2019/11/28

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI
(التحذير من شرب الدخان)
Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz
Allah ya yi masa rahama
Tarjamar Abubakar Hamza
Hakika dalilai na shari’a sun yi nuni cewa lallai shan tabar sigari yana daga al’amura na haram a shar’iance, wannan kuma saboda abinda shan tabar ya kunsa na dauda da cutarwa masu yawa, domin Allah Subhanahu bai halatta ababen ci da shag a bayinsa ba face wadanda sukakasance masu dadi masu amfani.
Amma wanda ya zama zai cutar da su; ga addininsu, ko duniyarsu, ko zai jirkita musu hankulansu, to lallai Allah ya haramta susu su, saboda Allah Mabuwayi da daukaka yafi tausayinsu akan kansu, kumashine Mai hikima Masani; cikin zantukansa da ayyukansa da shari’arsa da kaddararsa; saboda baya haramta abu saboda wasa, kuma baya halittar abu domin barna, kuma baya umurni face da abinda bayi suke da fa’ida acikinsa, saboda Allah Shine Mafi hikimar masu hikima, mafi jin-kan masu jin kai, kuma shine Masanin abinda yake dacewa da bayi, kuma mai amfani a gare su; a nan da can, kamar yadda Allah ya ce: "Lallai Ubangijinka Mai hikima ne Masani". Kuma Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Lallai Allah ya kasance Masani Mai hikima". Kuma ayoyin da suke dauke da wannan ma’anar suna da yawa.
Daga cikin dalilan Alkur’ani akan haramci taba akwai fadin Allah Ta’alah a cikin suratul Ma’idah: "Suna tambayarka me aka halatta musu? Ka ce: an halatta muku abubuwa masu dadi". Kuma a cikin suratul A’araf ya ce, ainda yake sifanta annabinmu Muhammadu: "Yana umurtarsu da kyakkyawa, kuma yana hana su abin ki, kuma yana halatta musu daddada, yana haramta musu dauda", har karshen ayar.
Sai Allah, a cikin ayoyin nan biyu masu karamci ya bayyana cewa bai halatta wa bayinsa ba, face daddadan abubuwa; wanda sune abin ci, da abun sha masu amfani. Amma nau’ukan abin ci da abin sha masu cutarwa ga addini ko jiki ko hankali, to lallai suna cikin munanan abubuwan da aka haramta.
Kuma hakika likitoci da wadanda suka san mecece taba da cutarwarta,sun yi ijma’i cewa, lallai taba tana cikin  abun sha masu cutarwa mai girma, kuma sun ambata cewa taba sababi ne cutuka masu yawa,kamar cutar kansa, da mutuwar farat daya (tsayawar zuciya) da wasunsu.
Kuma duk abinda ya kasance a haka, to babu makawa kan haramcinsa, da wajabcin kiyayarsa.Kumabai dace mai hankali ya rudu da yawan masu shan taba a Duniya ba, domin Allah Ta’alah a cikin littafinsa mabayyani ya ce: (S.AW) ya ce: "Kuma idan ka yi biyayya ga mafi yawan wadanda suke bayan kasa, za su batar da kai daga hanyar Allah, ba komai suke bi ba face zato, kuma sub a komai ba ne, face makaryata".
Kuma ya ce: (S.AW) ya ce: "Ko kana zaton mafi yawansu suna ji ko suna hankalta, su ba komai ba face dabbobi, A’a! sune suka fi bacewa daga hanya".
Don haka, Tabar sigari shanta baya halatta, ko sayar da ita ko ayi tijararta, saboda abinda ke cikin hakan na cutuwa mai girma, da munanan abinda take haifarwa.
Kuma abinda ya wajaba ga wanda yake shan taba (sigari) shine ya mayar da lamurransa ga Allah Ta’alah, yay i nadamar abinda ya gabata, ya yi azamar, ba zai koma mata ba. Wanda ya tuba da gaske, sai Allah Ta’alah ya karbi tubarsa, kamar yadda Mabuwayi da daukaka ya fada: "Kuma ku tuba zuwa ga Allah gaba daya –Ya ku Muminai-, domin ku samu babban rabo". Kuma Allah ya ce: "Kuma ni mai yawan gafara ne, ga wanda ya tuba, kuma ya yi imani, yay i aiki na kwarai, sannan ya shiryu". Kuma Annabi (S.AW) ya ce: "Wanda ya tuba daga zunubi, kamar wanda bashi da zunubi ne", Ibnu-Majah ya ruwaito.
Muna rokon Allah ya gyara halin Musulmai. Kuma ya tsare su daga dukkan abinda yake saba wa shari’arsa, Lallai shi Mai ji ne Mai amsawa.

TSAWATARWA KAN WAKA DA KAYAN KIDA (التحذير من الغناء وألات الطرب)

TSAWATARWA KAN WAKA DA KAYAN KIDA
(التحذير من الغناء وألات الطرب)
Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz
Allah ya yi masa rahama
Tarjamar Abubakar Hamza
Lallai sauraron waka haramun ne, abun kyama, kuma yana cikin sabubban rashin zukata da kaikashewarsu, da kangewa su daga ambaton Allah, da kin yin sallah.
Kuma hakika mafi yawan ma’aboba ilimi sun fassara fadin Allah Ta’alah: "WA MINAN NAASI MAN YASHTARIY LAHWAL HADISI".
“Daga cikin Mutane akwai masu sayen zancen wargi …” zuwa karshen ayar, da cewa shine: Waka.
Kuma Abdullahi dan Mas’ud (R.A) yana yin rantsuwa cewa lallai:  shine: Waka.
Idan kuma ya zama a tare da wakar akwai kayan wargi, kamar sharewa, da tsinke, da kamman, da ganga, to haramcin yafi tsanani.
Wasu Malamai sun ambaci cewa, Wakar da ta hadu da kayan wargi to haramun ne da ijma’i.
Don haka, wajibin shine a kiyaye aikata hakan.
Kuma hakika ya inganta daga Manzon Allah (S.A.W) lallai shi ya ce: (S.AW) ya ce: "Wasu Mutane za su kasance daga al’ummata, suna neman halatta zina (Alhira) da alharir (ga Maza), da giya, da kayan kida".
Abun da ake nufi da (Alhira) shine farji na haram, wato zina.
(Ma’azif) shine: Waka, da kayan kida.
Ina maka wasiyya da sauran Mutane da sauraron Iza’atul Kur’anil karim, da shirin: Nurun alad darb, saboda a cikinsu biyun akwai fa’idodi mkasu girma, kuma sauraronsu aiki ne da zai shagaltar da kai daga sauraron waka da kayan kade-kade([1]).

([1])MAJMU’U FATAWA IBNU-BAAZ, (3/423).

TSAWATARWA DAGA DAUKAN FOTO (التحذير من التصوير)

TSAWATARWA DAGA DAUKAN FOTO
(التحذير من التصوير)
Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz
Allah ya yi masa rahama

Tarjamar Abubakar Hamza
Yabo naAllah ne shi kadai.
Salati da sallama su kara tabbata ga wanda babu Annabi a bayansa, Bayan haka:
Hakika hadisai masu yawa sun zo daga Annabi (S.A.W) a cikin littatafan Sihah da Masanid da Sunan, masu nuni akan haramcin daukar foton dukkan abu mai rai; dan adam ne ko waninsa, wasu kumaakan lamarin keta labulen da a jikinsa akwai fotuna, da umurni kan shafe fotuna, da tsinuwa ga masudaukar foto,  da bayyana cewa sune Mutanen da suka fi samun tsananin azaba a ranar kiyama.
Kuma lallai zan Ambato maka wasu daga cikin hadisai ingantattu,wadanda suka zo a wannan babin, kuma sai na bayyana menene daidai a wannan mas’alar,idan Allah ya so.  
Ya zo cikin Sahihul Bukhariy da Muslim, daga Abu-Hurairah (R.A) ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Babu wanda yafi girman zalunci, kamar wanda ya tafi yana yin halitta, kamar halitta ta, sai su halicci kwayar zarrah, ko kwayar hatsi, ko alkama", Lafazin na Muslim ne.
Kuma a cikin Bukhariy da Muslim daga Ibnu-Mas’ud (R.A) ya ce: Manzon Allah (S.AW) ya ce: "Lallai Mutanen da suka fi tsananin azaba a ranar kiyama sune masu daukar foto".
Kuma ya zo a cikin Bukhariy da Muslim daga Abdullahi dan Umar (R.A) ya ce: Manzon Allah (S.AW) ya ce: "Lallai wadanda suke sana’anta wadannan fotunan za a musu azaba ranar kiyama, sai a ce musu: ku rayar da abinda kuka halitta", Lafazin na Bukhariy ne.
Kuma Bukhariy ya ya ruwaito a cikin Sahihinsa daga Abu-Juhaifah (R.A) lallai Annabi (S.AW) ya yi hani kan cin kudin jini, da kudin kare, da dukiyar karuwanci. Kuma ya la’anci mai cin riba, da wanda ya bayar da ita, da mai canza halitta, da wanda ta nemi a canza mata, da mai yin foto".
Kuma an ruwaito daga Ibnu-Abbas (R.A) ya ce: Na ji Manzon Allah (S.AW) yana cewa: "Wanda ya dauki wani foto a Duniya, za a tursasa masa ya busamasa rai, kuma ba zai iya ba", Bukhariy da Muslim.
Kuma Muslim ya fitar da hadisi daga Sa’id dan Abul Hasan, ya ce: Wani Mutum ya zo ga Ibnu-Abbas sai ya ce: Ni Mutum ne da nake daukar irin wadannan fotunan; ka min fatawa akansu? Sai ya ce: Matso kusa da ni, sai ya kusance shi, har ya sanya hannunsa akan kansa, sannan ya ce: "Dukkan mai yin foto yana cikin Wuta, za a sanya masa dangane da kowane foton da ya dauka, za a sanya mata rai, ta rika azabtar da shia cikin Jahannama". Sai ya ce: Idan babu makawa sai ka yi, to ka yi foton bishiyoyi, da abinda bashi da rai.
Shi kuma Bukhariy ya ruwaito fadinsa: Idan babu makawa sai ka yi, ne a karshen hadisin da ya gabata kafin wannan, da irin lafazin da Muslim ya ambato shi.
Kuma wadannan hadisan da abinda ya zo da ma’anarsu, suna yin nuni a zahiri, kan haramcin daukan foton duk wani abu mai rai. Kuma sun nuna cewa aikata hakan yana daga manyan zunuban da aka ambaci narkon Wuta akansu.
Kuma lallai sun game, duk nau’ukan foto, sawa’un foto ne mai inuwa, ko maras inuwa, kuma sawa’un foton a jikin Katanga ko labule ko riga ko madubi ko littafi ko a wanin haka yake.
Kuma babu banbanci a cikin haka, tsakanin foto masu jiki, da irin wadanda akazana su a jikin labule ko littafi ko makamancin haka, ko tsakanin fotunan ‘yan Adam da wasunsu; na daya daga halittu masu rai, ko tsakanin tsakanin fotunan masu mulki da malamai ko wasunsu, ballamarin haramcin foton masu mulki da maluma da sauran Mutanen da ake girmamawa shi yafi tsanani; domin an fi fitinuwa da wadannan. Kuma kakkafa fotunansu a majalisosinsu da makamancin haka, da girmama su yana cikin mafi girmar hanyoyin shirka, da yin bauta ga wanin Allah, kamar yadda hakan ya auku ga Mutanen annabi Nuhu.
Salatin Allah ya kara tabbata ga Annabinmu; Muhammadu, da iyalansa, da kuma amincinsa([1]). Amin.  

([1])MAJMU’U FATAWA IBNU-BAAZ, (4/ 210), a takaice.

TSAWATARWA GA MAZA KAN TSAWAITA TUFAFI (التحذير من إسبال الرجال)

TSAWATARWA GA MAZA KAN TSAWAITA TUFAFI
(التحذير من إسبال الرجال)
Na Shehun Malami Muhammadu dan Salih Al-usaimin
Allah ya yi masa rahama

Tarjamar: Abubakar Hamza
Sake tufafi nau’i biyu ne:
NA FARKO: Ya kasance da takama da alfahari, Wannan yana daga cikin zunibin kaba’irai, kuma ukubarsa tana da girma, domin ya zo a cikin Bukhariy da Muslim, daga hadisin Abdullahi bn Umar, lallai Annabi (S.A.W) ya ce: Wanda yaja tufafinsa da takama, Allah ba zai yi dubi gare shi ba, ranar kiyama". Kuma an ruwaito daga Abu-Zarrin Algifariy (R.A), lallai Annabi (S.A.W ) ya ce: “Mutane uku, Allah ba zai yi magana da su ba ranar kiyama, kuma ba zai yi dubi a gare su ba, kuma ba zai tsarkake su ba, kuma suna da azaba mai radadi Ya ce: Sai Annabi ya maimata hakan sau uku, Abu-Zarrin ya ce: Sun tabe sun yi hasara Ya Ma’aikin Allah! Su wanene Ya Manzon Allah (S.A.W)? Ya ce: Mai sake tufafinsa, da mai yin gori, da mai tallata kayansa da rantsuwar karya”. Wannan nau’in shine sake tufafin da ya hadu da takama (da girman kai), Kuma a cikinsa akwai narkon nan; na azaba mai tsanani; wanda kuma shine fadin: Allah ba zai yi dubi ga mai aikata shi ba, kuma ba zai yi magana da shi ba, kuma ba zai tsarkake shi a ranar kiyama ba, kuma yana da azaba mai radadi.
Wannan gamewar da ta zo a cikin hadisin Abu-Zarrin (R.A) an kebance ta, da abinda ya zo a cikin hadisin Abdullahi bn Umar (R.A), sai narkon da ya zo a cikinsa ya kasance ga wanda ya aikata hakan (wato, take tufafinsa) cikin takama (da girman kai) kawai; saboda aikin da kuma horon iri daya ne, a cikin hadisan biyu.
NAU’I NA BIYU NA TSAWAITA TUFAFI: Shi ne ya take su bada takama ko girman kai ba, Wannan kuma haramun ne, kuma ana tsoron ya kasance cikin laifukan kaba’irai, saboda Annabi (S.A.W) ya fadi narkon Wuta akansa, domin ya zo a cikin Sahihul Bukhariy, daga Abu-Hurairah (R.A), lallai Annabi (S.A.W) ya ce: "Abinda ya zama kasa da idanun sawu biyu, na tufafi, to yana cikin Wuta".
Shi wannan hadisin ba zai kasance an kebance hukuncinsa da hadisin Abdullahi dan Umar ba (wato, ba za a ce, azabar ta takaita ne ga wanda ya take tufafinsa da takama kadai ba); saboda ukubar da ta zo a cikin hadisan biyu ta banbanta da juna. Da kuma saboda hadisin Abu-Sa’id Alkhudriy (R.A) wanda ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Tufafin Mumini zuwa rabin kwabri ne, Babu laifi ko ya ce: Babu matsala akan abinda ya kasance a tsakanin kwabrinsa da tsakanin idanun sawu biyu. Amma abinda ya kasance kasa da idanun sawu toyana cikin Wuta, Kuma wanda ya ja tufafinsa da takama (alfahari) Allah ba zai yi dubi gare shi ba", Malikya ruwaito shi, da Abu-Dawud, da Nasa’iy da Ibnu-Majah,da Ibnu-Hibbana a cikin sahihinsa.
Sai Annabi (S.A.W) ya banbance tsakanin wanda ya ja tufafinsa da takama (da girman kai), da Mutumin da tufafinsa sukakasance a kasa da idanun sawunsa biyu (ba tare da takamaba, ya bayyana narkon azabar kowanne daga cikinsu).
Saidai Mutumin da ya kasance tufafinsa yana zamewa ko zobewa ya rufe masaidanun sawunsa biyu,ba tare da nufi ba, alhalin yna bin tufafin nasa yana daga shi, to wannan babulaifi akansa, domin a hadisin Abdullahi da Umar da ya gabata, lallai Abubakar (R.A) ya ce: "Ya Manzon Allah! Lallai daya daga cunar tufafina yana zamewa,saidai idan ina binsa, (ina dago shi), Sai Annabi (S.AW) ya ce: "Kai bakakasance daga cikin masu aikata hakan da takama (girman kai ba)"([1]).

([1])MAJMU’U FATAWA WA RASA’LIL USAIMIN, (12/ 308-309).

TSAWATARWA DAGA ASKE GEMU (التحذير من حلق اللحية)

TSAWATARWA DAGA ASKE GEMU
(التحذير من حلق اللحية)
Na Shehun Malami Muhammadu dan Salih Al-usaimin
Allah ya yi masa rahama

Tarjamar Abubakar Hamza
Aske gemu haramun ne, saboda saba wa Manzon Allah ne  (S.A.W), domin Annabi (S.A.W) ya ce: "Ku cika gemu, ku rage gashin baki". Kuma saboda askwar ficewa ne daga shiriyar Manzanni, zuwa ga shiriyar masu bautar Wuta (Majusawa) da Mushirkai.
IYAKAR GEMU (LIHYAT) –Kamar yadda masanan harshen Larabci suka fada- shine: Gashin da ya tsiro a fiska, da muka-mukai biyu, da kumatu biyu; Ma’anar wannan shine: Duk abinda ya tsira a jikin kumatu biyu, ko a muka-mukai biyu, da haba, to wannan yana daga cikin gemu (lihyat). Kuma cire wani abu daga cikin hakan ya shiga cikin sabo, domin Annabi (S.A.W) ya ce: "Ku cika gemu", "Ku sake gemu", “Ku tara gemu”,  Ku ajiye gemu”. Wadannan kuma sai suka nuna cewa, lallai bai halatta a cire wani abu daga jikin gemu ba. Saidai saboda kasancewar sabo mataki-mataki ne, sai aske gemun gaba dayansa yafi muni, akan yanke wani abu daga jikinsa, domin askewan yafi girma kuma yafi rage shi nuna sabawar mai aikata hakan ga Sunnah. Wannan kuma shine gaskiya, kuma ita ce, tafi cancantar a bi ta.
Kuma ka tambayi kanka: Mai zai hana ni karbar gaskiya, da yin aiki da ita, domin yardar da Allah tare da neman ladansa? Don haka, kada ka fifita son rai, da ganin damarka,ko abinda abokai suke so, akan yardar Ubangijinka, Allah Ta’alah ya ce: "Amma wanda ya ji tsoron tsayuwa ga UbangijinSa, sai ya hana ransa abinda take so * To lallai Aljannah ita ce, makoma a gare shi” [40-41].
Shi kuma rage gashin gemu, ya saba wa abinda Annabi (S.A.W) ya bada umurni a cikinj fadinsa:  Ku tara gemu”,  "Ku bar gemu", "Ku sake gemu"; Don haka, Wanda ya so bin umurnin Manzon Allah (S.A.W) da bin shiriyarsa (S.A.W), to kada ya ciri wani abu daga gemunsa; domin shiriyar Manzon Allah (S.A.W) ita ce, kada Mutum ya cire wani abu daga gemunsa. Kuma hakan (wato tara gemu) ita ce shiriyar Annabawan da suka gabace shi, saboda dukkanmu mun karanta fadin Allah Ta’alah dangane da Haruna ga annabi Musa: "Ya dan mamata: Kada ka kama min gemuna, ko kaina". Wannan kuma dalili ne akan cewa, lallai Annabi Haruna yana da gemun da za a iya damkewa. Kuma hakan shine shiriyar cika-makon annabawa; Muhammadu (S.A.W) domin gemunsa ya kasance mai tarin yawa, cikakkke. Don haka; Duk wanda ya so ya bi Annabi cikakken bi, ya kuma  bi umurninsa sau da kafa, to kada ya aske komai daga gemunsa; ta fiskar tsawonsa ko fadinsa.
Wasu Mutane a farkon farin fitowar gemunsu, ya kan kasance gashi ne a rarrabe, sai Mutum ya ce: zai aske shi, domin gashin su fito gaba daya a tare. Wannan kuma ba daidai ba ne; saboda Mutum zai iya askewan, ya zama ya saba umurnin Annabi (S.A.W) da aikata hakan, sai kuma ya mutu gabanin sake tsirowar gemun. Wajibin shine ya bar gemun kamar yadda ya kasance,saboda idan gemun y agama girmansa ko fitowansa, to ya kan taru cikin yanayi mai kyau.
Allah ne Mai datarwa ([1]).

([1]) MAJMU’U FATAWA WA RASA’LIL USAIMIN, (11/ 125-126).

TSAWATARWA AKAN WAKA, DAUKAR HOTO, ASKE GEMU, SAKE TUFAFI GA MAZA, DA SHAN TABAR SIGARI التحذير من: الغناء والتصوير وحلق اللحية وإسبال الرجال وشرب الدخان

TSAWATARWA AKAN
WAKA, DAUKAR HOTO, ASKE GEMU, SAKE TUFAFI GA MAZA, DA SHAN TABAR SIGARI
التحذير من:
الغناء والتصوير وحلق اللحية وإسبال الرجال وشرب الدخان

Na
Shehunan Malamai
Abdul'aziz Dan Abdullahi Ibnu-Baaz
Da
Muhammadu dan Salkih Al’usaimin

Tarjamar
Abubakar Hamza Zakariyya Misau

TSAWATARWA DAGA ASKE GEMU
(التحذير من حلق اللحية)
Na Shehun Malami Muhammadu dan Salih Al-usaimin
Allah ya yi masa rahama
Aske gemu haramun ne, saboda saba wa Manzon Allah ne  (S.A.W), domin Annabi (S.A.W) ya ce: "Ku cika gemu, ku rage gashin baki". Kuma saboda askwar ficewa ne daga shiriyar Manzanni, zuwa ga shiriyar masu bautar Wuta (Majusawa) da Mushirkai.
IYAKAR GEMU (LIHYAT) –Kamar yadda masanan harshen Larabci suka fada- shine: Gashin da ya tsiro a fiska, da muka-mukai biyu, da kumatu biyu; Ma’anar wannan shine: Duk abinda ya tsira a jikin kumatu biyu, ko a muka-mukai biyu, da haba, to wannan yana daga cikin gemu (lihyat). Kuma cire wani abu daga cikin hakan ya shiga cikin sabo, domin Annabi (S.A.W) ya ce: "Ku cika gemu", "Ku sake gemu", “Ku tara gemu”,  Ku ajiye gemu”. Wadannan kuma sai suka nuna cewa, lallai bai halatta a cire wani abu daga jikin gemu ba. Saidai saboda kasancewar sabo mataki-mataki ne, sai aske gemun gaba dayansa yafi muni, akan yanke wani abu daga jikinsa, domin askewan yafi girma kuma yafi rage shi nuna sabawar mai aikata hakan ga Sunnah. Wannan kuma shine gaskiya, kuma ita ce, tafi cancantar a bi ta.
Kuma ka tambayi kanka: Mai zai hana ni karbar gaskiya, da yin aiki da ita, domin yardar da Allah tare da neman ladansa? Don haka, kada ka fifita son rai, da ganin damarka,ko abinda abokai suke so, akan yardar Ubangijinka, Allah Ta’alah ya ce: "Amma wanda ya ji tsoron tsayuwa ga UbangijinSa, sai ya hana ransa abinda take so * To lallai Aljannah ita ce, makoma a gare shi” [40-41].
Shi kuma rage gashin gemu, ya saba wa abinda Annabi (S.A.W) ya bada umurni a cikinj fadinsa:  Ku tara gemu”,  "Ku bar gemu", "Ku sake gemu"; Don haka, Wanda ya so bin umurnin Manzon Allah (S.A.W) da bin shiriyarsa (S.A.W), to kada ya ciri wani abu daga gemunsa; domin shiriyar Manzon Allah (S.A.W) ita ce, kada Mutum ya cire wani abu daga gemunsa. Kuma hakan (wato tara gemu) ita ce shiriyar Annabawan da suka gabace shi, saboda dukkanmu mun karanta fadin Allah Ta’alah dangane da Haruna ga annabi Musa: "Ya dan mamata: Kada ka kama min gemuna, ko kaina". Wannan kuma dalili ne akan cewa, lallai Annabi Haruna yana da gemun da za a iya damkewa. Kuma hakan shine shiriyar cika-makon annabawa; Muhammadu (S.A.W) domin gemunsa ya kasance mai tarin yawa, cikakkke. Don haka; Duk wanda ya so ya bi Annabi cikakken bi, ya kuma  bi umurninsa sau da kafa, to kada ya aske komai daga gemunsa; ta fiskar tsawonsa ko fadinsa.
Wasu Mutane a farkon farin fitowar gemunsu, ya kan kasance gashi ne a rarrabe, sai Mutum ya ce: zai aske shi, domin gashin su fito gaba daya a tare. Wannan kuma ba daidai ba ne; saboda Mutum zai iya askewan, ya zama ya saba umurnin Annabi (S.A.W) da aikata hakan, sai kuma ya mutu gabanin sake tsirowar gemun. Wajibin shine ya bar gemun kamar yadda ya kasance,saboda idan gemun y agama girmansa ko fitowansa, to ya kan taru cikin yanayi mai kyau.
Allah ne Mai datarwa ([1]).
TSAWATARWA GA MAZA KAN TSAWAITA TUFAFI
(التحذير من إسبال الرجال)
Na Shehun Malami Muhammadu dan Salih Al-usaimin
Allah ya yi masa rahama
Sake tufafi nau’i biyu ne:
NA FARKO: Ya kasance da takama da alfahari, Wannan yana daga cikin zunibin kaba’irai, kuma ukubarsa tana da girma, domin ya zo a cikin Bukhariy da Muslim, daga hadisin Abdullahi bn Umar, lallai Annabi (S.A.W) ya ce: Wanda yaja tufafinsa da takama, Allah ba zai yi dubi gare shi ba, ranar kiyama". Kuma an ruwaito daga Abu-Zarrin Algifariy (R.A), lallai Annabi (S.A.W ) ya ce: “Mutane uku, Allah ba zai yi magana da su ba ranar kiyama, kuma ba zai yi dubi a gare su ba, kuma ba zai tsarkake su ba, kuma suna da azaba mai radadi Ya ce: Sai Annabi ya maimata hakan sau uku, Abu-Zarrin ya ce: Sun tabe sun yi hasara Ya Ma’aikin Allah! Su wanene Ya Manzon Allah (S.A.W)? Ya ce: Mai sake tufafinsa, da mai yin gori, da mai tallata kayansa da rantsuwar karya”. Wannan nau’in shine sake tufafin da ya hadu da takama (da girman kai), Kuma a cikinsa akwai narkon nan; na azaba mai tsanani; wanda kuma shine fadin: Allah ba zai yi dubi ga mai aikata shi ba, kuma ba zai yi magana da shi ba, kuma ba zai tsarkake shi a ranar kiyama ba, kuma yana da azaba mai radadi.
Wannan gamewar da ta zo a cikin hadisin Abu-Zarrin (R.A) an kebance ta, da abinda ya zo a cikin hadisin Abdullahi bn Umar (R.A), sai narkon da ya zo a cikinsa ya kasance ga wanda ya aikata hakan (wato, take tufafinsa) cikin takama (da girman kai) kawai; saboda aikin da kuma horon iri daya ne, a cikin hadisan biyu.
NAU’I NA BIYU NA TSAWAITA TUFAFI: Shi ne ya take su bada takama ko girman kai ba, Wannan kuma haramun ne, kuma ana tsoron ya kasance cikin laifukan kaba’irai, saboda Annabi (S.A.W) ya fadi narkon Wuta akansa, domin ya zo a cikin Sahihul Bukhariy, daga Abu-Hurairah (R.A), lallai Annabi (S.A.W) ya ce: "Abinda ya zama kasa da idanun sawu biyu, na tufafi, to yana cikin Wuta".
Shi wannan hadisin ba zai kasance an kebance hukuncinsa da hadisin Abdullahi dan Umar ba (wato, ba za a ce, azabar ta takaita ne ga wanda ya take tufafinsa da takama kadai ba); saboda ukubar da ta zo a cikin hadisan biyu ta banbanta da juna. Da kuma saboda hadisin Abu-Sa’id Alkhudriy (R.A) wanda ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Tufafin Mumini zuwa rabin kwabri ne, Babu laifi ko ya ce: Babu matsala akan abinda ya kasance a tsakanin kwabrinsa da tsakanin idanun sawu biyu. Amma abinda ya kasance kasa da idanun sawu toyana cikin Wuta, Kuma wanda ya ja tufafinsa da takama (alfahari) Allah ba zai yi dubi gare shi ba", Malikya ruwaito shi, da Abu-Dawud, da Nasa’iy da Ibnu-Majah,da Ibnu-Hibbana a cikin sahihinsa.
Sai Annabi (S.A.W) ya banbance tsakanin wanda ya ja tufafinsa da takama (da girman kai), da Mutumin da tufafinsa sukakasance a kasa da idanun sawunsa biyu (ba tare da takamaba, ya bayyana narkon azabar kowanne daga cikinsu).
Saidai Mutumin da ya kasance tufafinsa yana zamewa ko zobewa ya rufe masaidanun sawunsa biyu,ba tare da nufi ba, alhalin yna bin tufafin nasa yana daga shi, to wannan babulaifi akansa, domin a hadisin Abdullahi da Umar da ya gabata, lallai Abubakar (R.A) ya ce: "Ya Manzon Allah! Lallai daya daga cunar tufafina yana zamewa,saidai idan ina binsa, (ina dago shi), Sai Annabi (S.AW) ya ce: "Kai bakakasance daga cikin masu aikata hakan da takama (girman kai ba)"([2]).
TSAWATARWA DAGA DAUKAN FOTO
(التحذير من التصوير)

Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz
Allah ya yi masa rahama
Yabo naAllah ne shi kadai.
Salati da sallama su kara tabbata ga wanda babu Annabi a bayansa, Bayan haka:
Hakika hadisai masu yawa sun zo daga Annabi (S.A.W) a cikin littatafan Sihah da Masanid da Sunan, masu nuni akan haramcin daukar foton dukkan abu mai rai; dan adam ne ko waninsa, wasu kumaakan lamarin keta labulen da a jikinsa akwai fotuna, da umurni kan shafe fotuna, da tsinuwa ga masudaukar foto,  da bayyana cewa sune Mutanen da suka fi samun tsananin azaba a ranar kiyama.
Kuma lallai zan Ambato maka wasu daga cikin hadisai ingantattu,wadanda suka zo a wannan babin, kuma sai na bayyana menene daidai a wannan mas’alar,idan Allah ya so.  
Ya zo cikin Sahihul Bukhariy da Muslim, daga Abu-Hurairah (R.A) ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Babu wanda yafi girman zalunci, kamar wanda ya tafi yana yin halitta, kamar halitta ta, sai su halicci kwayar zarrah, ko kwayar hatsi, ko alkama", Lafazin na Muslim ne.
Kuma a cikin Bukhariy da Muslim daga Ibnu-Mas’ud (R.A) ya ce: Manzon Allah (S.AW) ya ce: "Lallai Mutanen da suka fi tsananin azaba a ranar kiyama sune masu daukar foto".
Kuma ya zo a cikin Bukhariy da Muslim daga Abdullahi dan Umar (R.A) ya ce: Manzon Allah (S.AW) ya ce: "Lallai wadanda suke sana’anta wadannan fotunan za a musu azaba ranar kiyama, sai a ce musu: ku rayar da abinda kuka halitta", Lafazin na Bukhariy ne.
Kuma Bukhariy ya ya ruwaito a cikin Sahihinsa daga Abu-Juhaifah (R.A) lallai Annabi (S.AW) ya yi hani kan cin kudin jini, da kudin kare, da dukiyar karuwanci. Kuma ya la’anci mai cin riba, da wanda ya bayar da ita, da mai canza halitta, da wanda ta nemi a canza mata, da mai yin foto".
Kuma an ruwaito daga Ibnu-Abbas (R.A) ya ce: Na ji Manzon Allah (S.AW) yana cewa: "Wanda ya dauki wani foto a Duniya, za a tursasa masa ya busamasa rai, kuma ba zai iya ba", Bukhariy da Muslim.
Kuma Muslim ya fitar da hadisi daga Sa’id dan Abul Hasan, ya ce: Wani Mutum ya zo ga Ibnu-Abbas sai ya ce: Ni Mutum ne da nake daukar irin wadannan fotunan; ka min fatawa akansu? Sai ya ce: Matso kusa da ni, sai ya kusance shi, har ya sanya hannunsa akan kansa, sannan ya ce: "Dukkan mai yin foto yana cikin Wuta, za a sanya masa dangane da kowane foton da ya dauka, za a sanya mata rai, ta rika azabtar da shia cikin Jahannama". Sai ya ce: Idan babu makawa sai ka yi, to ka yi foton bishiyoyi, da abinda bashi da rai.
Shi kuma Bukhariy ya ruwaito fadinsa: Idan babu makawa sai ka yi, ne a karshen hadisin da ya gabata kafin wannan, da irin lafazin da Muslim ya ambato shi.
Kuma wadannan hadisan da abinda ya zo da ma’anarsu, suna yin nuni a zahiri, kan haramcin daukan foton duk wani abu mai rai. Kuma sun nuna cewa aikata hakan yana daga manyan zunuban da aka ambaci narkon Wuta akansu.
Kuma lallai sun game, duk nau’ukan foto, sawa’un foto ne mai inuwa, ko maras inuwa, kuma sawa’un foton a jikin Katanga ko labule ko riga ko madubi ko littafi ko a wanin haka yake.
Kuma babu banbanci a cikin haka, tsakanin foto masu jiki, da irin wadanda akazana su a jikin labule ko littafi ko makamancin haka, ko tsakanin fotunan ‘yan Adam da wasunsu; na daya daga halittu masu rai, ko tsakanin tsakanin fotunan masu mulki da malamai ko wasunsu, ballamarin haramcin foton masu mulki da maluma da sauran Mutanen da ake girmamawa shi yafi tsanani; domin an fi fitinuwa da wadannan. Kuma kakkafa fotunansu a majalisosinsu da makamancin haka, da girmama su yana cikin mafi girmar hanyoyin shirka, da yin bauta ga wanin Allah, kamar yadda hakan ya auku ga Mutanen annabi Nuhu.
Salatin Allah ya kara tabbata ga Annabinmu; Muhammadu, da iyalansa, da kuma amincinsa([3]). Amin.  
TSAWATARWA KAN WAKA DA KAYAN KIDA
(التحذير من الغناء وألات الطرب)
Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz
Allah ya yi masa rahama
Lallai sauraron waka haramun ne, abun kyama, kuma yana cikin sabubban rashin zukata da kaikashewarsu, da kangewa su daga ambaton Allah, da kin yin sallah.
Kuma hakika mafi yawan ma’aboba ilimi sun fassara fadin Allah Ta’alah: "WA MINAN NAASI MAN YASHTARIY LAHWAL HADISI".
“Daga cikin Mutane akwai masu sayen zancen wargi …” zuwa karshen ayar, da cewa shine: Waka.
Kuma Abdullahi dan Mas’ud (R.A) yana yin rantsuwa cewa lallai:  shine: Waka.
Idan kuma ya zama a tare da wakar akwai kayan wargi, kamar sharewa, da tsinke, da kamman, da ganga, to haramcin yafi tsanani.
Wasu Malamai sun ambaci cewa, Wakar da ta hadu da kayan wargi to haramun ne da ijma’i.
Don haka, wajibin shine a kiyaye aikata hakan.
Kuma hakika ya inganta daga Manzon Allah (S.A.W) lallai shi ya ce: (S.AW) ya ce: "Wasu Mutane za su kasance daga al’ummata, suna neman halatta zina (Alhira) da alharir (ga Maza), da giya, da kayan kida".
Abun da ake nufi da (Alhira) shine farji na haram, wato zina.
(Ma’azif) shine: Waka, da kayan kida.
Ina maka wasiyya da sauran Mutane da sauraron Iza’atul Kur’anil karim, da shirin: Nurun alad darb, saboda a cikinsu biyun akwai fa’idodi mkasu girma, kuma sauraronsu aiki ne da zai shagaltar da kai daga sauraron waka da kayan kade-kade([4]).
TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI
(التحذير من شرب الدخان)
Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz
Allah ya yi masa rahama
Hakika dalilai na shari’a sun yi nuni cewa lallai shan tabar sigari yana daga al’amura na haram a shar’iance, wannan kuma saboda abinda shan tabar ya kunsa na dauda da cutarwa masu yawa, domin Allah Subhanahu bai halatta ababen ci da shag a bayinsa ba face wadanda sukakasance masu dadi masu amfani.
Amma wanda ya zama zai cutar da su; ga addininsu, ko duniyarsu, ko zai jirkita musu hankulansu, to lallai Allah ya haramta susu su, saboda Allah Mabuwayi da daukaka yafi tausayinsu akan kansu, kumashine Mai hikima Masani; cikin zantukansa da ayyukansa da shari’arsa da kaddararsa; saboda baya haramta abu saboda wasa, kuma baya halittar abu domin barna, kuma baya umurni face da abinda bayi suke da fa’ida acikinsa, saboda Allah Shine Mafi hikimar masu hikima, mafi jin-kan masu jin kai, kuma shine Masanin abinda yake dacewa da bayi, kuma mai amfani a gare su; a nan da can, kamar yadda Allah ya ce: "Lallai Ubangijinka Mai hikima ne Masani". Kuma Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Lallai Allah ya kasance Masani Mai hikima". Kuma ayoyin da suke dauke da wannan ma’anar suna da yawa.
Daga cikin dalilan Alkur’ani akan haramci taba akwai fadin Allah Ta’alah a cikin suratul Ma’idah: "Suna tambayarka me aka halatta musu? Ka ce: an halatta muku abubuwa masu dadi". Kuma a cikin suratul A’araf ya ce, ainda yake sifanta annabinmu Muhammadu: "Yana umurtarsu da kyakkyawa, kuma yana hana su abin ki, kuma yana halatta musu daddada, yana haramta musu dauda", har karshen ayar.
Sai Allah, a cikin ayoyin nan biyu masu karamci ya bayyana cewa bai halatta wa bayinsa ba, face daddadan abubuwa; wanda sune abin ci, da abun sha masu amfani. Amma nau’ukan abin ci da abin sha masu cutarwa ga addini ko jiki ko hankali, to lallai suna cikin munanan abubuwan da aka haramta.
Kuma hakika likitoci da wadanda suka san mecece taba da cutarwarta,sun yi ijma’i cewa, lallai taba tana cikin  abun sha masu cutarwa mai girma, kuma sun ambata cewa taba sababi ne cutuka masu yawa,kamar cutar kansa, da mutuwar farat daya (tsayawar zuciya) da wasunsu.
Kuma duk abinda ya kasance a haka, to babu makawa kan haramcinsa, da wajabcin kiyayarsa.Kumabai dace mai hankali ya rudu da yawan masu shan taba a Duniya ba, domin Allah Ta’alah a cikin littafinsa mabayyani ya ce: (S.AW) ya ce: "Kuma idan ka yi biyayya ga mafi yawan wadanda suke bayan kasa, za su batar da kai daga hanyar Allah, ba komai suke bi ba face zato, kuma sub a komai ba ne, face makaryata".
Kuma ya ce: (S.AW) ya ce: "Ko kana zaton mafi yawansu suna ji ko suna hankalta, su ba komai ba face dabbobi, A’a! sune suka fi bacewa daga hanya".
Don haka, Tabar sigari shanta baya halatta, ko sayar da ita ko ayi tijararta, saboda abinda ke cikin hakan na cutuwa mai girma, da munanan abinda take haifarwa.
Kuma abinda ya wajaba ga wanda yake shan taba (sigari) shine ya mayar da lamurransa ga Allah Ta’alah, yay i nadamar abinda ya gabata, ya yi azamar, ba zai koma mata ba. Wanda ya tuba da gaske, sai Allah Ta’alah ya karbi tubarsa, kamar yadda Mabuwayi da daukaka ya fada: "Kuma ku tuba zuwa ga Allah gaba daya –Ya ku Muminai-, domin ku samu babban rabo". Kuma Allah ya ce: "Kuma ni mai yawan gafara ne, ga wanda ya tuba, kuma ya yi imani, yay i aiki na kwarai, sannan ya shiryu". Kuma Annabi (S.AW) ya ce: "Wanda ya tuba daga zunubi, kamar wanda bashi da zunubi ne", Ibnu-Majah ya ruwaito.
Muna rokon Allah ya gyara halin Musulmai. Kuma ya tsare su daga dukkan abinda yake saba wa shari’arsa, Lallai shi Mai ji ne Mai amsawa.

([1]) MAJMU’U FATAWA WA RASA’LIL USAIMIN, (11/ 125-126).
([2])MAJMU’U FATAWA WA RASA’LIL USAIMIN, (12/ 308-309).
([3])MAJMU’U FATAWA IBNU-BAAZ, (4/ 210), a takaice.
([4])MAJMU’U FATAWA IBNU-BAAZ, (3/423).

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...