2015/04/01

SHUGABANNI NA KWARAI, DANA BANZA

ZAVAVVUN SHUGABANINKU SUNE  … (01)

(خيار أئمتكم)
Annabi Muhammadu (s.a.w) mai gaskiya abin gaskatawa, ya yi bayanin zavavvun shuganni, daga na banza (ashararu), a cikin hadisin da Imam Muslim ya rawaito shi [lamba: 1855], A inda yake cewa:
عَنْ عَوْفِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه، عَنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«خِيَارُ أَئِمَّتِكُمُ: الَّذِينَ تُحِبُّونَهُمْ وَيُحِبُّونَكُمْ، وَيُصَلُّونَ عَلَيْكُمْ وَتُصَلُّونَ عَلَيْهِمْ.
وَشِرَارُ أَئِمَّتِكُمُ: الَّذِينَ تُبْغِضُونَهُمْ وَيُبْغِضُونَكُمْ، وَتَلْعَنُونَهُمْ وَيَلْعَنُونَكُمْ».
قِيلَ: يَا رَسُولَ اللهِ، أَفَلَا نُنَابِذُهُمْ بِالسَّيْفِ؟
فَقَالَ: «لَا، مَا أَقَامُوا فِيكُمُ الصَّلَاةَ، وَإِذَا رَأَيْتُمْ مِنْ وُلَاتِكُمْ شَيْئًا تَكْرَهُونَهُ، فَاكْرَهُوا عَمَلَهُ، وَلَا تَنْزِعُوا يَدًا مِنْ طَاعَةٍ»
Hadisi daga Sahabi mai suna Aufu xan Malik (r.a), daga Manzon Allah (s.a.w) yace: "Zavavvun shugabanninku sune: Wadanda kuke sonsu, suma suke sonku, kuma kuke yi musu addu'a, suma suke yi muku addu'a.
Su kuma shugabanninku ashararu sune: Wadanda kuke qinsu, suma suke qinku, kuma kuke tsine musu, suma suke tsine muku"
Sai aka ce: Ya ma'aikin Allah, Shin baza mu yi fito-na-fito da su da takwabi ba –ma'ana: da shugabannin banza ashararu-?
Sai yace: A'a, Matuqar shun tsayar da sallah a cikinku.
Kuma idan kuka ga wani abin da kuke kinsa daga shugabanninku, to sai ku kyamaci aikata shi, Amma kada ku tsame hannunku daga yi musu biyayya".
        A wani lafazin kuma, haka yake:
«خِيَارُ أَئِمَّتِكُمُ الَّذِينَ تُحِبُّونَهُمْ وَيُحِبُّونَكُمْ، وَتُصَلُّونَ عَلَيْهِمْ وَيُصَلُّونَ عَلَيْكُمْ. وَشِرَارُ أَئِمَّتِكُمُ الَّذِينَ تُبْغِضُونَهُمْ وَيُبْغِضُونَكُمْ، وَتَلْعَنُونَهُمْ وَيَلْعَنُونَكُمْ».
قَالُوا: قُلْنَا: يَا رَسُولَ اللهِ، أَفَلَا نُنَابِذُهُمْ عِنْدَ ذَلِكَ؟
قَالَ: «لَا، مَا أَقَامُوا فِيكُمُ الصَّلَاةَ، لَا، مَا أَقَامُوا فِيكُمُ الصَّلَاةَ.
أَلَا مَنْ وَلِيَ عَلَيْهِ وَالٍ، فَرَآهُ يَأْتِي شَيْئًا مِنْ مَعْصِيَةِ اللهِ، فَلْيَكْرَهْ مَا يَأْتِي مِنْ مَعْصِيَةِ اللهِ، وَلَا يَنْزِعَنَّ يَدًا مِنْ طَاعَةٍ».
          Ma'anan wannan lafazin daidai yake da wanda ya gabace shi, Sai dai xan banbanci kaxan ta qarshensa, kamar haka:
"Ku saurara! Duk wanda wani shugaba ya shugabance shi, Sai ya ga shugaban yana aikata wani abu na savon Allah, to ya kyamaci abinda yake yin a savon, Amma kada ya tsame hannunsa daga yi masa biyayya".
Saqon da hadisin ke xauke da shi –wallahi- a fili yake, don haka baya buqatar ta'aliqi.

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...