HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله علي وسلم)
JUMA'A, 21/RABIYUL AUWAL/1437H
Daidai da 01 /janairu /2016m
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI ALIYU XAN ABDURRAHMAN AL-HUZAIFIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
Godiya ta tabbata ga Allah; Ubangijin qasa da
sama, Mai amsa addu'a, Wanda yake faran bayi da ni'imomi, Kuma yake yaye
mummuna da bala'i, Ina yabon Ubangijina kuma ina godiya a gare shi, Ina tuba
zuwa gare shi, ina neman gafararSa, Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya
sai Allah shi kaxai yake bashi da abokan tarayya, Ma'abucin buwaya da girma.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma
shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa ne wanda aka turo shi da shrai'a
cikakkiya, mai haske.
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka
ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da
iyalansa da sahabbansa masu rigaye zuwa ga aiyukan biyayya ababen godiya.
Bayan haka:
Ku kiyaye dokokin Allah da taqawa, iyakar
kiyayewa, saboda duk wanda yayi riqo da taqawa to sai Allah ya haxa masa
alkhairi a duniyarsa da lahirarsa. Wanda kuma ya nisanci taqawa to sai ya tave
a qarshen lamuransa, ko da kuwa duniyarsa ta fiskance shi.
Ya ku Musulmai!!
Lallai Allah ya qaddara sabbuban alkhairori,
da samun rabo a duniya da lahira, Kuma ya qaddara sabbuban sharrukan duniya da
lahira, saboda haka; Duk wanda ya yi riqo da sabbuban alkhairi da rabauta to
sai Allah ya lamunce masa samun gyaruwan rayuwarsa ta duniya, A lahira kuma zai
kasance yana da kyakkyawan makoma, yana mai dawwama cikin aljannonin ni'imah,
tare da rabauta da samun yardar Ubangiji Mai rahama. Allah (تعالى) yana cewa:
"Ba komai ba ne sakamakon kyautatawa face
kyautatawa" [Suratur Rahman: 60].
Wanda
kuma yayi aiki da sabbuban sharri, to sai ya girbe sakamakon aikinsa, a
rayuwarsa ta duniya, da kuma bayan mutuwa. Allah yana cewa:
"Wanda ya aikata
mummunan aiki za a saka masa da shi, Kuma ba zai sami wani masoyi ba, baicin
Allah, kuma ba zai sami mataimaki ba" [Suratun Nisa'i: 123].
Ku
saurara!
[Yin
addu'a] Lallai yana daga cikin sabbuban gyaruwa da kawo gyara, da
rabauta, da yawaitar samuwan alkhairori, da tunkuxe fitintinun da suke sauka,
da uqubobi, da xauke musibun da ake cikinsu, da baqin ciki: YIN ADDU'A
da ikhlasi, da zuciya da take halarce, tare da yin naci, Saboda Ubangiji
Mabuwayi da xaukaka yana son a riqa yin addu'a, kuma yayi umurni da shi. Shi
kuma addu'a yana yin amfani akan abinda ya sauka, da wanda bai sauka ba (na
musibobi), Allah (تعالى)
yana cewa:
"Kuma Ubangijinku ya ce: Ku roqe ni zan amsa
muku, Lallai waxannan da suke kangarewa daga bauta mini, za su shiga jahannama
qasqantattu" [Ghafir: 60].
Kuma
addu'a shine Bauta, kamar yadda ya zo a cikin hadisin Annu'uman xan Bashir (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), Ya ce:
"Addu'a shine bauta (ibada)",
Abu-dawud ya ruwaito shi da Attirmiziy, kuma yace: Hadisi ne mai kyau
ingantacce.
Kuma an ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Babu wani abu wanda yafi matsayi a
wurin Allah fiye da addu'a", Attirmiziy ya ruwaito shi, da
Ibnu-Hibbana a cikin sahihinsa, da Alhakim, kuma yace: Isnadinsa ingantacce ne.
Kuma
Addu'a abun kwaxaitarwa ne akansa a kowani lokaci, kuma ibada ne wanda Allah ya
ke bada sakayya akansa da mafi girman sakamako, Kuma addu'a yana tabbatar da
ababen nema gabaxayansu; kevantattu, da waxanda suka game, na addini, da na
duniya, a cikin wannan rayuwar da bayan mutuwa.
Kuma saboda amfanin da addu'a yake da su masu
girma Allah ta'alah ya shar'anta yinsa a cikin ibadodin da aka farlanta, a
matsayin wajibi ko mustahabbi, saboda rahamar Ubangijinmu da karramawa da yin
baiwa, domin bayi muyi aiki da wannan sababin; da Allah ya sanar da mu Shi.
Kuma lallai da Allah bai sanar da mu yin addu'a ba, to da kwakwalenmu basu
shiryu izuwa gare shi ba, Allah (تعالى)
yana cewa:
"Kuma aka ilmantar da ku, abinda Ku da
ubanninku baku sani ba" [Suratul An'am: 91].
Don haka; Yabo da godiya na Allah ne, yabo mai
yawa, mai daxi, mai albarka, kamar yadda Ubangijinmu yake so, kuma kamar yadda
Ubangiji ya yarda.
Kuma
buqatar yin addu'a a ko-da-yaushe ta kan yi tsanani, Musamman a wannan zamanin,
Wanda fitintinu suka bayyana, kuma suka yawaita, tare da saukar bala'oi da
annoba masu halakarwa, da kuma saukar ababen baqanta rai, ga Musulmai, da
bayyanar qungiyoyin bidi'a; waxannan da suke rarrabe kan Musulmai, kuma suke
halatta zubar da katangaggen jini da kwasar dukiya ta haramaun, suke kuma
kyamar ilimi da ma'abutansa, kuma suke yin fatawa da jahilci, da kuma vata. A
lokacin da maqiyan Musulunci suke taruwa don murqushe shi, suke kuma shisshirya
makirce-makirce akan masu Imani, su kuma Musulman suke tavar da junansu, suke
rarrabewa, suke savani, a tsakaninsu. A kuma lokacin da dangogin cutuwa suka
riski kowanne daga cikin xaixaikun Musulman da aka fitar da su, daga gidajensu,
da zalunci, kuma cutuka suka shafe su, buqatunsu suka zama da wahala, Lallai a
irin waxannan halaye masu tsanani; waxanda Musulmai suke quna da wutansu a
garurrukan da fitintinu suka kunnuBuqatuwar yin addu'a tana yawaita.
Kuma
lallai haqiqa Allah yayi yabo akan waxanda suke roqonSa, suke kuma qanqan-da
kai izuwa gare shi Mabuwayi da xaukaka; IDAN har manyan lamura ko tsanani suka sauka akansu, Allah (تعالى) yana cewa dangane da iyayenMu guda biyu
(Adamu da Hauwa'u عليهما السلام):
"Su biyun, suka ce:
Ya Ubangijinmu! lallai ne Mu mun zalunci kayukanmu, idan har baka gafarta mana
kayi rahama a gare mu ba, zamu kasance daga cikin masu hasara"
[Suratul A'araf: 23]. Kuma Allah (تعالى)
yace:
"Kuma tabbas zamu jarrabe ku da wani abu na
tsoro da yunwa da tawaya cikin dukiya da rayuka da 'ya'yan itatuwa, Kuma ka yi
bishara ga masu haquri * Waxannan da idan musiba ta same su, sai su ce: Lallai
Mu daga Allah muke, kuma lallai Mu zuwa gare shi masu komawa ne * Waxannan
akansu akwai albarku daga Ubangijinsu, da wata rahama, Kuma waxannan sune
shiryayyu" [Suratul Baqarah: 155].kuma Allah mabuwayi da xaukaka
ya faxa dangane da annabi Yunus (عليه
السلام):
"Kuma annabi Yunus sa'ad da ya tafi yana mai
fushi, sai yayi zaton cewa ba za mu quntata masa ba, sai yayi kira a cikin
duffai, cewa: babu abin bautawa face kai, tsarki ya tabbata a gare ka, lallai
Ni kasance daga azzalumai" [Suratul Anbiya'i: 87].
Hadisi ya zo daga Sa'ad xan Abiy-Waqqas (رضي الله عنه) yace, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Addu'ar annabi Yunus wanda kifi ya
haxiye, a lokacin da ya roqi Allah alhalin yana cikin kifi, babu wani Mutum
Musulmai da zai yi roqo da shi, face Allah ya amsa masa addu'ah",
Ahmad ya ruwaito shi, da Attirmiziy, da Alhakim, kuma yace: Isnadinsa
ingantacce ne.
Kuma
a yayin da Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya
kirayi qabilar Saqifu zuwa ga Musulunci, sai suka qi karvar da'awarsa, sannan
suka jefe shi da duwatsu, sai ya roqi Ubangijinsa yana mai cewa:
"Ya Allah ina koka raunin qarfina zuwa
gare ka, da qarancin dabarata, da qasqancin da nake da shi a wurin Mutane, Ya
mafi rahamar masu rahama; izuwa ga Wa; zaka jivintar da Ni; zuwa ga maqiyin da yake
xaure min fiska, ko kuma izuwa ga wani maqiyin da ka mallaka masa lamarina,
Idan baka yi fushi da ni, ba; to bani da damuwa, Saidai kuma lafiyarka ita tafi yalwa a gare ni. Ina neman
tsari da hasken fiskarka wanda ya haskaka duffai, kuma lamarin duniya da lahira
suka gyaru da shi, kada fushinka ya sauka akaina, Komawa naka ne, har sai ka
yarda, Babu dabara babu qarfi face daga wurinka".
Da
yin addu'oi ne, ake fiskantar tsanani da ababen vacin rai, na abubuwan da Mutum
ba zai iya tunkuxe maka su ba; saboda Yazo daga Sauban (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Babu abinda ke tunkuxe qaddara sai
addu'a, kuma babu abinda yake qara tsawon rai sai xa'a ga iyaye da sada
zumunci, Kuma lallai mutum ana haramta masa arziqi saboda wani zunubin da ya
aikata", Ibnu-Hibbana ya rawaito shi a cikin sahihinsa, da
Alhakim, kuma yace: Isnadinsa ingantacce ne.
An ruwaito daga Abdullahi xan Umar (رضي الله عنهما), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), yace:
"Lallai addu'a yana amfani daga abinda
ya sauka, da kuma wanda bai sauka ba, Ya ku bayin Allah; Sai ku lazimci yin
addu'a", Attirmiziy ya ruwaito shi, da Alhakim.
An ruwaito daga Abu-Hurairata (رضي الله عنه) yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: Lallai Allah (تعالى) yana cewa:
"Ni, Ina yadda bawana ke zatona, kuma Ni
ina tare da shi idan ya roqe ne", Bukhariy ya ruwaito shi,
da Muslim.
Kuma lallai wannan lada da falala ya kai yadda
ya kai (A ce, Allah yana tare da bawansa; idan ya roqe shi!).
Kamar
yadda Allah yayi zargi ga waxanda suke
barin roqon Allah ko addu'a a lokacin da uqubobi suka sauka, ko bayyanar fitintinu;
Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma haqiqa mun kama su, da azaba, saidai
basu qanqan da kai ga Ubangijinsu ba, kuma ba sa yin tawali'u"
[Suratul Muminuna: 76]. Kuma Allah mabuwayi da xaukaka yace:
"Kuma lallai mun aika zuwa ga al'ummai daga
gabaninka, sai muka kama su da tsanani da cuta, tsammaninsu za su qanqan da kai
* To, don me lokacin da tsananinmu ya je musu basu yi tawali'u ba, Sai
zukatansu suka qaiqashe, kuma Shexan ya qawata musu abinda suka kasance suke
aikatawa" [Suratul An'am: 42-43]. Kuma Allah (تعالى) yace:
"Kuma ba mu aika wani annabi a cikin wata
alqarya (sai suka qaryata shi) ba, face mun kama mutanenta da azaba, da cuta,
tsammaninsu za su qasqantar da kai" [Suratul A'araf: 94].
Kuma
lallai qin yin addu'a, a lokacin tsanani dogewa ne, akan zunubai, da kuma raina
lamarin kamu ko damqar Ubangiji mai tsanani, Allah (سبحانه) yana cewa:
"Lallai damqar Ubangijinka mai tsanani ce"
[Suratul Buruj: 12].
Kuma
lallai shi addu'a sababi ne mai girma na sauqar alkhairori da albarkoki, da
tunkuxe sharri, ko xauke shi, daga mai yin addu'ar.
Kuma
yin addu'a shine sababin da ya fi qarfi domin fita daga sharrin da ya auku, da
mummunan yanayin da ake ciki, Allah (تعالى)
yana cewa:
"Kuma da Ayyuba a lokacin da ya kirayi
Ubangijinsa lallai ne Ni, cuta ta shafe ni, kuma kai ne mafi rahamar masu
tausayi * Sai muka amsa masa, sa'annan muka kwaranye abinda ke a tare da shi na
cuta, Kuma muka kawo masa iyalansa da kwatankwacinsu tare da su, saboda rahama
daga gare mu, da tunatarwa ga masu ibada" [Suratul Anbiya'i: 83-84].
Kuma Allah (تعالى) yace:
"Ko, Wane ne ya ke amsawa mai buqata, idan
ya roqe shi, kuma ya kwaranye mummuna" [Suratun Naqml: 62]. Ai,
Babu wani da yake aikata hakan, sai Allah (تعالى).
Kuma Allah (سبحانه)
yace:
"Ka ce Wane ne yake tsirar da ku daga duffan
tudu da ruwa, kuna roqonsa bisa ga qanqan da kai, kuma a voye; Lallai ne idan
ka tsiratar da mu daga wannan (masifa), zamu kasance masu godiya * Ka ce: Allah
ne, yake tseratar da ku daga gare ta, da kuma dukan baqin ciki, Sa'annan sai ku
kuma ku ci-gaba da yin shirka" [Suratul An'am: 62-63].
Shi
Musulmi wajibi ne akansa ya riqa addu'a da kwaxayin Allah (تعالى) ya gyara masa sha'anoninsa, gabaxaya,
yana mai xaga buqatunsa zuwa ga UbangijinSa gabaxayansu, ya riqa roqonSa kowani
abu. Kuma mafi girman abin nema shine aljannah, da kuvuta daga aukawa wuta,
Allah (تعالى) yana faxa a cikin
hadisin Qudusiy:
"Ya ku bayina! dukkaniku vatattu ne, sai
wanda na shiryar da shi; ku nemi shiryarwata; in shiryar da ku. Ya ku bayina!
dukkaninku mayunwata ne sai wanda na ciyar da shi; sai ku nemi ciyarwata; in
ciyar da ku. Ya ku bayina! kowanenku tsirara ya ke; babu tufafi sai wanda na tufatar
da shi; sai ku nemi tufatarwata, in tufatar da ku. Ya ku bayina ! lallai kuna
yin laifi dare da rana, ni kuma ina gafarta zunubai gabaxaya; sai ku nemi
gafarata; in yi muku gafara", Muslim ya ruwaito shi daga hadisin
Abu-zarri (رضي الله عنه). Ma'anar hadisin kuma
shine: Ku roqe ni shiriya, da ciyarwa, da tufatarwa da gafara.
Kuma y azo a cikin hadisi cewa:
"Xayanku ya riqa roqon UbangijinSa
koda akan igiyar takalminsa ne (da ya tsinke), da gishirin abincinsa".
Kuma
dayawa, addu'a ta kan canza abinda yake gudana a tarihi daga sharri zuwa ga
alheri, ko kuma daga abu mai kyau zuwa wanda yafi shi kyau, Allah (تعالى) yana cewa dangane da Babanmu annabi
Ibrahim (عليه الصلاة والسلام):
"Ya Ubangijinmu! Ka aiko a cikinsu, wani
manzo, daga gare su, yana karanta musu ayoyinka, kuma yana karantar da su
wannan littafin da hikima, kuma yana tsarkake su, lallai ne kai, kai ne
Mabuwayi Mai hikima" [Suratul Baqara: 129]. Kuma an ruwaito daga Abu-Umamah
(رضي الله عنه), yace: Na ce: Ya ma'aikin Allah! Menene
farkon lamarinka? Sai yace: Ni addu'ar babana ne annabi Ibrahim, kuma
busharar annabi Isah, Sai mamata ta gani a mafarki cewa wani haske ya fita daga
gare ta, wanda har ya haskaka benayen qasar Sham",
Ahmad ya ruwaito shi.
Kuma saboda wannan addu'ar ta annabi Ibrahima;
Musulmai suka kasance cikin alheri madawwami, kai, dukkan dumiya itama wannan
addu'ar ta shafe su.
Haka,
addu'ar da annabi Nuhu (عليه الصلاة والسلام)
itama ta kasance alheri ga muminai masu tauhidi, sharri ga mushirkai.
Haka
addu'ar da annabi Isah (صلى الله عليه وسلم)
zai yi; shi da sahabbansa waxanda za a killace su a jikin dutsen AXXUR, a
qarshen zamani itama zata kasance nasara ce ga muminai, sa'annan halaka ga
YAJUJU da MAJUJU, waxanda suke kamar farar da za ta game dukkan qasa (duniya),
Mafi sharrin halitta, masu tsananin varna da qetare iyaka da qirman kai, saboda Ya zo cikin hadisin Annawas xan Sam'an
(رضي الله عنه) bayan annabi Isa ya kashe MASIHU
AD-DAJJAL:
"Sai Allah (تعالى) yayi wahayi ga annabi Isah (صلى الله عليه وسلم) cewa: Lallai ni na fitar da wassu bayi,
waxanda wani bashi da ikon yaqarsu, Sai ka killace bayina a wajen dutsen
Ax-xur. Sai Allah ya tayar da Ya'ajuju da ma'ajuju alhalin suna gaggawa daga
kowani tudun qasa; Sai na farkonsu su shige ta jikin wani qaramin teku na xabariya, sai su shanye
dukkan ruwan da ke cikinsa, Sai na qarshensu su zo shigewa sai su ce: Lallai
wannan, da akwai ruwa a cikinsa, To, sai a killace annabin Allah Isah (صلى الله عليه وسلم)shi da sahabbansa; har sai ya kasance kan
Saniya yafi alheri ga xayansu, fiye da dinari xari ga xayanku a yau, to daga
nan, sai annabin Allah; Isah ya bayyanar da kwaxayinsa shida sahabbansa (رضي الله عنهم) wa Ubangijinsu maxaukaki; ta hanyar
roqonsa, Sai Allah (تعالى)
ya saukar da tsutsotsi a wuyan Ya'ajuju da Ma'ajuju, sai su wayi gari sun mutu,
kamar mutuwar rai guda xaya. Sa'annan sai annabin Allah; Isah da sahabbansa su
sauka kan qasa, saidai kuma ba za su sami daidai da taqi xaya ba, a doron qasa
face gawar Ja'ajuju da ma'ajuju da warinsu ya cike shi; Sai annabin Allah; Isah
ya bayyanar da kwaxayinsa shida sahabbansa (رضي الله عنهم) wa Ubangijinsu maxaukaki; ta hanyar
roqonsa, Sai Allah (تعالى)
ya turo da wassu tsuntsaye, waxanda suke kama da wuyan raqumi, sai su tattare
su; su kai su, su jefa, a wurin da Allah (تعالى) ya nufa", Muslim ya ruwaito
shi.
Kuma
addu'ar da annabi (صلى الله عليه وسلم)
shugaban halitta, yayi; shi da
sahabbansa, a yaqin badar, itama ta kasance wata nasara ce ga Musulunci, har
abada, kuma tavewa ce, ga kafirci har abada; Allah (تعالى) yana cewa:
"A lokacin da kuke neman agajin Ubangijiku
sai ya amsa muku; da cewa: lallai ne Ni zan taimaka muku da dubu daga cikin
Mala'iku, a jere" [Suratul Anfal: 9]. Sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) yayi ta yin addu'a, kuma ya nace, wajen
yin addu'ar, har sai da mayafinsa ya faxi, A nan ne, Abubakar (رضي الله عنه) ya rungume shi, sa'annan ya ce: Yadda kake yin magiya wa Ubangijinka, ya isa,
ya ma'aikin Allah! Kuma lallai Allah zai cika maka abinda ya yi maka alkawari.
Kuma
lallai yin addu'ar taimakon gaskiya, da ruguje varna, yana daga nasiha ga Allah
da littafinSa, da ManzonSa, da jagororin Musulmai, da kuma sauran Mutanensu.
Kuma
babu wanda zai guje wa yin addu'a, yana mai qaurace masa face wanda ya tozarta
rabonsa a duniya da lahira, sa'annan ya tozarta abinda ya wajaba akansa na
haqqin Musulunci da Musulmai. Ya zo a cikin hadisi cewa:
"Duk wanda bai himmatu da lamarin
Musulmai ba to baya cikinsu".
Kuma
da a ce, za mu yi ta bibiyar fa'idodin addu'a da albarkokinsa, da alherorinsa,
da natijojinsa, daxaxa, kuma ababen mamaki, to da, ambaton hakan yayi tsayi. Saidai
abinda muka riga muka yi ishara, a baya, ya isar.
Kuma
lallai addu'a yana da SHARRUXA, DA LADDUBA;
Kuma yana daga cikin sharruxan addu'a: Cin
abinci na halal, da sanya tufar halal, Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace wasahabinsa Sa'ad xan Abiy-Waqqas (رضي الله عنه):
"Ka kyautata abincinka; sai a amsa
maka addu'arka".
Kuma yana daga cikin sharruxansa: Riqo da
Sunnah, da kuma amsawa Allah (تعالى); ta hanyar aikata abubuwan da ya yi umurni, da nisantar
abubuwan da yayi hani, Allah (تعالى)
yana cewa:
"Kuma idan bayina suka tambaye ka dangane da
ni, ka ce: Lallai ni, a kusa nake, ina amsa addu'ar mai addu'a idan ya roqe ni,
Sai su nemi amsawata, kuma su yi Imani da ni, tsammaninsu za su shiryu"
[Suratul Baqara:186]. Kuma Allah (تعالى)
yace:
"Kuma yana amsawa waxannan da suka yi imani,
suka kuma aikata aiyukan kwarai, kuma
yana qara musu sakamako daga falalarsa" [Suratush Shurah: 26].
Mutumin da aka zalunce shi, shi kuma ana amsa masa, idan yayi addu'a; koda kuwa
kafiri ne, ko xan bidi'a.
Kuma
yana daga cikin sharruxansa: Yin ikhlasi da halarto da zuciya, da yin naci,
wa Allah, da yin gaskiya cikin neman mafaka, daga Ubangiji (تعالى), Allah ta'alah yana cewa:
"Sai ku roqi Allah kuna masu tsarkake addini
a gare shi, ko da kuwa mushirkai sun qi" [Suratul gafir: 15].
Ya zo cikin hadisi cewa, "Allah baya
karvar addu'a daga zuciya rafkananniya mai wargi".
Kuma
yana daga cikin sharruxansa: Kada ya yi, addu'a da savo, ko yanke zumunta,
kuma kada ya qetare iyaka, cikin addu'a.
Kuma yana
daga cikin sabbuban amsa addu'a: Yin yabo wa Allah (تعالى) da sunayensa mafiya kyau, da
sifofinsa maxaukaka, tare da yin salati wa annabi (صلى الله عليه وسلم); Ya zo cikin wani hadisi cewa; Lallai
annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ji wani Mutum
yana cewa:
"Ya Allah, lallai ne Ni ina roqonka
, da shaidawata cewa babu abin bautawa da gaskiya sai kai, Makaxaici, Wanda ake
nufi da biyan buqata, wanda bai haifu ba, kuma ba a haife shi ba, kuma bashi da
wani wanda yake daidai da shi, Sai yace: Lallai ne, ka roqi Allah da sunanSa da
yafi girma; wanda idan aka roqe shi da shi ya kan bayar, idan kuma aka yi
addu'a da shi, ya kan amsa", Abu-dawud ya ruwaito shi, da
Attirmiziy, kuma yace: Hadisi ne mai kyau (hasan).
Da kuma Ibnu-Majah da Ibnu-Hibbana, da
Alhakim, daga hadisin Buraidah (رضي الله
عنه).
An kuma ruwaito daga Fadalah (رضي الله عنه), yace: Wata-rana Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana zaune, sai wani Mutum ya shigo yayi
sallah, Sa'annan ya ce:
"Ya Allah, ka gafarta mini, ka yi
mini rahama, Sai Annabi (صلى الله
عليه وسلم) yace: Ka yi gaggawa ya kai mai sallah,
Idan ka zo sallah; sai ka zauna, to ka yi godiya wa Allah da abinda ya cancance
shi, San'annan sai ka yi min salati, Sa'annan sai ka roqi Allah",
Ahmad ya ruwaito shi, da Abu-dawud, da Attirmiziy, kuma yace: Hadisi ne hasan.
A cikin wani hadisin kuma:
"Lallai addu'a yana rataye tsakanin
sama da qasa har sai ya yi salati wa Annabi (صلى الله عليه وسلم)".
Kuma
yana daga cikin ladduban addu'a da sharruxan karvarsa: Kada ya yi gaggawar
amsawa, A'a yayi haquri, Ya zo a cikin hadisi cewa:
"Za a amsa wa xayanku matuqar bai yi
gaggawa ba; yace: Na roqa, na roqa, amma ba a amsa mini ba",
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi, daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه).
Kuma
lallai, dawwama kan addu'a (da yawaita yinsa), a tare da shi akwai amsawa, Ya zo
cikin hadisi cewa:
"Babu wani Musulmi a bayan qasa,
wanda zai roqi Allah da wata addu'ar face, Allah ya bashi ita, ko kuma ya
tunkuxe masa wani mummunan kwatankwacinta, matuqar bai roqi sabo, ko yanke
zumunta ba. Sai wani Mutum yace: To, lallai za mu yawaita! Sai yace: Allah zai
fi ku yawaitawa", Attirmiziy ya ruwaito shi, kuma yace: Hadisi ne,
hasan sahih, kuma Alhakim ya ruwaito shi daga riwayar Abiy-Sa'id, sa'annan ya
yi qari a cikinsa: Ko kuma, a ijiye masa kwatankwacin addu'arsa.
Kuma
ya dace, Musulmi ya yi kirdadon lokutan amsa addu'a, An ce wa Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم):
Wace addu'a ce, aka fi amsawa? Sai yace:
"Ta qarshe dare, da bayan sallolin farilla",
Attirmiziy ya ruwaito shi, yace: Hadisi ne, hasan, daga hadisin Abiy-Umamah.
Kuma ya zo cikin wani hadisin cewa:
"Ubangijinmu yana sauka zuwa ga
saman duniya, a cikin xaya bisu ukun dare na qarshe; Sai ya ce: Wa zai yi roqo
sai na amsa masa, Wa zai tambaye ni sai na bashi, Wa zai nemi gafarata sai na
gafarta masa", Bukhariy ya ruwaito shi, da Muslim daga hadisin
Abu-hurairah.
Da
kuma tsakanin kiran sallah da yin iqamah, Nan ma ba a mayar da addu'a: Ya zo
cikin hadisi cewa:
"Lokacin da bawa yafi kasancewa kusa
da UbangijinSa shine a lokacin sujjada; Sai ku yawaita addu'a",
Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Abu-hurairah.
Da
kuma lokacin ganin ka'abah, da lokacin saukan ruwa, da hali na buqatuwa, da
bayan khatamar alqur'ani gabaxaya, da bayan yin sadaka.
Ka yi mamakin
girman rabauta, da nasara, da samun ladan Mutumin da ya killace zuciyarsa, ga
Allah (تعالى); yana roqonSa,
yana fatanSa, yana kuma dogara akanSa, yana neman taimakonSa.
Da
kuma tavewa, da girman shirka ko kafircin wanda yake roqon kabari, ko yake
neman agaji daga Annabawa (عليهم الصلاة والسلام),
da waliyyai, ko yake roqonsu koma bayan Allah (تعالى),
ko yake xaga buqatunsa zuwa ga wani mala'ika makusanci, ko wani annabi mursali;
saboda Annabawan Allah (عليهم الصلاة والسلام)
sun zo ne, don kiran Mutane, cewa su keve Allah (تعالى) da yin roqo a gare shi, sa'annan su
kaxaita shi da bauta shi kaxai. Su kuma waliyyai an umurce mu da mu riqa yin
aiki irin nasu, sa'annan mu so, su, kuma aka hane mu, kan roqonsu, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma lallai masallatai na Allah ne, kada ku
roqi wani tare da Allah"[suratul Jinn: 18]. Kuma Allah (تعالى) ya ce:
"Kuma ka ce: Kawai ni, ina roqon Ubangijina
ne, kuma ba zan tara kowa da shi ba" [Jinn: 20].
Kuma wanda baya halarce, da matattu babu wani
daga cikinsu da yake amsa addu'a; saboda addu'a babu mai amsa shi idan ba Allah
Mabuwayi da xaukaka ba, Allah (سبحانه)
yana cewa:
"Kiran gaskiya nasa ne, Waxanda kuma suke
roqa baicinsa basa amsa musu da komai, face kamar mai shumfuxa tafukansa zuwa
ga ruwa domin ya kai ga bakinsa, kuma shi ba mai kaiwa gare shi ba ne, Kuma
kiran kafirai (ga wanin Allah) bai zama ba, face a cikin vata"
[Suratur Ra'ad: 14]. Kuma Allah (تعالى)
yace:
"Babu wanda ya fi vata fiye da wanda ke roqon
wanin Allah, wanda ba zai amsa masa ba, har ranar qiyama, alhalin (waxanda ake
roqan) sun gafala da kiran masu kiran * Kuma idan aka tattara mutane, za su
kasance abokan gaba a gare su, kuma za su kasance masu kafircewa ga bautan da
suka yi a gare su" [Ahqaf: 5-6].
Kuma Allah (تعالى)
yace, alhalin yana bada labarin aiyukanSa:
"Yana shigar da dare a cikin yini, kuma yana
shigar da yini cikin dare, kuma ya hore wata da rana; kowannensu yana gudana
zuwa ga ajali ambatacce. Wannan shine Allah Ubangijinku, mulki nasa ne, kuma
waxanda kuke roqa waninSa basa mallakar ko da fatar kwallon dabino * Idan kuka
roqe su, to ba za su ji kiranku ba, koda sun ji to ba za su amsa muku ba, kuma
a ranar qiyama za su kafirce wa shirkarku, kuma babu mai baka labari, kamar
wanda ya sani", [Faxir: 13-14].
Kuma
lallai Allah bai yi izinin a roqi waninSa ba, duk irin kusancin da yake da shi,
Allah (تعالى) yana cewa:
"Almasihu ya ce: Ya ku 'ya'yan Isra'ila, Ku
bauta wa Allah; Ubangijina, kuma Ubangijinku; lallai ne duk wanda ya yi shirka
da Allah to, lallai Allah ya haramta masa aljanna, kuma makomarsa itace wuta,
kuma babu wassu mataimaka ga azzalumai" [Ma'idah: 72].
Ya zo cikin hadisi cewa: "Wanda ya mutu
alhalin yana roqon wani koma bayan Allah ya shiga wuta",
Bukhariy ya ruwaito shi daga hadisin Abdullahi xan Mas'ud (رضي الله عنه).
Ya
kai Musulmi!!
Wannan shine
littafin Allah, da hadisan ManzonSa (صلى الله
عليه وسلم) suna bayyana maka cewa, lallai ADDU'A
shine BAUTA, kuma lallai Allah mabuwayi da xaukaka shine kawai ya kevanta da
addu'a, ba a yinsa sai ga Allah maxaukaki, kuma duk wanda ya haxa wani da Allah
a cikin addu'a to wannan mushirki ne mai babbar shirka.
Kuma kada wani ya yi koyi da wani cikin vata
da shirka; saboda shirka da kafirci basu auku a cikin 'ya'yan Adam ba face, da
sababin taqalidanci, da bin mutane vatattu, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma shin wancan, shine mafi zama alheri ga
liyafa, ko kuma itaciyar zaqummi * Lallai Mu mun sanya ta fitina ga azzalumai *
Lallai ita wata bishiya ce, wadda take fita daga asalin wutar jahima * Fudarta,
kai kace kayukan shexanu ne * Lallai su haqiqa masu ci ne daga gare ta,
sa'annan masu cika cikinsu ne daga gare ta * Sa'annan suna da wani gauraye a
kanta, daga ruwan zafi * Sa'annan lallai makomarsu izuwa ga wutar jahimu take *
Lallai su, sun iske Ubanninsu suna vatattu *
Sai suka kasance akan gurabansu suke ta yin gaggawa"
[As-safat: 62-70].
Kuma Allah (ta'alah) yana cewa:
"Kuma ku roqi Ubangijinku da qanqan da kai,
da kuma a voye, Lallai ne shi, baya son masu qetare iyaka"
[A'araf: 55].
ALLAH
YAYI MINI ALBARKA, NI DA KU A CIKIN ALQUR'ANI MAI GIRMA.
HUXUBA TA BIYU
Yabo
da godiya sun tabbata ga Allah Mai rahama, Mai jin qai, Mabuwayi Mai hikima,
Ma'abucin sunaye da suka fi kyau, da sifofi maxaukaka.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai
Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, Maxaukakin da Yafi xaukaka.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma
shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa ne Zavavve.
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da
albarka, ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa Masu
taqawa.
Bayan haka:
Ku kiyaye dokokin Allah, sai ya gyara muku
aikyukanku, sa'annan ya sanya ku daga cikin masu rabauta a yanzu, da kuma bayan
komawa izuwa ga makoma.
Ya ku Bayin Allah!
Ku kasance,
masu bayyanar da kwaxayi zuwa ga Allah, masu dawwamar da yin roqo a gare shi (da
yawaitawa); saboda Duk wanda ya roqi Allah baya tavewa, wanda kuma ya yi fatan
samun Allah ba a hana shi.
Kuma kowani Mutum yana da buqatun da suke sabuntuwa, da ababen
nema a kowani lokaci masu yawa; Don haka; Sai kowa ya roqi UbangijinSa, duk
abinda ya san alheri ne. ya kuma nemi tsarin Allah duk abinda ya san sharri ne.
Kuma mafi girman abin roqo shine neman samun yardar Allah, da
kuma aljannah.
Shi kuma mafi girman abinda ake neman tsari daga gare shi,
shine wuta.
Kuma Mutum Musulmi ya yi naciyar roqon abinda ya dame shi, daga
wajen Ubangijinsa; saboda Allah Mawadaci ne, Mai karimci, Abun godiya, Mai
yawan baiwa, Mai girma, Mai iko, Allah maxaukaki yana cewa:
"Ya ku bayina! Da, na-farkonku da na-qarshenku,
da mutanenku da aljanunku zasu tsaya a bigire xaya, sai kowanne ya roqe ni, sai
in bada kowanne xaya abinda ya roqa; to ba zai rage komai daga cikin abinda ke
wurina ba sai kamar gwargwadon abinda allura ta rage; idan aka tsoma ta a cikin
ruwan teku", Muslim
ya ruwaito shi/
Kuma
mustahabbi ne, Musulmi ya riqi addu'oi masu gamewa, waxanda suka zo daga Annabi
(صلى
الله عليه وسلم), kamar faxinsa maxaukakin sarki:
"Ya Ubangijinmu ka bamu mai kyau a Duniya, a lahira ma mai kyau, ka
kare mu daga azabar wuta" [Baqara: 201].
Da kuma misalin
"Ya Allah, lallai ne Ni ina roqonka aljanna da abinda ya kusantar
zuwa gare ta na zance ko aiki, Kuma ina neman tsarinka daga wuta da kuma abinda
ya kusantar zuwa gare ta na zance, ko aiki".
Ya ku bayin
Allah!
"Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati
ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani ku yi salati a gare shi domin
amintarwa"
[Ahzab: 56].
Addu'a ….
……………….
……………….
……………….