LADDUBAN CIN ABINCI A MUSULUNCI:
Lallai addinin musulunci ya zo mana da ladduba masu muhimmanci a lokacin da musulmi ya yi niyyar cin abinci, ko yake tsakiyar ci, ko bayan ya kammala, ga bayaninsu kamar haka:
1. Faxin "bismillah" a lokacin fara cin abinci:
Wannan kuma saboda hadisin Umar xan
Abiy-salamah (RA) yace: Na kasance yaro qarqashin
kulawar Manzon Allah –r-
kuma hannuna ya kasance yana yawo a cikin akwashin abinci, sai yace:
"يَا غُلاَمُ! سَمِّ اللَّهَ، وَكُلْ بِيَمِينِكَ،
وَكُلْ مِمَّا يَلِيك. فَمَا زَالَتْ تِلْكَ طِعْمَتِي بَعْد"([1]).
Ma'ana: (Ya kai yaro! Ka ambaci sunan Allah, ka ci da hannunka
na dama, ka kuma ci daga abinda ke gabanka. –Jabir yace:- Daga wannan lokacin
ban gushe ba; wannan ne irin cin abincina).
2.
Cin abinci da hannun dama:
Wannan kuma sunna ne saboda hadisin da ya gabata.
- Mutum ya ci gabansa: Shima
wannan sunna ne saboda hadisin da ya gabata. Sai dai idan mutum ya san
cewa mutumin da suke cin abinci tare ba zai cutu ko kyamaci yawo da hannu
a cikin kwaryar abincin ba, to a nan babu laifi idan ya ci daga ko-ina na
kwano; saboda hadisin Anas (RA) a qissar
"telan nan da ya gayyaci Manzon Allah (r) i zuwa ga wani abinci"
Anas yace:
"فَرَأَيْتُهُ –يعني النبي r- يَتَتَبَّعُ الدُّبَّاءَ مِنْ حَوَالَيِ القَصْعَة"([2]).
Ma'ana: (Sai na ganshi –yana nufin: Annabi r-
yana bibiyan kabewa daga geffan kwano).
Ko kuma idan mutum ya kasance yana cin abincin ne shi kaxai;
babu wani a tare da shi, ko kuma abincin akwai launukan abubuwan ci da dama; a
irin wannan halin ya halatta ya ci abincin da ke gaban waninsa; matuqar
dai bai cutar da wani da hakan ba.
- Cin abinci akan ledar cin
abinci (Sufurah): Wannan kuma saboda hadisin
Anas xan
Malik (RA) yace:
"مَا أَكَلَ نَبِيُّ الله r
عَلَى خِوَانٍ، وَلاَ فِي سُكُرُّجَةٍ، وَلاَ خُبِزَ لَهُ مُرَقَّقٌ.
قال: فقُلْتُ لِقَتَادَةَ: فعَلاَمَ كانوا
يَأْكُلُونَ؟ قَالَ:
عَلَى هذه السُّفَرِ"([3]).
Ma'ana: (Annabin Allah –r- bai tava
cin abinci a kan "khiwaan([4])",
ko a kan "Sukurrujah([5])"
ba, haka kuma ba a tava yi masa al-khubuz mai laushi ba. Yace, sai nace wa Qatadah:
To, a kan me suka kasance suke cin abinci? Sai yace: A kan waxannan
"sufurori([6]);
-ledodin cin abinci").
- Makruhi ne cin abinci a kishingixe: Wannan
kuma saboda hadisin A'ishah (RA) tace:
"قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، كُلْ -جَعَلَنِي اللَّهُ فِدَاكَ- مُتَّكِئًا؛ فَإِنَّهُ أَهْوَنُ عَلَيْكَ، فَأَصْغَى
بِرَأْسِهِ حَتَّى كَـادَ أَنْ
تُصِيبَ جَبْهَتُهُ
الأَرْضَ، قَالَ: لا، بَلْ آكُلُ كَمَا يَأْكُلُ الْعَبْدُ، وَأَجْلِسُ كَمَا يَجْلِسُ
الْعَبْد"([7]).
Ma'ana: (Nace: ya ma'aikin Allah! Ka ci abinci –Allah ya
sanya ni na zamo fansarka- a halin kishingixa;
saboda zai fiye maka sauqi, Sai manzon Allah –r- ya karkata kansa har sai da goshinsa ya yi
kusan tava qasa, sai yace: A'a! zan ci
abinci ne kamar yadda bawa ke cin abinci, zan kuma zauna kamar yadda bawa ke
zaunawa). Da kuma saboda hadisin Abu-juhaifah (RA) yace: Manzon Allah (r) yace:
"إِنِّي لا آكُلُ مُتَّكِئًا"([8]).
Ma'ana: (Lallai ni bana cin abinci a kishingixe).
- Mustahabbi ne hanuwa daga aibata
abincin da mutum baya son cinsa: Wannan
kuma saboda hadisin Abu-hurairah (RA) yace:
"مَا عَابَ رَسُولُ اللَّهِ r
طَعَامًا قَطُّ، إِنِ اشْتَهَاهُ أَكَلَهُ، وَإِلا تَرَكَه"([9]).
Ma'ana: (Manzon Allah –r- bai tava
aibanta abinci ba; idan ya yi sha'awarsa sai ya ci, in kuma bai yi ba, sai ya
bari).
- Mustahabbi ne cin abinci daga
geffan masaki, makruhi ne kuma cinsa daga tsakiyar kwarya: Wannan
kuma saboda hadisin Ibnu-abbas (RA), daga Annabi (r) lallai shi an zo masa da
masaki da aka sanya kwavavviyar
gurasa (alkubuz)
da nama mai suna (Sarid), Sai yace:
"كُلُوا مِنْ جَوَانِبِهَا، وَلا تَأْكُلُوا مِنْ
وَسَطِهَا؛ فَإِنَّ الْبَرَكَةَ تَنْزِلُ فِي وَسَطِهَا"([10]).
Ma'ana: (Ku ci daga geffan masakin, kada ku ci daga
tsakiyansa, saboda albarka tana sauka ne a tsakiyarsa).
- Mustahabbi ne cin abinci da
yatsu guda uku, da kuma suxe
yatsun bayan kammalawa: Wannan
kuma saboda hadisin Ka'ab xan
Malik (RA) yace:
"كَانَ النَّبِيُّ r يَأْكُلُ بِثَلاثَةِ أَصَابِعَ، وَلا
يَمْسَحُ يَدَهُ حَتَّى يَلْعَقَهَا"([11]).
Ma'ana: (Annabi –r- ya
kasance yana cin abinci da 'yan yatsunsa guda uku, baya kuma goge hannunsa har
sai ya suxe su).
- Mustahabbi ne cinye abinda ya
zuba ana tsakiyan cin abinci, ko wanda ya warwatsu: Wannan
kuma saboda faxinsa (r):
"إِذَا سَقَطَتْ لُقْمَةُ أَحَدِكُمْ فَلْيُمِطْ
عَنْهَا الأَذَى وَلْيَأْكُلْهَا، وَلا يَدَعْهَا لِلشَّيْطَان"([12]).
Ma'ana: (Idan lomar xayanku
ta faxi
to sai ya kaxe mata kura, sannan ya cinye ta, kada ya barta ga shexan).
- Mustahabbi ne suxe
kwaryar da aka ci abinci, da kuma lashe yatsu: Wannan
kuma saboda faxin Anas
(RA) a cikin hadisin da ya gabata:
"وَأَمَرَنَا –يعني النبي r- أَنْ نَسْلُتَ الْقَصْعَة"([13]).
Ma'ana: (Kuma ya umurce mu –yana nufin Annabi r-
da mu katse kwaryar abinci). Ma'ana: mu suxe ta, mu
kuma bibiyi abinda ya rage a cikinta na abinci. A wata riwayar kuma aka ce:
Annabi –r-
ya umurce mu da mu suxe 'yan yatsu da kuma akwashi, yace:
"إِنَّكُمْ لا تَدْرُونَ فِي أَيِّه الْبَرَكَة"([14]).
Ma'ana: (Saboda lallai ku ba ku san a ina ne daga cikin
abincinku albarkar ta ke ba!).
- Faxin
"alhamdu lillah" a qarshen
abinci:
Saboda
hadisin Abu-umamah (RA) yace: Manzon Allah (r) ya kasance idan aka xage
akwashin abinci –bayan kammala cinsa- daga gaba-gare shi Sai yace:
"الْحَمْدُ لِلَّهِ حَمْدًا كَثِيرًا طَيِّبًا مُبَارَكًا
فِيهِ, غَيْرَ مُوَدَّعٍ, وَلا مُسْتَغْنًى عَنْهُ رَبَّنَا"([15]).
Ma'ana: (Yabo mai yawa daddaxa
mai albarka sun tabbata ga Allah, Allah Ubangijinmu ba a barin yi masa xa'a,
ko kuma ace an wadata ga barinsa). Da kuma saboda faxinsa
(r):
"إِنَّ اللهَ لَيَرْضَى عَنِ الْعَبْدِ أَنْ يَأْكُلَ
الأَكْلَةَ فَيَحْمَدَهُ عَلَيْهَا، أَوْ يَشْرَبَ الشَّرْبَةَ فَيَحْمَدَهُ عَلَيْهَا"([16]).
Ma'ana: (Lallai Allah yana yarda da bawa, idan ya ci abinci
ya gode masa akanta, ko ya sha abun sha ya gode masa akansa).
([5]) "Sukurrujah"; Masaki ne qarami da ake
sanya miya kaxan don a ci
a cikinsa.
Itama wannan kalma ce ta "farisanci".
La'alla
abinda ya sanya Manzon Allah (r) ya qi ya ci a
cikin "khiwaan" saboda kasancewarta daga al'adan "ajamawa",
da ke kasancewa a kan wani hali aiyananne.
Kuma
la'alla wannan sababin shi ya hana shi ya ci a cikin masakin
"sukurrujah".
No comments:
Post a Comment