2015/10/08

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI saw Juma a 26 zulhijjah 1436h ta Assubaitiy








HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (r)
JUMA'A, 26/ZULHIJJAH/1436H




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
Godiya ta tabbata ga Allah  wanda ya shiryar da bayinSa, ya kuma kiyaye su daga kaidi da makirci,  Ina gode masa, tsarki ya tabbata a gare shi, kuma ina yaba masa akan wadaci da talauci,    Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, halitta tasa ce, kuma umurni nasa ne.      Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonsa;  ya nuna wa al'ummarsa hanyar xaukaka da cin nasara.    Allah ya yi qarin salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, duk lokacin da dare yayi duhu, ko kuma alfijir ya keto.

Bayan haka:
Ina yin wasiyya a gare ku, da ni kaina da bin dokokin Allah,     Allah yana cewa:
"Ya ku waxanda suka yi imani ku kiyaye dokokin Allah, iyakar kiyayewa, kuma kada ku mutu face kuna musulmai" [Aali-imraan: 102].

            Allah (تبارك وتعالى) ya halicci babanmu annabi Adamu (u),     Amma sai Shexan ya tsayu wajen yin gaba da shi, da kuma kulla makirce-makirce a gare shi don neman ya vatar da shi, 
Suma kuma sauran annabawa anyi musu nau'ukan makirce-makirce da makida, kuma an quqqulla zamammakin shawari don cutar da su,    

Annabi Yusufu (u) 'yan'uwansa na jini sun qulla makirci a gare shi,  amma sai yayi haquri kan cutarwarsu, kuma Allah (تعالى) yayi magana kan qarshen lamarinsa a inda yake cewa:
"Lallai yadda lamarin yake,    Duk wanda ya bi dokoki (taqawa), kuma yayi haquri To lallai Allah baya tozarta ladan masu kyautatawa" [Yusuf: 90].

Shi kuma annabi Ibrahimu (u) an tara itatuwa, an kunna wuta; don a qona shi, sannan aka jefa shi a cikinta,    Amma sai ta zama sanyi da aminci;   makircinsu kuma ya lalace,    kamar yadda Allah (تعالى) yake cewa:
"Kuma sun yi nufin makidar halaka shi,  Sai muka sanya su suka zamto sune maqasqanta" [Saafaat: 98].

Annabi Isah (u): Mutanensa sun yi masa makida, sun kuma quqqula makircin kashe shi, da tsire shi,    Amma sai Allah (تعالى) ya tseratar da shi daga sharrinsu.

Sun yi makida da qulle-qulle wa annabi Musa (u) har Allah (تعالى) yake cewa:
"Lallai abinda suka aikata kaidi ne na mai sihiri, Kuma mai sihiri baya rabauta a duk inda ya zo" [Xaha: 69].

Kuma rundunar da Abraha ya zo da ita, sun yi makidar rushe xakin ka'abah,   Sai Allah ya lalata makircinsu, "Ashe bai sanya kaidinsu cikin vata ba?   Sai ya turo musu da tsuntsaye jama'a-jama'a  *   Suna jifarsu da wasu duwatsu na yunvun wuta    *    Sai ya sanya su kamar karmamin wanda aka cinye" [Fiil: 2-5].

Maqiya sun gama tattara lamarinsu,     suka yi makirci wa Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم),     Amma sai makircinsu ya tafi zuwa ga: GUSHEWA,    Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma suna yin makirci,    Allah shima yana yin makirci,     Allah kuma shine mafi alherin masu makirci" [Anfaal: 30].

KUMA YANA DAGA CIKIN SIFOFIN MA'ABOTA MAKIRCI:
Qin cika alkawari da ha'intarsu:
A lokacin yaqin da ake kira: BI'IRU MA'UNA, An kashe mutane saba'in daga cikin maxaukakan sahabbai (ta hanyar cin amana).    Allah (تعالى) yana cewa:
"Ya ku waxanda suka yi imani kada ku ha'inci Allah, da Manzo,    Sai ku ha'inci amanoninku alhalin kuna sane" [Anfaal:  27].
Kuma Manzon Allah (صلىى الله عليه وسلم) ya kasance yana neman Allah ya tsare shi daga yin ha'inci;      Sai yace:
"Kuma ina neman tsarinka daga yin ha'inci;    kasancewarsa mummunan abin voyewa".

            Kuma lallai munafiqai sun kasance Sune tushen mafi girman makircin da Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya sha fama da shi,     wannan kuma saboda MATSAYARSU ta kan canzu tayi launi-launi, HALAYENSU kuma su kan rikixe su riqa canzawa,    Allah (تعالى) yana faxa dangane da munafiqai:
"Kuma idan suka haxu da waxanda suka yi Imani sai su ce: Mun yi imani,    Idan kuma suka kevanta zuwa ga shexanunsu sai su ce: Lallai mu muna tare da ku,    abin sani kawai, mu muna yin izgilanci ne" [Baqarah: 14].     Ya sake faxa akansu:
"Ashe basu sani ba ne, lallai Allah yana sanin abinda suke asirtawa, da abinda suke bayyanarwa" [Baqarah: 77].
Ma'ana: Ashe ba su sani ba ne, cewa lallai Allah yana sanin dukkan abinda suke voyewa na makirci da kafirci,      da kuma abinda suke bayyanarwa na imani, da soyayya.


KUMA YANA DAGA CIKIN SIFOFIN MA'ABOTA MAKIRCI:
Bayyana a lokacin da aka shiga jarrabawa da ibtila'i, ko aukuwar wassu lamura masu girma,   da yin farin ciki idan musiba ta aukawa musulmai,   Idan kuma nasara ta samu musulmai ko yin rinjaye, da yalwar arziqi to sai su ji qunci da baqin ciki da vacin rai,      Idan kuma musiba ce ta sauka wa musulmai, ko kuma bala'i ya auka a gare su to sai maqiya su yi ta annashawar farin ciki, da nuna girman kai,    Allah (تعالى) yana cewa:
"Idan kyakkyawan abu ya shafe ku sai ya baqanta musu,     Idan kuma mummuna ne ya shafe ku sai su yi farin ciki da shi" [Aali-imraan: 120].

KUMA YANA DAGA SIFOFIN MAKIRAI:
Girmama musibar da ta auku, da farautar wuraren da aka yi tuntuve, ko aka kuskure, tare da qoqarin yaxa su,     Da kuma qoqarin nuna jahiltar nasarorin da aka cimma, ko  kyawawan aiyukan da aka gabatar,      Wannan kuma shine abin kai-komon masu qulli a zuci; mahassada.

v      ************************

YANA KUMA DAGA CIKIN KAIDI KO MAKIRCI:
Nufan yara samari don vatar da su, da kalmar baka ce (wato: magana), ko ta hanyar hotuna, ko da wani tunani,   ta kafafen yaxa labaru, da hanyoyin sadarwa na zamani,    Kuma aikata haka yafi girman hatsari fiye da turo rundunoni masu yawa, tare da makaman kisan wulaqanci,     vatar da samari ta hanyar yaxa aqidun zafin kai da qetare iyaka,    saboda cimma rikitattun manufofi,    da neman mallake kwakwalen samari,  da shamakance tsakaninsu da tsakanin malumansu,     domin farautarsu da yin tasiri akansu daga baya yayi sauqi,   daga WASSU MUTANEN DA AKA JAHILTA; waxanda ba a sansu a fagen ilimi, ko aiki ba.

                YANA DAGA CIKIN AIYUKAN MASU QULLI A ZUCI:
 Shusshuka qungiyoyi masu aikata kashe-kashe, a garurrukan musulmai, domin su zama makamashin (ashana, fetur) da zai fara qona samarin,   ya kuma rushe kyakkyawan abinda suka fiskanta na rayuwarsu, da garurrukansu.

                    YANA KUMA DAGA CIKIN HANYOYIN MAKIRCI:
Suranta wannan addinin (na musulunci) da/ koma-baya, da riya cewa shine addinin rashin tsari, da wauta, ko dabbanci (da kuma riya cewa ba a iya zaman lafiya da musulmi),    ta hanyar kawo hotunan zubar da jinane,    ko kuma ta hanyar zartar da nau'ukan kisan walaqanci Daga waxanda suka cusa kayukansu cikin sahun musulmai,     ko waxanda suka sanya rigar addini.

                YANA KUMA DAGA CIKIN MISALAN MAKIRCI:
Qirqiran qarerayi, da yaxa jita-jita masu munanan manufofi,
Kuma lallai ayoyi bayyanannu sun zo don su yi gargaxi kan tafiya da masu qawata magana don ta yi saurin yaxuwa,    Sun kuma faxakar kan faxan daidai,       da kuma hani kan cilla magana a duk yadda ta zo, ba tare da yin tunani, ko bincikar ta ba,      (Allah yana cewa):
"Ya ku waxanda suka yi imani ku kiyaye dokokin Allah (taqawa),  kuma ku faxi magana ta daidai" [Ahzaab: 70].
A cikin wannan ayar, lallai an faxakar kan/    kyautata zance, da sanin manufarsa da inda ya dosa,    gabanin bin munafiqai akansa, ko kuma bin masu yaxa qarerayi.     
Haka zalika ayar ta faxakar kan faxin manargacin zance, wanda zai yi jagoranci zuwa ga aiki managarci.

            YANA DAGA CIKIN MAKIRCI:
Watsa shakku a cikin musulmai kan jagorori da shugabanninsu,   ta hanyar qaryata tabbatattun abubuwa,  ko kuma qirqiran na qarerayi.

                YANA DAGA CIKIN MISALAN SHIRYA MAKIRCE-MAKIRCE:
Fitar da fatawowin shubuha da fitina,      Wannan kuma zai bayu zuwa ga yaxuwar varna, da kuma sanya mata riga irin ta gaskiya.
Kuma yana daga cikin abubuwan mamaki:    Yadda baqin fatawowi suka yaxu a wannan zamanin,     waxanda aka jirkita qarya da gaskiya a cikinsu ga marasa ilimi,  Sai masu gaggawan yaxa baqin maganganu suka yi ta rige-rigen yaxa su,   Sai kuma suka haifar da munanan tasiri ga al'umma,  da cutarwar da ta kai maqura wajen muni.

                KUMA YANA DAGA CIKIN HANYOYIN SHIRYA MAKIRCE-MAKIRCE:
Hana mutane bin gaskiya, ta hanyar aikin tayar da sha'awowi ko alaqoqi tsakanin maza da mata.   Da kuma dulmuyar da samari cikin kayan sanya maye.

                KUMA YANA DAGA CIKIN AIYUKAN MAKIRAI:
Tayar da fitintinu da rashin kwanciyar hankali,    da raba kan musulmai,   da kuma ruro wutar tsanani da bala'oi;     wannan kuma domin lamarin gina al'umma da bunqasata ya dakata a qasashen musulmai,      kuma domin himmomi su tafi zuwa ga magance matsalolin da waxancan fitintinun suka jawo,    da yin aiki domin qoqarin kashe wutar da fitintinun suka kunno.

                KUMA YANA DAGA CIKIN MAKIRCIN MAKIRAI:
Shirya qarerayi;     domin yaxa ruhin jin rauni ko samar da karayar zuci, da jiyar da musulmai cewa an ci nasara akansu,    Allah (تعالى) yana cewa:
"Waxanda mutane suka ce musu: Lallai mutane sun haxu akanku;    ku ji tsoronsu,    Sai hakan ya qara imani a gare su,   har Suka ce: Allah ya isar mana, kuma madalla da Shi; abin dogaro" [Aali-imraan: 173].      
Kuma abinda ya zo cikin wannan ayar shine babbar kariyar da muminai suke fakewa izuwa gare ta; a lokutan da musibu da bala'oi suke yin dabaibayi a gare su.      Kuma duk yadda bala'oi suka yi tsanani to lallai basa qara komai ga muminai sai TABBATUWA, DA IMANI, DA MIQA WUYA.
Kuma lallai tarihin wannan al'ummar mai girma: Ya kan sanyaya rai, ya kuma sanya mutum ya ji cewa lallai nasarar tana nan tana tafe, saboda kasancewarsa tarihi ne na girma,  da kuma amintuwa cewa lallai Allah zai xauki fansa kan duk wanda yayi zalunci ko yayi xagawa.     Allah (تعالى) yana cewa:
"Lallai kamun Ubangijinka mai tsanani ne   *   Kuma lallai shine yake farar halitta sai kuma ya dawo da ita" [Buruuj: 12-13].
 (a kan haka) MUNA KYAUTATA ZATONMU GA UBANGIJINMU, KUMA MUN AMINTA DA ADALCINSA;   KASANCEWARSA MAI TAIMAKON WALIYYANSA, MAI KUMA YIN RINJAYE AKAN MAQIYANSA, Allah (تعالى) yana cewa:
"Yayin da Muminai suka ga rundunoni sai suka ce: Wannan shine abinda Allah da ManzonSa suka yi mana alkawari,   kuma Allah da Manzonsa sun yi gaskiya,      Kuma ganinsu bai qara musu komai ba face imani da miqa wuya" [Ahzaab: 22].

v      ************************

            Lallai yana daga cikin KIYAYEWAR da ALLAH yake yi wa GASKIYA da MA'ABOTANTA:   Yadda dukkan nau'oin makirci da kaidi suke rugujewa a jikin qarfin tabbatuwar wannan al'ummar, matuqar tana riqe da gadon annabta,        Koda kuwa a wassu zamanin al'ummar ta kan yi rauni.  Saidai kuma kyakkyawar makoma da qarshen lamarin ya kan zama na wannan al'ummar ne,    Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma ka ce: Gaskiya ta zo, Varna kuma ta gushe, lallai varna ta kasance mai gushewa ce" [Isra'i: 81].  Da kuma faxinsa:
"Kuma haqqi ne akanmu: Taimakon muminai" [Rum: 47].

            Kuma lallai AL'UMMAR MUSULMAI wata cutuwa zata iya samunsu sakamakon makircin makirai, ko kaidin masu kaidi,    Wannan kuma ya kan kasance ne saboda Allah ta'alah ya jarrabi muminai,    ya kuma buxe ko yaye lamarin munafiqai,     sa'annan ya jarraba tabbatuwar musulmai.    Saidai kuma duk yadda lamarin makirci da kaidi ya kai, to yana taqaituwa cikin QADDARAR Allah,   kuma cikin da'ira ko kewayen NUFINSA,       Kuma lallai mummunan makirci baya komawa sai kan wanda ya aikata shi,    kamar yadda Allah yake cewa:
"Kuma lallai mummunan makirci baya komawa sai ga ma'abotansa" [Faxir: 43].

            Kuma lallai HAXIN KAN MUSULMAI, DA HAXUWAR ZUKATANSU shine hanyar cin nasara da xaukaka, kuma ginshiqin da ake gina qarfinsu,    Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma kada ku yi jayayya sai ku raunana sai qarfinku ya tafi" [Anfaal: 46].

            Kuma al'ummar musulmai dole su haxa tsakanin riqo da sabbuban cin nasara da kuma yin tawakkali ko dogaro ga Allah (سبحانه),    Kuma duk wanda ya jingina lamarinsa zuwa ga Allah, Sai Allah ta'alah ya isar masa, ya kiyaye shi, kuma ya bashi kariya,    Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma duk wanda ya dogara ga Allah to ya isar masa, Lallai Allah ya iyar ga lamarinSa, kuma lallai haqiqa Allah ya sanya qaddara ga kowani abu" [Xalaq: 3].

            "Kada kayi baqin ciki lallai Allah yana tare da mu" [Taubah: 40],    Wannan kalma ce da Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya faxe ta, alhalin yana cikin kogo tare da abokinsa (Abubakar), a lokacin da kafirai suka kewaye su,    Sai Allah ya tseratar da shi, ya kuma kiyaye shi, ya bashi nasara.      Don haka (لا تحزنْ إنّ الله معنا) tana haifar da samun natsuwa da kwanciyar hankali,    tare da xebe cire tsammanin samun nasara daga zukata.

                KUMA LALLAI ANA TOTTOSHE QOFOFIN MAKIRCI: Da tabbatuwa akan gaskiya,   da yin riqo da alqur'ani da Sunnah,    tare da komawa zuwa ga maluma a lokaci ko wuraren fitina,      da mayar da lamari zuwa ga shugabanni a cikin hukunce-hukunce ko lamarin amincin al'ummah.

            Siffantuwa da TAQAWAR ALLAH, da YIN HAQURI suma suna raunana tsananin makirci,     kuma su kan tunkuxe cuta,    Allah (تعالى) yana cewa:
"Wancan kuma ya kasance, saboda lallai Allah mai raunana kaidin kafirai ne" [Anfaal: 18].

            Kuma lallai amincin wannan qasar; wato qasar masallatai masu alfarma guda biyu;      Masarautar larabawa ta Saudia,   Shine ginshiqin samun amincin dukkan al'ummah,   saboda kasancewarta zuciyar wannan al'ummar wanda yake bugawa,     Kuma lallai munana wa wannan qasar munanawa ne ga amincin al'ummar musulmai (bakixaya).     Kuma jikin wannan al'ummar ba zai gushe ba cikin alkhairi matuqar dai zuciyar tana bugawa,     saboda alkhairin wannan qasa ya game,  aiyukanta na kirki kuma basa qarewa.       Kuma tabbatuwanta cikin aminci, da bata kariya daga makircin makirai, da kuma kaidin masu qulli a cikin zukata = ABU NE da shari'a ta ke neman samar da shi, kuma wajibi ne na addini akan kowani musulmi.

Kuma 'ya'yan wannan qasar; masu hankali sun san da haka,   kuma zasu ci-gaba da bada gudumawa da wayewarsu wajen rurrusa tsare-tsaren masu jiran su ga matsala ta auku.

            Kuma duk wanda ya yi qoqarin cutar da amincin wannan qasar,   to lallai yana yin hidima ne ga maqiyan wannan addinin na musulunci,      Kuma wannan qasar zata ci-gaba da zama a kiyaye; da kiyayewar Allah,    tana tsaye, cikin bunqasa,      Allah (تعالى) yana cewa:
"Idan kuka yi haquri, kuka yi taqawa, Kaidinsu ba zai cutar da ku da komai ba" [Aali-imraan: 120].

            Allah yayi mini albarka da ku, a cikin alqur'ani mai karamci, ya kuma amfanar da mu da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Ina faxar maganata wannan, ina kuma neman gafarar Allah, wa NI da KU, da kuma sauran musulmai, ku nemi gafararSa,    lallai shi mai gafara ne mai rahama.
HUXUBA TA BIYU
            Yabo na Allah ne; muna gode masa, kuma muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kayukanmu da munanan aiyukanmu,    Duk wanda Allah ya shiryar to babu mai vatar da shi,   Wanda kuma y avatar babu mai shiryar da shi,    Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokin tarayya,     Kuma ina shaidawa lallai Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne,  
            Ya Allah kayi salati wa Annabi Muhammadu da iyalan annabi Muhammadu kamar yadda kayi salati wa annabi Ibrahima da iyalan annabi Ibrahim, lallai kai abun godiya ne, mai girma.
            Ya Allah ka yarda da khalifofi shiryayyu;    Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu,    da Iyalan annabi da sahabbansa masu karamci, ka haxa da mu da baiwarka, da rahamarka, ya mai mafificin kyauta.
            Ya Allah ka xaukaka musulunci da musulmai….


       Huxubar ta qare,,,          ,,,          ,,,

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...