2015/05/11

AIYUKAN SHUGABANNI

MANYAN AIYUKAN SHUGABANNI GUDA GOMA

A littatafanmu na musulunci anyi bayanin aiyukan da suke kan shugaba, da kuma alhakin da ke rataya a wuyansa, Daga cikinsu akwai abinda ya zo cikin littafin "AL-AHKAM AS-SULXANIYYAH na malamin nan da ya rasu kusan shekaru dubu baya; mai suna: Abul hasan Aliyu bn Muhammadu Al-mawardiy (marigayi a shekarar hijira ta 450)" A inda yake cewa:
 "مهام الخليفة ومسئولياته": وَاَلَّذِي يَلْزَمُهُ مِنَ الْأُمُورِ الْعَامَّةِ عَشَرَةُ أَشْيَاءَ:
"AIYUKAN SHUGABA, DA ABUBUWAN DA SUKE RATAYA A WUYANSA: Lallai lamuran da suke wajaba akansa na gamammun aiyuka: Abubuwa ne guda goma", Sai yace: 
أَحَدُهَا: حِفْظُ الدِّينِ عَلَى أُصُولِهِ الْمُسْتَقِرَّةِ، وَمَا أَجْمَعَ عَلَيْهِ سَلَفُ الْأُمَّةِ، فَإِنْ نَجَمَ مُبْتَدِعٌ أَوْ زَاغَ ذُو شُبْهَةٍ عَنْهُ، أَوْضَحَ لَهُ الْحُجَّةَ، وَبَيَّنَ لَهُ الصَّوَابَ، وَأَخَذَهُ بِمَا يَلْزَمُهُ مِنَ الْحُقُوقِ وَالْحُدُودِ؛ لِيَكُونَ الدِّينُ مَحْرُوسًا مِنْ خَلَلٍ، وَالْأُمَّةُ مَمْنُوعَةً مِنْ زَلَلٍ.
Ma'ana: "NA XAYA: Kiyaye addinin mutane, akan ginshiqansa tabbatattu, da kuma abinda magabatan wannan al'ummar suka yi ittifaqi akansa –ijma'i-. Idan wani xan bidi'a ya vullo, ko kuma ma'abocin wata shubuha ya karkata ga barin miqaqqen addini to sai shugaba ya fitar masa da hujja a fili, ya kuma bayyana masa gaskiya. Sa'annan in ta kama sai ya kwato haqqoqin da suke wurinsa, ko ya zartar masa da haddin da ya cancanta, saboda a kiyaye wa mutane addininsu daga tasgaro, al'umma kuma a hane ta, kauce masa". Ya ci gaba da cewa: 
الثَّانِي: تَنْفِيذُ الْأَحْكَامِ بَيْنَ الْمُتَشَاجِرِينَ، وَقَطْعُ الْخِصَامِ بَيْنَ الْمُتَنَازِعِينَ حَتَّى تَعُمَّ النَّصَفَةُ، فَلَا يَتَعَدَّى ظَالِمٌ، وَلَا يَضْعُفُ مَظْلُومٌ.
"NA BIYU: Zartar da hukunce-hukunce tsakanin vangarori biyu da suke faxa, da yanke husumar da ta shiga tasakanin masu jayayya, har adalci ya game kowa-da-kowa, ta yadda mai zalunci ba zai wuce iyaka ba, Wanda kuma aka zalunta ba zai yi rauni (wajen neman haqqoqinsa) ba". Ya ci gaba da cewa:
الثَّالِثُ: حِمَايَةُ الْبَيْضَةِ وَالذَّبُّ عَنِ الْحَرِيمِ؛ لِيَتَصَرَّفَ النَّاسُ فِي الْمَعَايِشِ، وَيَنْتَشِرُوا فِي الْأَسْفَارِ آمِنِينَ مِنْ تَغْرِيرٍ بِنَفْسٍ أَوْ مَالٍ.
"NA UKU: Kiyaye iyaka, da kare abun da aka hana, domin mutane su samu sake cikin rayuwarsu, su kuma watsu cikin tafiye-tafiyensu da aminci, ba tare da an ruxe su cikin rayukansu, ko kuma a cikin dukiya ba". Ya ci gaba da cewa:
وَالرَّابِعُ: إقَامَةُ الْحُدُودِ؛ لِتُصَانَ مَحَارِمُ اللَّهِ تَعَالَى عَن الِانْتِهَاكِ، وَتُحْفَظَ حُقُوقُ عِبَادِهِ مِنْ إتْلَافٍ وَاسْتِهْلَاكٍ.
"NA HUXU: Tsayar da haddodi; domin a kare abubuwan da Allah ta'alah ya haramta daga keta alfarmarsu, a kuma kiyaye haqqoqin bayinsa daga lalata su, ko halaka su". Sannan yace:
وَالْخَامِسُ: تَحْصِينُ الثُّغُورِ بِالْعُدَّةِ الْمَانِعَةِ وَالْقُوَّةِ الدَّافِعَةِ؛ حَتَّى لَا تَظْفَرَ الْأَعْدَاءُ بِغِرَّةٍ يَنْتَهِكُونَ فِيهَا مُحَرَّمًا، أَوْ يَسْفِكُونَ فِيهَا لِمُسْلِمٍ أَوْ مُعَاهَدٍ دَمًا.
"NA BIYAR: Sanya garkuwa a dukkan kafafe ko iyakoki da nau'ukan tsaro da za su hana shigowar maqiya ko su tunkuxe su bayan shigowarsu, Wannan kuma don kada maqiyan a cikin gafalar mutane su samu su kekketa alfarmar abubuwa na haram, ko kuma su zubar da jinin musulmi ko kafirin aman". ya ci gaba da cewa:
وَالسَّادِسُ: جِهَادُ مَنْ عَانَدَ الْإِسْلَامَ بَعْدَ الدَّعْوَةِ حَتَّى يُسْلِمَ أَوْ يَدْخُلَ فِي الذِّمَّةِ؛ لِيُقَامَ بِحَقِّ اللَّهِ تَعَالَى فِي إظْهَارِهِ عَلَى الدِّينِ كُلِّهِ.
"NA SHIDA: Yaqar mutumin da ya yi taurin kai ga musulunci bayan an kira shi zuwa gare shi har sai ya musulunta ko kuma ya shiga cikin kafiran amana, Wannan kuma don a tsayar da haqqin Allah ta'alah, na cewa zai xaukaka musulunci akan addinai gabaxayansu". Ya ci gaba da cewa:
وَالسَّابِعُ: جِبَايَةُ الْفَيْءِ وَالصَّدَقَاتِ عَلَى مَا أَوْجَبَهُ الشَّرْعُ نَصًّا وَاجْتِهَادًا، مِنْ غَيْرِ خَوْفٍ وَلَا عَسْفٍ.
"NA BAKWAI: Tattara ganima da zakka, kamar yadda shari'a ta wajabta, qarara, ko da ijtihadi, ba tare da tsoro ba, ko zalunci". Ya ci gaba da cewa:
وَالثَّامِنُ: تَقْدِيرُ الْعَطَايَا وَمَا يَسْتَحِقُّ فِي بَيْتِ الْمَالِ مِنْ غَيْرِ سَرَفٍ وَلَا تَقْتِيرٍ، وَدَفْعُهُ فِي وَقْتٍ؛ لَا تَقْدِيمَ فِيهِ وَلَا تَأْخِيرَ.
"NA TAKWAS: Yanka gwargwadon kyautuka, da duk abin da aka cancanta na dukiya daga baitul mali, ba tare da wuce iyaka ko mammaqo ba, da bada shi ga waxanda suka cancance shi a cikin lokacinsa; babu gaggawa, kuma babu jinkiri". Ya ci gaba da cewa:
التَّاسِعُ: اسْتِكْفَاءُ الْأُمَنَاءِ وَتَقْلِيدُ النُّصَحَاءِ؛ فِيمَا يُفَوَّضُ إلَيْهِمْ مِنَ الْأَعْمَالِ، وَيَكِلُهُ إلَيْهِمْ مِنَ الْأَمْوَالِ؛ لِتَكُونَ الْأَعْمَالُ بِالْكَفَاءَةِ مَضْبُوطَةً، وَالْأَمْوَالُ بِالْأُمَنَاءِ مَحْفُوظَةً.
"NA TARA: Neman ma'aikatan da suka dace kuma aminai, da rataya aiyuka ga waxanda za su kyautata shi, ga duk aiyukan da zai xora ga wassu, ko ya wakilci da zai bayar na dukiya, Wannan kuma domin aiyuka su zamto an rataya su ga waxanda za su iya aikata su, dukiya kuma ga aminan da za su iya kiyaye su". Ya ci gaba da cewa:
الْعَاشِرُ: أَنْ يُبَاشِرَ بِنَفْسِهِ مُشَارَفَةَ الْأُمُورِ، وَتَصَفُّحَ الْأَحْوَالِ؛ لِيَنْهَضَ بِسِيَاسَةِ الْأُمَّةِ، وَحِرَاسَةِ الْمِلَّةِ، وَلَا يُعَوِّلُ عَلَى التَّفْوِيضِ تَشَاغُلًا بِلَذَّةٍ أَوْ عِبَادَةٍ، فَقَدْ يَخُونُ الْأَمِينُ وَيَغُشُّ النَّاصِحُ"
"NA GOMA: Ya rinqa dubiyar dukkan lamura da kansa, yana bincika halayen da lamura suke ciki, domin ya tsayu da kansa wajen jagorantar al'umma, da kare musu addini. Kada kuma ya yarda da wakiltawa ko-yaushe, saboda neman hutun jin daxi, ko shagaltuwa da wata ibada; saboda ta yiwu wanda aka aminta das hi ya yi ha'inci, ko wanda aka san shi da aiki mai kyau wata rana ya yi algus".
          Daga qarshe muna yin fatan alkhairi ga shugabanni, muna kuma roqon Allah ya taimake su kan sauke dukkan nauyin da yarata akansu, amin!. Salati da sallama su qara tabbata ga manzon Allah annabinmu Muhammadu da da iyalansa da sahabbansa gabaxaya.

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...