TA YAYA MA AIKACI ZAI SAUKE AMANA?!
(كيف يؤدِّي الموظَّفُ الأمانةَ)
(Hanyoyin da ma'aikaci zai bi wajen sauke nauyin dake
kansa!)
NA
AS-SHEIKH ABDUL-MUHSIN BN HAMD AL-ABBAD
Allah ya kara datar da
shi, ya kuma taimake shi
Fassarar:
Abubakar Hamza
ABUBUWAN DA SUKE CIKIN LITTAFIN
|
SHAFI
|
Abubuwan da suke cikin littafin
|
2
|
Gabatarwa
|
3
|
AYOYI MASU KARAMCI DA SUKE MAGANA KAN SAUKE AMANA
|
3
|
|
|
HADISAI DAGA MANZON ALLAH ( S A W ) KAN BADA AMANA
|
5
|
|
|
MA'AIKACI YAYI AIKINSA DA KWAZO DA KUMA IKHLASI, ZA A BASHI
LADANSA A DUNIYA DA LAHIRA:
|
7
|
|
|
KIYAYE LOKACIN DA AKA KEBE MA AIKI DON AIKATA ABINDA ZAI BUNKASA
AIKIN:
|
8
|
|
|
ABIN LURA WAJEN ZABEN MAI KWADAGO DA MA'AIKATA
|
9
|
|
|
MANYAN MA'AIKATA ABIN KOYI NE = WAJEN KWAZO KO KASALA GA
KANANANSU
|
11
|
|
|
MU'AMALANTAR MA'AIKACI GA WANINSA DA IRIN ABINDA YAKE SON A
MU'AMALANCE SHI DA SHI
|
12
|
|
|
MA'AIKACI YA GABATAR DA WANDA YA RIGA ZUWA SAI WANDA KE BIYE,
DAGA MABUKATA (MAZOWA WURINSA)
|
14
|
|
|
SIFFANTUWAR MA'AIKACI DA SIFFAR KAMEWA TARE DA KUBUTA KO BARIN CIN
RASHAWA, DA NIISANTAR KARBAR KYAUTA
|
15
|
|
|
|
|
بسم الله الرحمن الرحيم
Malam a farkon littafinsa –bayan yayi bismillah– Sai yace:
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai, Yabo da aminci
cikakku guda biyu sun tabbata ga shugaban Manzanni kuma jagoran masu tsoron
Allah, Annabinmu Muhammad da kuma Iyalansa da Sahabbansa da wadanda suka bi su
da kyautatawa har zuwa ranar sakamako. Bayan haka:
Wannan takarda ce karama da na rubuta don yin nasiha
wa ma'aikata; da fatan su sauke tare da aiwatar da abinda aka rataya a wuyansa
na aiki ta fiskar da ta dace, Lallai na rubuta ta da fatan ma'aikatan su amfana
da ita, haka; don ta taimake su wajen gyara niyyarsu, da kuma kokari cikin
aikinsu da kuma tsayuwa wajen aikata wajibinsu.
Ina kuma rokon Allah ta'alah aikata daidai da dacewa,
gare mu gaba daya.
AYOYI MASU KARAMCI DA SUKE MAGANA KAN SAUKE AMANA:
Daga cikin ayoyin da suke magana kan sauke/ kiyaye
amana da barin ha'inci:
}إنَّ
الله يأمرُكم أنْ تُؤدُّا الأمانات إلى أهلها وإذا حكمتم بين الناس أنْ تحكموا
بالعدل إنَّ الله نعمّا يعِظكم به إنَّ الله كان سميعًا بصيرًا{النساء: ٥٨
Ma'ana:
"Lallai Allah yana umurtarku da ku bada amanoni zuwa ga ma'abotansu, kuma idan za kuyi hukunci
tsakanin mutane ku yi hukunci da adalci, lallai Allah madalla da abinda yake
muku umurni da shi, lallai Allah ya kasance mai ji ne mai gani" [Nisa'i:
58].
Ibn
kasir ya fada a tafsirinsa: (Allah) madaukaki ya bada labarin cewa lallai shi
yayi umarnin bada amanoni zuwa ga ma'abotansu, ya zo cikin hadisin Alhasan bn
samurah lallai manzon Allah (s.a.w) yace:
((أدِّ الأمانة إلى مَن
ائتمنك، ولا تخنْ مَن خانك)).
Ma'ana:
ka mayar da amana zuwa ga wanda ya baka amana, kuma kada ka ha'inci wanda ya
ha'inceka''. Imamu Ahmad da ma'abota littafin "sunan" ne suka ruwaito
shi.
Wannan kuma ya game dukkan amanoni na wajibi akan
mutum na daga hakkokin Allah mai
girma da daukaka akan bayinsa; na sallah da zakka da azumi da kaffarori da kuma
bakance, da wassun haka, daga cikin abinda Allah ya bawa mutum amana, kuma bayi
basa tsinkaya akansa (ganinsa).
Da
kuma hakkokin
bayi sashinsu zuwa ga sashe; kamar jingina da wassunsa wadanda mutane ke bada
amanarsa ba tare da sun tsinkayar da shaidu ba akan haka;
Sai
Allah mai girma da daukaka ya yi umurni da a bada shi, duk kuma wanda bai
aikata haka ba a duniya to za'a dauka daga wajensa ranar kiyama".
Da kuma saboda fadinsa madaukaki:
}يا
أيُّها الذين ءامنوا لا تخونوا الله والرسول وتخونوا ءماناتكم وأنتم تعلمون{
[ الأنفال: ٢٧ ].
Ma'ana: "Ya ku wadanda suka yi imani kada ku
ha'inci Allah da wannan Manzon, kuma ku ha'inci amanoninku alhalin kuna sani"
[Anfaal: 27].
Ibn
kasir yace: Shi kuma ha'incin ya game dukkan zunubai; manyansu da kananansu, wadanda
suka takaita (ga mutum) da wadanda suka tsallake shi zuwa ga waninsa, Aliyu bn
Abiy Dalhatu yace daga ibn Abbas (r.a):
"وتخونوا
أماناتكم ": الأمانة التي ائتمن الله عليها العباد".
Ma'ana
sai ku ha'inci amanoninku" na nufin: amanonin da Allah ya nemi bayi su
bayar, wato : farillai, yana cewa kada ku ha'inci =kada ku warware su.
A
wata riwayar kuma ya ce:
"لا تخونوا الله
والرسول" يقول: يترك سنته وارتكاب معصيته".
Ma'ana:
kada ku ha'inci Allah da wannan Manzon) da barin sunnoninsa da kuma fadawa
cikin sabonsa"
Da kuma fadin (Allah) Madaukaki:
}إنَّا
عرضنا الأمانة على السماوات والأرض والجبال فأبَيْنَ أنْ يحمِلنَها وأشفقنَ منها
وحملها الإنسان إنَّه كان ظلوماً جهولاً{ [ الأحزاب: ٧٢ ]
Ma'ana:
(Lallai mune muka bijiro da amana ga sammai da kassai da duwatsu sai suka ki
daukarta, suka kuma tsorata daga gareta, Sai shi kuma mutum ya dauke ta, lallai
shi ya kasance mai yawan zalunci ne, mai yawan jahilci"[Ahzaab: 72].
Ibn-kasir
yace- bayan ya ambaci zantuttukan maluma da maganganunsu kan tafsirin "amana";
Wanda daga cikinsu akwai:
1-
Biyayya da da'a
2-Farillai
3-Addini
4-Haddi
mabanbanta.
Sai yace: " Duk kan wadannan maganganu
wani baya goge wani; saboda dukkansu sun yi ittifaki, kuma suna komawa zuwa ga
taklifi da karbar umarni da hani tare da sharadinsa;- wanda shine: Duk kuma wanda
ya tsayu wajen haka to za'a bashi lada akai. Idan kuma ya bar hakan a hora shi;
Sai mutum ya karbe shi -tare da rauninsa da jahilcinsa da zaluncinsa; In banda wanda Allah ya datar da shi, Allah ne kawai
abin taimako).
Da kuma fadin Allah madaukaki:
}والذين
هم لأماناتهم وعهدِهم راعون{. [ المؤمنون: 8]
Ma'ana:
sune wadanda dangane da amanoninsu da alkawarinsu masu lura ne" [Muminuna:
8].
Ibn-kasir
yana cewa :"In an basu amana basa ha'inta, idan akayi alkawari dasu kuma
basa sabawa, wannan kuma shine siffofin muminai; kamar yadda ya zo cikin hadisi
ingantacce:
"آية المنافق
ثلاث: إذا حدَّث كذب, وإذا وعد أخلف, وإذا ائتمن خان" وفي رواية: إذا حدث كذب,
وإذا عاهد غدر, وإذا خاصم فجر".
Ma'ana:
alamomin munafuki guda uku ne: idan yayi zance sai yayi karya, idan yayi
alkawari kuma sai ya saba, sannan idan aka bashi amana sai yayi ha'inci''.
A
wata riwayar kuma: "Idan yayi magana sai yayi karya, idan yayi alkawari
kuma sai ya ki cikawa, haka kuma idan yayi kusuma (fada sai aka raba su) sai ya
fajirce".
HADISAI
DAGA MANZON ALLAH ( S A W ) KAN BADA AMANA
Daga cikin hadisai daga Manzon Allah ( s
a w ) kan kiyaye amana, da kuma hani kan tozartata:
Na daya: Daga Abu-hurairah (r a) Lallai yace:
"بينما النبي r
في مجلس يحدث القوم, جاءه أعرابي فقال: متى الساعة؟ فمضى رسول الله r
يحدث, فقال بعض القوم: سمع ما قال فكره ما قال, وقال بعضهم: بل لم يسمع, حتى إذا
قضى حديثه, قال: أين أُراه السائل عن الساعة؟ قال: ها أنا يا رسول الله, قال:
فإذا ضُيّعت الأمانة فانتظر الساعة, قال: إضاعتها؟ قال إذا وسد الأمر إلى غير أهله
فانتظر الساعة" رواه البخاري. (59).
Ma'ana: "Wata rana Annabi (s a w) yana wani
majlisi yana bada hadisi wa mutane sai wani balaraben kauye ya zo; yace: Yaushe
ne tashin kiyama?! Sai Manzon Allah (s a w) ya ci gaba da bada hadisinsa; Sai wassu daga
cikin mutanen suka ce: ya ji abinda ya fada sai kuma ya kyamace shi (ya ki), Wassun
kuma suka ce: a'a; annabi bai ji ba.
Bayan
ya gama hadisinsa sai yace: '' Ina zan ga mai tambaya kan lokacin kiyama!?
Sai
yace: Gani nan ya Manzon Allah! Sai yace: Idan aka tozarta amana to ka jira
tashin kiyama!
Sai
yace: yaya ne tozartata?
Sai
yace: Idan aka jingina al'amari na shugabanci zuwa ga wanda bai dace
da shi ba to ka jira kiyama''. Bukhari ne ya ruwaito shi (59)
Na biyu: Daga Abu Hurairah (r.a) Lallai shi yace: Manzon Allah
(s a w) yace:
"أدِّ الأمانة إلى من ائتمنك, ولا تخُن
مَن خانك".
Ma'ana:
ka mayar da amana zuwa ga wanda ya baka ita, kuma kada ka ha'inci wanda ya
ha'inceka'' Abu Da'uda ne ya ruwaito shi (3535) da Tirmiziy (1264) kuma yace:
hadisi ne حسن
غريب [Duba/ As-silsilatus
sahihatu na Albani (lamba: 424)].
Na Uku: Daga Anas (r.a) yace: Annabi ( s a w ) yace:
"أول ما تفقدون
من دينكم: الأمانة, و آخره: الصلاة".
Ma'ana:
"Farkon abinda zaku rasa daga addininku shine: AMANA, na karshensa kuma
sallah". [Khara'idiy ne ya ruwaito shi cikin makarimul akhlak (28), Duba
littafin/ as-silsilatus sahihah na Albaniy (lamba: 1739)].
Na hudu: Daga Abu hurairah (r.a) daga Annabi (s a w) lallai
yace:
"آية المنافق
ثلاث: إذا حدث كذب, وإذا وعد أخلف, وإذا ائتمن خان".
Ma'ana: alamomin munafuki guda uku ne: (1) Idan
yayi zance sai yayi karya (2) Idan yayi alkawari sai ya karya (3)
Idan aka bashi amana kuma sai yayi ha'inci". Bukhariy (33) da Muslim (107)
ne suka ruwaito shi.
MA'AIKACI YAYI AIKINSA DA KWAZO DA KUMA IKHLASI, ZA A BASHI
LADANSA A DUNIYA DA LAHIRA:
Idan ma'aikaci ya tsayu wajen yin aikinsa da kwazo,
yana kuma fatan ladan Allah, to sai ya kubutar da wuyansa, sannan ya cancanci
ladan aikin (Albashi ko waninsa) a nan gidan duniya, sannan kuma ya rabauta da
lada a gidan lahira.
Kuma hakika nassoshin shari'a sun zo suna nuni cewa
lallai lada kan abinda mutum ke aikatawa na aiyuka kawai ya kan kasance ne idan
aka nemi ladansa kuma aka nufi Allah da neman ganin fuskarsa da aiki; Allah mai
girma da daukaka yana cewa:
}لا خير في كثيرٍ من نجواهم إلا من أمر
بصدقة أو معروفٍ أو إصلاحٍ بين الناس ومن يفعل ذلك ابتغاء مرضاة الله فسوف نؤتيه
أجرًا عظيمًا{ [ النساء:
١١٤].
Ma'ana:
"Babu alkhairi cikin dayawa daga ganawarsu sai dai wanda yayi umarni da
sadaka, ko yin aiki da abu mai kyau, ko sulhu a tsakanin mutane, duk wanda ya
aikata haka yana mai neman yardar Allah to da sannu zamu bashi lada mai
girma" [Nisa'i: 114].
Kuma
Bukhariy (55) da Muslim (1002) sun
ruwaito daga Abu mas'ud (r.a) lallai Manzon Allah (s a w) yace:
"إذا أنفق الرجل على أهله يحتسبها فهو
له صدقة".
Ma'ana: "Idan mutum ya ciyar da
iyalansa- alhalin yana neman lada akan haka- to wannan din sadaka ne a gare
shi".
Kuma
Annabi (s a w) yace wa Sa'ad bn Abiy-wakkas:
"ولستَ تنفق
نفقة تبتغى بها وجه الله إلا أُجِرتَ بها, حتى اللقمة تجعلها في في امرئتِك".
Ma'ana: "Ba
za ka ciyar da wata ciyarwa ba kana mai neman fiskar Allah da ita, face an baka
lada akanta, kai! Har loma da zaka sanya a bakin matarka'' Bukhari (5354) da
Muslim (1628) ne suka ruwaito shi.
Wadannan nassoshin sun yi nuni cewa lallai musulmi
idan ya bayar da abinda ke kansa na wajibin bayi a kansa to wuyansa ya kubuta, kuma
sa'annan abin sani kawai zai samu lada ne (a wajen Allah) idan ya nemi ladan (ya
kuma yi ikhlasi) kuma ya nemi fiskar Allah (Tsarki da daukaka sun tabbata a
gare shi).
KIYAYE LOKACIN DA AKA KEBE MA AIKI DON AIKATA ABINDA ZAI BUNKASA
AIKIN:
Ya zama wajibi (dole) ga dukkan ma'aikaci (aikin
hukuma da waninsa) ya cike dukkan lokaci da aka kebe masa; kar yayi wassu
al'amura na daban ba aikin da ya zama dole ya aikata a cikinsa ba, kamar kuma yadda
ba zai cike lokacin ko sashensa ba da wani abinda maslaharsa ce kawai (ba na
aiki ba), ko maslahar waninsa idan ta zama bata da alaka da aikin; saboda
lokacin aikin ba mallakar ma'aikaci ba ne; kai dai lokacin mallakin aikin da
aka karbi kudi don aikata shi ne.
Hakika As-sheiku Almu'ammar bn Aliyu Albagdadiy (wanda
ya rasu a shekarar hijira 507) yayi nasiha wa Nizamal mulki Alwazir wa'azi mai
ratsa jiki mai amfani, daga cikin abinda ya fada a farkonta "Sananne ne
-ya kai sadrul islam- lallai dayan wadanda ake jagorantarsu (wadanda ba
shugabanni ba) suna da zabi cikin masu nufo su da masu zuwa musu; (ta yadda) idan
sun so sai su sadar, idan kuma sun so sai su yanke, Sai dai kuma duk wanda ya
tufata da shugabanci, to shi kam bashi da zabi kan wanda ya nufo shi da wanda
ya zo masa; saboda duk wanda ya zama shugaban wassu halittu, to shi fa hakika kamar
dan-kwadago ne, saboda ya sayar da lokacinsa ya kuma karbi kudinsa; don haka; Babu
wani abu da ya rage masa a yininsa da zai sarrafa shi cikin zabinsa, kai! Bashi
da damar yin sallar nafila ko ya shiga wajen yin i'itikafi …; saboda wancan
nafila ne, wancan kuma farilla ne dole".
Daga cikinta kuma akwai fadinsa- alhali yana masa
wa'azi -:
"فاعمُر قبرَك كما عمَرتَ قصرَك".
Ma'ana:
kuma ka raya kabarinka kamar yadda ka raya benin gidanka", [Duba zailu dabakatil
hanabilah (1/107)].
Kuma lallai kamar
yadda mutum ke kwadayin ya karbi ladansa (ko albashinsa) a cike ba nakasu,
sannan baya so a tauye masa wani abu daga ciki; to haka kuma ya zama dole
akansa kada ya tauye komai na lokacin aiki wajen sarrafa shi ba'a abinda zai
zama maslahar aikin ba. Kuma hakika Allah ta'alah ya zargi masu tauye ababen
awu da ma'aunai wadanda ke neman hakkokinsu a cike, sannan su tauye hakkokin
wassunsu Yace:
}
ويلٌ للمطففين *
الذين اكتالوا على الناس يستَوفون * وإذا كالوهم أو وزنوهم يُخسرون * آلا يظنُّ
أولئك أنَّهم مبعوثون * ليومٍ عظيم * يوم يقوم الناس لربِّ العالمين { [ المطففين:
1 – 6 ]
Ma'ana: ''kwarin azaba ta tabbata ga masu tauyewa,
wadanda idan suka auna daga mutane suke neman cikawa, kuma idan suka auna musu,
ko suka gwada musu (wato a sikeli) suke tauyewa, shin wadancan kam basu da
tabbacin cewa lallai su abun tayarwa ne, ga wani yini mai girma, yinin da
mutane zasu tsaya gaba ga ubangijin halittu?! [Mudaffifina: 1-6].
ABIN LURA WAJEN ZABEN MAI KWADAGO DA MA'AIKATA:
Tushe wajen
zaban kowane ma'aikaci (na hukuma ko waninsa) shine ya zama:
1. Mai karfi
2. amintacce;
Saboda da karfi ne zai iya tsayuwa da aikin da
ake nema daga wajensa, da amana ne kuma, zai yi shi ta fiskar da wuyarsa zata
kubuta, kuma da amana ne zai iya ajiye abubuwa a gurabansu … Hakika Allah ya
bada labarin daya daga cikin 'ya'yan mutumin garin Madyana, da kuma fadinta wa
mahaifinta - yayin da (Annabi) Musa (a.s) ya shayar musu da dabbobinsu - :
}
يا أبتِ استأجِرْهُ إنَّ خير من استأجرْت القويُّ الأمين {
[
القصص: ٢٦ ]
Ma'ana:
Ya babana! Ka nemi ya rika maka kwadago, lallai mafi alkhairin wanda ka nemi
aikinsa shine: mai karfi, kuma amintacce" [Kasas: 26].
Sannan Allah yana cewa – dangane da ifritu daga cikin aljanu
wanda ya baiyana wa (Annabi) sulaiman (a.s) shirinsa kan kawo al'arshin
Bilkis-:
}
أنا
آتيك به قبل أنْ تقوم من مقامك إني عليه لقويٌّ أمين {[
النمل: ٣٩ ]
Ma'ana:
"Ni zan zo maka da shi kafin ka tashi daga wajen zamanka, kuma lallai ni
akansa (kawo al'arshin) lallai mai karfi ne kuma amintacce" [Naml: 39];
Ma'anar wannan shine: lallai shi (ifritu) ya hada tsakanin ikon daukar al'arshinta,
da kuma halarto da shi, tare da: kiyaye shi da kawo shi da duk abinda ya kunsa
(wannan kuma shine amana, a nan).
Sannan
Allah ya bada labarin Yusuf (a.s) cewa
lallai shi ya ce ma wannan sarkin:
} قال اجعلني على خزائن الأرض إنِّي حفيظٌ عليم {[
يوسف: ٥٥ ]
Ma'ana:
''Ka sanya ni (jagora) kan taskokin kasa; lallai ni mai kiyayewa ne
masani" [Yusuf: 55].
Kishiyan "karfi da amana" kuma sune "rauni
da ha'inci"; wanda kuma sune tushe ko ginshiki wajen kin zaben (mutum) a
matsayin ma'aikaci, kuma sune abubuwa na hakika da zasu halatta tobe (mutum) ko
tsige ma'aikin daga (aiki). Wannan kuma shi dalilin da ya sanya Umar bn khaddab
(r.a) ya nada Sa'ad bn Abiy-wakkas a matsayin gomna a garn Kufa, sannan aka
samu wawayen cikinta suna sukansa, kuma suka kawo saransa wajen khalifa Umar
(r.a); Sai (Umar) ya ga cewa maslaha tana hukunta ya tobe shi; saboda (1)
tunkude fitina, (2) kuma saboda
kada wani daga cikinsu ya masa ta'addanci.
Sai dai Umar (r.a) a rashin lafiyan rasuwarsa ya
aiyana mutane shida daga sahabban manzon Allah (s a w) da za a zabi khalifa
daga cikinsu a bayansa kuma daga cikinsu din akwai sa'ad bn Abiy-wakkas (r.a) sai kuma yaji tsoron
kada wani yayi zaton cewa: tobewan da Umar (r.a) yayi wa (sa'ad r.a) daga
gomnan garin Kufa (sababinsa shine) saboda rashin cancantarsa da wannan
shugabanci; sai ya kore abun da za a iya zaton da fadinsa:
"فإنْ أصابت
الإمرةُ سعدًا فهو ذاك, وإلا فليستعن به أيُّكم ما أُمِّر؛ فإني لم أعزِلْه عن عجَزٍ
ولا خيانةٍ".
Ma'ana:
"Idan shugabancin ya samu Sa'ad to shikenan, idan kuma a'a to duk wanda
aka shugabantar ( a matsayin amirul mu'uminin ) ya nemi taimakonSa; saboda
lallai ni ban tobe shi ba wai saboda gazawa, ko kuma ha'inci", Bukhariy ne
[lamba: 3700] ya ruwaito shi.
- Ya zo cikin sahihu Muslim [lamba: 1825] daga
Abu-zarri (r.a) lallai yace:
"قلت لرسول الله! ألا
تستعملني؟ قال: فضرب بيده عليّ منكبِي ثم قال: ((يا أبا ذر! إنك ضعيف وإنها أمانة,
وإنها يوم القيامة خِزْيٌ وندامة, إلا مَن أخذها بحقها، وأدّى الذي عليه فيها)).
Ma'ana: '' Nace wa Manzon Allah! Shin ba za ka ban
aiki ba? Yace: Sai ya doki kafadata da hannunsa sannan yace: ya kai aba-zarrin!
Lallai kai fa mai rauni ne, lallai kuma shi (aiki) amana ne, sannan kuma lallai
shi (aikin) ranan tashin kiyama tabewa ne da nadama, sai dai wanda ya dauke shi
da hakkinsa, sannan ya bada abinda ke kansa a cikinsa". Kuma lallai a cikin
sahihu Muslim [lamba: 1826] daga Aba-zarrin (r.a) lallai Manzon Allah (s a w)
yace:
((يا
أبا ذر إني أراك ضعيفًا, وإني أحبُّ لك ما أحبُّ لنفسي, لا تأْمرَن علي اثنين, ولا
توليَّن مالَ يتيم)).
Ma'ana:
'' Ya kai Abu zarrin lallai ni ina ga kai mai rauni ne, kuma lallai ina so maka
abinda nake so wa kaina;! Kada ka zama shugaban mutane guda biyu, kuma kada ka
jibinci dukiyar maraya".
MANYAN MA'AIKATA ABIN KOYI NE = WAJEN KWAZO KO KASALA GA KANANANSU:
Idan manyan
ma'aikata suka tsayu wajen aikata abinda ya wajabta akansu cikakken tsayuwa to
sai ma'aikata kanana mabiyansu su yi koyi dasu, (kamar yadda kishiyan hakan shima daidai ne)
kuma lallai kowane shugaba cikin wani aiki to za a tambaye shi kan kansa da
wadanda yake shugabanta, kamar yadda Manzon Allah (s a w) yake cewa:
((كلكم راع ومسؤول
عن رعية؛ فالأمير الذي على الناس فهو راعٍ عليهم وهو مسؤول عن رعيته, والرجل راع
على أهل بيته وهو مسؤول عنهم, والمرأة راعية على أهل بيت بعلها وولده وهي مسؤولة
عنهم, والعبد راعٍ على مال سيده وهو مسؤول عنه, ألا فكلكم راع, وكلكم مسؤول عن رعيته)).
Ma'ana:
"Dukkan ku masu kiyo ne, kuma ababen tambaya kan abinda aka basu kiyo,
shugaba da ke kan mutane mai kiyo ne a kansu kuma shi abun tambaya ne a kansu, Mutum
mai kiyo ne ga iyalan gidansa, kuma shi abin tambaya ne a kansu, Bace mai kiyo
ce kan gidan mijinta da yaransa kuma ita abar tambaya ce akansu, Bawa mai kiyo ne
ga dukiyar shugabansa kuma shi abin tambaya ne akansa, Ku saurara!! Dukkan ku
masu kiyo ne, kuma dukkan ku abun tambaya ne kan abinda aka baku kiyo",
Bukhariy [lamba: 2554] da Muslim ne [lamba: 1829] suka ruwaito shi daga
Abdullahi bn umar (r.a).
Don haka; Idan manyan ma'aikata suka kiyaye aiyukansu
cikin lokuta, gabadaya Sai su zama abin koyi mai kyau ga wadanda suke
karkashinsu,
Wani Mawaki yana cewa:
"وإنَّك إذْ ما
نأت ما أنت آمِرٌ ...
|
به تلفِ مَن إياه تأمُر آتيا".
|
Ma'ana: "Kuma lallai kai idan ka
aikata abinda kake umarni da shi, to za ka samu wanda kake masa umarni na zuwa
da abinda kayi umarnin.
Ma'anar wannan
shine: Idan har ka umarci waninka da ke kasa da kai cewa ya aikata wajibinsa,-
sai kuma kayi rigaye wajen tsayuwanka da wannan wajibin- to zaka samu waninka
yana mai amsa maka, kuma yana mai tsayuwa da abinda ka umurce shi.
MU'AMALANTAR MA'AIKACI GA WANINSA DA IRIN ABINDA YAKE SON A
MU'AMALANCE SHI DA SHI:
Ita nasiha sha'aninta a cikin musulunci
yana da girma; shi yasa Manzon Allah yace:
((الدين النصيحة, قالوا: لِمَن
يا رسول الله؟ قال: لله, ولكتابه, ولرسوله, ولأئمة المسلمين, وعامتهم)).
Ma'ana:
"Addini shine nasiha, sai suka ce ga wa?- ya Manzon Allah- sai yace: Ga
Allah, da littafinsa, da manzonsa, da kuma shugabannin musulmai da sauran musulmai''
Muslim [lamba: 55] ne ya ruwaito shi daga Abu-rukayyah Tamimu bn Aus Addariyyi
(r.a). Shi kuma Jarir bn Abdullahi albajaliy (r.a) yace:
"بايعْتُ رسولَ
الله r
على إقام الصلاة, وإيتاء الزكاة, والنصح لكل مسلمٍ".
Ma'ana: '' Nayi mubaya'a wa Manzon Allah (s a w) kan
tsayar da sallah, da bada zakka, da kuma nasiha ga kowane musulmi'' Bukhari
[lamba: 57] da Muslim [lamba: 56] suka ruwaito shi.
Kuma kamar yadda kowane ma'aikaci idan yana da bukata
a wajen waninsa yake son waninsa ya mu'amalance shi mu'amala mai kyau to shima
wajibi ne ya mu'amalanci waninsa da mu'amala mai kyau; Manzon Allah (s a w)
yace:
((فمَن
أحبَّ أن يُزحزح عن النار، ويدخل الجنة فلتأته منيّته وهو يؤمن بالله واليوم الآخر,
وليأتِ إلى الناس الذي يُحبّ أنْ يؤتى إليه)).
Ma'ana:"
Duk wanda yaso a kawar da shi ga barin wuta, a kuma shigar da shi aljanna to
mutuwarsa ta zo masa alhalin yana mai imani da Allah da ranar karshe, ya kuma
zo wa mutane da kwatankwacin abinda yake son a aikata masa" Muslim [lamba:
1844] ne ya ruwaito shi cikin hadisi dogo daga Abdullahi bn Umar (r.a). Ma'anan
wannan shine: "Ka mu'amalanci mutane da irin abinda kake son su
mu'amalance ka da shi.
Kuma
Annabi (s a w) yana cewa:
((لا يؤمن أحدكم حتى
يحب لأخيه ما يحبّ لنفسه)).
Ma'ana:
"Imanin dayanku baya cika har sai ya so wa dan uwansa abin da yake so wa
kansa ''Bukhari (13) da muslim (45) ne suka ruwaito shi daga Anas (r.a)
Kuma
hakika Allah ya zargi wanda ya ke mu'amalantar waninsa da sabanin abinda ya ke
son a mu'amalance shi da shi cikin fadinsa madaukaki:
}
ويلٌ للمطففين *
الذين اكتالوا على الناس يستَوفون * وإذا كالوهم أو وزنوهم يُخسرون { [ المطففين: 1 – 3 ]
Fassaran
ayoyin ya gabata.
Manzon Allah ( s a w ) yana cewa:
"إنَّ الله عز وجل حرَّم
عليكم عقوق الأمهات, ووأد البنات, ومنعًا وهات, وكره لكم ثلاثا: قيل وقال, وكثرة
السؤال وإضاعة المال".
Ma'ana: "Lallai Allah mai girma da
daukaka ya haramta muku kin biyayya wa iyaye, da bunne 'ya'ya mata, da
kuma hani da bani (rowa da kwadayi). Kuma
ya kiye muku aikata abubuwa guda uku: jita-jita, da yawan tambaya (ko tambayar kure) da kuma tozarta dukiya''
Bukhari [lamba: 2408] da Muslim [lamba: 593] ne suka ruwaito shi daga Almugirah
bn shu'ubah (r.a).
A
cikin wannan hadisin Annabi (s a w) ya zargi mutumin da ke tara dukiya mai
hanawa; wanda yake karba, baya bayarwa;
Kuma hakika
Allah ya tunatar da majibinta marayu da cewa sun kasance su kan ji tsoro ga
kananan zurriyarsu- da (za a kaddara) su bar su, yace:
}
وليخشَ الذين لو
تركوا من خلفِهم ذرِّيةً ضِعافًا خافوا عليهم فاليتقوا الله وليقولوا قولاً سديدًا
{
[
النساء: 9 ].
Ma'ana: "Su ji tsoro; Wadanda da sun
bar zurriya masu rauni - a bayan rasuwarsu- za su kasance masu jiye musu tsoro (to
irin wadannan mutanen da suke tsorace wa kananan 'ya'yansu tozarta a bayan
rasuwarsu to su sani cewa: iyayen marayun nan suma gabanin rasuwarsu haka suke
dangane da 'ya'yansu; don haka) su ji tsoron Allah kuma su fadi magana da ta dace" [Nisa'i:
9].
Ma'anarta kuwa: kamar yadda su suke son a
kyautata wa zurriyarsu masu rauni bayan rasuwarsu, to suma dole ne akansu su
kyautata wa marayu da suke shugabantarsu.
MA'AIKACI YA GABATAR DA WANDA YA
RIGA ZUWA SAI WANDA KE BIYE, DAGA MABUKATA (MAZOWA WURINSA):
Yana daga adalci kada ma'aikci ya jinkirta wanda ya
riga daga cikin (mazowansa) masu bukata, ko kuma ya gabatar da wanda yayi
jinkiri (ya zo a karshe), (saboda adalci
shine): gabatarwan ya kasance- a wajensa- gwargwadon rigaye, kuma cikin haka
akwai hutu ga ma'aikacin tare da Mazowan nasa mabukata, Kuma hakika dalili ya
zo cikin sunnar manzon Allah (s a w) a kan haka; Daga Abu Hurairata (r.a)
lallai shi yace:
"بينما النبي r
في مجلس يحدث القوم, جاءه أعرابيٌّ فقال: متى الساعة؟ فمضى رسول الله r
يُحدِّث, فقال بعض القوم: سمِع
ما قال فكره ما قال, وقال بعضهم: بل لم يسمع, حتى إذا قضى حديثَه قال: أين أُراه
السائل عن الساعة؟ قال: ها أنا يا رسول الله, قال: فإذا ضُيِّعت الأمانةُ
فانتظر الساعة قال: كيف إضاعتها؟ قال: إذا وُسِّد الأمر إلى غير أهله
فانتظر الساعة".
Fassaran hadisin ya gabata.
Bukhariy ne [lamba: 59] ya ruwaito shi.
Dalili daga wannan hadisin shine: lallai
Manzon Allah (s a w) bai amsa wa mai tambaya kan tashin kiyama ba sai bayan
gama bada hadisi ga wadanda suka rigaye shi.
Ibn-Hajar ya fada cikin sharhinsa: ''Daga
(wannan hadisin) zamu koyi cewa: Daukar darrusa ya kan kasance ne gwargwadon
rigaye, haka kuma (al'amarin) fatawowi da hukumomi da wassunsu'' (suma zasu
kasance gwargwadon rigaye).
Ya zo cikin tarjama ko tarihin Abu
ja'afar muhammad bn Jarir Addabariy, a cikin LISANUL MIIZAAN na Hafiz ibn Hajar;
fadinsa: ''Kuma ibn asakir ya fitar (da wannan maganar) daga Abiy-ma'abad Usman
bn Ahmad Addainuriy, lallai yace: Na halarci majlisar Muh'd bn jarir Addabariy
sai fadlu bn ja'afar bn alfura-at alwazir (minista) ya zo, sai dai kuma wani
mutum ya riga shi, sai Dabariy yace wa wannan mutumin: shin ba za kayi karatu
ba ne? Sai yayi nuni zuwa ga wannan ministan, sai dabariy yace masa idan layi
ya zo kansa kada ka damu da (kogin) dijlat, ko furat.
Nace: (mai magana shine: Ibn-hajar) wannan
yana cikin fa'idodin da wannan malami Ibn jarir ya bayar (lada'if) da kuma
balagarsa, tare da rashin damuwarsa da 'yan duniya (masu kudi ko masu mulki).
SIFFANTUWAR MA'AIKACI DA SIFFAR
KAMEWA TARE DA KUBUTA KO BARIN CIN RASHAWA, DA NIISANTAR KARBAR KYAUTA:
Wajibi ne kan kowane ma'aikaci ya kasance mai kamewa,
ya kuma zamanto mai izza a ransa, mai wadatar zuci, tare da nisanta ko barin
cin dukiyar mutane da barna, na daga abinda ake gabatar masa na rashawa ko da kuwa
an kira shi: kyauta; saboda idan ya dauki dukiyar mutane ba tare da hakki ba to
ya cinye ta ne da barna; shi ko cin
dukiya da barna na daga cikin sabbuban rashin karbar addu'a; Imam Muslim
[lamba: 1015] ya ruwaito a cikin sahihinsa daga Abu-hurairah (r.a) lallai shi
yace:
"أيها الناس!
إن الله طيِّب لا يقبل إلا طيِّبًا, وإنَّ الله أمَر المؤمنين بما أمَر به
المرسلين, فقال: (يا أيها الرسل كلوا من الطيبات واعملوا صالحا إني بما تعملون
عليم) وقال: (يا أيها الذين ءامنوا كلوا من طيبات ما رزقناكم) ثم ذكر الرجل
يطيل السفر, أشعث أغبر, يمد يديه إلى السماء : يا رب! يا رب!! ومطعمه حرام, ومشربه
حرام, وملبسه حرام, وغذي بالحرام فأنى يستجاب لذلك!".
Ma'ana: " Ya ku mutane lallai Allah mai tsarki
ne, baya karbar aiki sai mai tsarki, kuma lallai Allah ya umurci muminai da irin
abinda ya umurci manzanni da shi; yace ya ku wadannan manzanni ku ci daga
dadada /tsarkaka kuma ku aikata mai kyau; lallai ni dangane da abinda kuke
aikatawa masani ne" Sannan yace: "Ya ku wadanda su kayi imani ku ci
daga dadadan abinda muka azurta ku" sannan sai ya ambaci wannan mutumin da
ke tsawaita tafiya, mai yawan kullewar gashi, mai yawan kura, yana mika hannu
zuwa ga sama; yana cewa: ya ubangiji! Ya ubangiji!! Alhalin abincinsa haramun
ne, abin shansa haramun ne, tufarsa ta haramun ne, kuma an ciyar da shi daga
haramun, to ta yaya za'a amsa ma wannan?!".
Daga cikin dalilai da suka fito fili wajen horarwa da
kyamatarwa kan cin dukiya da barna, akwai hadisin da Bukhariy ya ruwaito cikin
sahihinsa [da lamba: 7152] daga Jundub bn Abdullah (r.a), yace:
"إنَّ أول ما يُنتِن
من الإنسان بطنُه فمَن استطاع أن لا يأكل إلا طيِّبًا فليفعل, ومَن استطاع أنْ لا
يُحال بينه وبين الجنة بملء كفٍّ مِن دمٍ هراقه فليفعل".
Ma'ana: "Lallai farkon abinda zai
fara wari daga jikin mutum shine: cikinsa; Don haka: duk wanda ya samu damar
kada ya ci, sai abu mai tsarki to ya aikata, kuma duk wanda ya samu damar kada
a shamakance tsakaninsa da tsakanin Aljanna da cikin tafin hannu na jini da ya
zubar da shi, to ya aikata".
Da kuma abinda Bukhariy ya sake ruwaitowa
[lamba: 2083] daga Abu-hurairah (r.a) daga Annabi ( s a w ) lallai yace:
"ليأتينَّ على الناس
زمانٌ؛ لا يبالي المرءُ بما أخذ المال, أَمِن حلالٍ أم مِن حرامٍ".
Ma'ana: "Lallai wani lokaci zai zo
wa mutane wanda mutum ba zai damu da mai
ya dau dukiya ba; shin daga halal ne ko daga haram ne!", A wajen
wadannan -masu daukar, wadanda basu damu ba- lallai halal kawai shine: abin da
ya fado a hannu, haka kuma haram shine: abinda bai iso zuwa ga hannun mutum ba,
Yayin da shi kuma halal -a musulunci- shine abinda Allah da manzonsa (s a w)
suka halatta, shi kuma haram : shine
abinda Allah da manzonsa suka haramta.
Hakika!
Dalilai da suke hana ma'aikata karbar komai na dukiya sun zo daga sunnar Manzon
Allah (s a w) koda kuwa an kira shi da suna: kyauta ne! Daga cikinsu; akwai
hadisin Abu Humaid assa'adiy (r.a) lallai shi yace:
"استعمل رسول الله r
رجلا من الأسد, يقال له: ابن اللتبية على الصدقة فلمّا قدِم قال: هذا لكم, وهذا لي؛
أهدي لي, قال: فقام رسول الله r
على المنبر, فحمد الله وأثنى عليه, وقال: ما بال عامل؟! أبعثه فيقول: هذا لكم,
وهذا أهدي لي؟! أفلا قعد في بيت أبيه أو في بيت أمه حتى ينظر أيهدى إليه أم لا ؟!
والذي نفس محمد بيده! لا ينال أحد منكم منها شيئا إلا جاء به يوم القيامية يحمله على
عنقه, بعير له رغاع, أو بقرة لها خوار, أو شاة تيعر, ثم رفع يديه حتى رأينا عفرتَى
إبطيه, ثم قال: اللهم هل بلغت مرتين".
Ma'ana: "Manzon Allah (s a w) ya aikatar da wani mutum daga (kabilar) asa-d
kan zakka ana ce da shi ibn Lutbiyya, yayin da wannan mutum ya dawo sai yace:
wannan naku ne, wannan kuma nawa ne an bani kyauta, sai yace: sai Manzon Allah
ya tsaya akan minbari, ya gode wa Allah kuma ya yaba masa, sannan yace: me ya
samu ma'aikaci da zan tura shi, amma sai yace: wannan naku ne wannan kuma an
bani shi kyauta?! Me yasa ba zai zauna a gidan ubansa ko a gidan uwarsa don
yaga za a masa kyautan ne ko kuma a'a?! Na rantse da wanda ran Muhammadu ke
hannunsa ! Dayanku ba zai samu komi daga cikin kyautar ba face ya zo da shi a ranar
tashin kiyama yana dauke da shi a wuyansa; Rakumi ne yana ta fitar da sauti (رغاع), ko kuma saniya ce tana kuka (خوار), ko akuya ce tana ta fitar da
sauti (me, me, يعر). Sannan sai
ya daga hannayensa don yin addu'a har sai da muka ga hasken hamatarsa, sannan
yace: Ya Allah shin na isar? Ya maimaita wannan addu'ar har sau biyu. Bukhariy
[lamba: 7174] da Muslim [lamba: 1832] suka ruwaito shi, wannan kuma lafazin Muslim
ne.
Ya zo a cikin littafin sahihul Bukhari
[lamba: 3073] da Muslim [lamba: 1831] –lafazin na Muslim ne,- daga Abu-hurairah
(r.a) lallai yace:
"قام فينا رسول الله r
ذات يوم, فذكر الغلول فعظّمه وعظم أمره, ثم قال: لا ألفين أحدكم يجيء يوم
القيامة على رقبه بعير له رغاء يقول يا رسول الله! أغثني فأقول: لا أملك لك شيئا؛
قد أبلغتك.
لا ألفين أحدكم يجيء
يوم القيامة على رقبته فرس له حمحمة, فيقول: يا رسول الله! أغثني فأقول: لا أملك
لك شيئا, قد أبلغتك.
لا ألفين أحدكم يجيء يوم
القيام على رقبته شاة لها ثغاء, يقول: يا رسول الله! أغثني فأقول: لا أملك لك
شيئا, قد أبلغتك.
لا ألفين أحدكم يجيء
يوم القيام على رقبته نفس لها صياح, فيقول يا رسول الله! أغثني, فأقول: لا أملك لك
شيئا.
لا ألفين أحدكم يجيء يوم
القيام على رقبته رقاع تخفق, فيقول: يا رسول الله! أغثني, فأقول: لا أملك لك شيئا,
قد أبلغتك.
لا ألفين أحدكم يجيء
يوم القيام على رقبته صامت, فيقول: يا رسول الله! أغثني, فأقول: لا أملك لك شيئا؛
قد أبلغتك".
Ma'ana: "Manzon Allah ya tashi –wata rana– a
cikin mu; ya ambaci daukar wani abu cikin ganima kafin a rabata (wato: gululi) sai
ya nuna hatsarinsa sannan ya girmama lamarinsa, Sai kuma yace: Ba zan samu
dayanku da zai zo ranar tashin kiyama yana dauke da rakumin da ke kuka a
wuyansa, sai yace: ya Manzon Allah ka taimake ni, face nace da shi: babu abinda
zan iya yi maka (bazan mallaka maka komai ba), kuma hakika na isar maka.
Kuma ba zan samu dayanku da zai zo ranan
tashin kiyama yana dauke a wuyansa da dokin da ke yin haniniya, sai yace: ya Manzon
Allah ka taimake ni face nace: bana iya mallaka maka komai; saboda na isar
maka.
Ba zan samu dayanku da zai zo ranar
tashin kiyama yana dauke a wuyansa da akuyar da take kuka ME, ME sai yace: ya Manzon
Allah ka taimake ni! Face nace: ba zan mallaka maka komai ba; saboda na isar
maka.
Ba zan samu dayanku ba da zai zo ranar
tashin kiyama yana dauke a wuyansa da wata rai (mutum) da take ta IHU, sai
yace: ya Manzon Allah ka taimake ni; face nace: bana iya mallaka maka komai;
don hakika na riga na isar maka.
Ba zan samu dayanku da zai zo ranar
tashin kiyama yana dauke a wuyansa da tufar da take kadawa, sai yace: ya Manzon
Allah ka taimake ni, sai nace: ba zan iya mallaka maka komai ba; don na riga na
isar maka.
Ba zan samu dayanku ba da zai zo ranar
tashin kiyama na dauke a wuyansa da zinariya ko azurfa ba; sai yace: ya Manzon
Allah ka taimake ni, face nace: ba wani abun da zan iya mallaka maka; saboda na
riga na isar maka".
الرِّقاعُ
Da ya zo cikin hadisin shine: tufa, shi
kuma:
الصامتُ
zinariya da azurfa.
Daga cikinsu
akwai hadisin Abu-humaid assa'adiy (r.a), lallai Manzon Allah (s a w) yace:
"هدايا العمال غُلولٌ".
Ma'ana: "kyautukan da ake baiwa ma'aikata
gululi ne". Ahmad ne [lamba: 23601] da waninsa suka ruwaito shi. [Ka duba
takhrijin hadisin cikin irwa'ul galili na Albaniy (2622)].
Wannan hadisin
ma'anarsu daya da hadisin Abu-humaid assa'idiy (r.a) da ya gabata cikin kissar Ibnul
lutbiyya da ta gabata.
Daga cikinsu
akwai : hadisin Adiyyu bn umairah (r.a) lallai yace: na ji Manzon Allah (s a w)
yana cewa:
"من
استعملناه منكم على عمل فكتمَنا مخيطًا فما فوقه, كان غُلولاً يأتي به يوم القيامة".
Ma'ana: "Duk wanda muka bashi wani
aiki daga cikinku sai ya boye mana koda gwargwadon allura ko abinda ke sama da shi
to wannan gululi ne da zai zo dashi a ranar tashin kiyama", Abu-dawud
[lamba: 2943] ne ya ruwaito shi da isnadi ingantacce, kuma Albaniy ya inganta
shi.
Kuma ya zo a cikin
"tarjamar" iyadhu bn Ganam (r.a) a cikin littafin sifatus safwati na
ibnul-Jauziy (1/277) wanda kuma shi gomna ne da Umar ya nada a garin Hims,
lallai shi yace: wa wassu daga cikin danginsa- a cikin wata kissa mai tsayi:
"فو الله! لأنْ
أُشَقَّ بالمنشار أحبُّ إليَّ مِن أنْ أخون فِلسًا، أو أتعدى".
Ma'ana: "Na rantse da Allah! A tsaga
ni da zarto kasha biyu shine yafi soyuwa a gare ni akan nayi ha'incin kwandala,
ko na ketare iyakar aiki da dokokinsa (na yi ta'addanci).
Ibnul kayyim
ya fada a cikin littafin "I'ilaamul muwakki'ina" (3/154) cikin
dalilan (shari'a da suka haramta dukkan abinda zai kai zuwa ga buduwar anyar
barna, wadanda ake musu lakabi da:
(سدُّ
الذرائع)
(wato: toshe kofofin barna):
((الوجه
الخامس والعشرون: أنّ الواليَ والقاضيَ والشافعَ ممنوعٌ
مِن قبول الهدية، وهو أصل فساد العالم، وإسناد الأمر إلى غير أهله، وتولية الخونة
والضعفاء والعاجزين([1])،
وقد دخل بذلك من الفساد ما لا يحصيه إلا الله، وما ذاك إلا لأن قبول الهدية ممن لم
تجر عادته بمهاداته ذريعة إلى قضاء حاجته، "وحبُّك الشيءَ يُعمِي و يُصِم"،
فيقوم عنده شهوةٌ لقضاء حاجته مكافأة له، مقرونة بِشَرَهٍ، وإغماض عن كونه لا يصلح)).
Ma'ana:
"Fiska na ashirin da biyar: lallai gomna (shugaba) da alkali da wanda zai
yi shafa'a (ceto) an hana shi karbar wata kyauta, wannan kuma shine tushen
lalacewar duniya da kuma jingina al'amari zuwa ga wanda bai cancance shi ba,
tare da shugabantar da maha'inta da masu rauni da gajiyayyu. Kuma hakika barnan
da ba wanda ya san adadinta sai Allah shi kadai ta shiga wa mutane ta wannan
kofar (shugabanni da alkalai su karbi kyauta) dalili kuwa: lallai karbar
kyautan mutumin da a al'adance baya baka kyauta; hanya ce da ya bude don neman shima
a rika biya masa bukatarsa (Larabawa kuma suna cewa): (Sonka ga abu na
makantar da kai ya kuma kurmantar). Daga nan sai sha'awar shima ya biya masa
bukatunsa ya tsayu a cikin zuciyarsa, neman ya ga ya saka masa, da kuma kokarin
saka shi cikin daula, tare da rintse idanu kan kasancewar la'alla wannan mutum
bai cancanci hakan ba".
INA ROKON
ALLAH MAI GIRMA DA DAUKAKA YA DATAR DA KOWANE MA'AIKACI DAGA CIKIN MUSULMAI KAN
GABATAR DA AIKINSA TA FISKAR DA ZATA YARDAR DA ALLAH MAI YAWAN ALBARKA
MADAUKAKI. SANNAN LADA DA KYAKKYAWAN KARSHE A DUNIYA DA LAHIRA YA DAWO MASA.
KUMA YABON
ALLAH DA SALATINSA DA ALBARKARSA SU KARA TABBATA AKAN BAWANSA KUMA MANZONSA
ANNABINMU MUHAMMADU, DA IYALANSA DA SAHABBANSA.
((وأصل
فساد العالم: إسناد الأمر إلى غير أهله، وتولية الخونة والضعفاء
والعاجزين)).
Ma'ana:
"Tushen lalacewar duniya ya fara ne daga: Jingana shugabanci ga wadanda
basu cancance shi ba, da dora maha'inta shugabanci da mulki, ko kuma masu rauni,
da gajiyayyu da ba za su iya yinsa ba".
Dalili
kuwa akan wannan shine hadisin Abu-hurairah (r.a) daya gabata a kusa-kusa wanda
a cikinsa Annabi (s a w) ya amsa wa mutumin da ya tambaye shi yaushe za a yi
tashin kiyama? da fadinsa: Idan aka tozarta amana (shugabanci) to ka jira tashin
kiyama, Sai yace: Yaya nene tozarta ya ke? Sai yace: Shine idan aka jingina
al'amari na shugabanci zuwa ga wanda bai cancance shi ba; to ka jira kiyama".
No comments:
Post a Comment