WAXANDA ALLAH ZAI SANYA SU
A QARQASHIN INUWARSA RANAR DA BABU WATA SAI TASA
Daga
Abu-hurairah (Allah ta'alah ya yarda da shi) daga Annabi (tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi) cewa:
"سَبْعَةٌ
يُظِلُّهُمُ اللهُ فِي ظِلِّهِ يَوْمَ لَا ظِلَّ إِلَّا ظِلُّهُ: الْإِمَامُ
الْعَادِلُ، وَشَابٌّ نَشَأَ بِعِبَادَةِ اللهِ، وَرَجُلٌ قَلْبُهُ مُعَلَّقٌ فِي
الْمَسَاجِدِ، وَرَجُلَانِ تَحَابَّا فِي اللهِ اجْتَمَعَا عَلَيْهِ وَتَفَرَّقَا
عَلَيْهِ، وَرَجُلٌ دَعَتْهُ امْرَأَةٌ ذَاتُ مَنْصِبٍ وَجَمَالٍ، فَقَالَ: إِنِّي
أَخَافُ اللهَ، وَرَجُلٌ تَصَدَّقَ بِصَدَقَةٍ فَأَخْفَاهَا حَتَّى لاَ تَعْلَمَ شِمَالُهُ مَا تُنْفِقُ يَمِينُهُ،
وَرَجُلٌ ذَكَرَ اللهَ خَالِيًا فَفَاضَتْ عَيْنَاهُ".
Ma'ana:
"Vangarori guda bakwai
Allah zai sanya su a inuwarsa ranar da babu wata inuwa sai tasa; Shugaba adali,
da Saurayin da ya rayu cikin bautar Allah, da Mutumin zuciyarsa a rataye ta ke
da masallatai, da Mutane biyu da suka yi soyayya don Allah, suka haxu akan haka, suka kuma rabu akan haka, da Mutumin da mace
ma'abociya matsayi da kyau ta kira shi don yin lalata sai yace: Lallai ni ina
tsoron Allah, da Mutumin da ya bada wata sadaka; ya voye ta; hatta hagunsa bai
san abinda damanya ya bayar ba, da Mutumin da ya ambaci Allah a keve sai
idanunsa guda biyu suka yi hawaye". [Littafin sahihul Bukhariy, lamba:
660, da Sahihu Muslim, lamba: 1031].
Allah ta'alah kawai muke roqo da ya sanya mu daga cikin waxanda a ranar tashin alkiyamah zasu rabauta da kasancewa
qarqashin inuwarSa, ranar da babu wata inuwa sai tasa. Ya
kuma taimake mu wajen aiki da wannan hadisi, ta kowace fiska. Amin!
No comments:
Post a Comment