HADISAI HAMSIN
KAN QA'IDODIN MUSULUNCI
42
للنووي، و8 تتمة لابن رجب الحنبلي
NA
IMAM ANNAWAWIY DA IBNU-RAJAB
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
الحديث الأول:
عن أمير المؤمنين أبي حفص عُمَرَ بْنَ الْخَطَّابِ رضي الله تعالى عنه قال:
سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ:
«إِنَّمَا الأَعْمَالُ بِالنِّيَّاتِ، وَإِنَّمَا لكل امْرِئٍ مَا نَوَى، فَمَنْ
كَانَتْ هِجْرَتُهُ إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ فَهِجْرَتُهُ إِلَى اللَّهِ
وَرَسُولِهِ، وَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُه لدُنْيَا يُصِيبُهَا، أَوِ امْرَأَةٍ
يَنْكِحُهَا فَهِجْرَتُهُ إِلَى مَا هَاجَرَ إِلَيْهِ».
رواه إماما المحدثين: أبو عبد الله محمد ابن إسماعيل بن إبراهيم بن المغيرة
بن بردزبه البخاريّ، وأبو الحسين مسلم ابن الحجاج بن مسلم القشيري النيسابوري، في
صحيحيهما اللذين هما أصح الكتب المصنفة.
HADISI NA FARKO:
An karvo
daga sarkin muminai, Baban Hafs, Umar xan Alkhaxxabi (r.a) yace: Na ji Manzon
Allah (s.a.w) yana cewa: "Dukkan aiyuka suna tare da niyya,
kuma lallai kowane mutum yana samun sakamakon abinda yayi niyya; Wanda
hijirarsa ta kasance saboda Allah ne da Manzonsa to sakamakon hijirarsa tana ga
Allah da Manzonsa. Wanda kuma hijirarsa ta kasance saboda wata duniya ce da zai
same ta, ko kuma wata matar da zai aure ta, to sakamakon hijirarsa yana ga
abinda yayi hijira dominsa.
Shugabannin
maluman da suka rubuta littatafan hadisai ne suka ruwaito shi; Wato: Baban
Abdullahi Muhammadu xan Isma'ila xan Ibrahima xan Almugiyrah xan Bardizbah,
(AlBukhariyy), Da kuma AbulHusaini Muslimu xan Alhajjaju xan Muslimu, Alqushairiyyu
Annaisaburiyyu. A cikin ingantattun littatafansu [Sahihul Bukhariyy, lamba: 1,
da Sahihu Muslim, lamba: 1907], waxanda kuma sune mafi ingancin littatafan da
aka rubuta.
الحديث الثاني:
عن عمر رضي الله تعالى عنه أيضًا قال: بَيْنَمَا نَحْنُ عِنْدَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ذَاتَ يَوْمٍ، إِذْ طَلَعَ عَلَيْنَا رَجُلٌ شَدِيدُ بَيَاضِ
الثِّيَابِ، شَدِيدُ سَوَادِ الشَّعَرِ، لَا يُرَى عَلَيْهِ أَثَرُ السَّفَرِ،
وَلَا يَعْرِفُهُ مِنَّا أَحَدٌ، حَتَّى جَلَسَ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَأَسْنَدَ رُكْبَتَيْهِ إِلَى رُكْبَتَيْهِ، وَوَضَعَ
كَفَّيْهِ عَلَى فَخِذَيْهِ، وَقَالَ: يَا مُحَمَّدُ أَخْبِرْنِي عَنِ
الْإِسْلَامِ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «الْإِسْلَامُ
أَنْ تَشْهَدَ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَتُقِيمَ الصَّلَاةَ، وَتُؤْتِيَ الزَّكَاةَ،
وَتَصُومَ رَمَضَانَ، وَتَحُجَّ الْبَيْتَ إِنِ اسْتَطَعْتَ إِلَيْهِ سَبِيلًا»،
قَالَ: صَدَقْتَ، قَالَ: فَعَجِبْنَا لَهُ يَسْأَلُهُ، وَيُصَدِّقُهُ، قَالَ:
فَأَخْبِرْنِي عَنِ الْإِيمَانِ، قَالَ: «أَنْ تُؤْمِنَ بِاللهِ،
وَمَلَائِكَتِهِ، وَكُتُبِهِ، وَرُسُلِهِ، وَالْيَوْمِ الْآخِرِ، وَتُؤْمِنَ
بِالْقَدَرِ خَيْرِهِ وَشَرِّهِ»، قَالَ: صَدَقْتَ، قَالَ: فَأَخْبِرْنِي عَنِ
الْإِحْسَانِ، قَالَ: «أَنْ تَعْبُدَ اللهَ كَأَنَّكَ تَرَاهُ، فَإِنْ لَمْ
تَكُنْ تَرَاهُ فَإِنَّهُ يَرَاكَ»، قَالَ: فَأَخْبِرْنِي عَنِ السَّاعَةِ،
قَالَ: «مَا الْمَسْئُولُ عَنْهَا بِأَعْلَمَ مِنَ السَّائِلِ» قَالَ:
فَأَخْبِرْنِي عَنْ أَمَارَتِهَا، قَالَ: «أَنْ تَلِدَ الْأَمَةُ رَبَّتَهَا،
وَأَنْ تَرَى الْحُفَاةَ الْعُرَاةَ الْعَالَةَ رِعَاءَ الشَّاءِ يَتَطَاوَلُونَ
فِي الْبُنْيَانِ»، قَالَ: ثُمَّ انْطَلَقَ فَلَبِثْتُ مَلِيًّا، ثُمَّ قَالَ
لِي: «يَا عُمَرُ أَتَدْرِي مَنِ السَّائِلُ؟» قُلْتُ: اللهُ وَرَسُولُهُ
أَعْلَمُ، قَالَ: «فَإِنَّهُ جِبْرِيلُ أَتَاكُمْ يُعَلِّمُكُمْ دِينَكُمْ».
رواه مسلم.
HADISI NA BIYU:
An ruwaito daga Umar (r.a) yace: Wata rana
muna wurin Manzon Allah (s.a.w), Sai wani mutum ya vullo mana, mai tsananin
farin tufafi, mai tsananin baqin gashi, babu wata alamar tafiya a tattare da
shi, har ya zauna kusa da Annabi (s.a.w); Sai ya jingina guiwoyinsa zuwa
guiwoyinsa, ya kuma xora tafukansa akan cinyoyinsa, yace: Ya Muhammadu, bani
labari akanMusulunci? Yace: Ka shaida
babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma annabi Muhammadu manzon Allah ne,
kuma ka tsayar da salla, kuma ka bada zakka, kuma ka yi azumin watan ramadana,
kuma ka yi hajjin xaki; idan ka samu hanyar zuwa gare shi. Sai yace: ka yi
gaskiya, Sai muka yi mamakinsa; yana tambayarsa kuma yana gaskata shi.
Sai yace: ka bani labari akan imani? Yace: Ka
yi Imani da Allah, da Mala'ikunsa, da littatafansa, da Manzanninsa, kuma ka yi
Imani da qaddara na alkhairinsa dana sharrinsa.
Yace: To ka bani labari akan
"ihsani"? Sai yace: Shine ka bauta wa Allah kamar kana ganinsa,
idan kai baka ganinsa to shi yana ganinka.
Yace: To ka bani labari akan qiyamah? Sai
yace: Wanda ake tambayarsa akanta bai fi wanda yayi tambayar sanin lokacinta
ba. Sai yace: To ka bani labara kan
alamominta? Sai yace: Baiwa ta haifi uwar gijiyarta, kuma zaku ga marasa
takalma, tsiraru, masu kiyon dabbobi suna yin gini masu tsayi.
Yace: Sannan sai ya tafi, sai na zauna na wani
lokaci, Sa'annan sai yace: Ya kai
Umar shin ka san wanene mai yin wannan tambayar? Sai yace: Allah ne da manzonsa
suka sani. Yace: Lallai shi mala'ika Jibrilu ne, y azo muku, domin ya
karantar da ku addininku". Muslim yaruwaito shi [lamba: 8]
الحديث الثالث:
عَنِ أبي عبد الرحمن عبد الله بْنِ عُمَرَ بن الخطاب رضي الله عنهما،
قَالَ: سمعتُ رَسُول اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يقول: «بُنِيَ
الْإِسْلَامُ عَلَى خَمْسٍ، شَهَادَةِ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَأَنَّ
مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، وَإِقَامِ الصَّلَاةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ،
وَصَوْمِ شَهْرِ رَمَضَانَ، وَحَجَّ الْبَيْتِ». رواه
البخاري ومسلم.
HADISI NA UKU:
An ruwaito daga Abu-abdirrahman, Abdullahi xan
Umar xan Alkhaxxabi (r.a) yace: Naji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "An
gina musulunci akan abubuwa guda biyar; Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya
sai Allah, kuma Muhammadu manzon Allah, da tsayar da salla, da bada zakka, da
yin hajjin wannan xakin, da azumin watan ramadana".
Bukhariyy [8] da Muslim [16] suka ruwaito shi.
الحديث الرابع:
عن أبي عبد الرحمن عَبْدِ اللهِ بن مسعود رضي الله عنه، قَالَ:
حَدَّثَنَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ -وَهُوَ الصَّادِقُ
الْمَصْدُوقُ-: " إِنَّ أَحَدَكُمْ يُجْمَعُ خَلْقُهُ فِي بَطْنِ أُمِّهِ
أَرْبَعِينَ يَوْمًا نُطْفَةً، ثُمَّ يَكُونُ فِي ذَلِكَ عَلَقَةً مِثْلَ ذَلِكَ،
ثُمَّ يَكُونُ فِي ذَلِكَ مُضْغَةً مِثْلَ ذَلِكَ، ثُمَّ يُرْسَلُ الْمَلَكُ
فَيَنْفُخُ فِيهِ الرُّوحَ، وَيُؤْمَرُ بِأَرْبَعِ كَلِمَاتٍ: بِكَتْبِ رِزْقِهِ،
وَأَجَلِهِ، وَعَمَلِهِ، وَشَقِيٌّ أَوْ سَعِيدٌ، فَوَالَّذِي لَا إِلَهَ غَيْرُهُ
إِنَّ أَحَدَكُمْ لَيَعْمَلُ بِعَمَلِ أَهْلِ الْجَنَّةِ حَتَّى مَا يَكُونُ
بَيْنَهُ وَبَيْنَهَا إِلَّا ذِرَاعٌ، فَيَسْبِقُ عَلَيْهِ الْكِتَابُ، فَيَعْمَلُ
بِعَمَلِ أَهْلِ النَّارِ، فَيَدْخُلُهَا، وَإِنَّ أَحَدَكُمْ لَيَعْمَلُ بِعَمَلِ
أَهْلِ النَّارِ، حَتَّى مَا يَكُونُ بَيْنَهُ وَبَيْنَهَا إِلَّا ذِرَاعٌ، فَيَسْبِقُ
عَلَيْهِ الْكِتَابُ، فَيَعْمَلُ بِعَمَلِ أَهْلِ الْجَنَّةِ، فَيَدْخُلُهَا
"
HADISI NA HUXU:
An ruwaito daga Abiy-abdurrahman, Abdullahi
xan Mas'ud (r.a), yace: Manzon Allah (s.a.w) ya bamu labari, kuma shine mai
gaskiya abun gaskatawa, cewa: "Lallai xayanku ana tara halittarsa a
cikin mahaifiyarsa kwanaki arba'in yana maniyyi, Sa'annan sai ya kasance jini
gwargwadon haka, sa'annan sai ya kasance tsoka gwargwadon haka, Sa'annan sai a
turo Mala'ika zuwa gare shi; sai ya busa masa rai, sai a umurce shi da kalmomi
guda huxu; rubuta arziqinsa, da ajalinsa, da aikinsa, kuma shaqiyyi ne ko mai
rabo ne, Na rantse da wanda babu wani abin bautawa idan ba shi ba; Lallai
xayanku zai yi ta yin aiki irin na 'yan aljanna, har sai ya zama babu wani abu
a tsakaninsa da tsakaninta sai zira'i, sai littafi ya rigaye shi; sai yayi aiki
irin na 'yan wuta; sai ya shige ta. Kuma lallai xayanku zai yi ta yin aiki irin
na 'yan wuta, har sai ya zama babu wani abu a tsakaninsa da tsakaninta sai
zira'i, sai littafi ya rigaye shi; sai kuma yayi aiki irin na 'yan aljanna; sai
ya shige ta".
Bukhariyy [3208] da Muslim [2643] suka ruwaito
shi.
الحديث الخامس:
عن أم المؤمنين أم عبد الله عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا، قَالَتْ:
قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ أَحْدَثَ فِي
أَمْرِنَا هَذَا مَا لَيْسَ فِيهِ، فَهُوَ رَدٌّ»، رواه
البخاري ومسلم. وفي رواية لمسلم: «مَنْ
عَمِلَ عَمَلًا لَيْسَ عَلَيْهِ أَمْرُنَا فَهُوَ رَدٌّ».
HADISI NA BIYAR:
An
ruwaito daga Ummul Mu’uminina Ummu Abdullahi Aishatu (R.A) tace manzon Allah
(SAW) yace: “Wanda ya qirqiro wani abu cikin lamarinmu wannan abin da babu
shi a cikinsa to a mayar masa” Bukhariyy [2695] Muslim [1718]
suka ruwaito shi. A wata riwayar Muslim: “Wanda ya aikata wani
aikin da babu umarninmu a kai, to an mayar masa”.
الحديث السادس:
عن أبي عبد الله
النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ رضي الله عنهما قال: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ: «إِنَّ الْحَلَالَ بَيِّنٌ، وَإِنَّ
الْحَرَامَ بَيِّنٌ، وَبَيْنَهُمَا مُشْتَبِهَاتٌ لَا يَعْلَمُهُنَّ كَثِيرٌ مِنَ
النَّاسِ، فَمَنِ اتَّقَى الشُّبُهَاتِ اسْتَبْرَأَ لِدِينِهِ، وَعِرْضِهِ، وَمَنْ
وَقَعَ فِي الشُّبُهَاتِ وَقَعَ فِي الْحَرَامِ، كَالرَّاعِي يَرْعَى حَوْلَ
الْحِمَى، يُوشِكُ أَنْ يَرْتَعَ فِيهِ، أَلَا وَإِنَّ لِكُلِّ مَلِكٍ حِمًى،
أَلَا وَإِنَّ حِمَى اللهِ مَحَارِمُهُ، أَلَا وَإِنَّ فِي الْجَسَدِ مُضْغَةً،
إِذَا صَلَحَتْ، صَلَحَ الْجَسَدُ كُلُّهُ، وَإِذَا فَسَدَتْ، فَسَدَ الْجَسَدُ
كُلُّهُ، أَلَا وَهِيَ الْقَلْبُ» رواه البخاري ومسلم.
HADISI NA
SHIDA:
An
ruwaito daga abu Abdullahi; Nu’umanu xan Bashir, (R.A) yace: Na ji Manzon Allah
(S.A.W) yana cewa, “Lallai halal a bayyane yake, kuma lallai haram a bayyane
yake, kuma a tsakaninsu akwai al’amura masu rikitarwa, waxanda dayawa daga
cikin mutane ba su san su ba. Duk wanda ya nisanci abubuwa masu rikitarwa,
hakika ya nemi kubutar da addininsa da mutuncinsa. Wanda ya auka cikin abubuwa
masu rikitarwa, to ya auka cikin haram. Kamar makiyayi ne da yake kiwo a gefen
shinge, yayi kusa ya shiga (kiwo) a cikinsa. Ku saurara! Kowane sarki yana da
iyaka. Ku saurara! iyakar Ubangiji itace abubuwan da ya haramta. Ku saurara!
Lallai a cikin jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru, dukkan jiki ya gyaru, idan
ta lalace, dukkan jiki ya lalace. Ku saurara! wannan ita ce zuciya”,
Bukhariy [59] da Muslim [].
الحديث السابع:
عَنْ أبي رقية تَمِيمٍ
بن أوس الدَّارِيِّ رضي الله تعالى عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ، قَالَ: «الدِّينُ النَّصِيحَةُ» قُلْنَا: لِمَنْ؟ قَالَ: «لِلَّهِ
وَلِكِتَابِهِ وَلِرَسُولِهِ وَلِأَئِمَّةِ الْمُسْلِمِينَ وَعَامَّتِهِمْ»،
رواه مسلم.
HADISI NA
BAKWAI:
An
ruwaito daga Abu Rukayya; Tamim xan Aus Ad-dari (R.A) yace: Annabi (S.A.W)
yace: “Addini nasiha ne ! sai muka ce, ga wa ? Sai yace, “Ga
Allah, da littaffansa da Manzonsa, da shugabannin musulmin da dukkan mutane”, Muslim
ne ruwaito shi [55].
الحديث الثامن:
عَنْ ابْنِ عُمَرَ رضي
الله تعالى عنهما أنّ رَسُول اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «أُمِرْتُ
أَنْ أُقَاتِلَ النَّاسَ حَتَّى يَشْهَدُوا أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَأَنَّ
مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ، وَيُقِيمُوا الصَّلَاةَ، وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ،
فَإِذَا فَعَلُوا، عَصَمُوا مِنِّي دِمَاءَهُمْ، وَأَمْوَالَهُمْ إِلَّا
بِحَقِّهَا، وَحِسَابُهُمْ عَلَى اللهِ تعالى»، رواه البخاري ومسلم.
HADISI NA
TAKWAS:
An
ruwaito daga Abdullahi xan Umar (R.A) yace:
lallai Annabi (S.A.W) yace: “An umarce ni da in yaqi mutane,
har sai sun shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma lallai annabi
Muhammadu manzon Allah ne, su tsayar da sallah, kuma su bayar da zakka, idan
sun aika haka, to sun kare jininsu da dukiyoyinsu daga gare ni, sai haqqin
musulunci, hisabinsu yana wajen Allah maxaukakin sarki”.
Bukhariy [25] da Muslim [22] suka ruwaito shi.
الحديث التاسع:
عَنِ أبي أَبي
هُرَيْرَةَ عَبْد الرَّحْمَنِ بن صخر رضي الله عنهم قال: سَمِعت رَسُولَ اللهِ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «مَا نَهَيْتُكُمْ عَنْهُ،
فَاجْتَنِبُوهُ وَمَا أَمَرْتُكُمْ بِهِ فَأْتوا مِنْهُ مَا اسْتَطَعْتُمْ،
فَإِنَّمَا أَهْلَكَ الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ كَثْرَةُ مَسَائِلِهِمْ،
وَاخْتِلَافُهُمْ عَلَى أَنْبِيَائِهِمْ»، رواه البخاري ومسلم.
HADISI NA
TARA:
An
ruwaito daga Abu Huraira; Abdur-rahman xan Sak-rin (R, A) yace, naji Manzon
Allah (S.A.W) yana cewa: “Duk abinda na hane ku to ku nisance shi,
abinda na umarce ku, ku zo da shi gwargwadon iko. Kuma lallai abinda ya halakar
da wadanada suka zo kafin ku shine yawan tambayoyinsu, da savawarsu ga
Annabawansu” (Bukhariy 7288) da Muslim 1337).
الحديث العاشر:
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ
رضي الله عنه، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
"إِنَّ اللهَ تعالى طَيِّبٌ لَا يَقْبَلُ إِلَّا طَيِّبًا، وَإِنَّ اللهَ
أَمَرَ الْمُؤْمِنِينَ بِمَا أَمَرَ بِهِ الْمُرْسَلِينَ، فَقَالَ: {يَا أَيُّهَا
الرُّسُلُ كُلُوا مِنَ الطَّيِّبَاتِ وَاعْمَلُوا صَالِحًا، إِنِّي بِمَا
تَعْمَلُونَ عَلِيمٌ} [المؤمنون: 51] وَقَالَ تعالى: {يَا أَيُّهَا
الَّذِينَ آمَنُوا كُلُوا مِنْ طَيِّبَاتِ مَا رَزَقْنَاكُمْ} [البقرة: 172]
ثُمَّ ذَكَرَ الرَّجُلَ يُطِيلُ السَّفَرَ أَشْعَثَ أَغْبَرَ، يَمُدُّ يَدَيْهِ
إِلَى السَّمَاءِ، يَا رَبِّ، يَا رَبِّ، وَمَطْعَمُهُ حَرَامٌ، وَمَشْرَبُهُ حَرَامٌ،
وَمَلْبَسُهُ حَرَامٌ، وَغُذِيَ بِالْحَرَامِ، فَأَنَّى يُسْتَجَابُ له؟ رواه مسلم.
HADISI NA
GOMA:
An
ruwaito daga Abu hurairata (R.A) yace, manzon Allah (S.A.W) yace: “Lallai
Allah ta'alah mai tsarki ne kuma baya karvar abu sai mai tsarki, Allah ya umarci
muminai da irin abinda ya umarci manzanni da shi; yace: Ya ku manzanni ku ci daga daxaxan abubuwa, kuma ku yi aiki
nagari. Sannan (Allah) ya faxa: Ya ku waxanda suka yi imani ku ci
daga daxaxan abububawan da muka azurta ku. Sannan
Annabi (S.A.W) ya ambaci wani mutum; wanda yake tsawaita tafiya, gashin kansa
yayi gizo, yayi kura, yana mika hannayensa zuwa sama, yana cewa: Ya rabbi ya
rabbi!! Saidai kuma abincinsa na haram ne, abin shansa haramun ne, tufafinsa
haramun ne, an ciyar da shi da haram, ta yaya za a amsa masa (addu’arsa)?! Muslim
[1015].
الحديث الحادي عشر:
عَنْ أبي محمد الحسن بن
علي بن أبي طالب سبط رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم وريحانته رضي الله عنهما،
قَالَ: حَفِظْت مِنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «دَعْ
مَا يَرِيبُكَ إِلَى مَا لَا يَرِيبُكَ»، رواه الترمذي والنسائي، وقال
الترمذي: حديث حسن صحيح.
HADISI NA
GOMA SHA XAYA:
An
ruwaito daga Abu Muhammadu; Hasan xan Aliyu xan Abu xalib, Jikan Manzon Allah
(S.A.W) abin qaunarsa yace: Na haddato daga Manzon Allah (S.A.W) yace: “Ka qyale
duk abinda yake sanya ka kokwanto zuwa abinda ba ya maka kokwanto”.
Tirmiziy [2520] da Nasa’iy [5711] suka ruwaito shi, Tirmiziy yace: hadisi ne mai kyau, ingantacce.
الحديث الثاني عشر:
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي
الله عنه، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: مِنْ
حُسْنِ إِسْلاَمِ الْمَرْءِ تَرْكُهُ مَا لاَ يَعْنِيهِ». حديث حسن، رواه
الترمذي وغيره وهكذا.
HADISI NA
GOMA SHA BIYU:
An
ruwaito daga Abu Hurairata (r.a) yace: Manzon Allah (S.A.W) yace: “Yana
daga kyan musulunci mutum barin abinda bai shafe shi ba”.
Tirmiziy da Ibnu-Majah [2318] [ 3976].
الحديث الثالث عشر:
عن أبي حمزة أنس بن
مالك رضي الله عنه خادم رسول الله صلى الله عليه وسلم عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لاَ يُؤْمِنُ أَحَدُكُمْ حَتَّى يُحِبَّ
لِأَخِيهِ مَا يُحِبُّ لِنَفْسِهِ»، رواه البخاري ومسلم.
HADISI NA
GOMA SHA UKU:
An
ruwaito daga Abu Hamza, Anas xan Malik (R.A) yaron gidan Annabi (S.A.W) yace:
Manzon Allah yace: “Xayanku ba ya zama mai cikakken imani har sai yaso wa
xan'uwansa irin abinda yake so wa kansa”, Bukhariy [13] da Muslim [45]
suka ruwaito shi.
الحديث الرابع عشر:
عن ابن مسعود رضي الله
عنه قال: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "لَا
يَحِلُّ دَمُ امْرِئٍ مُسْلِمٍ، إِلَّا بِإِحْدَى ثَلَاثٍ: الثَّيِّبُ الزَّانِي،
وَالنَّفْسُ بِالنَّفْسِ، وَالتَّارِكُ لِدِينِهِ الْمُفَارِقُ لِلْجَمَاعَةِ»، رواه
البخاري ومسلم.
HADISI NA
GOMA SHA HUXU:
An
ruwaito daga Abdullahi xan Mas’ud (R.A) yace: Manzon Allah (S.A.W) yace: “Jinin
mutum musulmi baya halatta sai da xaya daga cikin laifuka guda uku: magidancin
da yayi zina, da rai wacce ta kashe rai, da wanda ya bar addininsa ya rabu da
jama’a”. Bukhariy [ 6878] da Muslim [1676].
الحديث الخامس عشر:
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي
الله عنه، عَنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ
كانَ يُؤْمِنُ بِاللهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ فَلْيَقُلْ خَيْرًا أَوْ لِيصْمُتْ،
وَمَنْ كَانَ يُؤْمِنُ بِاللهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ فَلْيُكْرِمْ جَارَهُ، وَمَنْ
كَانَ يُؤْمِنُ بِاللهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ فَلْيُكْرِمْ ضَيْفَهُ»، رواه
البخاري ومسلم.
HADISI NA
GOMA SHA BIYAR:
An
ruwaito daga Abu Hurairata (R,A) yace: Lallai Annabi (S.A.W) yace: “Wanda ya
yi imani da Allah da ranar qarshe, ya faxi alheri ko yayi shiru. Wanda ya yi
imani da Allah da ranar qarshe to ya girmama maqobcinsa. Wanda ya yi imani da
Allah da ranar qarshe to ya girmama baqonsa”. Bukhariy da Muslim
[6918], [48]suka ruwaito shi.
الحديث السادس عشر:
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ
رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، أَنَّ رَجُلًا قَالَ لِلنَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ: أَوْصِنِي، قَالَ: «لاَ تَغْضَبْ» فَرَدَّدَ مِرَارًا، قَالَ: «لاَ
تَغْضَبْ»، رواه البخاري.
HADISI NA
GOMA SHA SHIDA:
An
ruwaito daga Abu hurairata R.A yace: Wani mutum yazo, yace da Annabi: Kayi min
wasiyya sai yace: “Kada ka yi fushi”, sai yayi ta maimaita buqatarsa,
sai (Annabi) yace, kada ka yi fushi. Bukhariy [6116] ya ruwaito shi.
الحديث السابع عشر:
عَنْ أبي يعلى شَدَّادِ
بْنِ أَوْسٍ رضي الله عنه، عَنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ،
قَالَ: «إِنَّ اللهَ كَتَبَ الْإِحْسَانَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ، فَإِذَا
قَتَلْتُمْ فَأَحْسِنُوا الْقِتْلَةَ، وَإِذَا ذَبَحْتُمْ فَأَحْسِنُوا الذَّبْحَ،
وَلْيُحِدَّ أَحَدُكُمْ شَفْرَتَهُ، فَلْيُرِحْ ذَبِيحَتَهُ»، رواه مسلم.
HADISI NA
GOMA SHA BAKWAI:
An
ruwaito daga Abu Ya’alah; Shaddadu xan Ausi (R.A) daga Annabi (s.a.w) yace: “Allah
ta’alah ya wajabta kyautatawa ga kowanne irin abu; Idan za ku yi kisa ku
kyautatawa kisan, Idan za ku yi yanka; ku kyautata yankan, kowanne xayanku ya
wasa wuqarsa; ya hutar da abin yankansa”. Muslim [1955] ya ruwaito shi.
الحديث الثامن عشر:
عَنْ أَبِي ذَرٍّ جندب
بن جنادة، وأبي عبد الرحمن معاذ بن جبل رضي الله عنهما عن رسول اللهِ صَلَّى
اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: اتَّقِ اللهِ حَيْثُمَا كُنْتَ، وَأَتْبِعِ
السَّيِّئَةَ الحَسَنَةَ تَمْحُهَا، وَخَالِقِ النَّاسَ بِخُلُقٍ حَسَنٍ»، رواه
الترمذي وقال: حديث حسن، وفي بعض النسخ: حسن صحيح.
HADISI NA
GOMA SHA TAKWAS:
An
ruwaito daga Abu Zarri; wato Jundubu xan Junadata, da Abu Abdurrahman; wato
Mu’azu xan Jabal (R.A), yace: Manzon Allah (s.a.w) yace: “Ka kiyaye dokokin Allah, a duk
inda kake, kuma ka biyo da kyakkyawan aiki bayan mummmuna; sai ya shafe shi,
kuma ka xabi’anci mutane da kyakkywar xabi’a”. Tirmizi [1987] ya
ruwaito shi. Yace: hadisi ne mai kyau (hasan). A wani bugun kuma: mai kyau
ingantacce (hasanun sahihun).
الحديث التاسع عشر:
عن أبي العباس عبد الله
بن عباس رضي الله عنهما قال: كُنْتُ خَلْفَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللَّهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَوْمًا، فَقَالَ: يَا غُلاَمُ إِنِّي أُعَلِّمُكَ كَلِمَاتٍ،
احْفَظِ اللَّهَ يَحْفَظْكَ، احْفَظِ اللَّهَ تَجِدْهُ تُجَاهَكَ، إِذَا سَأَلْتَ
فَاسْأَلِ اللَّهَ، وَإِذَا اسْتَعَنْتَ فَاسْتَعِنْ بِاللَّهِ، وَاعْلَمْ أَنَّ
الأُمَّةَ لَوْ اجْتَمَعَتْ عَلَى أَنْ يَنْفَعُوكَ بِشَيْءٍ لَمْ يَنْفَعُوكَ
إِلاَّ بِشَيْءٍ قَدْ كَتَبَهُ اللَّهُ لَكَ، وَلَوْ اجْتَمَعُوا عَلَى أَنْ
يَضُرُّوكَ بِشَيْءٍ لَمْ يَضُرُّوكَ إِلاَّ بِشَيْءٍ قَدْ كَتَبَهُ اللَّهُ
عَلَيْكَ، رُفِعَتِ الأَقْلاَمُ وَجَفَّتْ الصُّحُفُ» . رواه الترمذي وقال
حديث حسن صحيح. وفي رواية غير الترمذي: «احْفَظِ اللهَ تَجِدْهُ أَمَامَكَ،
تَعَرَّفْ إِلَيْهِ فِي الرَّخَاءِ، يَعْرِفْكَ فِي الشِّدَّةِ، وَاعلم أَنَّ مَا
أَخْطَأَكَ لَمْ يَكُنْ لِيُصِيبَكَ، وَمَا أَصَابَكَ لَمْ يَكُنْ لِيُخْطِئَكَ،
واعلم أَنَّ النَّصْرَ مَعَ الصَّبْرِ، وَأَنَّ الْفَرَجَ مَعَ الْكَرْبِ، وَأَنَّ
مَعَ الْعُسْرِ يُسْرًا» .
HADISI NA
GOMA SHA TARA:
An
ruwaito daga Abdullahi xan Abas (R.A) yace: Na kasance a bayan Manzon allah
(S.A.W) wata rana sai yace da ni, “Ya kai yaro! Zan sanar da kai wasu
kalmomi: Ka kiyaye Allah, sai ya kiya ye ka; ka kiyaye Allah za ka same shi a
gaba gare ka (yana yi maka jagoranci); idan zaka roqa to ka roqi Allah; idan
zaka nemi taimako ka nemi taimakon Allah. Ka sani, da al’umma za su taru kan su
amfane ka da wani abu, ba za su iya amfanar da kai komai ba , sai da abinda
Allah ya rubuta maka. Idan kuma da al’umma za su taru kan su cuce ka da wani
abu, ba za su cuce ka ba, sai da abinda Allah ya rubuta maka. An xauke
alkaluma, takardun kuma sun bushe”. Tirmiziy [2516] ya ruwaito shi,
yace hadisi ne mai kyau ingantacce.
A wata riwayar kuma wacce ba ta (Imam) tirmiziy ba, “Ka kiyaye dokar Allah, zaka samu Ubangiji a gabanka, ka nemi sanin Allah a lokacin da ka ke cikin yalwa, zai san da kai a lokacin da kake cikin tsanani. Ka sani duk abinda ya kuskure maka, to bai kasance zai same ka ba. Duk kuma abinda ya same ka bai kasance zai kuskure maka ba. Ka sani, lallai cin nasara yana tare da haquri, yayewar musiba kuma tana tare da baqin ciki, kuma lallai a tare da tsanani akwai sauki”.
A wata riwayar kuma wacce ba ta (Imam) tirmiziy ba, “Ka kiyaye dokar Allah, zaka samu Ubangiji a gabanka, ka nemi sanin Allah a lokacin da ka ke cikin yalwa, zai san da kai a lokacin da kake cikin tsanani. Ka sani duk abinda ya kuskure maka, to bai kasance zai same ka ba. Duk kuma abinda ya same ka bai kasance zai kuskure maka ba. Ka sani, lallai cin nasara yana tare da haquri, yayewar musiba kuma tana tare da baqin ciki, kuma lallai a tare da tsanani akwai sauki”.
الحديث العشرون:
عن أبي مَسْعُودٍ عقبة
بن عمرو الأنصاري البدري رضي الله عنه قال: قال رسول الله صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ: "إِنَّ مِمَّا أَدْرَكَ النَّاسُ مِنْ كَلاَمِ النُّبُوَّةِ
الأُولَى: إِذَا لَمْ تَسْتَحْيِ فَاصْنَعْ مَا شِئْتَ"، رواه البخاري.
HADISI NA
ASHIRIN:
An
ruwaito daga Abu Mas’ud; Uqbatu xan Amru Al’ansariy Albadariy (R.A) yace:
Manzon Allah (s.a.w) yace: “Yana daga cikin abinda mutane suka riska
daga zancen annabtar farko; idan har ka zamo ba ka jin kunya to ka aikata duk
abinda kake so”, Bukhariy [3483].
الحديث الحادي والعشرون:
عن أبي عمرو –وقيل: أبي عمرة- سُفْيَانَ بْنِ عَبْدِ اللهِ رضي الله عنه قَالَ:
قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ، قُلْ لِي فِي الْإِسْلَامِ قَوْلًا لَا أَسْأَلُ
عَنْهُ أَحَدًا غَيْرَكَ، قَالَ: "قُلْ: آمَنْتُ بِاللهِ، ثُمَّ اسْتَقِمْ"،
رواه مسلم.
HADISI NA
ASHIRIN DA XAYA:
An
ruwaito daga Abu amrin, ko abiy Amrata, sufyan xan Abdullahi (R.A) yace: Nace:
Ya Manzon Allah (s.a.w) fada min wata Magana, a cikin addinin musulunci wanda
ba zan sake tambayar waninka ba game da ita? Sai yace: “Ka ce na
yi imani da Allah, sannan ka daidaitu”, Muslim ya ruwaito shi.
الحديث الثاني والعشرون:
عن أبي عبد الله جابر
بن عبد الله الأنصاري رضي الله عنهما أن رجلاً سأل رسول الله صلى الله عليه وسلم
فقال: أَرَأَيْتَ إِذَا صَلَّيْتُ الْمَكْتُوبَاتِ، وَصُمْتُ رَمَضَانَ،
وَحَرَّمْتُ الْحَرَامَ، وَأَحْلَلْتُ الْحَلَالَ، وَلَمْ أَزِدْ عَلَى ذَلِكَ
شَيْئًا، أَأَدْخُلُ الْجَنَّةَ؟ قَالَ: " نَعَمْ "، رواه مسلم. ومعنى
حرمت الحرام: اجتنبته، ومعنى أحللت الحلال: فعلته معتقدًا حله.
HADISI NA
ASHIRIN DA BIYU:
An
ruwaito daga abu Abdullahi Jabir dan Abdullahi Al’ansari (R.A) yace wani mutum
ya tambayi Annabi (s.a.w) yace: Ba ni labari idan na sallaci salloli na wajibi,
na azumci watan Ramadan, ha halatta halal, na haramta haram. Ban qara komai a
kan haka ba, shin zan shiga Aljanna? sai Annabi (s.a.w) yace: “Eh! Za
ka shiga aljanna”, Muslim ne ya ruwaito shi [15].
Ma'anan: (Na haramta haram shine: Na nuisance
shi.
Ma'anan: Na halatta halal shine: Na yi aiki da
shi ina qudurta halaccinsa).
الحديث الثالث والعشرون:
عَنْ أَبِي مَالِكٍ الحارث
بن عاصم الْأَشْعَرِيِّ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «الطُّهُورُ شَطْرُ الْإِيمَانِ وَالْحَمْدُ لِلَّهِ
تَمْلَأُ الْمِيزَانَ، وَسُبْحَانَ اللهِ وَالْحَمْدُ لِلَّهِ تَمْلَآَنِ -أَوْ
تَمْلَأُ- مَا بَيْنَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ، وَالصَّلَاةُ نُورٌ،
وَالصَّدَقَةُ بُرْهَانٌ، وَالصَّبْرُ ضِيَاءٌ، وَالْقُرْآنُ حُجَّةٌ لَكَ أَوْ
عَلَيْكَ، كُلُّ النَّاسِ يَغْدُو فَبَايِعٌ نَفْسَهُ فَمُعْتِقُهَا أَوْ
مُوبِقُهَا»، رواه مسلم.
HADISI NA
ASHIRIN DA UKU:
An
ruwaito daga Abu Malik; Haris xan Asim Al-ash’ariy yace: Manzon Allah (s.a.w)
yace: “Tsarki rabin imani ne, faxin subhanallahi tana cika mizani,
faxin subhanallahi da Alhamdulillah suna cika, ko kuma kowacce xaya tana cika abinda
yake tsakanin sama da qasa, Sallah kuma haske ce, Ita kuma sadaka hujja ce,
Haquri haske ne, Alkur’ani hujja ne a gare ka, ko a kanka. Dukkan mutane suna
jijjifi da safe, daga cikinsu akwai mai zuwa sayar da kansa, ko dai ya ‘yantar
da kansa ko kuma ya halakar da kansa”, Muslim ya ruwaitoshi [223].
الحديث الرابع والعشرون
عَنْ أَبِي ذَرٍّ رضي
الله عنه، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِيمَا يرويه عَن ربه
عز وجل أَنَّهُ قَالَ: «يَا عِبَادِي إِنِّي حَرَّمْتُ الظُّلْمَ عَلَى
نَفْسِي، وَجَعَلْتُهُ بَيْنَكُمْ مُحَرَّمًا فَلَا تَظَالَمُوا.
يَا عِبَادِي كُلُّكُمْ ضَالٌّ إِلَّا مَنْ هَدَيْتُهُ، فَاسْتَهْدُونِي
أَهْدِكُمْ.
يَا عِبَادِي كُلُّكُمْ جَائِعٌ، إِلَّا مَنْ أَطْعَمْتُهُ،
فَاسْتَطْعِمُونِي أُطْعِمْكُمْ.
يَا عِبَادِي كُلُّكُمْ عَارٍ، إِلَّا مَنْ كَسَوْتُهُ، فَاسْتَكْسُونِي
أَكْسُكُمْ.
يَا عِبَادِي إِنَّكُمْ تُخْطِئُونَ بِاللَّيْلِ وَالنَّهَارِ، وَأَنَا
أَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا، فَاسْتَغْفِرُونِي أَغْفِرْ لَكُمْ.
يَا عِبَادِي إِنَّكُمْ لَنْ تَبْلُغُوا ضَرِّي فَتَضُرُّونِي وَلَنْ تَبْلُغُوا
نَفْعِي، فَتَنْفَعُونِي.
يَا عِبَادِي لَوْ أَنَّ أَوَّلَكُمْ وَآخِرَكُمْ وَإِنْسَكُمْ وَجِنَّكُمْ
كَانُوا عَلَى أَتْقَى قَلْبِ رَجُلٍ وَاحِدٍ مِنْكُمْ، مَا زَادَ ذَلِكَ فِي
مُلْكِي شَيْئًا.
يَا عِبَادِي لَوْ أَنَّ أَوَّلَكُمْ وَآخِرَكُمْ وَإِنْسَكُمْ وَجِنَّكُمْ
كَانُوا عَلَى أَفْجَرِ قَلْبِ رَجُلٍ وَاحِدٍ، مَا نَقَصَ ذَلِكَ مِنْ مُلْكِي
شَيْئًا.
يَا عِبَادِي لَوْ أَنَّ أَوَّلَكُمْ وَآخِرَكُمْ وَإِنْسَكُمْ وَجِنَّكُمْ
قَامُوا فِي صَعِيدٍ وَاحِدٍ فَسَأَلُونِي فَأَعْطَيْتُ كُلَّ إِنْسَانٍ مَسْأَلَتَهُ،
مَا نَقَصَ ذَلِكَ مِمَّا عِنْدِي إِلَّا كَمَا يَنْقُصُ الْمِخْيَطُ إِذَا
أُدْخِلَ الْبَحْرَ.
يَا عِبَادِي إِنَّمَا هِيَ أَعْمَالُكُمْ أُحْصِيهَا لَكُمْ، ثُمَّ
أُوَفِّيكُمْ إِيَّاهَا، فَمَنْ وَجَدَ خَيْرًا، فَلْيَحْمَدِ اللهَ وَمَنْ وَجَدَ
غَيْرَ ذَلِكَ، فَلَا يَلُومَنَّ إِلَّا نَفْسَهُ»، رواه مسلم.
HADISI NA
ASHIRIN DA HUXU:
An
ruwaito daga Abu zarrin Al’gifariy (R.A) daga Annabi (s.a.w) cikin abinda
Annabi yake ruwaitowa daga Ubangijinsa; lallai Allah mabuwayi da xaukaka
yace: “Ya ku bayina! Lallai na
haramta wa kaina zalunci, kuma na sanya zalunci ya zama abin haramtawa a
tsakaninku.
Ya ku bayina! dukkaniku vatattu ne, sai
wanda na shiryar da shi; ku nemi shiryarwata; in shiryar da ku.
Ya ku bayina! dukkaniku mayunwata ne sai
wanda na ciyar da shi; sai ku nemi ciyarwata; in ciyar da ku.
Ya ku bayina! kowanenku tsirara ya ke babu
tufafi sai wanda na suturta shi; sai ku nemi suturata, in suturtar da ku.
Ya ku bayina ! lallai kuna yin laifi dare da
rana, ni kuma ina gafarta zunubai gabaxaya; sai ku nemi gafarata; in yi muku
gafara.
Ya ku bayina! Lallai ku ba ku isa ku cutar
da ni ba ballantana ku cutar da ni, Kuma ba ku isa ku amfanar da ni ba,
ballantana ku amfanar da ni.
Ya ku bayani da ace na farkonku da na
qarshenku, da mutanenku da aljanunku, ku kasance a bisa ga zuciyar wani mutum
xaya cikin mafi taqawar Allah; to da
hakan ba zai qara komai a cikin mulkina ba.
Ya ku bayina da ace na farkonku da na
qarshenku, da mutanenku da aljanuku ku kasance a bisa zuciyar mafi fajirci to
hakan ba zai rage komai dangane da mulkina ba.
Ya ku bayina! da ace na farkonku da na
qarshenku, da mutanenku da aljanunku zasu tsaya a bigire xaya, sai kowanne ya
roqe ni, sai in bada kowanne xaya abinda ya roqa; to ba zai rage komai daga
cikin abinda yake wurina ba sai kamar gwargwadon abinda allura ta rage; idan
aka tsoma ta a cikin ruwan teku.
Ya ku bayina! Lallai waxannan ayyukan ku ne, na ke qididdige su a
gare ku, sa'annan sai in cika muku sakamakonsu; duk wanda ya samu alheri to, ya
gode wa Allah. Wanda kuma ya samu wanin haka, kar ya zargi kowa sai kansa”, Muslim
ne ya ruwaito shi.
الحديث الخامس والعشرون:
عن أبي ذر رضي الله عنه
أَنَّ نَاسًا مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالُوا
لِلنَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: يَا رَسُولَ اللهِ، ذَهَبَ
أَهْلُ الدُّثُورِ بِالْأُجُورِ، يُصَلُّونَ كَمَا نُصَلِّي، وَيَصُومُونَ كَمَا
نَصُومُ، وَيَتَصَدَّقُونَ بِفُضُولِ أَمْوَالِهِمْ، قَالَ: " أَوَلَيْسَ
قَدْ جَعَلَ اللهُ لَكُمْ مَا تَصَّدَّقُونَ؟ إِنَّ بِكُلِّ تَسْبِيحَةٍ صَدَقَةً،
وَكُلِّ تَكْبِيرَةٍ صَدَقَةً، وَكُلِّ تَحْمِيدَةٍ صَدَقَةً، وَكُلِّ تَهْلِيلَةٍ
صَدَقَةً، وَأَمْرٌ بِالْمَعْرُوفِ صَدَقَةٌ، وَنَهْيٌ عَنْ مُنْكَرٍ صَدَقَةٌ،
وَفِي بُضْعِ أَحَدِكُمْ صَدَقَةٌ، قَالُوا: يَا رَسُولَ اللهِ، أَيَأتِي
أَحَدُنَا شَهْوَتَهُ وَيَكُونُ لَهُ فِيهَا أَجْرٌ؟ قَالَ: «أَرَأَيْتُمْ لَوْ
وَضَعَهَا فِي حَرَامٍ أَكَانَ عَلَيْهِ فِيهَا وِزْرٌ؟ فَكَذَلِكَ إِذَا
وَضَعَهَا فِي الْحَلَالِ كَانَ لَهُ أَجْرٌ»، رواه مسلم.
HADISI NA
ASHIRIN DA BIYAR:
An
ruwaito daga Abu zarrin Al'gifariy (R.A) yace: Lallai wassu mutane daga cikin
sahabban Manzon Allah (s.a.w) sun ce da Annabi (s.a.w), ya Manzon Allah!
ma’abota dukiya sun tafi da lada suna yin sallah kamar yadda muke yi, suna yin
azumi kamar yadda muke yi, kuma suna sadaka da sauran dukiyarsu, Sai Annabi yace:
“Shin Allah bai baku abinda zaku
yi sadaka ba! Lallai dukkan wani tasbihi da za ku yi sadaka ne, dukkan kabbara
sadaka ne, dukkan hamdala sadaka ne, kuma dukkan wata hailala sadaka ne, dukkan
umarni da kyakkyawa sadaka ne, hana mummunan aiki sadaka ne, kuma a gavar
kowannenku akwai sadaka, Sai sahababai suka ce: Ya Manzon Allah!
yanzu xayanmu zai biya buqatarsa, kuma ya zama yana da lada? Sai ya ce: Ku bani
labari, da ace zai sanya gavar tasa a cikin haram; shin zai kasance yana da
zunubi ? to haka, idan ya sanya ta a cikin halal zai kasance yana da lada”, Muslim
ya ruwaito shi.
الحديث السادس والعشرون:
عن أبي هريرة رضي الله
عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «كُلُّ سُلَامَى مِنَ النَّاسِ
عَلَيْهِ صَدَقَةٌ، كُلَّ يَوْمٍ تَطْلُعُ فِيهِ الشَّمْسُ» قَالَ: «تَعْدِلُ
بَيْنَ الِاثْنَيْنِ صَدَقَةٌ، وَتُعِينُ الرَّجُلَ فِي دَابَّتِهِ فَتَحْمِلُهُ
عَلَيْهَا، أَوْ تَرْفَعُ لَهُ عَلَيْهَا مَتَاعَهُ صَدَقَةٌ» قَالَ:
«وَالْكَلِمَةُ الطَّيِّبَةُ صَدَقَةٌ، وَكُلُّ خُطْوَةٍ تَمْشِيهَا إِلَى
الصَّلَاةِ صَدَقَةٌ، وَتُمِيطُ الْأَذَى عَنِ الطَّرِيقِ صَدَقَةٌ». رواه
البخاري ومسلم.
HADISI NA
ASHIRIN DA SHIDA:
An
ruwaito daga Abu hurairata (R.A) ya ce: “Dukkan gavvai na mutane akwai
sadaka akansu, Kowanne yini da rana take hudowa a cikinsa da zaka sasanta
tsakanin mutane biyu sadaka ne, ka taimaki mutum game da dabbarsa, ka xora shi
a akanta, ko ka sauke masa kayansa daga kanta sadaka ne, ita ma kalma daddaxa
sadaka ce, kuma dukkan taku da zaka yi tattaki zuwa sallah sadaka ne, kuma ka
dauke abu mai cutarwa daga kan hanya sadaka ne”.
Bukhariy (2989) da Muslim (1009) suka ruwaito shi.
الحديث السابع والعشرون:
عَنِ النَّوَّاسِ بْنِ
سِمْعَانَ رضي الله عنه عن النبي صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: «الْبِرُّ
حُسْنُ الْخُلُقِ، وَالْإِثْمُ مَا حَاكَ فِي نَفْسِكَ، وَكَرِهْتَ أَنْ يَطَّلِعَ
عَلَيْهِ النَّاسُ»، رواه مسلم. وعَنْ وَابِصَةَ بْنِ مَعْبَدٍ رضي الله عنه،
قَالَ: «أتيتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فقَالَ: جِئْتَ
تَسْأَلُ عَنِ الْبِرِّ؟» قُلْتُ: نَعَمْ، قَالَ: «اسْتَفْتِ قَلْبَكَ، الْبِرُّ:
مَا اطْمَأَنَّتْ إِلَيْهِ النَّفْسُ، وَاطْمَأَنَّ إِلَيْهِ الْقَلْبُ،
وَالْإِثْمُ: مَا حَاكَ فِي النَّفْسِ، وَتَرَدَّدَ فِي الصَّدْرِ، وَإِنْ
أَفْتَاكَ النَّاسُ وَأَفْتَوْكَ»، حديث حسن. رويناه في مسندي الإمامين أحمد
بن حنبل والدرامي بإسناد حسن.
HADISI NA
ASHIRIN DA BAKWAI:
An
ruwaito daga Annawas xan Sam'an (r.a),
daga Annabi (s.a.w) yace: “Albirru shine: kyakkyawan halayya, Shi kuma
Ismu shine: Abinda yayi maka susa a cikin ranka, kuma kake qin mutane su ganshi”, Muslim
ya ruwaito shi.
An
ruwaito daga Wabisa xan Ma'abad, yace: Na zo wajen Manzon Allah (s.a.w) sai
yace: Ka zo ka tambayi ma'anan albirru? Sai nace: E na'am, Sai yace: “Ka yi
fatawa wa zuciyarka, Albirru: shine abinda rai ya nitsu zuwa gare shi, zuciya
itama ta samu nitsuwa da shi. Shi kuma ismu: Duk abinda ya yi susa a cikin rai,
kuma ya yi ta kai-komo a cikin qirji, koda mutane sun baka fatawa, sun kuma yi
ta baka fatawa”. Hadisi ne hasan, Mun ruwaito shi a cikin littatafan
Musnad guda biyu; Ahmad xan Hanbal, da Addarimiy, da isnadi hasan.
الحديث الثامن والعشرون:
عَنْ أبي نُجيح
عِرْبَاضِ بْنِ سَارِيَةَ رضي الله عنه، قَالَ: وَعَظَنَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مَوْعِظَةً بَلِيغَةً، وَجِلَتْ مِنْهَا الْقُلُوبُ وذَرَفَتْ
لَهَا الْأَعْيُنُ، فقُلْنَا: يَا رَسُولَ اللهِ، كَأَنَّ هَذِهِ مَوْعِظَةُ
مُوَدِّعٍ، فَأَوْصِنَا، قَالَ: "أُوصِيكُمْ بِتَقْوَى اللهِ عز وجل وَالسَّمْعِ
وَالطَّاعَةِ وَإِنْ تأمر عليكم عَبْد، فَإِنَّهُ مَنْ يَعِشْ مِنْكُمْ فسيَرَى
اخْتِلَافًا كَثِيرًا، فَعَلَيْكُمْ بِسُنَّتِي وَسُنَّةِ الْخُلَفَاءِ
الرَّاشِدِينَ الْمَهْدِيِّينَ، عَضُّوا عَلَيْهَا بِالنَّوَاجِذِ، وَإِيَّاكُمْ
وَمُحْدَثَاتِ الْأُمُورِ، فَإِنَّ كُلَّ بِدْعَةٍ ضَلَالَةٌ"، رواه أبو
داود والترمذي وقال: حديث حسن صحيح.
HADISI NA
ASHIRIN DA TAKWAS:
An
ruwaito daga Abu Nujaih, wato: Irbadu xan Sariya (R.A) yace: Manzon Allah
(s.a.w) yayi mana wa’azi; wa’azi mai isarwa; wanda zukata suka tsorata, idanu
suka zubar da hawaye. Sai muka ce: Ya Manzon Allah (s.a.w) kamar wa’azin mai
bankwana; to kayi mana wasici, Sai yace, Ina muku wasici da bin dokokin
Allah, da kuma ji da bi, ko da bawa ne ya zama shugaba a gare ku, lallai wanda
ya rayu a cikinku da sannu zai ga savani mai yawa, na umarce ku da yin riqo da
sunnata, da sunnonin halifofi shiryayyu. Ku riqe ta da haqoranku (Fiqa), kuma
ku kiyaye fararrun ala’mura; domin kowace, bidi’a vata ce. Abu
dawud [4607] da Timiziy yace wannan hadisi ne mai kyauingantacce.
الحديث التاسع والعشرون:
عَنْ مُعَاذِ بْنِ جَبَلٍ رضي الله عنه قال: قلت يا رسول الله أَخْبِرْنِي
بِعَمَلٍ يُدْخِلُنِي الْجَنَّةَ، وَيُبَاعِدُنِي مِنَ النَّارِ. قَالَ:
"لَقَدْ سَأَلْتَ عَنْ عَظِيمٍ، وَإِنَّهُ لَيَسِيرٌ عَلَى مَنْ يَسَّرَهُ
اللهُ عَلَيْهِ، تَعْبُدُ اللهَ وَلَا تُشْرِكُ بِهِ شَيْئًا، وَتُقِيمُ
الصَّلَاةَ، وَتُؤْتِي الزَّكَاةَ، وَتَصُومُ رَمَضَانَ، وَتَحُجُّ الْبَيْتَ"
ثُمَّ قَالَ: "أَلَا أَدُلُّكَ عَلَى أَبْوَابِ الْخَيْرِ؟ الصَّوْمُ
جُنَّةٌ، وَالصَّدَقَةُ تُطْفِئُ الْخَطِيئَةَ كما يطفئ الماء النار، وَصَلَاةُ
الرَّجُلِ فِي جَوْفِ اللَّيْلِ " ثُمَّ تلا: {تَتَجَافَى جُنُوبُهُمْ عَنِ
الْمَضَاجِعِ} حَتَّى بَلَغَ،
{يَعْمَلُونَ} [السجدة: 17] ثُمَّ قَالَ: "أَلَا أُخْبِرُكَ بِرَأْسِ الْأَمْرِ
وَعَمُودِهِ وَذُرْوَةِ سَنَامِهِ؟" فَقُلْتُ: بَلَى يَا رَسُولَ اللهِ.
قَالَ: "رَأْسُ الْأَمْرِ الْإِسْلَامُ وَعَمُودُهُ الصَّلَاةُ،
وَذِرْوَةُ سَنَامِهِ الْجِهَادُ" ثُمَّ قَالَ: "أَلَا
أُخْبِرُكَ بِمِلَاكِ ذَلِكَ كُلِّهِ؟" فَقُلْتُ لَهُ: بَلَى يَا رَسُولَ
اللهِ. فَأَخَذَ بِلِسَانِهِ، فَقَالَ: " كُفَّ عَلَيْكَ هَذَا"
فَقُلْتُ: يَا نبي الله، وَإِنَّا لَمُؤَاخَذُونَ بِمَا نَتَكَلَّمُ بِهِ؟
فَقَالَ: "ثَكِلَتْكَ أُمُّكَ يَا مُعَاذُ، وَهَلْ يَكُبُّ النَّاسَ فِي
النَّارِ عَلَى وُجُوهِهِمْ، أَوْ قَالَ: عَلَى مَنَاخِرِهِمْ، إِلَّا حَصَائِدُ
أَلْسِنَتِهِمْ؟"، رواه الترمذي وقال: حديث حسن صحيح.
HADISI NA
ASHIRIN DA TARA:
An
ruwaito daga Mu’azu xan Jabal (R.A) yace: Nace ya Manzon Allah bani labarin
wani aiki da zai shigar da ni aljanna, kuma ya nisantar da ni daga shiga wuta,
sai ya ce: Haqiqa ka yi tambaya game da abu mai girma, saidai abu ne mai
sauqi ga wanda Allah ya sauqaqe shi a gare shi; ka bauta wa Allah ba tare da ka
haxa shi da wani ba, kuma ka tsayar da Sallah, kuma ka bada zakka, kuma ka
azumci Ramadan, sannan ka ziyarci xakin Allah. Sannan sai yace: Shin ba
zan shiryar da kai qofofin alheri ba? Azumi garkuwa ne, sadaka kuma tana shafe
kurakurai kamar yadda ruwa ke kashe wuta. haka sallar mutum a cikin yankin
dare. Sannan ya karanta faxin Allah: (Gefen jikinsu yana nisantar gurin
kwanciyar su) har ya kai inda Allah yake cewa: ‘ya ‘amaluun.
Sannan sai yace: Ba zan ba ka labari dangane
da, kan wannan al’amarin ba, da ginshiqansa, da qololuwar tozonsa? Sai nace:
Eh. Sai yace: Kan wannan lamarin shine: Musulunci. Ginshiqinsa kuwa sallah.
Qololuwar tozonsa kuma shine: Jihadi”.
Sannan yace: Ba zan baka labarin abinda yake
mallakar hakan gabaxayansa ba? Sai nace: Bani labari.
Sai ya kama harshensa yace: Ka kiyaye wa kanka
wannan! Sai na ce: Shin yanzu za a kama mu da maganar da muka yi? Sai yace: Da
mahaifiyarka ta rasa ka, ashe akwai abinda yake jefa mutane a wuta kan
fuskokinsu, (ko yace) kan hancinsu sai sakamakon abinda harshensu ya girbe musu”. Tirmiziy
[ 2616] ya ce hadisi ne mai kyau ingantacce.
الحديث الثلاثون:
عَنْ أَبِي ثَعْلَبَةَ الخشبي
جرثوم بن ناشر رضي الله تعالى عنه عن
رَسُول اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: «إِنَّ اللهَ فَرَضَ
فَرَائِضَ فَلَا تُضَيِّعُوهَا، وَحَدَّ حُدُودًا فَلَا تَعْتَدُوهَا، وَحَرَّم
أَشْيَاءَ فَلَا تَنْتَهِكُوهَا،وَسَكَتَ عَنْ أَشْيَاءَ رحمة لكم غَيْر نِسْيَانٍ
فَلَا تَبْحَثُوا عَنْهَا»، حديث حسن رواه الدارقطني وغيره.
HADISI NA
TALATIN:
An
ruwaito daga Abu Sa’alabata; wato: Jursumu xan Nashir (R.A). yace: “Lallai
Allah Ta’alah ya farlanta farillai, kada ku tozarta su, ya kuma sanya iyakoki;
kar ku ketare su, ya haramta wasu abubuwa, kada ku keta alfarmominsu, ya yi
shiru game da wassu abubuwa don jin qai a gare ku, ba don mantuwa ba, kar ku
bincike su”. Hadisi ne hasan, Daraquxuniy da waninsa suka ruwaito shi.
الحديث الحادي والثلاثون:
عَنْ أبي العباس سَهْلِ
بْنِ سَعْدٍ السَّاعِدِيِّ رضي الله عنه، قَالَ: جاء رَجُلٌ إلى النَّبِيّ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ دُلَّنِي عَلَى عَمَلٍ
إِذَا أَنَا عَمِلْتُهُ أَحَبَّنِي اللَّهُ وَأَحَبَّنِي النَّاسُ؟ فَقَالَ: «ازْهَدْ
فِي الدُّنْيَا يُحِبَّكَ اللَّهُ، وَازْهَدْ فِيمَا فِي أَيْدِي النَّاسِ
يُحِبُّكَ النَّاسُ»، حديث حسن، رواه ابن ماجة وغيره بأسانيد حسنة.
HADISI NA
TALATIN DA XAYA:
An
ruwaito daga Abu Abbas; Sahlu xan Sa’ad Assa’idiy (R.A) yace: Wani mutum ya zo
wajen Annabi (S.A.W) ya ce: Ya Manzon Allah! Nuna min aikin da idan na aikata
shi, Allah zai qaunace ni, mutane suma za su qaunace ni? Sai ya ce: “Ka yi
zuhudu cikin lamarin duniya, sai Allah ya qaunace ka, kuma ka nisanci abin
hunnun mutane, sai mutane su qaunace ka”, Hadisi ne hasan, Ibnu-Majah ne
ya ruwaito shi [4102] da waninsa ta hanyoyi masu kyau.
الحديث الثاني والثلاثون:
عَنْ أبي سعيد سعد بن مالك بن سنان الخدري رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ
اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَال: «لَا ضَرَرَ وَلَا ضِرَارَ»،
حديث حسن، رواه ابن ماجة والدارقطني وغيرهما مسندًا، ورواه مالك في الموطإ مرسلاً
عن عمرو بن يحيى عن أبيه عن النبي صلى الله عليه وسلم، فأسقط أبا سعيد، وله طرق يُقوِّي
بعضها بعضًا.
HADISI NA TALATIN
DA BIYU:
An
ruwaito daga Abu Sa’idu, wato Sa’ad xan Malik xan Sinan Al-Khudiry (R.A) yace:
Manzon Allah (S.A.W) yace: “Babu cuta babu cutarwa”.
Hadisine hasan, Ibnu Majah ya ruwaito shi, [2341] da Daraquxuniy [228] da
waninsu Musnadan. Haka Imamu Malik ya ruwaito shi a cikin Muwaxxa Mursalan
daga Amru xan Yahya, daga babansa, daga Annabi (s.a.w); bai ambaci Abu sa’id
ba.
Amma hadisin yana da hanyoyin da sashinsu ya
ke qarfafa sashi.
الحديث الثالث والثلاثون:
عن ابن عباس رضي الله
عنهما أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "لَوْ
يُعْطَى النَّاسُ بِدَعْوَاهُمْ لَادَّعَى رِجَالٌ أَمْوَالَ قَوْمٍ
وَدِمَاءَهُمْ, وَلَكِنَّ الْبَيِّنَةَ عَلَى الْمُدَّعِي, وَالْيَمِينَ عَلَى
مَنْ أَنْكَرَ"، حديث حسن، رواه البيهقي وغيره هكذا، وبعضه في الصحيحين.
HADISI NA
TALATIN DA UKU:
An
ruwaito daga Abdullahi xan Abbas (R.A) ya ce: Manzon Allah (S.A.W). ya ce: “Da za a
bai wa mutune (abinda suka faxa) daga da’awarsu, to da wadansu sun yi da’awar
dukiyar wadansu da jininsu’ saidai hujja tana kan mai da’awa, rantsuwa kuma
tana kan wanda ya yi musu”, Hadisi ne hasan, Baihaqiy ya ruwaito shi,
da waninsa. Wani sashi na hadisin yana cikin Bukhariy da Muslim.
الحديث الرابع والثلاثون:
عن أبي سعيد الخدري رضي
الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «مَنْ رَأَى مِنْكُمْ
مُنْكَرًا فَلْيُغَيِّرْهُ بِيَدِهِ، فَإِنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَبِلِسَانِهِ،
فَإِنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَبِقَلْبِهِ، وَذَلِكَ أَضْعَفُ الْإِيمَانِ»، رواه
مسلم.
HADISI NA
TALATIN DA HUXU:
An
ruwaito daga Abu Sa’id Al-Khuduriy (R.A) yace: Na ji Manzon Allah Annabi
(S.A.W) yana cewa: “Duk wanda ya ga abin qi, to ya gusar da shi da hannunsa, idan
kuma ba shi da iko to ya gusar da shi da harshensa, idan bai samu iko ba, to
sai ya qi abin a zuciyarsa, wannan kuma shi ne mafi raunin imani”, Muslim
ne ya ruwaito shi [49].
الحديث الخامس والثلاثون:
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ
رضي الله عنه، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا
تَحَاسَدُوا، وَلَا تَنَاجَشُوا، وَلَا تَبَاغَضُوا، وَلَا تَدَابَرُوا، وَلَا
يَبِعْ بَعْضُكُمْ عَلَى بَيْعِ بَعْضٍ، وَكُونُوا عِبَادَ اللهِ إِخْوَانًا؛
الْمُسْلِمُ أَخُو الْمُسْلِمِ؛ لَا يَظْلِمُهُ وَلَا يَخْذُلُهُ، ولا يكْذبُه،
وَلَا يَحْقِرُهُ، التَّقْوَى هَاهُنَا -وَيُشِيرُ إِلَى صَدْرِهِ ثَلَاثَ
مَرَّاتٍ-، بِحَسْبِ امْرِئٍ مِنَ الشَّرِّ أَنْ يَحْقِرَ أَخَاهُ الْمُسْلِمَ،
كُلُّ الْمُسْلِمِ عَلَى الْمُسْلِمِ حَرَامٌ؛ دَمُهُ، وَمَالُهُ، وَعِرْضُهُ»
رواه مسلم.
HADISI NA
TALATIN DA BIYAR:
An
ruwaito daga Abu Hurairata (R.A) yace: Manzon Allah (S.A.W) yace: “Kada ku
riqa yi wa juna hassada, kuma kada ku yi kore (cikin kasuwanci), kada kuyi
qiyayya da juna, kada ku juya wa juna bayanku, kuma kada sashenku ya yi ciniki
a cikin cinikin xan'uwansa. Ku kasance bayin Allah ‘yan'uwan juna. Musulmi
xan'uwan musulmi ne, baya zaluntar sa, kuma baya qin taimakonsa, kuma baya yi
masa qarya, kuma baya wulaqantar da shi. Taqawar Allah da bin dokokinsa yana
nan (har sau uku) -Yana nuna qirjinsa-,” Ya ishi
mutum sharri, ya riqa raina xan'uwansa musulmi. Jinin kowanne musulmi da
dukiyarsa da mutuncinsa, haramun ne a kan musulmi”. Muslim
ne ya ruwaito shi [2564].
الحديث السادس والثلاثون:
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ
رضي الله عنه، قَالَ: عن رَسُول اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَنْ نَفَّسَ عَنْ مُؤْمِنٍ كُرْبَةً مِنْ كُرَبِ الدُّنْيَا، نَفَّسَ اللهُ
عَنْهُ كُرْبَةً مِنْ كُرَبِ يَوْمِ الْقِيَامَةِ.
وَمَنْ يَسَّرَ عَلَى مُعْسِرٍ، يَسَّرَ اللهُ عَلَيْهِ فِي الدُّنْيَا
وَالْآخِرَةِ.
وَمَنْ سَتَرَ مُسْلِمًا، سَتَرَهُ اللهُ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ.
وَاللهُ فِي عَوْنِ الْعَبْدِ مَا كَانَ الْعَبْدُ فِي عَوْنِ أَخِيهِ.
وَمَنْ سَلَكَ طَرِيقًا يَلْتَمِسُ فِيهِ عِلْمًا، سَهَّلَ اللهُ لَهُ بِهِ
طَرِيقًا إِلَى الْجَنَّةِ.
وَمَا اجْتَمَعَ قَوْمٌ فِي بَيْتٍ مِنْ بُيُوتِ اللهِ، يَتْلُونَ كِتَابَ
اللهِ، وَيَتَدَارَسُونَهُ بَيْنَهُمْ، إِلَّا نَزَلَتْ عَلَيْهِمِ السَّكِينَةُ،
وَغَشِيَتْهُمُ الرَّحْمَةُ وَحَفَّتْهُمُ الْمَلَائِكَةُ، وَذَكَرَهُمُ اللهُ
فِيمَنْ عِنْدَهُ.
وَمَنْ بَطَّأَ بِهِ عَمَلُهُ، لَمْ يُسْرِعْ بِهِ نَسَبُهُ»، رواه مسلم بهذا اللفظ.
HADISI NA
TALATIN DA SHIDA:
An
ruwaito daga Abu hurairata (R.A) daga Annabi yace: “Wanda
duk ya kautar wa mumini wani baqin ciki daga cikin baqin cikin duniya to Allah
zai kautar masa da wani baqin ciki daga baqin cikin qiyama. Duk wanda ya kawo
sauqi ga wanda yake cikin tsanani, Allah zai kawo masa sauqi a duniya da
lahira. Wanda ya suturce musulmi, Allah zai yi masa sutura a duniya da lahira.
Lallai Allah yana taimakon bawa matuqar bawan yana taimakon xan'uwansa musulmi.
Wanda ya kama wani tafarki yana neman ilmi a cikinsa, Allah zai saukake masa
hanyar shiga aljanna. Babu wasu mutane da za su taru a cikin wani xaki cikin
xakunan Allah, suna karanta littafin Allah, suna yin darasinsa a tsakaninsu da
juna, face sai nutsuwa ta sauka a kansu, rahama ta lulluve su, Mala’iku kuma su
kewaye su, Sai kuma Allah ya ambace su ga waxanda suke wajensa. Wanda duk
aikinsa ya yi sanxa da shi, to dangatakarsa ba za ta yi gaggawa da shi ba”. Muslim
ne ruwaito shi [2699].
الحديث السابع والثلاثون:
عن ابن عباس رضي الله عنهما عن رسول الله صلى الله عليه وسلم فيما يرويه عن
ربه تبارك وتعالى قال: «إِنَّ اللهَ كَتَبَ الْحَسَنَاتِ وَالسَّيِّئَاتِ،
ثُمَّ بَيَّنَ ذَلِكَ، فَمَنْ هَمَّ بِحَسَنَةٍ فَلَمْ يَعْمَلْهَا كَتَبَهَا
اللهُ عِنْدَهُ حَسَنَةً كَامِلَةً، وَإِنْ هَمَّ بِهَا فَعَمِلَهَا كَتَبَهَا
اللهُ عِنْدَهُ عَشْرَ حَسَنَاتٍ إِلَى سَبْعِمِائَةِ ضِعْفٍ إِلَى أَضْعَافٍ
كَثِيرَةٍ، وَإِنْ هَمَّ بِسَيِّئَةٍ فَلَمْ يَعْمَلْهَا كَتَبَهَا اللهُ عِنْدَهُ
حَسَنَةً كَامِلَةً، وَإِنْ هَمَّ بِهَا فَعَمِلَهَا كَتَبَهَا اللهُ سَيِّئَةً
وَاحِدَةً»، رواه البخاري ومسلم في صحيحيهما بهذه الحروف. فانظر يا أخي وفقنا
الله وإياك إلى عظيم لطف الله تعالى، وتأمل هذه الألفاظ، وقوله عنده إشارة إلى
الإعتناء بها، وقوله كاملة للتأكيد وشدة الإعتناء بها، وقال في السيئة التي هم بها
ثم تركها كتبها الله عنه حسنة كاملة فأكدها بـ (كاملة) وإن عملها كتبها سيئة
واحدة، فأكد تقليلها بـ (واحدة) ولم يؤكدها بـ (كاملة) فلله الحمد والمنة، سبحانه
لا نحصي ثناء عليه، وبالله التوفيق.
HADISI NA
TALATIN DA BAKWAI:
An
ruwaito daga Dan Abbas (R.A), daga Manzon Allah (S.A.W), cikin irin abinda ya
ruwaito daga Ubangijisa yace: “Allah ya rubuta ayyukan alheri
da munana, sannan ya bayyana hakan, Wanda duk ya himmatu zai aikata wani
kyakkywan aiki sai bai samu aikatawa ba, Allah zai rubuta masa kyakkyawan aiki
guda xaya cikakke a wurinsa, idan kuma ya himmatu zai aikata wani kyakkywan
aiki sai kuma ya aikata shi, to Allah zai rubuta masa lada guda goma; izuwa
ninki xari bakwai, zuwa ninki dayawa. Idan ya himmatu zai aikata mummuna sai
kuma bai aikata ba Allah zai rubuta masa kyakkyawa guda xaya cikakke a wurinsa,
idan kuma ya aikatata to Allah zai rubuta masa mummunan aiki guda xaya”.
Bukhariy da Muslim [6491] [131] a cikin
sahihan litattafansu, da waxannan harrufan.
Ka
yi dubi, ya kai xan'uwana –Allahya datar da mu, da kai- zuwa ga girman
tausasawan Allahta'alah, kuma ka yi tunani cikin laffuzan wannan hadisin. Kuma
faxinsa (a wajensa) na yin nuni kan yadda Allah ya bada muhimmanci kan
wannan lamarin. Faxinsa kuma (cikakkiya) don qarfafawa ne, da kuma qara
bada muhimmanci. Sai faxin hadisin dangane da mummunan aikin da bawa ya yi niyyar
aikatawa, sa'annan sai ya bar aikata shi (Allah zai rubuta kyakkyawa cikakke
a wurinsa), sai hadisin ya qarfafa maganar da kalmar (cikakke). (Idan
kuma ya aikata ta, to sai ya rubuta mummuna guda xaya), a nan kuma, sai ya
qarfafi maganar don ya qarantata, ta hanyar amfani da kalmar (guda xaya),
ba da kalmar (cikakkiya) ba. Godiya da baiwa na Allah ta'alah ne, ba za
mu iya qididdige yabo ba a gare shi. Kuma datarwa na Allah ne!
الحديث الثامن والثلاثون:
عن أبي هريرة رضي الله
عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: "إِنَّ اللَّهَ تعالى قَالَ:
مَنْ عَادَى لِي وَلِيًّا فَقَدْ آذَنْتُهُ بِالحَرْبِ، وَمَا تَقَرَّبَ إِلَيَّ
عَبْدِي بِشَيْءٍ أَحَبَّ إِلَيَّ مِمَّا افْتَرَضْتُ عَلَيْهِ، وَلَا يَزَالُ
عَبْدِي يَتَقَرَّبُ إِلَيَّ بِالنَّوَافِلِ حَتَّى أُحِبَّهُ، فَإِذَا
أَحْبَبْتُهُ: كُنْتُ سَمْعَهُ الَّذِي يَسْمَعُ بِهِ، وَبَصَرَهُ الَّذِي
يُبْصِرُ بِهِ، وَيَدَهُ الَّتِي يَبْطِشُ بِهَا، وَرِجْلَهُ الَّتِي يَمْشِي
بِهَا، وَلإِنْ سَأَلَنِي لَأُعْطِيَنَّهُ، وَلَئِنِ اسْتَعَاذَنِي
لَأُعِيذَنَّهُ، وَمَا تَرَدَّدْتُ عَنْ شَيْءٍ أَنَا فَاعِلُهُ تَرَدُّدِي عَنْ
نَفْسِ المُؤْمِنِ، يَكْرَهُ المَوْتَ وَأَنَا أَكْرَهُ مَسَاءَتَهُ "،
رواه البخاري.
HADISI NA
TALATIN DA TAKWAS:
An
ruwaito daga Abu Hurairata, (R.A) yace, Manzon Allah (s.a.w) yace: Allah
ta’alah yace: “Duk wanda yayi gaba da waliyyina to na bashi sanarwa yazo
yayi yaqi da ni. Bawana ba zai kusance ni da wani abu da na fi qauna, sama da
abinda na wajabta masa. Bawana ba zai gushe ba yana kusanta ta da nafiloli har
sai na qauna ce shi, idan na qaunace shi, sai na kasance jinsa, da yake ji da
shi, da ganinsa da yake gani da shi, da hannunsa da yake damqa da shi, da
kafarsa da yake tafiya da ita. Wallahi idan ya roqe ni zan bashi, kuma wallahi
idan ya nemi tsarina zan tsare shi”, Bukhariy ne ruwaito shi (6502).
الحديث التاسع والثلاثون:
عن ابن عباس رضي الله
عنهما أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «إِنَّ اللَّهَ تَجَاوَزَ لي عَنْ
أُمَّتِي الْخَطَأَ، وَالنِّسْيَانَ، وَمَا اسْتُكْرِهُوا عَلَيْهِ»، حديث حسن
رواه ابن ماجة والبيهقي وغيرهما.
HADISI NA
TALATIN DA TARA
An
ruwaito daga xan Abbas (R.A) yace: Manzon Allah yace: “Allah ya
yafe wa al’ummata abinda ta yi da kuskure, da wanda ta yi da mantuwa, da abinda
aka tilasta su akansa”. Hadisin ne mai kyau Ibnu majah ne ya ruwaito shi (2045) da
baihaki a cikin sunan.
الحديث الأربعون:
عَنْ عَبْدِ اللَّهِ
بْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، قَالَ: أَخَذَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِمَنْكِبِي، فَقَالَ: «كُنْ فِي الدُّنْيَا
كَأَنَّكَ غَرِيبٌ أَوْ عَابِرُ سَبِيلٍ» وَكَانَ ابْنُ عُمَرَ، يَقُولُ: «إِذَا
أَمْسَيْتَ فَلاَ تَنْتَظِرِ الصَّبَاحَ، وَإِذَا أَصْبَحْتَ فَلاَ تَنْتَظِرِ
المَسَاءَ، وَخُذْ مِنْ صِحَّتِكَ لِمَرَضِكَ، وَمِنْ حَيَاتِكَ لِمَوْتِكَ»،
رواه البخاري.
HADISI NA
ARBA'IN:
An
ruwaito daga Abdullahi xan Umar (R.A) yace: Manzon Allah ya dafa kafaxata
sannan yace: “Ka kasance a duniya tamkar baqo, ko kuma wanda yake kan hanya”. Xan
Umar (R.A) ya kasance yana cewa: Idan kayi yammaci kar ka jira safiya, idan
kuma ka wayi gari to kar ka jira yammaci, ka riqi aikin alheri lokacin
lafiyarka, saboda lokacin rashin lafiyarka, ka riqi aikin alheri lokacin
rayuwarka, saboda ka amfana lokacin mutuwarka, Bukhariy ne ya ruwaitoshi.
[6416].
الحديث الحادي والأربعون:
عن أبي محمد عبد الله
بْنِ عَمْرٍو بن العاص رضي الله عنهما، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى
اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "لا يُؤْمِنُ أَحَدُكُمْ حَتَّى يَكُونَ
هَوَاهُ تَبَعًا لِمَا جِئْتُ بِهِ"، حديث حسن صحيح، رويناه في كتاب
الحجة بإسناد صحيح.
HADISI NA
ARBA'IN DA XAYA:
An
ruwaito daga Abu Muhammadu; watoAbudullahi xan Amru xan Aas (R.A) yace: Manzon
Allah (s.a.w) yace: “Xayanku ba ya zama mumini har sai son zuciyarsa tana biyayya
ga abinda nazo da shi”. Hadisin ne ingatacce, mai kyau mun ruwaito shi a cikin
littafin Hujja da isnadi ingantacce.
الحديث الثاني والأربعون:
عن أنس رضي الله عنها قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: قَالَ
اللَّهُ تَعَالَى: يَا ابْنَ آدَمَ إِنَّكَ مَا دَعَوْتَنِي وَرَجَوْتَنِي
غَفَرْتُ لَكَ عَلَى مَا كَانَ مِنكَ وَلاَ أُبَالِي.
يَا ابْنَ آدَمَ لَوْ بَلَغَتْ ذُنُوبُكَ عَنَانَ السَّمَاءِ ثُمَّ
اسْتَغْفَرْتَنِي غَفَرْتُ لَكَ، وَلاَ أُبَالِي.
يَا ابْنَ آدَمَ إِنَّكَ لَوْ أَتَيْتَنِي بِقُرَابِ الأَرْضِ خَطَايَا
ثُمَّ لَقِيتَنِي لاَ تُشْرِكُ بِي شَيْئًا لأَتَيْتُكَ بِقُرَابِهَا مَغْفِرَةً، رواه الترمذي وقال: حديث حسن صحيح.
HADISI NA
ARBA'IN DA BIYU:
An
ruwaito daga Anas xan Malik (R.A) yace: Na ji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: “Allah
maxaukakin sarki yana cewa: Ya kai xan Adam! Lallai ba zaka bauta min ba, kuma
ka sanya rai game da rahamata face na gafarta maka, ba tare da na damu ba. Ya
kai xan Adam da ace zunubanka za su cika sashen sama gabaxaya, sannan sai ka
nemi gafarata sai in gafarta maka. Ya kai xan Adam! da ace zaka zo min da cikin
qasa gabaxaya zunubi ne, sannan sai ka gamu da ni, ba tare da ka haxa ni da
kowa ba, ni kuma zan kawo maka gafara, cikin qasa”. Tirmizi
ne ruwaito shi [3540]. Yace: hadisi ne
mai kyau, ingantacce.
الحديث الثالث والأربعون:
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ
رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ، قَالَ رسول الله صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ: «أَلْحِقُوا الفَرَائِضَ بِأَهْلِهَا، فَمَا أَبْقَتِ الْفَرَائِضُ فَلِأَوْلَى
رَجُلٍ ذَكَرٍ»، خرّجه البخاري ومسلم.
HADISI NA
ARBA'IN DA UKU:
An
ruwaito daga xan Abbas (R,A) yace: Manzon Allah yace: "Ku
riskar da kowanne rabon gado sananne ga ma’abotan wannan rabon, abinda kuma ya
ragu to a baiwa namiji wanda ya fi kusanci", Bukhariy (6732) da
Muslim ne suka ruwaito shi.
الحديث الرابع والأربعون:
عن عائشة رضي الله عنها
عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «الرَّضَاعَة تُحَرِّمُ مَا تُحرِّمُ مِنَ
الوِلاَدَةِ»، خرّجه البخاري ومسلم.
HADISI NA
ARBA'IN DA HUXU:
An
ruwaito daga Aisha (R.A) tace: Manzon Allah yace: "Shayarwa
tana haramta abin da haihuwa take haramtawa". Bukhariy da Muslim
[2656] [1444] suka ruwaito shi.
الحديث الخامس والأربعون:
عَنْ جَابِرِ بْنِ
عَبْدِ اللهِ، أَنَّهُ سَمِعَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
عَامَ الْفَتْحِ وَهُوَ بِمَكَّةَ يقول: «إِنَّ اللهَ وَرَسُولَهُ حَرَّمَ
بَيْعَ الْخَمْرِ، وَالْمَيْتَةِ، وَالْخِنْزِيرِ، وَالْأَصْنَامِ»، فَقِيلَ:
يَا رَسُولَ اللهِ، أَرَأَيْتَ شُحُومَ الْمَيْتَةِ، فَإِنَّهُ يُطْلَى بِهَا
السُّفُنُ، وَيُدْهَنُ بِهَا الْجُلُودُ، وَيَسْتَصْبِحُ بِهَا النَّاسُ، فَقَالَ:
«لَا، هُوَ حَرَامٌ»، ثُمَّ قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ عِنْدَ ذَلِكَ: «قَاتَلَ اللهُ الْيَهُودَ؛ إِنَّ اللهَ حَرَّمَ
عَلَيْهِم الشُّحُوم فأَجْمَلُوهُ، ثُمَّ بَاعُوهُ فَأَكَلُوا ثَمَنَهُ»، خرّجه
البخاري ومسلم.
HADISI NA
ARBA'IN DA BIYAR:
An
ruwaito daga Jabir xan Abdullahi (R.a) yace: Naji Manzon Allah a shekarar buxe
garin Makka, a lokacin yana Makka yana cewa: "Lallai Allah da
Manzonsa sun haramta sayar da giya da mushe da alade, da gunki".
sai aka ce: Ya Manzon Allah! ba mu labari game da kitsen mushe; domin ana
shafawa a jikin jirgin ruwa, ana shafawa a fata, kuma mutane suna kunna fitilu
da shi? Sai yace: a’a wannan haramun ne. Sannan sai Manzon Allah yace: "Allah
ya la’anci yahudawa; saboda yayin da Allah ya haramta musu kitse; sai suka
narkar da shi. sannan suka sayar da shi, suka kuma cinye kuxinsa". Bukhariy
da Muslim (2236) (1581) suka ruwaito shi .
الحديث السادس والأربعون:
عَنْ أَبِي بُرْدَةَ،
عَنْ أَبِيهِ، عَنْ أَبِي مُوسَى الأَشْعَرِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، أَنَّ
النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بَعَثَهُ إِلَى اليَمَنِ، فَسَأَلَهُ
عَنْ أَشْرِبَةٍ تُصْنَعُ بِهَا، فَقَالَ: «مَا هِيَ؟» قَالَ: البِتْعُ
وَالمِزْرُ، فَقُلْتُ لِأَبِي بُرْدَةَ: مَا البِتْعُ؟ قَالَ: نَبِيذُ
العَسَلِ، وَالمِزْرُ نَبِيذُ الشَّعِيرِ، فَقَالَ: «كُلُّ مُسْكِرٍ حَرَامٌ»،
خرّجه البخاري.
HADISI NA
ARBA'IN DA SHIDA:
An
ruwaito daga xan Abu Burda daga babansa, daga Abu Musal Ash’ariy (R.A) yace:
Annabi ya tura shi qasar Yemen sai ya tambaye shi dangane da wani abin sha da
ake yi a can sai yace: menene abin? Sai yace: “ Albit’u da Almizru “ sai akace
da Abu burda menene Albit’u sai yace: Wani tsimi ne da ake yi da zuma, almizru
kuwa wani tsimi ne da ake yi da alkama. Sai Annabi yace: "Duk abu
mai sanya maye haramun ne", Bukhariy ne ruwaito shi. [4343].
الحديث السابع والأربعون:
عن الْمِقْدَامَ بْنَ مَعْدِي كَرِبَ، قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: "مَا مَلَأَ آدميٌّ وِعَاءً شَرًّا مِنْ
بَطْنٍ، بحَسب ابْنِ آدَمَ أُكُلَاتٌ يُقِمْنَ صُلْبَهُ، فَإِنْ كَانَ لَا
مَحَالَةَ، فَثُلُث لطَعَامه، وَثُلُثٌ لشَرَابه، وَثُلُثٌ لِنَفْسِهِ"، رواه أحمد والترمذي والنسائي وابن ماجه، وقال
الترمذي: حديث حسن.
HADISI NA
ARBA'IN DA BAKWAI:
An ruwaito daga Miqdamu xan Ma’adi Yakrib
(R.A) yace: Naji Manzon Allah yana cewa: "Xan Adam
bai tava cika wani masaki ba wanda yafi sharri, sama da cikinsa. Ya ishi xan
Adam, waxansu yan lomomi wanda za su tsaida gadon bayansa, Idan dole sai ya ci
abinci da yawa sai ya kasa cikinsa kashi uku, kashi xaya na abincinsa, kashi
biyu na ruwa, kashi xayan kuma ya bar shi wa numfashinsa".
Ahmad da Tirmiziy da Nasa'iy da Ibnu majah.Tirmiziy yace: Hadisi ne mai kyau.
الحديث الثامن والأربعون:
عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ
عَمْرٍو رضي الله عنهما، عن النبي صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
"أَرْبَعٌ مَنْ كُنَّ فِيهِ كَانَ مُنَافِقًا، وَإنْ كَانَتْ خصلةٌ مِنْهُنَّ
كَانَتْ فِيهِ خَصلةٌ مِنْ النّفَاقٍ حَتَّى يَدَعَهَا؛ إِذَا حَدَّثَ كَذَبَ، وَإِذَا
وَعَدَ أَخْلَفَ، وَإِذَا خَاصَمَ فَجَرَ، وَإِذَا عَاهَدَ غَدَرَ"، خرّجه
البخاري ومسلم.
HADISI NA
ARBA'IN DA TAKWAS:
An
ruwaito daga Abdullahi xan Amru (R.A) daga Annabi (s.a.w) yace: “Abubuwa guda
huxu wanda suka kasance tare da shi ya kasance munafiqi, wanda kuma siffa xaya
ta kasance tare sa shi to yana da siffar munafirci; a tattare da shi; har sai
ya bar ta; Idan zai yi magana yayi qarya. Idan yayi alkwari sai ya sava. Idan
anyi rigima da shi, sai ya qetare dokar Allah, Idan kuma aka qulla alkawari da
shi sai ya yaudare ka. Bukhariy da Muslim, [34] [ 58] suka ruwaito shi.
الحديث التاسع والأربعون:
عن عُمَرَ بْنَ
الْخَطَّابِ رضي الله عنه عن النبيّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قال: "لَوْ
أَنَّكُمْ كُنْتُمْ تَوَكَّلُونَ عَلَى اللهِ حَقَّ تَوَكُّلِهِ، لَرَزَقَكُمْ
كَمَا يَرْزُقُ الطَّيْرَ، تَغْدُو خِمَاصًا وَتَرُوحُ بِطَانًا"، رواه
الإمام أحمد والترمذي والنسائي وابن ماجه وابن حبان في صحيحه والحاكم، وقال
الترمذي: حديث حسن صحيح.
HADISI NA
ARBA'IN DA TARA:
An
ruwaito daga Umar xan Khaxxab (R.A) daga Annabi yace: "Da
ace za ku dogara ga Allah haqiqanin dogaro da Allah ya azurta ku, kamar yadda
ya ke azurta tsuntsaye, suna sammako da yunwa, amma sai su dawo da yamma suna
qoshe". Imam Ahmad da Tirmiziy da Nasa’i da Ibnu-Majah, da
Ibnu Hibban a cikin sahihnsa, da Hakim. Tirmiziy yace:, Hadisi ne mai kyau
ingantacce.
الحديث الخمسون:
عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ
بُسْرٍ، قَالَ: أَتَى النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رجلٌ، فَقَالَ:
إِنَّ شَرَائِعَ الْإِسْلَامِ قَدْ كَثُرَتْ عَلَيْنَا، فَبَابٌ نَتَمَسَّكُ بِهِ
جَامِعٌ؟ قَالَ: "لَا يَزَالُ لِسَانُكَ رَطْبًا
مِنْ ذِكْرِ اللهِ عز وجل"، رواه
الإمام أحمد بهذا اللفظ، وخرّجه الترمذي وابن ماجه وابن حبان في صحيحه بمعناه،
وقال الترمذي: حديث حسن غريب.
HADISI NA HAMSIN
An
ruwaito daga Abdullahi dan Busur, (R.A) yace: Wani mutum (mazaunin karkara ) ya
zo wurin Annabi (s.a.w) yace: Ya Manzon Allah! shari’oi sun yi mana yawa; a
bamu wani babi gamamme da zamu riqe. Sai Annabi yace "Kada
harshenka ya bushe wajen anbaton Allah". Ahmad ne ya ruwaito shi
[188, 190] da wannan lafazin, kuma Tirmiziy da Ibnu-Majah, da IbnuHibbana a
cikin sahihinsa da ma'anarsa, Tirmiziy yace: hadisi ne hasan garib.
No comments:
Post a Comment