HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 21/Sha'aban/1440H
daidai da 26/AFRILU/ 2019M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ALIYU DAN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
KYAUTATA MA RAI DA HALITTU
(الإحسان إلى النفس والخلق)
Shehin Malami
wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy–Allah ya tsare shi- ya yi
hudubar juma'a mai taken: KYAUTATA MA RAI DA HALITTU,Wanda kuma
a cikinta ya tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Godiya
ta tabbata ga Allah Mabuwayi Mai yawan baiwa, ya yalwata ni'imarSa ga bayinSa;
a zahiri da badini. Masu imani da shi sukan kasance a gare shi masu godiya,
Kafirai kuma suna inkarin ni'imominSa. Kuma Ubangijinmu Ta'alah yana bada
baiwar falalarSa ko yaushe, kuma har abada. Kuma masu da'a basu iya tsayuwa da
cikakken da'arsa. Kuma masu sabo -don rashin godiyarsu- basu cutar da shi;
Shine Wadatacce da zatinSa da sunayenSa da sifofinSa, Madaukaki da darajarSa,
da buwayarSa da girmanSa. Kuma halittunsa a cikin kowace kyaftawar ido mabukata
ne a gare shi.
Ina
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin
tarayya, Mulki nasa ne, godiya tasa ce, Mai rinjaye akan bayinSa; dukkansu a
gare shi masu kan-kan da kai ne.
Kuma
ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne ManzonSa, kuma
zababbe daga cikin halittunSa.
Ya
Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka
Muhammadu da iyalansa da sahabbansa, salati da sallama masu dawwama, har zuwa
ranar tayarwa.
Bayan
haka
Ku
yi taqawar Allah Ubangijinku, domin saboda idan Mutum ya yi riqo da taqawa zai
rabauta da alkhairori, kuma zai samu mafi xaukakar darajoji. Wanda kuma ya
nisanci taqawa, tavewa da wulaqanci za su dabaibaye shi, kuma zai dulmuya cikin
ramukan azaba.
Ya
ku Musulmai
Lallai
addininku addini ne na kyautatawa; wato kyautatawa ga rai, da kyautatawa ga
halittu; saboda babu wani umurni a cikin addini ko hani, kuma babu wata shari'a
face kyautatawa ce ga rai, da kyautatawa ga halittu. Wannan kuma shi yake
lamunce wa Bayi samun sa'idar Duniya da ni'imar Lahira. Allah Ta'alah ya ce: "Allah
baya nufin sanya muku qunci, saidai yana nufin ya tsarkake ku, kuma ya cika ni'imominSa
akanku, tsammaninku za ku yi godiya" [Ma'idah: ]. Kuma Allah
Ta'alah ya ce: "Kuma Allah yana sani, kune baku sani ba" [Bakara:
]. Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Lallai
Allah yana umurni da adalci da kyautatawa da baiwa ma'abutan kusanci. Kuma yana
hani akan alfasha da munkari da zalunci. Yana muku wa'azi tsammaninku za ku
wa'azantu" [Nahl:].
Kuma har cikin
tsayar da haddodi da ukubobi waxanda ake yinsu ga mai laifi; a cikinsu akwai
alkhairi ga mai laifin; ta hanyar kange shi daga aukawa ga wannan
laifin (a karo na gaba) ko makamancinsa, da tsawatarwa ga wasu Mutane kan
aikata laifuka da haddodi, da kuma kankare wa masu laifin kuma masu savo zunubansu,
Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya faxa dangane da Mutumin da aka tsayar masa da haddi, a
zamaninsa: "Ina rantsuwa da wanda raina yake hannunsa, lallai shi a
yanzu yana cikin koramun Aljannah yana fantamawa a cikinsu" Bukhariy ya ruwaito shi, da Muslim daga
hadisin Abu-hurairah -رضي الله عنه-.
Kuma
tsayar da haddodin da Allah Ta'alah ya shar'anta, kyautatawa ne ga dukkan
al'ummah, ta hanyar kange zalunci da qetare iyaka da sharri ga al'ummar, da
kiyaye al'amarin tsaronsu, da zaman lafiyarsu da alfarmominsu, Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Haddi guda xaya da za a tsayar a bayan qasa, yafi alheri
ga Mutanen Duniya fiye da a saukar musu da ruwa na tsawon kwanaki arba'in" Ahmad da Nasa'iy da Ibnu-Majah suka ruwaito
shi daga hadisin Abu-hurairah -رضي الله عنه-.
Kuma mafi kyan
kyautatawa ga halittu shine tunkuxe ukubobin da ake qaddarawa, ta hanyar
yin aiki da hukunce-hukuncen shari'a; saboda ba a iya tunkuxe gamammun ukubobin
da suka sauka, face ta hanyar yin aiki da hukunce-hukunce na shari'a. Allah
Ta'alah ya ce: "Ka ce: Shine yake da iko, akan ya turo muku
da azaba daga samanku, ko ta karkashin kafofinku ko ya karkasa ku kungiyoyi;
sai sashenku ya xanxana wa sashe akuba, Ka duba yadda muke jujjuya ayoyi, da tsammanin
ko za su fahimta" [An'am: ].
An ruwaito
daga Zainab 'yar Jahsh -رضي الله عنها- ta ce: "Manzon Allah
-صلى الله عليه وسلم- ya taso a firgice, ya ce: Bone ya tabbata ga Larabawa dangane
da wani sharri wanda ya kusanto, A yau an buxe wani abu na ginin Yajuju da Majuju,
gwargwadon wannan, sai ya qulla casa'in, Sai na ce: Ya Manzon Allah! Shin za a halaka
mu, alhalin akwai Salihai a cikinmu? Sai ya ce: Idan dauxa ta yawaita!", Bukhariy
da Muslim suka ruwaito.
Qullin
"casa'in" wato, ya lankwashe manuniyar yatsarsa ta koma tushenta.
Idan dauxa
ta yawaita, shine idan kayan bugarwa da maye da giya da zina da luwadi suka
yawaita.
Sai ka yi
dubi -Ya kai Musulmi- zuwa ga girmar rahamar Allah a gare mu; ta yadda ya
shar'anta mana abinda a cikinsa akwai kyautata wa ga rayukanmu, kuma akwai kyautatawa
ga halittu; saboda Ubangijinku Mai gafara ne, Mai yawaita qaunar bayi, Mai
jin-kai, Masani, Mai hikima, Mawadaci, Mai karamci.
Yana daga MANYAN
ABINDA ALLAH TA'ALAH YA SHAR'ANTA, AL'AMARIN ZAKKAH, Wanda watan Ramadhana
mai albarka mai karamci yake tunatar da mu akanta, domin a cikin lamarin zakkah
akwai kyautata wa ga rai, da kyautata wa ga halittu, wanda Musulmi ya sani, da
wanda babu Mtumin da ya game sani da shi, face Allah Mai jin-kai.
Kuma ibadar
zakkah an gwama ambatonta da sallah, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma
ku tsayar da sallah, ku bayar da zakkah, kuma ku baiwa Allah rance mai kyau, kuma
duk abinda kuka gabatar ga rayukanku na alheri to za ku same shi a wurin Allah,
yana mafi alheri da girman lada" [ :].
Don haka, Zakkah
kyautata wa ce ga wanda ya bayar da ita; saboda albarka zata sauka a cikin
dukiyarsa, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma duk abinda kuka ciyar
na wani abu, to shine zai bada mayewarsa, kuma shine mafi alherin Masu azurtawa" [].
Kuma
zakkah tana kiyaye dukiya daga musibu, an ruwaito daga Umar -رضي الله عنه-, daga Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Da xai, dukiya bata lalacewa a tudu ko a teku, face
saboda hana zakkah", Xabaraniy ya ruwaito shi, a cikin littafin
Al'ausax.
Kuma an
ruwaito daga A'isha -رضي الله عنها-,
daga Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Sadaka ko kuma ya ce: Zakkah bata cakuxa da dukiya face
ta lalata ta" Xabaraniy ya ruwaito shi.
Zakkah
Musulmi yana kyautata wa kansa da ita, sai ya kare ta daga azaba, an ruwaito
daga Abu-hurairah -رضي الله عنه-,
daga Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Babu ma'abucin zinare da azurfa, wanda baya bayar da haqqinta,
face idan yinin qiyama ya kasance, an narka su kamar allunan wuta, sai a riqa
babbaka su a wutar Jahannama, ana qoqqona gefensa da fiskarsa da bayansa, duk
lokacin da aka je qarshe sai a sake dawo masa da su, a wani yinin da tsawonsa
shekaru dubu hamsin, har a yi hukunci a tsakanin bayi, sai ya ga hanyarsa, imma
izuwa ga Aljannah ko zuwa Wuta. Sai aka ce: Ya Manzon Allah! Ina labarin raqumi?
Sai ya ce: Babu ma'abucin raquman da baya bada haqqinsu, yana daga cikin haqqinsu
tatsansu a ranar da suka zo mashaya (don baiwa matafiya), face a ranar kiyama
an shumfuxa shi a sahara mai faxi madaidaiciya, a hali mafi tsoka, ba za a rasa
ko xan yaye xaya daga cikinsu ba, za su riqa tattake shi da kofatonsu, suna
cizonsa da bakunansu, duk lokacin da na farkonsu suka shige sai a dawo masa da
na qarshensu, a wani yini wanda tsawonsa shine shekaru dubu hamsin. Sai aka ce:
Ya Manzon Allah! Ina labarin shanu da awaki? Sai ya ce: Kuma babu ma'abucin
shanu da awaki wanda baya bada haqqinsu, face a ranar qiyamah an shumfuxa shi a
sahara mai faxi madaidaiciya, ba zai rasa wani abu daga cikinsu ba, suna
tunkurarsa da qahonsu, suna tattake shi da kofatonsu, duk lokacin da na
farkonsu suka shige sai a mayar masa da na qarshensu, a wani yini wanda
gwargwadonsa shine shekaru dubu hamsin" Bukhariy da Muslim suka
ruwaito shi, da wannan lafazin. Da wasunsu.
Mai bada
zakkah yana kyautata wa kansa ne ta hanyar ninninka lada, Allah Ta'alah ya ce: "Wanda
ya zo da kyakkayawa to yana da kwatankwacinsa goma" [].
Saboda kyakkyawa xaya ana ninka shi da kwatankwacinsa goma, har zuwa ninki xari
bakwai, zuwa ninki mai yawa, kamar yadda ya zo cikin hadisin Abdullahi dan
Abbas.
Kyakkyawa
a ranar Lahira babu wanda zai bada kyautarsa koda a makusanci ne.
Kuma
zakkah kyautata wa ne ga fakirai, kuma hakkinsu ne da Allah ya farlanta shi
akan mawadata.
Zakkah
tana daga zaman tare da tausayin juna da rahama da jin-kai da kyakkyawar alaka
tsakanin Musulmai, kuma rayuwa bata dadi kuma bata gyaruwa face a inuwar jinkai
da taimakakkeniya, kuma hakika Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya yi wasiya da al'amarin fakirai da miskinai da masu rauni,
kuma ya bayyana cewa, Allah yana bada nasara ne kuma ya bada arziki saboda su,
a inda yake cewa: "Ba a baku nasara a azurta ku, face saboda masu rauninku"
Bukhariy ya ruwaito shi, daga hadisin Sa'ad dan Abu-wakkas -رضي الله عنه-.
Kuma
Annabi -عليه الصلاة والسلام- ya ce:
"Ku nemi samun yardata a
al'amarin raunan Mutane, saboda ana taimakonku a azurta ku saboda masu rauninku"
Abu-Dawud ya ruwaito shi, da isnadi mai kyau, daga hadisin Abud darda'i -رضي الله عنه-.
saboda
Ubangiji -Mabuwayi da daukaka- yana tare da karyayyun zukata, masu tawali'u.
Kuma
fakirai za su yi husuma da mawadata akan hakkinsu da aka tozarta, an ruwaito
daga Anas -رضي الله عنه-,
daga Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Bone ya tabbata ga mawadata dangane da fakirai a ranar
kiyama, za su ce: Ya Ubangijinmu lallai sun zalunce mu hakkokinmu da ka
farlanta mana akansu, Sai Allah Ta'alah ya ce: Ina rantsuwa da buwayata da
girmana, zan kusantar da ku, kuma wallahi zan nesanta su"
Dabaraniy ya ruwaito shi a cikin littafin Assagir da Auwad.
Zakkah
Allah -سبحانه- ya farlanta ta a cikin ZINARE DA AZURFA idan suka kai nisabi,
kuma cikin nisabin kowanne daga cikinsu za a bayar da xaya bisa huxun xaya bisa
goma ( 1/40). Kuma nisabin zinare shine giram tamanin da biyar (85), ko abinda
ya kai qimarsa na kuxaxen takarda; sai ya bada zakkar wannan nisabin da abinda
ya qaru akan hakan.
Amma idan kuxinsa
ya kasance na takardu ne, to qa'idar ita ce a duk riyal xari ya fitar da riyal
biyu da rabi.
Kuma abin
kwalliya (na zinari) wanda aka taskance a cikinsa akwai zakkah, haka zinarin
kwalliya wanda ake amfani da shi shima akwai zakkah a cikinsa, idan ya kai
nisabi, a ingantacce zancen ma'abuta ilimi, saboda gamammun dalilai.
Nisabin AWAKI
kuma awaki arba'in ne (40), sai ya bayar da akuya xaya, duk abinda ya qaru
kuma sai ka nemi bayaninsa ta hanyar tambayar ma'abuta ilimi.
Nisabin SHANU
kuma shine shanaye talatin (30), kuma haka, za a bada tabi'ah.
Nisabin RAKUMA
kuma shine rakuma biyar (5) sai a bada akuya, duk kuma abinda ya qaru akan
haka, sai ka tambayi Malamai akansa.
Kuma KAYAN
KASUWANCI, DAGA KOWANE ABU, wanda aka tanade shi domin sayarwa da neman
riba, na filaye da motoci da wanin haka, akwai zakkah a cikinsa, to sai ayi
qima ga kayan sayarwan. Kuma duk abinda ya kai nisabi daga qimar sai a fitar da
xaya bisa huxun xaya bisa goman qimar, bayan shekara ta qare.
Kuma
zakkah tana wajaba daga ABINDA YAKE FITOWA DAGA QASA; na kwayan da ake
riqonsa a matsayin abinci, da dabino da zabib. Idan har ya kai nisabi sai ya
bayar da xaya bisa goma (1/10) idan aka shayar da shi, ba tare da wata wahala
ba. Amma idan aka shayar da shi da wahala, to za a bayar da rabin xaya bisa
goma (1/20), kamar yadda hadisi ya zo da hakan. Kuma NISABIN ABINDA YAKE
FITOWA DAGA QASA shine sa'iy xari uku (300), da sa'in Annabi -صلى الله عليه وسلم-, kuma gwargwadon sa'iy shine kilo biyu da kamar giram arba'in
(2, 40g).
Kuma
abinda ba zakkah ba; na abinda Musulmi yake ciyarwa na wajibi da mustahabbi, za
a bayar da lada ga Musulmi akansa, kuma masu tsere suna yin tsere domin samun
alherorinsa, musamman kuma a cikin watan Ramadhana mai albarka, an ruwaito daga
Abu-hurairah -رضي الله عنه- , daga Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Babu wani da zai yi sadaka da dukiyar halal, kuma Allah
baya karba sai halal, face Mai rahama (Allah) ya dauke ta da hannunsa na dama,
koda dabino ne; sai ta bunkasa a hannun Mai rahama, har ta kasance tafi dutse
girma, kamar yadda dayanku yake girmar da 'dan rakuminsa"
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma an
ruwaito daga Umamah -رضي الله عنه-,
daga Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Aikin tallafi yana kare mummunan qaddara, kuma sadakar
voye tana yaye fushin Ubangiji, kuma sada zumunci yana qara tsawo da albarkar
rayuwa" Dabaraniy a cikin littafin Alkabir ya ruwaito shi.
Kuma an
ruwaito daga Abu-hurairah, daga Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: e: "Sadaka tana yaye fushin Ubangiji, kuma tana tunkude
mummunan mutuwa".
Kuma an
ruwaito daga Aliyu -رضي الله عنه-,
daga Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: e: "Ku yi gaggawar sadaka; domin bala'i baya tsallake ta".
Sai ka yi
dubi -Ya kai Musulmi- kan karamcin Allah da baiwarSa da falalarSa; yadda ya
bamu dukiya mai tarin yawa mai faxi, kuma ya yarda a bayar kuma a ciyar da
kaxan, sannan yake bada sakamako mai girma akan hakan.
Kuma da
Mawadata za su riqa fitar da zakkar dukiyarsu, da a cikin Musulmai ba za a samu
faqiri ba, Allah Ta'alah ya ce: "Ka ce wa Bayina da suka yi
imani: su tsayar da sallah, kuma su ciyar daga abinda muka azurta su, a asirce
da kuma a bayyane, gabanin yinin da babu kasuwanci a cikinsa ya zo, kuma babu
wata soyayya" [ : ].
Allah
ya mini albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma, ,,,.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA
TA BIYU
Godiya
ta tabbata ga Allah Ma'abucin girma da karramawa, da buwayar da ba cin mata.
Ina yin yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa akan ni'imominnSa da muka sani da
waxanda ba mu sani ba; domin baiwa da ni'ima nasa ne.
Ina
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake bashi da abokin
tarayya Mai tsarki Mai amintarwa.
Kuma
ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa Mai
qira zuwa ga dukkan alheri da aminci.
Ya Allah
ka yi daxin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu, da
iyalansa da sahabbansa masu karamci.
Bayan
haka
Ku ji
tsoron Allah Ubangijinku; ta hanyar kusantarsa da kyawawan ayyuka, da nisantar
munana; domin ku rabauta da dukkan alkhairori a cikin rayuwa da bayan mutuwa.
Ya
ku Mutane
Lallai
Allah ya tsawatar da ku daga makiyinku; wato Shexan, wanda yake kange Bayi daga
dukkan alheri, kuma yake qira zuwa ga dukkan sharri, domin mabiyansa su
yawaita, kuma ya vatar da mataimakansa; sai ya ce: "Ya
ku Mutane, lallai alqawalin Allah gaskiya ne, don haka kada rayuwar Duniya ta
ruxe ku, kuma kada mai ruxi (Shexan) ya ruxe ku daga Allah * Lallai ne Shexan
maqiyi ne a gare ku, sai ku riqe shi maqiyi, kuma lallai yana qiran qungiyarsa
ne domin su kasance ma'abuta wutar sa'ira" [ : ].
Kuma
lallai ta'addanci mai raxaxi wanda ya auku, wanda ya nufi ofishin wasu jami'an
tsaro, a ranar lahadin da ta gabata aiki ne na savo kuma varna ne a bayan qasa
kuma laifi ne mai girma, kuma ficewa ne daga jama'ar Musulmai da kuma
shugabansu, kuma qoqarin kaseh rayukan da basu ji ba kuma basu gani ba, kuma
ta'addanci ne ga al'amarin tsaro da zaman lafiyar wannan qasa, kuma yaxa
firgici ne da tsoro (a zukata).
Kuma mun
kasance haqiqa muna fatan waxannan wanda Shexan ya qawata musu ayyukansu su xau
izina daga ayyukan ta'addancin da suka auku a baya, sai su komo zuwa ga daidai,
su bar ayyukan ta'addanci. Amma sai gashi sun bayyana dogewa akan ayyukan
varna.
Kuma duk
wanda ya yaqi Allah da ManzonSa kuma ya tafi a bayan qasa yana varna, to lallai
bai cutar da kowa ba face kansa.
Kuma wajibi ne su yi tunani kan abinda
ta'addancin yake haifarwa; Shin zaman tashin hankali suke son kawowa wanda za a
kasa yin sallolin juma'a dana jam'i?
Shin
abinda suke nufi shine hautsinin da za a riqa zubar da jinane, a kuma halatta
haram a kekketa alfarma?
Ko suna
nufin kawo yamutsin da za a riqa kwashe dukiyoyi, ana rusa abinda aka mallaka?
Ko wanda
yake aikata hakan, so yake yi ya kashe kansa, alhalin Allah ya tanadi narko ga
wanda ya kashe kansa a cikin faxinsa: "Kuma kada ku kashe
kanku, lallai Allah ya kasance Mai rahama akanku * Kuma duk wanda ya aikata
haka, da ta'addanci da zalunci, to lallai za mu shigar da shi wata wuta" [ :
].
Allah ya
tsare mu daga fitina masu vatarwa, kuma ya tsare mu daga faxawa wuta. Annabi -صلى الله عليه وسلم-, ya ce: "Wanda ya kashe kansa da wani makami, to makaminsa yana
hannunsa, yana sossoka shi a cikinsa, a cikin wutar Jahannama yana mai dawwama
a cikinta har abada", Bukhariy
da Muslim suka ruwaito shi, daga hadisin Abu-hurairah -رضي الله عنه-.
Ya ku
Bayin Allah!
"Lallai
ne Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan Annabi, Ya ku wadanda suka yi
imani ku yi salati a gare shi, da sallamar aminci"
[Ahzab: 56].
No comments:
Post a Comment