninsu ne matuqar an
nisanci kaba'irai", Muslim ya ruwaito shi. "Kuma
Mutumin da watan ramadhana ya shiga sa'annan ya fita, ba a gafarta masa ba,
Allah ya turbuxa hancinsa da turvaya", Tirmiziy ya ruwaito shi.
Dayawa daga taimakon da aka yi wa Musulmai ta hanyar basu
nasara ya kasance ne a cikin watan azumi (na ramadhana), kamar buxe garin
Makka, da yinin rarrabe gaskiya da qarya (lokacin Badr, to يوم الفرقان).
Kuma a cikin watan
ramadhana ginshiqan ibadodi suke haxuwa, kuma aiyukan alkhairi da Imani suke
yawaita. Kuma a cikinsa Allah ya shar'anta aiyukan da suke nauyaya ma'auni.
Kuma yana daga SHIRIYAR MANZON ALLAH (صلى الله عليه وسلم) Yawaita nau'ukan bauta a cikin watan
ramadhana. Kuma yana qara kwazo a cikin dararen ramadhana da yininsu; irin
abinda baya aikatawa a sauran watannin da ba shi ba.
Kuma akan haka Magabatan
wannan al'ummar suke, da kuma salihan bayi. A lokacin da mutuwa ta zo wa Amir
xan Abdulqais, sai ya kama kuka, Sai ake ce masa, Me ya sanya ka kuka? Sai ya
ce:
"Ba wai ina yin
kuka ne don tsoron mutuwa, ko don kwaxayin duniyar (da zan rasa ta) ba, Saidai
ina yin kuka ne, kan qishin da tsananin zafin rana ke haifar da shi –wato:
azumi-, da kuma dena sallar dare "qiyamullaili".
Mafificin aiyukan kusantar Allah shine: IKHLASIN
AIYUKA GA ALLAH, DA TAUHIDI, da kuma BIN SUNNAR ANNABI (صلى الله عليه وسلم).
Ita kuma SALLAH ita ce ginshiqin addini, kuma haske ga muminai. Kuma da ita aiki ke
inganta, ya samu karvuwa. Kuma ita ce farkon abinda za a yi hisabi wa bawa a
cikin addininsa, kuma lallai bai san ramadhana ba wanda ya yi barci bai yi
sallar farilla ba. Kuma lallai ya gafala ga sunnar ramadhana wanda yayi kasala
bai yi sunnoninsu da sallolin rawatib ba.
Shi kuma AZUMIN WATAN RAMADHANA alamar yin biyayya da
xa'a ya tattaru ne a cikinsa (taqawa). Allah ya farlanta shi akan Mutane, kuma
ya sanya shi ya zama xaya daga cikin rukunnan musulunci, Allah (سبحانه) yana cewa:
"Ya ku waxanda suka
yi Imani an wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta shi ga waxanda suke
gabaninku"
[Baqara: 183].
Kuma Allah ya kevance azumi wa kansa, savanin sauran
aiyukan, sannan ya sanya sakamakonsa ya zama ba tare da qidayawa, ko hisabi ba,
Manzon Allah (صلى
الله عليه وسلم) ya ce:
"Dukkan
aiyukan xan Adam ana ninnika masa, kyakkyawa xaya da kwatankwacinsa goma, har
zuwa ninki xari bakwai, har zuwa abinda Allah ya nufa", Ibnu-Majah ya
ruwaito shi.
Azumi ibana ne -a cikin Musulunci- mai girma, Abu-Umamah (رضي الله عنه) ya ce:
"Na zo wajen
Annabi (صلى الله عليه وسلم) sai na ce: Ka umurce ni da wani abu,
wanda zan koye shi daga wurinka, sai ya ce: Ina umurtarka da yin azumi, saboda
babu kamarsa",
Annasa'iy ya ruwaito shi. "Kuma duk wanda ya yi azumin
ramadhana yana mai Imani da neman lada, to an gafarta masa abinda ya gabata na
zunubansa",
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi. "Kuma irin jarabawar da ake
yi wa mutum cikin iyalansa da dukiyarsa da kansa da 'ya'yansa da makwabcinsa azumi
yana kankare su",
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma lallai yin azumi ya kan zama fansa ne (fid-ya) ga
wasu aiyukan, ko kuma kaffara a gare su. Kuma da yin azumi bawa ke suturce
kansa daga faxawa cikin zunubai, da wuta, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Azumi garkuwa ne",Tirmiziy ya ruwaito
shi.
"Kuma warin
bakin mai azumi yafi daxi a wurin Allah (تعالى)
fiye da turaren almiski", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma a cikin gaggauta buxa
baki, da jinkirta sahur alherin wannan al'ummar yake.
Kuma a ranar qiyama azumi
zai zo yana mai neman a bashi ceton ma'abutansa, "Sai azumi
ya ce: Ya Ubangijina! Lallai na hana shi cin abinci da ababen sha'awarsa cikin
yini; sai ka bani cetonsa. Sai alqur'ani shima ya ce: Ya Ubangijina! Lallai na
hana shi yin barci da dare, ka bani cetonsa. Ya ce: Sai a basu ceton", Ahmad ya ruwaito
shi.
Kuma ita aljannah Allah ya
yi tanadinta ga mutumin da ya daxaxa maganarsa, kuma a jikinta akwai wata qofa
mai suna: ARRAYAAN, Babu mai shiga aljannah ta cikinta face masu azumi. Kuma
idan suka shige ta sai a ce musu:
"Ku ci, ku sha cikin
daxin rai, saboda abindakuka gabatar a cikin yini da suka shuxe" []. Mujahid –رحمه الله- ya ce: "Wannan
ayar ta sauka ne kan masu azumi".
Kuma da wannan watan (na ramadhana) farin ciki ke sauka,
Manzon Allah (صلى
الله عليه وسلم) ya ce:
"Mai azumi
yana da dangin farin ciki iri biyu da zai yi su; (Na farko): Idan ya buxe
bakinsa sai ya yi farin ciki da zuwan lokacin buxa-baki. (Na biyu:) Idan kuma
ya sadu da UbangjinSa sai ya yi farin-cikin yin azuminsa", Bukhariy ya ruwaito
shi.
Kuma azumi dukkansa alheri ne, Allah (سبحانه) yana cewa:
"Kuma ku yi azumi
shine yafi alheri a gare ku" [Baqara: 184].
Kuma lallai shi azumi yana da MANUFOFI da HIKIMOMI masu
girma, saboda a cikin azumi ne bawa ke yin aiki na kulawa da UbangijinSa a
asirce da a bayyane, kuma zai bi dokokinSa da taqawa, domin ya rabauta da samun
aljannarSa, da kuma Yardarsa, sannan ya katange shi daga aukawa cikin fushinSa
da wutarSa. Kuma a cikin azumi akwai qoqarin tabbatar da ibadar haquri kan
yin biyayya, da haquri kan qaddarorinSa, da nisantar hane-hanensa, da sava
masa. Shima
kuma gyaran kai da qoqarin tsarkake zuciya yana samun qarin kamala a cikin
watan azumi. Kuma kiyaye gavvai, da tsarkake halayya sune busharar mai azumi ta
gaggawa,Manzon Allah (صلى
الله عليه وسلم) ya ce:
"Idan ranar
azumin xayanku ya kasance to kada ya yi kwarkwasa, kada ya yi Shewa, Idan wani
mutum ya zage shi, ko ya nemi yin faxa da shi sai y ace: Lallai ni mai azumi ne", Bukhariy da Muslim suka
ruwaito shi.
Kuma sha'awowi suna raunana da yin azumi, kuma zuwa ga
hakan Annabi (صلى
الله عليه وسلم) ya shiryar da mutumin da ya gaza kan yin aure, a inda ya ce:
"Wanda kuma
bai samu ikon aure ba, ina horonsa da yin azumi, saboda azumi a gare shi kamar
fixiya ne",
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma da yin azumi ake samun lafiyar jiki, da kwakwale, da
taushin zuciya, da samun kusancin Allah; Mai rahama. Kamar yadda azumi ke
katange gavvai daga aikata savo, kuma ya tavar da Shaixanu. Kuma da yin azumi
bawa zai qara gane wasu ni'imomin da Allah ya yi a gare shi; sai ya yi godiya,
Allah (تعالى) yana cewa (a qarshen ayar azumi):
"Kuma domin ku cika
qidaya…"
[185].
Kuma da yin azumi bayi suke qara gane rauninsu, da kuma
buqatuwarsu zuwa ga Ubangijinsu.
Kuma a cikin azumi, sauqin musulunci da rangwamensa suna
qara bayyana, a inda ya yi hani kan wucel (وصال), kuma ya sunnanta yin sahur, da jinkirta shi, da kuma gaggauta
buxa baki. Kamar yadda yayi rangwamen karya azumi ga matafiyi, da maras lafiya,
da mai ciki da mai shayarwa.
A cikin watan ramadhana, lamarin sunnancin sallolin dare
yana qara qarfafa, kuma sallar dare tana cikin sifofin 'yan aljannah "Sun kasance kaxan
ne, daga cikin dare suke kwantawa" []. "Kuivinsu suna nisantar wuraren
kwanciya, suna roqon Ubangijinsu cikin tsoro da kwaxayi" [].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Wanda yayi
tsayuwar ramadhana (sallah) yana maiimani da neman lada, to an gafarta masa
abinda ya gabata na zunubansa", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
"Wanda yayi
sallah tare liman har y agama, to an rubuta masa ladan tsayuwan dare", Tirmiziy ya ruwaito
shi.
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance idan goman qarshe suka shiga sai ya tamke
kwarjallensa, ya raya darensa.
Kuma a cikinsu ake samun lailatul qadari, "Wanda ya
sallace ta yana mai Imani da neman lada to an gafarta abinda ya gabata daga
zunubansa",
Bukhariy da Muslim.
Ita kuma SADAKA hujja ce (da take nuna imanin mai yinta),
kuma mafificinta ita ce sadakar da aka yi ta a watan ramadhana. Idan yunwa da
qishi suka kama ka, to sai ka tuna 'yan'uwanka waxanda a tsawon rayuwarsu suke
fama da hakan.
Kuma Allah Mai karimci ne,
yana son yinkyauta.
Shi kuma Annabinmu (صلى الله عليه وسلم)
shine yafi dukkan mutane kyauta, kuma kyautat tasa tafi yawa a cikin watan
ramadhana, a lokacin da mala'ika Jibrilu yake saduwa da shi don yayi bitar
alqur'ani. Kuma lallai shi, shi yafi kyautar alkhairi fiye da sakakkiyar iska. Saboda ba a roqonsa wani
abu face ya bada shi.
Sai ku ciyar daga dukiyarku ta halal, kuma ku nemi
ladanku a wajen Allah. Saboda da yin sadaka ake samun albarkar dukiya, da
tsarkin rayuka. Kuma kowani mutum yana qarqashin inuwar sadakarsa a ranar
tashin qiyama. Kuma yana daga cikin waxanda zai sanya su qarqashin inuwar
al'arshinSa "Da mutumin da ya bayar da wata sadaka, sai ya voye ta, har ya
zama haqunsa bai san abinda damansa ya ciyar ba", Bukhariy da Muslim.
Kuma shi mumini baya raina abu, saboda dayawa dirhami
xaya ka riga dirhami dubu.
Kuma yana daga cikin sadakoki: SHAYAR DA RUWA DA CIYAR DA
ABINCI, "Duk wanda ya baiwa mai azumi abin buxa-baki to yana da
kwatankwacin ladansa, ba tare da ya tawaye wani abu daga cikin ladan mai azumin
ba",
Tirmiziy ya ruwaito shi.
Kuma Abdullahi xan Umar (رضي الله عنهما) ya kasance yana yin azumi, saidai kuma
baya yin buxa-baki sai tare da miskinai.
Shi kuma haxa yin sadaka da azumi yana daga ababen da
suke hukunta shiga aljannah.
Duk wanda ya yi kyauta wa bayin Allah to sai Allah yayi
masa kyauta da falala, kuma sakayya ta kan kasance daga jinsin aiki, Manzon
Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Lallai a
cikin aljanna akwai wasu xakuna, waxanda ake ganin zahirinsu daga cikinsu, ake
kuma ganin cikinsu daga wajensu. Sai wani balaraben qauye ya tashi
yace: Na wanene xakunan, ya Manzon Allah! Sai ya ce: Na mutumin da ya daxaxa
Magana ne, ya ciyar da abinci, ya dawwamar da yin azumi, kuma ya yi sallah da
dare alhalin mutane suna barci", Tirmiziy ya ruwaito shi.
Ita kuma YIN UMRAH
a cikin watan ramadhana tana daidai da yin hajji.
Wanda yafi mutane yawan
lada a cikin wannan watan shine wanda ya fi su, yawaita ambaton Allah. Kuma
mafi alherin zikiri shine TILAWAR ALQUR'ANI mai girma. Allah (سبحانه) yana cewa:
"Lallai waxanda suke
tilawar littafin Allah, suka tsayar da sallah, kuma suka ciyar daga abinda muka
azurta su, a sirrance da a bayyane, suna fatan wata tijara ce, wanda bata
lalacewa…"
[].
"Kuma duk
wanda ya karanta wani harafi daga cikin littafin Allah, to yana da lada mai
klyau akansa, ita kuma ladan za a ninka ta har sau goma", Tirmiziy ya ruwaito
shi.
"Wanda ya gwanance a karanta qur'ani yana tare da jekadu
masu karimci masu biyayya (mala'iku)", Muslim.
Kuma a cikin kowani dare daga ramadhana mala'ika Jibrilu
(عليه السلام) ya kasance yana yin
bitar alqur'ani (darasu) tare da annabinmu. A shekarar da ya rasu a cikinsa
kuma, yayi bitar har sau biyu. Kuma Azzuhuriy –رحمه الله- ya kasance idan watan ramadhana ya shiga, yak an ce:
"Kawai,
karatun alqur'ani ne, da ciyar da abinci".
Yana kuma daga cikin samun rabo Fiskantar littafin Allah
da yin karatunsa da zukatan da suke halarce, da yin tunani na tadabburi cikin
ayoyinsa, da yin aiki da waxanda ba asoke su ba (محكم).
Babu wani abu da yafi matsayi a wurin Allah fiye da ADDU'A,
kuma shine sila miqaqqe tsakanin bawa da UbangijinSa, kuma ba a riqan tsani a
cikinsa, ko wani shamaki, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma idan bayina
suka tambaye ka akaina, ka ce: Lallai ni Makusanci ne, ina amsa addu'ar mai
addu'a idan ya roqe ni, Sai su nemi amsawata, suyi Imani da ni, tsammanin za a
shiryar da su"
[Baqarah: 186].
Kuma addu'ar mai azumi ba a
mayar da ita. Kuma addu'ar da aka fi amsawa ita ce wanda aka yi ta a cikin
dare, ta qarshe, da qarshen sallolin farilla.
Shi kuma I'ITIKAAF qarin kusanci zuwa ga Allah, kuma
Sunnah, A'isha (رضي
الله عنها) ta ce:
"Manzon
Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana yin 'I'itikafin kwanaki
goman qarshe na ramadhana, har Allah mabuwayi da xaukaka ya karvi ransa",Bukhari da Muslim
Azzuhuriy –رحمه الله- yana cewa:
"Mamakin
lamarin musulmai waxanda suka bar yin I'itikaaf, saboda lallai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم)
be bar yin I'itikafi a goman qarshe ba tun da ya shiga garin Madina har Allah
ya karvi ransa".
Su 'ya'ya amana ce, kuma karama, kuma Allah zai tambaye
ka akansu. Kuma da gyaruwansu zaka amfana bayan mutuwarka, sai darajarka ta
xaukaka a wurin Ubangijinka. Don haka wajibi ne akan mai azumi ya lura da
'ya'yansa da iyalansa, kuma ya zama mafi alherin mai taimako a gare su wajen
yin biyayya wa Allah; sai ya riqa shiryar da jahilinsu, yana tunatar da wanda
ya gafala daga cikinsu. Sannan ya sabar wa qananan yaransa kan yin azumi da
sallar dare, da gaggawan aikata duk abinda zai yardar da Ubangiji Mai rahama,
Arrubayyi'i 'yar Mu'awwaz (رضي
الله عنها) ta ce:
"Mun kasance
muna yin azumi, kuma muna sanya yaranmu qanana yin azumi", Bukhariy da Muslim.
Kuma cikin BIYAYYA WA IYAYE, da SADAR DA ZUMUNCI akwai
xaukakar daraja. Kuma lallai samun yardar Ubangiji tana cikin yardan iyaye guda
biyu. Fushinsa kuma yana cikin fushinsu. Kuma a cikin kwanaki masu falala xa
nagari ya kan qara kusanci zuwa ga iyayensa, da kuma qarin hidima a gare su.
Kuma duk wanda ya yi kira zuwa ga wata shiriya, to yana
da kwatankwacin ladan waxanda suka bi shi, har tashin alqiyama, Kuma Allah ya
shiryi mutum xaya ta hanyarka ya fi alheri a gare ka fiye da jajayen raquma.
ABOTA TA-GARI taimako ne, kuma samun qarfi ne, kuma duk
mai hankali ba zai tava wadatuwa da it aba "A lokacin da ya ke
ce wa abokinsa kada ka yi baqin ciki lallai Allah yana tare da mu" [Taubah:].
Kuma yana daga cikin alamomin gyaruwa KIYAYE HARSHE , da
LAZIMTAR AIKI, Kuma idan Allah ya nufi sharri da wasu mutane to sai ya sanya
su, su lazimci musu, ya kuma hana su yin aiki.
Kuma ita TUBA qofarta a buxe ta ke, kuma kyautar Allah
abar bayarwa ce, Kuma wanda aka datar da shi shine mutumin da yake kwankwasa
qofar tuba. Ya ke kuma yawaita naciyar roqon UbangijinSa.
Kuma duk wanda ya sabar wa
harshensa da neman gafara to sai ya riski lokacin ba a mayar da addu'ar mai
addu'a. kuma madalla da mutumin da ya samu ladan "istigfari" dayawa a
takardun awunsa!
A cikin aiyukan xa'a daxin mumini da farin cikinsa suke,
da kuma tsiransa da rabautarsa. Kuma bin dokoki da taqawa basa rabuwa da shi,
cikin darensa da yininsa. Kuma shi musulmi baya zama sakaka babu aiki; saboda
mutuwa tana nemansa.
Kuma duk wanda ya yi hisabi
wa kansa to ya rabauta, Wanda kuma ya rafkana to ya yi hasara.
Wanda yak e yin nazari kan
qarshen lamura ya tsira.
Kuma madalla da mutumin da
ya bar sha'awar yau, domin dacewa da alqawarin gaibu da aka yi masa; bai ganshi
ba.
A UZU BILLAHI MINASH
SHAIXANIR RAJIM:
"Kuma ku yi gaggawa
zuwa ga wata gafara daga Ubangijinku, da aljanna; faxinta girman sammai ne da
qasa, An tanada su ga masu bin dokokin Allah" [Hajj: 74].
ALLAH YAYI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALQUR'ANI MAI
GIRMA. …
HUXUBA TA BIYU
Godiya ta tabbata ga Allah
kan kyautatawarSa; Yabo kuma nasa ne
bisa ga datarwarSa da kuma ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya; Ina mai girmama sha'aninSa.
Ina kuma shaidawa lallai
annabinmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa ne.
Allah yayi daxin salati a
gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da kuma sallama mai yawa.
Ya ku musulmai…
Kusantar Allah ta hanyar barin amfani da ababe na halal
baya yin wani amfani, sai bayan an kusance shi da aikata ababen farilla, da
nisantar abubuwan haram. Kuma idan z aka yi azumi, to jinka da ganinka da
harshenka da hannayen ya kyautu su yi azumi tare da kai. Kuma kada ka sanya
ranar azuminka ya zama kamar ranar cinka.
Sai ku kiyaye –Ya ku bayin
Allah- azuminku daga ababen da za su vata shi, ko su tauye shi. Kuma ku kiyayi
aikata haramun, da jin haramun, da kallon ababen haramun, saboda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Duk wanda bai
bar zancen qarya ba, da yin aiki da shi, to Allah bashi buqatar cewa ya bar
abincinsa da abin shansa ba", Bukhariy ya ruwaito shi.
Duk mutumin da saki ganinsa
to sai hasararsa ta dawwama, nadamarsa tayi tsayi.
Ita kuma mace ta-gari
akanta akwai hijabin kunya, da kyakkyawan sutura mai suturcewa, tana yin nesa
da cakuxuwa da mazajen da aure ya halatta a tsakaninsu, da shiga kasuwanni, da
fitowa ba tare da buqata ba.
Sannan ku sani;
Lallai Allah ya umurce ku da yin salati da kuma
sallama ga Annabinsa
Sai yace, a cikin mafi kyan
abinda aka saukar:
"Lallai ne Allah da
Mala'ikunSa suna salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda su ka yi imani, ku yi
salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].
Ya Allah!
Ka yi salati da sallama da
albarka, ga annabinmu Muhammadu,
Kuma Ya Allah!
Ka yarda da khalifofi
shiryayyu, waxanda su ka yi hukunci da gaskiya, kuma da shi, su ka kasance suke
yin adalci, Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, da kuma sauran sahabbai
gabaxaya, Ka haxa da Mu tare da Su, da kyautarka da karamarka, Ya Mafi kyautar
masu kyauta.
Ya Allah!
Ka xaukaka Musulunci da
Musulmai, ka qasqantar da shirka da Mushirkai, kuma ka ruguza maqiyan addini,
Kuma ka sanya –Ya Allah!- Wannan qasar cikin aminci da natsuwa, da
wadaci da walwala, da kuma sauran qasashen Musulmai.
Ya Allah!
Ka gyara halin Musulmai a
kowani wuri.
Ya Allah!
Ka sanya qasashensu su zama
wurin aminci da zaman lafiya, Ya Mai qarfi, Ya Mabuwayi,
Ya Allah!
Ka karva mana azuminmu da
sallolinmu
"Ya UbangijinMu ka
bamu mai kyau a duniya, ka bamu mai kyau a lahira, kuma ka kare mu daga azabar
Wuta"
[Baqarah:
201].
Ya Allah!
Ka datar da shugabanmu zuwa
ga shiriyarka, ka sanya aikinsa cikin yardarka.
Kuma ka datar da xaukacin
jagororin lamuran musulmai zuwa ga aiki da littafinka, da yin hukunci da
shari'arka, Ya ma'abucin girma da karramawa.
Ya Allah!
Ka kawo aminci a
iyakokinmu, kuma ka bada nasara wa rundunoninmu, kuma qarfafe su akan gaskiya, Ya Ubangijin talikai.
Bayin Allah!!!
"Lallai ne, Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa
makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku
wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah Mai
girma da daraja zai ambace ku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari,
kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke
aikatawa.
No comments:
Post a Comment